Breaking News

Tabarmar Kashi Book 1 Page 29-30

 


Page 29




          Duqawa yayi yayi kissing goshin fadeelan,ita kuma tayi masa addu'a kamar kowanne lokaci


"A dawo lafiya abby,Allah ya tsareka ya bada sa'a" wannan addu'ar yana ji da ita,yakanji kamar ta fita ne daga bakin mahaifiyarsa sometimes


"Wannan yarinya akwai iyayi,ko iyayin waye kika kwaso haka oho" hajiya qarama dake kallonta tana qaramar dariya ta fada,shima yana jinsu,sun saba irin wanann wasan dake kama da wasan jika da kaka,do haka ko waiwayosu baiyi ba ya wuce ya shige motar da tuni jason ya bude masa. A ciki ya samu sajjad yana jiransa,ya kalli agogonsa sannan ya dubeshi


"Dr yace muje shagari quaters tukunna ko?,nasan zamu kashe kamar awa daya a can din" wani kallo ya watsawa sajjad din bayan ya zauna sosai cikin kujerar


"Awa dari zamuyi" fashewa da dariya sajjad yayi har yana duqawa,yadda yayi maganar ya tabbatar masa a wuya yake


"To ai shikenan,ba laifi,saina gayawa Dr kana buqatar awanni dari,ayi postponing meeting din zuwa wasu kwanakin a gaba"


"Will you keep quiet sajjad?" Ya fada a nutse yana lumshe idanunsa hadi da budesu


"Afwan" ya fada yana dariya,sannan ya maida kansa ga google da ya shiga,yana duba sabbin kayayyaki da sauran companies suka saki a satin,gudun kada suyo kaya iri daya,amma can qasan ransa cike fal yake da dariya da kuma annashuwar abinda Dr ya yiwa toufeeq din,bayan shekaru kusan biyar,yau dr ya karyawa toufeeq record,abinda yasan cewa duk duniya banda shi ba wanda ya isa ya masa hakan.


          Ko cikin motar shuru yayi kamar wanda ke tunani,bini bini ya duba agogon hannunsa,shi ko hanyar unguwar bayason bi bare ya isa ga gidan,ya danna wani madanni daga gefansa,wanda saqo zai kaiwa driver din dake gaba na buqatar ya qara speed na motar.


         Cikin mintuna qalilan suka isa qofar tafkeken gate din gidan, driver din yana shirin dannan hon don a basu damar shiga farfajiyar gidan toufeeq ya dakatar dashi


"Inaga ta fito kawai mu dubata,no need sai mun shiga har cikin gidan" waiwayowa sajjad yayi ya kalleshi


"What kind of dubiya is this?,ka taba jin ance wanda za'a duba shi zai fito?" Kafin yayi wani yunquri sajjad ya bawa driver din umarnin shiga ciki.


         Hon biyu kacal me tsoron qofar ya buda gate din yanason ganin su waye,Dr mamman dake zaune daura dasu yana duba jarida yace ya bude,kosu waye da alama sanannu ne. Wanann din dabi'arsa ce,lokaci bayan lokaci yakan zauna a bakin gate din da kansa tare da me gadin,ya girmi baaba habu,amma shi dinma dattijone kamar shi,zaman nasa a wajen lokaci lokaci yana yiwa baaba habu din dadi,akwai kyakkyawar mu'amala da fahimtar juna a tsakaninsu,sannan hakan yana sake baiwa dr girema damar fahimtar matsaloli da kusakurai da za'a iya gyarawa.


            Rufe news paper din yayi sanda motar ta gama tsayawa,toufeeq da sajjad suka fito,miqewa yayi sanda suke sajjad ya nufoshi toufeeq na biye dashi a baya.


"Barka da yamma" shi da sajjad din suka fada kusan lokaci guda


"Barka kadai yan samari daga ina?"


"Daga kamfanin MT JARMA muke,munzo duba jikin daya daga cikin ma'aikatan mu ne Khadija"


"Ma sha Allah,amma kai din yaron Dr ne?" Abba ya fada cikin sakin fuska yana duban sajjad, murmushi sajjad yayi ya juya yana dubam toufeeq


"Ga dansa nan" matsowa taoufeeq din yayi,abba ya miqa masa hannu sukayi musabaha,sannan ya waiwaya ga jamilu wanda ke aikace aikace a gidan


"Yi musu jan gora zuwa setting room,sai ka yiwa ita sãahar din magana"


"Muna kan hanya ne abba,ko zamu samu ganinta?" Toufeeq ya datsi hanzarinsa,kai ya jinjina


"Babu damuwa,rakasu ta can baya,naga wucewar 'yar uwarta gurin,na tabbatar suna tare" godiya sajjad yayi sannan sukabi bayan wanda aka kira da jamilu.


           Sake zurfafa ganinta afifa dake zaune tana fuskantar sãahar tayi tare da son tantance abinda idanunta ke gane mata,a youngest handsome millionaire,a business tycoon Muhammad toufeeq jarma. Yana takowa majestically,takun da ya banbanta dana sauran maza,koda a yanzun yanayin tafiyarsa daban da tasu sajjad da kuma jamilu.


       Sãahar ta bada baya,ta tabbatar ba zata iya ganin meke faruwa a bayanta ba muddin ba ita ta tabota ba,so amma tana gudun reaction dinta,kada taje tayi misbehaving,don haka ta maze,taci gaba da kurbar mamakinta ita kadai,har zuwa sanda suka qaraso gurin.


         Sallamar jamilu ta saka sãahar waiwayawa,abinda ya bata damar ganin abinda ya sanqarar da tunaninta,lokaci guda idanunsu suka gauraya cikin na juna,a take kowa izzarsa ta motsa,haushin dan uwansa kuma ya sake motsa musu. Me wannan dan izzar yakeyi cikin gidansu?


"Alhaji ne yace a rakosu" jamilu ya fada cikin rusunawa,gamar fadar tashi kuma tayi dai dai da miqewar sãahar,ta fara dauke wayarta headphone da sauran tarkacen da tazo gurin dasu,don ba zata iya hada numfashi da mutumin nan ba,bare har magana ya shiga tsakaninsu. Tana gama debewa ba tare data waiwaya ba tayi gaba da zummar dauke system dinta a inda afifa ta ajjiye mata,ta duqa takai hannu,saidai kafin hannun nata yakai ga sauka a kai wani hannun ya dauketa ya aje gefe.


          A nutse ta dago da fusatattun idanunta,ta zubesu cikin nasa sanda yake tsaye a gabanta,hannunsa guda daya zube a aljihun wandonsa,shima ita yake kalla


"Nan fa ba MT JARMA COMPANY bane,bare kace zaka sakamin doka ko iyaka daga yin duk abinda nayi niyya" gyara tsaiwarsa yayi,yana jinjina qarfin halin yarinyar,da qwarewa wajen rashin kunya da tsiwa


"Koda ba MT COMPANY bane,amma anan din,cikin tsakiyar gidan naku ina iya ladabtar dake iya yadda naso......tunda qafafun naki sun warke,ina tunanin wani sabon tabon kike da buqata daga wajena.......Me kike a gida bayan kin warke?" Ya jefa mata tambayar cikin izza yana kafeta da ido. Mamaki ne ya cikata,tayi kasaqe tana kallon qarfin hali irin nasa,ya tsareta da tuhuma kamar wani ubanta. Zare idanunsa yayi daga kallonta,ya duba agogon hannunsa minti goma sha biyar kacal yayi niyyar qonawa a dubiyar da Dr ya tirsasa masa yayita,kuma ta cika,dago idonsa yayi ya sanya hannunsa a aljihun rigarsa,ya fiddo wayarta data bari a mota ya cilla mata


"Ki tabbatar kin dawo aiki ranar Monday,ko kuma ki rasa aikinki" abinda ya fada kenan,ya zagayeta ya wuce.


          Da kallo ta bishi cikin tsananin bacin rai,ya isheta ya kaita maqura,ita ba yarinyarshi bace da zai dinga yi mata irin wannan izzar,tabbas a yau dai baici bulus ba,zata koma aiki amma kuma saita rama abinda yayi mata,tabbas zai biya da farashi me tsada.


           Ta qofar baya ta wuce ta bulla sassansu,a parlor ta samu afifa da maama a zaune,bata tsaya ba sai tayi wucewarta ciki,tana kuma shiga daki ta maida muqulli ta rufe qofar,ta zauna tana fidda zazzafan huci daga bakinta,tsanarsa na sake ratsa mata jininta.


           Sai da suka daidaita akan hanya sajjad ya dubeshi


"Da ka sanya muka bar gurin,ina fata ba wani abu mara kyau ka yiwa yarinyar mutane ba"


"Kanta na yanke zan siyar" ya amsa masa a taqaice


"A yadda kake da zafin rannan,idan ka fara yankan kai an mata sun shiga uku,kafin shekara 'yammatan garinku sun qare inaga" maganar sajjad din taso bashi dariya,sai kawai yadan murmusa kadan da iya labbansa yana girgiza kai,sajjad din yana ci masa tuwo aka yadda yaga dama,amma ba komai,shi da shi kar tasan kar ne.


***********Cikin karsashi da tare da maido dukka azamarta gangar jikinta ta shiga company din ranar monday,abu na farko data fara yi shine hada dukkan documents da report data fara aiki a kansu,ta tattara dukkan wasi bayanai,harda hardcopie data aikawa office din ceo din bai saka hannu ba,ta zauna cikin kwanaki hudu ta tura zuwa email din Dr ahmad jarma,tace ya duba musu,idan komai yayi,suna buqatar sanya hannunsa zasu fara aiwatar da komai.


          A dare daya ya duba dukkan bayanan,bai samu gamawa ba sai kusan qarfe uku na dare. Sosai ya jinjinawa kaifin basira da qwaqwalwa irin na sãahar din,yayi saluting nata sosai,tunanukanta da yadda ta iya tsara abubuwa sai yake masa yanayi da tsari da ra'ayin toufeeq dinsa,tsarikan nata sunyi bala'in burgeshi,don haka baiyi jinkiri ba ya sanya mata hannu a gaba daya guraben da ake buqatar sahalewarsa,don aiwatar da ayyukan da kuma fidda kudade daga asusun kamfanin.


           Sanda documents din suka isketa murmushi ta saki,sai taji kanta sakayau,kamar Dr din ya share mata wani fage da zata aiwatar da dukka ayyukanta hankali kwance ba tare data bi ta office dinsa ba har ya samu damar da zai bata mata rai,taci alwashi!,kuma tana da yaqinin wannan itace hanya guda daya da zata qona masa rai.


             Sati na gaba ta fara gudanar da komai,aka fitar da kudade akayi hiring mutanen da zasu bada gudunmawar farfado da kamfanin,cikin sati guda ta sauya komai ta kuma fara gudanar da al'amuranta hankali kwance.


            Wata guda kacal company ya fara ci gaba,kawo yanzu kusa duk wanda ya kwana ya tashi cikin company din yasan da zamanta,ta maida kanta busy sosai ta yadda zatayi abinda ya dace,wanda zai faranta ran Dr,ya kuma daga kima da martabar yayanta, she's very hard worker,wannan ya qarawa ma'aikatan qwazo da karsashin aiki,ta kuma samu soyayya sosai daga garesu hadi da martabawa,wannan ya fara sanya mata so da qaunar aikin cikin ranta kadan kadan ba tare data farga ba.


********Cikin satittikan da suka biyo baya gaba daya aiki takeyi tuquru cikin kamfanin,duk wani abu daya zama nauyinta ne akafadarta yake tayi qoqarin ganin ya tafi dai dai,gaba daya bata sake bi takan abinda ya danganci office din CEO ba,duk da tana sane da file dinta dake gurinsu,ta zuba idanu ne taga ko zata samu saqo daga gurinsu,yau ne ko gobe ne,shuru dai.


           Ba jimawa ta fara samun soyayya daga wajen employees sosai,duk wanda yaga yadda take tafi da aikinta yasan cewa tasan abinda takeyi,da yawa ta tafi da zukatansu,mafi yawansu sun fada a soyayyarta,saidai kwarjininta da yadda bata sakewa mutane fuska musamman maza ya sanya suke shakkar tunkararta. Ta kame kanta sosai,ta kuma sake shata layi ga duk wanda ta fuskanci dan rawar kaine. A hankali sai aikin nata ya fara shiga jikinta,ta fara jin qaunar aikin,saita samu kanta da daura damarar yin dukkan wani abu da zai kawoma kamfanin ci gaba,ko don albarkacin Dr mahmud da ya dauketa kamar diyar cikinsa,don cikin watanni biyun da tayi sai hudu yana kiranta,ya shaida mata yana samun bayanin yadda aketa samun ci gaba daga bakin sajjad. Ba wani sanin sajjad din tayi cancan ba,amma zata iya shaida fuskarsa da kuma nasa muqamin.


          Ta bangaren toufeeq aikinne yaso hadar masa,nasa company din da yake shirin kafawa daya baro ana processing budeshi abubuwa sunyi nisa,ana da buqatarsa,dole yayi wani irin busy sosai,yake kasa hankalinsa gida biyu yayi aikin MT JARMA GROUP OF COMPANY sannan yayi na MAHFAD FACTORY,kwata kwata baya samun kansa sai dare,nan ma lokutan baccin nasa bame yawa bane sosai,yana qoqarin yakicewa ya dawo gida ne kadai saboda fadeela bayason abinda zai sanya ta dinga jin kewa,ko ta nemi wani abun ta rasa bata samu ba.


*_RAI DANGIN GORO_*????????????????


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


VIP????

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????

[21/08, 6:54 pm] Mimah Yusuf: *H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

https://arewabooks.com/u/huguma


Page 30


       *_RAI DANGIN GORO_*



        Yadda ayyuka suka dauki zafi cikin company din,da yadda hadin kai ke samuwa daga dukka ma'aikatan ya sanya cikin satin basu damar samar samar da wasu games don nishadi a kowanne department.


          Ranar Monday bata wuce awa daya da shigowa office ba,miss sameera ta shigo,fuskarta dauke da murmushi tace


"Kin samu gayyata daga CSO Chief security officer na MT JARMA COMPANY,yau zasu gabatar da nasu game din na hack day,during break hours". Hannu ta miqa ta karba mini computer din da miss sameera ke duba saqonni irin wannan tana duba saqon da aka aiko din. Kai ta gyada kadan sannan tace


"Babu matsala,ki tunamin idan time yayi"


"In sha Allah"  ta fada tana dan russunawa cikin girmamawa,sannan ta juya ta fita. Fitar tata da yayi dai dai da shigowar kiran ahmad gana wayarta.


          Har ta dauke kai taci daga da aikinta kamar ba zata daga ba,sai kuma wata zuciyar ta nuna mata kamatuwar yin hakan,koda batason tayi wayar dashi a qalla ta bashi uzurin da zai sanya ta zamewa amsa wayar tasa,tun ranar da yazo gidansun har yau bata sake daga wayarshi ba bare ya sanya ran samun damar sake ziyartar.


           Lokacin data daga wayar a zaune yake,amma sai gashi ya miqe tsaye saboda farinciki,maganar gaskiya ya kira ne kawai,bawai don yana da wani tabbacin na zata daga ba, sassanyar muryarta ta saukar masa da kasala lokaci daya,ya koma ya zauna yana dafe wayar qamqam a kunnensa


"Am so sorry,na katse miki aiki ko?,nasan yanzu lokacin aiki ne" ya katsi hanzarinta tun kafin ma tace komai


"Ayimin afuwa,na kasa daina kiranki ne,amma ko iya haka Am really grateful "


"Why did you call me?" Ta tambayeshi kai tsaye


"I want hear you,i missed your sweet voice" ko kadan maganar tasa bata burgeta ba,saima bata mata rai da tayi,ko kadan bata jiran jin yabo daga bakin kowanne namiji a yanzu


"Okay,It's working hours now,can you turn off the phone?"


"Can i call you later please?" Ya fadi cikin kwantar da murya,hakanan taji yau din ta kasa musa masa,sai kawai tace masa


"Allah ya kaimu" daga haka bata tsaya jiran jin amsarsa ba ta datse kiran. Tana ci gaba da aikin amma rabin hankalinta yana kan hanyar da zata bi ta yakice mahmud daga rayuwarta,ta fuskanci wani banzatar da lamuransa da takeyi sam baya damunsa,kamar ma ko a jikinta wai an tsikari kakkausa,qara qaimi kawai abinsa yakeyi. Duk kuma yadda yakai ga sonta bata jin ko kusa ko alama zata iya aurensa,bama shi kadai ba,ta tattara al'amarin aure gaba daya ta rufe shafinsa,bata sani ba ko sai a qiyama.


              Sanda miss sameera ta shigo ta gaya mata lokaci yayi saita duba agogo,ta tsaya tayi sallar azahar,duk da cewa akwai sauran lokaci,farkon muhtarinta ne a sannan. Coffee tasha rabin cup,sannan ta gyara yafen mayafinta daya zauna sosai a kanta,ya dace kuma da doguwar rigar atamfar jikinta,wadda dinkin yabi jikinta kamar domin ita aka halicci atamfar da dinkin gaba daya,jikinta sai fidda sirrintaccen qamshin nan nata yakeyi,saika dauka yanzu yanzu ta gama fesa turarukan nata,kabbasa ce me dan karen qamshi data dade da bin jikinta,bayan body mist da sauran turaren kaya da take using dasu masu dan karen tsada da kyau,tana iya kashe ko nawa ne ta siya turare,ba kamar sauran tarkacen makeup ba da har yau saidai a siya mata,don ba wani damunta sukayi ba,gwara gwara powder ma.


         Tare suka taho da miss sameera,suna dan tattaunawa akan abinda ya shafi aikinsu. Dab da zasu gifta office dinsa idanunta ya sauka a kansu,can qasan ranta tayi qwafa gami da duke kanta,don ko ta qofar office din bason gifatawa takeyi ba bare wani abu ya kaita,har ya hadata mu'alama da mamallakinsa.


          Babban hall din company a nan ta taras da ma'aikata masu yawa,kowa yana saman kujerarun da aka warwatsa a gurin, gurin sama na musamman aka bata ta zauna tana maida hankalinta ga babban allon majigin dake iya nuna yadda kowanne abokin aiki ke qoqarin yin kutse a na'urar dan uwansa amma wancan yana tosheshi. Tun bata jima da zama ba wasan ya dauki hankalinta sosai,bama ita kadai ba,kusan duk wanda yake wajen abun ya matuqar qayatar dashi,mayun na'ura aka hada team dinsu guda kowa yana qoqarin baje fasaharsa.


              Sosai wasan ya dauki zafi,ya kuma dauki hankula,har haka ya sabbaba tashin 'yar hayaniya a hall din saboda ana gab da gangara a wasan.


              Ba zato ba tsammani sai gashi ya bayyana a gurin,da yawa basu lura da shigowar sa ba,har sai daya fara zuwa tsakiyar hall din,sannan kowa ya fara shiga taitayinsa,cikin girmamawa kowa ya fara duqar da kansa yana miqa masa gaisuwa. Ko gaisuwar mutum daya bai amsa ba,yaci gaba da takowa ciki,cikin izza da qasaitarsa,hannayensa zube a aljihun suit dinsa,fuskarnan a dinke tsaf kamar ko yaushe,murtukewar kuma da bata taba hana bayyanuwar kyansa.


          Bai tsaya ba har ya isa ga kujerar da CSO yake tsaye a gabanta,yadan russuna cikin girmamawa


"You are welcome sir" ya fada a ladabce,yana mamakin yadda akayi yasan da game din,bayan basu tura takardar gayyata office dinsa ba. An rasa zaququrin da zai tura ne saboda zallar shakkarsa da sukeyi,dukkansu jikkinansu sun basu bazai dauki wannan da muhimmanci ba bare ya halarta.


         Idanunsa masu kaifi ya zube masa yana jifansa da kallon da ya sanyashi qas da kansa,cikin husky voice dinsa data qara wani zurfi da bacin rai a cikinta yace


"what nonsense are you doing here?" Kadan ya dago ya saci kallonsa,yadan sosa kansa sannan yace a ladabce


"Ba shirme bane sir,and It's not a joke, it's a game to strengthen the security team"


"Who gave you permission to do it?,a tsakiyar ranakun aiki saboda rashin sanin muhimmancin ayyukanku?"


"Sorry sir,munyi requesting wa office din president,da muka samu tabbacin zuwanta munyi tunanin wannan ya wadatar......". Ambatar sunanta yasa ya gama fahimtar inda komai ya dosa,tunda ya shigo da safen yaci karo da sabbbin ma'aikatan da baisan da zamansu ba dama,yaga kuma aikace aikace masu yawa da shi yasan bai sanya hannu don a gabatar dasu ba,saboda yana da nashi plan din da yakeson ya kammala a qaddamar dasu duka a tare kuma lokaci daya.


              Waiwaya yayi yana duban sashen da take,tana zaune akan seat dinta,har zuwa yanzu bata tashi ba,hakanan bata motsa ba,tana ci gaba da latsa system din gabanta,duk da cewa an dakatar da komai amma ta shiga wani sashe daban,zakayi tsammanin batasan me yake faruwa cikin hall din ba.


         Kafeta yayi da idanu,ransa yana sake baci,wato she doesn't care?,me yasa Dr zai saurin aminta da ita ne ma wai?,meye dalili?,baisan sharrin mata ba,they can do whatever don suga sun shiga jikinka,sun samu aminci da yardarka,sannan daga bisani su cutar da kai,bayan dogon lokacin da suka dauka tare da kai,bazai sake barin haka ta faru ba!,har abada!!.


           Matsawa yayi gaba kadan yana fuskantarta,cikin izza ya motsa bakinsa yana magana da ita da wani irin zafi


"Where did you get all this courage mr president?,me yasa kikeson ki dinga yin gaban kanki bayan baki cancanci hakan ba?" Cikin matuqar mamaki ta daga kai,kanta tsaye ta saka idanunta cikin nasa birkitattun idanuwan wadanda ke cike fal da memories masu zafi dake sake zafafa kansa


"What are you trying to say?" Ta tambayeshi itama kai tsaye


"Kin fahimci komai,dukka wadan nan abubuwan da kike gudanarwa me hakan yake nufi?,baqin fuskar ma'aikata da kika kwaso babu cikakken bincike tantancewa ko tattaunawa da wadanda suke da haqqi da abun,me hakan yake nufi?" Wani irin kallo ta jefa masa,zuwa lokacin tana jin takai geji,ta kuma gaji da sauraron maganganunsa masu kama da ya shirya ci mata mutunci,saita miqe tana fuskantarsa kai tsaye cikin rashin tsoro da kuma rashin shakka,saidai kafin tace komai muryar sajjad ta mamaye gurin.


           Tun sanda ya shiga office dinsa saima data tura masa information na cewa ana can ana game din,a nufinta na b'ata sãahar da kuma kawo rigima a tsakaninsu,tace masa ya fita zuwa hall din yaji hankalinsa bai kwanta ba da fitar tasa ba,saboda tun daren jiya yasan cikin mugun bacin rai yake,saboda kiransa da NADEEYA tayi ta gaya masa saqo daga AMEESHA,ita kanta nadeeyan tayi nadamar kiran,ta dauka komai yana zuwa ya wuce,ta zaci zuciyarsa ta sassauto ashe ba haka bane,ta tafka kuskuren daya dami zuicyarta,tun jiya kuma take kiransa amma har zuwa yanzun bai daga wayar ba,abinda yasa ko kamfanin da zafi zafinsa ya iso yau,sai Allah kuma ya kade azal bata sauka kan kowa ba har ya isa office dinsa,shi yasa yanzun da yaji ya fita sai yabi bayansa,don shi yasan da game din,ya jima ma zaune cikin hall din yana kallon yadda suke abun cikin gwaninta sa qayatarwa.


"everybody outside please!" Nan da nan employees din kawunansu ke a qasa cikin d'ari d'ari da rashin jin dadin maganganun da yake gayawa president din tasu suka fara qoqarin fita cikin gaggawa,kamar basu da buqatar dama gani da jin abinda yakeyi matan,banda wasu tsiraru cikin mata da basu so hakan ba,dama su din ta shige musu hanci da qudundune,tako ina ta sha gabansu,sun rasa yadda zasu fatota,ciki harda saima dake lafe a bakin qofa.


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


VIP????

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????


*H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

https://arewabooks.com/u/huguma


No comments