Breaking News

Kyalkyalin Kauna 44

 EPISODE 4️⃣4️⃣






Juyawa Yasmeen tayi ahankali zata tafi saikuma ta tsaya chak kafin dasauri tajuyo takalleshi kaman yanda yake kallonta bai motsa daga inda yakeba, dakewa tayi takai bayan hannunta ta share fuskanta tace “ko kaine the only namijin daya rage aduniya bazan taba aurenka ba, kuma kuma baka isa ka kashe su Baba ba sai lokacin su yay…..” wani kalan kallo yamata dayasa maganan ya makale awuyanta ahankali yace “are you underestimating me? Ni?” Faduwa gabanta yayi tana kallonshi tana kara kallonshi mutumin daya sa akayi kidnapping ita da Nana da Farida babu abinda bazai iyaba, baki tabude zatai magana saikawai kuka yacita takasa magana irin kukan rasa mezakayi dinnan kariga kasan anfi karfinka, kukan tsaka mai wuya, tasowa yayi ahankali ya tsaya agabanta he feels kaman yay hugging nata, handky yaciro yamika mata makemai kafada tayi taki karba hakan yasa yakai hannunshi yakama hannunta yasa mata kafin yay folding hannunshi a kirji yace “destiny family ki lies on your hand, bazaki iya sadaukar da rayuwanki ma iyayenki ba, inhar kin aureni har abada babu abinda zai sami yan uwanki da iyayenki idan bakiyi ba I will take revenge dan ayanzu Babanki ya nemi tsokanata an kashe case yakama direbana again and you know I don’t forgive! Stop crying” yafadi ahankali hakan yasa ta tsayar da kukan, ahankali  kaman mai lallashi yace “will you marry me”? Hararanshi tayi tareda turomai baki tace “babu abinda zanyi da criminal irinka dan Mafia” dan murmushi yayi ganin tanamai tsiwa kafin murya chan kasa kaman dan baby yana kallon fuskanta yace “I’m hungry” har cikin jikinta taji kalman saikuma tajuya tawuce tafita daga office din yabita da kallo ko kallon Dan batayi ba tawuce masallacin school nasu, zama tayi wajen alwalan mata takifa kanta a guiwa what kind of life is this? Wannan wani kalan tsaka kai wuya tashiga, wazata gayamawa, mutumin nan babu abinda bai saniba game da Baba dasu yaranshi harda su Baffa, idan yakashe Baba fa da Ammi da Nana da Farida fa dasu Baffa wazai rage mata aduniya? Amman idan ta yarda ta aureshi bazai musu komi ba kuma ta yarda bazai musu ba dan kaman yana sticking to alkawari, ijiyan zuciya tasauke ta dago tai tagumi tai shiru tana kallon waje daya all this while tanaji azuciyanta tanaso ta ganshi deep down she misses him har kuka take idan ta tunashi amman yau daga ganinishi saitaji inama bata ganshi ba, lectures din dabata koma kenan ba sai wajajen 3 ta nufi gate hakan yasa Aliyu shima yatafi ganin ta tafi dan Baba yace karyabari tasan yana binta, Keke ta tare ta shiga shagon Maman Intee tasa akaita dudda bama tasan dalilin dayasa tace chan ba.




Clinic da Hamad ke aiki yasa Dan yakaishi, suna shiga parking Dan yayi saukowa yayi glasses nashi akan idanunshi babban hospital ne ahankali yake tafiya harya shiga ciki, direct wani office yawuce budewa yayi yashiga kai tsaye daidai Hamad na duba BP wani tsoho dake zaune kan kujera yana sanye da lab coat hakan yasa ya tsaya jikin kofa shiba karaso ciki ba yana kallon Hamad, dasauri Hamad yay murmushi yace “Baba kaje pharmacy zan aika musu da magungunan da za’a baka” godiya tsohon yayi yatashi yazo yafice hakan yasa Hamad yace “kaikuma meya kawoka wajen aiki na”? Maida kofan Maheer yayi yarufe  bayan tsohon yafita sannan yakaraso ciki yana kallon Hamad dake kallonshi, instead of yazauna kan chair wajen observation bed na office din yayi yahau yazauna wayanshi yaciro yana dubawa Hamad duk yana kallonshi yadade baiga miskili kaman Maheer ba ganin baida niyyan magana yasa yazauna yashiga tura magungunan da za’a bama tsohon daya fita to pharmacy kaman daga sama yaji Maheer yace “I want to get married!” Durun dum! Maganan yasauka akan Hamad dasauri yadago kanshi ya kalli Maheer din da kaman bashine yayi magana ba, karasa tura sakon Hamad yayi sannan yataso yazauna kan table yana facing Maheer tareda rungume hannunshi a kirji yace “wazaka aura? Hope ba wanchan matar data haifeka kake shirin aure ba sabida dan ciwon datayi kanka” shiru Maheer yayi sai danna waya yake kaman bazaiyi magana ba saikuma ahankali yace “not she” dasauri Hamad yace “to wakake so ka aura Maheer”? Wannan karan yakai kusan 3min baice komiba kafin ahankali yace “that girl” “which girl”? Hamad ya tambayeshi da sauri dudda already shi yasan wace girl Maheer yake nufi, sake shiru Maheer yayi kafin chan yace “Fateema” “you mean Yasmeen? Yarinyar dakai kidnapping nazo namata treatment”? Murya chan kasa Maheer yace “eh, yarinyar comissioner of police” dasauri Hamad yace “yarinyar da Babanta ya kwace kayanku ai tafadamin ranan” shiru Maheer yayi bai kara cewa komiba sai danna waya dayake wanda Hamad yasan bawai wani abun kirki yake dannawa ba, yadade yana kallon Maheer saikawai yasauko daga table din yakaraso gabanshi hannu yasa ya karbi wayan hakan yasa Maheer yadago kanshi dasauri, sa wayan Hamad yayi a aljihunshi tareda folding hannunshi a kirji cikeda seriousness yace “Maheer kasan what u are telling me kuwa? Yarinyar comissioner of police dayake nemanka ruwa a jallo yay arresting kakeson ka aura? How? Tayaya? Did you even know abinda kakeyi? Maheer kanaso kaje prison ne? Eh”? Hamad yay maganan cikeda damuwa, dan shiru Maheer yayi yana kallonshi idanunshi sunyi ja anatse yace “I don’t care about anything I just wants to marry her” dasauri Hamad yace “is she the reason dayasa ka nemi lecturing a school dinsu”? Gyadama Hamad kai Maheer yayi ahankali, sake yin shiru Hamad yayi yana kallon Maheer din kaman yanda yake kallonshi kafin anatse yace “Maheer son yarinyar kake ne?” Shiru yayi yakasa magana Hamad yace “talk to me, are you in love with her”? Lumshe idanu Maheer yayi kafin yabude murya chan kasa yace “I don’t know, I don’t understand myself, I don’t even know the meaning of all this things danakeyi, I don’t know anything again, all I know, all I see is just her” dudda Hamad so yake yayi murmushi daurewa yayi yace “to tayaya zaka dumfari wannan dan sandan kace zaka auri yarshi kaima kasan bazai taba bakaba wannan ma super story ne, sokake asirinka ya tonu yarinyar ai she will tell Baban ta wayekai” girgixamai kai yayi cikeda damuwa anatse yace “he will never know nine, I will handle the girl” dasauri Hamad yace “tayaya? Wai Maheer kasan me aure kuwa? Aure is not one of your tricks fa? You can’t handle aure kaman yanda kake handling harkan cocaine, Maheer wai kakosan wat you are getting kanka into kuwa?” Lumshe idanu Maheer yayi saikawai yasauko daga bakin gadon azuciye zai wuce yayi kofa hannunshi Hamad yarike yace “ina zaka muna magana”? Azuciye Maheer yajuyo cikin tsananin fushi yace “why are you asking me all this questions? Kasan menake going through? Kasan meke damuna? See Hamad I don’t believe in Marraige you know that but nima bansan meke damuna ba this girl has become like parasite tazo tashiga jinina she’s everywhere in me, the thought and everything is driving me mad, Hamad I see her in my dreams, I see her idan nabude idanu, I see her in everything danake, tunda tashigo rayuwana I can’t handle anything again, not me not my empire, what do you want me to do inba in aureta ba? Maybe if she’s close to me bazan dingajin abinda nakeji ba but why do you keep questioning me Hamad why why why”? Bakaramin baci ranshi yayi ba yayi shiru saikuma chan yanuna kanshi yace “kasanni sama da kowa d normal Maheer daka sani it will take me not less than 2hrs I will kidnap this girl nadauketa tadawo wajena har abada and nothing will happen but no banyi all this ba I want to marry her legally base on addini nasan tana taredani ne amatsayin matan aure not yarinyar danai kidnapping wrongly but why are you asking me all this questions is it because I come to you I can do this myself kasan dahaka ko”? Kafadanshi Hamad yakama anatse yace “calm down Maheer kaima kasan I will always support you, you are the only brother danake dashi aduniya uhmm tambayoyin danake maka is just to look out for u Maheer yanzu mekake so”? Lumshe idanu Maheer yayi Hamad yabishi da kallo wato idan Allah yatashi kamaka baya maka da kyau rana daya Allah ya jarabi Maheer da mahaukacin son yarinyar mutumin dakeson kaishi gidan yari. Bude idanunshi Maheer yayi ahankali yace “inaso karakani muje nama Baba maganan aje a nema mini aurenta sannan mu taushe any loophole dan nasan kafin ya bada auren yarinyar nan saiyay binciken sama da kasa” shiru Hamad yayi yana kallonshi anatse yace “yarinyar fa”? Ahankali Maheer yace “I will handle her ita” jimm Hamad yayi yana kallonshi saikuma yace “wacchan matar fa yazakai da ita” dan yatsine fuska Maheer yayi yace “batama cikin lissafi na she’s not relevant and she will never know” ahankali Hamad yace “Maheer” kallonshi Maheer yayi baice komiba, shiru Hamad yayi yana kallon idanun Maheer din all abinda yagani is sincerity da tsantsan so, gyadamai kai yayi yace “shikenan I will support you nadawo gida anjima sai muje muma Baba magana idan yaso shida Mallon Sani sai suje gidan su ko” gyadamai kai Maheer yayi kafin ahankali yasaki dan murmushi yajuya yafice daga office din Hamad yabishi da kallo har cikin ranshi yasan this is first step na shiryuwan Maheer, idan ta wannan sanadin Allah yakeso ya gyarashi to Allah ya tabbatar da Alkhairi yakara raba shi da matan nan dan she’s not Khair in his life.


✨KK✨

No comments