Kyalkyalin Kauna 46
EPISODE 4️⃣6️⃣
Bata wani jima da shiga ciki ba Maman Intee taleko tana murmushi tace “tace tuwo kake so ko wlh bamu cikayin tuwo akasa ba amman yanzun nan zata maka dan Yasmeen makes the best tuwo da miyan kuka a shagon nan” adan kunyace ya gyadamata kai ciki Maman Intee takoma ganin Yasmeen kikam atsaye bata fara komiba yasa Maman Intee tashiga salati tareda kama baki tace “yau ina ganin bakin hali, yanzu baraki daura miya awuta ba nina tayaki yin tuwon ba kin tsaya kikam kaman gunki anan, ke bakiji dadi Allah yabaki mutumin arziki haka ba yaro gashi matashi ga kyau ga aikin yi abinshi, ga uwa uba kunya ke kinsan yanda mijin aure ke wuya kuwa, je daura miya kafin na makeki” wucewa tayi tana turo baki tahau daura miyan kukan itakuma Maman Intee ta tayata daura ruwa, Maman Intee tajuyo ganin tahada sawa yasa tace “to hadamai juice na pineapples da banana da kwakwa tunda bamu da zobo yau” batai musu ba tawuce tashiga hadawa tanayi tana gamawa tasa a fridge dan yay sanyi.
Cikin 15min sun hada tuwo da miya Maman Intee tasa tahada komi a tray ga man shanu abin yayi kyau daukowa tayi tafito daga kitchen din, dago kanshi Maheer yayi yana kallonta kaman yazo ya karbe tray a hannunta but baiso yataso tsoro yasa ta kabar hakan yasa bai tasoba har wajen tazo ahankali ta ijiye tray zata juya dasauri yarike hijabinta karaf hakan yasa takasa motsi tajuyo takalleshi murya chan kasa Maheer yace “sit down” duk yanda taso tamai musu kasawa tayi ahankali sabida yanda ya tsareta da idanu tazauna tasauke kanta kasa, tuwon yakalla dake tiriri da zafinshi saikuma yakalleta murya chan kasan makoshi yace “thanks” kin kallonshi tayi still, spoon yadauka yana kallonta yanda maroon hijabin yamata kyau, gashin giranta sun kwanta sosai, yakai spoon din cikin tuwo ya gutsuro ya dangwala amiya shi wlh yamanta tuwon da zafi yakai bakinshi wani kalan konamai lips da harshe tuwon yayi baisan lokacin dayasaki spoon din kasa ba yace “auuuchhhhh!” da sauri Yasmeen takalleshi jin faduwan spoon akasa, hannunshi yakai wajen bakinshi yabude mouth dinshi yana fifita da hannunshi yana hura bakinshi daya kasa hadiye tuwon dake tafarfasamai harshe, he looks super cute and innocent and so sweet yanda yakeyi mantawa tayi dakomi dasauri tasa hannunta tadauki glass cup da cold pineapple juice datamai keciki tabashi batare datai magana ba tsabagen yanda yakejin zafi cup din yakarba hannunshi ya gogi nata dasauri yakai bakinshi yahausha da sauri da sauri wani kalan mugun dariya abin yabata, murmushi tayi tareda daukekai zuwa one side cikin kukkuni chan kasa tace “rago kawai” “me kikace?” Taji muryanshi ahankali yay maganan dasauri takalleshi suka hada ido har lips nashi sun kara pink sabida yanda tuwon ya konasu, dan hararanshi kadan tayi cikeda tsiwa tace “ni badakai nake ba” dan murmushi kadan yayi yasauke cup din kasa yakalleta yace “ni kika cema rago”? Sake dauke kanta tayi cikin kunkuni tace “kunne kaman na maciji” “nine maciji”? Juyowa tayi tadan kalleshi tana zaro idanu takasa magana idanunta yabi da kallo dasukaji kwallin Ammi batare daya dauke idanunshi daga kanta ba yace “you have the most beautiful eyes I’ve ever seen in my entire life Fateema” dasauri Yasmeen tasauke kanta gabanta nafaduwa yatsunta tashiga wasa dashi bata kara dago kanta ba, tass yacinye abincin ya shanye juice din tareda lumshe idanu wlh yakoshi kaman cikinshi zai fashe, wannan tuwon yamafi na rannan daya sayo dadi, she is such a talented cook, duk yawace yawacen dayayi aduniya bai tabacin abinci Mai dadin abincinta ba.
Zaro kudi yayi daga aljihunshi 20k ya ijiye a gefen tray din kafin yamike tsaye ahankali yana kallonta, yace “kicema Anty natafi” dagokai tayi anoke ta kalleshi, glasses na idanunshi yamaida kan idanunshi anatse yace “by 4 kibar nan and go back home banson ki kai 5” dan juyamai idanu tayi azuciyanta tace “sannu ubana” anatse yawuce yafita daga shagon adan sace tabishi da kallo kaman tace yadawo batamasan mesa ba, sai alokacin taga kudin daya ajiye dasauri tadauka duka duka abincin dayaci 7k ne wannan plenty money fa, daidai nan Maman Intee tafito ganin kudi yasa da sauri takarba tace “badai kudin abincin yabiya ba akan mene yana surukina to be” turo baki Yasmeen tayi ta kwashi tray tawuce ciki abinta.
Karasa taya Maman Intee ayyukanta tayi jin ana kiran la’asar haka nan maganan shi yafado mata arai, dudda tana gayama kanta bazatabi umarnin shi ba samin kanta tayi da saka hijabi tama Maman Intee sallama kan zata tafi tatafi, tana fita Keke tagani already pake agaban shagon, Mai keke yace “Hajiya kece Yasmeen ko wani bawan Allah yabiyani na ijiyeki agida yabani ledan nan kuma nabaki” Keken yajuya yadauko wani cute leda mai kyau daga bayan keken yamikama Yasmeen dake tsaye tana kallonshi, ledan ta kalla takasa amsa mai keken yace “amshi mana Hajiya” ahankali tasa hannu ta amsa, Mai keke yace “yauwa to shigo mutafi” kalle kalle tashigayi awajen saikuma ahankali tai bismillah tashiga tariga ta sadakar ita wannan mutumin tasan ko kasheta yay niyyan yi yanzu zai iya gwara tabishi ahankali kawai surabu lpy Baba ya tsokano shi.
Saida taga hanyar da akebi aje anguwansu akabi hankalinta yadan kwanta, ahankali tabude ledan dake hannunta chocholates ne ciki dayawa irin expensive cute chocolates din nan dasauri ta maida ledan tarufe tacigaba da kallon hanya, nunamai har anguwansu tayi har kofar gidansu mai keken yakaita sai alokacin tasauke ijiyan zuciya tasauka mai keken yatada kekenshi yatafi abinshi itakuma tabude jakanta ta wurga ledan chocholate din sannan ta rataya jakanta tai sallama tashiga gidansu daidai Ammi na fitowa da kitchen rikeda kula tace “ba biyar zaki dawo ba incedai lafiya”? Murmushi ta kakalo tace “Ammi lecturer 4-5 wai bazata zo ba” Gyadamata kai Ammi tayi tace “to jeki rage kayan jikinki kizo kici abinci” murmushi tayi tawuce dakinsu su Farida ne kadai aciki jefar da jakanta tayi kasa tana kokarin cire hijabi chocholate din suka watso daga jakan dawani kalan sauri da Farida da Sa’a suka kwasa tareda daukan jakan, Farida tahau bude chocholate zatakai baki tace “waya baki hadaddun chocholates din nan Anty Yasmeen”? Dasauri Yasmeen dabama tasan Chocolate din sun watse ba kokarin cire kaya take takallesu dawani kalan sauri ta yarda rigan nata tazo wajensu ta fizge jakanta da chocholate dake hannun Farida tazuba ajakan back tarike jakan gam tace “wayace ki budemin jaka”? Dasauri Farida tace “laaaa Ya Sa’a dan Allah ba ita ta jefar da jaka ba suka zubo”? Dan dariya Sa’a tayi dan ita harta karanta wata yar karaman takardan ciki tace “wlh saurayi ne yabata ai harna karanta takardan saisa dukta tsure” dasauri Yasmeen takalli Sa’a ahankali tace “wace takarda?” Dariya Sa’a tayi tace “duba jakan ki” dasauri Yasmeen tabude jakan wata yar karaman takarda ne da note jiki da akayi da byro handwriting din so fine.
Take Care
MM❤️
Aka rubuta dawani kalan sauri taboye takardan abayanta daga Sa’a har Farida suka kwace da dariya ganin yanda tayi tana zaro ido, Sa’a tace “dalla chill bazamu fadama Baba ba mudai kibamu chocholate muci” hararan Sa’a tayi tace “baram bayarba” zata juya Sa’a ta fizge jakan tabude ta kwashi chocolate son ranta taraba biyu ta watsama Farida rabi tace “Allah sanya alheri first boyfriend din Yasmeen, her first love, nasan yanzu duk afirgice kike sabida Baba kika natsu kya bamu labarin shi ko Farida” kasa magana Faridan tayi tana danne dariyanta bakinta cikeda chocholate yarda jakan kawai Yasmeen tayi tajuya tafita daga dakin dan zuwa dakin Ammi cus she’s loosing her mind.
Post Comment
No comments