Breaking News

Matar makaho 76-77

 


Page7⃣6⃣&7⃣7⃣

Bayan Auren abie da safina, a lokacin safina tafito da duk wani mugun h


alinta a gidan, ta buwayi kowa, har dada bata ragarwa ba, shikuma abie daman ba sonta yake ba,  shiyasa sam koh ana meeting, safina naci musu mutunci baya saka bakinsa a maganar, tunda su suka kakkaba masa ita, badason rasa ba.


A lokacin safina tasaka sumayya a gaba da duka zagi, sai da dada ta sanar da abie, ranan da yasan abinda safina ke aikata wa yarinyar sa in baya nan, baraxanan  sakin ta yayi ya zazzage ta, kai ranan anyi kwanan bacin rai a gidan.


safina ganin auren ta zai iyya mutuwa yasa ta shafawa kanta lafiya, bata koh ga maciji da sumayya, daman ba'a hannunta take ba, a hannun Dada ne.



Lokacin da sumayya takai shekara 12, har lokacin safina(momy)bata haihuba, kuma abie bai wani damuba, tunda yana da sumayya, duk wani soyayya da kulawa sumayya na samu a gidan, baga bappanayen taba, ba dada ba ga abien ta, momy ce kawai bata kaunar ta, har lokacin safina na tare da nafisa, duk da nafisar ta koma gidan tsohon mijinta, lokacin.


Haka kawai sumayya ta waye gari duk yan gidansu basa kaunar ta, daga su babuji har matan su, dada karan kanta bata shiga tsabgarta sai in babu mutane a wajen, ga tsoron momy da suke, da bin umurnin ta kome tace jiki na bari zasuyi inka cire abie,  sosai sumayya ta shiga wani irin mawuyacin hali, abie inta ne kawai ke tsaya mata akan kome, baya taba yarda a cutar da ita, kuma duk wanda yama yarsa abu a ranan zaiga bacin ransa, ana hakan ne fa momy rana tsaka ta dake sumayya, wai ta b'ata mata labulen d'aki da lalle, a ranan abie saki d'aya ya mata ya korata.


Amma safina taki tafiya, dada tace sayya maidata d'akin ta, ganin matsaloli da sumayya keta fuskarta a lokacin, ga kananun shekaru, abin harya fara tayar mata da kewar mahaifiyarta, yasa abie saka a FGGC boarding school, ta cigaba da rayuwan ta a hostel, shikad'ai ne gatan ta, sai wata rana Dada tana zuwa mata visiting a boye, kuma tace mata karta fad'awa kowa tazo wajen ta, sumayya koh marmarin komawa gidansu hutu batayi, amma hakan take komawa in anyi hutu tana Allah Allah a dawo hutu.




Sumayya lokacin da ta cika budurwa, ta tashi da wani irin hali, akwai jijida kai da ganin tafi kowa, kasancewar ta mai kyau, ga Arzikin gidan su, ga rashin sabo da mutanen gidan,  ga rashin mafadi don har lokacin xaman hostel take.



Sumayya inta dawo hutu duk yanda saurayi zai biyota, saita raina masa arziki gani take kamar tafi karfin sa, in kuma yakasan ce mai kudi sosai, sai taga kamar zata samu wanda ya fisa, in mai kyaune sai taga kamar nan gaba zata samu wanda ya fisa kyau, sumayya nada kawaye, koh saurayin kawarta ta gani ta ringa dariya kenan, tana kushe sa mummuna talaka kaza kazan, wasu Friends inta da dama in auren su ya tashi basa gayyatanta, saboda rainin wayo da take zuwa ta musu a wajen biki.


Lokacin da sumayya tayi candy, taci jamb A lokacin tana da shekara 18, aka shiga university sai abin ya d'ara na da, ganin yanda ake tururin sonta, babu ranan da zata fita ba'a biyo taba, hatta cikin gidan su Abdul(wanda lokacin da sukaje gida, bayan aure aka mata wulakanci, yace zai rage musu hanya ita da khadija)da kaninsa sunsha dambe akanta, Amma haka ta murza ido tace basu mata ba, karshe dai Abdul aure yayi,  harda yaransa biyu ya fita harkar sumayya.


Sumayya bata gane kuranta ba, sai lokacin da takai shekara 23 lokacin ta kammala digree inta har tayi service, zuwa lokacin duk samarin ta sunja jiki da ita, kowa yana baya baya koh hira suke ta sako musu zancen aure, sai su kama kaucewa wasu kamma gudu suke, rabin kawayen ta duk sunyi aure, sai d'aid'aikune suka rage.


Bayan dawowar ta gida lokacin yaran gidansu sun d'ara nada, a yawa wasu sunyi aure wasu na aiki, itama rashin miji yasa abie nema mata aiki a bank nasu dayake aiki , dayake statistic ta karanta, tana aikinta tana samun Albashin ta, Amma maganar samari fa babu yanzun, ita karan kanta aure take so Amma babu mazan, ga kyau ga aiki ga kudi, mijine kawai matsalar ta.



Shekara 2 sumayya tana aiki a bank lokacin tana da shekara 25 a duniya, ganin haka yasa dada nema mata maganin farin jini, amma ina tayi tayi abin shuru, karshe dai dada ta nemi kanin abdul ya dawo su daidaita da sumayya, amma ba kunya a idon abie yace shi bazai aure sumayya ba, yarinya yar 15 xai nema ya aura ba rikekkeyaba abinnan yama abie zafi matuka, hakan yasa sa zagin kanin Abdul sosai abin ya zama babban magana.


Wannan dalili yasa babuji rantsuwa sai sumayya ta fitoh da mijin aure nan da wata uku, tunda dai zaman ta a gida fad'a zata had'a  a tsakanin su, kamar yanda momy ta kitsa musu, don Abie indai akan sumayya ne baya ganin kowa da gashi, jin abinda akace ma sumayya yace sam bai yarda ba, ga yaransu su kubra da miemie sun girmi sumayya ba'a saka musu ka'ida ba sai yarsa.



Kuka dada tasa akan abie zai nuna musu iko da sumayya, abinda ya sa abie yarda kenan, sumayya har wata uku ya shige bata samu miji ba, su babuji sukace aikin da take shiya hanata aure, hakan yasa sukasa abie dakatar da aikinta.



Sumayya kam ganin an rabata da aikin ta da tafi so, don lagon sumayya kenan, kace zaka kaita garin su mamanta, koh kace makaranta, hakan yasata d'aukar takardun ta, ta tafi asibiti neman aiki babu wanda ya sani.


Dayake result nata nada kyau, yasata samun aiki a pharmacy tana musu lissafin kudin magani.


Kullum take fita aiki, ba tare da aisan ina take zuwa ba, abie bincike yayi ya gano aiki take zuwa, wannan ne  dalilin kwace mata ducument da yan uwan mahaifinta sukayi, sannan suka rabata da aikin ta.


Ta dawo zaman gida, daga baya taga bazata iyya ba, tanemi shagon make-up tana zuwa training,  daman ta iyya lalle, da sukaga ba sarki sai Allah, yasasu barinta tana zuwa koyon make-up in, basu hanata ba.


Sumayya ta cigaba da koyon make-up, har ta iyya aka sallame ta, taso abie ya bude mata nata shagon, Amma yaki karshe dai kawaye da yan gidansu, in sun tashi aure koh yan unguwansu take ma, ana hakan ne lokacin Aikin hajji yayi, kamar koda yaushe daman duka gidan ake tafiya hajji koh wani shekara, amma bana sunce baxasu ba, sumayya da abie suje.


Ba musu sumayya suka tafi aikin hajji, wanda zuwa lokacin bazata iyya kirga sau nawa taje ziyaran d'akin kaba ba, bayan sallah abie ya dawo, sumayyya kam daman akwai yar babuji dake aure a saudi, kin dawowa tayi ta zauna agunta har sai da tayi wata 7,lokacin ta cika shekara 26 ta dawo,  kamar wasa tana  dawowa yan gidan sukace sun mata miji, akwai wanda ya ganta yana so, hankalin sumayya ya tashi a lokacin, amma abie ya kwantar mata da hankali, akan zaiyi bincike akan mijin.



Duk yanda abie yaso yan uwansa su sanar dashi waye ne mijin, sunki Amsa d'aya suke basa, shine sun isa da yarsa, haka ba yanda ya iyya dagashi har sumayya suka zubawa sarautan Allah ido, sumayya duk azanta wani shararen mai kudi za'a aura mata, koh d'aya daga cikin samarin gidan.



Abu kamar da wasa, ya zama gaske don maganar auren sumayya babu inda baije ba,  sai shirye shirye ake duk da ba auren soyayya bane, sumayya ta kwantar da hankalin ta koh banza tasan mijin classic za'a bata koh ajeboter.



RANAR D'AURIN AURE

Sai da sumayya ta tuno da mahaifiyar ta, haka kawai ranan tunda ta tashi sai kuka take,  shi karan kansa abie a zullumin rabuwa da yarsa yake, yasan ba'a kyauta mata ba sam.


A waje kofar gidan shugaba, ake shirye shiryen d'aurin aure, sumayya dake d'aki da kawayen ta Ansha kwalliya kamar me, za'a aure classic kanta sai wani kara fashewa yake yanzun kam koh kukan ta daina,  ji kawai sukayi Ana Alhamdulilahi An d'aura auren sumayya Abdulsalam shugaba, tare da Angon ta Muhammad Al'ameen yusuf, akan sadaki naira dubu 20, da mamaki sumayya tace "dubu ishirin kuma?wani irin mijine haka dubu ishiri ai mu tunda muke aure a gidan nan ba'a taba biyan sadaki haka ba"


Kawarta ce ta kalleta, kai sumayya sadaki fa Albarkansa ake nema, ba yawa ba kika sani koh mijin Alu-sunnah ne, irin samarin nan ne ustaxai, ga gemu ga d'angalalen wando kinsan fa irin su sunfi dadi love.


Gabaki d'aya kawayen dake d'akin dariya suka saka da shewa, don harga Allah sun d'auka mai zafi sumayya zata aura, sanin da suka ma halinta na rainako, ke ina ga fa irin samarin nan ne yan  20 something zuwa 30.


"Allah ya sauka bakin ki ya sare guntun kashi, habba 30 ai nima na fara jin kamshin, 30 ina laifin 35 irin ya bani shekara 9 nan" sumayya ta bata amsa 


Duka suka kwashe da dariya, ana ta nishadi, kamar daga sama suka fara jin hayani yana tashi a babban falon gidan, muryar abie ne yake cewa bai yarda da auren nan ba, bazai yafe ba arasa wa za'a aurawa yarsa sai miskini, saboda babuji yaga ba yar gaddafi bane koh Abubakar shiyasa har ya iyya had'ata da yaron nan, yau sai an raba auren bai yarda ba, jin haka yasa sumayya da kawayen ta rugawa da gudu suka shigo falon don jin ba'asi.



MAKAHO ne ya ganta yana so, ba sai a basa ba tunda ba manemi bane da ita, babuji yace.


Kafun abie yayi magana sukaji timmmm sumayya ta yanke jiki ta fad'i jin wai MAKAHO aka aura mata ita sumayya.


***********

Bayan sumayya ta farfado duk borinta da masifar abie, dada tace a yau innan sai ankai sumayya gidan mijin ta, koh ta d'aga masa nono, ba yanda abie ya iyya yana ji yana gani aka sabi yarsa a mota, tare da babban mota na kayan d'akin ta, dana gara wanda kome set uku aka mata gado uku kujeru uku firij uku kome uku uku aka mata hada kayan kitchen, kawayen ta fa sun samu abin yi, sai dariya suke suna yad'a mata bakar magana,  especially wa'inda sukayi aure, sumayya a ranan tayi kuka har saida tayi Addu'a Allah ya d'auki ranta,saida wata yar uwar su na gembu ta mata wa'azi kar bacin rai yasa tayi sabo.



Ai bata tashi ganin bacin rai ba, saida motar su tayi fakin a kofar gidan Adara, wani gidane irin na talakawa mai jan kasa sai kofar gidan da babu kofa, lulubi aka mata suka shiga gidan, amma kamar ba gidan da za'a kawowa amarya ba, babu wanda ya tarbesu asalima kowa harkar gabansa yake kamar ba'aga zuwansu ba, tambayar kofar amarya sukayi aka nuna musu, wani samurmurin d'aki koh kewaye sa ba'ayi ba, d'akine d'aya kankani wani rubebe dashi, ihu sumayya tasa ta tsunguna agun tana sakin kuka itakam tata ta sameta.


Ga auren MAKAHO ga talauci dame zataji,  Allah ya isa ta farama su babuji, tana sun cuceta, a hakan dai aka wuce d'akin, yar uwar dada ce ta tura rubebben kofar da koh sakata bazai zauna ba tsaban rubewarsa, suna bude dakin ba laifi a wanke yake sai dai babu kome sai cinyayen taburma da ghana must go na kaya kad'ai a d'akin, su karan kansu masu jeren ma sun rasa ta ina zasu fara, wanda aka kawowa set uku shine aka samu d'aki d'aya karami.


Da gudu sumayya ta b'anbara ta bar gidan, kawai su dada na zaune sukaga amarya ta faso da gudu ta dawo gida"wallahi bazan xauna agidan shan ba"wannan shine abinda sumayya tace, kuma ba wanda yayi maagana.


Wannan hajiya yar uwar dada ita tayi waya aka kira mata kafinta, a take yaxo shida abokan aikinsa uku,suka buga musu kofar daki, a ka cire tsohon dayake yammane, wasu daga cikin yan uwan,  kwana sukayi washe gari kafintoti suka gama aikinsu, sun kewaye kofar da falange an mata band''aki a kofarta, an saka silif da kitchen da baranda, Amma fa kaya bai d'auka ba koh set d'aya basu samu shigaba,  haka aka juya da sauran kayan.


Abie da kansa a ranan da , dadare ya dawo da sumayya bisa umurnin dada,haka aka watse aka bar sumayya da halinta,  wasu sun mata wa'azi wasu kam magana suka gaggaya mata.


Sumayya tunda suka watse aka barta kuka take,  gashi dare ne tana zaune akan gadon tana kuka cikin bakin cikin wannan al'amari,  sai a ranan wani irin kewar mahaifiyarta ya kamata da ace mamarta na tare da ita da abubuwa zasu mata sauki.


Duke take tana kuka baji ba gani wai itace da aure a irin wannan gida.................



Tas sumayya ta sanar da Ammar duk irin wahalar da tasha, da burinda taci na ganin tayi wa muhammad wulakanci, harsai yaji a jikinsa kafun tanemi sakin ta, amma saboda kyawawan halinsa da hakurinsa don babu abinda sumayya bata masa ba, amma bai taba nunawa koh a fuska ba, bai taba riketa , da wani manufa a ransa ba, kullum kokarin faranta mata yake, wannan sune makamin da yayi tasiri wajen mallakar zuciyar sumayya,  taji zata rayu dashi a haka, sannan ta d'auki auren su da Al'ameeen isharane Allah ya nuna mata, akan halinta, kuma ta karbe kaddarar ta, tazauna da mijinta....


cigaban labari.........

"Sannan yau suce wai na rabu dashi akan me"?


D'aga ido Ammar yayi ya kalli sumayya da khadija dake kuka, lokaci guda, sumayya!!ya kira sunan ta.


"Na'am"


Kukan ya isa haka abinda nakeso dake shine ki d'auki duk abinda ya faru a matsayin jarabawa, kamar yanda kikace, naji duk abinda iyayen ki suka miki, Amma ke me kika fahimta akan auren ku da muhammad, da gaske bashi yace yana sonki ba?


Gyara xama sumayya tayi ta zayyana masa labarin muhammad, da irin wahalhalun da yasha.


Tabbas Ammar ya tausayawa rayuwar su muhammad, kuma a cikin labarin sa da sumayya ya auna wasu abubuwa da dama akai, sai kuma abu na biyu, sumayya kina nufin mamar ki sunan ta hafsa sannan yar maiduguri ce?


"Eh Amma bansan  a ina take a maidugurin ba"


Amma naji mahaifin ki yace zai kaiki wannan karon.


"Ni yanzun bata maiduguri nake ba, ta mijina nake"


Sumayya kiyi hakuri ki koma gidan naku,  tunda naga iyayenki zama a gidan Adara ne basaso kiyi, in Allah yasa Al'ameen ya dawo,  kinga shikenan sai ki dawo d'akinki, in ma basason zaman gidan ne, nizan nema muku wani gidan saiku koma, amma a halinda kike cikin nan ya kamata ki kula da kanki, juna biyu ne dake ga dp ki na hawa, koh kinaso ki rasa babyn nakune?


"Ah ah yaya Ammar"sumayya ta amsa masa.


Yauwa koh kefa kiyi hakuri ki koma gidan kinji?insha Allah auren ki da muhammad bazai mutu ba.


Kuka sukaji da karfi a gefen su, khadija ce ke kuka.


Kee lafiya menene haka?


Kallonsa khadija tayi da haushi jin tambayar da ya mata, toh ba kai bane kake cewa Aunty ta tafi, toh ni kuma in zauna dawa?


Da goggo mana zaki zauna, ba za'a bude makaranta gobe monday ba?saiki cigaba da zuwa kafun yayan ki ya dawo.



Kuka khadija ta sake, shikenan aunty yanzun tafiya zakiyi ki barni.


Toh koh zaki bita ne gidan nasu?koh taki bin umurnin iyayen ta akanki?khadija iyaye fa ba wasa bane?ammar yace cikin haushi


Shuru ta masa, sai ga likita yazo ya basu sallama, don sumayyar ba wani jin jiki tayi ba,   ruwan da aka saka mata ya kare.


Suna Fitowa taga Ahlin gidansu tim a cike a haraban  asibitin, kala batace musu ba Tana bin Ammar a baya,  ga khadija a gefe.


Tashi sukayi suka bisu a baya har packing space, sumayya motar Ammar tayi niyar shiga Amma dada tayi tsalle ta dire akan ba inda sumayya zata shiga, sai motar gidansu.


"Kinsan Allah dada in kika matsamin saina fasa bin naku naga ta tsiya" sumayya tace.


Yi hakuri kawalli jeki shiga na Abokin mijin naki.


Shiga motar sumayya tayi ta kalli khadija dake tafiya a hankali kamar kwai ya fashe mata a ciki, daga ka ganta kasan tana cikin matsanan cin damuwa, "ya Ammar ka fad'a musu bazan koma yau ba sai gobe, sutura driver yazo ya d'auke ni inna shirya kayana"


ba musu  Ammar ya fita a motar daidai lokacin khadija ke kokarin shiga, yaje ya sanar dasu basu wani d'aga hankalisu ba sukace goben insha Allah abie da kansa zaizo d'aukar ta, in kayan sawane ma?ta bari kawai za'a saya mata sabbi.


Amma sumayya tace ita sai ta kwana washe gari zata koma gidan su.


Bayan isar su sumayya gida, Ammar tafiya yayi, khadija ta kalli Auntin ta, yanzun Aunty da gaske zaki tafi ki barni?shikenan ni babu yaya babu ke banida kowa yanzun sai goggo?


"Khadija baxan barki ba koh babu yayan ki Zan kula dake, guduwa zamuyi daga jalingo, gobe goben nan da asuba zamu bar gari..............🍀🍀🍀



✨Ruqeenjalal✨



🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

No comments