Breaking News

Matar makaho 1

 



 🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃

 

✨✨Godiya ta tabbata ga Allah  da ya nuna mini wannan Rana da Zan fara rubuta lbr na na farko cikin hukuncin ubangiji Allah ka bani ikon gamawa lfy 🤲✨

✨Tsokaci wannan shine novel Ina na farko  Koh da za'a ga mistake Koh typing error amini afuwa 👌

Free page


Page 1️⃣

Kuka nake baji ba gani bakin ciki ke dankare a cikin zuciya ta Wanda in har banyi kuka ba bazanji saukin suba Wai ni ce amarya amaryan ma na makaho mara ido na daga lulubena kasanciwar dakin akwai wutan nepa  glop ya haska Koh ido shiya bani Daman ganin daki dakin da Koh a mafarki van taba tunanin akwai ranan da Zan iyya rayuwa a irin Shiba Wai yau shi ake Kira da dakina na aure ni sumayya bansan lokacin da wani irin kuka ya sarkeni ba cikin takaici Mai tarin yawa ya Allah me naiwa Yan uwan mahaifina  da suka sakamin da wannan rayuwa Mai na tsare musu da suke mini irin wannan muguwar tsana da hassada ya Allah duk wannan magana cikin kuka nake yinsu  



Tsaye yake yafi minutes 30 Amma ya kasa karasawa cikin kofar wani irin fargaba ne dankare a cikin ransa Wai yau shine da mata sukutum Koh a mafarki Bai taba tunanin aure ba  kasan shiwarsa makaho maraya kuma Mara galihu sai abinda ya nemawa kansa Amma yau har Mata aka basa wance Bai taba tunanin samun taba amasayinsa na miskini  Anya zata karbesa a matsayin miji zata yarda ta rayu dashi cikin akwai Koh babu wannan sune abinda suka tsaya masa a Rai yayi ta maza ya daga kafarsa hade da Bismillah Yana tafiya da sandar sa Yana ma kansa jagora zuwa filin  kewayayeyyen kofar su Dan madaidaici ya juya ya tura kofar ya rufe harda lalubar sakata ya saka  a sannu a hankali yake takawa har yaji ya taba Dan tudu kadan  hakan ya nuna Masa ya iso dakalin kufar daki haurawa yayi sama Yana lalube tar yaji ya laluba ginin daki Yana bin ginin a hankali har yaji ya shafa window yanabi a hankali har yaji ya Kama labule mai masifan laushi da kamshi Wanda tunda yake a rayuwarsa Bai taba tunanin zai taba irinsaba kasan shewarsa  mutunne shi Dan babu ruwana ba ya maula Koh bara baya neman taimakon kowa in dai na abin duniya ne sai dai na lalurarsa Wanda ya zamto Masa dole 


Da sallama a bakinsa ya daga labulen tare da jingina sandar sa a kofar dakin ta waji ciki ciki na amsa sallamar itama Dan ta zama dole na daga kaina ina kallon wanda Koh ba'a fadaba nasan shi ake nufi da ango makaho cikin wani irin takaici nake kallonsa don matashine Wanda bazai Gaza shikara 28 zuwa 30  ba laifi makanta da wahalan rayuwa su kadai za'a kira cikas a tare dashi don kyekkyewa ne na karshe dogo fari tas wanda wahala ta kodar da fatarsa Amma duk da haka fatar daga Gani zatayi matsifar laushi   gemu mayalwaci sosai  ga idanu masu girma da haske amma mara amfani a ganina bakinsa madaidaici Mai shegen kyau ga hanci har baka Mai yalwan gera don daga gani yanada yalwan gashi sosai sai gashin kansa Mai yawa amma rashin samun wadasheshen gera sai ya Yi wani iri Amma daga Gani gashine na Fulani  asali duk da babu datti don fes Kan take  kiransa na zaratan mazane masu Kiran karfin sosai na kurawa kayan jikinsa ido wani kudadden yadine na shadda wando da riga Mai guntun hannu Wanda suka Sha ruwa sosai wai su ya saka kenan ranan aurensa daga Gani sune na gindin akwatin sa Koh Bai fada ba ni Kam na raya a Raina  kauda fuska nayi kamar bansan mutun ya shigo ba shi kuma cikin sanyin jiki da lalube yaji ya taka wani cafet Mai shigin laushi a cikin dakin duk da baya gani yasan tabbas Mai tsadane Koh me na dakin Nan don Bai mantaba dazun khadija take Masa gulma wai dakin Aunty'amarya Mai kyau da Kaya irin na gidan murtala Hon na unguwan su harma nata yafi nasu kyau tun daga lokacin jikinsa ya kara sanyi don ya tabbatar ba yar kananun mutane bane aka aura Masa a matsayinsa na makaho  da lalube ya iso tsakiyar dakin Wanda yaji abubuwa Kamar filo a xuzxube a kasar cafet in dakin  a hankali ya zauna tare da aje ledan dake hannun sa baka cikin zazzakar muryarsa Mai cike da Kamala ya gai Dani Koh juyuwa vanyiba don bana son ganin sama  bare  na sake Jin ya sake furta Ina wuni nayi wani dogon tsaki  Jin haka yasa shi Jin wani mummunan faduwar gaba Amma baice kome ba yayi shuru  munkai minti goma babu Mai shiwa kome sai Karan fanka Kiran OX babba wance Taki bawa dakin wani irin iska Mai sanyi  sosai  cikin rawar murya yace ga kaza nan kici sai muyi nafina mu gode wa Allah cikin zafin nama da takaici na hayyaya Koh Masa cikin fada Wanda duk Wanda ya sanni yasan ba halina bane Kuma Koh kyau Bata mini ba nace baza'a ci matseyacin kazar kaba kuma sallah kayi tayi har alfijir ya ketoh Bai shemin kome ba Amma kallo daya namar nasan maganar ta dake sa sosai  a hankali ya laluba yafita waji yayi iyya nemar buta Koh Randa baiji inda aka aje ba saboda duk kayan kofar an sauya Mata zama kasanciwar sabbi aka kakkawo hakan yasa ya koma dakin a hankali da sallama Ina dai zaune Ina  kalonsa yazo ya fara lalube a hankali ya daga labulen ya tura kofar ya rufe harda sakata cikin nutsuwa Naga ya fara lalube  ban ankaraba naji ya lalubu ni cikin wani irin shock daga ni harshi muka Masa baya shikam harda buge kafar sa da katakun gado cikin i'ina nace meye haka cikin Dan sanyi jiki yace kiye hakuri ina neman gadone Zan kwanta cikin gadara nace  wallahih bazan kwanta dakai gado daya ba gadai kujira a Chan jika kwanta a hankali ya fara lalube Ina dai zaune Ina kallonsa  haka ya ringa zagaya dakin daker ya gane kujiran a hankali ya zauna ya cire rigansa ya kwanta  a hankali cikin lumsheshen kujira na alfarma 3sita Nima kayan na cire tunda dai ba idone dashiba na ragi daga ni sai brz da siket nayi adu'a  na kwanta a hankali nake sauke ajiyar zuciya har bacci ya dauke ni  shikam ya kasa bacci sai tunane tunane yake yanason yin lafilfilu Amma ba Hali tunda baisa inda zai samu ruwa ba a kofar tasu Kuma baison zuwa rijiya a Darin nan gudun wani a cikin mutanen gidan su gansa su Masa abinda suka Saba rashin mutunci  a sannu a sannu wani bacci Mai Dadi ya daukesa don a tsawon rayuwarsa Bai taba bacci ana zafi da fanka ba sai yau lol asuba da gari amarya da ango 


Free page ban yarda da a sayarmin da littafi ba😠pls


Jinjina ga Yan Free books💃🏼💃🏼💃🏼


No comments