Breaking News

Tabarmar Kashi Book 1 Page 31-32

 


Page 31




       Da hanzari sajjad ya tari numfashinsa,don bayason yace komai kada al'amuran su qarasa jagulewa


"Please toufeeq Calm down,don't make harsh words" bai ko waiwayo ba ko ya saurareshi ba ya tako zuwa gabanta,ya bada kusanci sosai a tsakaninsu irin wanda bai taba yi ba. Ranqwafawa yayi yayi mata rumfa saman kanta yana dubanta


"Nawa ne kasonki?!" Ya fada da wata irin kakkausar murya. A birkice take kallonsa,sosai maganarsa ta daketa,sai yanzu ta fahimci inda ya sanya gaba ma gaba daya,yana nufin wani ha'inci ta qulla ko ko meye?,kamar yasan me take tunani saiya sauqaqe mata ta hanyar sake bayyana mata abinda yake nufi


"Nace nawa ne share dinki?,tsakanin kawo ma'aikata da sauran ayyukan!,nawa kika tsara samu!,nawa kika samu!,ki gayamin zan ninka miki,amma ki fita daga rayuwarmu!" Duk da cewa bata shirya zubda hawayenta ba amma ta gagara riqesa,a take ya zarto daga idanunta ya sauka saman lallausan fuskarta da bata iya riqe komai ma ballantana ruwan hawaye saboda santsi da sulbinta,ta kafeshi sosai da ido kamar wadda ta warke daga ciwon makanta,cikin matsanancin fushi tace


"wanne irin mutum ne kai mara kirki?,mara iya mu'amala?,wanda baisan kima da martabar dan adam ba?,me yasa dukka zancanka kudi!,me yasa kake hangen kudi sune gaba da komai?,kana tunanin aiki daku na nufin in zama baiwa?,ko mara 'yanci?,ko kuma aiki daku na nufin zan mallaki wata dukiya?saboda kun mallaki yanke talauci?,Mr Muhammad.........idan baka sani ba yau ka sani,banyi aiki daku bisa radin kaina ko kuma don ina nema ba.....nayi aiki daku ne bisa dole da kuma takura neman alfarma da kuma ganin kimar yaaya na, karamcin mahaifinka kuma ya zama silar wanzuwata a nan gurin......baka da matsayin da zan nema sa hannunka akan ayyukan kamfanin nan,duk abinda kake tunanin na aikata.....yes na aikata din,na samu kaso me tsoka wanda hankali bazai dauka ba,na tara arziqin da yafi na mansa musaa dukka a jikinku,do your worst,I don't care or fear......ba dai dukka taqamarka kora ga ma'aikaci ba?,zaka iske resigning letter dinku a wajen sameera,ka riqe tsiyarka ka bawa wanda kaga dama" ta qarasa fada kuka sosai yana qwace mata,sannan ta soma fita daga hall din da sassarfa kuka na sake qwace mata.


              Da sassarfa sajjad yabi bayanta shi da mr hamza,saidai cikin rashin sa'a ta rufe office din,a yanayin da take sun tabbatar ba zata sauraresu ba,sai suka barwa miss sameera dake tsaye saqon idan fa bude ko tazo fita don Allah kar ta barta,ta tsaidata ta sanar dasu.


             A office ya sameshi yana kai kawo,ya cika ya batse kamar zai fashe


"Burinka ya cika,hankalinka kuma ya kwanta" sajjad ya fadi shima cikin bacin rai


"Stop sajjad,don't aggravate my anger,bakaji me ta fada bane?,I will surely punish her" ya qarasa fada yana dukan bayan kujera da hannunsa a zafafe. Kallonsa kawai sajjad yakeyi,yama rasa abun fada,wanne irin tashin hankali ne haka suka tashi dashi yau,sai kawai ya zaro wayarsa ya fara dialing number Dr.


             Tana kuka tana rubuta resigning letter din,bawai tana kuka kan barinta aiki bane, a'ah,tozartata da yayi a gaban mutanen da suke ganinta da kima da mutunci,maganganun daya gaya mata,wanda shine mutum na biyu a duniya daya taba gaya mata magana masu zafi irin haka. Ta kammala rubutawa kai tsaye ta turawa sameera,tace bayan ta tura musu a rubuce tayi printing as hard copy,ta riga ta yanke har abada ita da companyn,bama iya kamfanin kadai ba,duk wani aiki da yayi kamanceceniya da wanann ta barshi har abada.


          Da hanzari take tattara dukka wasu kaya da suke da alaqa da ita tana hadasu a wata jaka,ta taka zata cire wata calendar dinta kanta yayi mummunan sarawa,ta koma da baya babu shiri ta dafe kanta da hannayenta biyu tana kiran sunan Allah,idan batayi wasa ba alamu sun nuna ciwon kan da taketa gujewa motsawarsa a yau zai motsa din. Batason ciwon ya sameta a nan,don haka ta bude qofar,ta leqa ta kira sameera. Yanayin da taga uwargidan nata ya sanya hankalinta tashi,nuni tayi mata da iya kayan data samu cirewa ta miqa mata key tace ta saka mata a mota. Sameeran na fita ta miqe da qyar,ta yafa mayafinta ta zura takalminta ta taka a hankali tana ficewa daga office din,zuciyarta na karyewa,wani sashen na zuciyar tata tana ban kwana da dukka abinda ya shafi MT JARMA,bankwana na har abada.


_uhmmm,ko shin da gaske bankwanar ne?,ko kuma akwai sauran kallo?,masu karatu,ku gyara zama da kyau,akwai fa sauran kallo,zamu shiga gaba ta biyu na labarin,gaba me matuqar muhimmanci,muje zuwa_??????????????????????????????????????????



Da kallon mamaki maama kin bita sanda ta shiga gidan


"Ke kuma me ya faru na ganki a gida a irin wannan lokacin?" Idanunta fal da hawaye da taketa qoqarin shanyewa tace


"Ba komai maama"


"Qarya kike ban yarda ba" ta fada tana tattara hankalinta a kanta tare da barin duk abinda takeyi. Hawaye ne ya zarto a fuskar sãahar din,tasa bayan hannunta ta share


"Na ajjiye aiki maama" fuska tadan baata kadan


"Dalili dame?" Kai kawai ta shiga girgizawa,bakinta ya kasa furta komai,tana jin daci da ciwon abinda yayi mata har saman harshenta,ga kanta da yake sara mata sosai kamar zai rabe gida biyu


"Jeki,Allah ya kyauta" maama ta fadi saboda yadda taga ta gaza furta komai,koma meye tasan zataji idan yayunta ko afifa sukazo.


          Komai ta zube a qasan daki ta isa gado ta kwanta rub da ciki tana fashewa da kukan da takeson saki tun dazun, idanunta a lumshe tana bitar maganganun daya yayyaba mata,tayi nadama da dana sanin sanin kamfanin ma gaba daya bare wasu mutane dake da alaqa dashi.


              Sai data shafe kusan awa daya sanann ta laluba magani tasha, tayi kuma sallar azahar don tasan zaiyi wuya batayi bacci ba,idan kuma tayin lokacin yana iya kubce mata. Kamar yadda ta zata din kuwa,lokaci kadan baccin yayi awan gaba da ita,saidai dukka cikin barcin ba komai sai mafarkai,wadanda dukka toufeeq ne a ciki da tarin cin mutunci da cin zarafinsa a gareta.


             Knocking din baaba rabi ne ya tayar da ita


"Hajiya tace ki fito hakanan kici abincin rana"


"To" ta amsa mata,ta sa hannu ta shafi fuskarta,tana tuna yadda ya zabga mata mari a mafarki,kwatan kwacin marin da ta taba ji ya zabgawa wata,kai ta girgiza ta miqe a hankali ta wuce bandaki. Alwala ta dauro,sannan ta dawo ta cire kayan jikinta. Wata sof cotton shirt ta saka me gajeran hannu royal blue,me adon furanni da gold colour,sai spaghetti skirt daya dace da rigar,tasa comb ta sake gyara gashinta daya hargitse saboda baccin da tayi,ta qara turare a jikinta ta dauki wayarta dake da tarin miscall ta kashe ba tare data tsaya duba kiran waye da waye ba,ta tabbatar dai harda kiran dan anace mahmud a ciki.


             A parlor ta samesu,maama da baaba rabi dake gyara freezer din parlor din


"Barka da fitowa farar d'iya" ta fada tana murmushi


"Barka baaba rabi,ya aikin?


"Alhamdulillah "


"Ma sha Allah " ta fadi tana qarasawa kusa maama ta zauna,wadda har yanzun binta take da kallo


"Me za'a kawo miki?" Baaba rabi ta tambaya


"Barshi baaba,zan dan huta ne kadan sannan naci abincin,zan zuba da kaina" ta amsa mata tana daukar remote ta canza channel.


          Bayan wucewar baaba rabin kallonta maama tayi


"Kunyi waya da yayanki ne?" Saida gabanta yadan fadi,tasan yaaya muhyiddeen take magana a kai tabbas,batason ko sau daya ya roqeta ta koma aikin nan,don ba zata iya ba muddin wannan mutumin yana a cikin kamfanin


"Bamuyi ba,ko ya kira din inajin bacci nake a sannan" kai ta kada


"Me ya sanya kika ajjiye aiki sãahar?" Shuru ne ya biyo baya na 'yan sakanni,tanata qoqarin hadiye bacin ranta sannan ta motsa bakinta


"Bazan iya ba maama,dansa bashi da kirki sam,baya ganin kima da girman kowa,duk wata mace dake aiki a kamfanin kallon baiwa yake mata,ko wata mara daraja da batasan martabar kanta ba"  shuru maama ta danyi sanann ta numfasa


"Amma dai kinsan qarfe daya baya amo ko?,kuma ko meye halin mutum sai k........." Qarar wayarta ya katse mata maganar,sai t maida hankalinta a kai ta daga wayar ta sanyata a free.


          Dr mamman girema ne,wanda kafin su gama wayar sun sanya sãahar din cikin tunani,tabbas inda dukka maza irin mahaifinta ne,su kuma mata duka zasu kasance kamar mahaifiyarta ba ko tantama da ba'a samu mutuwar aure ba,koda an samu din ma saboda sabanin da baya wucewa tsakanin bayi,to zaiyi matuqar qaranci.


             Tuwon alkama yace yanaso miyar danyar kubewa,batason ta zauna tayita zaman tuna mutumin da a wajenta bashi da wani amfani sam,banza ma ta fishi,don haka sai ta wuce ta debi abincinta taci,tana kammalawa ta shiga kitchen da kanta ta dorawa abban nata tuwon.


           Tunda akayi sallar magariba taji yaa muhyi din tare da abba suka shigo gidan ta qule a daki taqi yarda ta fito,saidai ana gama sallar isha'i saiga maama da kanta


"Ki dauki abincin can ki kaiwa abbanku,zan shiga wanka" hakanan ta miqe jiki a sabule,ta fidda hijabinta ta maida gurbinsa da dan qarami ta fito ta debi kayan abincin ta wuce sassan Dr mamman.


           A ladabce ta zauna ta gaidasu dukkansu,don yau kafin ta fita basu hadu da abban ba,ta zauna sosai ta fara serving nasu duka su biyun da suketa tattaunawa akan harkokin da suka shafi kasuwancin da suke na hadin gwiwa a tsakaninsu. Ta ajjiye musu komai tana shirin miqewa abba daya gama wanke hannunsa yace


"Dawo ki zauna mana ummin abba" murmushi kadan tayi,ta dawo ta zauna din,sai da ya fara cin abincin sannan yace


"Me ya faru ne yau a MT JARMA?" Kanta ta sunkuyar tana jin rauninta yana dawowa,kamar yanzun abun yake faruwa,amma dole ta bude baki tayi magana da harshen da zasu fahimceta


"Na ajiiye aiki yau abba,ku  yimin afuwa abba kai da yaa muhyi na rashin neman sahalewarku kafin aiwatar da hakan,abun yazo a gaggauce ne,sannan kuma a gabar da bazai bada damar yin hakan ba"


"Me ya faru?" Abban ya sake jefa mata tambayar. Bata rufe komai ba ta zayyane musu,tun haduwarsu ta farko har zuwa abinda ya wakana yau din. Ta qarashe maganar tana hawayen takaici.


          Ga mamakinta sai taga abban ya saki murmushi yana girgiza kai


"Dake dashi dukka quruciya ce take damunku da kuma zafin kai,tare da wasu memories da suketa hunting rayuwarku,shikenan dai,bakin alqalami ya riga ya bushe,dr jarma ya kirani da kansa,yace bazai tilastaki ba akan ajjiye aiki da kikayi,yace a baki haquri a madadinsa da dukka ma'aikatan,sannan ya tura kudi a baki saboda hobbasar da kikayi kika daga kamfaninsa zuwa matakin gaba,kika gyara matsalar da suke fuskanta kaso sittin cikin d'ari" ya qarashe fadi yana duban fuskarta. Batace komai ba sai kai data girgiza,taji dadi da bai nema alfarmar lallai ta koma ba,don bataso ya roqeta abinda ba zata sake iyayi masa shi ba.


"Dama aiki ba dole bane,aure ne dole" abban ya sake fadi,maganar data bugeta sosai,ta kuma sakata dago kanta da sauri ta kalli abban,shima idanunsa yana kanta,ya jinjina kai alamun tabbatar mata da hakan


"Tunda taqi tsayawa ta fahimci kowa abba bazaiyiwu taci gaba da zama babu auren kuma ba aikin ba,Allah baya barin bawa babu aikin yi,akwai irin aikin da takeso din abba,idan na dawo daga tafiyar nan ta wata daya zuwa biyun nan zan applying mata" kai ya sake jinjinawa yana tsame hannunsa daga tuwon


"Banqi ta taka ba,amma duk da haka ta maida kai ta fidda miji,saboda lokaci tafiya yakeyi,kuma har yanzu ke din yarinya ce qanqanuwa ballantana kice kin girmi yin aure a yanzu". Gaba daya babu abinda maganganunsu sukayi sai dagula mata lissafi,dan ciwon kan data samu ya ragu sosai ya dinga qoqarin dawowa saboda damuwa,ga gidan babu kowa bare ta samu me debe mata kewa,tanaso tayi magana da anty farheen to amma tasan tabbas yaa muhyi yana gidan,don tafiyar tasa sai zuwa wani satin,sai kawai ta hada kayanta a washegari tabi afifan nata zooroad.


            Ranar da taje qin cewa afifan komai tayi,itama bata matsanta ba sukaci gaba da hutunsu,har sai data huce,ranar suna ta raka afifa gyaran farce da fuskarta,suna hanya tana driving ta bata labari. Sosai afifa bataji dadin ajjiye aikin ba,duk da itama taji ba dadi akan yadda abun ya faru tsakaninta da toufeeq din,saidai itama ta gaya mata


"Ba kowanne namiji ke iya fuskantar mace ya bata uzuri ba,ya kuma banbance rashin kunya da tsaiwa akan haqqinta ba,bare mutum irin MT da Allah ya yiwa baiwar kyau kudi da ilimi da kwarjini....."


"To hell with his kudi da kwarjinin,ya dauka ina cikin shirgin wawayen 'yammatansa ne da zan dauki irin wannan?,ki daina yabonsa please kina batamin rai afifa.....bakisan wayeshi bane,saboda baki taba mu'amala dashi ba,he was arrogant beyond belief,good look don't always signal kindness" dariya afifa tayi


"Wato kin fahimci kyansa ya janye hankalina sosai ko?"


"chapter close a beg" yatsunta biyu ta sanya tayi signal na zipping bakinta,bata kuma sake cewa komai din ba,sai suka shiga wata hirar ta daban.


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


VIP????

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????


*H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

https://arewabooks.com/u/huguma



Page 32



*********K'arfe kusan takwas ne na dare,saman titin dake wadace da fitilu yake tuqin yau da kansa,kuma shi daya,abinda ba kasafai yake faruwa ba. Sanye yake da wata maroon and golden hoodie captan abaya na maza saqar qasa turkiyya,dogon hannu gareta,ya saki hular a bayansa,hakan ya bawa kyakkyawar fuskarsa damar fitowa sosai,cike da wannan turbunewar da kuma rashin fara'a daya zame masa dabi'a.


          Kiran dr jarma ne ya fito dashi,don yana zaune shida fadeela a part dinsa suna buga game data tubure itakam yau tare zasuyi,da qyar ya lallabata ya maidata gurin nanny dinta sannan ya fito,tare da alqawarin zai dawo da wuri su qarasa. Baisan kiran na meye ba,amma alamu sun nuna a gaggauce yake neman nasa.


            Cikin rukunin gidajen dake sharada NNDC QUARTER,mayalwacin layin dake shimfide da kwalta da kuma fitilu a jere reras,kowanne gini dake layin abun kallo ne,wannan yana wane wancan,a haka yaci gaba da tafiya bayan ya ragewa motar gudu,da alama ya kusa isowa gidan daya nufaci zuwa.


            K'ofar wani mansion house dake dauke da ginin bene hawa biyu ya tsaya,ya danna hon na farko, kafin yayi na biyu security din dake sanye da baqaqen uniform da suke kama dana police ya buda masa qofar,a nutse ya sanya hancin motar zuwa cikin makekiyar harabar gidan. Biyu daga cikin security dinne suka bude masa qofar cikin girmamawa da qauna me tarin yawa suke gaidashi,ya amsa musu yana rufe motar,ya jefa key din a aljihun rigar tasa,ba tare daya ciro hannuwan nasa ba yaci gaba da takawa zuwa cikin kamar maijin sanyi. Bawai sanyi yakeji ba,kawai yana jin wani iri ne da yanayin yadda dr din ya kirashi.


           Kai tsaye ya kutsa zuwa hanyar da zata sadashi da falon gidan,ya tsaya yayi knocking,duk da cewa gidan mahaifinsa ne,amma hakan ba sakashi shiga kai tsaye ba,duk sanda yazo gidan sai ya tsaya ya nemi izini don cikar dokar addinin musulunci.


          K'ofar aka bude,labiba ce,sanye da wata doguwar riga da tasha tattara daga qirji,ta bude daga qasa sosai,kanta cike da qananun kitso da gashin doki,sao farata zaqo zaqo data sanyawa hannayenta tamkar wata dabbar daji,amma ita a gurinta hakan ado ne na wayayyun mata masu aji(wallahi wallahi wallahi muddin kinsan daya daga cikin wadan nan abubuwan dabi'unki ne to kiyi gaggawar dainawa tun kina raye kina da lafiya,qarin gashi haramunne koda mijinki zaki yiwa,ko meye zaki sanyashi a kitsonki a qara miki tsahon gashinki haramunne,hakanan saka farce shima haramunne,haramunne haramunne,koda faratan hannunki bai halasta ki tarasu ki barsu baki yanke ba,haramunne barin farce yayi zaqo zaqo bare har kije ki biya kudi a dora miki shi,kina 'yar adam amma kinason kiyi kamanceceniya da dabba?,suke da wanann siffa ta akaifa ko qumba masu tsaho,acikin tsarki na addinin musulunci,bansa aske gashin maara dana hammata harda yankan farce sai yiwa yara shayi(kaciya), ma'aiki baya taba fadar magana wallahi wallahi ta tashi a banza,idan yace abu haramunne mu yarda mubi,ba wani kwaskwarima da malaman zamani masu son zuciya zasuyi ma maganarsa ta koma halak,haram haram ce,halal halal ce,Allah yasa mufi qarfin zakatanmu????????).


             Sau daya tak ya kalleta ya kauda idanunsa,sannan ya gewayeta ya sanya jikinsa zuwa falon


"Sannu da zuwa yaa toufeeq" ta furta tana bin bayansa hadi da binsa da wani mayen kallo,bai amsa mata ba yaci gaba da kutsa kai,masu aikin dake kai kawo a parlor din suka yi masa barka da zuwa sannan suka kauce daga gurin.


"Abban yana samansa" ta fada cikin yauqi da kwarkwasa,wanda sau tari wani lokaci ita kanta batasan hakan tana faruwa ba,tsabar yadda zuciyarta ne ta afu ason samun soyayyarsa.


"Ya toufeeq" ta kira sunansa,waiwayowa yayi ya watsa mata wani irin kallo daya takura zuciyarta guri guda ya sanyata harbawa,saita duqar da kanta qasa tana wasa da yatsunta


"Yaa toufeeq,am sorry for what happened last time,tsautsayi ne in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba" qaramin tsaki yaja,yayi gaba ya fara takawa zuwa stairs din dake cikin falon.


         Binsa tayi da kallo har ya bacewa ganinta,hannuwanta ta yarfar kamar zata saki kuka,ta tsani wanann miskilancin nasa,yana matuqar dafaata da dagula mata lissafi,sai ta koma ta zauna saman daya daga cikin qayatattun kujerun falon tana dafe da kanta,dai dai sanda daya daga cikin masu aikin gidan ta qaraso cikin rusunawa


"Ranki ya dade,abincin daren,na kammala fa"


"Dalla matsa ki ban guri" ta fada mata cikin tsawa tana jan tsaki


"Allah ya baki haquri" ta fadi tana janye jikinta daga gurin tunda ragowar mutuncinta,tasan tsaf zata iya ci mata zarafi,ta juya ta koma cikin kitchen din,cikin ranta tana Allah ya qara da yadda toufeeq din yake wajiga rayuwarta. Sake daga kai tayi ta dubi stairs din,gurin mommynta takeson zuwa,to amma ta sani,tunda ya iso ko ruwan giya tasha bata isa hawa saman ba har sai ya sauko,saita kwashe qafafunta ta mayar saman kujerar ta kwanta tana dakon fitowarsa,a ranta tana tsara yadda zasu kebe ita dashi ko na minti talatin ne kacal.


           Da sallama a bakinsa ya shiga falon bayan dr yayi masa izini,tana duqe tana zuba masa lemo a cup,kakkaurar mace wankan tarwada me tsaho da jiki,wanda kana dubanta zakasan ba hausa fulani bace.


          Da fara'a a fuskarta ta dago tana cewa


"Wata sabon gani,kaine yau a gidan namu?" Dan binta yayi kadan da kallo yana mamakin furucinta,A GIDAN NAMU,sai baice mata komai ba,ya taka a nutse ya isa daura da mahaifinsa,kwata kwata baisan me yasa bai taba jin matar ko daukarta da wani daraja ba,duk da tsahon shekarun data kwashe tana amsa sunan MATAR MAHAIFINSA,sannan dai dai da rana daya bata taba gwada masa wani hali ba,amma haka kawai take takenta baiyi masa ba.


"Ina ka baromin kishiyata?" Ta sake fada cikin fadada fara'arta,maimaikon ya amsa mata tambayarta sai ya buge da fadin


"Barka da dare"yayi furucin kamar ba da ita yake ba,yana maida dubansa ga mahaifinsa,cike da kulawa tace


"Barka kadai Muhammad,ya ayyuka,ya akaji da kacaniyar jama'a" ta tambayeshi cikin nuna kulawa.


"Alhamdulillah" ya amsa mata a taqaice,sam bata damu ba,don ta saba da irin wanna halayyar tasa,saita fara kwashe kayan abincin dake gurin tana dubansa


"Me za'a kawo maka?" Kai ya girgiza,baisan sai yaushe zatayi fushi ba ta daina tambayarsa abinda zaici ba duk sanda yazo gidan,bayan tafi kowa sanin baya cin abinci daga hannun kowa kuma a ko ina ba,sai a wasu kebantattun hannuwa da gurare.


"Alhamdulillah,basai na saki hidima ba" murmushi ta kumayi


"A'ah kace dai ba zakaci ba kamar kullum"


"Yi tafiyarki ki rabu dashi,kada Allah yasa yaci din" Dr ahmad ya fada,wanda tunda ya shigo lemonsa yake kurba yana kuma kallon labarai daga NTA network news.



"Zaici ne wataran ai" ta fada da dariyarta tana yin gaba. Sau daya tak kalmar ta shiga kunnensa amma ya gama fahimtar abinda take nufi ba tare da ita tayi zaton zai fahimta din ba.


"Barka da warhaka" ya fada cikin girmamawa,sauke qafafunsa dr ahmad yayi qasa yana ajiye cup din hannunsa gami da bashi amsa duka lokaci guda


"Kai ya kamata a yiwa barka ai,irin wannan aikin da kayi na cin zarafin yarinyar dana nema alfarmar a bani aronta,ka kuma sanya tabar aiki lokaci guda,to kaga kai ka cancanci a yiwa barka" bai barshi yace komai ba dr din ya tsinke da fada,ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba,daga qarshe yace


"Ka ajjiyemin komai daya shafi company dina kaima na sallameka,na gode da iya taimakon daka bani,ka koma bakin taka dukiyar" daga haka ya miqe ya wuce bedroom dinsa yana bar masa falon.


           Kasa motsawa yayi daga gurin,yanajin tamkar ya hadiyi zuciya ya mutu,tsahon tasowarsa bayan shudewar matsalolin da suka sanyo kai a rayuwarsu tun zamanin quruciyarsa,bazaice ga lokacin daya zauna yayi masa fada me zafi irin haka ba,sai yanzu?,a dalilin yarinyar?,ya jima a gurin sannan ya miqe a nutse yana sauka qasan,fuskarsa cike fal da fushi da kuma bacin rai,ta zama silar gurbata kyakkyawar alaqar dake tsakaninsa kenan da mahifinsa lokaci guda?.


            Suna zaune a falon,hajiya mansura(matar dr ahmad jarma) tare da labiba,ganin yazo zai wucesu ba tare daya kalli kowa a cikinsu ba,kamar ma baisan da zamansu ba hajiya mansura ta magantu


"Harka sauko?,kun gama kenan?" Da so samu ne yayi wucewarsa,to amma ko babu komai ita din mata ce ga mahaifinsa,zata iya cin darajar mahaifin nasa koda qanqani ne


"Eh" ya amsa bayan ya waiwayo yana dubanta hannayensa zube a aljihun rigarsa. Kwarjini ya mata sosai,tadan daburce amma saita maze ta hanyar sakin murmushi


"Ammm,tafiyarku daya da qanwarka,nace ko ta bika saiku tafi tare?" Ido kawai ya lumshe wanda ke nuna ya amsa kenan,ya juya ya fita a falon.


          Da mugun gudu ta sauko daga saman kujerar,ko ina na jikinta yana rawa


"Mommy,ki bada kayana gobe usaina ta kaimin"


"Ki tsaya ki tafi da kayarki,goben akwai inda zan aiketa"


"Tsaf zai tafi ya barni idan na tsaya jiran hada kaya" tayi maganar a lokacin ma takai bakin qofa.


         Lokacin data isa tuni ya tayar da motar,abinda ya tabbatar mata inda ta qara wasu mintuna saidai tazo ta tarar da wajen wayam. Gaba ta bude zata shiga,cikin kaushin murya yace


"Koma baya!" Jiki a sanyaye ta maida murfin ta rufe,ta koma bayan ta zauna,ranta ba haka yaso ba,taso zaman kusa dashi,ta yadda duk maganar da zatayi masa ta tafi cikin kissa da kuma jan hankali.


"Yaa toufeeq" ta kira sunansa sanda suka dauki hanya sosai


"I don't want to hear anything from you har mu qarasa gida,if not kuma,i will drop you" kallonta ta maida ga titunan da suke wucewar,yadda suka dauki shuru saboda daukewar qafa da ababen hawa sakamakon dare daya fara yi,marufar asirinta yin shurun,don tasan kadan ne daga aikinsa ya sauketan kamar yadda ya furta. Ranta ya quntata sosai,dukka wani plan nata ya rushe,manufar da yasa tacewa Mommy tayi masa magana ya sauketa ma ya tashi a banza.


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


VIP????

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????

[22/08, 4:31 pm] +234 907 013 9442: *H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

https://arewabooks.com/u/huguma

No comments