Breaking News

Kyalkyalin Kauna 47

 EPISODE 4️⃣7️⃣





Kusan atare dagashi har Hamad sukakai gida, Hamad yafara isowa sai shi daga baya, wucewa ciki yayi Dan biyeda shi, afalo yasami Baba da Hamad zaune suna magana, kafin ma yayi magana Baba yace “Maheer” anatse Maheer yace “Na’am Baba” “taho nan” dan juyowa Maheer yayi yakalli Dan da idanu yamai alamu yatafi sama yahuta wucewa wurin Baba yayi waje yasamu yazauna kusada Hamad yasauke kanshi kasa dan yasan maganan shi Hamad yama Baba, shiru dukansu sukayi chan Baba yace “kalleni Maheer” dago kanshi ahankali Maheer yayi yakalli Baba dake da bakin glass kaman Baba yanagani yace “Maheer zan maka tambayoyi biyu kagayamin tsakaninka da Allah dan Hamad yafada mini komi daga farko zuwa karshe, baka tabamini karyaba Maheer tunda kake yaro kawowa yau dan haka ka amsani tsakaninka ga Allah” Baba yadanyi shiru sai chan yace “kanaso ka auri yarinyar nan dan kaci mata mutunci ne ka wulakantata kodan ka kara tozarta mahaifinta sabida yataba kayanka??? Kaa gayamin gaskiya Maheer” shiru Maheer yayi kafin chan yace “a’a Baba” shiru Baba yayi tun yana karami Allah yabashi baiwan gane idan mutum yana karya ajikinshi kodan sabida shi makaho ne Allah yabashi baiwan oho, cikin kwantacciyan murya Baba yace “sai tambaya tabiyu kanason yarinyar ne Maheer”? Hakanan Maheer jiyayi gabanshi yafadi, wannan karan yakusan kai 5min yakasa amsa maganan kafin chan cikin murya mai taushin gaske tsakanin shi ga Allah dakuma zuciya daya yace “nima bansani ba Baba” dan shiru Baba yayi yana kallonshi sunnar da kanshi kasa Maheer yayi kusan 10min suka bata ahaka kafin Baba yasauke ijiyan zuciya yace “tashi katafi zan kira Malam Sani yau zaije yama Baban ta magana yaneman mana izini idan ya yarda cikin satin nan zamuje sai ayi magana kutashi kutafi” cute smile Maheer yasaki yatashi ahankali yawuce sama shikuma Hamad ya tsaya batare daya tashi dagakan wajen ba yana kallon Baba cikeda mamaki dan baiyi tunani Baba will accept maganan nan dawuri haka ba, dan murmushi Baba yasaki dan yasan Hamad na zaune awajen har yanzu, anatse yace “hanyar shiriya Maheer ya dauko Hamad I have to support him dudda nasan kalubale na gabanshi, akasin hakan zai iya jefashi yaje yayi wani babban kuskuren dayafi komi muni, tashi kaje soon u will understand abinda nayi dakuma abinda hukunci na ke nufi” harya tashi Baba yadauki wayanshi yamikamai yace “gashi kiramini Malam Sani, idan kaje sama ka karbi address na gidan su yarinyar saika turama Malam Sani ta wayanka” ijiyan zuciya Hamad yasauke yayi ma Baba dialing number sannan yawuce yatafi sama yana tunanin kiran telanshi dan dinkama Maheer manyan kaya dan bazasu neman aure yana sanye da kananun kaya ba.



As usual wuraren 6 na yamma Baba yadawo gidan saida yafara duba yaran dan yau babu islamiyya sannan yawuce daki, wanka yayi agurguje ya chanza kaya zuwa shadda yasa hula yafito dan tafiya masallaci atare suka fita da Baffa da Baba Karami dan suma sun dawo daga kasuwa.


Ana idar da salla andanyi jawabi suka fito suna gangarowa Baffa namusu magana kan kayan gonna da aka samu a gonan Baban su, wani magidancin mutum suka gani akofar gidansu tsaye jikin wata yar mota corolla tsaf tsaf dashi yaci manyan kaya harda Malum malum suna karasowa cikeda girmamawa yabasu hannu yace “Assalamu Alaykum barkanmu dai” dasauri Baffa dan yafisu raha yace “barkanmu bismillah naga kaman mu kake nema ko”? Atsanake yace “kwarai kuwa nazo naganku ne gaskiya kam ni ina matsayin kaman dan aike ne, wajen Malam Ibrahim nazo”


Yay magana yana kallon Baffa, Baba dashi kadaine babu wata fara’a akan fuskanshi bawai kuma ko wulakanci bane no he’s just a serious person, sanin halin Baba yasa dasauri Baffa yace “incedai bawata matsala bane, ga kanina nan shine Ibrahim Meya faru”? Dan dariyan dattawa mutumin yayi yace “to dafarko dai sunana Malam Sani nine babban aminin Malam Maheer Makaho wanda a gaskiya shiya aikoni nan na nemi izini wajenku” anatse Baba da sai alokacin yah magana yace “izinin mene”? Ahankali yace “Kunsan dayake makaho ne baya iya fita sosai ya aikoni ne nazo na nemi izini awajenku yanaso yazo axauna ya nemawa danshi Maheer izinin neman auren diyarku Fateema” wani kalan gyara tsayuwa Baba yayi dan maganan ta saukanmai kaman aradu, baki yabude zaiyi magana Baffa sanin halinshi yadagamai hannu yace “waye dan nashi a ina yasan Fateema? Sannan ita tasan shi”? Anatse Malam Sani yace “ehh to kusan zan iya cewa Fateema tasanshi amman bawai irin sannin dakuke tunani ba dan banjin wata magana ma yataba hadasu ba danshi Maheer lecturer ne a makarantan su yana koyar da English ma duka department dake makarantan, yasami Baban shi yau kan yanaso afara sanarda iyayenta idan sun bashi izini sai afara neman aurenta gaskiya banjin suntaba magana bama” kusan Baba zai iya cewa ya yarda dan wayanta akai akia yake bincika wa kuma da aka dauketa wayan all through na hannunshi ba’a taba kiranta daidai da 1 miss call ba” anatse Baba yace “ba yanzu zan aurar d……” tareshi Baffa yayi da sauri ta hanyar sakin ma Malam Sani murmushi yace “gobe juma’a zaku iya zuwa bayan juma’a dan bayan salla bama komawa kasuwa agida muke yini” murmushi Malam Sani yayi yace “Masha Allah to too Allah ya zabamana abinda yafi alkhairi, bari na barku ku shiga gida to saida safenku” yasake babbasu hannu suka gaisa, motanshi ya shiga yaja yabar wajen Baffa yakalli Baba da bacin rai dan dama baiwani huce sosai ba dudda Baba yabashi hakuri yace “kana kokarin gayamusu baka shirya aurar da Yasmeen ba kasan alamomin gidan mutunci kuwa”? Baffa yanuna motan mutumin daya wuce yace “gidan mutunci ne da yaron kwarai awannan zamanin zasuzo sufara tambayan izinin iyaye kafin dansu yama yima diyarka magana, kadaisan bazan taba bayarda Yasmeen banyi bincike ba kabar ganin kanka kaine dan sanda kaine ka iya bincike kasan abubuwa nafika sanin rayuwa Ibrahim, kabari gobe suzo muga yaron idan natsuwanshi yayi zamu bashi izini ya nemi Yasmeen inyaso saina hada bikinta dana Sa’a dan iyayen yaron sunzo kasuwa sun samen, kuam iyayen yaron sun damen sunaso asa rana nan da wata daya kanajina” badan yasoba Baba yace “eh” Baffa yakalli Baba karami yace “koba hakaba” anatse yace “hakan yayi Yaya, Yasmeen ta isa aure ai” jinjina kai Baffa yayi jin ana kiran isha’i yace “mutafi muyi isha’i kawai gabadaya” duk suka juya suka wuce mosque, koda suka dawo sama sama Baba yaci abincin yawuce dakinsu Yasmeen dukansu na zaune adakin harda Nana suna hira suna dariya ganin Baba yasa sukai tsit, binsu yayi da kallo one bye one sannan yasaki labulen yawuce yashiga dakinsu, direct kan kujera yayi yazauna Ammi dake zaune ganinshi haka yasa tace “lafiya Baban Nanah kanka ciwo yake ne”? Girgixa mata kai yayi baice komi ba yawuce yatafi uwarka da kawai.


Har wajajen dayan dare Baba yakasa bacci juye juye yake hakan yasa cikeda damuwa Ammi ta kunna wutan dakin takalleshi shima kallonta yayi saikuma yatashi yazauna tareda folding hannu akirji cikeda damuwa Ammi tace “wai menene Baban Nanah am getting worried? Meke troubling naka haka ka kasa bacci sai juye juye kake” shiru yayi yana kallon Ammi kasa dannewa yayi yace “wani mutumi dazu yazo tambayan neman Auren Yasmeen shine Baffa yace suzo gobe” wani kalan murmushi Ammi tayi da abin harsaida yasa Baba sakin baki dasauri tace “waye shi”? Cikeda dan bacin rai Baba yace “nima bansani ba sai gobe idan sunzo amman ance yaron lecturer ne a school nasu” wani kalan murmushi Ammi tayi kaman anmata albishir da kujeran makka hannu ta daga sama tace “Ya Allah ka tabbatar da Alkhairi kabawa Yasmeen miji mai sonta sama da yanda Baban ta ke sona” dan tsaki Baba yayi kawai yakoma ya kwanta tareda juyamata baya dariya Ammi tayi da shewa tace “wlh Baffa Yamin daidai aka biyemaka bazaka taba aurar da yaran nan ba” kashe wutan tayi tadawo rungume Baba tayi tace “zonan wlh saikai farin ciki” daganan salon labarin ya chanza.


✨KK✨



✍🏻M SHAKUR


No comments