Breaking News

Kyalkyalin Kauna 72



Adamu shi Neman hanyan rabasu yakeyi har abada, soyake Hajiya ta tsaneshi sosai, amman har yanzu makiran matan kaman bakar mayya taki tsananshi shi bai taba ganin irin wannan obsessive love ba kuma bazai taba bari Su dawo ba koda shine last Abu da zaiyi in his life bazai taba bari Hajiya da Pablo Su dawo ba Dan haka maganan boka ko malami wlh bazai bari tayi ba ko ana haa maza haa mata kota mayi  sai yaje ya bata duk inda aka burne wani Abu sai yaje ya hako wlh over his dead body ya bari Su dawo , wannan soyayyan da takema  Pablo so yake ya dawo kanshi, all abubuwan na empire daya barma Su Nas Hajiya ta tattaro komi ta bashi yazama shine ke ruling empire da kuma me empire just like yanda Pablo yayi shima. Da sauri yace "Hajiya akanme zaki wani bata kudi ki nemi malami yanzu baga akikin malamin farkon ya karye ba dudda yayi aiki for years but yanzu ai ya karye dudda ance aikin na har abada ne yaro ya rufe ido ya karta miki  rashin mutunci harda karta miki mari yace bashi bake, ai matsalan shine ko yanzu kinje kinyi wani asirin dole  nan gaba zai karye shima ko shikenan kin dinga yawon zuwa wajen malamai kenan? Besides ma malaman yanzu yan damfara ne babu abinda suka iya ba kaman na da ba irin Wanda ya miki aikin farkon nan at least ta dalilin shi kin rike Maheer kusan shekaru 14yrs kenan ko tunda tun yana 8yrs, but trust me yanzu ko an miki asiri yayi kokari yayi tasiri to 1yr Dan haka kibar zancen nan kawai" yayi shiru cike da makirci ganin Hajiya ta natsu tana kallonshi da alamu bayanin na shiganta yace "Hajiya saurareni kiji, babu abinda yakai kina tareda mutum yana cikin hayyacinshi idan dai shawarata kike nema gwara Pablo ya dawo miki dakanshi da kafanshi cikin hayyacinshi yana kuka yana miki magiya da kururuwa yana rokonki ki maidashi ki daukeshi back wlh yafi da wannan wani bin malaman da zakiyi, ki gwada plan dina kiga shiyafi komai sauri CP kadai zai miki aikin da boka zasuci miliyoyin kudi a hannunki kema kin San Baban yarinyar mashahurin Dan bala'i ne da taurin kai, shine mutumin Dana San kap  duniyan nan zai ladabtar da Pablo kaman yanda shine Dan sanda na farko dayama Pablo abinda ba'a taba mai ba wato kama kayanshi so he can do the work for us ke kawai set the trap mukoma gefe musha kallo" sosai Hajiya ta gamsu da maganan Adamu hakan yasa tasauke ajiyan zuciya taci gaba da typing da sauri sauri, Adamu yazo kusa da ita  yana kallon yanda takeyi yana nuna mata ta gyara nan ta cire chan Dan profile din yayi zafi ta yanda Baba zai ma Maheer mugun kamu na tsana.


Yasmeen yanda taga Maheer wlh saida ta firgita buda  motan  yayi ya shiga dasauri takai hannunta ta dafa kafadanshi ahankali tace "Maheer" zuba mata jajayen idonshi yayi kafin yadauke kanshi ya kunna motan  yaja yanda yake gudu yasa yasmeen ta rungume hannunshi daya dake  hannunta cikin tsantsan lallashi tace " Dan Allah calm down kaji babu abinda ya sameni fa, calm down plsss mijina" ina  Maheer bama yajinta Dan yanada anger issue, dakyar suka kai gida saida yayi jamming motan da gate ya kashe motan kawai ya karbe hannunshi dake hannun Yasmeen ya sauko daga motan daidai maigadi na fitowa jin an daki mota  Maheer yabi gefanshi ya shiga gida yana tafiya kaman zai fadi, bude kofa Yasmeen tayi ta dauki jakanta ta fito maigadi nacewa lafiya Hajiya kota kanshi bata bi ba itama yayi cikin gida dasauri damuwa sosai akan fuskanta, bude parlor tayi  baya  ciki  dasauri tayi  sama ganin kofar dakinshi bai idasa rufewa ba yasa tayi  jimm  tana  kallon kofan ahankali tasa hannunta ta share hawayen daya zubo mata murya can kasa tace "bazan taba barinka cikin kunci ba idan da kayi yanzu kanada  ni  , you are not alone mijina", ajiye jakanta tayi kan kujeran nan parlor sama ta cire hijabinta ta ijiye tajuya da gudu gudu sauri sauri tasauka kasa ta wuce kitchen, freezer ta bude ta debo ice cubes dayawa ta dauki strawberry da water melon da lemon tasa ta yayyanka ta watsa Su a blender da ice din ta dauko  sugar syrup ta zuba Dan tana son juice din yayi zaki choi  Dan zaki na kauda fushi ta nika tadauko wani fine glass cup dogo ta juye  ta yanka lemon tai decorating a gefe ta saka straw tadauke wani small tray ta daura cup din akai ta fito daga kitchen din tai stairs dasauri zuwa gaban dakinshi, ahankali ta tura kofan dayake  bai rufe duka ba kofan ya bude yana kwance kan gado ya dunkule kaman maraya ya lumshe idanunshi dakin duhu hasken falon ma yasa ta iya hangoshi, maida  kofan tayi ta rufe ta taho ahankali haar zuwa bakin gadon tazauna tareda ajiye tray akasa gefen kafanta takai hannunta ahankali tadaura kan hannunshi murya chan kasa tace " Maheer dina" shuru kaman bashi ta kira ba, dudda yanda takejin kuka hana kanta tayi tace "da ina  yarinya anytime nai fushi ko kuma ina  kunci haka Ammi will always call me tabani alewa idan bata bani alewa ba she will make sure tabani wani Abu dakeda zaki, maybe mazankwaila, cingam kokuma ta bani cube na sugar guda daya tace nasha koyaya nake  Fushun nan I promise you zanji na nemi Fushun na rasa, it works like magic" Dan murmushi tayi gently ta saka hannunta cikin hannunshi tarike gam  cikin muryan lallashi sosai tace "nima yau I've made something for my husband sabida  he's angry will you stand up and take it"? Shiru Maheer yayi hakan ya kara taba Yasmeen wani mugun tausayinshi takeji adan  hankali  ta kwanta da fuskanta tasa kan hannunshi ta hura mai iskan bakinta tayi kan hannun  awani kalan hankali  muryanta nadan rawa tace p.......please......" Ta dago tare da jawo hannunshi alamun ya tashi ga mamakinta sai taga yataso ahankali dawani kalan sauri ta dauki cup din daga kan tray din wani kalan matsowa dab dashi tayi Dan har tanajin hucin numfashin dayake mai zafi takai traw din bakinshi tace " I will feed you today na yarda  u are my child oya haaaaaaa" gently Maheer ya bude bakinshi tasamai straw din ya zuka lumshe idanunshi yayi jiyayi sanyi da zaki da tsamin lemon  din duka sun amsa akanshi kaman an watsa kankara saman wuta dakeci sosai haka yaji, kusan Rabin cup ya sha at a go ya zare kanshi yajuya  zai koma ya kwanta dasauri Yasmeen ta rikemai hannu hakan yasa yajuyo ya kalleta girgiza mai kai tayi kafin a ahankali ta juya ta ijiye cup din akasa sannan tajuyo takalleshi gently tashige jikinshi ta rungumeshi ahankali tareda kwantar da kanta saman kirjinshi, cikin bala'in taushi lafazi tace "mijina gagarabadau, jarumin jarumai, namiji mai suna Maheer, babban mutum, kyakkyawa, dogo mai dogon hanci,yaro son kowa kin Wanda ya rasa, rabon  Fateema, burin Fateema, mijina Fateema, faarin cikin Fateema, waya tabamin farin  cikina? Waya batama Dan gatana rai? Waya tabamin abin alfaharina mutumin dashi kadai nake ji nakuma ke gani adoron fadin duniya nan kakap, ranka shi Dade,takawanka lfy, adade anayi sai mai gaskiya, zakaran gwajin dafi, murucin kan dutse, anja  dakai kaci, an fafata dakai kaci akanme jarumina zai bari yanzu Su suci? Su basusan nawa  ba irin Nasu bane  ko so kake  na fita  filin  daga naje  na yakesu eh ranks shi Dade? Sosai Maheer ke kallon fuskan yasmeen barinma bakinta daketa yanko zance dashi bai taba jin yanason Abu kaman yanda yaji yakeson Yasmeen yake kuma kara son yasmeen ba, normally idan yana fushi babu uban  Wanda ya Isa yasa shi magana  wlh amman Yasmeen broke that rule cikin muryanshi da bata fita  sosai yana kallon Yasmeen yace " waya koya miki magana haka?".


No comments