Breaking News

Matar makaho 90-91

 


Page9⃣0⃣&9⃣1⃣


"Daga yau banason kara  gani koh jin ka kira khadija a waya yafi sau biyu a rana, na gaji da halinku kunce ba soyayya kuke va ?sannan kai bakada aiki sai kiranta karfa ka manta kai d'alibin kiwon lafiya ne, bai kamata kana wasa da karatu ba"?


Insha Allah Aunty za'a kiyaye.


"Sannan ke kuma khadija kinga dai kokarin shiga ss 2 kike, kuma niyata in kika dage saina miki registration in waec next year,  amma tunda wasa zaki saka a ranki bismillah zakiyita zama har 21 years a secondary"


Shap wayaga maman aji, kalamu yace yana dariya.


"Kaga banason shashanci kalamu, ina muku fad'a kana sako wasa"


Sorry Aunty zamu kiyaye yace yana kallon khadija, ke akwai sauran shinkafa ki zubamin yau nanne na tuwo ta dafa?


Babu kawai khadija tace tana mikewa  ta shiga daki.


"Kaga kalamu tashi akwai macaroni data dafa a tukunya kaje ka iba tunda kitchen in ba bakon ka bane, karku dameni da surutu kaina ciwo yake".


Mikewa yayi ya shiga kitchen in ya ibo makaroni da miyar kifin gesha, yana ci yana latsa wayarsa don yanzun sumayya bata surutu kamar da.


*************

Muhammad basu farka ba kuma ba'a tadasu ba sai kusan 10 na safe suka farka don kansu, wanka sarki yayi sosai yaji sauki jikinsa yayi karfi, kaya ya saka muhammad ma wanka yayi yasha jumfa da aka kawo masa mai masifar kyau da tsada, abincin karyawa aka jera musu a daining tare suka karya su biyu suna hira gwanin sha'awa, a hankali sarki yace muhammad wai nikam ban tambaye ka kaninku ba?


Wanne kenan Abbajo?


Kanin salim mana.


Ai macece khadija tananan.


Allah sarki yanzun fa shekarun ta 18 da wata 9 ta kusa 19?nasan itama yanzun ta kusa nabila koh?


Eh Abbajo ta girma abinta.


Allah ya raya mini ku ta farkin islama?


Ameeen, haka suna ci suna hira har suka gama yusuf ya gyara rawanin sa yana rike da hannun muhammad sukayi fada.


Ana bude musu kofa suna shiga saida gaban muhammad ya fad'i, ganin wasu jajayen buzaye, cikin su harda baba da gidado da badaru a zazzaune, sosai fadar ta cika makil da manya da yara alamu dai yusuf yasan da taron, sake hannun muhammad yayi ya zauna a kujeransa  yama muhammad nuni da kasan cafen.


Ba musu muhammad ya zauna a hankali, yayinda mutane kibinsa da kallo na mamaki sosai.


 a hankali yusuf yasa hannu ya ja rawanin fuskar sa, take fuskar nan mai kamala da dattako ya bayyana koh yaransa basu samun ganinta a araha irin na yau, kowa na kasa yusuf ne kawai a kujera.


Gyaran murya yusuf yayi, Asslamu Alaikum warahamatullahi wabarkatuhu.


Gabaki d'aya jama'an dake falon suka amsa masa sallamar.


Na gode Allah daya nuna mini wannan rana,  wanda ban taba tsammanin ganinsa nan kusa ba, koh ince ban taba sa ran ganinsa ba,Ayau xan sanar daku yan uwana don duk fadar nan yan uwana ne  in aka cire mutane uku,ayau xan sanar daku abinda nasan dayawan cikin ku zasuyi mamaki,   muhammad Al'ameen, d'aya daga cikin masu aikin gidan nan D'anane, kuma shine a gabana.


Gabaki d'aya falon ya d'auki surutan mutane, daker aka samu ya lafa, yaci gaba da magana, nasan dole jama'a zasuyi mamaki Amma banda mahmah mahaifiyata, don ita tana d'aya daga cikin mutanen da suka san da wannan magana,mahmah ya kira sunan mahaifiyar sa dake xaune a gefe.


Na'am .


A taushashe yace, Mahmah ina son ki sanar dasu Asalin abinda ya faru shekarun baya da suka wuce, bani da koshin lafiya sosai kuma inbabu damuwa ina son kiyi da hausa wa'inda basa ji, Ramadan yana fassara musu.


Gyara zama mahmah tayi ta fara magana kamar haka.


*SHEKARUN BAYA DA SUKA WUCE* 

 Masarautar karfe shine cikekken sunan masarautar gidan nan, wanda ke d'auke da tambarin zaki ya samo asaline tun bayan shekaru da suka shude, ka'idar masarautar  ne duk yarima mai jiran gaso za'a makala masa sarka na magajin masarauta, sarkane daya samo asali daga makafan masarauta,  duk wanda ya d'aura sarkan badai tsafi jifa koh tsibbo ya kamasa ba saida ikon Allah.


mutallaf shine cikekken sunan mahaifin yusuf, a lokacin sarki ne yana da matarsa ta farko mai suna Hauwa-kulu sai dai Allah bai basu haihuwa ba har girma ya soma kama mutallaf don a lokacin harya haura shekara 50, hakan yasa kasa kara aure ya auro Hajara cikin ikon Allah shekara na zagayo wa hajara ta haifa masa yarinya mace, duk da yaso d'a namiji Amma hakan bai hanasa murnan samun mace ba, aka saka mata sunan hauwa-kulu yama uwar gidan sa takwara, haka hajara tayi ta haihuwar mata har hudu rus, sosai tsoro ya shiga zuciyar mutallaf, koh baida rabon d'a namjine kasancewar su a zuriyarsu ana yawan haihuwar mata, sama da maza gashi yana son magaji ga girma ya kamasa, Amma daga baya saiya maida lamuransa ga Allah, yaran nan kaf a wajen hauwa suke ita ke kula dasu kasancewar ta bata taba haihuwa ba kuma zaman lafiya suke da hajara.


Hajara ta sake samun ciki sam wannan karon mutallaf bai kwallafawa ransa namiji zai haifa ba sam, cikin ikon Allah hajara ta haifi d'a namiji yaro yaci suna yusuf, tunda aka haifi yusuf mutallaf ya d'auki son duniya ya d'aura masa bama shi kad'ai ba duk wani masoyinsa nason yusuf, kuma aka d'aura masa sarkan magajin masarauta, saida hajara ta haifi yusuf daga shi bata kara haihuwa ba.


Yar kaninta hauwa ta d'auko tana riko mai suna zahra, lokacin yusuf nada shekara goma sha biyar, sosai zarah keson yusuf ganin saukin kansa babu izzah koh nuna isa mutum ne na mutane, bai d'auki son mulki ya sakawa ransa ba wannan yasa zahra keson maganar sa.


A lokacin da yusuf ya cika shekara 20 yayi haddan Alkur'ani mai girma da haddisai,  yana cigaba da karatunsa na gaba da secondary, hauwa ta kwanta ciwo wanda kafun ta mutu saida ta nemi Alfarman mutallaf daya had'a aure tsakanin yar d'an uwanta zahra da yusuf, koh bayan ranta za'a tuna da ita a masarautan karfe, kuma zuriya vai kare tsakanin ta da mutallaf ba, babu wani shamaki mutallaf ya Amince mata.


Bayan mutuwar hauwa mutallaf ya tada maganar auren yusuf da zahra, daman zahra nason yusuf wanda kowa ya sani sai dai shi yusuf inne bayayinta a lokacin, yaso gardama da nuna shifa Aure ba yanzun ba sai ya girma,  Amma mahaifinsa ya murza ido akan lalle lalle auren Addanayen sa da za'ayi guda biyu Kafshatu da maisara tare za'a had'a da nasa, yusuf yayi iyya yinsa akan bayason zahra,  abasa dama ya nemo wance zai aura Amma ina mutallaf yace bazai Aminta ba.


Rana bata karya Saidai uwar deya taji kunya, a ranan da aka zartar amatsayin ranan d'auren auren yusuf da yan uwansa ya cika, Amma abin takaici an waye gari babu yusuf a gidan Sarauta.


Sarki ya shiga tashin hankali Amma daga baya saiyayi zuciya akan duk inda yusuf yaje wata rana zai juyo gida, in ma bai dawo ba yama kansa, haka aka d'aura auren zahra da wani d'an uwanta.


Tunda sarki ya rasa yusuf ya shiga wani irin matsanancin damuwa, ganin an share shekara goma babu yusuf babu a lamansa a lokacin hajara ta sake haihuwar na miji zulkiflu, sosai sarki yayi murna ya samu wani d'a na miji,  sai dai ganin girma ya fara kamasa gashi shekaru naja yana sonyin murabas Amma babu magajiiiii.


Shekaru sunja Amma shuru babu yusuf babu labarin sa, har hajara ta sake haihuwar wani d'a na mijin (Ramadan)dayake daman ita akwai kuruciya a tare da ita, Yusuf kam bai dawo ba shekaru sai tafiya suke har mahaifin sa ya kwanta ciwon ajali mai tsanani, a lokacin zulkiflu ya girma yakai saurayi, ga yan uwansa mata duk sunyi aure su hudu gashi mazajen su manya ne a kasa wasu kuma sarakuna.


Hade Hannu sukayi aka bazama neman yusuf kasa da kasa Amma ina ba'aga yusuf ba gashi jikin mutallaf sai kara tsanani yake,  baida magana saina d'ansa yusuf yana son ganin d'ansa kafun numfashinsa na karshe.


Rana tsaka saiga shi an gano yusuf yana NIGERIA Kuma a ranan aka samu labarin An kaisa prison, bai kwana ba aka cirosa washe gari sai gasu a NIGER Har gaban mahafinsa dake kwance aka dukar dashi.


Ganin halinda yusuf yaga mahaifinsa a take kuka ya kamasa tare da neman yafiyar mahaifinsa, sai a lokacin nadama tazo masa ganin yanda uban ya tsufa matuka, shekaru sunja, da ba'a d'aukosa ba da shikenan daker ya sake ganinsa sai wani ikon Allah.


Mutallaf dake kwance cikin ciwo yace bazai taba yafe masa ba har sai ya masa Alkawari?


Ba musu Yusuf yace ya Amince a take mutallaf yace koh bayan ransa bai yarda ya sake taka nigeria ba, koma menene zai kaisa baiyarda ba sannan ya masa Alkawarin zai auri lawiza(kanwar zahra) don cikawa hauwa burinta na had'a jini da zuriyar su.


A take yusuf yasa kuka yana sanar da mahaifinsa cewa yana da mata da yara a nageria, a basa dama ya d'auko su kuma ya Amince da auren lawiza.


Kin Yarda mutallaf yayi ganin haka yasa yusuf D'aukar wannan Alkawari, shi kuma mutallf ya yafe masa duniya da lahira tare da sakamasa Albarka, anyi haka washe gari aka d'aura auren yusuf da lawiza sati mai zuwa aka nad'a yusuf a matsayin sarkin masarautar karfe, a wannan rana mutallaf yabar duniya.


Tunda yusuf ya zama sarki shikenan Rayuwar sa ta sauya bashida aiki sai tunani gabaki d'aya ya kwallafa ransa akan nigeria, yaso tura mutane aje a duba rayuwar da iyalansa keyi Amma hajara ta gargadesa akan rashin biyayya ga mahaifinsa da karya Alkawari, sannan tace bata son kowa yasan da maganar.


Yusuf  rayuwa suke da matar sa lawiza za'ace sai a hankali, batasan wan abu wai dadin aure ba, asalima yusuf ya samu ciwon zuciya wanda kullum gaba gaba yake duk wani abinda za'ayi don ganin yusuf ya dawo da walwalarsa anyi Amma abin yaci tura.


Hatta yan uwansa da dangi ya shanja musu ba kamar yusuf da aka sani daba.


Bayan wasu shekaru lawiza ta haifi yara biyu mata muwaddat da muhibbat, sai nabila yar kafshatu ce wance hajara ke riko a gidan sarauta.


An dawo labari..........

Tabbas yusuf nada yara ni shaidace mahmah tace tana hawaye.


Jama'a da dama dake fadan sunsha mamakin abinda ya faru wai yusuf nada iyali, Amma ba'a sanar da kowa ba acikin zuriyar su, sannan wasu suna ganin rashin kyautawar abinda aka ma yusuf, lawiza kam kuka ta sake yanzun daman yusuf nada wasu yaran kamar muhammad, amma tana matsayin matarsa a kasa sanar da ita, mikewa tayi zata bar falon, alamu yusuf ya mata data koma ta zauna, ba musu ta koma ta zauna.


Al'ameen ne ya dubi mahmah yanzun kina nufin kice mini kece mahaifiyar abbajo?


Kwarai nice hajara kakar ka uwar yusuf...


Yanzun kun kyauta kenan abinda kuka ma mahaifina ace mutum an yanke masa alaka da yaransa duk wani hakkin su daya rataya a wuyansa ? kai koh ashariya wannan ba daidai bane,  mijinki bai kyauta wa mahaifina ba.


Ya kyauta masa muhammad, nine ban kyauta ma mahaifinka ba,  a Ranar da aka nad'a  yusuf kafun mutallaf ya bar duniya munyi wani magana dashi akan yusuf...............


✨Ruqeenjalal✨


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

No comments