Breaking News

Kyalkyalin Kauna 64

 


EPISODE 4️⃣8️⃣





EPISODE 48




To Jama’a anan nakawo karshen FREE EPISODES na wannan littafin nawa Mai suna KYALKYALIN KAUNA wato SPARKLES OF AFFECTION✨



Wannan aure zai yu kuwa??

Yaya Baba zaiyi idan yagano Maheer shine Pablo Escobar??

Kuna ganin kafin aure ko bayan aure ne Baba zai gano gaskiya???

Hajiya zata taba barin Maheer da Yasmeen suyi zaman aure???

Hmmmm!!! Kubiyoni.


Idan kinason cigaba da karanta littafin nan all you have to do is pay ko 1k or 500 into 3107021073 Aisha Muhammad first bank.


Zakimin magana a WhatsApp wa.me/+7012181461 sainai adding naki a paid group.


Group na 1k is 2updates daily banda alhamis da juma’a.


Group na 500 is 1update daily banda alhamis da juma’a.


And inada EXCLUSIVE shi a Email nake musu update yanzu haka sun wuce ku is 5k.

4episode daily❤️



Please patronize my little work, and appreciate my talent, show me support ta hanyar subscribing ki shiga paid group.



Thank you I love you all❤️


https://vm.tiktok.com/ZM2U8NPMo/

Kusan duka yaran gidan babu wanda yasan akwai wani abu dazai faru yau Baffa dai yasa Baba karami yasayo drinks harda su Maltina da ruwan gora, matan gidan kuma harda Ammi aka hau girki yaran gidan kuma duk suka tafi school, Baba sabida haushi tun 6 yatafi aiki Baffa dai saida yakirashi ya jaddadamai biyu tamai agida, Yasmeen 9 ta tafi school abinta yau har 6 takeda lectures.



Ana idar da sallan juma’a Baba yadawo gida gidan an gyara yay kal kal an shimfida manya manyan tabarmai a compound kasan bishiya girgixa kai kawai yayi yawuce ciki wanka yayi ya shirya cikin babban kaya harda Malum Malum da hula ya fesa turare yafito waje daidai ana sallama Baffa ya kalleshi yace “muje mu shigo dasu” baiyi musu ba suka fita atare, Hamad ne ke tuki sai Maheer agefenshi Maheer yasaka wata faran shadda jumper da hulan Hamad akai wlh kaga Mageer zaka dauka ango ne, Malam Sani da Baba sai limamun anguwan su wanda yake abokin Baba ne sosai, duk suna tsaitsaye Baba yafara fitowa daga gidan kallo daya Maheer yamai yasauke kanshi kasa sabida yanda Baba yamai wani kalan kwarjini a ido gaisawa su Baba sukayi dasu Malam Sani hakan yasa Hamad yataho tareda dan jan Maheer daya kasa motsi Malam Sani yace “surukin naku akwai bala’in kunya, wannan shine yayan shi Hamad” yanuna Hamad dake bama Baffa hannu Baffa yakarba cikeda murmushi yace “ina gajiya” sannan yanuna Maheer da kanshi ke kasa yace “wannan shine Maheer” ahankali Maheer yabama Baba dake kallonshi hannu karban hannun Baba yayi murya chan kasa Maheer yace “ina yini” ba yabo ba fallasa Baba yace “lpy lau” tareda karbe hannunshi, Baffa yace “bismillan ku kushigo” shiga ciki sukayi Ammi dasu Yaya ta window suke lekawa kaman yara dukansu are so excited Ammi tace “waye surukin nawa naga samari biyu” Yaya tai pointing Maheer dake sunnar dakai tace “daga ganin mai kunyan chan shine mai neman Yasmeen” wani kalan murmushi Ammi tayi tace “surukina badai kyau ba kaman bakin balarabe Masha Allah tubarkallah” shewa sukayi, jin Baffa na kwala musu kira yasa duk suka saka hijaban su suka daddauki su drinks da ruwan gora suka fita dashi, anatse Baffa yace “ga iyayen Fateema nan” gaggaishe su sukayi Maheer yakasa dagokai suka wuce suka koma daki sannan Baffa yace “to bismillan ku”.


Gyaran murya Baba Makaho yayi yace “to godiya ya tabbata ga Allah ubangiji daya hallice mu ya raya mu sa’an nan ya nuna mana wannan rana, dafarko dai sunana Alhaji Maheer Makaho, haka aka haifeni da makanta, gaskiya dana taso iyayena basu da shi ahaka ahaka dai nasamu wata makauniya irina marigayiyi mukai aure Allah yamata rasuwa yanzu” atare kowa yace “Allah gafarta mata” ahankali yace “Ameen” sannan yace “bazan muku karyaba dalilin d’ana ne nazo gidan nan yau, yarana biyu da Hamad wanda shi likita ne saikuma Maheer pharmacy yakaranta amman bai sami aiki dashi ba Allah yabashi aikin koyarwa english kaman yanda nafadi, banda shi duka yaran nan nawa da scholarship sukai karatu akasan waje Alhamdulillah” Baba yasakeyin shiru kafin chan yace “yaran nan yarane dasuka taso na koya musu ladabi biyayya natsuwa da bin Allah ma’aiki, Maheer yasameni da maganan yaga wata daliba a makaranta sunanta Fateema yanaso soyayya irin ta aure bawai soyayyan da akeyi a zamanin nan ba, saidai yabukace ni dana fara ganawa da iyayenta amai izini yanemeta tukunna dan bai dace yatari yarinya a school yana mata magana ba karatu tazo yi a school ba soyayya ba” jinjina kai Baffa yayi maganan na shiganshi, cikeda dattaku Baba yace “to gani ga babban aminina da yarana gakuma Liman shima aminina ne kuma zai iya wakiltata ako’ina munzo mu nemama danmu iznin neman auren diyarku idan babu kowa, idan suka daidaita nan bada jimawa ba ayi aure da izinin Allah to mekuka ce”? Shifa Baffa yasan halin kaninshi to bazai taba bari yakori mutanen arziki da mutunci haka bane dake neman Yasmeen ba, anatse Baffa yay gyaran murya yace “a gaskiya naji dadin wanna halin karamcin irin naku da sannin amfanin iyaye, sannan babu wani wanda ke neman aure Yasmeen wato Fateema dan haka nabashi izinin nemanta idan har komi ya daidaita saimu hada bikinsu taredana yayarta Sa’adatu da za’ayi nan da wata daya In sha Allahu” murmushi kowa yayi ana Alhamdulillah, Baba da tunda suka zauna Maheer yake kallo atsanake yace “Fateema is AS genotype dinta, menene genotype dinka”? Kowa bin Baba yayi da kallo Baffa kaman ya make Baba dan baisan what’s all this ba yanzu aka fara magana za’azo kan genotype nan gaba, dan dagokai Maheer yayi yakalli Baba kafin ya sunnar da kanshi kasa dasauri, cikeda kamala yace “ni AA ne Abba” hamdala Baffa yayi hakanan yaji yanason Maheer wlh dan yaron ga kunya ga sanyi ga rashin magana, daukansu Baba bazaice komiba yace “I need general blood test naka from a well known hospital saikuma” yadanyi shiru bai damu da yanda kowa ke kallonshi ba Baba yace “ban yarda ka taremini yarinya a titi ko a school ba ban yarda ba, Fateema karatu nakeso tayi banson tai loosing focus, ranan lahadi zan iya baka kadinga zuwa har nan daki a falon mahaifiyarta ka ganta kuyi magana na tsawon awa daya” gyadamai kai Maheer yayi ahankali, Baba yace “banson yawan kira, kira once in a day ya isa” sake gyadamai yayi” Baba zai kara magana Baffa yatareshi da sauri ta hanyar cewa “to Masha Allah, yanzu dai in sha Allahu tunda yau juma’a ranan lahadi saiyazo shida yarinya su zanta zamu kira yarinyar mu tambayeta idan tai na’am dashi zamu danyi yan binciken mu kafin mukiraku mu sanar daku kuzo asa rana da izinin Allah” dasauri Baba yace “zata cigaba da karatu” wannan karan Baba Makaho bai bari Maheer ya amsaba dan kafin yay magana yace “In sha Allah ai ilimi gatan bawa ne, ilim adon diya mace Fateema  zata cigaba da karatu harsaitaji ya isheta” Baba zai kara magana Baffa yace “to bismillan ku muci abinci” badan Baba yaso ba ya kalli Baffa sannan yadauke kai.


Sosai su Baba Makaho suka saki jiki sukaci abinci Hamad ma vaci dan abincin gidan dadi Maheer nedai vakasaci sai wasa yake da spoon har aka gama, gaggaisawa akayi Baffa bai kara bama Baba room to talk ba suka shishigayin sallama Baffa na karban nambobin wayansu dakuma adreshin gidansu, sannan Baffa yakalli Maheer daketa sussunar dakai yace "muna jiranka ranan lahadi" gyadamai kai ahankali Maheer yayi sannan suka fiffice suka tafi.Koda suka dawo gida Baffa bai karabi takan Baba ba, Baba yatafi office kawai dan baiso abinda Baffa yamaiba kawai babu yanda ya iyane dan bazai iya ja dashi ba.6 dot suka fito daga lectures fitowa tayi daga class ga mamakinta Baba tagani gaban ajinsu yana kallonta kuri, ahankali tace "Baba, ina yini" dan murmushi yasakin mata yasa hannu yakarbi jakan nata tareda kama hannunta kaman yar yarinya yace "mutafi" awani kalan kunyace ta gyadamai kai tareda binshi har zuwa inda yay parking sai kallonsu ake, budemata mota yayi tashiga ta zauna yasamata jakan ajiki yarufe yazagaya ta dayan side din yazauna yaja motan, sundanyi nisa suna tafiya kaman daga sama yace "wani yataba miki magana a school din nan kan soyayya"?

Dasauri takalli Baba gain hankalin shi nakan tuki vasa ahankali tace "a'a Baba" bai karace mata komiba agaban wani shagon abubuwan Habib yoghurt ya tsaya fita yayi yace "kijirani" kusan 13k ya kashe a shagon ya damo fura dayawa for kowa na gidan Nana kadai yasayama zallan yoghurt dan ita bata iyashan yoghurt mai hade da furaba har yanzu sannan yadauko ledan yazo yabude motan yabama Yasmeen karba tayi yamaida kofan yarufe yazagayo yashiga yatada motan suka wuce gida suna kaiwa bai shiga gida ba yawuce mosque dan anfara salla a masallaci itakuma Yasmeen tawuce cikin gida, babu kowa a tsakar compound dan kowa na daki yana salla sallama tayi ta shiga dakin Ammi daidai Ammi na sallame Salla Nana agefenta jiye ledan yoghurt din tayi gaban Ammi tareda zare hijabin ta yar akasa ta kwanta tadaura kanta kan kafan Ammi dakekan dadduma tace "wasshhh Ammi nagaji wh, Nana kawomini abinci na naci" tashi Nana tai dasauri ta wuce tafita dan zuwa dakinsu tadauko kulan abincin Yasmeen fuskan Yasmeen Ammi tashafa tace "yau wasu mutane sunzo neman aurenki" wani kalan faduwa gaban Yasmeen yayi dasauri takalli fuskan Ammi tareda tashi zaune kirjinta nawani kalan rawa, dan dariya kadan Ammi tayi tace "to matsoraciya relax Babanki yagansu yace yaron yazo yaganki jibi lahadi, saikin ganshi kafin ayanke decision kinji" gyadama Ammi kai tayi ahankali daidai

Nana tashigo da kulan tace "Anty

Yasmeen gashi" karba tayi ahankali itama tajawo ledan yoghurt din tace "Baba yasayo mana fura" karba Ammi tayi ta shiga rarrabawa adaddafe Yasmeen taci abincinta duk yunwan datakeji kasaci tayi sosai takarbi fitan ta tafita daga dakin zuwa dakinsu ijiye komi tayi tafita tayi alwala tadawo salla tayi sanan tajuyo takalli su Sa'a da tunda tashigo suke kuskus ganin taki tajuyo yasa suka kwashe da dariya Sa'a tace "wayaga Yasmeen amarya, ni wl naji dadi sosai Allah sa ahada bikinmu tare" wani mugun harara Yasmeen tamata baki tabude zatai magana sai kuka baki daga Farida har Sa'a suka saki baki suna kallonta yanda hawaye ke sauko mata tana kai bayan hannu tana gogewa da sauri sunki tsayawa dudda ba kuka take da karfi ba, Farida dasauri ta rarrafo zuwa wajenta kaman itane babba ahankali cikeda so tace "Anty Yasmeen bakiso kiyi aure kibar gidan nan saisa kike kuka"?

Gyadamata kai Yasmeen tayi ahankali dan bazata taba iya fadin abinda ke damunta ba dasauri Farida ta rungumeta tace "kidena kuka please kinji Anty

Yasmeen babu inda zaki nima banso kibarni wazai dinga dafa mana indomie da abinci mai dadi, wazai dinga kawomana su cake da zobo daga shago eh" itama Farida tahau kuka, tsaki Sa'a tasaki tace "wIh kunci kun koshi ne van iska to dan kuji dukanku har Nana saitayi aure wata rana tabar gidan nan" sake rushewa da kuka sukayi daga Yasmeen har Farida babu mai lallashin wani hakan yasa Sa'a tamike tace "wlh bani zakusa a trouble ba dan Baba yashigo yaganku kuna kuka kunga tafiyata wajen baabata' ficewa tayi daga dakin abinta, da kyar Farida tai shiru sannan tadago kanta fuskanta ta share tass sannan takalli

Yasmeen dake kuka, hannunta takai kan fuskanta ta sharemata hawayen tass tace"kidaina kuka, ba ance ran Sunday zaizo ba tunda bakison Auren saiki fadama Baba kinji" Gyadamata kai Yasmeen tayi ahankali, Farida tace "tashi to muyi salla idan mun idar saikiyi raka'a biyu ta istikhara ki nemi zabin Allah" batai musu ba tashi tayi suka fice sukayi alwala sukai isha'i sannan tayi istikhara abinta tagama takwanta kan dadduma tai shiru tunani yamata yawa, she's thinking of Maheer kaman ba gobe, koyaya tai numfashi shine kawai takeji azuciyanta, she's afraid of him, tana tunanin yanda zata aureshi bayan tasan criminal ne, tana tunanin abinda Zaima su Baba da duka yan gidansu idan tafadi dan tasan zai iya tunda har ya iya kidnapping dinsu duka, yasan makarantan su yasan ajinta yasan wajen aikinta yasan number a number ta daga yan gidansu sai Maman Intee kedashi ya

akayi yasamu oho yasan gidansu ta

tsinke da lamarin shi yanda yace zai

kashe su baba zai iva data zama sanadin

da iyayenta zasu mutu gwara tazama

sanadin dazasu rayu all abinda tasani

shine idan har akeai next life bazata taba

bari Baba yazama police ba infact she

hates the job sabida kana haduwa da

criminals daban daban dazasu addabeka

da family ka gashi yanzu she's the only one day can save Baba da duka yan

gidansu, all this aside shi Maheer din ko

Pablo nema oho akwai wani iri datakeji

azuciyanta gane dashi first of all tanason

yanda yake kamshi bata tabajin kamshin

turare aduniya kai dadin nashi ba,

saikuma yanada bala'in kyau saisa

bataso tana kallonshi bata taba ganin

namiji Mai kalan kyanshi ba, manyan

idanunshi, digon hancinshi, bakinshi da

pink lips nashi, bakin cikakken giranshi

da gashin kanshi dana saje bala'in mata

kyau suke, tsayinshi na burgeta sosai,

saikuma everything about yanda yake magana da yanda yake share mutum da

yanda yake daukan lokaci kafin yabada

amsa da kuma muryanshi ita bama zata

iva lissafawa ba komi nashi na mutuwan

burgeta kara wayanta yayi dasauri

tabude idanubta lallabawa tayi ta mike

dagakan dadduma tawuce wajen jakanta

data rataye tabude taciro wayanta

message taga tanada shi dasauri tashiga bude messege din gain daga bakuwar number ne, wani kalan ijiyan zuciya ta sauke takara natsuwa kafin ta kalli sakon tana kara bude manvan idanunta danta karanta da kyau.

"Sw..." tadanyi shiru Farida dake rubutu akasa tana kwafe note tace "me kike kokarin karantawa nazo na karanta miki"?

For the first time in her entire life tai rejecting akaranta mata abu dasauri tace

"'a" kwanciya tayi da gudu kan gado taja bargo tarufe har kanta Farida takalleta saikuma tai murmushi tacigaba da rubutunta.

E3

Daga wayan Yasmeen tayi cikin bargo tana kallon sakon ahankali sabida kar muryanta yafito ma sosai tace "Swe.. saikuma dasauri tace "sweet! Eh sweet ne" kafin ta kalli next kalman tace

"d…..

....dr..." dasauri tace "dreams" ahankali tace "sweet dreams. MM" wani sweet smile tasaki ta manna hancinta kan wayan akunyace mistakenly tai dialing number kawai duu duuu taji alamun ringing, dawani irin sauri tazare wayan dagakan fuskanta ahaukace ta yaye bargon tafito tace "Wayyoo Allah" tashiga daddanna call din tana katse kiran Farida tasaki baki tana kallonta, wurgar wayan tayi chan gefe bayan takatse kaman ta fashe da kuka, daidai kira na shigowa wayan zaro idanu tayi kaman zasu fado kasa. Maheer dake kan couch adakin Hamad ne yadan lumshe idanu kafin yasaci kallon Hamad dake gefenshi yana aiki a system, tashi yayi ahankali yazura slippers yawuce yafita daga dakin Hamad yabishi da kallo kafin ahankali yace "munafikin miskili kawai your MM doesn't just stand for Maheer Maheer, harda Munafikin Miskili" last room din dake corridor Maheer yawuce yashiga, dakin a gyare tsaf kashe wutan akin yayi ya kunna AC dakin yawuce yahau kan gadon ya kwanta daidai Yasmeen nacewa "Hello, waye"? Ita adole so take ta nunamai bata gane waye ba, dan murmushi yasaki kadan kafin cikin wani soft calm voice yace "idanunki ne" dudda yadan gaban Yasmeen ke dari dari amman saida maganan yasa tasaki dan murmushi tana kara satan kallon Farida dake rubutun ta abinta taga ko tana kallonta, murguda baki tayi cikin murya yar karama chan kasa ta yanda ko Farida dake dakin barataji metake cewa ba tace

"me kake kirana ni"? Dan murmushi kadan Maheer yayi jin vanda takemai tsiwa cikeda son shima yakara tunzurata yace "ai ke kika kirani" jitayi kaman zata nitse akasa takasa magana, murya chan kasa yace "why are you feeling bad?" Dan shiru yayi kafin cikin murya mai bala'in dadi yace "zaki iya kirana anytime afterall very soon zan zama mitinki" hararanshi tayi kaman yana gabanta cikeda kulewa tace "ni bazan aureka ba"

"nikuma zan aureki Fateema!" Faduwa

gabanta yayi sosai tarasa mesa duk idan

yakirata sai gabanta yafadi hakan yasa

takasa magana hawaye ya fito daga

idanunta dasauri tasharesu da bayan

hannu. "Mesaki kuka yanzu"? Yay

tambayan ahankali bin dakin tayi da kallo ko yasa camera ne yake ganinta dasauri

tace "kasa camera ne adakin muma

yanzu?" Dan murmushi kadan yayi yace

"idan naso zan iva sawa but no bansa

ba" adan hankali tace "to ya kayi kasan

ina kuka"? Shiru yayi baice komiba

harsaida tacire wayan daga kunnenta

takalli screen di ganin yanakai still yasa

ta maida wayan kunnnenta tace "hello"

cikin tattausiyan mura batare daya amsa

hellon taba yace "my soul is connected

to yours saisa nasan u were crying" shiru

tayi batasake cewa komiba, murya chan

kasa yace "ina mai kukan nan kaman ke

Nana Aisha?" At this point tafara tunani

mavbe aliani ne mutumin nan vasan duka

sunansu na gaskiya, shiru tayi saikuma

tace "meruwanka da ita" murya chan kasa yace "she's now my sister in law,

itada Farida da Sa'adatu, Fateema kuma

itace matata" shiru kawai tayi tana

saurarinshi tana lumshe idanu wh kaman

karya daina magana muryanshi dadi

sosai, turo baki tayi tace "nidai saida

safe" cikin dan kakkausan murya babu

alamun wasa yace "nasallameki ne"? ahankali tace "a'a" dan shiru yayi kusan

1min baice komiba ahankali vace "have u had ur dinner?" Ahankali tace "eh"

"mekikaci"?Kwanciya tayi ahankali daidai zata bada amsan taji muryan Baba yana magana da

Baffa zai shigo dakin atsorace tace

"Baba yazo bye" tura wayan karkashin pillow tayi ta runtse idanunta tai lamo daidai Baba yay sallama yashigo Farida tace "Baba sannu da zuwa" karasawa gaban Farida yayi yace "yauwa Farida ya akayi bakiyi note a school ba" adan tsorace gain yanda ya kafeta da ido tace "Baba kaine na ciwo ne lokacin a class" dan sassauta mura yayi yace

"dakika dawo kin fadama Mamanki kanki na ciwo kinsha magani"? Gyadamai kai tayi ahankali tace "nasha" hannunshi yakai yataba goshinta kafin yakai wuyanta jin ba zafi yace "idan yasake damunki gobe lemme know zan kaiku hospital kiga Dr" anatse tace "to Baba" tashi yayi yakalli Yasmeen datai lamo itama Farida faduwa gabanta yake dan kada yakamata karasawa gaban gadon yayi yakalleta ganin kaman tai nisa abacci yasa yajuyo yakalli Farida yace "Ina Sa'adatu"? "Tana wajen Yaya" Gyadamata kai Baba yay cikeda gamsuwa Yasmeen yakara kallo yabi dakin da kallo kaman nai neman wani abu sannan yajuya yafita yace "saida safe kiyi addu'a kafin ki kwanta" "to Baba" Farida Farida tafadi ahankali tareda sauke jjiyan zuciya ganin yafita takalli Yasmeen tace "Allah yasoki bai kamaki kina waya ba hope dai kin katse wayan"? Dasauri Yasmeen tasa hannu taciro wayan daga kasan pillow ga mamakinta Maheer nakan layin dasauri takai wayan kan kunnenta tace "daman ban kasheba kai mesa baka kasheba" ahankali yace "ban sallameki ba" "to me kakeso?" Yasmeen tai maganan tana kallon kofan su jin antaba gain Sa'a ne tashigo yasa tasauke ijiyan zuciya, jin shiru baice komiba yasa ta turo baki cikin kunkunai tace "ni zanyi bacci" almost 10secs baice komiba kafin chan yace

"bakida kunya ko" dan dariya kadan tayi mara sauti tace "toka barni na kwanta baccin" yanda taja baccin saida yaji aranshi, anatse yasauke ijiyan zuciya cikin tattausan murya yace "good night Fateema" kasa magana tayi tai shiru tama rasa takamaimen metakeji danji tayi inama baice good night ba, anatse yace

"zanzo ranan Sunday by 3, 4 zan tafi" cikeda tsiwa tace "karka sake kazo gidan mu ni, kuma bara'a aureka ba din, bye"

dip ta katse wayan.


Ta tura wayan karkashin pillow dasauri tareda lumshe idanu wh batasan mesa ba bala'in dadin wayan dasukeyi takeji har aranta itadai tabani meke damunta ne haka, fuskanshi tafara gani ahaka daga baya bacci yay awon gaba da ita. Yau tunda ta tashi gabanta faduwa yake ita tunda take bata taba shiga irin wannan vanayin arayuwanta ba, wani bangare na zucianta na toron mutumin nan da shakkan shi sabida tasan criminal ne, koba komai ya gwada mata kadan daga halinshi, wani bangare na zucianta najin wani iri game dashi tun ranan Friday dasukai waya basu kara ba sotake yasake kiranta suyi magana taji muryanshi, tabude message nashi takaranta yafi sai dari na Sweet dreams din nan, tabude number shi takalla harta haddace akanta tsabagen yanda take tunaninshi she's just dying to hear from him, kewanashi infact babu abinda bamataji game dashi, wani bangaren na zucianta bayaso yazo gidansu yau amman har kasan ranta wh wl takosa taganshi, tarasa mezatai tunani to idan yazo su Farida suka ganeshi fa suka fadi koda yake Farida tace ita bata iya ta kalli fuskanshi ba Nana wannan daman

kuka take batasan shi ba

harsuka dawo daga hadda wuraren 1 tarasa meke mata dadi mix feeling takeji sosai daman gashi sunyi test

bata iya tayi komiba. Wuraren 1 aka bude labulen kofanta dasauri ta dago kanta Baba tagani yana sanye da manyan kaya dasauri ta tashi ta zauna tana jawo dankwalinta dan rufe kanta, Baba dake kallonta ganin tamai wani iri yace "kinyi salla"?

Gyadamai kai tayi ahankali, Baba dake kallonta ganin duktai wani iri yace

"baki da lafiva ne?" Baki tabude zatai magana saiga hawaye sharrr sun zubo dasauri Baba yasaki labulen yawuce yashiga dakin, abakin gadon su yazauna yana kallonta baice komiba itama kallonshi tayi kaman tafadamai abun da ya tsayamata awuya amman bazata ivaba batason tazama sanadin dazaisa akashe mata iyaye hannayenta kawai tadaura kan fuskanta tafashe da kuka sosai, Baba yakai cikakken 1min yana kallonta bai hanata kuka ba chan yace "Yasmeen" cikin kuka tace "naam Baba" hannunshi yakai saman fuskanta yazare hannayen taredakai bayan hannunshi yashare fuskanta tsaf yace "meke damunki"? Dan yasan kukan damuwa takeyi bana ciwo ba, vanda Baba ya tsareta da ido yasa ahankali cikin murya Mai balain rauni tace

"muni test a hadda ko daya ban iyaba

Baba, zasu karamin repeating ko halama nan gaba Nana tazo tafini aji, Baba maisa banda ilimi maisa har yanzu bana iya rubuta kowani kalan baki, nasan amsan tambayan but ban iya narubuta ba banda kokar...."

" kuka vakaracin kartinta dasauri

Baba yasata ajikinshi kankameshi tavi bayanta ya bubbuga yace "shiti kada ki kara cewa bakida kokari, kinada kokari kini bari akwai wata Malama da akamin maganan ta zan daukota tadinga zuwa gida tana miki all abubuwan kinji now stop crying" kara sosuwa zuciyanta yayi all Baba ever did was to support her daidai da sau daya Baba baitaba complaining cewa batada kokari ba dudda kowa na gidan nan yayi, baya gajiya da nema mata ilimi, baya gajiya da sata a makaranta daban daban, tayaya itama yanzu lokaci yayi bazatama mahaifinta hallaci ba, ta ceceshi koda mutuwa zatayi ta hanyar haka daya taba iyayenta gwara ta aureshin kome zaiyi yayi da ita idanma kasheni zaiyi yayi amman ya kale Baba yasa adaina binshi ya kyale yan uwanta. Sallama Ammi tayi tashigo ganin Baba dakin saida abin yabata mamaki baki tasaki tana kallon Yasmeen dataga idanunta sunyi ja dasauri itama tazo wajen tace "Yasmeen meya sameki"?

Takai hannunta tana cirota daga jikin

Baba, ahankali tace "muni test ban rubuta komi ba Ammi" Ammi jitayi zuciyanta ya sos dasauri ta rungumeta tana kallon fuskan Baba dake kallonta tace "stop crying a karatu the most important thing shine kanka yarike and Alhamdulillah kanki yarike was dan haka ki barma Allah komi watarana sai labari kinji saisa gara kiyi aurenki kihuta da wannan bakar wahalan dakike a makarantu" wani mugun harara Baba yama Ammi itama ta maida mishi hararan back, tashi yay yakalli Ammi yace "nafita idan yaron yazo kada yawuce awa daya agidana dan haka ku kiyaye" yay maganan da kakkausan murya yawuce yafice Ammi tabishi da kallo baki sake kafin tasauke jiyan zuciya tace "kaji dashi" tadago Yasmeen tace "ke dalla chan yau saurayinki zaizo duk kinbi kin kuka jibi idanunki, tashi kije kiyi wanka kizo dakina ina jiranki" makema Ammi wuya tayi cikin muryanta dakeda gobe na kuka tace "ni bazanyi wanka ba" haba Ammi takama tace "au yau shagwaban yatashi ne ahhh lallai Aiko mangareki zanyi anan niba Babanki bane dazai tsaya lallashinki ba, tashi muje ma abayin nawa zaki wanka" badan taso ba Ammi ta tasata agaba suka tafi dakinta wanka tasata tayi sannan tafito mata dawata sabuwar atampa superwax gal wanda na salla Baba ya dinka musu dan dazaran yasami kudi yake abubuwa da wuri duk a ijiye, kayan Ammi tanuna mata tace

"imaza saka kizo kigani" Ammi tasauke wani babban akwatinta tunna aure taciro wani gyale chantily milk sabo a leda tace

"kinga tsaraban gyalen da makociyar mu

Hajiya Mariya tabani yau ga amfaninshi"

Yasmeen dake jan zip na skirt din datasaka takalli Ammi cikeda rigima tace

"waye zai da gyale Ammi"? Hararanta Ammi tayi tace "wale tunda kaina nake cirowa gyalen" kaman Yasmeen zatai kuka tace "Ammi ni hiabi zan saka" akwatin Ammi tadauka tamaida sama tace "uku saura kwata fa kike shirmen nan wh Yasmeen nadade banga fitinanniyan yarinya irinki ba bari kiga naje nakira miki Sa'adatu da Farida" juyawa Ammi tayi tafita dakin Yaya tawuce Sa'adatu na zaune da Farida afalon da Yaya da Hajjo suna hira shigowa Ammi tayi ciki tace "Yaya yarinyar chan na sani ciwon kai wh, Sa'a keda Farida kuje ku mata kwalliya naciro mata gyale dan gidansu shi zata saka" tashi sukayi suka fita da sauri Yaya tace

"ai Yasmeen ni bantaba gani yarinya baiwar Allah irinta ba, Allah dai ya tabbatar da Alhairi" atare duk sukace Ameen. Yasmeen duk yanda take rigima bataso bataso saida Sa'a tamata kwalliya

53|

lafiyayye mai kyau tasamata jan baki tamata dauri daya fito da jelan gashinta ta daurin yay wani kyau Sa'a ta yafamata gyalen awuya daidai nan aka sallama cewa yazo Yayacw ta leko tace "ace yashigo" tunda Yasmeen taji haka gabanta ke faduwa sosai da Sa'a da

Farida suka kwashe da dariya Sa'a tace

"wlh yanda kikeyi kaman wata amarya

Yasmeen that means randa zaa kaiki gidan miji ba karamin kuka zakiyi ba" daidai nan Maheer yashigo cikin gidan, yana sanye dawata milk yadi anmai dinkin jumper dayamai kyau ga hula akanshi Ya Allah! Zaka dauka wani kalan angon e tundaga gate kamshin shi yacika ko'ina Farida ne tafito daga dakinsu takalleshi yana tsaye wajen gate aranta tace wow wanna kyakkyawan ne mutumin Innalillahi karasawa tayi har inda yake akunyace tace "ina yini Yayan mu"

Maheer yadade yana kallon Faridan, she's just like Yasmeen amman Yasmeen tafita kyau nesa ba kusa ba, murmushi yasakin mata mai sanyaya zuciya yace

"Anty Faridan mu" wani kalan kashe

Farida yayi da dadi tace "zo muje na

Kaika daki ance kashigo" anatse yace

"ok" tana tafiya yana biveda ita abayin gidan tsaf tsaf dudda ba gidan masu kudi ba amman ko datti daya bai gani ba, dakin Ammi tashiga tajuyo takalleshi tace

"bismillah" cikin dakin ya kalla kafin anatse yace "Assalamu Alaykum" yashiga ciki Farida ta amsa kuiera tanunamai tace

"kazauna wata one sitter yazauna akai sannan tashiga ciki cikin whispering tace

"Innalillahi Ya Sa'a kinga yanda saurayin

Anty Yasmeen keda kyau kuwa kuje ku gaishe shi bari naje dakin Yaya na kwasomai ruwa" fitowa falon tayi akunyace yawuce tafita Sa'a takalli

Yasmeen dava zauna tai kuri kaman jira take ace kule tafashe da kuka tace

"tashi muje" makemata kafada tayi hakan yasa Sa'a tace "wh zanje nagayama

Ammi" dasauri ta mike tsaye hannayenta narawa har saida Sa'a ta lura hakan yasa yakama hannunta tajawota suka fito, tunda suka fito Maheer yadaura idanunshi kan Yasmeen da kanta ke kasa har suka shigo cikin falon Sa'a ta zaunar da ita kan 1sitter dake facing Maheer sannan tajuyo takalli Maheer akunyace itama tace "ina yini" dan murmushi yamata yace "Yaya Sa'adatu ina yini" wani kalan dadi Sa'a taji akunyace tace

"sannu da zuwa bari naje" Gyadamata kai yayi tajuya tafita daidai lokacin Farida na shigowa da wani hadadden tray da kayan kwalama ke kai taba zuwa wani stool tajawo tadaura akai sannan itama tafice daga dakin bayan tasaci kallon Yasmeen da kanta ke kasa sai wasa da gyalen jikinta take.

Kusan 20min dukansu suna zaune adakin babu wanda yay magana acikinsu.


For the first time in those 20'min yajaye idanunshi daga kanta yakalli tray da aka kawomai zobo ne mai sanyi a jug da cup sai dambun nama da cincin dago kanshi yayi yakalleta ahankali yace "zoki zubamin drink nasha" kaman bazata dago kanta ba ahankali tadago kanta takalleshi suka hada idanu for the first time tunda yazo faduwa gabanta yayi sosai so take ta dauke idanunta amman ina takasa yay locking eye contact nasu strictly yamata pointing abin gabanshi da yatsa alamun tazo ta zubamai, bataso tayi bamataso ta tashi daga inda take amman takasa musu tashi tayi ahankali tamike tsaye tana jajjan gyalen jikinta tana lullube ko'ina najikinta sabida vanda yake mata lafiyayyen kallo ko kunya bayaji saikace baitaba ganinta babu hijabi babu mayafi bama, karasowa gabanshi tayi ahankali ta tsugunna taki kallonshi jug din tadauka duk yana kallonta ta tsiyayamai zobo a glass cup sannan ta jiye juice din tadauki cup din ahankali tadan dago kanta kaman mai tsoron kallonshi tamikamai hada idanu sukayi dasauri tadauke kai murya chan kasa tace "ka amsa hannuna yagaji". Dan murmushi kadan yasaki yana kallonta kaman yau yafara ganinta he just wants to understand dalilin dayasa tunda yasan yarinyar nan yarasa peace of mind he's just chasing after her, for how many years now baitaba abandoning sana'an shi ba but sabida yarinyar nan yabar komi tsabagen yanda take kanshi yazo in disguise zai aureta, what kind of charm tamai?

What kind of black magic? He just hope idan ya aureta zai dainajin abinda yakeji yacigaba da rayuwanshi. "Ni kadaina kallona" tafadi tana dauke kai tana kallon gefe, dan kunya yaji baice komi ba yasa hannunshi yadaura kan kan nata yahada hannunta da cup din tare batare dava karbi cup din ba yarike wani kalan zabura Yasmeen tayi sabida shocking din dataji dabadan yarike hannun nata da cup din da kyau ba data zubar da kofin da zobon, kallonshi tayi tana zaro idanu takalli kofa gudun kar wani yashigo kaman zatai kuka tana kallon kofa tace "ka sakeni pls kar wani yashigo dan Allah, dan Allah kaji" "to kalleni" juyoda idanunta tayi tazubamai su dasukaji kwalli dan lumshe idanu yay yabudesu murya chan kasan makoshi yace "why are you so beautiful Fateema"? Ya tambayeta cikin cool husky voice dayasa gabanta yafadi itama ta tsareshi da idanu takasa magana, murya chan kasa yace "I want u to be smiling sabida kowa yadauka kina sona and also" tasake zaro idanu tana kallonshi kara make murya yayi yace

"idan an tambayeki kan aurenmu kice yes" Gyadamai kai tayi da sauri tace "toka saken mini hannun" gently yasaki hannunta tareda karbe glass cup din Gyadamai kai tayi da sauri tace "toka saken mini hannun" gently yasaki hannunta tareda karbe glass cup din  dasauri tajuya takoma tazauna yabita da kallo everything about her is just too perfect, tamai kyau bana wasa ba kaman ba itaba everything about the outfit looks fabulous ajikinta, zama tayi daidai lokacin aka fara kiran sallan la'asar 3:45 dasauri takalleshi hada idanu sukayi yana rikeda cup na zobon data bashi dauke kanta tavi da sauri tareda ballamai harara tadan turo baki tace "kazo katafi Baba yace awa daya zakayi" dagakai yayi yakalli agogon dakin yace

"ban cinye time dina ba" juyowa tayi dasauri takalleshi gain baya tsoron Baba kaman ma Baba baya lissafi shi daidai

E3 lokacin Nanah tashigo dakin tana

kallonsu faduwa gaban Yasmeen yayi kar

Nana taganeshi murmushi Nana tayi tana kallon Maheer dan murmushi Maheer yasakin mata da sauri tai wajenshi zata shige jikinshi tace "Uncle" dan firgita kadan Maheer yayi dahar saida Yasmeen dake kallonsu ta lura, murmushi yama Nanah yace "how you"? Washe mai baki tayi tana kallonshi tace "Uncle kanada kyau sosai" murmushi shima yamata ganin yanda take kallonshi kaman tanaso ya dauketa ne yasa yakai hannu cikin aljihunshi yaciro dubu daya sabuwa fil yamika mata yace "gashi jeki sayi minti" dan kallon Yasmeen Nana tayi yace

"karbi kayanki kada ki kalli Anty Yasmeen" Aiko dasauri Nana ta karba tana murmushi tace "Allah amfana

Uncle" tajuva tafice daga dakin, mikewa tsaye yayi ahankali yakalli Yasmeen sannan yafara tafiya jin takunshi

Yasmeen take har zucivanta dasauri tamike tsave tana wasa da kasan gyalenta, wuceta yayi ya tsaya waien kofa yace "jeki gayama Ammi zan tafi" gyadamai kai tayi yafita daga dakin itama tafito ko kadan batasan yana wajen kofan ba saura kadan tafadi vatareta da hannu fizge jikinta tayi da gudu tana turamai baki yay murmushi tawuce dakin Yaya su Ammi duk suna waien tace "Ammi zai tafi wai yanaso yagaidaki" kallon su Yaya Ammi tavi dasauri tace "kie ku gaisa

E3 yakamata" hijabin Yaya Ammi takarba tasaka taja hannun Yasmeen din tace

"muje" fita tayi waje hangota yasa

Maheer dake tsaye gaban Dakinsu ya tsugunna kanshi akasa anatse yace "ina yini Ammi" cikeda kunya itama Ammi tace "dan Allah katashi Maheer, tashi tashi" girgiza kai yayi batare dayayi magana ba Yasmeen dake kallonshi tawani murguda baki, Ammi tai murmushi tace "Ya aiki Maheer? Allah yabaku sa'a, Allah kuma ya taimaka ka gaida Baban ka dan Allah" Gyadamata kai yayi yace "sai anima" cikeda murmushi Ammi tace

"mujima lafiya" wucewa yayi Ammi tanunama Yasmeen gate da hannu alamun tabishi ta makema Ammi kafada, fita yayi ko 10secs baiyi da fita ba wani almajiri yay sallama dawata yar jaka mai kyau ahannunshi yace "salamu alaikum ance nabawa Fatima wannan" yay maganan yana karasowa wajen su Ammi kallon ledan Ammi tavi tace "kai maida" dasauri yaron yace "yaja mota yatafi" hannu Ammi tasa ta amsa tareda bude yar jakan kayan zakine zalla su chocolates biscuit da sauransu ajiyan zuciya tayi ganin ba kudi bane tabama

Yasmeen tace "gashi jeki kaima su Yaya" daidai an bude gate hakan yasa dukansu suka kallo gate Baba ne yashigo, maida gate din yayi yarufe yajuyo yana kallon Yasmeen baima jira yakaraso cikin gidan ba daganan gate yakalli Ammi cikin fushi

E3 yace "why is this girl dress like this?"

Faduwa gaban Yasmeen yayi dana Ammi itama amman Ammi tadaure takalli

Yasmeen daga sama zuwa kasa kafin takalli Baba daya karaso gabansu tace

"ohhh kayan salla su nace tasaka saina bata gyalen da makotan mu suka bani tsaraban makka tas......

." "Akan mene zaki

sa Yasmeen tayafa gale sabida wani"

Baba yama Ammi wani kalan ihu da saida gidan ya dauka dasauri Yaya da Hajjo suka fito su Sa'a babu wanda ya iya yafito Yasmeen taboye bayan Ammi jikinta na rawa gain kaman Baba zai daketa, shiru Ammi tayi tana kallonshi batace komiba Baba fa kaman yadawo da bacin rai vanuna kanshi yace "wato ina miki magana kinmini banza ga shashasha namiki magana ko" anatse Ammi tace "to me kakeso nace nidai banga aibun wanna shigan datayi ba shigan mutunci ne full covered kaya da babban mayafi ma bawai karami ba naga kuma ba fita tayi ba tana nan da..

5:45 AM

@

"akan me kike lalata mini tarbiyan yarana kina koyamusu shigan banza, sabida wani zaizo wajenta ne zakisa tasaka gyale eh, ke wace irin mahaifiya ce ina tarbiya kina batawa!" Sai anan Ammi taji ranta ya sosu, amman ta daure juyawa tayi takalli Yasmeen dake bayanta tana rawan jiki tana kuka tace "wuce kije dakin Yaya" juyawa Yasmeen tayi zata tafi Baba

E3 yace "koyama yarana rashin biyayya yanzu kike ga mahaifinsu ina magana zakice ta tafi" dasauri Yaya tace "dan

Allah Baban Nanah kayakuri abin baiyi zafi haka ba, Maman Nanah ke bashi hakuri magana ta mutu" Ammi da ranta yagama baci takalli fuskan Baba tace

"wIh bazan bashi hakuri ba duk abinda zaiyi yayi nagaji tunda so kake mu raba hali atsakar gida agaban yaranmu to muyi Baban Nanah, nagaji da halin nan naka, kuma idan yaron nan zai dawo gobe still gyale zansa tayafa kome zakayi kavi kaji" wani kalan kakkausan kallo Baba kema Ammi yace "ni kike gayama magana haka"? Daga murya Ammi tayi kaman yanda yayi tace "eh nagaji nagaji da halinka nadaga din ka zaci kai kadai ka iya ihu, an gayamaka yaran nan kai kadai ka haifesu ne, me dan na bata babban mayafin nan ta yafa? Sunna ne idan namiji yazo neman aurenka yaganka yasan wazai aura wanna sunnar annabi ce so l don't understand, kazaci tsoron ka akeji ne, tunda akazo neman Auren yarinyar nan samfari iri iri kake fitowa dashi idan bakaso tayi aure ne kafito kafada saika dauketa da ita da kanni ta kajika aruwa kash...

...." hannu Baba

yadaga zai mari Ammi Baffa daya shigo gidan yanzun nan yace "kul Ibrahim, karkasake kayi kuskuren nan" tsayar da hannunshi Baba yayi azuciye yana kallon

Ammi dake kallonshi cikeda mamaki itane yadaga hannu zai mara haka, wucewa tayi fuuuuu daki Baffa yakaraso wajen yarufe Baba da fada, ga mamakinsu gani sukayi Ammi ta fito da jaka dasauri kowa vace "Maman Nanah" itama Yasmeen dake kuka tasowa tayi da gudu tazo gaban Mamanta tarike akwatin tace "Ammi ina zaki"? Baffa yace "me haka Maman Nanah" Yaya ma tace

"Mehaka Maman Nanah dan Allah?"Baba ya tsaya chak yana kallonta gabanshi na faduwa sosai.

Jin ana tambayan Ammi ina zata da jaka yasa Farida da Nana dasukai tsuru tsuru adaki suka fito da gudu, ganin

Ammin su rike da Babban akwati kowa na gidan ya zagayeta banda Baba dake gefe tsaye yana kallonsu yasa sukai wajenta da gudu gain yanda Yasmeen ke kuka tarike jakan gam yasa yasa suma duk sukasa hannu suma suka rike suka fashe da kuka duk sukace "Ammi ina zaki"?

Anatse Baffa dake kallon yaran yace

"please Maman Nana calm down kodan sabida yara matan nan uku dake kuka agabanki dan Allah kinji" dago kanta ahankali Ammi tayi duk yanda taso  hawayen datakeji takasa fashewa tayi da kuka tace "Baffa nagaji, for 20yrs yanzu kullum cikin jure cin mutuncin Baban Nanah nake kala kala kan yaran nan amman yau for the first time yazagi character na, yazagi tarbiyana ace ina lalata mai vara zan bata mishi Yasmeen tafara Iskanci abinda yake nufi kenan, i will not take that, nahakura da aurenshi, yaran ma na barmai tunda shine the perfect father and mother ma duka yaran nan wh wIh na barmai karyaji komi"tai maganan tareda kallon su Yasmeen da Nana da suka rirrike akwatin ta suna kuka tace "ku saki akwatin nan"

cikin kuka Yasmeen tace "Ammi dan

Allah kiyakuri" Farida tace "Ammi dan

Allah kada kitafi kibarmu" Nanah tace

"Ammi idan zaki tafi to saidai kitafi damu duka ko Anty Yasmeen baramu zauna da Baba mai mana fada ba harda ke ko Anty Yasmeen"

Gyadamata kai Yasmeen tayi tana kuka, sakin musu akwatin Ammi tayi tabi ta gefensu tawuce dasauri suka bita suna kuka zasu riketa ta daka musu tsawan da saida kowa ya firgita agidan tanuna Baba da hannunta dake tsaye kallonta kawai yake tace

"kuwuce kutafi waien Baban ku wlh  duk wacce ta tabini saina gaura mata mari harke Nana" duk wanda yaga

Ammi yasan tai fushi yau bana wasaba, tsayawa yaran sukayi juyawa tayi tawuce Farida da Nanah suka rungume Yasmeen suna kuka sosai ganin da gaske Ammi take tafiya zatayi tabarsu,

daidai Ammi tasa hannu zata bude gate duka yan gidan babu wanda yasan lokacin da Baba yamaje wajen hannunshi yasa yarike hannunta yacire daga gate din yajuya yasa all d sakata na gate din sannan ya tsaya jikin gate din yakalleta cikin fushi soyayya yace

"tunda fushi kike aani ai nina bata miki rai ko vent it out on me amman bazaki tafi kibar yarana suna kuka ba wh, kome zakimini kimin" sosai Ammi takalli Baba kaman yanda yake kallonta shifa mai hali bazai taba chanzawa bane, yanzu bai tsayarda ita dan kanshi ba saidan yaranshi, idanunta sunyi jazur tana kallonshi da takaici tace "Ibrahim tashin mini daga jikin gate" "cikeda dakewa dakuma taurin kai Baba yace "bazan tashiba"

cikin fushi Ammi tace "nace katashi idan nai loosing temper na zan iya abinda zanyi nadama daga baya" anatse Baba yace "do your worst amman dai baraki tafi ki barmini yara in agony ba kin haifesu zaki zauna mucigaba da basu tarbiya tare har zuwa ranan da Allah zai karbi rayukan mu" fashewa da kuka kawai Ammi tayi tashiga kaima Baba duka akirji tace

"nace ka matsamin nafita nabar gidanka ka matsa katashi nace, nagaji nagaji nagaji nagaji dakai Ibrahim" batare da Baba yahanata ba yace

"nikuma nan gaji dakeba zama dake yanzu nafara" gain haka yasa Baffa yakalli kowa yace "ku wuce dakin Yaya ku harsu zasu daidaita" dukansu dakin

Yaya suka shiga harda su Yasmeen

Baffa yamaida kofan yarufe yasa sakata.

Duk ta inda Ammi tasamu kaimai duka take tana kuka rungumeta Baba yayi tsamtsam ajikinshi gain babu kowa ahankali yace "dan Allah kiyakuri kiyafemini I am sorry please, haba wife ni zaki toxarta kice zaki tafi ki barni tayaya zanyi rayuwa babu ke Dan Allah ki yakuri" ina Ammi bata jinshi dan ranta yabaci, daukanta yay da karfi da yaji yatafi da ita dakinsu ya maida kofan yarufe yasa sakata yajuyo zatai magana yakama bakinta yawuce da ita uwardaka duk gardaman Ammi saida Baba ya wanke laifinshi tass azuciyanta sukai wanka yafito da jallabiya dan zuwa masallaci, dakinsu Yasmeen yabude yagansu zugum suna zaune idanunsu jazur gwanin ban tausayi kaman was marayu, ahankali yace "kutashi kuje kuyi salla" dasauri Yasmeen tace "Baba Ammi ta tafi" kafin Baba yabada amsa Farida tace

"Baba kayakuri" dasauri Nanah cikin tsiwan yarinta tace "Baba kadainama

Ammin mu fada, munason Ammin mu sosai ko Anty Yasmeen" kasa amsawa Yasmeen tayi Baba yadade yana kallonsu kafin anatse yace "Ammi bazata ko'ina ba, nabata hakuri and I promise bazan karama Ammin ku fada ba dagayau Baba yay kuskure Ammi tayafemai, kuje kuga Ammin ku" dasauri dukansu ukun suka tashi ta gefenshi suka fita suka wuce dakinta daidai Baffa vafito wani kalan mugun kallo yama Baba dasauri Baba yace "Baff..." Hannu Baffa yadagamai yace "I don't have anything to say to you duk wannan abubuwan dakake sabida bakason Yasmeen tayi aure ne ko, to bari kaji Ibrahim muna dawowa daga sallan nan zan kira Yasmeen inhar ta aminta tana sonshi zan aika amin binciken yaron inhar yasami shaidan kirki aura da

Yasmeen zany bana bukatan ko sisin ka mara mutunci kawai agabana kadaga hannu zaka kaiwa matarka mari kai son yara haukan ne metayi da bayida kyau?

Tsirara kazo kaga Yasmeen dazaka fara haukan nan" Baki Baba yabude zai bama

Baffa hakuri kawai yawuce abinshi. Ammi na zaune afalo duk su Yasmeen suka shigo duk suka tsaitsaya wajen kofa kallonsu tayi jitayi she's feeling guilty saisa bata taba biyema Baban su tayi fada dashi agabansu dan fada na affecting yara sosai, hannu tabude musu da sauri sukai jikinta, Yasmeen tace

"Ammi dan Allah kiyakuri kinji kidaina barin maganganun Baba na tabaki yana sonki sosai he didn't meant maganan dayayi wlh kinji Ammi"? Gyadama Yasmeen kai tayi sannan tai murmushi tace "yanzu enough of fadana da Baban mu mun shirya dan haka ya isa kuje kuyi salla" dukansu murmushi sukayi suka juva suka fice aga dakin tabisu da kallo.

Tana zaune awajen Baffa yayi sallama daga waje anatse tace "shigo Baffa" shigowa Baffa yayi shi kadaine yasami kujera yazauna yace "Maman Nanah babu wacce nake yabo agidan nan akan hakuri kaman ke nasan halin kanina sarai akanme zaki biyemishi kuyi fada gaban yara da kowa" ahankali Ammi tace "Baffa kavakuri bazan karaba" murmushi yayi yace

"Allah yamiki albarka" anatse Ammi tace "Ameen" kafin ahankali tace

"Baffa dan Allah ka tsaya akan lamarin auren nan da kanka, soyayyan da

Baban Nanah kema yaran nan yana neman rufemai ido wlh aurar da

Yasmeen ne bavaso yayi kwata kwata

Baffa to idan bai aurar da ita ba mezaiyi  Bokon bata ganewa gwarama Islamiya dasauki amman shima wajen rubutu duk abu daya, dazu bakaga kukan datayi da rana ba kan bata rubut komi a test din dasukayi ba, Baffa to tunda Allah yafito mata da miji yaro natsasse yanada aikin yi dazai rufamus asiri ya iya ciyar da ita to me wannan abubuwan dayakeyi eh Baffa" jinjina kai Baffa yayi yace "hakane, kada kidamu komi na hannuna anima zan kira Yasmeen wajena ni kadai tabani amsa zan aika shakikai na tareda Baba karami aje ayimin bincike idan komi lafiya lau zan kirasu ne Azo ada rana duk taurin kan Ibrahim bai isa yahanani abinda nasi yiba" gyadamai kai Ammi tayi tace Back

"nagode Baffa" tashi yayi jin ana kiran

Isha'i dan musamman sabida ita yau bai tsaya yaji karatun Umdatul Ahkam da akeyi a mosque dinba yabarki su Baba can yazo tabata hakuri yanata sallama yatafi.

Wuraren 10 Baffa ya aika Yaya data kiramai Yasmeen, Yasmeen dahar sun kwanta gyangyadi yasoma kwasanta dan tuni Baba yazo yamusu sallama

Yaya tabude kofansu dawuri dukkansu suka kalleta, Yasmeen takalla tace

"kizo Baffan ki na kiranki" ahankali ta sauka daga gado, hijabinta tadauka tasaka sannan tabi bayan Yaya suka I fito waje, anan waje Yaya takamo hannunta cikin whispering tace

"Yasmeen dan Allah Baffan ki ya tambayeki kice eh ki aure abinki kihuta. yaro kyakkyawa ga mota ga aikin yi me kikeso? Ba gwara aure ba da bakin masifan Baban ki da takuranshi, muje muje" binta abaya

Yasmeen tayi kirjinta na bugawa dim 

dim dim da sallama tashiga dakin,

Baffa ne kadai zaune kan kujera yana kallonta Yaya tawuce ta zauna kusada shi, zama tayi ahankali akasa tace

"Baffa gani" murmushi Baffa yayi yana kallonta cikeda so yace "nakiraki ne namiki tambayoyi kan mutumin dayazo wajenki yau"

yadanyi shiru yace "ance malamin kune a FCE?" Ahankali ta gadama Baffa kai tace "eh Baffa" shiru Baffa yayi kafin chan yace "inaso ki natsu ki bani amsa mai kyau dan koba komi at least ke kin had da Maheer din countless time amakarantan ku koda bai taba miki magana a school ba, atleast kin ganshi, kin sanshi, kinga yanayin halayanshi da yanayin rayuwanshi da dabi'un shi, sannan kuma yau yazo wajenki dan haka"

Baffa yay dan gyaran murya cikeda kamala dakuma taushin murya yace "kin amince kin yarda da ahada Auren ku Fateematul Zara'u?"

Wani kalan faduwa gaban Yasmeen yake batasan lokacin data shiga wasa da yatsunta na tasauke kanta akasa saika hawaye sharrrr, Yaya tai murmushi tace

"saisa kap gidan nan nafison Yasmeen tafi halinsu na arziki halin Mutan da idan an tambayesu sunason wane basa bada amsa saidai kaga hawaye" dan murmushi

Baffa yayi yakalli Yasmee yace "bani amsa Yasmeen idan bazaki iya magana ki  

ki gyadamin kanki idan kin varda idan baki yardaba kuma ki girgizakai" shiru tayi kafin takai bayan hannunta ta share was hawaye masu zafi dasuka zubomata ahankali ta gyadama Baffa kai wani kalan murmushi daga Baffa har Yaya sukai, Baffa yace "to tashi kitafi Allah miki albarka" tashi tayi tafita daga dakin tawuce dakinsu Farida tai bacci

Sa'a ne ke waya da Faisal dinta wucewa tayi wajenta ta kwanta ahankali ta rufa da bargo har kai kuka tayi sosai mara sauti har bacci yay awon gaba da ita.

Baffa ya aika aminanshi da Baba Karami bincike akan family dashi Maheer din shima Baba dakanshi yaje layin yayi bincike wanda baisamu ko mutum dava dava bada wani bad abu kansu ba saima yabonsu da ake aka fadama Baba basusan Maheer sosai ba dan baida magana baya shiga mutane gwara

Hamad, Maheer daga masallaci sai gida sai aiki sai anan hankalin Baba yadan natsu hakan yasa yazo yasami Baffa yace shima baiji wani bad abu ba anan gaban Baba Baffa yadauki waya yakira Baba Makaho vace

"zasu iva zuwa akarasa

magana asama rana".

Ranan Friday Baba Makaho da abokananshi wanna karan banda

Hamad sukazo akasa rana tsakanin 

Maheer da Yasmeen sati uku dan already

anci sati daya aka shiga shigowa da goro

da sweet da abubuwa daban daban inda

aka vanke musu sadaki 200k sukai

Na'am anyi raha anci ansha sanan suka

tafi aka watse.

Zaune duk suke a restaurant din an

kawo musu abinci daban daban duk

sunaci ita kadaine bataci sai dialing wani number take tana kaiwa

kunnenta Hj Sameera tace "Kiwa Allah

kici abinci kibar neman yaron nan

awaya" Shafa tace "halan ma guduwa

yayi" wani kallo Hajiya tamata kafin

"Maheer bazai taba iya guduwa ya barni ba sabida nine rayuwanshi, inamai tabbatar muku akwai abinda yarikeshi yahanashi kirana ne Kunsan kasan Iran sai ahankali amman Pablo bazai taba

¡ya rabuwa dani ba wIh bazai iyaba" tai maganan kaman wacce ta zare tsabagen tsoro hakan yasa Hj

Sameera tace "dan Allah kale Shafa da maganan banza, tayaya ma zai gudu ya barta bata baki labarin da akace tana asibiti vanda yazo yay nan nan da ita ba, kuma

saida yamata goodbye sex lafiyayye"

takalli Hajiya da idanunta yayi jazur

tace "dan Allah kema kidena damuwa

Pablo zai dawo kuma zai kiraki idan

yasami chan so chill vanda bayanan

din nan have fun abinki kinsan idan

yana nan baki iya fita ko nan da chan

idan kuma susa kikeso ki kira wannan

shashashan dudda baya miki abin

arziki amman kiyi maneji" kwashwwa

da dariya sukayi harda Hajiyan

daganan suka jata da hira ta manta da

abinda ke damunta anan waien takira

Adamu da gudu yazo kaman bashine

tacika mutunci a asibiti rannan ba wani

hotel suka tafi nan taje ta shakata

dashi at least yafi babu.

7:49 AM

Wasa wasa abin nama Yasmeen kaman

mafarki shirin bikinsu ake sosai gashin

har anfara mata gyaran jiki, Ammi nabata

wani kalan extra kulawa tana kovamata

abubuwa da dama dabata taba sanin

Ammi zata iya koyamata ba, cikin sati

uku har anci daya tun ranan Sunday da

Maheer yabar gidan bai sake kiranta ba

bata dake ganinshi ko a school ba, ta

karanta messege daya mata yanzu haka

sau dubu biyar a achool tawuce tagaban

office dinshi yafi akirga bata ganshi ba

bataga Dan ba wh jitake azuciyanta

kaman ta haukace batason auren nan

amman bata taba tunanin wani ba kojin

bakin cikin rashin ganinshi ba kaman

yanda takeji game da Maheer ba, gashi abinda yafi ci mata rai was ranan Sunday baimazo gidansu ba Ammi har saida ta tambayeta tawayance tace "sunje wani field work ne".

(O

Yana zaune akan gadon Hamad yabude

MacBook dinshi yana duba emails nashi wanda Hajiya tamai messages kusan 58 akan yakirata, she miss him bla bla bla, dan tsaki yayi yafita yashiga important message work turo kofan akayi tareda knocking hakan yasa yadago kanshi

Hamad ne rike da was manyan ledoji na dinkunan Maheer na manyan kaya yace

"Kaje Baba na kiranka" bin kayan Maheer

83| yayi da kallo kafin ya jive system din yatashi yafita daga dakin kasa ya sauka

Dan ne kadai afalon yana kallon ball dakin Baba yawuce sallama yayi yashiga dakin Baba dake zaune kan kujeranshi ya amsa yace "Maheer" kasa rawa yayi yazauna gaban Baba yace "gani Baba" shiru Baba yayi kafin anatse yace "ya gyare gyaran da akeyi abangaren naka"?

Anatse yace "gobe sukace zasu gama komi" "maisa bakaje ka gantaba Maheer ranan lahadi daya wuce?" Shiru Maheer yayi yakasa magana gain baice komiba yasa Baba yace "Maheer kaji tsoron Allah kaji" gyadama Baba kai yayi baice komiba, wata yar leda dake gefen Baba baka yadauka yamikama Maheer hakan yasa Maheer yakarba vana bude cikin ledan kudade yagani bandir bandir na yan dubu dubu da akalla zasukai hamsin

Baba vace "Maheer kudin nan naka ne" dasauri Maheer yakalleshi, hakan yasa Baba yace "Maheer banso kayi aure da kudaden nan dakake dasu na kayan maye inaso kai aure da pure halal kudi Maheer, kudaden gonaki na na kauye ne gabaki dayansu nasa an sayar mun sami miliyan goma, naka biyar da Hamad shima biyar kayi amfani dasu, kaida Hamad kuje gidan Malam Sani kabawa matanshi itada matan Liman su tayaku hada akwati dan sune zasukai akwatin dama kaji Maheer" ahankali Maheer yadauki ledan kudin yamaida kan cinyan

E3

Baba anatse yace "Baba maisa zaka saida gonakin ka sabida ni eh? Dan Allah ka maida kudin abaka gonakin ka back, Baba inada different kudi outside kudin business dina, Halal kudi a account dina dake dauke da sunana Maheer Maheer

(U

aka" dan shiru Maheer yayi ahankali yace "Baba business dina nada nashi business account inada account inada manager dasuke handling that account bantaba hada kudina da kudin business dina ba" ahankali Baba yace "Maheer a ina kasami kudi?" Dan shiru yayi kafin ahankali yace "Baba I have so many people dasuka min kyauta lokacin tunkan na girma ka tambayi Hamad tare mukaje inada shares dayawa a verious bank, inada share da so many organization outside nigeria Baba keep this money kaji" shiru Baba yayi kafin ahankali yace

"promise me bazaka ciyar ko tufatar da yarinyar nan da Haram ba" ahankali Maheer vace "I promise Baba, ko chocholate dana saya mata rannan is from my own personal money Baba trust me" ahankali Baba yace "nayi, yaushe zakabar business din nan to? Maheer kabar abubuwan nan tun yanzu kafin

E3 akamaka kaji dan Allah kaga yanzu aure zakayi kakusan zama cikakken namiji, yaushe zakabar business din nan kabar matanshi kariga ka girma ne kakeyi da ita eh"? Shiru Maheer yayi yana kallon Baba ahankali yadauke hannunshi daga jikin

(U

Baba yakoma inda yake ya zauna kaman bazaiyi magana ba yace "In sha Allah zan bari Baba kadingamini addu'a" sosai jikin

Baba yay sanyi yace "shikenan zan dinga maka tashi katafi to" tashi yayi yawuce yatafi.







YAFEBA, Mageer yayi sabida

Hamad na zaginta tace "hanashi kake ya tsagi tsohuwar banzan nan, hartanada darajan dazaka hana azageta"? Lumshe idanu Maheer yayi yabude su ahankali yace "you guys

should stop insulting her koba komi she gave me home" cikeda tsiwa Yasmeen tace "wani home? Gidan shaye shaye da kwayoyi ne home? This woman abused you? Took advantage of your innocence, yet kana hana

azageta" dasauri Hajiya ta chabe maganan tace "that's because he loves me and will always do" cikin ihu

Maheer da kanshi ke nema ya tsage yace "I never loved you Maryam! Stop saying it, don't love you, banson ana zaginki ne dan koba komi kin haifi dukanmu anan is not proper, please respect your old age kibar gidan nan right now" sosai Hajiya ke kallonshi kuka na zuwan mata tanuna kanta tace

"kace you never loved me?" Cikin ihu

Maheer yace "yes and I will say that again and again, Maryam bantaba sonki ba, bantaba sonki ba, kuma bazan taba sonki ba!" Gabanshi Yasmeen tashiga takalli Hajiya tace "ai kinishi ko mijina nada taste vasan what is worth loving and what not dan haka bar gidana before nasa a fitar dake" wani kalan kallo Hajiya kema Yasmeen batason tai attempting anything anan data ciro bindigan dake jakanta takashe Yasmeen but Maheer na nan, hannu tasa tagoge idanunta tass tawani kalan fashe da mugun dariya dukansu suka tsava suna kallonta kaman tahaukace sannan takalli

Yasmeen daga sama zuwa kasa tace

"kalleki kalleni nunamin abu daya dakika fini dashi".


No comments