Breaking News

Matar makaho 70-71

 


Page7⃣0⃣&7⃣1⃣


Inna Talatu ce tsaye, sai huci take cikin masifa, Wallahi indo in baki fita harkar yaron nan ba, saina saba miki mena fad'a miki akan sa?


Don Allah inna kiyi hakuri, bazan kara ba, tace tana mikewa tsaye.


Uban me kike mika masa a laida?


Inna aikana yayi fa.


Shige nace, tayi maganar tana hankad'a indo cikin gida.


Al'ameen kam da ido ya bisu, watoh a rayuwa koh baka ma mutum kome ba, in kaje waje sai kaga masoyi da makiyi, zaka ga ka burge wani, wani kuma haushi kake basa.


Tsoho kai kad'ai kake zaune ne?gidado daya fitoh gida yace.


Eh gidado, yace yana matsama gidadon ya zauna.


Gobe fa babu zuwa kiwo.


Meyasa?


Akwai shadi ne.


Ina da yamma ne,?muhammad ya tambaya.


Au harma kana da labari kenan?


Eh indoce take sanar dani wai bazata tallah ba.


Eh gaskiya gobe za'ayi wasa da yamma.


Chap sai kuma ya hanaka kiwo?basai muje mu dawo da wuri ba, itama indo taje tallan tah ta dawo da wuri ba.


Gaskiya ne, Amma mudai anan in za'ayi shadi duka yan kauye basa zuwa koh ina a ranan.


Ok kana nufin kaima kafun kayi aure saida aka farfasa maka baya? kamar yanda nake jin Labari, don mu an daina a garin mu.


Eh nima kafun na aure matata, duka akamin Hamsin, yace yana cire rigansa ya nunawa muhammad bayansa.


Zare ido Al'ameen yayi ganin wasu bulalu kwance a bayansa rututu duk da sun warke amma tabon su na nan, yanzun kana ji kana gani gidado aka maka wannan?


Eh yanzun kai yanda kake kaunar sumayya bazaka iyya tsayawa a bulale ka,  don ka mallake ta ba?


Zan iyya harma yafi wannan, indai akan tane.


Toh baka gani ba, nima zan iyya jurewa.


Gaskiya ne Allah yabar kauna, Al'ameen yayi maganar yana kallon gidado.


Haka rayuwa yake tafiya, A hankali A hankali har muhammad ya saba da rugar su gidado,  yanzun ya waye a kiwo, wata rana har raba shanu suke da gidado, kowa ya kama hanyar sa, tsakanin sa da yan gidan akwai mutun tawa da ganin darajan juna, duk yanda inna ke nuna masa kyama da masifa, bai taba koh d'aga ido ya kalle taba saboda darajan gidado da bappa.


Jikinsa Alhamdulilah shi karan kansa yaji sanji a jikin sa, ba kamar da ba, haka tsakanin sa da indo akwai mutunci, duk da ba shiga tsafgarta yake ba, amma makale masa data ke, yasa yakan d'an rage mata wani abin.


A sannu sannu gashi yanzun Muhammad na neman wata biyu, a ruga kuma yana cigaba da maganin sa.





**********************

Sumayya  ma tana nan da halinta nacin masara, sosai ta maida masara da kunun aya  abinci, duk lokacin da Ammar zaizo dubata duk da ba shiga cikin gidan yake ba , a waje yake tsayuwa, saiya kawo mata masara koh kunu, sosai take ganin darajan sa kamar d'an uwan ta na jini, tunanin muhammad kam har gobe bata daina ba, saidai ta rage, Ashe haka b'atan d'a da miji yake? har gwara mutuwa wannan ka gama tabbatar wa kanka ya tafi kenan.


Yau asabar babu makaranta, khadija ce ke wanke kayan ta a kofar sumayya, yayinda sumayya ke zaune a gefe tana latsa system nata, hannun ta rike da masara


Assalamu Alaikum,wani yarone yayi sallama a bakin shashen su sumayya.


Wa'alaikumu salam ta Amsa masa tana mikewa zaune, shigowa yayi da kwano a hannun sa ya mikawa sumayya, wai inji goggo Amina.


Amsa sumayya tayi tace,  yacewa goggo ta gode, budewa tayi gwaten shuwaka ne, yaji kyad'a da tsaki sosai, yawunta ya tsinke da sauri tamike ta d'auko shukali, ta faraci, "khadija ga gwate"


Ah ah aunty kici nagode


Kala sumayya batace ba, cigaba tayi dacin abinta, harta cinye tass, sai kuma taji bata son shan kunu aya sam, ruwa tasha sai kuma taji yawo ya cika mata baki.


Haka sumayya ta wuni tana zubar da yawo,  gashi ba yawo kad'an ba, karshe dai kunun nan rabawa yara tayi.


Tun daga Ranan sumayya ta maida gwaten shuwaka da macikan zogale, sune abincin ta sai goruba haka ta maidasu abinci, masara duk sun zama tsohon yayi, haka Ammar ma ya maida ganye abin kawowar sa, sam baya gajiya da hidimar sumayya.



Yau wata biyu kenan da batar Al'ameen, haka kawai taji a daren tana son cin tsire mai yajin bakuru, da cabbage, haka tasa khadija a gaba suka fita wajen mai nama tsallake sukaje suka saya, sunzo zasu tsallake titi kawai sukaga wani MAKAHO da d'an jagoran sa,  zasu tsallake titi alamu dai dare ne ya musu wajen bara.


Sosai sumayya tabisu da kallo hawaye na cika mata ido"ina suka kaimin mijina"?


Don Allah aunty kiyi hakuri, kinga mun samu kin samu lafiya karki sake jajibo ma kanki ciwo don Allah.


Shuru sumayya tayi suka tsallake titi,  suna zuwa gida bayan sunci namar ta kwanta akan gado , khadija na kujera,Har khadija tayi bacci itakam ta kasa, , haka ta raba dare idanun ta biyu tunanin Rayuwar da mijinta ya shigane ya dameta.


Da asuba da mugun ciwon kai ta tashi da zazzabi, khadija taso suje asibiti Amma haka ta ki zuwa, kafun azahar sosai cikin yayi tsamari



Cikin ikon Allah Saiga Ammar yazo, shiya kaisu asibiti, bayan sunga likita ya mata tambayoyi, yace nurse ta bata roba tayi fitsari akai lab.


Tunda sumayya taji haka, sam bata damu ba don ita ta d'auka koh ahone ire iren da aka mata, lokacin da hawan jini ya kwantar da ita.


Bayan wasu hours, nurse ce ta dawo da result a hannun ta, mikawa likita tayi ta juya ta fita.


a hankali likitar ya kalli Ammar ya kalli sumayya, harga Allah ya d'auka ma'aurata ne, Congratulation Aboki na matar ka na d'auke da cikin wata biyu da sati d'aya.


Ammar kallon sumayya yayi, daidai lokacin itama ta kallesa sai kuma suka sake kallon likita har suna had'a baki, "ciki"??


Eh ciki wani abune, ya tambaya da mamaki ganinsu haka.


Ah ah ba kome likita, Ammar yace yana kallon sumayya data d'aura hannu akan cikin ta, tanna hawaye na farin cikine?koh name oho baigane ba.


Am bayan wannan akwai wani abin, ya kamata aboki kana kwantar mata da hankali a matsayin ta na iyalinka,  ya kamata ka bata kulawa yanda ya kamata, yanzun juna biyu gareta Amma yanda take saka tunani a ranta, zaku iyya rasa baby ku, ciwon kannan nata tunani ne ya jaza mata, bp nata yahau, kuma bama son haka, a halinda take ciki yanzun nan.


Insha Allah doctor za'a kiyaye, Ammar ya Amsa kawai, yana karban takardar magani da likita ya rubuta musu.


Fita sukayi xuwa pharmacy, magani ya saya mata suka shiga mota, har lokacin hawaye sumayya take abin gwanin tausayi.


Kinga sumayya yanzun fa Dr yaja miki kunne akan damuwar da kike sakawa kanki, waike wace irin mutunce? kukar ne zai dawo dashi kome?


" na daina"kawai tace tana share hawayen ta.


Me zan sai miki?


Girgiza masa kai kawai tayi, Alamu batason kome.


Tsayawa yayi a bakin asibiti yasai mata Alale, ya dawo motar ya mika mata


Ba musu sumayya ta karba, ta rasa me yasa duk Abinda Ammar ya bata sai taji tanason ci.


a haka Rayuwa yake ta tafiya yau farin ciki gobe akatsensa yanzun cikin sumayya nada wata uku cip, bata laulayi haka cikin yazo mata, kamar babyn yasan babu Dad a kusa, saici yanzun kam kome ta samu ci take kamar me, koh zabe batayi.


Babu abinda ta nema ta rasa, Ammar na mata goma sha, shagari shike cefenen gidan ogansa, da duk abinda zata bukata shike bayar da kudi,asai mata, maganar lalle ma yanzun batayi sai make-up kawai shima Amare take ma, duk maiso tazo gida, a hakan take ta tara yan kud'aden ta, yanzun sunyi yawa a Account in khadija.


Yau dai tunda ta tashi da safe takejin wani irin nishad'i wanda batasan dalili ba, tana tashi da safe dayake yanzun sam batason saka riga,don rigunan sun mata kad'an, sosai nonuwan ta suka cicciko, have vest da zani ta maida su kayan sawan ta, ko mai bata shafawa saboda wari yake mata, haka turare ma koh wani iri bata Amfani dasu.


Zaune take a taburma ita kad'ai ta mimike kafa, don khadija ta tafi kasuwa, babu school yanzun suna hutun first time, kosai ne a gaban ta da kunun kyad'a tanaci, sosai sumayya tayi jiki tayi kiba, wuyanta har guru guru yayi, hips natan nan sun kara buduwa haka ma breast nata, daman akwaisu bare yanzun da dalili.


Sallama akayi a tsakar gidan, na muryoyin mutane abin ya bata mamaki jin kamar muryar sani, bata gama shan mamaki ba saida taji suna gaisawa da y'an gidan Adara dake tsakar gida, suna tambayar su kofar sumayya.


Mikewa tayi tsaye koh d'an kwali babu tsaban mamaki daga ita sai zani a kwankwaso da have vest, jin sun nufo kofar ta, kamar a mafarki Amma dai bara ta tsaya taga ikon Allah, bude kofar shashin ta akayi, da sallama



Suman wucen gadi tayi, wallahi ita harta manta da wasu shugaba family, sai sa'i da lokaci take tunasu, cigaba tayi da tsayuwa tanabin wa'inda suka shigo da kallo.



Dada ce a gaba sai matan uncles nata da yaransu harta surkunayen  su momy ce kawai babu, ko wance cikin shiga ta Alfarma kana ganin su kaga inda naira ta samu matsunguni, murmushin yakene koh wance a fuskar ta,  da kunya suma tsayen suke suna bin sumayya da kallo, kamar yanda itama ke binsu da kallo.


Mamakine ya kamasu ganin yanda sumayya ta koma, sam bazaka taba cewa auren talaka take ba, sumayyar suce ta zama buhu haka?


Takwarata bazaki bawa tsohowa wajen zama bane?gidan ki guda fa nazo, dada tace tana kara bin sumayya da kallon mamaki yar jikanta gabaki d'aya ta canja.



"Ga taburma bismillan ku"tace tana shiga d'aki hijab ta saka ta d'auko babban dardumar ta, ta kara shimfid'awa a gefe, ganin taburmar bazai d'auke suba, dardumar ma bai gama d'aukar suba wasu a bakin dakali suka zazzauna.


Zama sumayya tayi akan kujera tsugunu bayan ta d'auko sa a kitchen" ina kwanan ku"?


Lafiya sumayya, ya maigidan naki?


"Lafiya" kawai sumayya ta amsa kamar irin bata ganesu innan ba.


Yar nan kice kika dawo haka gaskiya aure ya karbeki sosai wallahi, Hajjo matar babuji tace


"Umm ikon Allah kenan ai hajiya, sai ya baka abinda wasu basu so ba"amsar da sumayya ta bata kenan tana cigaba dacin kosanta kamar irin taga sabbin fuskar nan.


Jikin dada yayi sanyi, ganin halin koh in kula da sumayya ta nuna musu, da ace dane koh makaranta sumayya ta dawo inta ganta saita mata oyoyo ta rungume ta, suna wasa da tsokanar juna irin na jika da kaka, amma yau kallon banza sumayya ta mata, kawalli yaufa wuni muka zo miki, gabaki d'ayan mun nan munyi kewar ki yar mu.


"eh dole kuzo mini jaje ai, tunda kunsace mijin hankalin ku ya kwanta, abinda ake so a gani dai insha Allah baza'a gansa ba, koh xaku mutu haka zaku ganni ku barni, don Mu Allah muka rike" tana magana tana shan kunun ta kamar ba ita ke magana va




Miemie ce ta mike, habba sumayya wannan wani irin banzar magana ne, ya zaki bude baki kina fad'awa hajjo da dada irin wannan magana?



"Keee mimi, ban kasa dake ba karki kuskura ki kwasa, dasu nake babu ruwan ki a maganar nan, kona karta miki layin rashin mutunci"


Eyeeee lallai sumayya, yaushe kika koma mara kunya haka?


"Kubra kenan rashin kunya ai dole na koya,  koh kin manta gidan da nake ciki ne"?sumayya ta bata Amsa


Habba sumayya wannan ba halinki bane, don Allah kiyi hakuri mu da kika gan munnan bamuzo don kara bata miki rai bane, munzo gyara abinda muka bata ne, aunty husna surkuwar uncle Abubukar tace.


"Keee Husna karki kuskura kisa baki a maganar nan, ina ganin mutuncin ki, sannan kina maganar ku gyara abinda kuka bata,  wani abin kuka bata da har xaku gyara?aini koh sanin ku banyi ba"


Mamakine  ya cikasu sumayya ta zama yar tasha, sun shiga uku, yarinyar da koh zagin yara bata iyya ba yau harda zagen manya haka.


Sumayya dafa iyayen ki maza muka zo gidan nan suna waje.


Kallon mammu sumayya tayi, jin abinda tace"meya kawo ku gida na kuma gayya guda haka"?


Munzo ne akan auren ki da yaron nan MAKAHO, tundadaman baso kike ba mumuka miki dole, sam yanzun bamu lamunce ba takardan ki xai baki baziki zauna da misk.................




*************

Muhammad dai yau shida indo , zasu cikin camaroon tallan nono, ta uzzura masa yau saiya rakata, dayake shima yana son zuwa cikin birni yasa sa binta, yau gidado ne kawai yaje kiwo, bappa da matar gidado wance cikin ta ya tsofa haihuwa yau koh gobe.


Cikin Cameroon suka shiga, indo na tallan nono shikam sai kallon gari yake abinsa,   basu dawo da wuri ba sai yamma lilis suka dawo.


Bappa ne xaune a bakin masallaci yayi tagumi, su Al'ameen suka same sa, gaidashi sukayi suka wuce cikin gida.


Da dare bayan isha'i Bappane da iyalansa zaune a tsakar gida harda Muhammad, hira ake sosai, tunda muhammad yazo gidan baitaba ganin sun zauna haka ana hira ba, harda inna da matar gidado lantana, 


Bappa bakajin dadi ne?


Gidado lafiya ta klau, bansan meke faruwa ba tunda na tashi yau nakejin babu dadi a jikina.


Toh Allah ya kyauta bappa, inna tace tana kallon sa don tun safe itama ta lura akwai abinda ke damun sa.


Ameen Talatu.



Amma bappa wani irin abune yake damunka haka?



Gidado mubar zancen nan kawai bashi da Amfani.


Kamo wani tadin akayi, sai hira ake muhammad nad'an saka baki kad'an kad'an in aka sakosa a zancen.



Sosai yau gidan bappa aka sha hira sai chan dare, muhammad ya musu sallama, kwanciya yayi bayan yayi Alwala yayi addu'ar bacci, haka kawai yake jin kirjinsa na bugawa, kwanciya yayi, yayi likimo a gado,har bacci ya d'auke sa.


Ta bangaren su bappa, sallama sukayi da juna bayan wucewar muhammad don shiya fara tashi, kowa yaje ya kwanta, Amma dai jikin su a sanyaye, yau dai indo taki kwana ita kadai a dakin ta, tace da innar ta zata kwana,  dole tasa inna komawa d'akin indo tabar bappa a dakin sa.



Da misalin karfe 1:14am agogon cameroon, Al'ameeen ya farka da salati jin ihu tako ta ina da salati, gari ya kaceme da hayaniya,  karan yara da matane kota ina, ga ruwan bindigogi dake tashi, da sauri ya dirka daga kan gadon jin inna na salati da karfi tana wuta wuta jama'a cikin yaren fulatanci

.................🍀🍀🍀🍀



Fan's🍋🥑 naga messenge inku ta PC nagode Allah yabar kauna wa'inda bamma reply ba sumin Afuwa abinne da yawa👌



🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯 

             ~ Na ~


 🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃


No comments