Breaking News

Kyalkyalin Kauna 45

Yasmeen na zaune a shagon Maman Intee


dan tunda tashigo tazauna Maman Intee nata mata hira, tana bata labarin yanda customers din nan nata suka daina zuwa yanzu bata ciniki sosai, bata iya magana kawai bin Maman Intee take da idanu da abinda ke damunta yafi karfin tunanin ta, harsaida Maman Intee tace “Kodai har yanzu bakiji sauki bane” tace a’a taji kanta kedan ciwo tasa hannu suka fara filling na samosas datakeyi.



Tana cikin hada salad wayanta dake cikin jaka yahau ringing faduwa gabanta yayi takalli agogo dasauri this is just 2:15 na rana Baba ne ke kiranta amman normally yau 5 zata gama lectures sabida duniya dataji yamata zafi ne yasa tazo nan shagon Maman Intee kota manta damuwanta, dasauri tagoge hannunta tawuce wajen jakanta tabude wayan taciro takalli screen din, wata bakuwar number ke kiranta  ba number Baba bane hakan yasa ahankali tace “waye wannan number kuma”? Maman Intee dake bama Intee nono tana jinta tace “ki dauka kiji ko waye” gyadama Maman Intee kai tayi ta danna wayan takai kunnenta cikin sassanyar muryanta tace “hello” har tsakiyan kanshi yaji dadin zakin muryanta, cikin wani irin cool romantic voice yace “inajin yunwa sosai Fateema, am outside shagon ku, bring food for m……” dawani kalan sauri Yasmeen tazare wayan daga kunnenta ta shiga daddanna screen din tana kokarin katse wayan harsaida Maman Intee tace “ke lafiya? Waye kika kashe wayan da gudu haka”? Rasa abinda zatace gabanta na faduwa sosai yasa tace “wa….wani mutumi ne” yanda tabada amsan zakasan tasan waye, dasauri Maman Intee tace “wani mutumi kuma”? Rasa abinda zatace tayi saitai shiru tana zaro manyan idanunta tana kallon Maman Intee tana maida wayan jaka da sauri, Maman Intee yar gari ce tasan whatsupp dan dariya tayi da shewa tace “yaushe kikai saurayi Yasmeen”? Zaro idanu Yasmeen tayi sosai tanuna kanta tace “ni” dariya sosai Maman Intee tayi ganin yanda tayi tace “kwarai kuwa ke, watanki nawa kina zuwa shagon nan inhar wayanki tai ringing kodai Baban ki ko Mamanki ne ke kira, bantabajin wani ya kiraki ba, yarinya har yarinya gaki kyakkyawan gaske black beauty abinki amman baki kula samari ni nasan duk sabida Baban ki ne yanzu dai waye wannan”? Rasa abinda Yasmeen zatace yasa tace “lecturer mu ne” wani kalan kecewa da shewa Maman Intee tayi tace “to meyake so”? Ahankali tace “uhmmmm cewa yayi yana waje wai yunwa yakeji” zaro idanu Maman Intee tayi tace “shine kika barshi tuntuni” hannu Maman Intee tasa tajawo Hijabi dagakan kofa tabata tace “maza saka kije ki shigo dashi nan” wani kalan miyau Yasmeen ta hadiye tana zaro idanu gabanta nafadi baki Maman Intee takama tace “ohh ni jama’a duk wanda yaganki yasan sabon shiga ce ke a harkan samari, idan tsoron Baban ki kike kinsan dai bazai taba kamaki anan ba ko menene amfanina idan bazanyi guiding naki ba, wuce jeki shigo dashi idan naganshi mai hankali ne dakaina zan kira Ammi ki namata wannan sanarwan, wuce kije kishigo dashi” Gyadamata kai Yasmeen tayi duk atsorace take ya akayi yasami number ta, ya akayi yayi tracing nata zuwa nan wannan wani kalan takadirin maye ne? Da gaske babu inda bazai iya samota ba, ahankali take tafiya kanta akasa har zuwa waje motan ita kadaice pake awajen hakan yasa takara hadiye wani kullutun abu awuya tawuce wajen motan kafin takai taga an bude kofar baya alamun nan zatazo hakan yasa takarasa wajen, ko cikin motan bata kalla ba kanta akasa tana wasa da dogayen yatsunta ahankali kaman yar yarinya tace “ance…….ance kashigo” tunda tafito yake kallonta hartazo wajen, hannayen ta datake wasa dasu ya kalla kafin yasaki dan murmushi softly yace “wayace in shigo”? Dan dagokai kaman barauniya tayi danta kallai karaf suka hada ido dasauri tasauke kanta kasa, murya chan kasa kaman mai shirin fashewa da kuka tace “Maman Intee” tana maganan tajuya da sauri tawuce ciki yabita da kallo wani irin sweet smile yasaki ganin dukya kara firgitata ganinshi datayi yazo nan kuma yakira number ta, ga mamakin Dan saukowa yayi daga motan tareda gyara zaman suit nashi ya da bakin glass na idanunshi yafara tafiya ahankali yawuce cikin shagon tana tsaye chan wajen kanta, kujerun dake wajen tanunamai da yatsa ahankali tace “kazauna” murya chan kasa yace “okay Wifey” dasauri takalleshi shima ita yake kalla tareda zare glasses na idanunshi daidai Maman Intee tafito tace “laaaa shine tabarka bata baka ruwa ba kaga shirmen Yasmeen ko” tajuya takalli Yasmeen dake rakube awajen kanta tace “wuce kije ki dauko ruwa sai kizo ki tambayeshi mai zaici yafito daga aiki keda kikasan harka da dalibai da wuya imaza” juyawa tayi tashige ciki itakuma Maman Intee takaraso wajen kan Maheer akasa kaman bashi ba yace “Ina yini Hajiya” washe baki Maman Intee tayi tace “ina Hajiya ai kirani da Maman Intee na ai yanzu an dawo daya, to ina gaji? Ya aiki? Yakuma fama da dalibai? Tacemini kai lecturer sune, Allah ubangiji ya taimaka” dan murmushi yayi kadan batare dayay magana ba ganin yanada kunya yasa tajuya takalli kofan ta kwala kara tace “ina ruwan zama kikai aciki” tajuyo takalli Maheer tace “Yasmeen fa akwai shirme abinka da yar fari, kuma yarinya ce she’s just 20yrs, FCE ma banjin tacika 2months da farawa ba dan Allah asamata ido dan gaskiya na yaba da natsuwa ka kaine saurayinta na farko wlh wlh aduniya, yaya sunanka”? Ahankali Maheer yace “Maheer” murmushi Maman Intee tayi daidai Yasmeen nakawo ruwan gora mai sanyi a tray ba zobo bakomi Maman Intee tasaki baki saikuma tace “bari naje ciki ni, Yasmeen yafada miki kome zaici idan ma babu saikizo ki dafamai kinji” Gyadamata kai tayi batai magana ba Maman Intee tawuce ciki itakuma Yasmeen ta ijiye ruwan akan table tajuya dasauri zata wuce karaf taji yarike kasan hijabinta amman irin rikewan dabazaka taba gane shine yarike ba dasauri tajuyo kaman zatai kuka ta tsaya tareda dauke kai, lumshe idanu yayi yabude su asanyaye, murya chan kasa yace “baraki tambayeni mezanci ba” batare data kalleshi ba makemai kafada tayi tahaderai tace “ka saken” dan juya mata idanu yayi yace “naki” dasauri takalleshi, wani cute smile yasakin mata dasauri tasauke kanta kirjinta na bugawa murmushi namai mugun mugun kyau, murya chan ciki kaman baiso wani yajisu yace “I want tuwo da miyan kuka da zobo” dan turo baki tayi batare data kalleshi ba tace “toni ka sakeni” ahankali yana kallonta yace “toni ki kalleni” juyowa tayi dasauri suka hada ido jin yanda yay magana kaman ita,  faduwa gabanta yayi ganin yanda kwayan idanunshi kewani irin kallonta kaman zai hadiyeta dasauri ta fizge hijabinta da karfi tawuce tai ciki yabita da kallo.

✨Kk✨


No comments