Breaking News

Matar makaho 88-89

 


Page8⃣8⃣&8⃣9⃣


Da sauri muhammad ya damke rawanin sa, ya hana Ramadan bude masa fuska, menene haka? banaso karka kuskura ka bude mini fuska.


Har lokacin jikin Ango rawa yake cikin mamaki yace a ina ka samu sarkan nan,  waya baka wanene kai?da karfi yace security.


Jama'an gurin duk sun mike banda sarki dake zaune akan kujera duk rikicin da ake baiko d'ago kansa ba bare yasan abinda ke faruwa.


Mustapha ne yayi magana a rude wallahi sarkan ne, sarkan magadan masarauta ne, a ina ka samo sarkan nan?yana maganar yana kai hannunsa wuyan Al'ameen zai duba sarkan.


Da sauri Al'ameen ya buge hannunsa, Shuru yayi yana kokarin barin filin, da sauri Ramadan ya jawo sa baya yana kwalawa Yayansa kira, da sauri sarki ya juyo yana kallon Ramadan da mamakin kiran gona da yake masa?


Yaya sarkan magada ne a wuyan wannan me kawo shayin, kuma yaki bari aga fuskar sa, bamu yarda dashiba suspect ne?


Ai kafun ma ya gama magana saiga sarki ya sauko a kujera da hanzari ya nufi inda suke tsaye, daga isarsa hannu yasa a kamo sarkan yana kallo sai kuma jikinsa ya fara rawa ya kamo rawanin fuskar muhammad.


Da sauri muhammad ya dafe Hannun sarki dake kan fuskar sa yana girgiza masa kai, alamun rashin son hakan.


Shima sarkin girgiza kai yayi, hakan yasa muhammad sauke Hannunsa akan na sarki.


A Hankali yake warware Rawanin kansa, tsaf gashinsa ya bayyana mai masifar tsawo da sheki, a hankali ya warware na fuskar sa, da sauri ya dafe kirjinsa cikin tsananin mamaki da sauri yace muhammad!!!!!bai karasa ba kawai hancin sa ya fara tsiyayo da jini a hankali ya fara lumshe ido sai kuma ya yanke jiki zai fadi, da azama muhammad ya taro mahaifinsa da sauri ya rungumi abinsa cikin matsanan ciyar mamaki jin sarkin ya Ambace sunan sa.


Zuwa fadawa sukayi aka kewaye sarki muhammad ne ya ciccibi sarki har cikin flat nasa, atake gida ya rude da koke koke, ga masu tsananin mamakin muhammad da abinda ya had'asu da sarki harya Ambace sunan sa?


Bayan Ankai sarki d'aki likita da abokan aikinsa suka rufu a kansa, yayinda Ahlin gidan ke make a babban falon fada, daga maza har mata harda wa'inda muhammad bai taba ganinsu ba, mikewa yayi zai fita a falon da sauri Mahmah ta riko hannunsa, ina zaka yaron nan?


Gidan mu mana ba aiki bane ya kawoni mama?yace yana kallon nabila dake rakube a jikin kujera fuska jajjawur ga jini ya taru a idanunta da gani dai ta maru.


Wani irin ka tafi kuma kaje ina baka ga Halinda d'ana yake ciki ba? kuma na tabbata yana farfadowa kai zai nemi gani.da gorancen hausar ta take magana.


Toh ni kuma so nake na tafi gida ranki ya dade, in Allah ya kaimu gobe ai zanzo aiki duk maganar da zamuyi sai muyishi?


Ramadan ne ya mike,Hala nan dajine da bazaka iyya kwana a cikiba?


Ban saba kwana  gida irin wannan ba,  kasa bacci zanyi, yace yana fita a falon babu wanda yayi yunkurin hanasa, sai rakasa da ido sukayi.


Muhammad na zuwa gida gabaki d'aya abin duniya ya damesa, amma baicewa baba kome ba, shima baiyi magana ba duk da yaga sarkan wuyan Al'ameen Amma baice kala ba.


Yau koh abincin dare kasa ci yayi,  badaru da gidado ne sukaci gabaki d'aya jikinsa yau A sanyaye yaki kome yanayi a sake kamar mai ciwon fata.


Har dare bai rumtsa ba, tunani kawai yake a ransa, donshi dai bai gane inda abinnan ya dosa ba, menene Alakansa da mutanen nan shi zaman kasar ma ya isheshi kuma ya rasa hanyar da zaibi yabar kasar gabaki d'aya, yau wani irin kewar iyalinsa yame dason jin duminta, ba irin tambayar duniya dasu gidado basu masa ba Amma bakome yake ce musu.


Da misalin karfe 2:30 sukaji ana bugun kofar gidan, babane ya fita zai duba koh lafiya yayinda muhammad ke kwance duk da idanunsa biyu Amma bai mike ba.


Baba bai jima da fita ba sai gasa ya shigo d'akin su muhammad, mikewa yayi yana kallon baba.


Muhammad ka fitoh ana sallama dakai?


Da mamaki yace dani kuma baba, sallamar ma tsakar dare?


Ka tashi daga gidan sarautane.


Gaskiya baba kace musu su bari sai gobe, koma menene in gari ya waye sai ayi bawai a tadani tsakar dare ba kamar tashin duniya.


Muhammad yaushe ka koma mara kunya ban sani ba?


Kayi hakuri baba


Tashi kawai kaje kaji da wani sako aka turosa?


Mikewa yayi kawai ya sanya kayansa ya fitoh a d'akin, kallon mutumin da aka aiko wajen sa yayi, lafiya malam?


Lafiya muhammad ana neman ka a fada.


Tsakani da Allah in Ana son ganin mutum sai azo tsakar dare ya kirasa ai naga gari zai waye?


Babane ya kallesa, muhammad ka iyye bakinka banason irin wa'innan kalami,  bai dace da kai ba, don haka ka bisa kuje bakasan menene dalilin kiranka ba,  ya kamata kaje kaji.


Baiyi magana ba kawai ya nufi hanyar kofar gidan, binsa a baya mutumin yayi daman da mota yazo ba musu muhammad ya shiga suka wuce.


Daga isarsu masarauta gidan kaman rana koh ta ina fitilune haske kaman farin wata, ga mutane a tsatsaye kamar rana bakin dake gidan duk basu tafi ba, Al'ameen na fita a motar gabaki d'aya aka ringa binsa da ido har suka ratsa babban falon sarki, suna shiga mahmah da lawixa harda su ramadan muwaddat nabila duk suna cike a falon wasu kamma kuka suke fuskar lawiza da mahmah jazir alamu kuka sukasha, da sallama ya shigo falon amsa masa sukayi suna mikewa tsaye gabaki d'ayansu, binsu yayi da ido sai kuma ya nufi kofar d'aya falon, ya shiga yana shiga duka suka rufa masa baya zuwa ciki, tunda ya tinkare kofar bedroom yake jin salati ga sunan sa da ake kira da sauri ya cusa kansa adakin.


Sarkine kwance akan gado yana tari jini na biyo bakinsa yana Ambatun sunan muhammad, ai Al'ameen baisan lokacin da yayi super ba ya isa garesa koh tsawon shekaru nawane bazai taba manta wannan fuska ba bare shekarun da baiwuce a kirgasu ba,  hawaye ne ya cika masa ido ganin halinda mahaifinsa abin sonsa ke ciki, duk da ya rayu da takaicin gudunsu dayayi Ya kuma sha Alwashin duk randa ya gansa zai basa mamaki shima, amma bai d'auka zai gansa a irin wannan halin ba, karasawa yayi garesa a hankali ya kamo hannayensa dake dafe a kirjinsa cikin kuka yace Abbajoooo!!!me nake gani haka ka rufa mana asiri kar maraicin ya mana yawa?


Ai jin muryar sa da sauri yusuf ya mike ya rungume d'ansa a zaune, tunda ya hau karagan mulki ba'a kara ganin hawayen saba sai yau, hawaye ne yake siyaya a idanunsa, ganin haka yasa muhammad fashewa da kuka mai matukar karfi yana banbare Abbajon sa a jikinsa, tare da kallon doctor dake gefe, habba bawan Allah jini nefa kebin bakinsa kun barsa haka?


Kayi hakuri yallaboi wallahi tun da ya farfado anyi anyi ya tsaya a basa taimako yaki gashi ciwonsa baison damuwa Amma yaki ya saida hankalinsa.


Jin haka yasa muhammad kokarin mikewa tsaye,Ai da sauri yusuf ya rikosa da karfi tamkar uwar da za'a rabata da jaririnta, fuskar muhammad ya rike sai kuma ya soma magana a hankali, tabbas jini yafi ruwa kauri, babu tantama wannan jini nane muhammad nane koh babu sarka a wuyanka akwai alamun jini muhammad ku yafe mini.


Ah ah Abbajo ka rufa mini asiri karkace haka kayi hakuri ka rayu damu yana magana yana kuka.


A hankali sarki yace muhammad dukkan mai Rai mamaci ne in lokaci yayi dole mu amsa kiran mahalincin mu.


Don Allah Abbajo kabar irin wa'inan magana, likita kazo ka taimaka masa, da sauri likitan ya maso da taimakon muhammad suka gogi masa jinin dake bakinsa ya taimaka masa ya shiga toilet ya shanja kayan daya baci, daidai ya fitoh har muhammad ya sauya zanin gado.


Yana fitowa ya kwanta likitan ya d'aura masa ruwa da Allurai ya fita, a hankali yusuf ya kama hannun d'ansa sosai ya zurawa muhammad ido yana kara tasbihi a zuciyar sa yaushe yabar muhammad yaro karami d'an shekara 13 Yau shine ya zama cikeken mutun tamkar shi a lokacin da ya barsu muhammad?badon shekaru ba koh yau duk wanda yaga muhammad zaice shine.


Na'am Abbajo.


Ya Aishan Adara?


Jin tambayar da ya masa sai da gaban sa ya fadi, a halinda mahaifin sa yake cikin nan bai kamata ya kara d'aga masa hankali ba, cikin sanyin jiki yace, Tana Lafiya Abbajo.


Murmushi yusuf yayi cikin karfin hali, nasan xuwa yanzun ta rage masifa koh? nama san itama ta tsufa kamar ni?


Hhh bata tsufaba tana nan da kyawun ta daka sani, kuma yanzun sam bata fad'a da kowa.


Ah ah muhammad fadi gaskiya dai nasan maman ku, saidai in ba'a bata mata rai ba?


Dafa gaske nake.


Ta yafe mini?


Babu abinda ka mata abbajo asalima ita ke neman yafiyar ka, don gaskiya yayi halinsa bayan bakai, meyasa Abbajo kayi fushi ka tafi ka barmu, kana rayuwan ka cikin mulki da kudi mukuma baka damu da kalar rayuwar da muke ba?


Girgiza kai kawai yusuf yayi baibawa muhammad Amsa ba, ya sake jefo masa wani tambayar, ya jikin salim nasan zuwa yanzun kam yagirma don zai fika jiki kasan jikin mamanku garesa?


Kwarai ma kuwa abbajo salim ya warke sosai sai godiyan Allah.


Su lawiza da suka jima a bakin kofa suna kallon ikon Allah wai me yusuf yake nufi da yaron nan ne basu gane ba, kasa magana sukayi ganin kamar ma basu san da zaman suba sai hira suke, hakan yasasu juyawa suka fita a d'akin ganin lokaci d'aya jikin yusuf yayi sauki gashi sam ba hausa suke ji sosai ba, duk da su mazan suna hausa tsabanin mata da kwata kwata bayi suke sosai ba sai jifa jifa,


Haka yusuf da muhammad suka ringa hira na yaushe gamo, Amma sam muhammad bai fad'awa yusuf mutuwar Aisha ba koh salim, sai asuba da sukayi sallah doctor yazo ya cirewa yusuf laidan ruwan, suka kwanta tare a Royel bed na sarki bacci ya d'auke su.


**************

Sumayya ciki ya shiga wata bakwai yanzun sosai tayi wani irin kumbura, har yakai yanzun bata iyya tashi da kanta sai khadija ta kama hannunta ta jata da karfi saboda nauyin cikin,  abincin ma yanzun bataci daga ruwan zafi sai tie koh nama.


Kalamu-wahid da khadija yanzun kam an dinke sosai suka shaku kalamu na zuwa gidan sumayya akai-akai gashi yanzun har kwaryan tuwo yake dashi akofar sumayya na rana,kamar yau sumayya ta gaji da kwanciyar da khafija keyi a kasan tiles hakan yasa ta kiran ta hade da mika mata kudi taje ta sai karamin katifa, Amsan kudin tayi tace bari tayi wanka.


Tana shiga d'aki messenge ta turawa kalamu akan zata fita, kafun ta shiga wanka.


Tana fitowa shiryawa tayi ta fita da niyar tafiya kasuwa, tana nufar get ta bude da murmushi a fuskar ta ganin kalamu tsaye sanye da  jamfa wando da riga yayi matukar masa kyau abinka da bakin mutun sanye da farin kaya, mota ya bude mata ta shiga shima ya zagaya ya shiga yaza suka cillah kasuwa.


Duk yanda yaso ya saya mata katifa da kudinsa taki yarda, yace zai cikimata ta d'auki babba, amma taki tace aunty zatayi hulo itakam babu ruwan ta.


Tare suka dawo kasuwa ya sauketa a get nasu, ta shiga da katifar ta da kanta don tace karya shigo kar aunty ta mata fad'a, sunje kasuwa dashi bada izininta ba, ba musu shima ya shige gidansu bai matsa mata ba.


Bayan isha'i sumayya ne  kwance a falo, yayinda khadija na cikin daki suna hira da kalamu a waya, kamar a mafarki taji sallamar sa a bakin kofar falon su, da sauri ta mike zaune tana mamakin sa na rashin fad'a mata yana zuwa Alhalin kuma waya suke da juna yanzun, kalamu!!!!


Ta cikin wayar taji yace ke don Allah fitoh ki bude mini kofa.


Ba musu ta fitoh a d'akin kallon sumayya dake falo a kwance, tana bude kofar ya shigo gaida sumayya yayi ta Amsa masa sama-sama don yanzun koh yawan magana bata so.


Aunty daman wajen ki nazo?


"Khadija basa wajen zama"


Zama yayi akan kushin da khadija ta aje masa, itama ta koma gefe ta zauna.


Aunty daman nace mezai hana khadija ta shiga islamiyyar mu ?nayi magana da ita tace nini tun saukar ta na farko bata kara komawa tushi ba.


"Gaskiya ne kalamu koni ina son khadija ta koma islamiyya, nama laila magana akan koh akwai islamiyya a kusa, shine tacemin yaranta babansu ke koyar dasu, ni kuma bana son khadija taje wajen sa d'aukar karatu"


Gaskiya ne Aunty kinga kuma zuwan weekend ne aje 3 adawo 5 ?


"Shikenan kalamu sai Allah ya kaimu next week sai na had'aku ka kaita don ni ba iyya taka kafar nake sosai ba"


Eh aunty daman na kammala mata kome yanzun ma uniform na kawo mata da form sai a cika mata sati mai zuwa ta fara zuwa.


"Lallai ma kalamu toh Allah dai biya ka"


Ameen ya Amsa yana kallon khadija dake murmushi a boye.


"Yauwa kalamu daman akwai abinda nake son na fad'a muku kaida khadija"?


Zuciyar suce a tare ya buga da sauri suka kalli juna sai kuma suka juya suka kalli sumayya har suna had'a baki, Aunty Allah dai yasa lafiya??


"eh daman akan kune, ba kome bane  illah abu d'aya zuwa biyu, ina so daga yau..............


✨Ruqeenjalal✨



🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

No comments