Breaking News

MAWAHIB Complete Hausa Novel

 💗MAWAHIB💗

   (Hot luv) 




Writing By Amnah El Yaqoub



1&2


Mawahib littafin kudi ne, kibiya 500 kacal ki karanta cikin salama 

0164549488 

Amina muhammad 

GTbank 

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 


_____


'Yanmata ne guda biyu suke tafiya cikin nutsuwa,kana ganinsu kasan bazasu wuce shekaru goma sha takwas ba,d'ayar tana Sanye cikin uniform na islamiya,tanada duhun fata kad'an,a hankali ta juya ta Kalli qawar tata, wadda take Sanye cikin kayan gida,babu uniform din ajikinta saide dogon hijab irinna d'ayar,wanda yazo mata har qasa,kalar hijabin ruwan toka yayi mutuqar qawata farar fatarta,Wanda kana gani kasan cewa hutu dakuma Jin dadi ya ratsa fatar tata. 


Jiddah tace"MAWAHIB,kiraba mana musu dan Allah"


Ahankali tajuyo dara daran idanunta wanda yayi kama Dana mejin bacci, ta Kalli qawar tata, sannan tace"musun me Jiddah?"


Wadda aka Kira da Jiddah tace"wallahi musu muke dasu Hassan da Hussainin gidanmu,nace duk unguwar Nan sukadai ne 'Yanbiyu matasa, shine sukace min wai Yaya ASHRAF din gidanku Shima 'Yanbiyu,nikuma nace ba 'Yanbiyu bane, Yaya Ashraf ne kadai yayanku,saboda nide tunda nake dake,Kuma duk yanda nake qawance dake,baki taba cemin kunada 'yanbiyu a gidanku ba"


Saida ta yatsina kyakykywar fuskarta mai cikeda gashin gira alamun batason maganar, sannan ta motsa dan qaramin bakinta Mai launin pink,tace" 'yanbiyu ne,d'ayan baya zuwa sosai shiyasa baki sanshi ba,ai kinsan Yaya Ashraf dinko?,toshima d'ayan kamar kinsan shi,yanda kikaga Yaya Ashraf Shima haka yake,yana Nan kullum yana fama da uniform,basuda banbancin kamanni, komai nasu iri dayane,nikaina idan suka hadu su biyun bana Iya banbance su,saboda komai iri daya suke sakawa,kawai de hali ne kowa da irin nasa"


Cikin mamaki Jiddah tace"ashe Ana Samun 'yanbiyu maza manya kamar Yaya Ashraf,? Amma Mawahib baki taba bani labarinsa ba"


Cikin sauri Mawahib tace"menene hadina dashi dazan baki labarinsa? wannan marar imanin inani inashi?, halinsa daya da mahaifiyarsu,duk yanda kike tunaninsa yawuce Nan,miskilancinsa yayi yawa,baida fara'ah,kenifa bari Kiji Infada miki na tsaneshi, tun saudaya dana ta6a yimasa laifi ya Sumar dani, daga ranar naji nasake tsanarsa"


Cikin sauri Jiddah ta zaro ido(😳)

Tace"nashiga uku Suma fa kikace?"


Cikin tabbatar wa Mawahib tace"suma kuwa,Ina zaune Yaya Ashraf yazo yacemin naje nagyara masa dakin su,Wai ashe shine zaizo daga Abuja,nikuma bansan ranar zai dawo ba,dana gama gyaran saina dan kishingida akan gadon su,nadan dora kaina a wani fillo Mai laushi,Bansan lokacin da bacci ya daukeni ba,daya dawo yaganni a'inda yake kwanciya,kuma nadora kaina akan fillonsa, shine ransa ya6aci,daya damqi gashin kaina bansan lokacin dana saki ihu ba,shine yasaka kaina a cikin sink din toilet dinsu yabude ruwan,nide nasan yasakani a ruwa,amma daga Nan bansake sanin inda kaina yakeba,Sai farkawa nayi naganni a kwance a gadon dakina"


Cikin tashin hankali Jiddah tace"innalillahi....amma Abbanki baice komai ba?"


"Jiddah mezaice tunda sun dauki power sun bashi?,haka itama NABIHA yata6a jimata targade ahannu,shiyasa nida ita bamaso yazo gida, musanman ma ni,na tsaneshi Jiddah"



Jiddah tayi ajiyar zuciya tace"A a Mawahib,kidena fadar haka,koba komai ai dan'uwan ki ne, gidanku daya,sannan kobabu wannan dangantakar,shidin dan'uwan ki ne musulmi, Kuma babu dadi ka dinga cewa ka tsani mutum,Amma Kuma nayi mamakin yanda naji labarinsa a wajanki,saboda su Hassan din gidanmu har cemin sukai idan yazo har kudi yake rabawa mutane abakin get dinku, wani lokacin ma harda kayan abinci,toke menene ma yakaiki kwanciya a gadonsa?"


Cikin sauri tace"Gadonsa ne shi kadai?gadon su ne shida Yaya Ashraf"


Jiddah tace"duk da haka nide Ina kokonto akan wannan halaiyar tasa dakika fadamin,mutumin dazai dinga yin Alkhairi da kudinsa na aljihunsa shine za'a yi masa wannan shedar?"


Cikin taqaici Mawahib tace"to Jiddah aikuma Sai kiyi,ya Ina fada miki mutum bashida Imani kina min maganar wani kudi,kudinsa na banza da wofi...? ni Kinga tafiya ta"


Tana gama wannan maganar tayi gaba tabar Jiddah a tsaye a wajan cikeda mamaki,Jiddah tasaki ajiyar zuciya tabi Bayan Mawahib da kallo, meyake damun qawarta ne?aiko wani taji yana aibata dan'uwan nata kamata yayi ace Sai inda qarfin ta Yaqare,amma suna gida daya,ana Samun wannan matsalar?(🤔)



******



Tana shiga gida, cikin fara'ah megadinsu dayake zaune a kofar get din gidan yace"yanmatan Mamy har andawo daga islamiyar?"


Cikin ladabi tace"Baba Musa nadawo, sannu da aiki"


Bata jira amsar saba taci gaba da tafiya tana qarewa manyan motocin gidan kallo Wanda suke sheqi da daukar ido tundaga ma'adanar su, taqaraso get na biyu, tabude tashiga,anan zahirin gidan yake, gidane hadadde wanda ya amsa sunansa gida,saide bashida fadi sosai,duk da hakan an qawatashi da adon furanni Masu kyawun launi,anan compound din gidan taci karo da mutanan gidan a zaune,manyan mata ne guda biyu, saikuma wata yarinya wacce bazata wuce sa'arta ba, cikin sakin fuska tayi sallama, Nabiha da hankalin ta kekan wayar dake hannun ta, tadago kanta da sauri Jin muryar yar'uwar tata,qawa, Kuma aminiyar ta. 


tace"Mawahib Kin dawo? Ya Sayyadi yayi dorin karatu?"


Cikin tsokana tasaki wani irin murmushi,murmushin yayi mutuqar yimata kyau har hakan yasa dimple dinta guda biyu suka futo sannan tace"anyi dori,Kuma anbada number,tunda yau da niyya kikaqi zuwa"


Hajiya KILISHI datake zaune gefe kan kujerar roba,lokaci daya tabi Mawahib dawata irin harara kamar idonta zai fado qasa,cikin izza da gadara,tareda tsantsar iko tace"   'ya'yan ma'aikata andawo Kenan,INA GANIN IKON ALLAH NI KILISHI,anfita angama yawon gantali andawo,nikam naga mijin wannan yarinya,Kuma fa ahakan ake neman miji nagari..."


Lokaci daya jikin Mawahib yayi wani irin sanyi,Nabiha ta sunkuyar da kanta qasa,alamun bataji dadin furucin hajiya Kilishi Akan Mawahib dinba,cikin sanyin jiki Mawahib tadubi Hajiya Kilishi,babbar mace ce Mai kimanin shekaru Hamsin da biyar,fara ce tas,batada digon baqi a jikinta, hutu dakuma Jin dadi ya boye shekarun ta, bazaka ce takai adadin wannan shekarun ba,tana kyau sosai,saide fuskar ta cike take da qunci da rashin walwala, cikin ladabi ta russuna tace"sannu da hutawa Momy" 


Hajiya Kilishi ta kawarda fuskarta gefe batareda ta amsa gaisuwar ba



Mawahib tasaki murmushi Mai ciwo, sannan ta dubi d'ayar matar datake zaune kusa da Nabiha, wadda a shekaru bazatafi Mamyn taba, tace"Mama sannu da hutawa"


Cikin sakin sakin fuska wadda aka Kira da mama tace"sannu Mawahib"


Cikin sanyin jiki tashige kitchen,kasancewar tasan yau girkin mamyn tane, Kuma Bata dawo da wuri daga wajan aiki ba, tasan har yanzu tana kitchen bata gama wasu ayyukan ba,tana shiga kitchen din kuwa taganta a tsaye tana duba farfesun ganda Wanda qamshinsa yagama cika kitchen din,kallo daya zaka mata ka tabbatar da cewa mace ce Mai aji dakuma tsari,uwa uba yar boko maiji da gayu, komai nata tana yinsa a nutse,manya manyan zobuna ne a hannunta na gold sunkai guda uku,Riga da zanine ajikinta na leshi kanta yana daure da dan kwali Amma duk da haka jelar kitsonta ya sauko harkan gadon bayanta, black beauty ce, kokadan bata kama da Mawahib, launin fatarsu daban, saide sanyin hali dakuma dabi'arsu da tazo daya, a hankali tace"Mamy sannu da aiki"


Batare data kalletaba tace"sannu da zuwa ya makaranta?"


Cikin rashin walwala tace"Lafiya kalau Mamy,bari inje in cire kayana inzo natayaki"


Kallonta tayi a Karon farko ta karanci akwai damuwa a fuskar 'yartata, amma Bata nuna mata komai ba,cikin hikima tace"A a,aina gama komai,dauki wannan salat din kawai kije ki yanka min,Abbanki yace ayi masa kwadon salat kafin yadawo"


Ahankali tasaki ajiyar zuciya,sannan tacire hijabin dake jikinta,doguwar rigar gown din dake jikinta ta atamfa ta baiyana,rigar ta kama jikinta sosai har hakan yasa shape dinta futowa fili,hips dinta yacika rigar dam,saida ta bubbude girkin da mamy din tayi tagani bayan farfesun ganda,harda fried rice,da Alalan dankali, da fried cabbage with meat,a hankali tadauki salat din ta futo daga kitchen din tanufi hanyar part dinsu, Hajiya Kilishi tabi bayanta da kallo,ta Kalli yanda uban Hips dinta suke juyawa acikin rigar kamar da niyya take kad'asu, ta watsa mata wata irin harara tace"ina ganin ikon Allah ni Kilishi"(😂) 


Tajuya ta Kalli matar datake gefenta tace"Sadiya,dole zanyi wa ALQALI magana yaje yasamu shugaban makarantar islamiyar  yaran nan ayi masa magana,ai bazai iyu abar yara suna zuwa makaranta babu uniform ba,suci wannan uwar kwalliya suna juyawa malamai kwankwaso,Kuma ahakan ake neman miji nagari....,bazan Iya cigaba da zama anan ba Sadiya,baqin cikin wannan yarinyar zai Iya illata ni,idan Kinga zaki Iya cigaba da Zaman jiran abincin, to bismillah Nina tafi,wannan horon yunwa har Ina? ai sai asa ulser ta tatashi". 


tana wannan sababin ,tajuya cikeda iko da izza irinta yayan mulki ta wuce part dinta. 


Mama Sadiya tayi murmushin qarfin hali a hankali tace"Allah yarufa asiri"



Sannan tadubi yarinyar ta Nabiha dake gefenta tana daddanna waya, tajuya taga tabbas Hajiya kilishi tashige part dinta, sannan tace"Nabiha yi maza kije kitchen idan akwai aiki a wajan Mamyn Mawahib ki taimaka mata"


Nabiha ta amsa cikin ladabi, sannan tashige kitchen din, Mama Sadiya saida tasake kallon part din Kilishi ta tabbatar de Hajiya Kilishin bataga lokacin da Nabiha tashiga kitchen dinba,sannan tasaki ajiyar zuciya ta wuce nata part din,tun dazu taso tatura mata Nabiha,domin ta taimaka mata da aiki tunda Mawahib din taje islamiya,to amma tsoro dakuma shakkar Hajiya Kilishi yahanata.


Tana shiga falonsu ta ajiye salat din ta wuce dakin ta tayi sauri ta watsa ruwa,ta futo Sanye da riga da wando,ta zauna adaya daga cikin rantsatstsun kujerun falon Masu launin ruwan toka,Sai qananun fillo dasuke Kai,ta dauki remote din esi ta kunna, sannan tafara yanka salat din cikin qwarewa,batafi minti ashirin da zama ba mamy ta shigo falon, tun daga bakin qofa ta qarewa 'yar tata kallo,tana ganin irin dirin da Allah yabata,Riga da wando ne a jikinta baqaqe, wandon gaba dayansa Iya gwiwarta yatsaya,rigar Kuma batada banbanci da vest saboda ko hannu Bata dashi,sai farar hula shara-shara Wanda kana Iya hango tulun gashin da Allah yabata, Wanda ta gajeshi a wajan mamy, a hankali tasaki ajiyar zuciya tace"kin kunna esi kinzo kin saka wannan kayan, banason shirme tashi kije ki sauya kaya,idan sanyi ya kamaki fa"


Cikin shagwaba tace"Mamy Ana Kiran sallah zancire fa"


Cikin tsare gida tayi mata kallo daya,babu musu ta ajiye wuqar hannun ta ta wuce dakin ta domin sauya kaya.



Lokacin sallah nayi kowa yashige dakinsa domin gabatar da sallar magrib,tana idar da sallar ta dauko Alqur'ani tabude tafara karanta inda aka biya mata dazu a islamiya,Bata dade da fara karatun ba mamy taturo qofar dakin ta shigo hannun ta daukeda counter tana dannawa,ta dubi Mawahib tace"kije kikaiwa su Yaya Abinci"


Badan tasoba tarufe Alqur'anin,tafice daga part din nasu zuwa babban kitchen din gidan,ta dauki abincin mama Sadiya tashiga part din tareda sallama,falon nasu yatsaru Iya tsaruwa da kujeru nasu launin dark green,babu tarkace sosai Bayan kayan kallo dayake falon, Kai tsaye ta wuce dinning dinsu ta ajiye abincin, sannan tashige dakin Nabiha,tana zuwa tazube akan gadon ta tace"sarkin danna waya,kina Nan kina sana'ar taki"


Nabiha tayi murmushi tace"to saina zauna shiru dan Allah? aigara indinga danna wayata"


Mawahib tace"hakane Kam,Nima yanzu tunda mungama exam ai yanzu zan maidata qawata"


Nabiha tace"Mawahib yaushe Yaya Ashraf zai dawo?"


Saida ta juya idanunta Mai kamadana Masu Jin bacci sannan tace"wallahi bansaniba Nabiha,jiyama bayan munfuto daga last paper nayi masa flashing, amma bai kirani ba,kikirashi mana idan magana zakuyi"


Ajiyar zuciya Nabiha tayi,cikin ranta tana jinjina maganar Mawahib datace ta kirashi,tayaya ne zata samu qwarin gwiwar kiransa bayan bataga fuskar hakan awajansa ba?

Cikin basarwa tace"to shikkenan,babu damuwa"


Cikin sauri Mawahib tatashi tace"bari inje inkaiwa Momy kilishi abincinta karnayi laifi"


Nabiha tace"wallahi kuwa,bare keda dama kamar qiris take jira"


Sallama tayi mata ta futo daga part din, takoma kitchen dinsu ta dauki abincin hajiya Kilishi sannan tawuce part dinta,gabanta yana tsinkewa.


Da'ita taci karo tana Bude kofar falon,qiris yarage subugi juna, cikin sauri Mawahib taja baya


Cikin 6acin rai Hajiya kilishi tace"Ina ganin ikon Allah ni kilishi, ai saiki dinga nocking kafin kishigo, idan anbaki iznin shigowa saiki shigo tunda bakida iko da part din bare kidinga shigowa Kai tsaye haka"


Ahankali ta sunkuyar da kanta qasa cikin ladabi tace"kiyi haquri momy, dama abinci ne nakawo"


Batareda ta kar6i abincin ba tace"bude nagani"


Cikin nutsuwa ta sauke kwandon dake hannunta, sannan ta bubbude mata abincin,Nan da Nan qamshin girkin yacika wajan,abincin ya tsaru kana gani, kasan girki ne nazamani. 


Yatsina fuska tayi tace"wanne irin gantalallen abinci ne haka zaki debo jiki kikawo min,?da alama kema haka zakije kinayi a gidan naki mijin....,kinga koma dashi kawai"


Babu musu Mawahib tarufe abincin sannan tadauko tanufi part dinsu dashi, tanajin yanda Hajiya kilishi take rufo qofar part din nata da qarfi.


Tana zuwa part dinsu dayake babu Nisa a tsakani, anan taci karo da Mamy tana zaune tana kallo,cikin mamaki mamy ta kalleta tace"yanaga kindawo da abincin?"


"Mamy nakai mata tace in dawo dashi"


Cikin yanayi na rashin damuwa Mamy tace"to Bari inkai mata dakaina"


Mamaki yacika Mawahib, babu musu tabata kwandon abincin, mamy ta karba tafice daga nasu part din tanufi part Hajiya Kilishi. 


Tana zuwa tatura kofar falon tashiga bakinta dauke da sallama,falo ne har falo,yaji kayan qawata gida da lafiyaiyun kujeru milk color,tareda kafet Mai mutuqar laushi dawani daddadan qamshi dayake tashi gamida sanyin esi,can gefe inda dinning yake, anan ta hangi Hajiya Kilishi tana qoqarin hada tea, Kai tsaye ta nufi wajanta tace"yaya ga abincin angama, Mawahib tacemin kince adawo dashi, kiyi haquri Yaya yau dinne munsamu marasa lafiya a asbiti dayawa,Ina shirin tahowa aka kawo wata mata tana naquda,nice natsaya nakula da'ita harta haihu,sannan nataho gida shiyasa na Makara bandawo da wuri nayi abincin ba, amma kiyi haquri Yaya"


Hajiya Kilishi tace"ina ganin ikon Allah ni Kilishi,nace kinyi wani laifi ne Maryam?kawai abincin naki ne yau bazanci ba,kinyi wata shinkafa haka a tsatstsaye bata dahuba,kiyi mana abincin da muka saba Namu na gargajiya kinqi, saina ki na Yan zamani, kega ma'aikaciya,wannan naman gandar daga ganinsa ko silala baiyi ba bare ayi batun dahuba"


Cikin ladabi tace"kiyi haquri Yaya, me kikeso nadafa miki yanzu?"


Hajiya Kilishi ba tace komai ba, tajuya tabar mamy a tsaye a wajan tashiga dakinta,mamy tasaki ajiyar zuciya ta wuce takai abincin dinning, sannan ta futo daga part din. 


Tana komawa part dinsu taga Mawahib a zaune tanashan farfesun data gama a hankali cikin yanga kamar batason ci,Wanda a zahiri ba yanga takeba,haka cin abincin yake, hankalinta yana kan TV, tana ganin shigowar mamy, ta ajiye plate din dake hannun ta takoma kusa da ita ta zauna, ta dora hannayen ta akan cinyar mamy, sannan ta kalleta cikin damuwa tace"Mamy, Wai dan Allah meyasa Momy Kilishi bata sona?menayi mata Mamy?"


Cikin kwantar da hankali mamy taqarewa 'yartata kallo tana ganin tsantsar yanda take kama da mahaifinta, a hankali tace"tana sonki mana,itace tace miki bata sonki?" 


"Mamy bata sona,dazu har cewa tayi wai itakam taga irin mijinda zan aura...,Mamy ahaka zamuci gaba da zama ne komai akai kinayin shiru?har cemin fa tayi wai nima ahaka zan qare danawa mijin idan nayi aure"


Cikin sauri mamy tace"insha Allahu ba'ahaka zaki qareba,mijinda zaki aura lafiya kalau zaki zauna, ba zakiyi irin wannan rayuwar ba"


Ahankali Mawahib tasaki ajiyar zuciya Jin furucin mahaifiyar tata,sannan tace"to Mamy meyasa ke bata sonki?"


"Wai waye yace miki bata sona? Kawai halintane haka, banason tambaya Mawahib,kitashi kije ki kwanta"



Mawahib littafin kudi ne, zaki biya naira 500 kacal, kokuma katin mtn 


0164549488 

Amina muhammad 

GTbank 


08033300034 







Amnah El Yaqoub ✍🏻



💗MAWAHIB💗

(Hot luv)

Writing By Amnah El Yaqoub


3&4


Mawahib littafin kudi ne kibiya 500 kacal ki karanta cikin salama 

0164549488 

Amina muhammad 

GTbank 


Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 




Ba dabi'arta ce yin musu da mahaifiyar tata ba,danhaka babu musu tatashi ta dauke sauran farfesun datake ci takai d'an qaramin kitchen dinsu dake cikin falonsu,sannan ta futo tazo dining tazuba wata uwar madara a cup, tazuba ruwan zafi kad'an, tad'auki cornflakes d'in dake gefe tazuba acikin madarar, sannan ta wuce dakinta.

Mamy tana ganin shigarta daki tasaki ajiyar zuciya,yanzu har Mawahib yarinya 'yar shekara sha takwas tagane tsanar da Hajiya kilishi tayi mata harta fara sata agaba tana tambayarta dalili? Itakam meta tsarewa matar nan ne? aikin gomnatin datake ne yazama matsala? kokuma wannan ne sakayyar dazata mata bayan rainon yaranta datayi mata Abaya? 


Labarinsu:

GIDAN ALQALI....,sunan da ake Kiran gidan dashi Kenan. 


Duk unguwar inde kace gidan Alqali to kowa yasan cewa gidansu Mawahib ake nufi,Alqali mutun ne shi mai ra'ayi d'aya, baya magana biyu,yanada dattako,kowa nasa ne, yanada faram-faram da mutane,kowa shedar kirki yake masa,amma duk da wannan sakin fuskar tasa hakan bai hana yakasa gudanar da gidansa yanda yakeso ba,shine yake kafa doka agidan,duk abinda yabada umarni shi akebi,kasancewar shine babba a gidan,sai qannansa guda biyu Alhaji khaleed dakuma qaramin su Alhaji Isah. 

Alqali fari ne tas,zaka Iya cewama ba bahaushe bane, amma bahaushe ne cikakke mutumin garin kano, yanada sauqin kai, kuma baya goyon bayan rashin adalci,tun yana qaramin ma'aikaci yake kokarin yin aikinsa da gaskiya da amanah,har Allah yabashi matsayin Alqali,wanda yazama abun koyi a wajan sauran Alqalai,babu ruwansa da kar6ar cin hanci, aiki kawai....🤗


su uku ne rak a wajan iyayensu wanda suka mutu suka bari,Alqali Ibrahim shine babba,da matarsa daya tun auren saurayi da budurwa wato HAJIYA KILISHI,lokacin da akayi auren sunsha surutun mutane ganinta fara tas kamar ba yar hausawa ba, shima kuma fari, wannan yace anhada kyau da kyau za'a ga irin yaran dazasu haifa,ire iren wannan surutun tun yana damunsu harya dawo yazame musu jiki, suna zaune lafiya tsawon wasu shekaru,Hajiya kilishi itace take kula da duka gidan zatayi girki Alhaji khaleed da Alhaji Isah zasuzo suci abincin su sutafi harkar gabansu. 

Tsawon lokaci shiru shiru babu haihuwa, tun 'yan gulma suna saka ran ganin abinda zasu haifa har suka haqura, saida aka dauki wasu shekaru kafin ubangiji ya azurtasu da samun haihuwa, karon farko Hajiya kilishi ta haifi yaranta 'yanbiyu dukansu maza,lokacin da akayi haihuwar kai tsaye Alqali yace a dinga 6oye yaran,saboda Allah yayi musu kyau kamar 'ya'yan larabawa,Kuma bakin mutane wani bazai furta Alkhairi ba, sun dauki kyan uwa dakuma na uba sun hada waje daya, sunada mutuqar shiga rai babu wanda zai gansu baiji aransa yana qaunar yaran ba, ranar suna aka sakawa babban sunan mahaifinsu Alqali wanda yarasu,sai suke  kiransa da ASHRAF,sai qaramin wanda aka sanya masa sunan mahaifin Hajiya Kilishi, suna kiransa da ARYAN....


Tun lokacin da kilishi ta haihu,take nan-nan da yaranta,kwata kwata batason abinda zai ta6a mata lafiyar 'yanbiyun ta, tanaji dasu kamar ranta,musanman ARYAN, wanda yaci sunan mahaifinta,ta dauki duk wani hope d'inta, ta dorashi akan ARYAN,idan har ta yiwa Alqali laifi to ta hanyar yaran yake hukuntata, saboda yariga yagano cewa yaran nata sune weakness dinta,tun suna zama Hajiya kilishi take gane-gane, yau taga maciji gobe kunama,idan d'aya yana kuka tad'aukeshi tana lallashinsa shima dayan saiya fara kuka,tarasa yanda zatayi ta lallashe su duka su biyun saboda haka saita ajiye d'aya idan d'ayan yayi shiru saita lallashi d'ayan,to duk ranar datayi hakan abincin gidan baya ciyuwa,haka zata dinga sakawa abinci wuta qarshe saide ayi asarar sa,data gane saitake had'asu duka su biyun take lallashin su,d'aya abaya,daya a hannu, daga lokacin bata sake ganin kunama ba,sai lokacin dasuke rarrafe idan sukai ta'adi tad'an dakasu alamun abinda sukai ba daidai bane,tana barin wajan taga wata baqar kunama,sai wata aminiyarta tabata shawara akar6o musu abincin maqota azuba musu akan murfin tukunya bazata sake ganin komai ba,haka akayi kuwa taje maqota takar6o abinci, tadauko murfin tukunya zata zuba musu Alqali yace karta fara, wannan duk canfi ne na mutane, Allah ne kawai yake kawo kunama amma ba yayansa ba,duk surutun mutane ne. 

a hankali rayuwa taci gaba da tafiya 'yanbiyu suka fara tafiya har suna fita kofar gida wasa,ba'a Isa adakesu ba yanzu Hajiya kilishi zata sa6a mayafi koda sanin Alqali ko babu saninsa,zataje har gidan yaron daya dukar mata 'yanbiyu tarama musu, sannan takamo 'ya'yanta sudawo gida, wannan halaiyar kwata kwata Alqali bayajin dadinta.


Amma hajiya kilishi inde akan yaran nan ne, to zaka Iya Jin kanta dakowa, kasancewarta yar sarauta idan aka taba su Ashraf,mantawa take ita yar sarauta ce taje ayi wacce za'a yi,kokadan batason abinda zai ta6a mata lafiyar su,lokacin da aka haifeta, a lokacin a kayiwa mahaifinta sarauta, shiyasa mahaifinta ya Sanya mata suna KILISHI.


tashin datayi a gidan sarauta yasa take wa kowa kallon raini da Kuma nuna Isa da taqama da izza,kana ganin yanda take gudanar da al'amuranta zakasan cewa jinin sarauta yana yawo a jikinta,ahakan ma saboda Alqali a tsaye yake agidansa, shiyasa take rissinawa. 


Bayan Alqali Ibrahim Sai qaninsa na biyu Alhaji KHALEED,adede wannan lokacin yayi aure, yaso yazauna agidansa shi kadai amma Alqali yace babu inda zaije, ya zauna a gidan duk suyi zamansu tare babu wanda zaibar cikin gida, Alhaji KHALEED ya auri Mama Sadiya mace mai kawaici da kawar dakai akan komai, kasancewarta mace mai tsoron fitina yasa zamanta da kilishi ya d'ore,bata Isa tayi komai ba saida iznin Kilishi, komai zatayi saita tambayeta,hakan yasa kilishi take qarajinta asama,kanta yana sake kumbura tana jinta eh lalle ita d'innan fa yar sarauta ce.


Alhaji Khaleed baifi wata shida da aure ba, Alhaji ISAH shima yataso da batun nasa auren,wato d'an qaramin su, babu abinda yayi na aure komai Alqali da Alhaji Khaleed ne sukai masa kasancewar sa shine qarami a cikinsu,kuma sunaji dashi tun bayan rasuwar iyayensu,to duk abinda Isah yace yana so suma shi suke so, tun yana yaro suka shagwa6a shi abinda yakeso shi suke masa,alokacin Maryam, wato Mamy tagama degree dinta nafarko fannin Nursing,yar asalin garin maiduguri, ganin wahalar datasha a karatun ta yasa ta fad'awa Alhaji Isah cewa itafa bayan auren nan zatayi aiki, bazata bar karatun ta yatafi ahakaba,tanaso tabawa yan'uwanta mata gudunmawa ta fannin karatun ta,Alhaji Isah yasamu yayunsa su Alqali yafada musu qudurin Maryam, Nan take Alqali yace ai babu komai,aikin nata ai 6angaren lafiya ne,inde har tana son d'an'uwan nasu to babu matsala tazo tayi aikinta.


Wannan mataki da Alqali ya dauka yayi bala'in qonawa kilishi rai, tayaya suna zaune agida,za'a bar yarinya tazo cikinsu tana aikin gwamnati? me suka rasa agidan daza'a zo musu da wani fi'ili na aikin gwamnati? hukuncin Alqali baiyi mata dadi ba, daga nan ne matsalar tafara faruwa tsakanin Mamy da Hajiya Kilishi.


Bayan Maryam, wato Mamy tayi sati buyu a gidan Alqali, a lokacin Alqali ya tarasu duka su ukun yayi musu maganar girki, tunda harkarsuce tacikin gida Yaya suke ganin zasu tsara girkin?


Nan take Mamy tace tunda tana aiki, tana ganin kawai kowa yayi nasa girkin,ba zai iyu ace saita dawo daga wajan aiki  sannan zata dafa musu abinci ba, lokaci daya Alqali yace hakan bazai iyu ba, shida qannansa qwaya biyu rak a duniya bazai iyu su raba girki ba,hakan yana nufin kenan dan autan su Alhaji Isah haka zata dinga barinsa da yunwa harsai ta dawo aiki ne zata dinga dafa masa abinci, a lokacin Mamy saita nuna masa cewa inde cikinsu ne daga ita Sai mijin ta Alhaji Isah,bazata bar mijin ta da yunwa ba, amma Alqali yace Bai yarda da wannan batu nataba,dole zasu hade girkin su, sai Mamy tace to tunda ita tana fita aiki, tana neman Alfarmar su Hajiya kilishi da Mama sadiya abar mata Iya weekend su sai suyi sauran ranakun, nan take Hajiya kilishi ta watsawa Mamy harara tace bazai iyu ba, a dinga yi kwana bibbiyu, babu wani weekend daza'a barmata,Alqali baiji dadin furucin kilishi ba, amatsayinta na babba a cikinsu kamata yayi ace taja matan qannan nasa a jikinta, su zama qawayenta kuma qannanta, koba komai matar autan nasu alfarma tanema akan su bar mata weekend din,kuma babu wanda yawuce yanemi alfarma, to har zai dauki mataki saiya fasa ganin harkar suce ta mata, daga haka taron ya tashi.


Ko wata uku ba'a yi ba,Hajiya kilishi taga Mamy bata musu girki akan lokaci, saita dawo daga wajan aikinta sannan ne zata fara shirin dora musu abinci, sauqinsu daya idan aikin yamma takeyi, to shine kafin tatafi take musu girkin,kuma Mamy Bata girkin gargajiya,saboda tana aiki da kudin ta take kashewa tayi girki mai rai da lafiya,wanda duk wanda yaci, saiya so ranar girkin ta yasake zagayo wa, to daga nan ne Kilishi tayiwa Alqali magana yakamata asake zama akan batun girkin nan, Maryam bata musu abinci akan lokaci idan aikin safe ne da'ita saita taso wajan karfe uku na aana sannan za'a fara shirin dora musu abinci,tosu yanzu sun yafe gara ta dinga yi da weekend din kawai,(😂) 

Alqali yayi murmushi bai tanka ba,tun farko abinda yahango musu kenan, shiyasa yaso subata weekend din, tunda Alfarma ta nema,sannan itace qarama a cikinsu kuma matar dan autansu, kamata yayi su ja yarinyar a jikinsu musanman ma ita Hajiya kilishi tunda itace babba, amma mugunta ta rufe mata ido, takasa gane hakan tun farko.


Haka Alqali yayi mursisi yaqi saka baki akan maganar girkin.


Mamy tanada masifar haquri,zaiyi wahala kaga 6acin ranta,tana zaune da kowa lafiya a cikinsu Kuma da zuciya daya, tanajin dadin yanda Mama Sadiya take janta ajiki,nan da nan sai suka saba, suka zama kamar qawaye,duk lokacin da Hajiya kilishi ta 6atawa mamy rai, Mama sadiya ce take bata haquri, kuma Mamy bata ta6a fadawa mijinta ba, saide tabar abun aranta.


Tunda tazo gidan ta lura kwata kwata Hajiya kilishi bataso su Ashraf suzo wajanta,koda wasa taga sunyi hanyar part din Mamy toda gudu zataje ta janye su, abun baya yiwa Mamy dadi, tana bala'in qaunar yaran, amma babu damar daukar su saide tadinga leqensu daga nesa. 



Hajiya kilishi ganin Alqali yaqi kula maganar ta dangane da girki, hakan yasa wata rana Mamy tana girki Hajiya kilishi taje ta sameta a kitchen din tayi mata tatas,Mamy ko uffan batace mataba, ganin Mamy taqi tanka mata yasa tafara zaginta, tayi mata zagi nacin mutunci,hartana fada mata yar gidan talakawa wadda take aiki saboda talaucin iyayenta, juya....wacce bata haihuwa tunda tazo gidan ko 6ari bata ta6a yiba(😥) 


Mamy bata ramaba saide kuka da takeyi duk da hakan tana bata haquri,ashe duk abinda ake Alqali yana ganinsu yazo wucewa,cikin 6acin rai yayiwa kilishi magana cikin tsawa,itama 6acin rai ya rufe mata ido tarama,nan take babu 6ata lokaci Alqali yabawa Hajiya kilishi jan Kati, yayi mata saki daya(🙆🏻‍♀️)


Sannan agabanta yaje yadauko Ashraf da Aryan yace yabawa Mamy su halak malak(😳)


A wannan lokaci kilishi hauka ne kawai batayi ba,taji tsanar Mamy tasake nunkuwa aranta,tanaji tana gani haka tabar 'yanbiyunta a hannun matar data tsana tafice tabar gidan Alqali.



A lokacin Mamy tajasu ajiki sosai kamar 'ya'yanta,musanman yanda takeson haihuwa amma gashi Allah bai bataba, idan taje asbiti taga mata sun haihu tadinga kula da yaran kenan bata kyamatarsu, hakan ne yaja mata farin jini a wajan aikinta,dama hajiya kilishi ce tayi mata iyaka da 'yanbiyun, amma tana sonsu sosai, Alqali yana danqa mata su kuwa tabude bakin aljihu tadinga yimusu siyaiya, shikuma yaro inde za'a bashi, musanman kayan chocolate to yanzu zaka siyeshi, tun basa sakin jiki da'ita har suka dawo suka saba da'ita,sune suka fara kiranta da MAMY, tun suna yara Mamy ta lura Aryan baya son surutu,yafison ya zauna yanata game da wayarta,koda tajashi da zance irin dan surutun nan na yara saide taga yace mata eh kokuma a a,saide in yanason abu zaice Ma-my inason sweet, kokuma Ma-my ruwa, kai tsaye de yace Mamy,ba zakaji yafadi hakaba, wannan saide Ashraf, amma shide Aryan a rarrabe yake kiran Sunanta.

Tayi amfani da hikima sosai wajan shawo kan yaran,haka kawai tana dawowa daga wajan aiki zata cire uniform dinta tasa qananun kaya tadinga goyasu sunata wasa saide Alqali yajiyo su sunata qyalqyala dariya,da yamma haka zata musu wanka ta shirya su tsaf suyi kyau, sufuta wajan wasan yara takai su suyi wasa son ransu, sannan su dawo gida,harta kai takawo idan zata fita aiki ma dasu take tafiya, kowa yasan su a wajan aikinta,qawayenta na wajan aiki har chocolate suke kawo musu, wasu Kuma kayan wasa suke kawo musu,mutane dayawa suna tunanin ma yaranta ne, saide su din farare ne sosai kuma identical twins kwata kwata baka banbance su,amma ita kam sarai tana ganesu, kai tsaye zata nuna Ashraf tace wannan ne babba, shikuma Aryan rashin surutun sanema yakesa nan da nan aganeshi, amma kuma idan shida Ashraf ne har mamakin yanda yake surutu take,inde dagashi sai dan'uwan ne yanzu zakaji yanata masa magana, daga qarshe a kaure da fad'a, saide fadan nasu baya zuwa ko'ina zakaga sun shirya, Mamy tasan halin kowa a cikinsu, Ashraf gaba daya halin Alqali yad'auko, babu ruwansa, inde yazo waje sai kasan yazo,haka idan tahada musu tea dasafe, gashi de tea din bawani zafin kirki gareshi ba,haka Ashraf zai dauka yasha abunsa, yayinda Aryan yadebo halin Hajiya Kilishi gaba d'aya,tun yana qarami Mamy ta fahimci yanada son girma, baya son raini, gashi de shine qarami amma Ashraf bai Isa yace ya girmeshi ba,kuma kokadan bayason zafi,shide kawai sanyi, idan tahada ruwan dumi zata musu wanka nan da nan zai fara kuka shi bazata masa da ruwan dumi ba saide na sanyi, ita kuma tana tsoron kar ruwan sanyin yayi masa illah, haka zata riqeshi yana kuka yana cewa ruwan da zafi, ahaka suke wankan kullum, idan Ashraf yaga Aryan din yana kukan ruwan zafin saiya saka hannunsa acikin ruwan, ya kalli Aryan din yace kaji ruwanfa babu zafi(😂) 

Darana kuwa taci karo dawata baqar kunama a qofar dakinta,cikin tsoro tajuyo aguje,suma suka bita da gudu suna dariya,mamaki ya kamata,tadauko abu zata kashe Ashraf yace shine zai kashe,yasaka hannu ya dauki kunamar shima Aryan yace saiya bashi,shikuma Ashraf yahana,lokaci daya kunama tahada su fada, ganin ana qoqarin fada akan kunama kuma gatanan tana ganinta qiri qiri a hannun Ashraf lokaci daya Mamy ta suma a tsaye, batasan lokacin data saki qaraba,tariga tabayar kunamar zata cutar dasu. 

ganin tana kuka yasa suka dawo wajanta suma suna kuka,saida tagama kukan tafara lallashin su anan taga babu kunamar a hannun su babu dalilin ta,haka tayi shiru da bakinta bata tambayesu Ina take ba. 



Haka Mamy tadinga kula dasu, yanda take kaffa-kaffa dasu yasa su kayi mugun sabo da Mamy, yanda suke liqe mata saika rantse itace ta haife su,ko dare yayi bazasu kwanta ba saide a jikinta, haka zata tofesu da Addu'ah har suyi bacci, saide cikin dare ta lallaba ta gudu wajan Alhaji Isah,suyi abinda zasuyi (🙈) 

kafin ace sun farka sun fahimci bata wajan su zata dawo cikinsu suci gaba da baccin, kuma hakan kokadan baya damun Alhaji Isah saboda qarancin kulawar dayake samu a wajanta, saima dadi da yakeji yanda take riqe 'ya'yan dan'uwansa kamar itace ta haife su.


Sun kwashi watanni a wajan Mamy,yau suyi fad'a tadinga rabiya, gobe azauna kalau ahaka har sukayi mugun sabo da'ita, komai Mamy,bakajin komai a bakin su sai maganar Mamy, ta rainesu yanda ya kamata, raino wanda zaiyi wahala yaro ya manta da uwar rainon sa. 



Ganin Alqali yayi mursisi baije bikon Hajiya kilishi ba, hakan yasa tadinga yiwa yan gidansu magana har sukuma suka yiwa Alhaji Khaleed da Alhaji Isah magana, suka basu haquri akan laifin kilishi suka roqesu Alfarmar suyiwa yayansu Alqali magana akan dawowar kilishi dakinta,domin sude bazasu Iya tunkarar sa da maganar ba, domin kuwa Alqali akwai kwarjini,hakan akayi kuwa, Alhaji Isa da Alhaji Khaleed sune suka shige gaba, aka maida auren Hajiya kilishi da Alqali Ibrahim,suka sake bawa yayan nasu haquri akan katsalandan din dasuka masa, badan Alqali yaso ba, haka yayi haquri kilishi ta dawo dakinta, bayan alqawari data dauka masa cewa hakan bazata sake faruwa ba. 


Mamy kuwa tayi tunanin ganin hajiya Kilishi tadawo zaisa su Ashraf su koma wajanta, saitaga yara sunyi mursisi sunqi komawa wajan Hajiya kilishi,irin murnar nan ma taganin uwa sude ba suyi ba, saida Alhaji Isah yasata tahada musu kayansu sannan yace tarakasu wajan mahaifiyar su, a lokacin data gama hada musu kayan harda kukanta, a lokacin yarinta tasa basu fahimci kukan me takeba,Ashraf ne yafara matsowa yana goge mata hawayen,amma shikam Aryan da bai Iya lallashi ba shima saiya kwanta a cinyarta yafara kuka (😂) 


Haka tarakasu wajan Hajiya kilishi, tayi mata sannu da zuwa ta amsa mata da qyar, itade Mamy ahaka ta futo tabarsu tareda mahaifiyar su.

Tunda Hajiya kilishi tadawo taji suna kiran Maryam da Mamy,babu 6ata lokaci tahanasu fadar sunan, saide suce Anty, sukuma basu saba da Anty ba, da Mamy suka saba, dan dolansu babu yanda suka Iya shine suke kiranta da Anty Mamy,maimakon suce Anty kadai,sai suka hada mata duka biyun suke kiranta da Anty Mamy 


Bayan wasu shekaru suna kammala primary school dinsu Mama Sadiya ta haifi yarta mace, aka sanya mata sunan Mahaifiyar su Alqali, suna kiranta da NABIHA, adede lokacin Alqali yafitar dasu qasar waje karatu,saida karatun su yayi nisa sosai sannan Allah yabawa Mamy ciki,ta haifi yarta mace mai tsananin kyau kamar balarabiya,mahaifinta ya sanya mata suna RUQAYYA,Mamy kuma take kiranta da MAWAHIB.

 

ma'anah (MAI YAWAN KYAUTA). 


Mawahib tun tana qaramarta Allah yayi mata diri,tanada jiki mai daukan hankalin samari, tanada sanyin hali kamar Mamy, kwata kwata batada hayaniya,Allah yayi mata baiwar hips kamar ita ta sakawa kanta,saide batada cikar qirji, boobs dinta ba manya bane kuma ba qananu bane, 'yan madedetane hakan ne yasa suke a tsaye qyam....

Mamy da Abbanta sunaji da'ita,sosai Mamy take siyo mata qananun kaya daga nashan is'ka harna bacci, haka zata saka kayan ta tayi uzurinta Iya part dinsu babu wanda yake mata magana, haka 6angaren kayan kwalliya ma ba'a barta abaya ba,idan Mawahib ta dauki kwalliya babu musu zakace mata yarinyar Momy da Daddy ce,saide bahaka bane,kawai Mamyntace ta tsaya mata take shigar ta yanda taga dama, tunda samarin gidan bawani zama suke ba. 



Aqasar waje su Ashraf sukai secondary school dinsu,suka dora da jami'ah,bayan sungama jami'ah suka nunawa Alqali cewa suna so suzo gida, yace su dakata suyi masters tukunnah,duk tsawon wannan shekarun Mamy tana nan a ransu, tun basa fahimtar mahaifiyar su Hajiya kilishi bata son Mamy, har suka dawo suka gane,idan suka tambaye ta awaya Ina Mamy nan da nan Hajiya kilishi zatayi kicin kicin darai ta nuna musu batason mu'amularsu da wannan matar.



Haka sukai haquri basuzo gidaba saida suka kammala karatun su kamar yanda Alqali yakeso, sannan suka dawo gida, anan sukaga an sauya tsarin gidan, ansake masa fasali, anyi masa get biyu,gida yakoma gidan zamani ankashe masa dukiya, a wannan lokacin Alqali yayi ritaya,yana zaune agida yana hutawa,duk wani nauyin kula da gidan yakoma kan Alhaji Khaleed mahaifin Nabiha, saikuma Alhaji Isah mijin Mamy, gida de ya sauya, saide halin Yan gidan dabai canja ba(😂),tunda suka dawo Ashraf yaga Nabiha da Mawahib shikkenan yake jansu a jikinsa, musanman Mawahib din Mamy, yana bawa Mawahib kulawa yanda ya kamata, jinta yake aransa kamar me,duk abinda takeso nan da nan zakaga yaje yasiyo mata,amma kwata kwata baya bawa Nabiha wannan damar, tsakanin sa da'ita saide gaisuwa amma fuska asake yake amsawa, shikuwa gogan ko a jikinsa, daga Mawahib din,har Nabihan, gaba dayansu baya shiga sabgarsu, kwata kwata baya son raini, suma su Mawahib da sukasan halinsa koda wasa basa shiga harkar sa. 


Bayan sunyi bautar qasa Ashraf yasamu aiki a NNPC dake Rivers state,shikuma Aryan dama burinsa yasamu aikin soja,kuma yasamu, har yakai matakin CAPTAIN,shiyasa su Mawahib suke kiransa da YAYA CAPTAIN, yana aikinsa a Abuja,bai cika zuwa gida sosai ba, Ashraf ya fishi zuwa gida.


Kamarsu daya da Ashraf sak,zaiyi wahala ka banbance su idan suka saka komai iri daya,suna fad'a ajunansu,saide fad'an nasu babu inda yake zuwa nan da nan zasu shirya, idan Ashraf yayi budurwa shima Aryan yana ganinta zaiji yana sonta, daga dawowar su daga qasar waje zuwa yanzu dasuke aiki Ashraf yayi 'yanmata dayawa, amma wai irin ya nunawa dan'uwansa sabuwar budurwar da yayi, sai shima Aryan din yace wallahi sonta yake (😲)


Babu yanda Ashraf zaiyi saide ya haqura da yarinyar tunda bazai iyu su auri mace daya ba, sunyi haka yakai sau biyar,kuma shima Ashraf din dan masifa kamar anyi masa dole muddin yasamu budurwa saiya nunawa Aryan ita,shikuma yana ganinta kai tsaye zai fada masa wallahi Shima yana sonta,haka Ashraf din zaiyi haquri yabar masa yarinyar kokuma su barta duka su biyun,shikuma captain Aryan baya kula yanmata bare ayi tunanin zai samo wata, yana zaune saide in dan'uwan yasamu, yace shifa duk duniya shima wannan yarinya yakeso,haka zasu haqura da yarinyar gaba dayansu.


Ashraf yanason ruwan zafi,halinsa sak irinna Alqali, shiyasa koda yaushe yake ta'ammali da tea,kuma babu ruwansa da zafin tea dinnan haka zaisha abunsa, amma captain Aryan bahaka bane, kokadan baya hada hanya da ruwan zafi, yafison ruwan sanyi, duk sanyin da ake agari bazaiyi wanka da ruwan zafi ba, dana sanyi zaiyi, wannan dabi'arsu ce tun suna Yara.


Har zuwa wannan lokacin Hajiya kilishi bataso su ra6i Mamy,amma har yanzu suna sonta,kuma suna mu'amula da'ita dan dole Hajiya kilishi ta haqura tabarsu.


Fatan Alqali da Hajiya kilishi shine su samu mata suyi aure, Hajiya kilishi ta dauki buri ta dorawa yanbiyunta kawai so take su samo mata yanmata nagani nafada na kece raini suyi aure irin auren 'ya'yan Masu dashi dakuma 'ya'yan masu mulki, amma har yanzu basu kawo kowacce yarinya gida ba,har gara Ashraf yana dan kula Mawahib,yana Jin dadi idan yaganta, yana sakata aiki kamar gyaran dakin su,girki marar wahala,yana wasa da dariya da'ita, amma baya kula Nabiha sosai, amma ita kullum tana tasa,bata da aiki sai tambayar Mawahib yaushe Yaya Ashraf zai dawo,? Sunyi waya da Yaya Ashraf?



Cigaban labari:



Dasafe Mamy tagama shirinta tsaf domin tafiya wajan aiki, tashiga dakin Mawahib taganta a kwance a gadon ta tayi d'aid'ai tana bacci,dogon gashin kanta duk ya barbaje akan katifar,tana sanye cikin wata yar 6ingilar rigar bacci gaba daya rigar iyakarta rabin cinyarta,hakanne yasa fararen cinyoyinta suka futo muraran,babu bra ajikinta amma yan madaidaitan boobs dinta suna nan a tsaye cak har kana Iya hango tsinin nipples dinta.


Mamy bata damu da kayan dayake jikin Mawahib ba, asalima itace take siyo mata su,tana duba agogon dake daure a hannun ta,mai mutuqar tsada, sannan tasaki dan qaramin tsaki tace"Mawahib tashi daga baccin nan haka, kina sana'ar taki ta bacci ko gidan baki gyaraba"


Cikin shagwaba tace"Mamy ramuwar baccin exam nake fa..."


"kitashi haka kiyi break fast kar yunwa ta kamaki,akwai kudi agefen gadona Abban ki yace ki dauka kije gyaran jiki,karki yarda kidawomin gida da wannan gashin naki babu gyara"


Idonta a lumshe tace"to Mamy saikin dawo"


Bayan Mamy tafita a hankali tazuro qafafunta qasa, tashafa shafaffan cikinta,sannan ta wuce toilet tayi brush, ta futo ta gyara musu part din nasu, ta kunna turaren wuta, ko'ina yadauki qamshi, sannan takoma daki tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga Abaya,wadda ta bude daga qasa, daga sama kuma ta fitar da shape din qirjin rigar, abincin tazuba tafara ci a hankali kamar bataso, adede lokacin Alhaji Isah Yafuto cikin shirin fita aiki,cikin sauri ta gaida shi, cikin mamaki yace"a a,karfe nawa yanzu baki tashi kinci abinciba sai yanzu kike break fast? meyake damunki ne Ruqayya? "


Saitayi wani sororo kamar bada ita yake magana ba,saboda ita kanta mantawa take Sunanta Ruqayya, saboda Mawahib din da'ake fada mata ya6oye Ruqayyan. 


Cikin shagwaba tace"Abba bacci nakeji sosai shiyasa"


Kansa ya girgiza yace"kiyi sauri kifuto Ina jiranki saina saukeki kafin in wuce"


Bai jira amsar taba yawuce, cikin sauri tahada tea tasha, sannan tadauko hand bag dinta yar qarama mai kyau, tazuba kudin da Abban yabata, sannan ta futo, key tasa tarufe part din nasu, sannan ta wuce part din Hajiya Kilishi kamar yanda Mamy takafa mata doka kullum taje part din kowa ta gaishe su, tun kafin ta qarasa part din taji wani qamshi mai dadi ya bugi hancinta,a hankali ta lumshe Idonta, sannan ta bude, qamshin yayi mata dadi, cikin nutsuwa tatura kofar falon tashiga, dashi tafara yin tozali da alama saukar dare yayi, shiyasa batasan da zuwan sa ba,kyakykywan saurayi ne mai kyau da aji kana ganinsa kasan zaikai shekara 37,sumar kansa sai wani sheqi take,ga wani saje daya sake qawata farar fuskar sa,yanada dan qaramin lips launin ja. 


tun kafin tagama qarasowa cikin falon Hajiya kilishi tafara watsa mata wani irin mummunan kallo,duk da tana shakkar Hajiya Kilishi, hakan baisa ta 6oye murmushin ganin Yaya Ashraf ba, cikin ladabi ta tsugunna tace"Momy Ina kwana?"


Daqyar Hajiya kilishi ta amsa,murya can ciki tace"lafiya..."

ta amsa tana qarewa surar jikinta kallo, shikuwa Ashraf kamar wanda tatafi da imanin sa tana shigowa haka yabita dawani irin mayen kallo,shi kansa baisan lokacin dayabita da wannan kallon ba,da alama yama manta da'inda yake zaune(😲) 


Tun kafin Mawahib ta gaida Ashraf,Hajiya kilishi tace"Ina ganin ikon Allah ni kilishi.....ke Kuma irin tarbiyar da uwar taki take baki kenan? bazaki Iya jira akaiki gidan miji ba tun a titi zaki fara nunawa duniya jikinki? Kuma ahakan kuke neman miji nagari ko? banga sallaman man dazai kwasa ba...."(😢) 


Cikin sauri Ashraf ya runtse idonsa,bayason wannan furucin datake yiwa Mawahib,bayajin dadinsa ko kadan. 


domin ya katse zancen, ya Kalli Mawahib wadda ta sunkuyar da kanta qasa tana wasa da dogayen yatsun hannunta, qiris yarage tafashe da kuka, yace"Mawahib zaki fita ne?" 


Cikin sanyin jiki tadaga masa kai batareda tace uffan ba,domin kuwa bazata Iya magana ba, inde tace zatayi magana to kuka ne zai biyo baya,a hankali tatashi ta futo daga falon. 


Tana fita Hajiya kilishi ta kalleshi Cikin fada tace"Ashraf kafita daga harkar yarinyar nan,banason Jin wata magana daga baya,koda wasa banason ganin wani abu yashiga tsakanin ku,naci buri akanku sosai,sonake kuyi aure nagani nafada auren kece raini,shiyasa ARYAN yake birgeni, saboda baya shiga sabgar wannan yarinyar"

Ashraf yayi murmushi tareda shafa sumar kansa yace" kiyi haquri Momy"


Tana barin part din Hajiya kilishi qunci da damuwa yasa ko kallon part dinsu Nabiha batayi ba bare tashiga, wani irin kuka ne ya taho mata,to amma data tuna Abban ta yana jiranta a waje, zai gane tayi kuka, Sai tayi sauri tadaga fuskarta sama, tana kokarin maida hawayen,tarasa me matar nan take nufi da'ita, nafarko ita batace tana son 'ya'yantaba, tarasa meyasa tasata agaba,kuma Mamy taqi fada mata Dalili.....








Yaya Ashraf anya kuwa? 🤔🤔








Amnah El Yaqoub ✍🏻


💗MAWAHIB💗



Writing By Amnah El Yaqoub


5&6




Bayan tagama abinda take bata dawo gidanba saida ta daidaici lokacin dawowar Mamy daga Asbiti yayi, sannan itama tadawo gidan, gashin nan nata kuwa yasha gyara sai qyalli yake,jikinta yayi sumul dashi kamar ka latsa jini yafuto, koda ta nunawa Mamy gyaran da'aka mata koda wasa bata fad'a mata yanda sukai da Hajiya Kilishi ba.



Washegari da daddare suna zaune afalo gaba dayansu,Mawahib tana sanye cikin kayan bacci riga da wando mai santsi,wandon dogone har qasa, sai 'yar qaramar riga, tayafa dan qaramin mayafi a jikinta,amma kana Iya hango yanda sumar gashinta ta kwanta a goshinta.


Abba ya ajiye cup din hannunsa mai daukeda fruit salat, yad'auki remote yana canja channel tareda fadin"dazu su Yaya Ibrahim suka tafi Abuja,sunyi min magana kozan samu zuwa to ayyuka sunmin yawa a office shiyasa nima ban bisu ba,yauce ranar da za'a karrama su ARYAN,yana d'aya daga cikin wanda shugaban qasa zai karrama su saboda qwazonsu a wajan aiki"


Mawahib dake danna wayarta tayi shiru tana Jin abinda Abbanta yake fad'a,a wannan baqin halin na Yaya Captain tarasa yanda akai harya samu yashiga jikin manya gashi hardashi za'a karrama. 


Cikin murna taji Abbanta yana fadin"Alhamdulillah Maryam kinga ma gashi suna nunawa a wannan tashar"


Cikin farinciki Mamy Tace"masha Allah,aikam gasunan,Alhamdulillah, Allah yasanya Alkhairi"


Cikin Jin dad'i Abba yace"ni gaba d'ayama sainaga Mawahib tana juyewa tana yin kama dashi,da idon,da hancin, da bakin,gaba daya na Captain Aryan ta d'auko"


Yajuya ya Kalli Mawahib da hankalinta yake kan waya ko inda TV take bata kalla ba,yace"koba hakaba 'yanmatan Abba?"


Ahankali tasaki wani murmushi mai kamada yaqe...

Sai a lokacin ta kalli tv,idonta ya sauka a kansa,kamar kullum yana nan da kyansa,kwantaccen sajen daya zagaye bakinsa irinna Yaya Ashraf yasake qawata farar fuskarsa kamar balarabe,jan lips dinsa d'an qarami mai mutuqar laushi sai sheqi yake kamar ya shafa musu lipstick,fuskar nan tasa ad'aure kana gani kasan babu wasa kamar ma baya farinciki da  karramawar da akayi masa,yana tsaye qyam ya qame waje d'aya,ga shugaban qasa da kansa yana sake gyara masa rank dinsa,ga manya manyan sojoji daga gefe kowa ya qame a tsaye, saida shugaban qasa yagama gyara masa rigarsa,sannan shikuma yasara masa,sannan aka fadi irin jajircewar dayake akan aikinsa, tareda kyautar kudi Naira million arba'in,anan aka buqaci daya daga cikin familynsa yazo su kar6i kyautar tare,kai tsaye Alqali yatura Ashraf,cikin nutsuwa Yaya Ashraf yataka yaje gaban Aryan din  suka kar6i kyautar tare,bama sai anyiwa mutane bayani ba,ana ganin ashraf wanda basu san cewa Captain Aryan 'yanbiyu neba, yau kam sun sani,tsirarun 'yanmata wanda suka samu damar zuwa wajan taron lokaci daya kallon su yakoma wajan Ashraf da Captain Aryan,kowa mamaki yake dama wannan miskilin Sojan 'yanbiyu ne?


Mawahib tagama qarewa Captain Aryan kallo, taga babu wata kama dasuke kamar yanda Abbanta yafada, banda fari dayake dashi irinnata ita bataga wani abun birgewa a wajan Yaya Captain ba bare har taji dadi dan ance suna kama.


Ganin yanda sauran sojoji suke  qara girmama shi kamar wani nagaske,hakan yasa Mawahib taji wani irin baqin ciki,sai yanzu ne tagane dalilin zuwan Yaya Ashraf gida,a hankali tatashi ta wuce dakinta.


Abba yabi Mawahib da kallo harta shige dakinta,yajuyo ya kalli Mamy yace"madam ya kamata fa asamawa Ruqayya qanne,naga tatafi daki kamar tana fishi,kuma nasan ba fishi take ba, kawai shagwa6a take ji ba'a tafi da'ita wajan taron nan na yayansu ba,shiyasa tatafi d'aki"(🙊)


Mamy tayi murmushi batace komai ba,shima Abba yayi dariya yace"emanah,tana ganin itace qarama a gidan shiyasa take shagwa6a son ranta,inda tanada qanne ai zata rage shagwa6ar"


Mamy tayi murmushi tace"Alhaji kenan,babu wani shagwa6a ita tasan meyake damunta"


Cikin jin dadi yabi ilahirin jikinta dawani irin mayen kallo sannan yace"Allah koh?"


Itama murmushin tasake yi batace dashi uffan ba,saboda tasan ma'anar kallon dayake binta dashi(🙈)


Washegari Hajiya kilishi ce ta kar6i girki,a qa'ida kuma inde itace tayi girki babu wanda take kaiwa part dinsa,saide kowa yaje yadauka,saboda itace babba,Mawahib bataje ta d'auko musu nasu abincin ba,saboda Mamy tana wajan aiki,shima Abba yafita bai dawo ba,ita kadai ce kuma ba yunwa take ji ba, tun safe aketa sallama a gidan,ana zuwa anayi wa Hajiya kilishi murnar karramawar da Captain Aryan yasamu,sai hayaniya akeyi, tana kwance afalonsu tana chat da Yaya Nabil,wani d'an kawunta dake maiduguri tana jiyo surutun mutane kala kala,bata fita d'aukar abincin ba saida taji hayaniyar mutane ta ragu a lokacin itama tagama chat d'inta,rana tayi sanyi, sannan ta futo,tana sanye cikin doguwar riga marar hannu,yadin rigar yanada laushi, daga gaban rigar anyi mata ado da baqin leshi,sai dan qaramin mayafi data d'ora akanta,babu kowa atsakar gidan,kai tsaye ta wuce kitchen tad'auko nasu abincin,futowar ta kenan daga kitchen din adede lokacin Hajiya kilishi tafuto daga part d'inta itada wata babbar mace da alama qawarta ce, cikin ladabi ta rissina tace"Momy Ina wunin ku"


Hajiya kilishi ta amsa a taqaice tace"lafiya"


Ita kuma d'ayar cikin murmushi ta amsa tana bin Mawahib da kallo harta shige part dinsu, saida taga shigewar Mawahib sannan ta maida kallonta wajan Hajiya kilishi tace"Matar Alqali,Ina kuka samo 'yar kyakykywar yarinya haka?"


Hajiya kilishi tace"Hajiya Mariya baki ganeta bane?"


Wadda aka kira da Hajiya Mariya tace"ina zansan wannan yarinyar?  duk zuwan danake bana ganinta,anya anan gidan take kuwa? Kina ganin yarinya jajir da'ita kamar wankan inji? Kiduba kiga wannan uban diri kamar ita tayi kanta,badan da 'yanbiyun samarinki a gidan ba aida nayiwa Farouq d'ina kamu..."


Hajiya kilishi tace" 'yar wajan Maryam cefa,da wanne samarin zaki had'ata?,inaaa! bade 'yanbiyu naba,har abada babu had'i, yanda kika gantannan kullum haka take yawo tana nunawa mutane jiki,ita ga tantiriya,kuma uwarta ce take koya mata komai,idan na kuskura nabari yarinyar nan ta auri d'ana aina kashe kaina, tun yanzu ma kafin ayi mata aure bad'ala iri-iri uwarta take koya mata,to inaga anyi aure? tana saka irin wannan kayan yanzu,idan tayi aure kuma wanne iri kike tunanin zata saka?kinsan 'yar maiduguri ce uwar, idan 'yarta ta auri dana kuma ai shikkenan sai yanda aka min dashi, kiduba kigani de yanda tashiga tafita a wajan malamai da bokaye saida tarabani da 'yanbiyu nah,basu Isa suzo gidan nanba saide kiga sunje part dinta sun tare,Ashraf ma dayazo shekaran jiya danyaga na tsaye masa ne, na Kuma saka masa ido,amma da abinci ma Infad'a miki saide yaci awajanta, to inda nakejin dad'i sauqina d'aya,yarinyar bata gabansu duka su biyun, musanman ma ARYAN...."



Cikin sauri Hajiya Mariya ta katse ta" ke dakata matar Alqali,wai kina nufin yarinyar nan ce 'yar wajan Maryam tagirma haka?"


Hajiya kilishi tace"hmm ai Ina ganin ikon Allah Hajiya Mariya,itace wallahi,ai kallon tsoro kikai mata,bakiga uban nonuwan taba"



Hajiya Mariya tayi ajiyar zuciya tace"to aikuwa matar Alqali tun wuri kitashi tsaye,inba hakaba kiyiwa kanki sakiyar daba ruwa..."


Cikin sauri Hajiya kilishi tace "wa?, Allah yatsare ni,ai har abada babu alkhairi a tsakanin ta da 'yanbiyu na,to Ina alkhairi ga yarinyar da batayi gadon haihuwa ba? Ita kad'ai uwarta tahaifa daga ita babu qari, ita kuwa bana tunanin ma idan tayi auren zata haihu, tunda batayi gadon haihuwa ba,to waima INA UBANTA?, har zuwa yanzu mude bamu ganshi da idonmu ba"(😳🙆🏻‍♀️tofa)


Hajiya Mariya tayi ajiyar zuciya tace"tabdi, aikuwa matar Alqali saiki dage,kuma kisawa 'ya'yanki ido sosai, kinsan maza da jarabar tsiya,da gane-gane, suna qyalla ido idan suka ganta shikkenan,musanman idan wannan dirin nata ya rud'esu,kina zaune saide kiji Ashraf yana cewa shizai aure ta shima Aryan yana fad'in shi zai aure ta...."(😂) 


Hajiya kilishi tayi ajiyar zuciya tace"kada ubangiji ya nunamin wannan baqar rana....to Hajiya Mariya ai bakisan wani abuba,gaba d'ayansu su biyun fa har yanzu basuda tsayaiyar budurwa,abun har tsoro yake bani, shekaru sunata tafiya sunqi aure, musanman Aryan, shi bashida magana, bansan yaya zaiyi yasamu mace ba"


Hajiya Mariya tace"tokode baqar aljana ce ta aure shi?"


Cikin sauri Hajiya kilishi tace"aiko farar aljana ce dole zaiyi aure shima ya ajiye zuri'ah"


"wannan gaskiya ne" cewar Hajiya Mariya, daga nan tarakota get dinsu na farko, sannan tadawo.



******



Da daddare Mamy tagama cin abinci suna zaune afalo gaba d'ayansu, yayanta dake maiduguri Alhaji Mustapha yakira wayarta, bayan sun gaisa yace"Maryam yaronki ne yasani wannan waya, kinganshi nan zaune tun yamma yazo yasani agaba lalle saina kiraki nafada miki shifa yanason Mawahib,yace nafada miki yanason ayi masa izni yafara zuwa wajanta zance "


Mamy tayi murmushi,tasan cewa yayan nata bashida wani da namiji Sai guda daya, sauran duka mata ne, cikin Jin dadi tace"Nabil kenan,yanzu nice nazama haka awajansa? bazai Iya kirana yafadamin da kansa yanason Mawahib ba saide yasaka kakirani kaida kanka Yaya?"


Gaban Mawahib ne yayi wata irin faduwa Jin maganar akanta akeyi,dama Yaya Nabil sonta yake shiyasa taga kwana biyu yana matsa mata da magana idan tahadu dashi a chat?

Bata gama tunanin datake ba taji Mamy tana cewa"a a, batada kowa Yaya, amma Nabil aina gida ne,Allah yasanya Alkhairi, Allah yasa rabon sa ce"


Bayan sungama wayar,cikin jin dadi Mamy ta Kalli Alhaji Isah tace"Abban Mawahib kaji wai Nabil din Yaya Mustapha ne yace afada mana yanason Mawahib"


Abba yayi murmushi ya Kalli gefenda Mawahib take zaune kamar ruwa ya cinyeta,cikin tsokana yace"yanmatana wai zaki aure shi kigudu kibarmu?"


Cikin kunya tatashi da sauri tafice daga part din nasu, tatafi wajan Nabiha. 


Alhaji Isah yayi murmushi yace" To Alhamdulillah, gaskiya naji dadi sosai, Nabil ai yanada hankali,zansamu su Yaya inyi musu maganar,shima saiki fada masa yazo suyi magana shida Mawahib din,idan sun sasanta kansu shikkenan, idan Allah yayi auren dashi,saita qarasa karatunta adakin mijinta"


Mamy tayi murmushi tace"hakane,amma gaskiya ni naso ace saita kammala karatunta sannan zatayi aure,banason irin neman aure da wurin nan,duka-duka ma nawa Mawahib din take?shekara goma sha takwas Alhaji wanne irin aure ne wannan zasuyi?"


Abba yayi murmushi yace"wanne karatu Maryam?yaushe tafara karatun? ko level two bata shiga bafa yanzu tasa qafa a karatun,kicire wannan tunanin aranki inde harshi Nabil din zai barta tayi karatunta ai Alhamdulillah, batun shekaru kuma bawata matsala bane,tawani fannin ma gara hakan, mijinta zai koya mata soyaiya da kansa, sannan kuma kinsan abinda mu iyaye mukeso akan yayanmu qaddara tana zuwa ta sauya shi,kiga abinda mukeso din bai faruba, ke kinaso ace tagama karatu, taqara shekaru, sannan tayi aure,nikuma abinda yake Raina shine naso ace ta auri Yayanta CAPTAIN ARYAN,dukansu dagashi har ita Ina musu sha'awar junansu"


Gaban Mamy ya yanke yafadi,cikin sauri tace"Alhaji kadena wannan maganar Dan Allah, Allah yasa Nabil din yazame mata mafi Alkhairi"


Cikin Sanyin jiki Abba ya amsa mata da "Amin" 



******



Tana zuwa dakin Nabiha tace"Nabiha nadena zuwa wajanki daga yau, ke bakida aiki saiki ki shige daki ki dauki wayarki,gaba daya kin manta dani"


Cikin murmushi Nabiha tace"to yi haquri,nadena, shikkenan? meyake faruwa naganki yanzu goma saura?"


Saida ta yatsina fuskarta sannan tace"kinsan me?wai Yaya Nabil ne yasa kawu Mustapha yayiwa Mamy magana wai yana sona" 


Nabiha tanajin haka tagyara zama tace"ke dan Allah?"


Mawahib tace"wallahi,Nina rasa yanda zanyi,gaskiya ni bana sonshi,amma zan aure shi kodan Momy kilishi, idan tadena ganina ai shikkenan, bazata sake fada mana magana nida Mamy naba"


Nabiha tayi ajiyar zuciya tace"hakane kam, amma gaskiya nide Mawahib nafi miki sha'awar Yaya Ashraf,saboda naga kamar yana ra'ayinki"


Cikin sauri Mawahib tazaro idonta(😳) tace"Rufamin asiri Nabiha,inani Ina 'ya'yan Momy kilishi?,sannan kuma yamin girma,banason tsoho, gara yaro dan ashirin dawani abu"


Nabiha tayi murmushi tace"lalle yarinyar nan, Yaya Ashraf ne tsoho? to bari Kiji wallahi irinsu akeso,sunfi yaran Iya soyayya....wallahi innice ke ko,yanda Yaya Ashraf dinnan yake kulaki,wallahi sainayi soyayya dashi Inga Yaya Momy kilishi zatayi,Yaya Captain nede dama bamu Isa mugwada hakan ba" (😂)


Mawahib tace"Nabiha ko amafarki bana fatan nayi soyaiya da 'ya'yanta, zama lafiya aiyafi zama dan sarki"


Haka suka dinga tattauna zancen har shadaya nadare,sannan Nabiha tarakota, sukai sallama


******


Washegari tun kafin tatashi daga bacci Nabil yakira ta yakai sau biyar tana bacci bata dauka ba,kuma wayar tana silent, saida tatashi taga messages dinsa dayawa,kusan guda hudu, duka babu wanda bai zuba mata kalaman soyaiya ba,kasancewar ta farin shigan soyaiya tafi minti ashirin tana daga kwance tanata aikin karanta saqonnin nasa,daga baya kuma tatashi tayi wanka ta shirya ta futo ta gyara musu gidan,bata dade da gama aikin ba Mamy tadawo kasancewar yau juma'ah da wuri take dawowa,sai bayan ansauko daga sallar juma'ah sannan Nabil yakira ta,sun dade suna waya tun Mamy tana mamakin Mawahib harta dawo ta daina ganin yanda take magana qasa qasa ita Ala dole da saurayi take waya, da abun ya isheta saita Kalle ta tace"Mawahib kije daki kiyi wayar mana"(😂) 


Babu musu tawuce dakinta,saida sukazo sallama dashi ne sannan yake fada mata zaizo gobe,me takeso yataho mata dashi, ta nuna masa batason komai, daga qarshe sukai sallama.


Saida daddare take fadawa Mamy Yaya Nabil zaizo gobe,Mamy tayi murmushi tace"Allah yakawo shi lafiya"


Washegari da sassafe taje tatashi Nabiha daga bacci,cikin Jin dadin bacci Nabiha tace"dan Allah Mawahib ki barni nayi bacci na"


Mawahib tace"kitashi dan Allah Yaya Nabil ne zaizo anjima, yamin waya yana hanya wallahi"


Cikin sauri Nabiha tatashi zaune tace"wai daga maidugurin zaizo?"


Tace"eh,bansan me zanyi masa ba,nahada masa drinks kawai yayi?"


Nabiha tace"haba Mawahib,ya mutum zaizo tundaga maiduguri amma mu bashi lemo, kinsan me? fita zamuyi muyo cefane muyi masa girki mai dadi, kinsan yau momy kilishi ce zatayi girki ba Mamy ba bare muce zamu bashi abincin gida,kuma wallahi momy kilishi abincin gargajiya takeyi, kawai kije kifuto muje driver yakaimu kasuwa muyo cefane mudawo"


Mawahib ta jinjina kanta tace"eh hakane kuma,to bari inje in shirya, kema kitashi dan Allah"


Cikin sauri suka shirya suka fita,driver yakaisu suka siyo abinda suke so, sannan suka dawo gida, suna dawowa ko zama ba suyi ba suka fada kitchen, kasancewar kayan maqulashe suka hada masa nan da nan suka gama kafin ma ace Hajiya Kilishi ta shigo kitchen din, Mamy de taga anata jera girke girke afalo cikin ranta tace"ikon Allah,zamani kenan"


Sai wajan qarfe uku na yamma yazo,kasancewar sa ba baqo ba a gidan yasa kai tsaye Mawahib ta shigo dashi falo,saurayi ne matashi bazai wuce shekara ashirin da bakwai ba. 


batayi kwalliya mai yawa ba,kawai light makeup tayi,tasaka riga da siket na leshi,tayafa mayafi dan madaidaici mai kyau, bayan sun gaisa ta gabatar masa da kayan ciye ciye, babu kunya yaci abunsa sosai, sannan takira masa Mamy suka gaisa, Mamy tadan dade a zaune tana tambayarsa 'yan'uwanta mutanan maiduguri, sannan ta koma daki tabarsu shida Mawahib din.


Cikin nutsuwa yafara yiwa Mawahib magana cikin sigar jan hankali domin kuwa ya lura bata taba soyaiya ba,a hankali a hankali harya dinga janta da zance harta sake dashi,nan da nan ya dinga sakata dariya sai gashi tun kafin yatafi taji ya kwanta mata arai kasancewar sa mutum mai barkwanci, maisata nishadi.

bai dade sosai ba yace zai tafi, kasancewar tafiyar akwai nisa,sai a lokacin takira masa Nabiha suka gaisa,dazata tafi yadauki 5k yabata, Nabiha tayi masa godia sosai, sannan tatafi, ita kuma Mawahib suka qarasa tattauna wa sannan ta futo zata rakashi,sunzo get nafarko ya kalleta yace"to Amarya ta,zan tafi,sai yaushe kenan?"


Kalmar daya fada ta amarya ta, itace tasa Mawahib dariya,har dimples dinta suna futowa, adede lokacin musa megadi ya budewa Ashraf get yasako hancin motarsa ciki,dasu yafara cin karo,tun daga nesa ya hangota tana yiwa wani qato murmushi, lokaci daya yanemi annurin fuskarsa yarasa,ko gama daidaita parking baiyi ba yafuto daga cikin motar ya nufi get na biyu,fuskar nan tasa a murtuke, Mawahib data dago daga dariyar datake lokaci daya tayi ido biyu dashi, mamaki ya kamata,kode Yaya Captain ne yadawo? to ai kuma idan shine yadawo dole zata sani,da tuni qofar gidansu ma yacika da jama'ah, to meyasamu Yaya Ashraf yayi irin wannan daure fuskar?gaba daya saiya koma mata Yaya Captain sak. 


Koda wasa baima kalli inda suke ba yabude get din zai shige,Nabil ya kalle shi cikin mutuntawa yace"barka da shigowa Ina wuni?"


Ba tareda ya kallesu ba yace"lafiya" 

 kamar anyi masa dole, yana shigewa ciki Nabil ya Kalli Mawahib yace"Sojan gidanku yadawo ne? naga shine baya fara'ah, kinsan niba ganesu nakeba"


Mawahib tayi wata dariya Mai kamada yaqe, tace"shine...,"


Saide cikin ranta tana mamakin sauya war Yaya Ashraf zuwa fishi, idan ta cewa Yaya Nabil bashi bane zai Iya tunanin wani abu, shiyasa tayi masa qarya cewa Yaya Captain ne.


Nabil yayi ajiyar zuciya yace"rannan naga bbc sunyi posting din karramawar da'aka musu,naga photon sa shida shugaban qasa, Allah yasanya Alkhairi"


Kanta aqasa tace masa "Amin ya Allah"


Motarsa yabude yadauko mata wata babbar leda fara, yabata yace "ki shiga da wannan ciki,babu yawa yar qaramar kyautata ce izuwa gareki"


Cikin sauri ta girgiza masa kai tace"A a,Mamy zatamin fada,babu ruwana ka barshi"


Murmushi yayi yace"naji, to ki kar6a zankirata awaya inyi mata magana"


Saida taji haka sannan ta kar6a tayi masa godia,yace zaije suyi sallama dasu Alqali sannan yawuce,tayi masa Addu'ah,sannan tajuyo zuwa cikin gida. 




Tana shiga part dinsu, ta tsinci muryar Yaya Ashraf cikin fishi yana fadin"Amma Anty Mamy yaushe tafara karatu da zaku barta tafara sauraron samari yanzu? waye yabata damar kula samari haka anyhow....?"


baima tsaya jin amsar da Mamyn zata bashi ba yajuya cikin 6acin rai zai fice daga part din,yana ganin Mawahib abakin qofa a tsaye da

uwar leda a hannunta yazo wucewa ta gefenta qiris yarage ya bigeta, cikin sauri ta matsa gefe, tsananin mamaki ya cikata dama shima yana fishi haka?(🤔)


Mamy takasa magana tabi Ashraf da kallon mamaki harya fice daga part din,a hankali tasaki murmushi ganin wannan qarfin hali nasa, gaba daya tagama gane inda yadosa,kuma hakan bazai ta6a iyuwa ba,koda ace Mawahib din tana sonshi dole zata haqura dashi, haka inma mazan gidan sukace zasu qullah to bazata yarda ba,saide wannan karon a saketa har abada tafice tabar familyn Alqali.







(wata sabuwa🥺😱)














Amnah El Yaqoub✍🏻


💗MAWAHIB💗



Writing By Amnah El Yaqoub



7&8





Cikin sanyin jiki ta qarasa shigowa falon,tazauna kusa da Mamy tace"Mamy me a kayiwa Yaya Ashraf tunda yashigo naga kamar yana fishi"


Cikin basarwa Mamy tayi murmushi tace"Fada yake saboda kinfara tsayawa da saurayi, baisan su Alhaji ne suka bawa Nabil damar zuwaba,tun ranar da mukai waya da Yaya Mustapha Abbanki yaje yasamu Yaya Alqali yafada masa komai" 


Ahankali Mawahib tasaki ajiyar zuciya tazauna,tabawa Mamy ledar hannunta cikin dari-dari tana tsoron kartayi mata fad'a,cikin murmushi Mamy ta kar6i ledar tace"Kawo miki yayi?"


Tace"eh, saida nace yabarshi shine yace zai fad'a miki" 


Mamy tace"to inbanda shirme menene naqin kar6a? koba maganar soyaiya Nabil ai yayanki ne,dani da mahaifinsa uwarmu daya ubanmu daya,bazanyi fad'aba danya baki wani abu,bari mugani menene aciki"


Tafadi hakan tana bude ledar,kayan kwalliya ne aciki masu tsada harda turarukan da chocolate dayawa,sai wata 'yar qaramar Envelope da dubu goma aciki,cikin murna Mamy tace"lalle Nabil,wannan uban kaya haka ai kinci qarfin albashin nasa,Allah yasanya Alkhairi,amma ya kikagan shi? ya miki?"


Cikin tsananin kunya taturo dan qaramin bakinta gaba tace"kai Mamy dan Allah....nide kidena min wannan maganar" 

cikin sauri tamiqe zatabar wajan, Mamy tana dariya tace"dawo ki dauke kayan ki,kije kikaiwa 'yar'uwar taki itama"


Cikin shagwa6a tadawo tabude kayan tadibawa Nabiha komai,sannan tatafi zatakai mata.



Nabiha tagama dudduba kayan da Mawahib takawo mata, cikin mamaki tace"Gaskiya kinyi sa'ah Mawahib,yaya Nabil da qarfin sa yafuto,kuma da alama da gaske yake tunda gashi ta wajan iyaye yafara neman,kuma daga gani bashida rowa,gashida fara'ah masha Allah, kinsan wannan kayanfa tsada ne dasu"


Mawahib tayi murmushi tace"nima shiyasa naji yafara birgeni,tunda yazo yaketa bani dariya,gashi bashida shekaru sosai irin mijinda nakeso,ke kinsan meyafaru dazu da yamma kuwa?Yaya Ashraf yadinga yiwa Mamy fad'a saboda na saurari Yaya Nabil,kuma fa Abbana yasan da zuwan nasa"


Nabiha tayi shiru tana sauraron Mawahib,tunda Mawahib d'in tafara magana dayake ita tafita shekaru da wayo, nan da nan ta dauki haske akan dalilin fadan Yaya Ashraf din, tayi shiru saida tagama jin qarshan zancen sannan tayi ajiyar zuciya tace"kinsan abinda nake tunani? Yaya Ashraf fa Ina zargin sonki yake"


gaban Mawahib yayi wata irin faduwa,cikin tashin hankali ta zaro idonta tace"dan Allah Nabiha? Innalillahi...naga takaina"


Nabiha tace"menene abun wani innalillahi...?  kinsan Allah sonki yake,kuma zakice nafada miki"


Mawahib tace"ai yanzu yaga Yaya Nabil,nikam babu ruwana, bazai ma fadamin ba, babu ruwana da Momy kilishi"


Cikin bada qwarin gwiwa Nabiha tace"kinsan Allah,ki ajiye wannan haqurin naki irinna Mamy agefe ki fuskanci rayuwa, wani lokacin idan biyaiya tayi yawa anfi yima is'kanci,kina mata biyaiya kamar itace takawo ki duniya,ni bakiga idan tana sababin tama wayata nake dauka ba?"


Cikin rawar murya Mawahib tace"bazan iyaba Nabiha,itama kamar uwa ce awajanmu, watarana ai sai labari,nan gaba kadan ma zanbar mata gidan har abada inkoma wajan Yaya Nabil maiduguri"


Nabiha tace"to ai shikkenan,saiki daina rawar jikin"

Sai a lokacin Mawahib ta Lura jikinta rawa yake tunda Nabiha tace mata Yaya Ashraf yana sonta, sun dade suna fira daga baya tayi mata sallama tatafi.


Washegari da safe takama weekend ne, Mamy tana gida bataje ko'inaba,itama Mawahib tun safe data gyara musu part din nasu takoma dakinta tagyara shi,tarasa meyasa tun safe gabanta yaketa faduwa,sai Addu'ah taketa maimaitawa aranta, tana gama gyara dakin Yaya Nabil yakira wayarta,tayi zamanta adakin suna wayarsu,

Mamy ce taqwala mata kira cikin sauri tayi sallama dashi tafuto,ganin Mamy tayi dauke da wani yaro yana kuka kad'an-kad'an, ita kuma Mamy sai jijjigashi take,Mamy ta kalle ta tace"d'auko hijabin ki kikai wannan yaron gidan Maman Fati,yanzu ta aiko shi nayi masa allura kuma naga yaron daya kawo shi kamar bazai riqe shi dakyau ba,nace yaje yaturo babba adaukeshi,kuma kinji shiru babu wanda yazo"


Tace"to Mamy"


Sannan tajuya dakinta tadauko hijabi tafuto,hayaniyar datake ji a waje ne yabata mamaki tarasa me'akeyi haka,Mamy ta nufo bayanta da yaron tace"yi sauri ki goyashi kikai matashi yaro yanata kuka tun dazu" 


tafad'i hakan tana dora matashi abayanta, Mawahib tasa zanin goyon tana kokarin goya yaron, tace"Mamy wai hayaniyar menake ji a waje? kosu Daddy ne suke rabon zakka?"


Cikin sauri Mamy tace"riqeshi ki goyashi ni,kin dameni da tambaya sauri nake,CAPTAIN ne yazo, inaso inyi sauri inyi masa ferfesu med'an sauqi"


tana fad'ar haka tayi d'akinta tabar Mawahib atsaye a wajan


Haushi yakama Mawahib,tabi bayan Mamy da kallo gabanta yana dukan uku uku,cikin ranta tace"mukam yau munshiga uku, bala'i yadawo"


tajuya ta kalli yaron dayake goye abayanta yana qishin-qishin din yin kuka,cikin haushi kuma a fili tace"Yanzu fisabilillah Mamy saboda wannan mutumin jikinta yake rawa haka? saikace wani mutumin kirki za'a je anayi masa wani farfesu? wahalalle yanzu haka da wannan uniform din nasa na kullum-kullum yazo"(😱) 


tasake juyawa ta kalli yaron dayake goye abayanta,tatuna maganar qawayenta 'yan makarantar su dasuke cewa goyo yana zubar da Nono, cikin fad'a tafara qoqarin sauke yaron daga bayanta tareda fadin"kaikuma sauko,wallahi bazan goyaka ba"

tasake rage muryarta taci gaba da fadin"Salon d'an nonon nawa duk su zube mijina yarasa na kamawa...."(🙊) 


Qamshin turaren daya bugi hancinta,wanda bata gama tantancewa nawaye ba yasa tajuya bayanta dasauri....,lokaci d'aya idonsu yahad'u dana juna,gabanta yayi wata irin fad'uwa,atake gumi yafara rufe mata fuska,idonta yayi tsilli-tsilli qarara tsoro ya baiyana a cikinsu,Addu'ah take aranta Allah yasa baiji maganganun datayi ba, kallonta yake fuskar nan tasa murtuk babu alamun fara'ah,amma hakan bai hana kyawunsa baiyana ba,kyakykywane ajin farko,kamar kullum yana sanye cikin kakinsa na Soja,kayan yayi mutuqar yimasa kyau,farar fatar jikinsa tabada hadin kai wajan qawata uniform din a jikinsa,agaban rigar bangaren hannun dama an rubuta CAPTAIN ARYAN,gefen hannun hagu kuma an rubuta NIGERIAN ARMY.



Jikinta ne yadauki rawa,cikin sauri tacire idonta daga nashi,gani take kamar wani abu ne yake futowa daga cikin nasa idon yana shigewa cikin nata idon,da sauri ta matsa ta bashi hanya, tayi wuf tafice daga part din nasu,saura qiris ta doka tuntu6e takayarda yaron hannunta,kai tsaye ta nufi get tafice daga gidan, saida taje bakin get din nasu sannan taga sauran mutane sunata daukar kayan abinci kama daga shinkafa har zuwa taliya da macaroni,gakuma wasu sojoji a tsaye agefe kowanne hannunsa daukeda bindiga, cikin sauri ta wuce kai tsaye taje takai yaron gidansu, sannan tadawo gida,tanaji tana gani part dinsu ya gagareta shiga,sai part dinsu Nabiha ta wuce.


Duk yanda sanyin esi ya ratsa dakin Nabiha, hakan bai hana Mawahib cire hijabin jikinta tana sake firfita dashi ba,Nabiha tace"meyake faruwa ne Mawahib naga sai gumi kike hadawa?"


Cikin rawar murya tace"nida Yaya Captain ne...,maganganu nasaki baki inata fada,bansan yana bayana ba,bansani ba yaji abinda nake fada ko baiji ba,amma kunya ta kamani, na aikata abinda ba halina bane Nabiha"


Cikin sauri Nabiha tace"innalillah....Yaya Captain kuma?to me kikace? wacce maganar kikayi?"


Mawahib tayi shiru tana tunanin me zata cewa Nabiha? nayi maganar nono kuma Yaya Captain yajini?kokuma nagama zaginsa tsaf kuma yajini? 


Cikin sauri ta girgiza kanta tace"kede abar kaza cikin gashinta,amma na tabbatar inde yaji abinda nafada,babu abinda zai hanashi dukana"


Nabiha tace"to yau kin janyo mana ruwa, kinganni nan? tunda naji hayaniya a waje nasan cewa shine yazo,shiyasa naqi fita ko nan da can"


Mawahib tace"to yanzu yaya zanyi Nabiha?"


Nabiha tace"wai akenki yayi kikaqi zuwa ne?"


Cikin rawar murya Mawahib tace"nace miki kidena tambayata abar kaza cikin gashin ta,ni wallahi yau babu inda zanje daga nan"


Tana fadar haka ta kwanta a gadon Nabiha tareda shigewa cikin bargo,gaba daya sai taji zazza6i yana neman rufeta.


Ba'ita ce tabar part dinsu Nabiha ba, saida aka kira sallar magrib, taji gidan shiru alamun duka mazan gidan suntafi masallaci, sannan ta lalla6o ta wuce part dinsu da gudu.


 da daddare suna zaune afalo da Mawahib da Abba dakuma Mamy suna kallo, Mawahib tana sanye cikin doguwar riga ta bacci amma mai kauri, su Mamy suna kallo suna fira kad'an kad'an, amma Mawahib gaba daya tunaninta baya kansu, shawara tagama yankewa aranta gara tahada kayanta tatafi maiduguri idan taji labari Yaya Captain yatafi, saita dawo, kokad'an bataji dadin zuwansa ba, ga kuma rashin kunyar data gama yimasa wanda bata saniba yaji ko baiji ba.


Abbanta yayi magana yaji shiru bata saka baki, a hankali yajuya ya kalle ta yace"yanmatan Abba, babu matsala deko?"


Kallansa tayi cikin ladabi tace" Abba babu matsala,amma inaso idan ka amince zanje maiduguri"


Abba Yajuya ya Kalli Mamy yace "lafiya zata tafi?"


Mamy tace"Alhaji nima sai yanzu naji zancen tafiyar"


Cikin mamaki yace"meyafaru zaki tafi,kuma tafiya babu shiri baki sanarda mahaifiyar kiba?"


Wani irin murmushin qarfin hali tayi sannan tace"Abba dama inaso naje hutu ne kafin hutun mu yaqare"


Abba yace"A a Ruqayya,yaushe kukai hutun ai baki gama hutawa ba,sannan ga yayanku yazo d'azu da yamma, kowa yana gida,bai kamata kitafi ba,ni kinyi masa murna ne akan karramawar daya samu?"


Wani irin qullutun taqaici ne yakama Mawahib,yanzu saboda Allah dan Yaya Captain yazo sai ahanata tafiya hutu maiduguri?

Cikin kwanciyar hankali ta shimfidawa Abbannata qarya tace"eh dazu mungaisa nayi masa ala sanya Alkhairi"


Tana rufe baki, aka turo qofar part din nasu aka shigo,wani irin qamshi mai dadi yadaki hancin Mawahib,sanin datayi cewa irin qamshin dazu ne, hakanne ya tabbatar mata da cewa Yaya Captain ne, hakanne yasa koda wasa batayi kuskuren dago kanta ba,cikin sallama suka shigo falon,dukansu su biyun  sanye sukeda wando three quarter, da riga marar hannu alamun kayan shan is'ka ne a jikinsu tunna yamma,gaba daya sai suka saje suka zama abu d'aya,saide fuskar mutum daya data kasance babu wasa akanta.


Mawahib tayi mutuwar zaune kamar ruwa ya cinyeta,saika rantse bata cikin falon.

Cikin farinciki Mamy tace"yan samari"


Captain yad'ora hannunsa akan daya daga cikin kujerun falon yace"Anty Ma-my...."


yakira sunanta a rarrabe,cikin murmushi tace"Captain"


Yaya Ashraf yace"Anty Mamy akwai sauran kunun madarar nan na dazu?"


Mamy tace"akwai, yana dinning bari in dauko muku"

Tafadi hakan tana kokarin tashi, Abba ya Kalle ta yace"yakamata kiyiwa 'ya'yanki fad'an ajiye iyali Maryam"


Mamy takawo musu kunun madarar wanda yaji kwakwa aciki har lokacin da zafinsa,tazuba musu a cup tabawa kowa,ta zauna a kujera tana fadin"to gasunan de Alhaji,inajin saimun fara tallarsu a yanar gizo"


Adede lokacin Yaya Nabil yakira wayar Mawahib,a hankali tasaki wata irin ajiyar zuciya,dama atakure take a wajan,idan tatuna maganar Nabiha datake cewa Yaya Ashraf yana sonta, tasake tunawa da kato6arar datayiwa Yaya Captain dazu, gaba daya saitajita atakure, a hankali tamiqe tanufi hanyar dakinta,Captain Aryan yana shan kunun madara yad'ago da manyan idonsa a hankali yabita da kallo,karaf idonsa ya sauka akan hips dinta,cikin sauri yad'auke kansa.


Shikuwa Yaya Ashraf kasa daina kallonta yayi, har saida yaga ta shige dakinta tareda rufowa.


Mamy tayi ajiyar zuciya ganin Mawahib tabar wajan,gaba dayansu tana lura dasu yanda suka bi yarinyar da kallo, musanman Ashraf da tun shigowar su ya kafeta dawani irin kallo,to shikuma Captain Aryan kallon na menene? a hankali gabanta yafara faduwa,amma data tuna da maganar Nabil, saitaji hankalin ta ya kwanta harta sake sukaita firarsu. 




Sun dade a part din Mamy sannan suka tafi dakin su,Ashraf yafara gyara musu lafiyaiyen gadon su,Captain yana danna wayarsa,d'ayar wayar tasa ce tayi qara, yadauka yana magana a hankali kamar da mace yake magana,Ashraf yayi tunanin Captain din yayi sabuwar budurwa ne, a hankali yadago yana kallon sa saiyaji yana cewa"A a bamu da irin wannan bindigar,idan zaka shigar da bayanan ka rubuta muna buqatar irinta,musanman saboda sababbin ma'aikata wanda zasu kar6i horo ok?"


Daga dayan 6angaren aka amsa masa, sannan ya ajiye wayar.

Ashraf yace"bansan yau zaka shigo gari ba, da nasa yaran nan sun gyara mana dakin,duk yayi datti wallahi"


Hankalinsa yana kan waya yace"nima bansan zan taho ba,kawai nagaji ne,kuma inason ganinka kaida Momy, shiyasa kawai nataho,toko muje gidanka mu kwana tareda wad'ancen sojojin?"


Ashraf yace"Rigima boy kenan....babu matsala mu kwanta kawai gobe saisu gyara mana,wai kasan yarinyar nan Zulaihat kuwa har yanzu tana nan tanata nacin kirana?"


Captain ya ajiye wayar hannunsa yace"karabu da'ita kawai,dan nima ganin farko danayi mata naji tamin..."(😲)


Ashraf yace"but... tabani tausayi, tana kuka tana tambayata meyasa zan yaudareta?"


Cikin rashin damuwa Captain yace"toya zatayi? Kashareta kawai kanemi wata"


Ashraf ya zauna abakin gadon ya kalli Captain yace"amma kasan idan nasake yin wata budurwar kace kana sonta saika raina kanka?"


Captain yace"to idan aka dace Ina sonta ya zakayi? zamu auri mace d'aya ne?"


Ashraf yadauki fillo yadora a cinyarsa sannan yace"wai kai baka ga Mawahib bane?"


Saida ya yatsina fuskarsa sannan yace"wace hakan?"(😲) 


Ashraf yayi masa wata irin harara sannan yace"Mawahib d'in Anty Mamy mana"


Cikin rashin kula Captain yace "Oh..."


Ashraf yace"kamarya oh.....?  wai kana nufin har yanzu kana nan kanaqin yarinyar nan?,ko saboda Anty Mamy yakamata kadena nunawa 'yarta qiyaiya...."


Cikin damuwa ya lumshe idonsa yabude sannan yace"Bansan jin maganar marar kunyar yarinyar nan Ash...,at all ma nibata gabana,ni maqiyin qasata shine maqiyina ba wannan qwailar ba...."(🙊😳😱)










(Captain Anya kuwa?🤔, to muje zuwa de 💃🏼💃🏼) 






Amnah El Yaqoub✍🏻


💗MAWAHIB💗



Writing By Amnah El Yaqoub



9&10




"please kadena min maganar ta"


Ashraf yace"dole inyi ma maganar ta kuwa, saboda Ina sonta, najira kadawo ne infara yima maganar,banason kai tsaye in yiwa su Daddy maganar, kaima kuma kadawo kace kana sonta"


Captain Aryan dayake kwance cikin wani irin fargici ya tashi zaune yace"inso wa? ni...? Inrasa wazan aura sai wannan abar?"


Cikin zafin rai Ashraf yace"yauka fara? sau nawa Ina nemo yarinyar dazan aura kana cewa kaima ita kakeso? ban'isa inyi sabuwar Baby ba, kaima saika sota, 'yanbiyu mata masu kama daya kakeso insamo mana? shiyasa nafara fad'ama maganar,kar inje infad'awa su Daddy inason Mawahib kaima ka dage kace kai sai ita..., inkasan kana sonta to tun wuri inyi shiru da maganar"


Cikin taqaici Captain Aryan yace"kaga Ashraf,dan Allah idan zakayi zancen 'yanmata, toka dena saka yarinyar nan aciki, idan zaka so kowacce irin yarinya tonima zan'iya sonta,saboda jinin mu ahad'e yake,zan'iya son dukkan 'yanmatanka,amma banda ita..."(🙆🏻‍♀️)


Ashraf yayi shiru yana qarewa dan'uwan nasa kallo, tunda yacewa Mawahib qwaila yake tantama aransa anya Aryan yana cikin hankalin sa kuwa?kokuma de ya makance? 

Ahankali yasaki ajiyar zuciya yace"kagama?" 


Kai tsaye Captain yace"ban gamaba,inaso kasani batada abubuwan dazaija hankali na har'insota,bazan ta6a sontaba har abada,nawuce ajinta,bata cikin tsarina,bata Isa takama qafar irin matar dazan aura ba, sannan kaima Ina gargadinka,karka bari Momy taji maganar nan ,kuma abinda ya shafeni kaima yariga ya shafeka,bana qaunar ta,saboda haka dole kaima karabu da'ita tunda bana sonta...."


Ashraf yace"saboda

kaine kakawo ni duniyar ko? to saina aureta,inyaso ka mutu" 


Cikin sauri Captain Aryan yace"saide kaika mutu,kuma baka Isa ka auretaba INDE INA RAYE"



Ashraf yace"tosaika hana mugani"


Yafadi hakan tareda sakin tsaki, ya dauke fillonsa yamaida shi qafafun Aryan,ma'ana sukai kaida qafa. 


Kusan minti biyar dukansu sukai shiru babu wanda yasake yin magana, sai can Captain Aryan shima yasaki tsaki yadauke fillonsa yadawo dashi  kusadana Ashraf.(😂)



Ashraf yana jinsa yayi shiru ya qyaleshi,Captain yaji shiru Ashraf bai kula shi ba duk da yadawo da fillonsa wajansa,a hankali yace"Ashraf..."


Ashraf yayi shiru yaqyaleshi, yasake sakin dan qaramin tsaki yace"Ashraf katashi kayi Addu'ah"


Babu musu Ashraf yatashi yafara Addu'ah,saida yagama addu'ar sannan ya kalli Captain Aryan yace"kai kayi addu'ar ne?"


shima Captain Aryan yanajin Ashraf din yayi shiru yarabu dashi(😂)

Ashraf yasan sarai yana jinsa,sai yayi murmushi kawai yad'ora hannunsa akan lallausar sumar Aryan din batare daya qara magana ba,yanajin lokacin da Aryan din yafara bacci, amma shi bai fara bacci ba yana tunanin yanda zai 6ullowa iyayensu akan maganar aurensa da Mawahib,har wajan qarfe biyu nadare yana tunanin mafita,yanajin yanda Captain Aryan yaketa juye-juye kamar akwai abinda yake damunsa,ahankali ya rufe idonsa har bacci yayi nasarar daukar sa. 



Cikin dare Captain Aryan yafarka dawani irin ciwon mara,tun yana daurewa harya fara ciza lallausan lips dinsa, ga esi yanayi adakin amma Captain Aryan sai gumi yake had'awa,ahankali ya runtse idonsa yana tuna shawarar da likita yabashi akan wannan ciwon cikin nasa yakamata ace yanemi mace yayi aure hakanne zai kawo qarshan jinyar,ahankali yatashi zai dauko maganinsa yaji bazai Iya miqewa ba.


Cikin sauri yafara tashin Ashraf, yace"Ash,tashi!!"


Cikin bacci Ashraf yabude idonsa a hankali,ganin Captain Aryan a zaune sai had'a gumi yake hakan yasa yatashi cikin sauri, yadora hannunsa a kafadar Captain din sannan yace"meyake damunka?"


Saida ya cija lips dinsa sannan yace"magani na,bani maganina"


Cikin sauri Ashraf yasauko daga gadon,yabude yar qaramar jakar da Captain din yazo da'ita ya dudduba sannan yaga maganin,wutar dake gefen gadon su ya kunna saida ya karanta yaga maganin menene, sannan yabashi,yaje fridge ya dauko masa gorar ruwa, cikin sauri Captain Aryan ya 6alli maganin yasaka a bakinsa, sannan yakafa gorar ruwan a bakinsa saida ya shanye shi tas, sannan yafara maida numfashi ahankali.


Ashraf ya dafashi yace"Aryan...,nayima magana kadena shan maganin nan,gara kazauna haka idan kayi mafarki shikkenan zakaji sauqin abinda yake damunka"


Captain Aryan da kansa yake sunkuye yad'ago ya kalli Ashraf yace"kullum zan zauna kenan banida aiki sai mafarki? ni bazanyi asarar abuna ba,na matata ne...."(🙈🙊)

Yaqarasa maganar cikin sigar shagwa6a kamar ba Soja ba


Dariya takama Ashraf,amma dayake yasan halin dan'uwan nasa akan wannan dariyar yanzu saiya fara yimasa masifa, saiya danne dariyarsa yayi murmushi yace"tokayi aure"


Cikin shagwa6a yace"niba wacce nakeso"


Ashraf yace"Okay...mugunta ce tasa kake rabani da 'yanmata na kenan ko? kai baka auraba niban aura ba"


Captain Aryan baice dashi uffan ba,yaja fillonsa ya rungume tareda runtse idonsa yana numfashi sama-sama har baccin wahala yadaukeshi. 


Ashraf yana zaune yana kallonsa saida yaga yayi bacci sannan shima ya kwanta agefensa yayi bacci.


Dasafe bayan sungama buga ball dakinsu suka dawo kowa yayi wanka,gaba dayansu suna daure da farin towel a qugunsu sai wani d'an qarami guda d'aya kowa yana goge sumar kansa, Ashraf yad'auki wayarsa ya dokawa Mawahib Kira, a lokacin tana zaune tanashan tea tagama gyaran part dinsu kenan, har zuwa lokacin Mamy bata tashi ba kasancewar yau weekend ne bata tashi da wuri, mamaki ya kamata,kiran Yaya Ashraf da wannan safiyar lafiya? gaba daya sai taji tsoron daga wayar kartaje tunanin Nabiha yazama gaskiya idan kiranta yayi domin yafada mata yana sonta mezatace masa? haka ta kasa daukan wayar harta katse, daga nasa 6angaren yasake kira akaro na biyu,sai a lokacin ta dauka cikin ladabi tace"yaya Ashraf barka da safiya"


Saida yasaki wani murmushi najin dadi sannan yace"yawwa Mawahib idan kingama abinda kike please kizo ki gyara mana dakin nan..."


Cikin ladabi tace"to Yaya"


Daga nan yakashe wayar yad'auki mai zai fara shafawa, Captain ya

kalle shi yace"yanzu kai bakaji kunya ba?kasa yarinya agaba kana wani kashe murya saika ce kasamu wata babbar mace,wannan abun kunya har'ina "(😖) 


Ashraf yayi murmushi yace"kaine kake ganinta amatsayin yarinya,amma Mawahib tanada abinda wata babbar ma batadashi,ka nemi mace kayi aure kaqi, ka dameni da juye-juye cikin dare dashan magani, kawai ka lalla6ani inbarma Mawahib,ninasan abinda nagani, kaima kuma idan ka qarewa yarinyar kallo zakasan akwai kayan alatu"


Captain Aryan yasaki wani irin tsaki,cikin 6acin rai yace"Ash...nifa yarinyar nan batada wani abu wanda zangani har inji sha'awarta"


Ashraf yabi Captain Aryan da kallon mamaki,to kodai saboda rashin zuwansa gida akai-akai shiyasa baisan yaya Mawahib din take ba? girgiza kansa yayi, da alama dan'uwan nasa baisan yarinyar ba.


Captain Aryan yace"kuma a'irin wannan yanayin nawa kwanaki wani me magani yakai office dinmu, a lokacin inajin kasala,bana yin gym kamar yanda nasaba"


Ashraf ya zauna abakin gadon nasu yaci gaba da shafa mai a jikinsa,shikuma Captain Aryan yana goge jikinsa da dan qaramin towel din hannunsa,cikin aji kamar bayaso yaci gaba da fadin"naji me maganin yana cewa da maiqo da zaqi da kasala duk maganin yana yi,to nima inajin kasala, sainayi tunanin nima irin nasu ne,nakar6a nasha,inashan maganin nan daga nan labari yafara sauyawa,nakifa kaina qasan table sai hada gumi nake,na riqe mara,da farko nafara jurewa, danaga abun bana qare bane ahaukace naje wajan mai magani najashi gefe,nafada masa abinda nakeji,shine yacemin ai yayi tunanin inada aure, maganin masu aure ne, yaje yanemo min wani abu kamar goro, nide ban tsaya na tantance menene ba nafara ci,shine naji dama dama..."


Ashraf ya kwashe da dariya,yace"tokaima kawai daga ganin suna shan magani kaima saika sha?"


Adede lokacin Mawahib tazo kofar dakin nasu,a lokacin Captain Aryan baibawa Ashraf amsa ba, ita Kuma Jin shiru tayi tunanin basa cikin dakin,ahankali tatura qofar dakin ta shigo, gabanta ne yafadi ganin murd'ad'd'an jikinsa abaiyane,cikinsa har wani hawa-hawa yake alamun yana motsa jiki,ga faffadan qirjinsa wani irin gashi mai laushi ya kwanta,bata ta6a ganin namiji hakaba,gaba daya saita diririce jikinta yadauki rawa taqame awajan, adede lokacin Captain Aryan wanda bai lurada zuwan Mawahib dakinba,yasaki wata irin dariya wadda tunda Mawahib take, bata ta6a ganin yayi dariya haka ba,cikin dariya yacewa Ashraf "ta'inda ake hawa batanan ake sauka ba?,inacin abinda yabani najini nadawo Normal,daga ranar ban sake cewa zansha ba"


Suka saki dariya gaba dayansu,yajuya zai goge kunnansa na hannun dama, karkatawar da zaiyi yaganta a tsaye idonta yayi tsuru-tsuru, lokaci daya annurin fuskarsa ya sauya,ya wullar da towel din dake hannunsa,cikin 6acin rai yadaka mata wata irin tsawa yace"stupid girl....mekikeyi anan!!!?"


tun kafin yagama rufe bakinsa Mawahib tajuya da gudu tabar wajan,yanda yaga uban Hips dinta suna kad'awa saboda gudun datake hakanne yasake 6ata masa rai, 'yar qanqanuwar yarinya hartasan tayi ciko...(😱)


Ashraf ya ajiye manda yake shafa wa yataso yaduba baiga kowa ba,cikin damuwa yace"miye haka Aryan? Mawahib ce tazo kakoreta ko?"


Cikin 6acin rai yace"tayaya yarinya zatazo taganni ahaka ta rainani?" 


Ashraf yace"nina kirata tazo tagyara mana dakinfa"


"ta barshi,kaima idan bazaka gyaraba kabarshi" 



Ashraf yace"kaine qarami,kaine zaka gyara"


Aryan yace"minti nawa kabani?"


Ashraf ya harare shi yace"au Allah? to ko zamuje a tambayi Momy?" 


Cikin sauri Aryan yace"muje"


Kamar wani abun arziqi zasuyi haka suka shirya cikin sauri kai tsaye suka nufi part din Hajiya Kilishi,suna shiga Ashraf yace"Momy"


Shima Aryan din yace"Momy"


Tasan duk lokacin dasuke mata irin wannan kira to musu sukeyi a tsakanin su,cikin sanin abunda ya kawosu Hajiya kilishi tace"ina ganin ikon Allah ni kilishi,shekaru ko? nasani, dan Allah kurabu dani zuwa yanzu yaci ace kun daina wannan musun"


Alqali dayake zaune yanashan tea yakallesu yayi murmushi,wankan shadda su kayi mai launin light blue,banda shine ya haifesu to zaiyi wahala ya banbance su saboda hatta agogonsu iri daya ne, hular dake kansu ma iri dayace,koda yaushe yana alfahri da 'ya'yansa,tsugunnawa sukai suka gaida shi, sannan Hajiya kilishi tafara hada musu tea din suma, Ashraf yanacin sultan Chips din dake gabansa yana turawa Mawahib text naban haquri,sannan yasake roqarta akan taje tagyara musu dakin itada Nabiha, Mawahib tana ganin text din ta fadawa Mamy, sannan taje tasamu Nabiha, suka nufi dakin su Yaya Ashraf din,suna zuwa suka fara gyara dakin,duk wani kaya dasuka ganshi babu ninki suka ninkesu, suka adana musu shi,saida suka wanke har toilet din komai yayi tsaf, a lokacin aka kira wayar Nabiha, ta amsa wayar tafita, Mawahib kuma ta dauki air freshener tana fesawa a dakin,tabude fridge din dakin tasake gyara lemuka da ruwan dasuke ciki,glass cup din dasuke kan fridge din suma tasake gogesu tana gyara musu zama, adede lokacin suka shigo dakin duka su biyun,Aryan yana ganinta ya daure fuska yanuna mata hanyar fita daga dakin, cikin tsawa yace"get out...."


Tsawar da yayi matane yasa ta tsorata batasan lokacin data saki cup din hannunta ba, nan take yafashe,bai damu da yanayin datake ciki na tsorata ba yasake daka mata tsawa yace"zoki fice nace"


cikin 6acin rai shima Ashraf yace"Mawahib karki fita"


Cikin sauri Captain Aryan ya'iyo kanta gadan-gadan,cikin sauri  tayi gudu ta6uya a bayan Yaya Ashraf,ganin Captain Aryan yana tattare hannun rigar sa hakan yasa Ashraf yasaka hannu zai kareta,Mawahib kuwa tana ganin Yaya Ashraf ya tareta tayi qasa tarage tsawon ta, tafice da gudu daga dakin.


Cikin 6acin rai Ashraf yace"wai dan Allah menene damuwar kane da yarinyar nan? Aaka kawai yarinya tana walwalarta harka tsorata ta kasa tafita babu nutsuwa"


Captain Aryan yana jinsa ya shareshi, Ashraf yaci gaba da fadin "meta tsare ma? haka kawai kasaka yar mutane agaba bakada buri wanda yafi ka zalunceta?"


Cikin 6acin rai Captain Aryan yace"wai Ashraf saboda wannan abar kakemin masifa?kanamin masifa saboda ita kamar wanda ka haifeni?"


Lokaci daya jikin Ashraf din yayi sanyi,koda suke fadansu saide akan abinda ya shafesu,amma basa fada saboda wani, bazaka ta6a Jin kansuba inde akan wani ne,saide akan abinda ya shafesu su biyu,to yanzu kuma ga Mawahib tana nema tashiga tsakani, cikin damuwa yasaka hannunsa yadafe goshinsa(🤦🏻‍♂️)


Sannan ya kalli Captain Aryan yace"meyasa naga kamar kana cikin damuwa ne?,meyake damunka?"


Cikin damuwa Captain Aryan yace"no,babu abinda yake damuna,kawai de banajin dadin yanda yarinyar nan take nema tashiga tsakanina dakai,kadena son abinda nakeso saboda ita,banajin dadin zaman,gara in tafi "


Cikin sauri Ashraf yace" babu inda zakaje"


sannan yakama hannunsa suka zauna abakin gado,ya Kalle shi yace"inajin wani iri wannan zuwan naka Aryan,may be idan katafi sainayi rashin lafiya kamar yanda nasaba,kokuma kai kayi"


Captain Aryan yace"kadena tunanin komai,babu abinda zai faru insha Allah,bani kad'ai nazo ba,akwai yaran dasuke tare dani,yakamata inkoma next time idan nazo nikad'ai saina huta sosai"


Cikin sanyin jiki Ashraf yace"to Allah yasa,yau ba muje wajan Anty Mamy ba"


Captain Aryan ya yatsina fuskar sa yace"inason ganin Anty Ma-my, but banason ganin wannan yarinyar..."


Ashraf yalumshe idonsa ya bude tareda girgiza kansa baice komai ba. 


Haka suka wuni a daki babu inda suka fita,saide suje sallah sudawo,Captain Aryan baya gajiya da zance inde tareda Ashraf ne,suyi fada su shirya kansu da kansu babu wanda yajisu. 


Da daddare suna kwance sunyi shirin bacci Captain Aryan yadauki wayarsa yakamo wani hadadden gida gari guda kamar ba'a qasar yake ba,yabawa Ashraf wayar yace"Ash kaga aikin gidan nan har sun gamashi,ansaka komai aciki,wannan komawar da zanyi a cikinsa zan sauka,matata ma nasa sun saka mata komai da komai kawai clothes ne babu,shima dan bansan size dinta bane danayi mata order ansaka mata kafin tashigo gidan, but....naso ace tareda ita zamu fara shiga"


Ashraf ya kalli photunan gidan yace"Wow...,gaskiya yayi kyau,banbancin sa da nawa na nan garin kadanne,naka farin fenti nawa brown,to amma kayi auren mana saika tafi da matarka kushiga tare tunda haka kakeso"


Captain Aryan ya girgiza kansa kawai sannan ya basar da zancen alamun bayaso,yace"nima kayan ciki har windows din duka brown ne,yayi kyau sosai,inaso wannan shekarar gaba daya yan gidannan sutafi aikin hajji,daga nan kawai saika taho muje muyi zamanmu a gidan muhuta kafin su dawo" 


Cikin farinciki Ashraf yace"babu damuwa Allah yakaimu,sannan bazaka samu lada kai kadai ba,kai kabiyawa su Daddy nikuma su Momy,sannan gaskiya ni bazan tare agidana yanzu ba,saina jira na auri Mawahib tukunna,sai mu koma tare rana daya,duk wasu yan'uwa zan basu sati daya sugama zuwa ganin amarya, daga nan kuma zan rufe gidan in fara amarci na hankali na kwance"


Cikin yatsina fuska Captain Aryan yace"mekace? kayi aure kuma kana kallon amaryar har tsawon sati daya?kayi aure bakayi komai ba a wannan ranar saika ce wani kidahumi?"


Ashraf yace"menene yakawo maganar kidahumi kuma Aryan?,kana nufin kai bazaka Iya jiran sati daya ba kenan? kaide matarka taga ta kanta wallahi,zan fadawa Daddy yayima aure" 


Cikin rashin damuwa Captain Aryan yace"gaskiya kam,because nide babu wasa,cikin kwana biyu ma zan'iya  yimata ciki"


Ashraf yanajin haka yakai masa dukan wasa,yariqe kunnansa yace"bakajin magana Aryan"


Dahaka sukai addu'ah suka kwanta cikin farinciki. 


Washegari yahada kayansa tsaf zaikoma bakin aikinsa,jikin Ashraf duk yayi sanyi,kokadan bayason tafiyar Aryan din baisan meyasaba,saida sukayi sallama da Hajiya Kilishi,bayan ya ajiye mata wasu manyan kudade a gabanta, sannan sukaje yayiwa Mama Sadiya sallama,itama ya ajiye mata kudi masu yawa akan kujera, sannan suka d'unguma suka tafi part din Mamy.



Suna shiga part din Mamy suka tarar da'ita tareda wata baquwa, babbar mace ce sosai tana zaune akan kujera da wayarta a hannunta tana dannawa, Cikin farinciki Mamy tace"Captain har tafiyar tatashi?"


Captain Aryan yayi murmushi ya kalli  agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa,yace"Anty Ma-my barka da safiya"


Ta amsa masa cikin girmamawa tareda shige wa dan qaramin kitchen din dake falon ta. 


 Ashraf ya kalli babbar matar dake zaune afalo yace"ina kwana"


Cikin walwala tadago kanta tace"lafiya kalau yagida"


Kafin Ashraf yabata amsa shima Captain Aryan cikin sauri ya rissina yace mata "Barka da safiya"


Ta kalleshi tace"masha Allah,yawwa sannunku"


Adede lokacin Mamy tafuto daga kitchen hannunta daukeda leda,tabawa Captain Aryan tace"ga dambun kaza"



Ya kalli ledar hannunta cikin shagwa6a yace"haba Anty Ma-my, gaskiya ni bazan tafi dashi a leda ba,saikace wani marar gata,Allah nide saide ki sauya min,haba Anty Ma-my kina d'an girmama ni mana,amma haka abu aleda?"

ya qarasa maganar cikin shagwa6a kamar zai fashe da kuka.


Mamy tace"naqi,bazan sauya maba, kaje kayi aure sai matarka ta dinga saka maka a flask"


Captain Aryan yayi shiru yana kallon wannan leda,duk girmansa Anty Mamy bazata sake girmama shi tazuba masa a qayataccen food flask ba?bai Isa yayi magana ba komai sai tace yaje yayi aure(😔) 


Ashraf yayi murmushi yazuba musu ido yana kallon wannan drama tasu, adede lokacin Mawahib tafuto daga dakinta tana sanye cikin riga da siket 'yan kanti, amma tasaka mayafi a jikinta, ganinsu yaya Captain a falon yasa taja ta tsaya daga nan bakin qofar d'akinta. 


Ashraf yana ganin futowar ta yamaida kallonsa gareta,yazuba mata manyan idonsa yana kallonta cikeda so. 



Qawar Mamy dake zaune agefe tana ganin abinda yake faruwa tayi dariya tace"Maryam wannan kamar yaran nan naki dakika yayesu ko?"


Cikin sauri Captain Aryan yajuya yana sake kallon matar, tunda yaji tana maganar lokacin da Anty Mamy ta yayesu yasan cewa tabbas babbar mace ce,kuma tasan yarintar su,yagama qarewa matar kallo kenan yajuyo zai maida kallonsa wajan Mamy anan idonsa yasauka akan Mawahib,sai akayi dace idonsa ya sauka cikin nata qwayar idon,lokaci daya bugun zuciyar su yasauya,cikin sauri kowa ya janye idonsa.


Mamy tayi murmushi tace"Sister Hadiza sune wallahi, gasunan duk sun girma"


Babbar matar da aka kira da Sister Hadiza tace"ikon Allah,kinga duk sun girma sun taroki kamar wasu qannanki, waye kwa me tsoron ruwan zafi acikinsu lokacin da aka musu kaciya?"(🙊🙈😂🙆🏻‍♀️)


Mawahib ta dago kanta da sauri ta kalli Sister Hadiza.


Cikin sauri Captain Aryan ya runtse idonsa, saboda yasan akansa ake maganar, shitake tambaya, yatuna Mawahib fa tana cikin falon nan,shikkenan matar nan tagama dashi,ta kunyata shi agaban wannan yarinyar, cikin sauri yafuto daga falon da ledar dambun kazansa a hannu yanaji kamar ya nutse awajan dan kunya(😂)


Ashraf yayi dariya shima yabi bayansa












(Sister Hadiza baki kyauta mana ba🤣   asauka lafiya captain 🙏🏻)






Amnah El Yaqoub✍🏻


💗MAWAHIB💗



Writing By Amnah El Yaqoub



11&12




Mawahib tayi murmushi tashige dakinta, cikin ranta tana fadin su Yaya Captain anji kunya. 



Yana fita qofar gida mutanan da su kasan da tafiyarsa duk suna tsaye,suna ganinsa kuwa suka fara yimasa addu'ar sauka lafiya,saida yayi musu ihsani kamar yanda yasaba duk tafiyar da zaiyi, sannan ya qarasa wajan iyayen nasa maza duka su ukun suna gefe a zaune,Alhaji Isah mijin Mamy ya kalle shi da fara'ah yace"Captain har zaka koma aikin bazaka zauna ko sati d'aya kayi manaba?"


Murmushi yayi,duk da kawu Isah kawunsa ne sunada damar dazasuyi wasa da dariya a tsakanin su amma basa wasan, yanajin girman kawun nasa sosai akwai mutuntawa a tsakanin su,amma kuma idan shida Ashraf ne haka zaka gansu suna wasa da dariya kamar yaya da qani, cikin murmushin yace"eh kawu,saboda nataho da wadancen ne shiyasa zan koma akan lokaci"

yafadi hakan yana juyawa yana kallon sojojin dasuka rakoshi su hudu, Alhaji Isah yace"eh hakane kuma,to Allah yakaiku lafiya,Allah yatsare hanya"


Cikin ladabi ya amsa da "Amin"

Sannan ya qarasa wajan Alhaji Khaleed da Kuma mahaifinsa Alqali, sukayi sallama, anan ne yake musu albishir din tafiyar su aikin hajji wannan shekarar gaba dayansu wanda zasu biya musu shida Ashraf, sunyi farinciki sosai,Alqali yasanya musu albarka duka su biyun,suna qarasowa jikin mota Captain Aryan ya rungume Ashraf wanda jikinsa yayi sanyi sosai akan tafiyar Aryan din, sannan yasake shi,Ashraf yariqe hannunsa yace"meyasa bazakubi jirgi bane?"


Captain Aryan yayi murmushi yace"saboda muma kanmu tsaron ne,muda ya kamata mubawa yan qasa tsaro idan muka fara gudun hanya yaya kenan? dani kadai ne sainabi jirgi Ash,amma yanzu duk wanda yaganmu ahanya zaiso yabiyo bayanmu saboda yasan zai samu tsaro da kariya awajan mu,insha Allah babu damuwa"

Ashraf yasaki ajiyar zuciya yace"to shikkenan,sai munyi waya"

Captain Aryan yagyada kansa sannan yashiga mota sukaja suka tafi.


Suna tafiya ahanya yana tuna irin kunyar da matar nan qawar Mamy tabashi agaban yarinyar nan Mawahib,koda wanne ido zai sake kallonta oho,danma ba sabgarta yake shiga ba bare tasake samun damar rainashi,sai yanzu ne yatuna dukansu matan gidan yabasu kudi amma banda Anty Mamy saboda ya futo cikin kunya ko sallamar kirki ba suyi ba,already yanada account number dinta, cikin sauri ya laluboshi yayi mata transfer, sannan yamaida wayarsa aljihunsa tareda lumshe idonsa,motar shiru babu surutu kasancewar sunsan cewa ogan nasu bayason surutu.



******


Har motocin su Captain Aryan sukai nisa aka dena hangosu Ashraf yana tsaye a wajan yakasa dena kallon hanyar, mamaki yakama Alqali, da alama akwai abinda yake damun Ashraf,qarara ga damuwa nan ta baiyana a fuskarsa,yana kallonsa saida ya dade atsaye a wajan sannan yajuya yashiga gida,shima kansa Alqali sai zaman qofar gidan ya gagareshi, Ashraf din baidade da shiga gidaba shima yad'oru abayansa ya shige, kai tsaye dakinsu Ashraf din yanufa,Ashraf yana ganin mahaifin nasa a dakinsu mamaki ya kamashi,saboda babu abinda yake kawo shi dakin saide in yanason ganinsu yakira su suje, zama yayi abakin gadon cikin fuskarsa ta kamala yadubi Ashraf yace"babu damuwa deko?"


Babu 6oye-6oye Ashraf yace"Daddy banason tafiyar Aryan,kuma nafada masa banaso yatafi shine yarabu dani ya shirya yayi tafiyarsa,nikuma inaji kamar wani abune zai sameshi"


Alqali yayi ajiyar zuciya yace"ka kwantar da hankalin ka,kayi masa addu'ah insha Allahu babu abinda zai faru sai alkhairi,kasaki jikinka kayi walwala kaji ko?"


Sai a lokacin Ashraf yasaki wata irin ajiyar zuciya,Alqali yasake kallon fuskarsa yagade har zuwa lokacin kamar akwai sauran magana, cikin hikima irin tasu ta iyaye yayi murmushi yace"tosaime kuma?"


Cikin kunya Ashraf yafara sosa kunnansa yace"Daddy dama....dama inaso inyima magana Daddy inaso ka nemamin auren Mawahib a wajan Kawu Isah,wallahi Ina sonta Daddy"


Tsananin mamaki yakama Alqali,kowanne irin so Ashraf yake yiwa Mawahib ya tabbatar badan qarami bane,tunda bai tsaya Iya cewa a nema masa auren ba, saida ya dubi tsabar idonsa yasake cewa yana sonta, Alqali yayi murmushi tace"to wannan aiba abun damuwa bane,abun farinciki ne ai wannan,saide kasan mahaifiyar ka batayi da mahaifiyar Mawahib din ko? to saboda kwanciyar hankalin ita yarinyar, yakamata kaje kasamu mahaifiyar ku da maganar idan har ta nuna tana son Mawahib din kaga babu damuwa koda ka aure ta zasu cigaba da zama lafiya a tsakanin su"


Ashraf yace"eh Daddy zanyi mata maganar ,ita naso nafara fadawa ma, to sai nafara yiwa Aryan maganar,dafarko yanuna bayaso, saidaga baya naga yabar maganar, amma nasan Momy zataso abinda nakeso"


Alqali tace"to Alhamdulillah,naji dadin wannan maganar taka,koba komai aurenka da Mawahib din zai Iya kawo shiryawar mahaifiyar ka da mahaifiyar ita Mawahib din,zan samu Alhaji Khaleed da shi Alhaji Isah akan maganar,Allah yayi maka albarka"


Cikin jin dadi Ashraf yace"Amin ya Allah Daddy"


Cikin sigar tsokana Alqali yace"shikkenan hankali ya kwanta?"


Cikin kunya Ashraf yace"eh Daddy"


Alqali yasaka hannu yashafa sumar kansa, sannan yafice daga dakin tareda rufowa.



******


Tafiyar su tayi nisa sosai har zuwa lokacin Captain Aryan idonsa a lumshe suke,kamar an jefo musu wani abu haka wani babban mutum sanye da farar shadda gamida babbar riga sai maiqo shaddar take yafado gaban motarsu Captain,lokaci daya direban su Captain Aryan yataka wani mahaukacin birki wanda yasa Captain din bude idonsa cikin sauri, motar tana tsayawa mutumin yanufo murfin motar tasu yana kokarin budewa yanayi yana waigen bayan sa, lokaci daya suka fara jin qaran harbi, cikin sauri Captain da sauran sojoji suka bude motar suka futo, Captain Aryan yadubi mutumin yana tambayarsa "meyake faruwa?"


Kwata kwata tashin hankali yahana Captain Aryan gane tsananin kamar da wannan mutumin yake da Mawahib,daga idonsa har cikakkiyar girarsa gaba daya basuda banbanci dana Mawahib, fari ne tas kamar ka latsa jikinsa jini yafuto, kafin mutumin yabashi amsa kamar daga sama sukaji taaaassss an iyo musu harbi, cikin tsananin tashin hankali mutumin nan yadubi Captain Aryan yace"ka taimaka min yaro, zasu kasheni, zasu kasheni ka taimaka min mubar wajannan basuda Imani zasu kasheni...."


Captain Aryan yanajin haka ya juya ya kalli sojojin dayake tare dasu, kallo daya yayi musu, suka gane abinda yake nufi nan take suka fitarda bindiga suka fara sakin wuta, lokaci daya wajen ya karade da qaran bindiga, har zuwa wannan lokacin Captain Aryan baiyi harbi ba, yana tsaye yariqe wannan babban mutumin ya 6oyeshi a bayansa


Daya daga cikin wanda suka kawo harin ne yazo daga bayansu Captain zai harbi mutumin,wannan mutumin yana ganin haka nan take ya lumshe idonsa yafara karanta kalmar shahada, saboda yagama tabbatar da cewa harbin da'aka iyo daga bayan nan yariga ya sameshi, yasan cewa yau tasa taqare mutuwar sa tazo,Captain Aryan dayake riqe dashi yajuya da sauri saboda qaran harbi dayaji, yana juyawa adede lokacin har bullet din yazo wajan su,cikin sauri yature wannan mutumin,yana tureshi adede lokacin bullet din yazo kai tsaye harbi yasauka agefen qirjin Captain Aryan, cikin sauri yasaka hannu yadafe wajan,yasaka hannunsa na dama ya dauko 'yar qaramar bindigar datake aljihun wandonsa babu 6ata lokaci shima yarama harbin,nan take kuwa wancen din yafadi qasa babu alamun numfashi atare dashi.


Sauran maharan suna ganin ankashe ogansu,suma suka gudu kowa yayi ta kansa, wannan babban mutumin kuwa yana ganin yanda Captain yatare masa harbi lokaci daya jikinsa yadauki rawa,yadora hannunsa aka kamar ba babba ba yafara kuka wiwi, cikin kuka yake fadin"lahaula wala quwata illa billahi aliyal azim,yaro meyasa kayi haka? meyasa baka bari sun kasheni ba? meyasa zaka sadaukar da rayuwarka saboda ni?"

Duk wannan maganganun dayake Captain Aryan baya jinsa, hannunsa dayasa yatare inda yaji shigar bullet din jikinsa gaba daya hannun ya6aci da jini,yawan jinin daya zubane yasa nan take jini yafara daukar sa, idanunsa suka fara lumshewa, atake jiri ya debeshi yazube a wajan,sauran sojojinsa suna ganin halin da Captain yashiga cikin sauri suka saka shi cikin mota,shima wannan mutumin cikin sauri yafada cikin motar sukaja da mugun gudu sukabar wajan,kai tsaye nasarawa state suka qarasa dashi saboda tafi musu kusa akan Abujan,wani private hospital suka qarasa dashi,motocinsu suna tsayawa wannan babban mutumin yabude motar yafuto sai hawaye yake kamar ba babban mutum ba, farar shaddarsa wacce take maiqo gaba daya ta6aci da jini, ganin yanda babban mutum kamar sa yake kuka wiwi, yasa hankalin ma'aikatan asbitin yadawo kansa, cikin sauri aka kawo musu dauki, aka turo dan qaramin gadon daukan majinyata zuwa gaban motarsu, cikin sauri aka dora Captain Aryan akai, wanda yake kwance babu alamun numfashi atare dashi nurses suna tura gadon zuwa dakin tiyata dasauri amma wannan babban mutumin cikin kuka  yake bin gadon yana fadin"likita ka taimakeni,kada yaron nan yamutu ta sanadi na,katemakeni likita"


Yana wannan surutun baisan ma sun qaraso zuwa dakin tiyatar ba,suna zuwa suka dakatar dashi sukuma suka shige ciki da Captain tareda rufo qofar



******



Da yamma Nabiha tana dakin Mawahib suna firar su,Nabiha tace"Mawahib Yaya Ashraf kuwa yafada miki yana sonki?"


Mawahib tace" Dama tunanin kine,ni har yanzu banga alamun hakaba,muna de mutunci kamar baya"


Jikin Nabiha yayi sanyi,ahankali tace"Mawahib Yaya Ashraf yana sonki...."


Cikin sauri Mawahib tace"koda yafadamin ko, bazan ta6a aurensa ba, saboda dan'uwansa yaya Captain baya sona,sannan mahaifiyar su Momy kilishi itama bata sona, to wanne irin zaman aure zanyi dashi?, kidena min wannan maganar Nabiha,Allah yamin tsari da auren 'ya'yanta"


Nabiha tayi murmushi tace"to shikkenan Mawahib yawuce"


Abba da Mamy suna zaune afalo Abba ya Kalleta yace"ina yarinyar nan take ne?"


Mamy tace"Mawahib? tana daki itada Nabiha tun dazu" 


Kafin yasake magana saiga Alqali da kansa shida Alhaji khaleed acikin falon nasu, mamaki yakama Abba da Mamy, cikin sauri Alhaji Isah yatashi tsaye yana cewa "Yaya kaida kanka? aida kun kirani nazo" 


Alqali yayi murmushi, suka nemi waje suka zauna,cikin ladabi Mamy ta tsugunna ta gaishe su,cikin ranta tana mamakin menene yakawo su Yaya Khaleed da Yaya Alqali har part dinsu yau?


Ahankali tajuya tashiga kitchen domin tahado musu dan abun motsa baki. 


******


Ashraf yayi wankansa ya shirya tsaf cikin qananun kaya nashan is'ka kamar yanda yasa ba, wayarsa yadauka yakira Captain Aryan saide wannan karon ma wayar taqi shiga,tun azahar yake kiransa yanason yaji kosun sauka lafiya amma wayar taqi shiga yarasa meyasa?


a fili yace"insha Allah lafiya...."


Sannan yafuto iai tsaye yatafi part dinsu, Hajiya kilishi tana zaune akan kujera tana waya cikin iko kamar yanda tasaba, Ashraf ya zauna agefenta yana sake try number Aryan...


Cikin wayar yaji tana fadin"banason atamfofi tsofaffi fa,masu tsada nakeso ki bayar akawo min guda goma,amma guda bibbiyu kala daya,kayan lefen 'yanbiyu na nake hadawa banason asaka kaya masu araha acikin lefensu". 


Ashraf yayi murmushi ya jinjina kansa alamun lalle Momy da gaske take (😂)

Can saiyaji tace"to shikkenan ki gaida Asalamiyya,saita kawomin din"


Yanajin takashe wayar ya Kalleta cikin zaquwa yace "Momy"


Cikin kulawa tace"Na'am Ashraf, yanaganka cikin farinciki ne ko an samomin sirika ne?"


Cikin murna yace" kamar kinsani Momy,ai harna fadawa Daddy ma a nemamin auren ta"


Hajiya kilishi ta gyara zamanta ta kalleshi dakyau, sannan tadaga hannunta sama tace"Alhamdulillah, Allah abun godia,saura Aryan kuma"


Tajuya tasake kallonsa tace"yar gidan waye afadin qasar nan?"


Cikin rashin damuwa yace"Momy Mawahib cefa...."


Hajiya kilishi saitaji kamar bataji bataji abinda yafada daidai ba,cikin son tabbatar wa tasake kallonsa sosai tace"wakace?"


Ashraf yayi murmushi yace"Mawahib din Anty Mamy cefa"


Cikin sauri Hajiya kilishi tamari fuskarta,incase in mafarki take tota farka (😂)

saida tasake marin fuskarta akaro na biyu taga de tabbas ba mafarki takeba babban danta Ashraf shine a zaune agabanta yana fada mata yanason jinin Maryam, cikin son tabbatar wa ta kalleshi tace"Ashraf kaine kake fadamin kanason ka auri 'yar gidan Maryam?"


Cikin sauri ya sunkuyar da kansa qasa,kafin yadago yabata amsa yaqa ta miqe tsaye, cikin sauri yadago kansa yace"Momy Ina zakije?"


Bata saurari abinda zaice mataba tanufi qofar fita daga part din nasu,cikin sauri Ashraf ya riqo hannunta,yace"Momy ki tsaya muyi magana Ina zakije?"


Hajiya kilishi gaba daya idonta ya rufe, burinta kawai taganta a gaban Mamy, ko sauraren Ashraf batayi ba tafizge hannunta tanufi part din Mamy


******




Tunda suka shiga dakin tiyata dashi har yanzu basu futo ba,wannan babban mutumin banda zagaya wajan babu abinda yake, hular kansa tana hannunsa yana firfita da'ita, gumi duk ya jiqa masa jiki, idanunsa yayi jajir har zuwa yanzu hawaye yake,sai zagaya wajan yake yana fadin"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un..."


Gashi mutane sun kasa zuwa kusa dashi su bashi haquri saboda sojoji guda hudu dasuke tsaye a wajan kowanne a cikinsu hannunsa yana dauke da bindiga,kana ganin yanda suke zare ido suna zagaya wajan,zakasan cewa ba qaramin mutum suka kawo asbitin ba.


Cikin sauri wannan mutumin yadauki wayarsa yayi kira,daga dayan 6angaren aka daga akace"ALHAJI MA'ARUF.... Ina kashiga ne naje gidan gonarka bansamekaba?"


Cikin kuka wannan babban mutumin wanda aka kira da Alhaji Ma'aruf cikin tashin hankali ya goge hawayen idonsa yace"Alhaji Bala akwai matsala,muna asbiti, yaro zai mutu a dalilina,kazo kasameni yanzu"


Alhaji bala daga nasa 6angaren yace"Yanaji kana kuka? gani nan zuwa, kayi haquri gani nan zuwa yanzu-yanzu, kuna wanne asbiti?".



******


Haly JASHERU venture's,munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba algus da ha'inci kayanmu daga Ethiopian ne prdct dinmu muna Ethiopian magic hair oil anti dandruff shampoo serum bdy cream hand cream magungunan chuttuka da na mata masu inganchi da qara lfy ajikin dan 

adam ga number kmr hk 07046665338 ko 07061664264 munada distributor ako Ina afadin kasarnan da ketare muna koya harkomin kasuwnchinmu ga masu bukata akan 5000 kacal


sannan munada tsuntsaye na kasashen waje tattabaru game bukata ko koya akwai riba kwarai aharkar mebuqata yasiya koya koya seyanemeni a number na kamar haka 07046665338 ko 07061664264, ku antayo ayi tafiyar daku,yar'uwa kikoyi sana'ah akan wannan farashi me sauqi kema ki kafa kanki💃🏼


******


Abba yadubi yayansa Alqali yace"to yanzu Yaya, Yaya zamuyi da maganar Nabil?"


Alqali yace"Nabil ai tambaya yayi yana so yafara zuwa wajanta zance,ba izni ya nema a bashi dama yakawo kayan neman aure ba,inda ace yakawo wani Abu gida,kokuma iyayensa sunzo sun sameni munyi magana dasu baki da baki, to bazan goyawa Ashraf baya ba,sannan inda ya shirya da tuni iyaye sun shiga cikin maganar"


Alhaji khaleed yace"to Yaya koda ace sunzo munyi magana ma,ai munada damar dazamu hana auren mubawa danmu,saboda gida bai qoshi ba,ai baza'a bawa daji ba, Yaya muna ganin yarinya me hankali da tarbiya, zamu bari wani daga nesa yazo ya dauketa 'ya'yansa dashi kansa su mori wannan tarbiyar tata, bayan mukuma gamu da samari agida har guda biyu ace mun kasa qwato wannan tarbiyar tadawo cikin gidanmu? nima Ina ganin tunda maganar Nabil din batayi nisa ba, abawa Ashraf din kawai..."


Kafin Alhaji khaleed yayi magana Hajiya kilishi ta bankado kofar falon tashigo idonta yarufe da masifa ko ganinsu Alqali dasuke zaune a falon batayi ba, Ashraf ma yabiyo bayanta yana kokarin riqe hannunta musanman shida yaga iyayensa maza a zaune a falon,Hajiya kilishi ta fizge hannunta ta qarasa shigowa cikin falon. 


Cikin masifa tadaga murya tafara qwalawa Mamy kira"Maryam! Maryam!! kina Ina?"


Mawahib da Nabiha dasuke zaune adaki suna kalle kallen video a Instagram din Nabiha sunajin wannan kiran da akewa Mamy sukasan cewa yau gidan ba lafiyaba, cikin sauri sukai wulli da waya suka futo,saide suna ganin su Alqali a wajan sai sukai turus suka tsaya abakin kofar dakin Mawahib din. 


adede lokacin Mamy takawowa su Alqali wani hadadden cake jikinta duk yayi sanyi tun lokacin data farajin mazan gidan suna tattauna maganar auren Mawahib da Ashraf, wanda a zahiri bazata yarda da wannan auren ba. 


Cikin Masifa Hajiya kilishi ta tunkari Mamy tace"Maryam kinji dadi,yau burinki yacika,kinshiga kin fita kin rabani da d'ana,naji dadi kuma na godewa Allah dayasa baki hada da CAPTAIN ba,shima dakin mallakeshi da yanzu 'ya'yana biyu suna fada akan AGOLAR 'YARKI"


Cikin sauri Mawahib ta kalli Hajiya kilishi tana maimaita kalmar 'Agola' acikin ranta....

Ashraf ya sunkuyar da kansa qasa yana tunanin kode Hajiya kilishi bata cikin hayyacin tane shiyasa take kiran Mawahib da Agola? a'iya saninsa Mawahib de Uncle Isah ne ya haifeta. 


Mamy tana Jin furucin Hajiya kilishi lokaci daya hawaye ya wanke mata fuska,kokadan takasa daga idonta ta kalli mutanan falon,wani irin kukan baqin ciki ne ya kamata take taci gaba da kuka harda shashsheka. 

Nabiha tadinga rarraba ido tana ganin mutanan falon gaba daya jikinta rawa yake tashiga shock sosai saboda basu ta6a ganin tashin hankali irin wannan ba


Alqali dayake zaune ransa idan yayi dubu toya 6aci,baqin cikinsa a gaban qannansa maza matarsa tazo tashigo babu da'a duk da tana ganinsa a zaune a wajan kokadan bashida kwarjinin dazai hana Kilishi ciwa Mamy mutunci kenan? koda tayi niyyar zagin Mamy ai idan ta ganshi a zaune ya kamata ace tayi haquri tabari yabar wajan tukunna, cikin baqin ciki yatashi tsaye baiyi wata-wataba yadauke Hajiya kilishi da mari (🙆🏻‍♀️😳)


Cikin sauri Ashraf yadago kansa ya Kalli iyayen nasa,baqin ciki ya kamashi yau Daddy ne yake marin momy? shi kuwa wanne irin yaro neshi da yayi silar da mahaifinsa zai daga hannu yamari mahaifiyar sa?


Cikin qunci Hajiya kilishi ta kalli qwayar idon Alqali tace"qarya nayi? Ina ubanta? har yau kun ganshi da idonku ne? to billahillazi dana Ashraf bazai ta6a auren SHEGIYA ba"


Cikin sauri Mamy da fuskarta tagama jiqewa da hawaye tace" 'yata ba shegiya bace Yaya...,kiyi haquri nima ko bayan ranki bazan bari 'yata ta auri danki ba"


Mawahib tanajin furucin Mamy ta tabbatar da cewa kenan maganar Hajiya kilishi gaskiya ne, cikin tashin hankali tace"Mamy?"

Bata Iya sake magana ba wani kuka yataso mata, cikin sauri ta shige cikin dakinta tashin hankali yasa har tana bige Nabiha bata sani ba, cikin sauri itama Mamy tabi bayan Mawahib din cikin kuka. 


Alhaji khaleed mahaifin Nabiha yatashi tsaye saboda bazai Iya jure ganin fadan yayan nasu shida matarsa ba, cikin sauri yafice daga falon, Nabiha ma da idonta yayi jajir cikin gudu tafice tabar part din. 


Alqali ya Kalli Hajiya kilishi yace"kinji dadi? kin tonawa yarinya asiri kinji dadi ko? yanda kike qoqarin ganin kin tozarta wannan yarinyar kisani Allah zai saka mata ta'inda baki ta6a zato ba,saboda bata tsare miki komai ba"


Alhaji Isah yatashi tsaye cikin sanyin jiki yace"yaya kayi haquri,yaya kilishi kema kiyi haquri insha Allah wannan maganar anbarta"


Cikin sauri Ashraf ma da jikinsa yayi sanyi ya kalli mahaifin nasa yace"Daddy kuyi haquri,tunda Momy bataso zan haqura"


Cikin 6acin rai Alqali yace"Aure babu fashi sai anyi shi inde Ina raye,saide in Mawahib ce dakanta tace bataso"

Daga nan yasakai yafice daga falon cikin fishi babbar rigar nan tasa sai tashi sama take. 



Cikin 6acin rai Hajiya kilishi tace"haka Nima muddin Ina raye, wallahi dana bazai ta6a auren wannan yarinyar ba"

itama tafice daga falon ko rufo musu qofar batayi ba, Alhaji Isah yaja Ashraf jikinsa ya rarrashe shi, sannan ya bubbuga bayansa alamar lallashi, yajuya yabi bayan Mamy wadda tashiga dakin Mawahib. 

Tarar dasu yayi dukansu suna kuka daga Mawahib din har Mamy. 

Cikin kuka Mawahib tace"mamy da gaske ni shegiya ce banida mahaifi? Abba ba shine ya haifeni ba?"


Cikin sauri Mamy tarufe mata baki tace"karki sake kiran kanki da wannan sunan,ke yar halak ce kamar 'ya'yanta"


Alhaji Isah yayi gyaran murya yace"Maryam kudena wannan koke koken dan Allah,Mawahib de koda ace batada mahaifi nime tsaya matane a kowanne hali take ciki,barema kunadani, bazan ta6a bari kuyi kukaba, kuyi haquri kudena kuka,ki rarrasheta tayi shiru,"

Yana fadar haka yafuto daga dakin cikin sanyin jiki. 


Mawahib ta Kalli Mamy cikin kuka tace"Mamy waye mahaifi na? kibarni natafi wajansa ko Momy kilishi zata daina yimin gori Mamy" 


Mamy ta goge hawayen idonta tace"karki sakemin maganar mahaifin ki Mawahib,babu abinda zai kaiki wajansa,zan maye miki gurbin sa ako'ina"


******


Cikin tashin hankali Ashraf yakoma dakinsa, yana zuwa yakama kansa dayake masa barazanar rabewa gida biyu,cikin tashin hankali yafurta"innalillahi wa Inna ilaihirraji'un...."


Cikin sauri yadauki wayarsa yafara kiran Captain Aryan, saide har yanzu wayar kwata kwata bata shiga, cikin baqin ciki yayi wulli da wayar yadafe kansa da hannunsa (🤦🏻‍♂️) 



******


Basu futo daga dakin tiyatar ba sai qarfe biyu  nadare,kai tsaye dakin hutu aka turashi,aka hana kowa shiga inda yake,Alhaji Ma'aruf yakasa zaune yakasa tsaye,sai leqen Captain yake ta glass din kofar dakin yana kwance andaura masa qarin jini babu riga a jikinsa, ansaka masa audiga da bandeji a'inda harbin ya sameshi, fuskarsa tayi wani irin fayau lokaci guda.


Har aka kira sallar asuba shida sojojin nan idonsu biyu,abokinsa Alhaji Bala shine de yake dan gyangyadi a zaune.


Saida gari yawaye sannan likita yazo inda suke,hannunsa daukeda file,ganin Alhaji Ma'aruf yana kuka tunda sukazo,kuma yahana kansa sukuni,sannan gashi fari tas kamar yanda Captain Aryan yake,shiyasa yayi tunanin ko shine mahaifinsa, kai tsaye yace "Alhaji kaine mahaifin marar lafiyar?"


Cikin sauri Alhaji Ma'aruf yace"eh nine,likita babu matsala deko?bai mutu ba yana nan da ransa ko?"


Likitan yabude file din hannunsa ya kallesu gaba daya yace"menene sunan marar lafiyar?" 


Daya daga cikin Sojojin nan take yace"Captain Aryan I. Alqali" 

Likita yayi rubuce rubuce a file din sannan ya kalli Alhaji Ma'aruf yace"kazo ka sameni a office"


Cikin sauri yabi bayansa zuwa office din,suma sojojin suka doru abayansu,Likitan da baisan menene a tsakanin suba ya juyo ya kalli Sojojin yace"babu damuwa,zamuyi magana ne dashi kawai"


Jin hakan yasa suka dakata daga bakin qofar.


Suna zama a kujera likita ya kalli Alhaji Ma'aruf yace"Alhaji yaronka yasamu harbi a haqarqarinsa,ma'ana qasan qirjinsa daga gefe, amma bullet din bai shiga canciki sosai ba, Alhamdulillah yanzu ma zamu Iya sallamar sa idan ya farfado daga dogon suman dayake, saide akwai matsala guda daya,Alhaji kayi haquri yaronka yasamu matsala bazai Iya haihuwa ba,saboda bullet din baishiga cikin qashin haqarqarin ba amma yagogi qashin wajan , shikuma wannan qashin da bullet din ya goga, maniyin namiji yana fara samuwa ne daga cikin jinin dayake yawo daga tsakanin qashin haqarqari zuwa qashin baya,zaiji sha'awa normal kamar yanda yasaba, but idan yayi aure yanzu, bazai samu maniyi mai lafiya kuma me kaurin dazai bawa matarsa ciki ba,saboda bullet din yariga ya gogi qashin wajan, amma zamu dorashi akan magani,sannan kuma ya kiyaye cin abinci barkatai,saide megina jiki,yakiyaye cin maiqo,saboda cin abu mai maiqo zaisa yasake samun qarancin maniyin, (low sperm count),amma idan yafara shan maganin da zamu dorashi akai,lokaci zuwa lokaci yana gwada mu'amular aure da matarsa insha Allah sperm dinsa zai dawo Normal,harma yasamu ciki...."


Cikin sauri Alhaji Ma'aruf yafashe da kuka yace"likita karka qarasa, karka qarasa likita shikkenan nacuci yaron nan...." 

 haka yataso yafuto daga office din kamar mahaukaci  kamar wanda baya hayyacinsa ya nufi kofa zai fice daga Asbitin,Alhaji bala yabi bayansa cikin sauri yana tambayar "Alhaji Ma'aruf Ina zakaje? Meyasamu yaron?"


Alhaji Ma'aruf bai kula shi ba saida yafuto harabar asbitin kuka yaci qarfinsa yazube a farfajiyar asbitin yana kuka,nan da nan mutane suka taru a kansa ana bashi haquri, dayawa daga cikin mutanan sunyi tunanin mutuwa aka masa,Alhaji bala dayayi tunanin Captain Aryan yarasu ya tsugunna yace"Haba Alhaji Ma'aruf shi mamaci ai addu'ah yake buqata,ba kuka zaka masaba, addu'ar mu yake buqata yanzu haka"(😳) 


Alhaji Ma'aruf yace"kabarni inyi kuka Alhaji Bala,banta6a jin na tsani kaina nayi tir da halina ba tun bayan barin Maryam cikin rayuwa taba sai yau"


Alhaji bala ya runtse idonsa sannan yabude yadafa kafadar Alhaji Ma'aruf sannan yayi qasa da murya yace"akwai mutane anan,kayi haquri ka tashi dan Allah" 

Alhaji Ma'aruf ganin mutane suna masa kallon wanda aka yiwa mutuwa hakan yasa cikin sauri yatashi tsaye kamar wanda aka tsikare shi yafice daga harabar asbitin yana doka sauri kamar wani mahaukaci,tuni yagama yanke hukunci acikin ransa. 


shima Alhaji Bala cikin sauri yad'oru abayansa suka fice daga asbitin. 



******



ahankali yafara bude idonsa harya gama budeshi gaba daya,yaqarewa dakin dayake kwance kallo,ya kalli kayan jikinsa,sai a lokacin yatuna da abunda yafaru,ahankali yasake lumshe idonsa sannan yabude,babu wani alamun Jin ciwo yatashi zaune kamar ba aiki ne a jikinsa ba,sojojin dasuke tsaye daga waje suna hangoshi ta glass din dakin cikin sauri daya daga cikinsu yakira likita, likitan yana zuwa tare suka shiga dashi,likita yana ganin Captain a zaune nan da nan da yashiga taitayinsa saboda yasan cewa asbitin nasu ya kar6i baqin fuska masu ban tsoro, ahankali yafara dudduba shi, sannan yahada allura yayi masa a hannunsa, ya kalleshi yace"yaya kakejin wajan ciwon?"


Cikin miskilanci yace" banajin komai doctor,zaka Iya sallama ta yanzu?"


Cikin sauri yace"za'a baku sallamar insha Allah,amma akwai magungunan da zakasha yanzu,tukunna"


Baice dashi komai ba sai d'aga kansa da yayi kawai alamun yaji. 

Likitan yabawa daya daga cikin Sojojin kati sannan yace"muna buqatar wannan magungunan"

Daga nan yafuto daga dakin. 


Captain Aryan ya dudduba gefensa baiga wayarsa ba yadago ya kalli sojojin dasuke tsaye yace"whare is my phone?"


Cikin sauri daya daga cikinsu yasara masa sannan yabashi wayar cikin ladabi yace"mun rufe wayar ne oga,saboda kada hankalin yangida yatashi" 


Cikin 6acin rai yace"kamarya kada hankalinsu yatashi?,idan mutuwa nayi ma haka zaku kashe waya bazaku Kira gida kufada musu halinda nake ciki ba?"


Kasa bashi amsa sukai saboda babu girma yana fada suna fada, cikin sauri ya kunna wayarsa,yafara neman wayar Ashraf



******


Ashraf yana zaune cikin damuwa, Alqali ya kalleshi yace"Ina tunanin nima akwai abinda yake faruwa,tun jiya Ina kira gaba daya nakasa samunsa"


Alhaji khaleed yace"yaya Ina ganin fa gara ka barshi yaje wajan aikin nasu yagano koba lafiya ba"


Adede lokacin kiran wayar Captain yashigo cikin wayar Ashraf, cikin sauri Ashraf dayake zaune yatashi tsaye yana fadin"gashinan yana kira Daddy"

Yadauki wayar tareda sakata a amsa kuwwa,cikin muryar sa maicikeda aji murya can qasa yace"Ash..."


Cikin sauri Ashraf yace"Aryan Ina kakai wayarka tun jiya da yamma Ina neman ka?" 


Lumshe idonsa yayi,a hankali yace"ka kwantar da hankalin ka,munsamu tsautsayi ne a hanya harma nasamu harbi...."


Alhaji khaleed da Alhaji Isah tareda Alqali sunajin haka suka saki wani irin Salati 

Cikin sauri Ashraf yace"harbi? innalillahi garin Yaya? saida nacema karka tafi,yanzu kana Ina? Yaya Harbin naka da sauqi?" 


Gaba daya ya rikice,kwata kwata baya cikin nutsuwarsa sai tambaya yake jerowa Aryan din

Captain Aryan yayi murmushin qarfin hali yace"Ash..."


Kafin yaci gaba da magana Alqali ya kar6i wayar yace"kuna wanne asbiti....?"


******


Alhaji Ma'aruf da abokinsa Alhaji Bala suka turo kofar dakin suka shigo gaba dayansu su biyun duk jikinsu yayi sanyi kalau, adede lokacin Captain Aryan yagama waya da yan gida ya ajiye wayar agefensa,Captain ya zuba musu ido yana kallon su musanman Alhaji Ma'aruf wanda har zuwa wannan lokacin rigar jikinsa tana nan da sauran jini ajikinta,sai yanzu Captain yaqare masa kallo yaganshi fari tas idan ba hausa yayi bama zaka dauka ba bahaushe bane,Alhaji Ma'aruf ya kalleshi, tun kallon farko daya masa yasan cewa wannan acikin sojojin ma akwai tsare gida, zama yayi agefen gadon yace"yajikin naka?"


Ataqaice yace"Alhamdulillah"


Daga nan sukai shiru gaba dayansu,Alhaji Ma'aruf yarasa ta'ina zai fara,gaba daya yaron yayi masa kwarjini, daqyar yasamu qwarin gwiwar kallon sojojin yace musu "Dan Allah kuyi haquri kud'an bamu waje inaso zanyi magana dashi" 


Sunajin abinda Alhaji Ma'aruf yafada amma ko kadan basu motsa daga inda suke ba,saida Captain Aryan ya kallesu sannan suka fice daga dakin. 


Alhaji Ma'aruf ya kalli abokinsa Alhaji Bala yace"Alhaji bala zauna mana"


Alhaji Bala dayake tsorace da ganin sojojin yaqaraso ya zauna akan kujerar dakin. 


Alhaji Ma'aruf ya kalli Captain Aryan yace"Captain Aryan ko?"


Fuskar Captain Aryan babu wasa Ataqaice yace  "yes" 


Alhaji Ma'aruf yayi ajiyar zuciya yasake kallon Captain Aryan cikin tausayawa yace"Aryan kayi haquri nayi maka babban laifi,bansanka ba, kaima baka sanni ba, amma ka za6i ka sadaukar da rayuwarka saboda ni,da nasan cewa abinda zai faru dakai kenan bayan tare harbin nan dakayi,da wallahi gara ni in mutu, akan wanna masifar tasameka"


Captain Aryan yayi shiru yanajin Alhaji Ma'aruf yana masa bayani,yarasa menene dalilin yin wannan dogon bayanin,aikinsa shine ya kula da yan qasarsa,bai dauki wannan abun da yayi abakin komai ba. 


Alhaji Ma'aruf ya goge zufar daya fara sannan yaci gaba da fadin"likita yace sakamakon wannan harbin daya sameka, ba lalle sperm dinka ya iya samarda haihuwa ba,amma zai doraka akan magani idan kafara shan maganin insha Allah watarana za'a dace"


Cikin sauri Captain Aryan ya Kalli Alhaji Ma'aruf,cikin ransa yafara furta Kalmar nan ta"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un...."


Ya lumshe idonsa yaci gaba da maimaita kalmar acikin ransa,Alhaji Ma'aruf yasake kallonsa sannan yaci gaba da fadin"Ina roqon alfarmarka kadubi girman Allah da darajar sa, kayafemin,nasan cewa nine sanadi,ta dalilina hakan tafaru dakai,sakamakon hakane yasa yanzu-yanzu naje masallaci nida Aminina Alhaji Bala,NA 'DAURA MAKA AURE DA 'YATA RUQAYYA" (😳🙆🏻‍♀️🙊😱)


Captain Aryan da idonsa yake lumshe yana maimaita Kalmar innalillah aransa,cikin sauri yabude idonsa ya zabura daga inda yake zaune,gabansa banda dukan uku uku babu abunda yake,wacce irin masifa ce ta sameshi haka? daga taimako?


Alhaji Ma'aruf ya kalleshi,cikin sanyin jiki yaci gaba da fadin"nasan yanda kakeji aranka,kuma nasan nime laifi ne awajanka,nasan cewa duk matar daka aura taji labarin cewa ga lalurar data sameka,zaiyi wahala ta zauna dakai,idanma ta zauna dakai to watarana zata gorantama akan hakan

wannan dalilin ne yasa nabaka 'yata tacikina, nasan cewa 'yata bazata ta6a goran tamaba har abada,saboda nasan cewa mahaifiyar ta batayi mata irin wannan tarbiyar ba,idan babu damuwa inaso ka had'ani da iyayenka zanyi musu bayanin komai"


Captain Aryan ya runtse idonsa cikeda damuwa,sannan yabude su,idanun sunyi jajir,gabansa banda faduwa babu abinda yake,kansa ya dauki ciwo kamar zai rabe gida biyu, cikin tashin hankali ya kalli Alhaji Ma'aruf yace"please ko zaka bani space?"


Ganin yanda yake cikin damuwa komai zai Iya faruwa hakan yasa babu musu Alhaji Ma'aruf yatashi,yasaka hannu cikin aljihunsa yad'auko wani d'an qaramin kati ya ajiye agefen Captain Aryan sannan yace"wannan shine katina,duk lokacin da hankalinka ya kwanta,kaji kana buqatar matarka,kakirani,zankawo ma matarka..."











Masha Allah...Mawahib de Allah yayi ta Auri miji nagari 😂


Yaya batun saka ranar Ashraf da Mawahib? 🤔


Shin Nabil zai haqura? 🤔


menene zai faru idan Captain Aryan yasan cewa wannan qwailar itace matarsa?🤔

Mezai faru idan labari yazo wajan Mamy? 🤔

Alqali yace inde yana raye Ashraf saiya auri Mawahib,shin kuna ganin Captain Aryan zai saketa ne?

Da alama yanzu ne Hajiya kilishi zataga tsantsar ikon Allah 😂

Alhaji Ma'aruf rashin sani yasa ya qulla qullalliya a gidan Alqali 💃💃

Yanzu labarin yafara,karki bari ayi bake ki, kibiya kudin ki, ki antayo paid group din Mawahib atafi dake💃💃💃

Alhamdulillah....anan nakawo qarshan free page's dina, duk meson cigaban littafin MAWAHIB, yabiya naira 500 kacal👌🏻


Yanzu kwamacalar tafara,akwai rikici agaba kala kala duk a gidan Alqali, koda kudinka saida rabonka 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼







Amnah El Yaqoub✍🏻



No comments