Breaking News

SAKAYYAH Book 3 PAGE 5

 



*WOHOHO IN KAJI ANA ?I GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*



_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan ka?en gida Shararriya kuma ?asaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin ma?i, garin Hakkin mayi, garin ?el?amhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Ri?i wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Mali?i mai masifar ?arfi da matse mace, ka masin Da?i har Ma?igan Akwai, kwanon ?asaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da in?antacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau ha?insa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Ri?i mai ?arfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin ?aure, tuwon ?auren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu...Se kuma fannin ?amshi kasance da Shu'umin ?amshi wanda ze gigita ?wa?walwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ?asaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ?aya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta ri?e ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

_Shin ko kinsan sihirtaccen ha?in da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Ka?an) ko kinsan hakan nada ala?a da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ?in ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntu?i number ta 08069423567 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afa?in Nigeria harma da ?etare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana mu?atawa kanmu lokaci...._



               

      ????????????????????sai.kunzo. sayan na gari maida ku?i gida,




Cikin dariya sosai ta ?arshe Maganar, sai kuma tayi saurin sa tafin hannunta na dama ta rufe bakinta, sabida jin yanda muryan Asma'u ya fito tana shesh-she?a.

Tare da saki sanyayyan kuka tana cewa.

“Dariya ma kike min Khausar?,Baki san halin da nake ciki bane wallahi zai kashe ni fa!”.

Da sauri Khausar ta gyara zamanta cike da tausaya wa tace.

”Kiyi ha?uri My Besty babu abinda zai kashe ki in Sha Allahu, wahala ce dai anshata kuma in sha Allah baza amaimaita irin taba”.

Sai kuma ta kalli Moddibo da idanunsa ke lumshe yana motsa la??ansa amma bisa duk kan alamu yana sauraron tattaunawar wa tasu tace.

“Kin manta nima lokacin haka kike ta min dariya idan kin tuna alokacin har ce miki nayi kema kwana nawa ya rage Miki amma kika cigaba da dariyar ki”.

Araunane Asma'u taja dogon numfashi tare da cewa.

“Baza ki gane bane Khausar Ni ba maganar dariya nake Miki ba Ni dai yanzu dan Allah ki daina yimin dariya,yanzu ina Yah Moddibo yake ki bashi wayar”.

Cikin tausayinta da kuma yanda take jin shesh-she?an kukanta Khausar tace.

“Menene? me zaki ce masa?”.

Asanyaye Asma'u tace.

“Ni dai dan Allah ki bashi wayar”.

Kai Khausar ta gya?a tare da cewa.

“Toh”.

Kana ta sanya wa Moddibo wayar akunnensa.

Ahankali ya juya ya kalleta kana ya ?aura hannunsa akan nata ya ri?e wayar.

Asma'u kuwa da muryanta ya gama dishewa da kuka tace.

“Yah Moddibo”.

Ahankali ya ?an runtse idanunsa yana mai jin tausayinta, rauninta, damuwarta, domin jinta yake tamkar jininsa tsatsonsa yana jinta tamkar yanda yake jin Rahama Aransa, cikin sanyi da tausasawa yace.

“Na'am Asma'u me ya faru? Me yake damunki?”.

Kuka ta fashe dashi cikin dashewar murya tace.

“Yah Moddibo bani da lafiya ni dan Allah kazo ka ?aukeni”.

Cikin fesar da numfashi Moddibo ya ?an gyara zamansa tare da cewa.

“Kiyi ha?uri Asma'u, Kwantar da hankalinki ki daina kukan ki fa?a min meke damunki!?,Mene matsalar ki?”.

Cikin son danne kukan dake taso mata tace.

“Bani da lafiya zazza?i nake ji ?afafuna, bayana, kaina, duk ciwo suke min”.

Ahankali yace.

“Toh kiyi ha?uri Yi shiru yanzu me kike so?”.

Tana shesh-she?an kuka tace.

“So nake ka kawo min Khausar kuma kaima kazo”.

Kai ya gya?a tare da fa?in.

“Toh kiyi shiru in Sha Allahu zan kawo miki ita”.

Cikin muryanta da bai fita sosai tace.

“Yanzu fa?”.

Kai ya gya?a mata kamar tana gabansa yace.

“Eh in Sha Allahu yanzu”.

Ya ?arashe maganar yana mai jin matsanancin tausayinta kasancewar yasan wanene Dr Jameel mutum ne mai shegen fitina kana yasaba neman mata ya saba ko yaushe rayuwarsa da mata sannan yasan tunda sukayi maganar Aurensa da Asma'u ya daina neman mata, tun lokacin yake fama da Azumi yasan ya tara fitinar da tafi ?arfinsa shi kansa shiyasa yake jin tausayinta dan ya san ya mata wawan ri?one.

Cikin sanyi ya fesar da numfashi kana ya cigaba da cewa.

“Kiyi ha?uri ki share hawayenki kuma ki daina kuka,  kukan da kike yi zai sa kiki zazza?i da ciwon kai”.

Kai ta gya?a kamar yana ganinta ta share hawayenta tare da cewa.

“Toh ka bawa Khausar ”.

”Toh”.

Yace kana ya mi?awa Khausar wayan tare da fa?in.

“Tashi, tashi ki shirya mu tafi”.

Khausar kuwa cikin sanyi da tarin tausayin aminiyar nata tace.

“Asma'u kiyi ha?uri ganin nan zuwa ki daina kukan dan Allah ”.

Ba tare data tsaida kukan nata ba tace .

“Nikam dan Allah kizo kuma idan akwai magani ki kawo min”.

Murmushi Khausar tayi kana ta kalli Moddibo da fuskarsa ta nuna damuwa numfashi ta fesar tare da cewa.

“Kamar ya in kawo kiki magani Asma'u!,Keda kike tare da Likita?,Ai ke kece gidan magani”.

Sabon kuka ta fashe dashi kana tace.

“Baza ki gane bane yanzu ma yamin allurai sannan yaban magunguna kuma duk nasha”.

Ajiyar zuciya Khausar ta sauke tare da cewa.

“Toh kiyi ha?uri in Sha Allahu zaki ji sau?i ”.

Kai ta gya?a tare da katse kiran kana ta mike suka fito.


 A Corridor sukayi kici?is da Innayi wacce bisa alamu taje ta gaida Didi ce ta dawo cike da kulawa ta kallesu kana tace.

“Lafiya ina zaku je?”.

Kallon Khausar Moddibo yayi kana cikin sauri yace.

“Zamu je tayi Anti nytel ne”.

Kai Innayi ta gya?a tare da cewa.

“Toh shikenan amma da sassafe haka?”.

Yana kallon Khausar data ?an lumshe Idanunta yace.

“Eh”.

Kai ta jinjina kana tace 

“Ok kuma naga wancan zuwan nata da daddare kuka je wannan kuma da sassafe?”.

Yana ri?e hannun Khausar acikin nasa suka nufi hanyar fita kana yace.

“Eh”.

Kai ta gyada tare da shigewa ta nugi kitchen.

Nan ta samu Hadimai da already sun fara girki.


Dr Jameel ne zaune dafe da kansa fuskarsa ?auke da Murmushi.

Cikin kasala da alamun rashin wadataccen bacci ya mu?e a sa?ule jin ana knowking ?in ?ofar.


 A hankali ya bu?e ?ofar ganin Khausar ce agaba yasa ya ?an ja baya cikin sauri Khausar ta wuce cikin falon tare da cewa.

“Barka da safiya Dr”.

Fuskarsa ?auke da ?ayataccen Murmushi yace.

“Barka dai Bestynmu”.

Sai kuma yayi saurin juyawa tare da rungume Moddibo cikin matsanancin farin ciki yace.

“Ka gama min komai Aminina kuma ?an uwana ka bani abinda ban ta?a samun irinsa ba arayuwata ta duniya”.

Ya lumshe idanunsa yana tuna irin garar daya kwasa awajen Asma'u kana ya cigaba da fa?in.

“Dukk biye-biyen neman Matana ban ta?a samun gamsuwa, nutsuwa, da kwanciyar hankali ba kamar akan wannan ?anwar taka kagama min komai”

?an tsuke fuska Moddibo yayi kana yasa hannunsa na dama ya make ?eyensa tare da rike ?unnensa yace.

“Ka kuwa san abinda kake fa?a?,”.

Still fuska ?auke da murmushi Dr Jameel ya gya?a masa kai tare da cewa.

“Na sani mana, nasan me nake fa?a kawai dai na rasa ta ya zan nuna farin cikina ne.

Ji nake kamar in kira Ummi in sa mata albarka saboda ta bani abu mafi daraja da da?in samuwa arayuwar duniya”.

Zare idanu Moddibo yayi kana yace.

“Baka da hankali fa”.

Kai Dr Jameel ya gya?a yana lumshe idanunsa kana har zuwa lokacin fuskar na ?auke da Murmushi yace.

“Sosai ma bani da hankali, Wallahi bani da ishesh-shen hankali saboda tun jiya da hankalina ya tafi cikin gajimare har yanzu bai dawo ba.

 Ni ka?ai nasan irin da?i da shaukin dana kasance”.

Da ?an ?arfi Moddibo ya matsa kunnensa wanda yasa Dr Jameel sakin ?aramin ?ara.

Moddibo kuwa yana cigaba da matsa kunnensa yace.

“Shine ka azabtar min da ?anwata da fitinar da baka kasheta ba na tsawon watanni ko?

shine yanzu dare ?aya zaka sauke akanta ko?”.

Langwa?ar da kai Dr Jameel yayi tare da cewa.

“?anwar taka ce tafi zuma da?i baki ?aya ta gigitani ta gigita min lissafi duk ta rikitani”.

?eyensa Moddibo ya kuma makewa da karfi kana ya wuce cikin falon.

Da sauri Khausar da tuni tayi ciki, ta juya ta kallesu kana tace.

“Dr ina Asma'u take?”.

Da hannu ya nuna mata Corridor da bedroom ?in su yake.

Da sassarfa ta wuce.

Moddibo kuwa zama yayi akan kujeran kana Dr Jameel ya zauna gefensa.


Asma'u kuwa cikin yanayin baccin daya fara ?ibarta ta fara jiyo sautin muryan Khausar cikin sauri ta yun?ura da niyyar tashi.

Da sauri Khausar ta tura ?ofa ta shiga Asma'u kuwa da wani irin sauri ta runtse idanunta kana ta koma ta zauna tare da sakin ?ara tana yarfe hannunta.

Cikin sauri Khausar ta matsa ta zauna kusa da ita kana ta ri?e hannunta tare da cewa.

”Allah sarki Asmeeyn Ummi an girma”.

Harara Asma'u ta galla mata da kumburarrun idanunta tace.

“Wani an girma?,An dai zalinceni!, Kawai ai wannan zalincine ba girma ba”.

Murmushi Khausar tayi wanda ya bayyanar da ho?oranta tace.

“Kema kiji abinda ake ji, kiji abinda ko wacce ?a mace take ji fatan mu dai Ubangiji Allah yayiwa iyayenmu albarka ya kuma saka musu da mafi kyawun sakamako da tarbiyyan da suka bamu Ubangiji Allah ya bamu zaman lafiya a gidajen aurenmu”.

Cikin shesh-she?a Asma'u tace.

“Ameen ya Allah amma Ni dai wallahi tare zamu tafi”.

Zare idanu Khausar tayi tare da cewa.

“Tare zamu tafi?,Na isa? A,a ni kam ba isa in ?auke wa Dr Mata ba”.

?an hararanta Asma'u tayi kana tace.

“Idan ke baki isa ba Yah Moddibo ya isa?”.

Sai kuma ta fara yunkurin mi?ewa tana cewa.

“Ina Yah Moddibo?”.

Ganin yanda take ciccije bakinta yasa Khausar fa?in.

“Ki zauna mana bakya jin zafi ne”.

Tana goge hawayen fuskarta tace.

“Ai nasha magunguna na fara jin yana raguwa sosai yanzu”.

Kai Khausar ta gyada tare da cewa.

“Toh yanzu ina zaki je”.

Tana cije gefen lip inta na ?asa tace 

“Zanje wajen Yah Moddibo”.

Dariya Khausar ta sanya tare da fa?in.

“Iyeee wai ke bakya jin kunya ne?”

Hararanta Asma'u tayi kana tace 

“Eh ?in bana ji,Ke lokacin da aka miki kunya kika ji?,Ina gaban su Ummi kika je kika rinka Zuba ta?ara son ranki”.

Dariya Khausar ta sake fashewa dashi ganin yanda Asma'u ke wani ciccije baki alamar har yanzu bata gama warware ba tace.

“Eh amma ai agaban mata nayi ba Maza ba”.

Shiru Asma'u tayi kana ta fara ?o?arin mi?ewa har ta mike ta fara tafiya mi?ewa Khausar tayi tabi bayanta tare da ri?e hannunta ahaka suka fito falon kallonsu Moddibo yayi ganin yanda Asma'u ke tafiyar yasa ya sunkuyar da kansa ?asa ya kalli gefe tare da cewa.

“Asmeeyn  Ummi kin fito?,”.

Cikin da shashshiyar muryanta tace.

“Eh Yah Moddibo ”.

Akuma dai-dai lokacin suka ?arasa cikin falon zama sukayi akan 2sitter ahankali Asma'u ta zame ta kwanta kana ta ?aura kanta akan cinyar Khausar.

Ahankali Khausar ta gyara zamanta kana ta tallafo kanta.

Moddibo kuwa ba tare da ta kuma sallonta yace.

“Asmeey zaki danne Baby fa”.

Murmushi Asma'u tayi duk da yanayin da take ciki saboda ya bata dariya ta lura Yah Moddibo yana masifar tattalin cikin nan juyawa Asma'u tayi ta kalli tudun cikin Khausar hannunta na dama tasa kan kitchen tare da cewa.

“Baby kayi ha?uri nima yau ina bu?atar cinyar Mamynka”.

Murmushi Khausar tayi kana tace.

“Yama isa tun kafin ya fito,ai tare ya ganmu ma”.

Ahankali Moddibo ya shafa sajensa yace.

“Adai barshi kar ta kura mishi”.

Dr Jameel dake Murmushi ya kalli Moddibo yace.

“Iyeee komai yaya dai yau zai bari ayi tattalin Umminsa”.

Murmushi suka baki ?aya kafin Moddibo ya kalli Asma'u yace.

“Ya jikin?”.

Asanyaye tace.

“Da sau?i Yah Moddibo ”.

Kallonsa ya mayar kan Dr Jameel tare da cewa.

“Ya baki magunguna ko? Kuma kinci abinci?” 

Kai ta girgiza tana ?an lumshe Idanunta tace.

“A'a banci ba”.

Shiru yayi kafin yace.

“Toh yanzu me zaki ci insa akawo Miki daga gida?.

Cikin sau?e numfashi Khausar tace.

“A'a bari in shiga kitchen in girka mata”.

Da sauri Moddibo ya girgiza kai tare da fa?in.

“A'a bana so”.

Kai ta langwa?ar tare da cewa.

“Yah Mu'allim zan iya mana agida ma ina shiga inyi girki ”

Cikin sau?e numfashi yace.

“Toh shikenan”.

Asma'u kuwa mi?ewa tayi tare da cewa.

“Toh mu tafi kitchen ?in tare”

Kai Khausar ta girgiza tare da cewa.

“A'a ke kam ki wuce bedroom ki kwanta naga kamar bacci kike ji”.

“A'a muje dai”.

Cewar Asma'u tana lumshe Idanunta.


Numfashi Khausar ta fesar tare da kallon yanda take lumshe idanu tace

.“A'a ke dai kije kiyi baccin”.

Ahankali tace.

“Toh”.

Hannunta Khausar ta ri?e suka wuce bedroom ?in kwanciya Asma'u tayi kana Khausar ta zauna gefenta tace.

“Amma kinyi amfani da Ruwan ?umi sosai?”.

Kai Asma'u ta gyada tare da cewa.

“Eh ya sassani kuma ya ban magunguna sannan yamin allurai kuma ya shafa min wani ma a wurin Alhamdulillah naji sau?i sosai yanzu ?azun fa ko numfashi nayi zafi nake ji kamar raina ake zarewa”.

Ajiyar zuciya Khausar ta sau?e kana tace.

“Toh ba komai yanzu dai bari na miki abinda zaki ?an ci mai zan dafa Miki?”.

Idanunta ta juya tare da taune lips ?in ta tace.

“Nikam ma bana jin yunwa”.

Cike da kulawa Khausar ta dafa kafa?arta tace.

“A'a ki dai fadi me kike so adafa miki?”.

Rau-rau tayi da idanuna tare da cewa.

“Nifa bana jin kwa?ayin komai”.

Shiru Khausar tayi na tsawon minti ?aya alamar tunani kafin ta mike tace.

“Bari dai naje kitchen in ga abinda zan Miki.

Ko dai in gasa Miki nama?

Dan nasan ki”.

Tana gyara kwanciyarta tace.

“Eh”.

Kai Khausar ta gya?a tare da wucewa kitchen.

  Kallon Moddibo Dr Jameel yayi kana yace.

“Yanzu kusan 1month fa kenan da Khausar taje anti nytel ya kamata ace gobe ko jibi ku samu ta sake zuwa”.

Cike da gamsuwa Moddibo ya gyara zamansa yace.

“Eh nima dama gobe ko jibi nake so muje,dama tun bayan 2weeks ma naso muje toh ya kama bikin nanne da muka tafi amma in sha Allah gobe ma zan kawo ta”.

Kai ya jinjina kana yace.

“Toh Allah ya kaimu”.

“Ameen”.

Ya amsa kana suka cigaba da hira...

    A gefen Khausar kuwa cikin sauri sauri ta gasawa Asma'u nama mai ?an romo-romo sai tashin ?amshi yake kana ta dafa Cous-cous da yaji Carrot da grean beans daya ?awata kyawunsa gashi yayi wasar-wasar abin sha'awa sai kuma tayi miyar hanta da yayi kyau sosai bayan ta gama ta zuba a Warmer kasancewar duka ayyukane masu sau?in yi ta ?auki na Moddibo da Dr Jameel ta kai musu Falo kana ta koma ta ?auki nasu ta wuce bedroom ?in Asma'u.


Tana shiga ta samu Asma'u na bacci jin alamun tana jin yunwa yasa ta zauna a tsakiyar ?akin kana ta zuba a plate ta fara ci.

Tana cikin ci ta ?ago kanta ta kalli Asma'u jin alamun Asma'u tayi motsi.

Asma'u kuwa cikin baccinta taji kamar sautin ?aran cokali tare da yunwar daya mur?eta ne ta mike ta zauna.

Dan ?an murmusu tayi sai kuma ta mi?e ta zauna.

Khausar dake kallonta tace.

“Ya dai”.

Cike da farin ciki ta  shafa cinyoyinta kana tace.

“Zafin ya tafi fa”.

Ajiyar zuciya Khausar tayi tare da kai spoon ?in bakinta tace.

“Haba dai”.

Cikin tabbatarwa ta gyada mata kai sai kuma ta sakin sanyayyar ajiyar zuciya tace.

“Wlh kuwa”.

Ta ?are maganar tana gyara zamanta.

“Masha Allah magunguna sun kama aikinsu”.

Cewar Khausar na Murmushi.

Asma'u kam cikin jin da?i tace.

“Wlh kam".

Warmer Khausar ta janyo tana ?ara musu abincin tace.

“Toh sa??o muci abinci”.

Kai ta gyada kana ahankali ta sa??o ta zauna suka fara cin abinci bayan sun gana Khausar tace.

“Akwai magungunan da zaki sha yanzu ne?”.

Kai ta girgiza tare da cewa.

“A'a sai bayan Azahar zan sake shan wasu”.

Tana tattara plate ?in waje ?aya tace.

“Toh shikenan”. Daga nan sukaci gaba da hira.


Wunin ranan dai haka Khausar ta yini agidan Asma'u koda Moddibo yace su tafi cewa tayi yayi ha?uri sai bayan Sallar Isha'i yazo ?aukar ta.


Tsaye suke a abakin gate kallon Asma'u Khausar tayi tare da cewa.

“In sha Allah daga nan zamu wuce gidan Addah Asiya”.

Cikin sanyin Asma'u tace.

“Wallahi nima ina son zuwa”.

Dr Jameel da baki ?aya nutsuwarsa ke kanta tace.

“Ki bari idan kin sake warware wa in Sha Allahu zan kai ki”.

Langwa?ar da kai tayi tare da cewa.

“Toh ba ance kwanan nan zasu tafi ba?”

Kai Khausar ta girgiza tace.

“A'a ance dai kwanan nan zasu koma kuma naji ance anan zai gama hutunsa”.

Kai Asma'u ta gyada tare da cewa.

“Toh shikenan In sha Allahu kafin su tafi zamu sake zuwa mu wunin mata ko?”.

Kai Khausar ta gya?a tare da fa?in.

“Eh in sha Allah”.

Daga nan sukayi sallama suka fita.

Suna fita kai tsaye gidan Asiya suka nufa.


Dai-dai lokacin kuma Asiya ce da Dr Zakariyya ke zaune a falo suna hira jin ana knowking yasa Dr Zakariyya mi?ewa ya bu?e.

Khausar ce agaba Asiya na ganinta ta mi?e da gudu taje ta rungumeta Moddibo kuwa cikin Murmushi yace.

“Addah Asiya abi ahankali”.

Murmushi tayi kana ta ri?e hannun Khausar tare da cewa.

“Adda Khausy tun shekaran jiya nake ta zuba ido ina so in ganki ban ganki ba”.

Cunno Baki Khausar tare da kallon Moddibo da suke magana da Dr Zakariyya tace.

“Yah Mu'allim ne ai”.

Murmushi Moddibo yayi kana ya marairaice fuska yace.

“Komai dai Ni ko wani laifi nawa ne komai ace Yah Mu'allim toh naji na ?auki laifina”.

Cikin narke fuska tace.

“Ato ai kasan hakane”.

Murmushi yayi.

Asiya kuwa kitchen ta shiga ta kawo musu abubuwan motsa baki ta?a ka lashe.

Khausar ce dai ta ?anci Amman shi Modibbo ko ruwa bai sheba.

Bayan sun gama hira kusan karfe goma na dare sukayi musu sallama suka tafi.


Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya Khausar na samun kulawar Uwar mijinta da danginsa Innayi ma na iya bakin ?o?arin ta kana suna waya da Momy, Ummu, Hajja Nana, akai-akai hakama Aunty Ru?ayya da Aunty Hajara.

 Bayan sati Uku Asma'u da Khausar suka je gidan Asiya suka yini mata bayan sati ?aya da zuwa su Asiya da Dr Zakariyya suka koma Indi'a...


Washe garin ranan da suka tafi a Nigeria Amina ce zaune a falo yayin da Hajiya Bunayya ke tsaye tana bubbuga ?afa tare dasa hannunta tana bubbuga mazaunanta jin yanda masifaffun tsutsotsin nan ke addabar rayuwarta wanda da ?anane suke fita yanzu kuma manya ne Amina kuwa Alhamdulillah bisa ga duk kan alamu jikinta yayi sau?i sosai kasancewar har ta fara maida ?ar ?ibanta alamun ta samu sau?i sosai-sosai.


Ahankali ta tallafe ha?arta tana kallon Mahaifiyarta ta zuwa yanzu ta fahimci tsutsotsin nan sun haukata mata mahaifiya saboda ko yaushe ?o?ari take ta cire zaninta ta yasar ita take ?o?arin hanawa kamar dai yanda yanzu ma take ?o?arin cirewa.

     Cikin sauri Amina ta mi?e cikin rauni da zubda hawaye tace.

“Dan Allah Umma kada ki cire zanin”.

Alalace ta juya ta harareta tare da cewa.

“Kada in cire zani in zauna kenan su cinyeni ke kin san abinda nake ji kuwa? baki ga tsutsotsin nan yanda suke cina ba ko kuma dan ke kin samu lafiya bake kike shan azaba yasa zakice haka, ai dacan da kike zazzaro harshe waya ce ki daina”.

Ta ?are maganar tana kwayewa Amina ?uwawunta tare da cigaba da fa?in.

“Ki ga fa”.

Cikin sauri Amina ta runtse idanunta kana tace.

“Innalillahi wa'inna alaihi raji'un”.

Ganin manya-manyan tsutsotsin dake cin Mahaifiyarta cikin matsanancin tashin hankali ta saki ihu dai-dai lokacin da Lami?o ya hau Farandar falonta saboda yanda Amina tayi ta kuka daren jiya akan cewa ya kai Hajiya Bunayya asibiti cikin sauri ya karaso Falon yayin da Momy ke biye dashi abaya ganin haka yasa Momy saurin ?aukan zanin ta daura mata.


      Ga mamakinsu sai suka ga Hajiya Bunayya ta fara buge-buge tare da ?aga hannu zata daki Momy cikin sauri Lami?o ya kamo hannayenta ya ri?e.

Dariya ta fara ?yal?yalawa alamun hauka ta tabbata tuburan ziraran.

 Kuka sosai Amina ta fashe dashi.

Dai dai lokacin Haiydar da Sulaiman suka shigo ganin haka yasa Sulaiman rungume Haiydar suka fashe da kuka cikin rauni da shesh-she?a Sulaiman yace.

“Haiydar kaga Ummana yanda ta koma”.

Shiru yayi ganin yanda take ?o?arin ?wace hannunta Momy kuwa duk da yanda take ?o?arin kawo mata duka sai da ta jawo zanin ta ?aura mata ta baya.


Wani irin abu ta fara kamar rawa kamar tsalle alamun dai hauka Muraran ziraran.

Kai Lami?o ya girgiza tare da juyawa ya kalli Gimbiya Dadu da tazo wacce hayaniyar dake faruwa ne yasa taxo tana shigowa taga Hajiya Bunayya keyi ta saki ?ara ta fa?i awajen atake a wurin ?arinta ?ai ya shanye tun, kafin a?agata ?arin jikin ta ya mace.

Cikin gigita da Ki?ima Lami?o ya kalli Haiydar kana yace.

“Haiydar jeka kira min bappanka”.

Cikin rawan jiki Haiydar ya juya ya fita yaje ya kirasa.

Hajiya Bunayya kuwa ?o?arin duka take kai masa ?ankwalin kanta ya since ya ?aure hannunta.

Dai-dai lokacin da ?anin nashi ya shigo cikin tashin hankali Lami?o yace.

“Yusuf ka ?auki Hajiya Bunayya ka Kaita Sycatry na cikin Taraba”.

Cike da damuwa yace.

“Innalillahi wa'inna alaihi raji'un Sycatry kuma?”.

Araunane Lami?o ya kalli Hajiya Bunayya dake wani irin fusga tana ?yal?yala dariya yace.

“Toh ya zamuyi Yusuf?Bata da wani amfani daya wuce mu Kaita Sycatry dama arayuwa duk abinda mutum zai yi yabi ahankali”.

Kuka sosai Bashir keyi tamkar ransa zai fita Lami?o kuwa cikin sanyi ya cigaba da cewa.

“Gashi tun ba aje ko ina ba Ubangiji Allah ya ha?a mata sakamakon aikin ta ya li?a mata su atsakiyar kanta sun zame mata matsala, muma sun zame mana matsala tun da komai yaya zukatanmu nada Imani zamuji tausayinta”.

Cikin azabebben kuka Amina ta kalli Lami?o tare da fa?in.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Ummana yanzu Sycatry za'a kai ta?”.

Cikin sau?e zazzafan ajiyar zuciya yace.

“Yanzu Amina anan za'a barta tayi ta hauka?,Mutane suna kallonta tana since zani idan mun barta anan cikin gari zata shiga tayi ta yawo tana bayyana tsaraici kinga ai baiyi ba”.

Cikin matsanancin kuka da shesh-she?a Amina ta gyada kanta tare da fa?in.

“Hakane kam Abba”.

Alh Yusuf kuwa janta yayi ya sata a mota.

Lami?o kuwa sai alokacin yaje ya ?aga Gimbiya Dadu da tuni ta sume.

Cikin ki?ima ya Kaita asibiti, inda duk binciken da akayi likitoci suka tabbatar masa da cewa ta kamu da ciwon ?arin jiki awanna ranan dai haka suka yini a asibiti koda ta farfa?o gefen bakinta ya karkace tana magana yawu na zuba cikin zubda yawu da magana irin na wanda suka samu shanyewar ?arin jiki tace.

“Ohhh nima dai ga karshena nayi ta cin ?a?an mutane ina ta zubar da cikin ?a?an mutane idan naga ?an da yamin mai?o in lashe in naga mai ciki inlamushe”.

Cikin sauri da matsanancin mamaki da tashin hankali Lami?o ya rufe mata baki tare da cewa.

“Dadu Ki daina fa?an haka dan Allah ki dai na fa?a ”.

Bakinta na tsulalar da yawu tace.

“Ai dole in fa?a ayyukana ne in ban fa?esu ba ya zanyi.

 Ni na aikata kana ganin kamar zargina mutane suke da suke cewa Ni mayyace.

Tabbas ni mayyace da gaske amma kai Allah ya tsare ka da ?an Uwanka dama nida ?ar uwata siya mukayi bawai tsatson mu bane”.

Araunane Lami?o yace.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un hasbunallahu wani'imal wakin”.

Haka yaita addu'oi wai ko zai samu ta bar tone-tone ta kama addu'a amman a banza.

Washe gari da safe aka sallamosu a asibiti suka dawo gida saboda Likitoci since babu abinda zasu iya mata dole yasa Lami?o ya nemo masu aiki wanda zasu ri?a kula da ita.


Yayin da Hajiya Bunayya da Hajiya Lami ke can asibiti suna can suna buga wash-shagare wallensu a haukace.


A kuma dai-dai wannan ranan Khausar ce zaune a falonta kunnenta ma?ale da waya tana hawaye cikin rauni tace.

“Yanzu Momy haka Umma da Hajiya Lami suka dawo?

Ita ma Gimbiya Dadu haka ta dawo?”.

Cikin sanyi da damuwa Momy tace.

“Wlh Khausar am ai rayuwar nan mu bita a sannu”.

Cikin zubda hawaye Khausar ta gyara zamanta tare da cewa.

“Dama Momy ina fa?a Miki kallon da Gimbiya Dadu take yimin yana ban tsoro kullum cikin kareta kike”.

Ajiyar zuciya Momy ta sauke kana tace.

“Toh Khausar baka da tabbaci ka isa ka tuhumi mutum ne?

ba kiji Manzon Allah (S.A.W.)yace _Azzhana zhambu Walau kana ha??un_ ai zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya amma yanzu da taxo ta fa?a da bakinta ai taga  *SAKAYYAR ta*”.

Kai Khausar ta jinjina tare da fa?in.

“Allah ya rufa mana asiri ya kare mu”.

Dai-dai lokacin Moddibo ya shigo ganin tana hawaye yasa yayi saurin shigowa ciki, tare da zama a gabanta kana ya sanya hannunsa ya share mata hawaye.

Yana mai kallonta,  sai kuma ta ?an sau?e ajiyan zuciya, ganin yanda ya zuba mata idanu yasa tace.

“Toh Momy sai anjima”.

Kana suka katse kiran.


    Ahankali ya janyota jikinsa ya ?aura hannunsa akan cikinta yana shafawa saboda yanzu cikin yashiga wata na biyar zuwa na shida haka yasa cikin ya ?an bayyana ya girma yayi ?as a jikinta gwanin ban sha'awa ganin yanayin fuskarsa yasa tace.

“Ya akayi Yah Mu'allim?”.

Fuska ya narkar da damuwa atare dashi yace.

“Minha kuka fa kike yi ya za'a yi kintam bayeni ya akayi?”.

Asanyaye ta bashi labarin da Momy ta bata ta fa?a mata sai abinda take ga sirrinsu ne bai kamata ya saniba ta ?an sakaya.

Jikinsa ya sake janyota ya rungumeta kana yace.

“Mu godewa Allah, Allah ya sake tsarkake zuciyanmu Allah ya hanamu samun damar da zamu cutar da wani, Allah ya hana wani ma samun damar da zai cutar damu.

Cikin sanyi da rauni ta gyara zamanta ajikinsa tare da cewa.

“Ameen”

Yana shafa gadon bayanta yace.

“Kuma ki daina damuwar nan ki ri?a yi musu addu'a Ubangiji Allah ya gafarta musu”.

Tana ?an lumshe Idanunta tace.

“In sha Allahu ”.

Sake janyota jikinsa yayi, bakinsa ya kai saitin kunnenta cikin wata kasalalliyar murya mai cike da shau?i da bege yace.

“Minha babu matsala ban takura ki bako?”.

Cikin lumshe idanu da yanda hannunsa ke yawo a sassan jikinta ta fesar da wani sanyayyan numfashi tana sake shiga jikinsa tace.

“Ya zanyi Yah Mu'allim tunda kana da bu?ata?Kuma dole in ?auke bu?atar ka tunda bana so wata ta ra?eka”.

Ya tsarsa manuniya da babba yasa ya kamo tsinin hancinta ya jijjiga tare da cewa.

“Kishi! Kishi!! Kishi!!!”.

Cikin Cunno baki ta langwa?ar da kai kana tace.

“Toh ba dole inyi kishi ba,

Idan banyi kishin kaba waye zai yi kishinka a duniya”.

Sai kuma ta marairaice fuska tace.

“Ka ?i kayi min al'?warin baza kayi min kishiya ba”.

Jawota jikinsa yayi ya rungumeta kana ya ha?e bakinsu waje ?aya daga nan yashiga sarrafa ta cike da bege da tarin ?aunarta...


Bayan wani ?an lokacin Alhamdulillah yanzu cikinta ya cika wata bakwai Cif-cif.

 Ahankali take sauka kan tsep ?in sau?a Falon Didi.

Didi dake zaune tayi saurin mi?ewa hangota da tayi kana ta ri?e hannunta cike da kulawa tace.

“Ba nace miki sau?an nan idan yana wahalar dake ki bari ba?,Idan kina son ganina ki ri?a kirana in zo ba”.

Murmushi tayi tare da fa?in.

“Toh ai Didi Likita ma da kansa yace na ri?a motsa jiki na zaman bazai yiba”.

Kai Didi ta jinjina tare da cewa.

“Haka ne kam ?ata zo ki zauna me kike so in dafa Miki?”.

Murmushi tayi kana ta maida kallonta kan Moddibo da Ibraahim dake shigowa cikin langwa?ar da kai Ibraahim yace.

“Toh koma menene za'a dafa adafa dani”.

Dariya Didi tayi tare da cewa.

“Wannan ba naku bane ”.

Murmushi Moddibo yayi tare da shiga Falon kana ya zauna agaban Khausar tare da janyo ?afarta ya ?aura akan cinyarsa yana ?an jan yatsunta sai kuma ya maida kallonsa kan Didi yace.

“Didi kalli ?afafun tan nan kamar kumbura sukayi?”.

Juyawa Didi tayi ta kalli ?afafun kana tace.

“Eh nima naga kamar kumbura sukayi amma Dr Eshaa tace bakomai dan tun shekaran jiya da naga kumburin na kirata tazo ta duba ta tace bakomai wannan Normal ne mafi akasari wasu na fuskantar haka daga ciki wata Bakwai kuma kaga kumburin bamai yawa bane”.

Ajiyar zuciya ya sau?e yana cigaba da matsa ?afafun yace.

“Toh shikenan ”.

Didi kuwa Kitchen ta shiga ta ?auko Pride rice da yaji Vegetables da naman zabbi sai Perpersoup ?in Kifi da yaji kayan ?amshi ta kawo fitowa dasu tayi da plate guda biyu ta zubawa Khausar kana tasa mata kifin agefe.

Kana ta zuba a?aya plate ?in tasa spoon biyu aciki ta ajiye atsakanin Moddibo da Ibraahim.

Daidai lokacin Rahama ta fito daga ?akinta ware idanunta tayi tare da cewa.

“Didi anyi Babu Ni ko?”.

Murmushi Didi tayi kana tace.

“Na isa ?ar Autana  bata ciba ?auko plate kizo ki ?ibi na ki”.

Kai ta gya?a kana ta juya ta shiga kitchen ta ?auko plate tazo ta zuba suka fara ci suna hira...


Yayinda hadimai keta zuryan aikace-aikacen yau da kullum.


 A haka rayuwa ta cigaba da tafiya Alhamdulillah Khausar na samun wadatacciyar kulawa daga wajen tako wani sashin, sosai rayuwa take tafiya zuwa yanzu cikinta ya cika wata tara Cif-cif amma dai na ?uda har yanzu bai zoba kuma.


 Cikin kulawa Asma'u da tazo mata yini, ta zuba mata ganin ta yun?ura ta nufi bedroom cikin sauri Asma'u tace.

“me kike so in kawo Miki?”.

Kai ta girgiza tare da fa?in.

“Bakomai kawai ina so in shiga bathroom ne yau tunda gari ya waye fitsari da ya?i ?arewa nake tayi”.

?an zare idanu Asma'u tayi tare da cewa.

“Fitsari kuma?,Kin fa ?awa Dr?”.

Kai ta girgiza kana tace.

“A'a ban fa?a masa ba bakomai ai”.

Cikin cikin kulawa Asma'u tace.

“Toh bari in tai maka Miki?”.

?ar dariya Khausar tayi tare da fa?in.

”Laaa da kin bari babu inda ke min ciwo fa”.

Cike sha?uwa Asma'u ta gya?a kai tace.

“Toh shikenan ”.

Khausar kuwa ban ?akin tashiga.

Asma'u kuwa wayarta ta dauka tare da kiran Dr Jameel yana ?auka tace.

“Hello Dr”.

Daga ?aya ?angaren cike da begenta yace.

”Na'am dear ya akayi?”.

Cikin sau?e numfashi da da kulawa tace.

“Kaga tun daga ?axun da muka zo zuwa yanzu bai wuce awa ?aya zuwa biyu ba ko?”...

Kai ya gya?a mata tare da fa?in.

“Eh”.

Numfashi ta fesar tare da cewa.

“Toh wallahi daga lokacin zuwa yanzu Khausar ina ga tashiga ban ?aki tayi fitsari ya kai sau biyar nace ta fa?a maka tace wai babu matsala kawai yau yawan fitsari ne take fama dashi”.

Da mamaki yace.

“Ha'a ikon Allah kuma tace ba abinda yake mata ciwo?”.

Kai ta gya?a tare da fa?in.

“Eh”.

Cikin sanin makamar aiki da yanayin masu ciki yace.

“Alamun na ?uda ne yana iya tashi ko yaushe”.

Cikin sau?e numfashi tace.

“Kuma fa tace babu abinda yake mata ciwo”.

Ajiyar zuciya ya sauke tare da fa?in.

“Eh ba komai bari idan ta fito sai ki ha?a Ni da ita”.

Kai ta gyada kana ta katse wayar, jim ka?an  Khausar ta fito.


Tana fitowa Moddibo na shigowa kasancewar Dr Jameel ya kirasa ya fa?a masa yana shiga ya kama hannunta ya zaunar da ita akan kujera kana ya zauna a?asan lallausan Darduma tare da k...



No comments