Breaking News

Matan Ko Mazan 13

 💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫





          ✍🏻M SHAKUR


EPISODE 1️⃣3️⃣

My people wai kunji labarin BUKKISH FABRICS N MORE??

Ku saurara kunji bantaba ganin masu harkan Atampas, laces dakuma lafiyayyun gangariyan ready to wear kaya ba dake badawa akan sari kwashakwasha kaman BUKKISH FABRICS N MORE ba, both

wholesales n retails sunayi, sunefa akama taken PAY LESS STAY IN FASHION, wato ki biya kudi kadan amman ki saka kayan yayi adama dake, ku tura musu message now ku kwashi kaya with little kudi, danna link din nan kimusu magana👇🏼

 wa.me/+2349034368170

Zaku iya duba shagonsu a TikTok- Bukkish fabrics n more 


13

Wuraren 5 Nura yatashi daga bacci, Hadiza dake gefenshi yakalla har lokacin bacci take, sauka daga kangadon yayi yawuce bayi, wanka yafito ya shirya cikin wani jallabiya yana zuba kamshi yazo gaban gadon yadago Hadiza like a baby softly yace “jekiyi wanka kizo kiyi salla My Didi” bude idanunta tarr Hadiza tayi takalleshi yamata wani irin kyau yau saita ganshi yafi koda yaushe kyau dasauri takai hannunta tadaura kan fuskanshi tana kallonshi everything is coming back to her daya faru da ita jiya, cikin murya mai raunin gaske tace “Nuri mafarki nayi ko? Ai baka auri Ummi yar aiki na ba ko”? Dan murmushi kadan Nura yayi yakai hannunshi yacire hannunta dagakan fuskanshi yace “tashi kije kiyi wanka kiyi salla Hadiza” yana maganan yawuce yabude kofa yafito dakin Ummi yabude yashiga bata kan gadon harta gyara gadon, yabi dakin da kallo komi a gyare tsaf jin karan ruwa abayi yasa yaje gaban bayin ya tsaya tareda knocking cikin cool voice yace “wankan me kikeyi? Mafarkina kikayi?” Ummi nacikin bayin akunyace tace “wanka kawai nakeyi, ina kwana Mijina dafatan kayi bacci mai dadi kuma katashi lafiya?” Dan ijiyan zuciya Nura yasauke ahankali, he loves how Ummi always greet him, gaisuwa takemai not common gaisuwa but gaisuwa mai dauke da details, baki yabude zaiyi magana  saikuma yace “ba’a magana abayi, maza kifito kiyi salla natafi masallaci” “uhm Uhm” tafadi amatsayin amsa hakan yasa yayi murmushi yace “naughty gurl” wucewa yayi yasauka kasa, yau monday he wants to see Hadiza ta chanza, he wants to be miji mai adalci, he just pray and hopes Hadiza will cooperate which he’s highly doubting it, dan yau girkin ta yakamata ita zatai girkin breakfast dasauransu, ijiyan zuciya kawai yasauke yatafi masallaci he’s just hoping zai dawo yaga tayi dama ga gidan na bukatan gyara.



Bayan Ummi tayi salla wani lafiyayen super tadauko tasaka cikin atampopin daya dinka mata dogon rigane fitted tazauna gaban madubi ta shafa hoda tasa kwalli tashafa wani pink janbaki sannan tayi dauri bayan tasaka dan kunne, shiru tayi tanason tafita taje ta daurama yaran nan girki zasuje school but tana shakkan Hadiza deep down kuma tasan idan tabari babu mai musu at the same time tana tsoron kada ace tayi shishigi bayan yau girkin Hadiza ne amman kuma tanaso tanunama Hadiza bawai dantaci mutuncin ta ta auri Nura ba ita kawai tanason Nura ne, kusan 3min tayi ahaka sanan tabude kofa kaman munafuka tafito ta maida kofan tarufe batare data bari yayi karaba tawuce tasauka kasa falo tafara gyarawa agurguje da dinning ta tattara duka kwanukan cokalan tawuce dasu kitchen tashiga hada abincin gida tanama Hajiya girki tana gyara kitchen din duka at the same time.

6 Nura yashigo gidan yau bai wani zauna a masallaci ba dan baiso Hajiya tafito daga daki ta nemi Ummi da bala’i, falon daya gani harya chanza kama yasa yayi shiru dan kawai ranshi yagayamai Ummi ne barin dayaji motsi a kitchen kitchen din yawuce a kofan ya tsaya yana kallonta tuwo take tukawa, ahankali yashiga cikin kitchen din dasauri Ummi tajuyo jin motsi ganin Nura ne yasa tayi murmushi tace “Sabahal khayri Baban Amanu” takowa yayi yazo inda take sai kawai ya rungumeta ta baya yana shakan kamshin datake yayi shiru itama saitai shiru tanajin saukan ijiyan zuciyanshi, bai damu dadan zufan datakeba ya goga gefen fuskanshi anata kaman mai whispering yace “maisa kika shiga kitchen yau ba girkin ki bane”? Dan shiru tayi kaman bazata ce komiba cikeda hikima tace “Anty tana zuwa aiki ni bana aiki, shine nace bari nafito nakama mata ta hanyar yin abincin kari saikuma inaso nama Hajiya girki dazataci kafin ta tafi asibiti, tunda nadawo nizan dinga mata abinci, ita nakema tuwon alkaman nan” shiru Nura yayi yana rungume da ita abayanta, akwai wani kalan hikima da Ummi kedashi da wlh ko educated mata dasaukai karatu daidaikune kedashi, yarinyar is good with words, Ummi is smart, tanada broad hikima kan zaman aure wanda yasan aikin Gwaggon tane, yanda ta tashi da safen nan tanama mahaifiyarshi girki abin warm his heart, dago kanshi yayi ya manna mata peck akumatu yace “godiya nake Hajiya Ummi” dasauri tace “nika dainamin godiya dan nama Mamana abinci” murmushi yasakeyi saikuma kawai yasaketa tareda juyoda ita yayi hugging nata so tight yace “thank you Hajiya Ummimy na” akunyace tazare jikinta daga nashi tace “tuwo zai kone” murmushi yamata sabida baiso tai wani abun yace “bari naje natada yaranki namusu wanka na shiryasu” dasauri Ummi tace “kabarshi zan musu zansa sanwan miyane nazo sama” girgizamata kai yayi yace “aikin zai miki yawa just do the cooking zan musu wankan” yawuce kofa saikuma yajuyo yace “kimini shayi” gyadamai kai tayi tace “angama maigidana” murmushi yayi yabita da kallo kaman yazo yamata wani abu saikuma dai yadaure yafita dan murmushi Ummi tayi dudda tanada damuwa tana cikin shakku da fargaban karya saketa bazata taba nunamai ba tama kanta alkawarkn nan.


Nura na zuwa sama baimaje dakin Hadiza ba dakin yaran yaje direct Aman yafara tarawa yakaishi bayi yasamai brush sannan yafito yaje dakin Amal yadauketa yakaita bayi yamata brush da wanka yafito da ita da towel yakoma dakin Aman yamai wanka shima wlh aikin yara is not easy yafito dashi da towel ya kwashi kayanshi sukazo dakin Amal anan yashiga shiryasu sunamai hira yana wasa dasu.

My people wai kunji labarin BUKKISH FABRICS N MORE??

Ku saurara kunji bantaba ganin masu harkan Atampas, laces dakuma lafiyayyun gangariyan ready to wear kaya ba dake badawa akan sari kwashakwasha kaman BUKKISH FABRICS N MORE ba, both

wholesales n retails sunayi, sunefa akama taken PAY LESS STAY IN FASHION, wato ki biya kudi kadan amman ki saka kayan yayi adama dake, ku tura musu message now ku kwashi kaya with little kudi, danna link din nan kimusu magana👇🏼

 wa.me/+2349034368170

Zaku iya duba shagonsu a TikTok- Bukkish fabrics n more 


Nan da nan Ummi tagama abincin Hajiya tahada breakfast tasoya chips ta sossoya eggs da sausage ta hadama su Amal abinci a lunch bag tadauko tafito zata ijiye a dinning tahada ido da Hadiza dake tsaye a dinning din tana sanye da riga da wani palazzo trouser mai shegen kyau na material pink tayi folding hannunta a kirji tana kallon Ummi da jajayen idanunta dasuka kumbura sukai jazur kaman mai ciwon ido abinku da faran fata, chak Ummi ta tsaya anan gaban kitchen din takasa karasowa dinning din ayanda zuciya ke diban Hadiza jitake kaman tazo ta shake Ummi tamutu gabaki daya, daga kafanta tayi tafara tafiya ahankali akuma zuciye tace “how dare you Ummi kika aure mini miji? Ni Hadiza kika aurama miji? Kin manta lokacin dana taimaka miki kina neman aiki ido rufe wayanda kikema aiki ada sunyi japa sun koma Canada anata gantali dake a Abuja ana nema miki gidan aiki baki samuba, na taimaki rayuwanki nabaki aiki nakuma biyaki da kyau, yan aiki da ake biya duba ashirin, dubu shabiya but ni nace zani dinga biyan ki dubu hamsin sabida duka gidana zaki kula dashi da yarana sabida bani zama ina fita aiki, sakkayan dazaki mini kenan ki aure mini miji, mijina Ummi? Nura na?” Ihu Hadiza tayi tana tafiya tace “ki daga fuska ki kalli kwayar idanuna bakar munafuka, algunguma, makira bakar mayya, butulu, shedaniya watsassiya, sai bayan kin aureshi zakizo ki kasa kallona kina sunnar da kanki kasa kaman baiwar Allah, dagakai ki kalleni Ummi, nace ki kalleni!” Hadiza tai maganan tana ihu daidai tana kaiwa gaban Ummi ta finciko gaban riganta gamgam tawani kalan jijjiga Ummi ta mugun makureta tana kallon fuskanta tace “wulakantacciyan yarinyar irinki harta isa ta aure mini miji, ni Ummi kina yar aiki na, sabida ina fita na barmiki gida kikai using opportunity nan kika auri miji na eh”? Hadiza tai maganan tana buga Ummi abango saida Ummi tasaki lunchbag din kasa tai kara Hadiza ta makure mata wuya tace “wlh, wlh, yau saidai afutar da gawanki ki daga gidan nan, ke! Dakikiyar yarinyar irinki tayi kadan tace inyi kishi da ita, bazan taba iya raba Nuri dakowa ba balle ke jinjiran yar iska kinajina? I will kill duk wacce tace zata auri Nuri na, dagani sai shi har lahira” “Hadiza!” Nura daya sauko tareda yaran suna surutu ya hangosu da gudu gudu ya sauko daga bene yazo wajen da sauri ya bambare hannun Hadiza daga wuyan Ummi yace “are u mad kasheta zakiyi”? Tari Ummi tahauyi sosai tana nishi idanunta sunyi ja, cikeda fada Hadiza tasake yowa kan Ummi tace “Nuri ba ruwanka awannan fadan is between me and this this munafukar makiran yarinyar” dasauri Nura yatura Ummi bayanshi daidai su Aman suna zuwa wajen da gudu zasuyi wajen Ummi suna “Anty Ummi sorry” rikesu Hadiza tayi dasauri tana tafarfasa tace “ku zonan ina zaku?” Dasauri Aman yace “wurin Anty Ummi, u hurt her Mom” cikin ihu Hadiza kaman zata make Aman tace “waye Ummi? Me kuka hada da ita? Who is that girl to you? Dagayau baku ba ita Aman kaida sister ka, Ummi is a bad evil person, babu wanda yataba cutata arayuwan nan kaman ita, bantaba nadaman abu arayuwana kaman nai nadaman ranan dana dauketa aiki ba, kar wanda yasake kiran sunanta cikinku agidan nan, Ummi is the worst evi…….” “Hadiza!” Nura yasake kiranta ranshi abace dasauri Hadiza takalli Nura tace “what!? Nura I said what kake kirana? Don’t tell me ka yarda cewa yar aikin nan son yarana take? Okay bakaso nagayama yarana she’s evil, Lemme tell you something today Yarinyar nan bata taba son yarana ba, she just use them tayi winning heart naka da nawa damuka yarda ta zauna gidanmu, bata taba son yarana ba, she use them taja ra’ayinka kasota, tunda ta kyallara ido taga muna biyanta 50k instead of 20-15k da ake biyanta a inda tabasa aiki ta kudurci aniyan saita aureka, saita zama matarka, saisa taja yaran jikinta sabida tasan you love yarannan morethan ur life sune the way to your heart, your weakest point Nura, open your eyes and see Ummi played you and me, Nuri Mezakayi da this village evil girl yar aiki fa eh Allah kadai yasan mazan mutane nawa taci, I will post her pictures on social media to makesure babu wanda yakara daukanta aiki a abujan nan tunda she’s a witch, ka barni naci bura’uban yarinyar nan Nuri tasan cewa Allah dayane” Hadiza takaima Ummi nushi Nuri yatare hannu ta hanyar rike hannunta gam cikin kakkausan murya yace “karkiyi kuskuren tabamin mata Hadiza stop all this thing!” Nura yayi ihu saikuma cikin turenci yace “I’ve given this respect leave this girl alone before I disrespect you in front of her” tafi Hadiza tayi tace “akwai disrespect daya wuce na kariga ka aurota ka kwanta da yar aikina taga kalan buranka dani uwar dakinta keci akwai Eh Nura talk!” Hadiza tai ihuu dayasa Nura ya runtse idanu yabude su ahankali yakalli Aman da Amal daduk ke kallon Maman nasu sunyi tsuru tsuru, dan juyowa kadan Nura yayi yakalli Ummi dake labe abayanshi yace “tafi dakinki” gyadamai kai tayi tawuce Hadiza zatayi kanta Nura yariketa gam, Hadiza tabita da kallo tana duramata ashar tace “munafuka, jibeta kaman bushashen kifin dayay kwantar a kasuwa oporoko, banda ma namiji kanshi kaman kan jarirai ne mezakayi da yarinyar nan mai kama da fiffiken kunkurun dayay shekara dari da uku aduniya eh, makira  zuciyanta yafi fatar jikinta baki, tanaji da lebe kaman wacce ke aiki agidan giy……” “Hadiza!” Nura yayi maganan yana fizgota su Aman suka fashe da kuka Nura yakalli yaran saikuma yasaketa yace “look at yaranki ko breakfast basuyi ba zasuje school kina haukan nan bakisan zaiyi affecting mental health da cognitive development nasu ba” cikin fushi tace “eh bazasuyi breakfast dinba ka gayama yarinyar chan bata ba yarana, kada ta kara dafa musu abinci kota musu wani abu, wlh ko hannunta nagani akan jikin yarana kome namata ita taja and kada ka ta kara shigan mini kitchen” Nura yana wani kallonta yace “kitchen banaki bane, duk wani abu naki na kitchen din nabaki dama ki kwashe ki ciresu daga kitchen din zan sayo wasu nasa cus Ummi will enter this kitchen and cook for me” Nura yakallesu yace “zo kuyi breakfast” rike hannun yaran tayi tace “Nura bari kaji yesterday you took advantage of my fragile state kayi yanda kaga dama dani not anymore, billahillazi Nura zan nuna maka cewa yimini kishiya was the worst mistake daka tabayi arayuwan ka, bakana fadin bakada kwanciyan hankali ba yanzu kafara ganin asalin rashin kwanciyan hankali, muzuba nidakai I will deal with you and deal with that thing daka kawomin gidan nan as matan ka, bakasan ba’a wasa da fire ba because u will get burn, Nura I will treat you f*ck up wallahi kuwa” sosai Nura ke kallon Hadiza but sabida yaran saiyayi shiru yatako har gabanta yaduka yakama Aman da Amal dake kuka looking terrified ya karbe su daga hannunta yace “bani yarana” yajuya zaiyi dinning dasu kafin yaje Hadiza tarigashi zuwa dinning din duka abincin da Ummi takai dinning dan breakfast Hadiza ta kabar, dasauri Nura yaja Aman baya dan yadauki Amal gudun karya kone da ruwan zafi yana kallon Hadiza, ahaukace ta duka ta kwashi lunchbox na yaran da Ummi ta watsar akasa dataji shaka dazu ta bude tana ciro komi tana zZzagewa akasa tace “baza’a aci abincin yar aikin ba, yarana bazasu karacin abincinta ba, nace baza’a ciba, angama cin abinci again, Nura that peace dakace bakasamu dani ba ajikin yar aikina zaka samu wlh, wlh, wlh bazaka sameshi ba, Nura u will never know peace now dakamin kishiya I swear by Allah” sosai Nura ke kallon Hadiza kaman ba itane tagama kuka jiya kaman wacce ke shirin mutuwa ba, baice mata komiba yajuya yakoma falo yazauna yaciro wayanshi yakira school din yaran yace abasu breakfsat da lunch yau daidai motan  school din zuwa, lallashin yaran yayi yadauko juice a fridge yabasu sannan yafita yasasu a school bus sannan yadawo cikin gida Hadiza na tsaye a tsakar falon tarike waist nata tan kallon Nuran.



Baiko kalleta ba yawuce zaiyi stairs tabishi da sauri tana ihu tana surfafa masifa tace “bakaji kunya na ba sabida kaine babban munafukan mazan duniya, Nura the president of MMA! Mugayen Maza Association, zaka kama ka auremini yar aikin dana samo nakawo gidan nan, kabita har kauyensu ka aureta kaje kayi honeymoon da ita batare daka dauki wayana ba for that 2weeks,  shine kanada audacity kazo da daddare ka lallabani kana samin jikinka ajikina jikinka daya hadu dana yar aikina eh Nura? I looked up to you kullum as a role model cus Nadade banga namiji mai hankalin kaba, but I was wrong gaskiyan bature ne dayace a fool at 40 is a fool forever dan tell me why will a sensible, educated wise old man zai kama ya aurowa matarshi yar aikinta? Nura yar aikina ka auromini sabida daidaicewa da wawatsula” uppan Nura baice mataba wardobe nata yabude yadauko kayanshi yawuce yafito daga dakin duk tana binshi yaje dakin Aman ya ijiye komi kan gado yafada bayin yayo wanka yafito yadauki cream din Aman yashafa still surfafa bala’i Hadiza take tsaf yagama yafito yasauka kitchen yaje yadauki babban kulan dake kan Island Hadiza takawo hannunta anan ne Nura yace “idan kikai kuskuren ko gigin taba abincin mahaifiyata Hadiza I will show inda haukanki ya tsaya anan nawa yafara” yana maganan yawuce ta yafita tabiyoshi tace “ai dama nasan kai mahaukaci ne dan mahaukaci kadai zai auroma matarshi yar aiki” fita yayi anan gaban kofa ta tsaya tana kallonshi dan bataso tafita tana fada, estate dinsu da ake ganinta as don aga tana fada, abincin ya ijiye a bayan mota ya kulle motan yadawo cikin gida Hadiza tasake binshi kitchen din yashiga ragowan friend Irish daya gani a pkate da egg yadauka, spoon yadauka yafito Hadiza nabiye dashi tace “ina zaka da abincin nan eh, Nuri ina zaka da abincin nan”? Dakin Ummi yabude yashiga biyoshi Hadiza tayi ciki ga mamakinta Nura just pushed her outside yamaida kofan yarufe yasa key tahau buga kofan da gudu tana ihu. “Nura ni kai pushing outside like that eh? Wlh wlh sainayi maganinka dakai da karuwan nan daka ijiye adaki” kallon Ummi yayi dayagani kwance kan gado kaman marainiya idanunta sunyi ja amman ba kuka takeba zama kusada ita yayi kan gadon yana ijiye abincin agefe murmushi Ummi tamai tace “shine saika kawomin abinci maisa kakemin aik…..” hannu yadaura akan bakinshi  alamun tamai shiru hakan yasa tai shiru yakai hannunshi yadagata wajen window dakin yayi da ita ya yaye window yadaga wuyanta yana dubawa yana tattabawa ganin yadanyi ja yace “dazafi” dasauri ta girgizamai kai tace “ba zafi” yana kallon kwayan idanunta ahankali yace “mesa baki gudu ba dakikaga zata miki wani abu ko kiyi ihu ki kira sunana what it tamiki wani illan?” Murmushi tamai tacire hannunshi daga wuyanta tace “Anty bazata min wani illa ba ba muguwa bace, kawai fushi take sabida mun mata laifi” dan shiru Nura yayi yana kallonta saikuma ahankali yace “Ummi aure ba laifi bane like I said ranan nan ko nan gaba naji ina bukatan wata matan zan iya nakara aure, mata hudu zan iya aura” Ummi na kallonshi tace “Anty na sonka sosai, kuma soyayyan yasa take fushi haka” yana kallon kwayan idanunta yace “kefa?” Murmushi tamai tace “nima ina sonka sosan bala’i, tafashashen so ma nake maka my Noor bai huce ba” yana kallon bakinta yace “Allah yar matata”? Dan dariya tamai tace “da gaske, ba Hajiya zakakai asibiti ba lokacin na tafiya kazo kaje” dan ijiyan zuciya yasauke yace “banso na bar gidan nan ahaka” dasauri Ummi tace “babu abinda zai faru kaje ka kai Hajiya asibiti abincinta na kitchen a flask kadauka” ahankali yana kallonta yace “nadauka” ganin ya tsaya yana kallonta yasa tace “menene?” Yana kallon kwayan idanunta yace “Aman da Amal yaranki ne kada ki rabu dasu sabida Maman su kinji” murmushi tamai tace “tom Baban Aman da Amal” rungumeta yayi ahankali yace “kiyakuri da abubuwan da Hadiza tafada miki kinji, kada ki riketa azuciyanki, kiyakuri Hajiya Ummi” dudda taji wani iri amman tadaure tafita daga jikinshi dasauri tace “komi yawuce katafi” Gyadamata kai yayi yace “biyoni ki rufe kofan da key” biyoshi tayi yace “kiyi breakfast zan dawo yanzun nan” gyadamai kai tayi yabude kofa yafice tasa key dasauri ganin Hadizan na tsaye awajen yawuce Hadiza tasakebin Nuri tana masifa tace “tell this girl ko dakin yarana takara shiga wlh saina watsar da ita, karta kara taba wani abu that belongs to me in this house wucewa Nuri yayi yawuce yashiga motanshi yabar gidan Hadiza ta dawo sama tashiga surfafa zagi na uwa da uba ma Ummi, Ummi tayi shiru.



Tashi Hadiza tayi ganin taki kulata tazo gaban dakin ta bubbuga tace “kifito mana idan ke diyar halas ce yadade da tsufa a inda yatafi yanzu, dagani saike agidan, kifito muyi magana woman to woman mace to mace, cus inada wasu abubuwa dazan fada miki kifito Ummi kibude kofan nan kifito” Hadiza tai dariyan keta tana tafiya tace “dan kauye dan kauye ne, ni wlh at this point ma tausayi kike bani Ummi, bari nafada miki wani sirri dabaki sani ba for free” tasake shiru tace “kinga Uwargidan miji itace kokon rayuwanshi, Ummi bar ganin kin zauna agidan nan kinga nida mijina munada yan matsaloli sai kikai yan dabarun ki na gidahuman kauye kikaja ra’ayinshi ya aureki to tsaya kiji wani abu dabaki sani ba game da mijina Nura”  Hadiza takara murmushi tace “Nura kwata kwata dakikan mata dabasuyi boko ba basa burgeshi kije ki tambaya kiji, Baban Nura professor ne a BUK abinda yadawo dasu kano kenan daga zamfara, Hajiya wannan dakike gani tsohuwan secondary school English teacher ce, kannen Nura kap dukansu graduate ne dasuka gama jami’a har Meena Kwanan nan tagama bautan kasama, kinganni nan Nura bai yarda ya aureni ba saida nagama jami’a gabaki daya muna dawowa garin nan yasa nacigaba da karatun wuce jami’a wato masters sabida dan boko ne shi, yanason yaga matarshi yar gayu yar boko tanuna ma business partners nashi, kinsan mesa nake gayamiki maganganun nan”? Hadiza tasake dariya tace “sabida ke dakikiyace jaka kuma, Nuran dakike gani kin aura yau Nuran daya sami yar karaman matsala da Hadizan shice, kije kano ki tambaya abaki labarin kalan soyayyan damukayi, ban bashi jikina ba damuwa da sha’awa kinsan mutum shiru shiru mara magana yasa yaga kaman yana sonki wlh Ummi kindaiji na rantse miki Nura baya sonki sabida baki cikin kalan ko siffofin matan dayakeso” wani abu Ummi taji ya tsayamata awuya chak yaki wucewa takasa hadiyewa, Hadiza tace “bansan ko kinji magananmu jiyaba, jiya nace yasakeki zan chanza Ummi kinsan meyace mini”? Hadiza tai maganan cikeda tsantsan tunzura mutum saikuma ta kyalkyace da dariya tana tafi tace “wohoho ta yanda zaki gane kin tafka shirme Ummi kin auri mijina kin dauka kin sami gidan mijin cemin yayi nafara chanzawa tukunna yagani, idan na chanza nakoma Hadizata nada zai sakeki ki tafi mucigaba da rayuwanmu mukadai hankali kwance” dasauri Ummi ta tashi daga gadon zuciyanta na rawa tanajin wani iri, Hadiza tace “haka yadinga lallabani har saida ya samu nabashi hakkinshi that means keba komi bace awajenshi ba sati biyu dakukai kuna amarci kaman yanacin kashi haka yaji saida ya kwanta dani jiya yajishi daidai, yajishi damdam yajishi yakoshi, kuma kada ki manta rashin jituwan damuka samu dani da dashi yasa yaje yama nemeki” hawaye Ummi taji sun sauko daga idanunta, Hadiza tace “Ummi ki rubuta ki ijiye kwanan nan Nura zai sake ki kibar gidan nan dan bazai taba hada jini da jakan kauye ba da turenci nan nan bata iyaba wlh saiya sake k…….” Bude kofan Ummi tayi dasauri tafito idanunta sunyi jazur tahada idanu da Hadiza for the first time tunda tadawo gidan tace “Hadiza kinyi kadan ki rabani da Nura” sosai Hadiza ke kallonta ganin idanunta sunyi ja maganan ta shigeta kenan yasa ta taka zuwa gaban Ummi Ummi ta tsaya chak tana kallonta ba gudu ba jada baya, Hadiza namata wani kalan kallo tace “nabaki daganan zuwa sati biyu saikinbar gidan nan dan baki da waje awajen mijina” Ummi na kallonta tace “Hadiza ban auri Nura dan na kuntata miki ba, shiya nemeni da aure na aureshi kuma magana daya zuwa biyu zan fadamiki, nifa nayi miji kuma naga wajen zama, zama kuma daram! Wallahi ko ana hamaza hamata bazan rabu da mijina ba, barima kiji mutuwa kadaice zata iya fitar dani daga rayuwan Nura!” Hannu Hadiza ta daga zata kaima Ummi mari Ummi tarike hannun gam idanunta sunyi masifan ja kirjinta na tafarfasa itama jin ance Nura zai saketa tace “Hadiza kul!” Ummi tazare mata idanu kaman yar daba tace “dazu nariga nabarki kinmin hukunci sabida nasan ban kyautamiki ba na auri mijinki daya nemeni amman yanzu kikai kuskuren dukana Hadiza kin tuna kalan dukan da Meena tamiki”? Ummi tayi maganan tana kallon kwayan idanun Hadiza kaman yanda Hadiza ke kallonta mamaki yagama kasheta, Ummi tace “wlh saina miki dukan dayafi wanda Meena tamiki domin shiru shiru ba hauka bane, dan hakin daka raina shine yafi tsole ido, kul Hadiza! Wallahi kul! Duk abinda zakiyi kiyi but Ummi tariga tayi miji, kuma taga gidan miji, danhaka zama daram, dam, damm ehe! Sai kija please ki rungumi sorry dan haka askus me” ta yarda hannun Hadiza a air tawuce takoma dakinta tarufo kofa tasa key Hadiza tasaki baki mamaki ya cinyeta har zuwa bone marrow, she was like wattt! Ita village girl dinnan tama rashin kunya haka? Askus, askus? Did she just said excuse me as askus me? Sai kawai Hadiza tahau dariyan kuka, she’s laughing so hard and crying so hard as well, ita Nura zai auroma wannan jahilan askus me yar kauyen yarinyan???? Wow lugubrious!!!!!




Mata Mata mata sau nawa nakira mu??? 

Please we should all learn to stop abusing opportunity sabida idan wasu suka sami that opportunity there’s nothing u can do in this world dazaisa su saki that golden opportunity daya shigo musu.


That is what happened between Hadiza and Ummi, Allah yama Hadiza kyautan close to perfect husband but she abuse everything and toss him outside like a coin, Ummi grabbed that coin tace atafau koda za’a guntule hannunta ne she won’t let go off wannan coin din, wazakuyi blaming wacce tai tossing coin din ko wacce grab the coin???


Sainaji daga gareku and always remember shi opportunity sau daya yake zuwa miki.

Allah ya kiyaye and see you’ll Saturday  Fanmily and Askus me❤️


WEEKEND PROMO💃💃


I have special announcement masu son shiga class na MATAN AURE you can all pay 1k now kafin Monday yakoma 2k, registration is still ongoing kafin murufe.

🔊🔊🔊🔊🎊🎊🎊🎊🎊


Don’t miss MATAN AURE dina class for anything, I will give you all!!

Sirri zan baku da dama

Zan koya muku how to love mijinki in your own way kaman yanda Ummi keyi.

Shagwaba, iya magana 🥰

Uwa uba iya kwanciya❤️, yanda ake siyan zuciyan miji, how to steal heart na Inlaws naki and so much more.😍

Idan kina tunanin asiri ko kayan mata ke siyan zuciyan miji come to my group na nuna miki gaskiya.

HAUSA CLASS NE BA TURENCI BA


REGISTRATION IS 1k NOW 


6353995766 M Shakur world Moniepoint

Send ur evidence of payment ta PC zanyi adding naki a group.

click on this link and chat me up directly +2347012181461

No comments