Breaking News

Matar makaho 89-99

 


Page 9⃣8⃣&9⃣9⃣


Zata fadi da sauri Ammar ya tarota cikin tashin hanki Ramadan ya bude firij inda ya gani a falon ya ibo ruwa watsa mata sukayi ta farfado cikin kidima take magana ina yake na tabbata d'an yusuf ne, don Allah ku taimaka ku kaini wajen sa na nemi yafiyarsa na tabbata muhammad ne, don salim baya kama da yusuf.


Da mamaki suka juya baya don yima Muhammad magana, sai kawai sukaga wayam babu shi ga kuma mamakin ina matan nan ta sansu.


Kuka take tana rokonsu su taimaka su kaita wajen muhammad, kwantar mata da hankali sukayi akan tayi hakuri ya koma inda suka sauka ne, kuma tare da yusuf suka zo, ai tana jin haka ta mike da sauri ta tsaya takalmi ta saka ta nufi kofar gida.


Ganin haka yasa su Ammar binta suna tambayarta ina zata?


Amsa ta basu akan gidan sarki zata wajen dasu yusuf suka sauka, jin haka yasa su binta a baya suna had'ata da Allah ta tsaya yanzun dai yana hutawa, amma ina bude get tayi zata fita daidai lokacin Alhaji suka dawo tsayawa yayi da motar sa yana tambyar zainab in zata? da mamaki don sam inba dalili mai karfi ba zainab sai tafi wata uku bata leka kofar gida ba.


Tambayarta yayi ina zata Amma ina ta kasa basa Amsa shuru tayi ta tsunkuyar da kai, Ammar dake gefenta shiyake sanar da uncle  insa ga inda zata, sata yayi ta koma amma kememmen Zainab taki komawa sai hawaye dayake bin fuskar ta, daka mata tsawa Alhaji yayi akan ta wuce ta koma ba musu ta juya tana kuka ta koma cikin gida, Ammar kam dariya abin ya basa watoh duk girman mace in batayi aure ba saikaga wani yaranta a tare da ita yanzun kamar Aunty zee ke kuka don ance bazata wani wajen ba.


Komawa ciki sukayi dukansu harda uncle in Ammar da mom, shiga  falon sukayi duka suka tsinci zainab na kuka a zaune zama sukayi baban ya fara rarrashinta don abin na zainab tsawa baya gyarasa.


Tambayar Ammar yayi cikekken bayani, Ba musu Ammar ya zayyana masa kome dayafaru da labarin su yusuf kuka zainab tasa tana sambatu akan kome ya faru dasu yusuf itace ummulkaba'isin kome daya same su.


Ajesu Alhaji yayi akan su zauna gobe daga shi harsu in saisu tafi wajen yusuf in tare.


Aiko washe gari da sassafe suka wuce gidan sarki Amma basuyi sa'a ba duk basanan sunje gidan su hafsa, waya Ramadan ya d'auka ya kira zulkifilu akan ya tambaya musu sunan unguwan da suke.


Bayan sun isa gidan da sallama suka shiga falon bayan an musu ido, zainab sai boye fuska take ganin sun had'a ido da yusuf dake mamakin ganinta da ubangari.


Zama ubangari yayi suka gaggaisa da juna anan ne ubangari ke neman yafiyar yusuf tare da rokonsa daya yafe ma zainab, duniya ta koya mata Hankali, duk da sun dawo Maiduguri Amma har yanzun batayi aure ba, kowa yazo wajenta sai tace bata so gashi yau tana da shekara 44 harta fara tsufa Amma shuru kullum cikin istigifari dake da nadamar abinda ta Aikata, ga mutuwar khairat daya shiga jikinta sosai don Allah yusuf da muhammad su yafe musu.


Daker aka samu muhammad ya yafe don yusuf kam a take ya yafe mata tare da neman izinin Aurenta, don zainab ta basa tausayi matuka tsawon shekara 44 ace batayi aure ba, yasan sonsa ke wahalar da ita duk da tsufa yaxo, Amma xuciyarta bai tsufa ba, ba musu Aka daidaita kome baban hafsa ma ya yafe ma abie, abin gwanin sha'awa su muhammad basu bar maiduguri ba saida aka saka sartin auren yusuf aka biya sadaki, Amma auren sai yusuf yaje nijar zasu dawo d'auren aure, duk wanda yaga fuskar zainab a lokacin zaisan lallai so ba karya bane don ta kasa boye farin cikinta.


Daga maiduguri Hafsa da kalamu dasu falmata suka wuce Abuja,saboda karatunsu, muhammad da Sumayya suka wuce Taraba harda  mahmah dasu dahdah, yusuf dasu ramadan sun wuce nijar daga Maiduguri.


Bayan komawar sumayya dasu Abie jalingo sukaci gaba da kula da jariransu yayinda muhammad ya kai khadija wajen hafsa tacigaba da zuwa makaranta daidai su tashi tafiya nijar in sumayya ta gama jego.


Kudi yusuf y sakarwa Al'ameeen a account ba kad'an ba, kamar yau suna zaune a falo su uku dashi da sumayya sai mahmah dake bawa na'ima madara gaggo na sallah a d'aki, hira suke anan ne muhammad ya kalli sumayya, ina so ki bani shawara matata cikin fulatanci yayi maganar sanin mahmah bataji.


Murmushi sumayya tayi tana kallon mijinta sai kuma ta basa amsa da hausa gudun kar su ware mahmah, "ina jinka dear"

Jin haka yasa mahmah mikewa ta basu waje.

Yauwa don Allah ki tayani nazari in sama wa yan uwana mafita don nayi nazari Abinda ke damun Adara abu biyu ne, akwai jalinci akwai bin jini na gado, akan halinsu shiyasa nake son na shawo kan lamarin nan kuma na rasa mafita ta ina zan fara?


"Gaskiya naji dadi daka ji a ranka Adara yan uwanka ne, baka kullace su a rai ba akan abinda suka maka ba, har kana nema musu tsira"?


Taya zan gujesu sumayya bayan dangin mahaifiyata ne, da kinsu ake da Abbajo bai yarda ya auri mami ba.


"Gaskiya ne ni a nawa shawaran abu na farko da zaka fara shine ka tarasu, kayi musu magana akan duk wanda yake da wance yake so koh wance take da saurayi tsayaye zaka aurar dasu, babu koh sisin iyayen su sannan ka gyara musu gidan tunda akwai fili saika ma samarukan d'akuna room and falo, suyi aure a ciki ka nema musu jari matan kuma asasu a islamiyya yara a had'a musu da boko, su kuma su inna ka basu jarin 50k  ga kowance su kama san'a, sai maganar shagari kaje ka sanar dashi akan ka basa shagon halak malak kaga zaifi samun natsuwa akan ya zauna da tantama tunda Ammar yace ya baka kyautane"


Gaskiya sumayya ngode matar Aljana Allah ya barmin ke baby, amma ya zanyi dasu bappa sulaiman?


"Ameeen dear, ni a ganina kamar daman ai suna da sana'arsu kadai taimaka wa mata da yara matasan zaifi in yaso daga baya saika basu abinda kaga ya dace"


Haka koh akayi washe gari muhammad yaje gidan adara kuma ya sanar da shagari ya barmasa shagon kyauta,  yaron har kuka yayi gwanin tausayi, sannan yanzun yasan khadija tafi karfinsa shiyasa ya fara kula wata yarinyar school nasu dake matsa masa.


Takardun makarantan sa muhammad kawai  ya d'auka a dakinsu, sauran kayan d'akin ya baiwa matan gidan Adara kyauta harda na kitchen.


Kafun wata d'aya duk samarin gidan adara da suka kai aure duk sun fitar da mata, haka ma matan don daman suna son auren, rashin kudine kawai, mazan ma wa'inda basu da budurwa jin auren bati da za'a musu yasa su neman yan mata cikin lokaci kankani, gashi ansa yara a boko ansa mata a islamiyya harda mazan ma.


Anyi bikin gidan Adara na gani na fad'a wanda ya samu hallartar jama'a da yawa kowa na tofa Albarkacin bakinsa, akan muhammad da Halakcin daya musu.


Sumayya ta kammala wankan jegon ta sati d'aya kenan, yau tun safe daga ita har muhammad in suna cikin farin ciki,adalilin khadija da kalamu da zasu zo yau don anyi hutun makaranta Khadija an kammala ss 1 zasu tafi 2, gashi yau daga ita har kalamu zasu zo Taraba tun asuba suke sanar dasu akan zasu bi fly, wanka sumayya tayi goggo tama yaranta wanka suka shirya cikin shiga ta Alfarma harda muhammad zasu je gaida maman Ammar, daga nan zasu bi Airport d'auko su Kalamu 4:00 na yamma.


Dayake yanzun muhammad ya iyya tuki shiya d'aukesu a motar zuwa Gidan su Ammar, suna fita a motar dayake zuwan bazata sukayi basu sanar da Ammar zasuzo ba, tsayawa muhammad yayi a tsakar gidan yayinda sumayya ta wuce ciki rike da na'ima ta bar masa na'ifa  da sallama ta shigo falon Amma babu kowa shuru kakeji,zama tayi koh masu gidan zasu fitoh Amma har minutes biyu bataga kowa ba, gashi Al'ameen sai kiranta yake akan yajita shuru saboda shi baya shiga gidan mutane ba tare da neman izini ba.


Mikewa tayi ta nufi wani kofar dake gefen falon don a tunaninta koh dakin su maimuna ne a falon harta kama handle in kofar zata bude sai kuma ta dakata jin maganar dake tashi a d'akin.

Muryar hajiyar Ammar ke magana, yanzun Ammar kanada wance ta fini ne ka zauna kana cutar da kanka ni bangane kanka ba gabaki d'aya ka chanja yau ciwo gobe lafiya?


Ammar ne ya bata Amsa, Mom babu fa abinda ke damuwa kawai dai banajin dadi ne.


Wani irin bakajin dadi, abinda ke damunka harda tunani da damuwa ba haka kake ba Ammar  nice fa na haifeka?


Mom daman wallahi na jima ina son khadija sai kuma yayi shuru bai karasa ba 


Wace khadijar?


Kanwar Al'ameen


Toh sai akayi yaya cewa tayi bata sonka?


Ah ah mama ban fad'a mata ba,daman naso na sanar da sumayya maganar sai kuma bakina yayi nauyi kar tace daman da wani manufa nake taimakon su, gashi banason yarinyar ta rainani.


Gyara zama mom tayi yana kara kallon Ammar tun ba yauba tasam d'an nata akwai son girma.


Toh shine ita da Auntin nata suka gudu Abuja ba tare da na zayyana mata abinda ke raina ba, kuma yanzun  kawai saina ganta da yaron nan kalamu kanin sumayya, kinga yanzun ai babu halin nace mata ina sonta tunda yanzun soyayya suke koma na fahimci tana son yaron.


Ammar ka bani mamaki wallahi ita tace maka soyayya suke?


Hamma mom kowa yagansu yasan masoya ne kuma nasan koh da ba sonsa khadija take ba Albarkacin sumayya zata yarda ta aure kalamun bare ma tana sonsa.


Kaga Ammar kafito ka sanar da yarinyar nan kana sonta bakasan me Allah zaiyi a lamarin nan naku ba, ka kwantar da Hankalinka kaji inso samune ma ka shirya kaje abujan?


Mom muhammad ya sanar dani khadija na zuwa.


Toh maza ka tashi ka shirya samun ta ganka tsaf dakai kabi yayanta Airport gobe kuma sai kaje gidan su ku gaisa kaga saika sanar da ita Amma ka dubi yanda duk kabi ka rame........


Jin abinda suke cewa yasa sumayya sauri tabar bakin kofar, jin alamun mom zata iyya fitowa da sauri ta bude kofar falo ta fita waje, muhammad dake tsaye a rumfa har yanzun rike da babyn sa, dan yanzun sunyi wayo sosai,ya tambaye ta Lafiya tun d'azun Ammar bai fito ba?


"Muje kawai ba kowa a gidan"


Da gaske?


"Don Allah ka shiga mu tafi gidan mu pls nace maka basa nan"


Ba musu muhammamd ya shiga motar yaja suka wuce gidan su sumayya.


Yad'an jima a gidan kafun kiran Ammar ya shigo wayarsa, sallama yama su dada ya wuce, bayan fitar Muhamamd ne dada ke sanar da sumayya akan ta kara ma abie magana akan Amina(goggo)ya aureta don ita hankalin matar ya burge ta, Amma duk yanda dada tayi akan ya yarda Ya nemi Amina tunda dai bata tsufa ba, da yarantanta Amma yaki Amince wa.


Sumayya karan kanta taji dadin Abin don babu shakka goggo macece ta gari duba da zaman da suke da ita yanzun a gida d'aya sam bata da dumuwa.


Sumayya ta samu Abie akan maganar daker saida takai ruwa rana kafun ya Amince da zancen,  A ranan dada ta sasa dole sai ya wuce gidan su Al'ameen sun daidaita da goggo tunda yanzun yaran basa gida sai mahmah ne kawai.


Muhammad da Ammar su sukaje suka d'auko su khadija a Airport gidan su Abie suka sauka daman sumayya na gidan sosai suka musu tarba ta musamman, Sannan a nan suke xancen Abie ya tafi zance gun goggo, aiko muhamamd yaji dadi don daman tunanin da yake kenan in ya tafi karatu abroad kamar yanda uncle zulkiflu yace masa next month zasu tafi America an sama masa gurbin karatu harda sumayya da yaransu don gida yusuf ya kama musu ashan haya, yanzun ma bikin Abbajo suke jira. 


Lokacin da abie ya dawo sosai yayi farin cikin isowar d'an nasa hira ne ya kara barkewa a tsakaninsu sai dare su sumayya suka tashi tafiya, kiran kalamu tayi da Khadija a compound ta tambayesu shin soyayya suke kuma su fad'a mata tsakanin su da Allah?


Dariya suka sake a tare sannan khadija tace wa sumayya ai tsakaninta da kalamu babu zancen soyayya asali ma Abota ce kawai da shakuwa don kalamu kamma yana da budurwa yar school nasu sunsha gaisawa da khadija a wayar Kalamu.


Hakan sosai yama sumayya dadi sallama sukayi da yan uwanta.


Sun isa gida muhammad kam kwanciya yayi ya barsu da khadija anan sumayya ke sanar da ita Zancen sonda Ammar ke mata, da kuma bata shawarwari da tuna mata irin Alkharin Ammar a karesu ya cancanci ta sosa koh Albarkacin Halakcin sa, saida ta tabbatar jikin khadija ya mutu murus kafun ta mata sallama ta wuce d'akin mijinta khadija kam tare da mahmah zasu kwanta.


Washe gari da safe bayan sun karya Al'ameen ke tambayar ta dalilin sasa su bar gidan su Ammar bayan kuma Ammar yace masa suna nan,sumayya ke sanar da muhammad zancen Ammar da abinda ta jiyo suna tattaunawa sosai muhammad yayi murna ba d'an kadan ba, haka mahmah khadija kam kunyane kamar zai kasheta, especially jin muhamamd ya shirya ya fita wai kar Ammar yazo ya samesa a gidan tunda wajen khadija zaizo.


Sumayya da khadija kitchen suka shiga bayan matsawa khadija datayi kafun ta yarda, suna aikin girki yayinda mahmah da goggo ke falo suna rirrike da yaran sumayya.


Wayar mahmah ne yayi kara a d'aki mikewa tayi da na'ima a hannunta ta shiga dakin ta d'auko wayar, ganin nabila ne yasata d'auka da sauri.


Ta bangaren nabila jin mahmah ta dauka jiki a sanyaye tace hello


Kedai nabila anyi yar banza, sallamar ma bazakiyi ba sai wani d'an banzan hello wai gaki baturiya koh?


Yi hakuri mahmah Assalamu alaikum


Amsawa mahmah tayi tana tambayar nabila lafiya?jin muryarta cike da damuwa


Dada kewarku nake yaushe akki (muhammada)zai dawo?


Toh watoh shi kike kewa kenan banda ni?


Yi hakuri harda kene mahmah


Toh make damunki nabila in baki fad'amin ba wa zaki fadawa?


Mahmah wallahi nifa son Akki nake don Allah kisa baki a maganar nan ki sanar da abba kice ke kikeso a had'amu ki taimaka mini mahmah.........


✨Ruqeenjalal✨🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃


✨Tsokaci A ranan 30/8/2021 na fara rubuta Wannan novel na matar makaho, gashi A yau 28/10/2021 na kammala cikin Yardan Allah kuskuren danayi a ciki Ubangaji ka yafe mini🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲


Free book🤧


No comments