Breaking News

Matar makaho 74-75

 


page7⃣4⃣&7⃣5⃣


Abdul'aziz wanda aka fi sani da shugaba, haifafen mambila plateau(Gembu) ne, Ainahin su fulanin gembu ne,  acan aka haifi Abdul'aziz,duk da yana kauye hakan bai hana shugaba karatu ba, yayi karatun sa na secondary kafun yayi  aure,  matar sa ta farko fatima wance ake kira da fa'i, ita ma yar gembu ce, auren dangi aka musu, kafun daga baya ya aure sumayya (Dada), a kauyen su yake rayuwar sa da matan sa biyu,da yaransa maza biyar, yaran fa'i uku, Abdul'aziz mai sunan babansa(babuji)sai Abubakar da gaddafi,sumayya(dada)nada maza biyu itama,  Usmanu sai Abdulsalam(Abie)shine autar gidan su, akwai kyakkyawar fahimta da zaman lafiya agidan, shugaba(Abdul'aziz)hakan ya samu asaline daga zaman lafiyar da matan keyi, zamane na kwatance a kauyen su, kaf kauyen babu gidan da zaka shiga kayi mamakin zaman kishiyoyi iri na gidan shugaba, sosai abin ke bawa wasu mazan sha'awa, don shugaba adaline a gidan sa, duk da auren soyayya sukayi da sumayya hakan baisa ya nunawa fa'i banbanci ba.


bayan wasu shekaru an samu fad'an kabilanci a gembu sosai,tsakanin mambilawa da fulani wanda yazamo sanadin mutuwar fatima uwargidan shugaba, da mahaifiyar shugaba, daman mahaifinsa ya jima da rasuwa, wasu da dama a yan uwansa sun rasa ransu, a rikicin da ya afku.


Bayan kome ya daidaita, shugaba ya saida duk wani kadara nasa na kauye wanda mahaifinsa ya mutu ya bar masa, don shikad'ai babansa ya haifa namiji sauran matane kuma duk sunyi aure, ya dandanka musu nasu gadon.


Jalingo babban birnin jahar Taraba, ya tattara iyalansa suka dawo jalingo, gida madaidaici shugaba ya saya, yasa yaransa a makaranta,  dada tana kula dasu kamar y'ay'anta na cikin ta, sam bata nuna musu banbanci da nata duk d'aya ta d'auke su, wannan abin shiya kara dasa soyayyar ta, a zuciyar mijinta.


Bayan wasu shekaru kudi sosai ya fara zama a Aljuhun shugaba, don business yake na manya manyan shaguna zanunuwa a kasuwa yana order daga kano, aje aje yakoma na mototi, Arziki kullum gaba gaba yake ga yaransa na makaranta, duk wanda ya gama secondary, kwasar waje yake turasa karatu.


Lokacin da yaransa suka fara nisa a boko , hakan yasa ya sakar musu wasu kud'ad'e su gwada tasu kasuwar, babuji da Abubakar sune suka fara kammala karatu, suka fad'a business abinka da yan boko, kuma kwararu a bangaren business,  kankace kome kudine ya zauna company suka kafa mai zaman kansa, tare da haden gwuwar junan su, sosai arzikin su ya fantsama.


Babuji da Abubakar a rana d'aya sukayi aure , wasu yaran jalingo suka aura wa'inda suka hadu a makaranta, bayan auren su,  saida suka haifi yara bibbiyu, kafun gaddafi da Usman sukayi aure.


Abdulsalam ya kammala karatunsa Amma sam yaki aure kaman yan uwansa,  duk yanda iyayen sa sukaso yayi sai abin yaki, dada har magani take saka masa a abinci koh Aljanane ta aura mata yaro, Amma ina shuru abu yaki kowa aka nuna masa yace baya so, bata masa ba hardai su gaddafi suma suka hayayyafa sosai , a lokacin yaran babuji biyar, na Abubakar uku, yaran gaddafi biyu, na usman hudu.


Bayan wasu yan shekaru shugaba ya kwanta ciwo, baiyi wani dogon  jinya ba Allah ya karbi rayuwansa, gadon da aka raba musu shi suka had'a suka gina katafaren gida a unguwan specialist, gabaki d'ayan su suka tattaro kan iyalansu suka dawo cikin gidan da zama, don a lokacin Babuji da Abubakar suna da company kansu har biyu, yayinda gaddafi yake aikin goverment, usmanu d'an siyasa ne, Auta Abdulsalam shi ma'aikacin Bank ne(Accounter)kasance warsu rikankun yan boko ga naira ga kyau, kowa yasan yanda fulanin gembu keda tsananin kyau.


Rayuwa ake a cikin shugaba family house mai kyau, daban sha'awa, mazan basu bawa  matansu daman da zasu kawo musu tashin hankali ba sam, koh kara kika kaiwa mijinki matar wansa ta miki kaxa, had'a meeting ake a kira kowa, ku maida maganar hakan yasa matan sam suka daina fad'awa mazajen su,  saidai ayi iyya mata da mata kasa kasa.


Auren Abdulsalam ne yaxo musu da sabon salo, saboda yarinyar da ya kawo akan ita zai aura, yar maiduguri ne Amma tana karatu a TSU, tazo bank inda yake aiki cire kudi, Allah ya had'asu kanuri ce, hakan yasa dada tace ita sam bata yarda da auren nan ba, bazasu aure babarbariya ba, abinda ya xamo cecekuce a gidan kenan, duk yanda Abdulsalam yaso fahimtar da ita son da yake ma yarinyar, abu yaci tura sam taki Amince wa katafau tace bata yarda ba, shikuma Abdilsalam yace muddin ya rabu da Hafsa toh shikam bazaiyi aure ba.


Aijin haka yad'agawa dada hankali don tasan sarai halin Abdulsalam, akwai kafiya kamar me, tayaya ma aka samu ya samo hafsar kullum yace yakusa aure shuru baiyi ba,  bare yanzu yace bazaiyi ba ai magana ta lalace.


Babu yanda ta iyya da banbakin su babuji ta Amince da auren hafsa, har maiduguri akaje  da zancen auren.


 su karan kansu iyayen ta sunso gardama amma ganin sannanen family ne,  yasasu karbansu da hannu bibbiyu, tare da kafa sharadin yarsu zata cigaba da karatu insun amince, zasu basu ita?


Amincewa kam sunyi saboda kaf gidan shugaba yan boko ne, hatta matan gidan na zuwa aiki, rainon yara ma dada keyi da masu aiki.


BAYAN AURE

Hafsa fa ta fara fuskan tan banbancin launi a gidan su Abdulsalam, kasancewar ta baka kuma kanuri, sabanin yan gidan shugaba farare ne, daga matansu har maza da yara gasu fulani kyawawa, don Abdulsalam baza'ace kyaune ya rud'asa akan hafsa ba, ah ah sonta ne kawai Allah ya diga masa  a zuciyar sa yaji baya ganin kyaun kowace mace sai nata, sosai ake nuna mata banbanci kuma ba wanda ya fara asasa hakan sai dada, haka zasu zauna suna hira daga sun ganta zasu koma yi da yare basa janta a jiki, inta matso garesu basa sonta rabesu sam, kansu a hade Amma ita sun ware ta.


Hakan dasuke, yama hafsa zafi, yasata watsar da kowa na gidan, ta kama karatunta daga ta dawo makaranta ta shiga kitchen tayi girkinta, zata haura upstair's, ta shiga d'aki bata fita sai mijinta ya dawo.


Abdulsalam yasha had'a meeting da korafi akan abinda akema matar sa, duk da bata fad'a masa ba, yaga alama yayunsa mazane kad'ai ke sonta.


A haka fa abu yaki chanjawa abubuwa sai cigaba suke a haka, hafsa zaman hakuri take a gidan, babu zagi babu duka, Amma ana nuna mata mugun hali kam, a hakan cikin hukuncin Allah ta samu ciki, wanda kaf gidan babu mai farin ciki sai ita da mijin ta da yan uwan mijinta, amma babu ruwan matan dasu dada da ita, gashe cikin yazo mata da laulayi, bata iyya aikin kome, kuma babu mai taimakon ta, karshe dai Abdulsalam d'aukar hutu yayi a bank ya zauna a gida yana kula da matar sa, amma abu yaki karshe dai kiran iyayen ta yayi aka turo masa kanwar hafsa,  tazo ta zauna da ita har cikin ya tsufa bata koma ba.


Wata ranan Alhamis hafsa ta tashi da nakuda tsakar dare, Abdulsalam da kanwar hafsa ne, suka kaita asibiti don baiko sanar da yan gidan tana nakuda ba, hospital aka kaita kafun asuba Ta santalo yarta kyakkaywa fara tas, jinin gembu mai tsananin kama da zuriyar gidansu, koh kama da hafsa batayi kome na babanta ne.


Sosai Abdul yayi farin cikin samun wannan baby, ga wani irin sonta daya ke sosai yaji son babyn sa, washe gari ne yan gidan suka tashi sukejin labarin haihuwar a bakin mazajen su, Dada da matan sunje asibiti bada son ransu ba, saidai ganin yanda Abdulsalam yahad'a wa kowa fuska,  gaisuwa ma dada kawai ya gaishar, ya shiga yad'auko kayan baby ya fita, hakan yasan su zuwa duba baby.


Ba karamin dadi sukaji ba ganin yarinya kamar su ta biyo, bama kamar dada a murna, zama tayi a asibitin taki tafiya ita kema yarinya wanka, duk da yar uwar hafsa tazo washe gari Amma dada ta karbi kome na baby, harsuka koma gida dada fa na leke da yarinya, ranan suna yarinya taci sunan dada sumayya ana kiranta da momcy, haihuwar sumayya shine musababin zaman lafiyar hafsa, sosai taga change agun dada haka ma matan gidan, sosai suka koma damawa da ita, itama bata rikesu a rai ba, a sannu sannu har itama ta fara jin fulatanci duk ta maida martani na bata wuya, amma babu abinda zaka fad'a da fulatanci bata sani ba, dayake gidan sosai suka rike yarensu, suna hausa Amma ba sosai ba.


Sumayya(momcy) tana da shekara hudu Abie inta ya shigar da ita makaranta, lokacin hafsa(ummi)ta kammala karatunta na jami'a ta fannin koyarwa, taso kara gaba Amma abie ya hana, aiki yasama mata na koyarwa a makarantar secondary, wannan kenan.


Sumayya na cika shekara biyar kanin Dada Allah ya masa rasuwa a gembu, dukansu sukaje taziya, bayan sadakan bakwai dada ta d'auko yarsa daya haifa guda d'aya, mai suna safina(momy), bayan dawowar safina family shugaba, sai abubuwa suka fara bullowa saboda tunda safina ta shigo gidan shikenan ta fara likewa Abdulsalam(abie)duk wani iyayinta abie baya kulata,  asalima sai ya daina zaman falo kwata kwata koh abinci ne saidai suci da ummi a d'aki, abin har yakai ga dada ta lura da hakan, sosai ta nuna masa bacin ranta akan yana nunawa safina mugun hali don tana zaune a gidansu.


Zama ya fara rashin dadi lokacin da safina ta fitoh karara tace ita abie take so, sam abi yaki zancen kuma ya nuna bazaiyu ba, ummi karan kanta a lokacin ba karamin bakin ciki taji ba, don gwara tayi kishi da kowa akan safina, irin yaran nan ne shegun kauye masu shiga idon mutane, gashi batada kunya sam.


Dada fa ta tuntube abie akan zancen ya nuna bazaiyu ba, hakan yasa dada bata tilasta masa ba ta watsar da xancen, abinda ya konawa safina rai kenan, kaf gidan babu mai supporting nata,  kowa ya nuna baya goyon baya akan zancen, harda matan babuji basa sonta.


Safina makaranta aka saka ta na islamiyya,  don sam taki zuwa boko duk yanda akayi bazata ba islamiyyar ma daker ta fara zuwa, zuwan ta islamiyya shiya had'ata da kawa nafisat, nafisa irin yaranan ne watsansu marasa jin magana, haduwar su da safina,  yasa nafisa nunawa safina abubuwa da yawa, ta kara kangarar mata da kai, bata tsoron uban kowa.


Abin yayi matukar d'agawa dada hankali duk yanda taso rabata da safina abin ya gagara, gashi a lokacin nafisa bazawarace harda y'a d'aya take dashi, hakan yasa dada mawa safina barazanan zata maidata kauye, amma safina koh a jikin ta, ta nunawa dada koh ta maidata kauye tasan hanya, duniya da fad'i.


Bayan wata uku da haduwar safina da nafisa,  lokacin sumayya nada shekara 6 a duniya, hafsa ta fara ganin change a zaman su,  sam yanzun zaman ba dadi tsakanin ta da mijinta, kullum cikin rikici suke wanda itama karan kanta batasan dalili ba, sosai abin ke damunta,  wasu lokacin har  Abdulsalam na dukanta, Amma bata taba fad'awa iyayen ta ba, koh wani nata saboda tanason mijinta,  sai kawarta wance suke karantar wa a makaranta d'aya, don lokacin kanwar ta da aka kawo mata lokacin cikin sumayya tayi aure, batada wani nata kusa.


Yau an waye gari da wani masifa a gidan shugaba, amma dada satan sarkan gwal inta, sosai tayita masifa tana zagin yan aikin gidan wance ke mata gyaran d'aki kamma koranta akayi, koh sati ba'a kara ba aka sake ma hajjo(matar babuji) sata, ba'a kama barawon ba, haka aka ringa sace sace kusan wata har rashin yarda ya shiga tsakanin juna, kowa na zargin d'an uwansa, ba yan aiki kad'ai ba.


Kamar yau aka sacewa Matar abubakar agogonta na demond, yau kam masifa aka sake akan sai anbi d'aki d'aki anyi bincike, sai an fitar da barawon don kaf gidan tunda safe babu bakon daya shigo koh ya fita, kuma kowa na gida ranan don weekend  ne.


Bincike aka ringayi har akazo d'akin hafsa, kamar a mafarki aka ga agogo da wasu sarkoki na dada a cikin wardrop na ummi abinda ya kawo cece kuce dacin mutuncin hafsa a gidan.


Daman mai hakuri bai iyya fushi ba don ita da iyya gaskiyar ta, bata d'auki kome ba yama za'ace a iyya tsawon zamansu bata taba sata ba? sai yau sannan ita aitafi karfin sata tunda bayar matsiyata bace ita, sosai ta fara maida martani kowa ya gaya mata bakar magan fad'a masa take ita ma, ana cikin haka abie ya dawo daidai lokacin dada ke zagin hafsa, ita kuma ta gaya mata bakar magana, daman tun asali bata son zaman ta da d'anta, shiyasa ta had'a baki aka lika mata sata.


Abie babu tambayar ba'asi yaja ummi d'aki ya rufe, duk da sumayya yarinya ce, amma a ranan tasan gidan shugaba sunyi ma mahaifiyar ta ba daidai ba, duka abie yama ummi kamar zai kasheta daker aka kwaceta.


Cikin kuka ummi ta kira kawar ta a waya don ta tsorata lokacin, ganin jini nabin kafafunta, bayan zuwan kawarta, asibiti ta kaita ashe karamin cikine da ita wanda likitoti suka tabbatar daya zube, ga rauni kota ina a jikinta, wayar hafsa kawarta ta d'auka ta kira iyayenta, ta fad'a musu duk abinda ke faruwa tun zaman hafsa a gidan, kamar yanda hafsar ta taba fad'a mata.


A ranan mutanen borno suka diro Taraba,  cikin tsananin bacin rai, direct hospital suka dosa, duk da isan dare sukayi,  ganin halinda hafsa take ciki abin yayi  matikar musu ciwo sosai, kotu suka maka abie Amma ina abin ya gaggara saboda iko da kudi da abie suka fisu dashi a jalingo, hakan yasa shari'a taki bima hafsa hakkinta, karshe dai mahaifinta yayi rantsuwa hafsa bazata zauna da Abdul ba, saiya sakar masa da yarinyarsa,  ba jinkiri agun abie ya saketa, ya basu takarda a hannu, wannan ciwon yasa mahaifin hafsa yace koh bayan ransa baiyarda hafsa ta kuskura ta sake taka gidan shugaba  koh da wasa ne babu ita babu sumayya, ta manta ma ta taba haifar y'a, yajama abie kunne mundin ya taka  kafa a gidansa koh sumayya , zai nuna masa ikonsu a maiduguri.


Wannan shine dalili koh ince musababin rabuwar sumayya da hafsa, su karan kansu yan gidan basuso sakin hafsa ba duk da abubuwan da ta sace musu, Amma bakin Alkalami ya bushe.


Bayan tafiyar hafsa sosai sumayya ke kewar mahaifiyarta,  kullum haka zatayi ta kuka a kaita wajen ummin ta, duk yanda dada zatayi rarrashe ki take, karshe da abie yagaji bulala yake mata kafun tayi shuru, a haka haka ta fara cire abin a ranta, soyayya sosai ake gwada mata a gidan baga dada ba wanda ita ke kula da ita yanzun, d'akinsu d'aya haka matan gidan na mugun sonta da mazan, wannan karon harda safina amasu nuna mata so, ba kamar daba  inta ganta kamar ta cinnnta a wuta, sosai yanzun sumayya ke wa yara lalle na wasa, daman tunda haka ta tashi da abin abien ta na kara mata karfin gwuwa, duk da kananun shekarunta don lokacin tana neman shekara 7.


A wannan lokacin ne safina ta sake yad'a manufarta nason auren abie, kamar wanshan karon ma abie yaki amince wa, amma dada ta murza ido tace bata yarda ba aure dole koh yaso koh yaki, haka abie yana ji yana gani aka D'aura masa aure da safina, batare da son ransa ba, sam sam yarinyar batayi masa ba yaji baya kaunar ta.


Tirkashi dada batasan wannan aure shine ummul'kaba'isin kome ba..............🍀🍀🍀🍀🍀


Anya gobe akwai update kuwa🤔🤔




🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃


No comments