Breaking News

Kyalkyalin Kauna 42

 EPISODE 4️⃣2️⃣






Jama’a ina sababbin amare da matan aure dasuke so su koyi abubuwan da basusan da akwaisu daba, M shakur dinku is back again with another banging class na MATAN AURE dazan fara muku next month dazaran nagama wannan novel din na KYALKYALIN KAUNA💃💃💃


Classes namu asabar da lahadi ne na tsawon wata daya wato 4 good weekend classes kenan.

Ki shigo class dina lemme teach you how to catch your husband a hannu ba kayan mata ba magani tsabagen iyawa kawai da kwarewa a harkan oza room🥰

Registration is 1k

Chat me up idan kinason shiga wannan class din nawa.

wa.me/+2347012181461


https://vm.tiktok.com/ZM2DAkuct/


9:30 tagama shiryawa dan sosai take murna yau Baba yabarta takoma school, wani Riga da skirts na material ne ajikinta mai kyau, kanta anyi shuku dayayi mata kyau sosai yakara fito da goshinta babu komi a fuskanta jakanta ta dauko da maroon hijabinta har kasa gogagge a hannu tafito daga dakinsu zuwa dakin Ammi, da sallama tashi Baba ne kadai zaune a falo ya shirya tsaf cikin shadda fara dan yau Friday yasa hula tamai kyau ganinta yasa yace “kin shirya”? Gyadamai kai tayi tace “eh Baba” tashi yayi dagakan kujeran yace “muje to” daidai Ammi tafito daga uwardaka tace “tsaya kagani nasa mata kwalli haba yarinya kullum idanu fari kaman ba budurwa ba” turobaki Yasmeen tayi ahankali kaman zatai kuka dan ita bataso, tsayawa tayi Ammi tasamata kwallin aiko take ta rikida, murmushi tayi Ammi tace “to saura janbaki” baki Baba yabude yace “banson shirme school zata ba gasan kwalliya ba” hannunta Ammi taja zuwa uwardaka tace “kai dama kafison kaga yaranka fuskokinsu kaman na maza basasa komi, Bakasan Yasmeen budurwa bace tana jami’a bata gayu ba saurayi” akunyace Yasmeen tace “Ammi” dungure mata kai Ammi tayi tace “dalla barni nai magana kunyan Baban naki kike ai dashi nake, sa’o’inki na gidan miji, ni wlh addu’a na ba dare ba rana Allah yafito miki da miji Allah baki miji nagari mai hankali” tai maganan tana daukan janbaki pink ta shafa mata a lips sannan tadauki brush ta gyara mata gashin giranta ita kanta Ammi saida tasake kallon Yasmeen din tace “ke kinganki Alhamdulillah, Allah kabani diyar yar kyakkyawa, yar budurwan Ammin ta iyyee” lokewa Yasmeen tayi akunyace daga falo Baba yace “let’s go Yasmeen shirmen mamanki yayi yawa” karban hijabinta Ammi tayi ta warware tasamata “wlh kinyi kyau Yasmeen” Ammi tafadi ahankali juyawa Yasmeen tayi tace “bye Ammi” Baba harya fice sallama Yasmeen tama su Yaya da Hajjo sannan tafice motan Baba tashiga Baba yatada motan yafara tafiya sundanyi nisa sannan yace “I don’t want kiyi paying attention to maganganun Mamanki, banson shirmen samari, kada kiyi kuskuren tsayawa kula samari awaje, inhar yaro nagari ne dayasan darajan iyaye idan kuma yana sonki da gaske kafin ma yakulaki zaizo yafara sanarda mu iyayenki mubashi izinin magana dake, inhar Allah yabaki miji bazan hanaki aure ba, amma dai concentrate on school okay banda wasa, kallon maza kokuma magana da maza am I clear”? Ahankali tace “eh Baba, naji” “kina bukatan wani abu”? Girgixa kai tayi tace “a’a” school sukakai Maheer na zaune a motanshi kaman a mafarki yaga Yasmeen tabude gaban wata mota datai parking gaban classes na department nasu tafito hakama Baba, wani kalan sanyi Maheer yaji ajikinshi yakara zuba mata ido yana kallonta tundaga kan takalmin datasa akafa zuwa saman hijabinta, zagayowa Baba yayi yazo ta inda take yana kallon fuskanta hannunshi yakai aljihunshi yazaro handky baiji kunyan kowa da dalibai dake zuwa wajen ba yace “wannan abin da mamanki tasamiki yay yawa” share janbakin yayi yarageshi sosai yarage kadan sannan yakalleta yamaida hannunshi aljihu yazaro dubu biyu yaciro jakanta ya karba yasa 2k ciki yace “ga transport naki idan kun tashi 5 zaki gama lectures yau ko”? Gyadama Baba kai tayi tace “eh Baba” karban jakan Yasmeen tayi Baba yakama hannunta yawuce da ita har ajinsu, class nasu yashiga sai kallonsu ake Yasmeen tasauke kanta akasa Baba nabin kowa na ajin da kallo just to makesure yarshi is safe wani kujera yakaita yace “take care kiyi karatu da kyau ki” gyadamai kai tayi duk kunya yacikata, kanta ya shafa kaman yar yarinya yajuya yafita daga ajin dalibai kowa na dariya kasa kasa wasu na cewa Daddy’s gurl, fitowa Baba yayi daga ajin duk Maheer na kallonshi jujjuyawa yayi yakalli ko’ina kaman mai duba wani abu sai chan Maheer yaga ya maida idanunshi wani bangare daban hakan yasa yakalli wajen dasauri Aliyu yagani Baba nama magana da ido, wani kalan murmushi yayi yace “CP if I want ur daughter ko security dubu kasa I will get her” dan dariya yayi yana kallon Baba daya wuce yatada motanshi yatafi, hakan yasa Maheer yace “let’s leave daganan kaini office dina”.




11 suka fito daga lectures din, jakanta tadauka dan wucewa auditorium yin English, ahankali take tafiya ita kadai dan batada kawa bata iyama yan ajinsu magana kodan harda kowa jijji dakanshi yake as per new student oho, ita kunyan abinda Baba kemata ma yasa ko dagakai ta kalli wata ko wani a aljin bata iyayi, wucewa tayi tana tafiyan nan ahankali anatse zuwa auditorium ancika sosai abinka da yan different department anzo ayi english da kyar tasamu sit a tsakiya ta zauna tareda ciro handout nata na english tana dubawa sai hayaniya ake kaman gidan biki, all of a sudden taji ajin yay tsit kaman anyi ruwan sama an dauke hakanan taji feet nata sun mata wani irin sanyi saiga kamshin turaren da har yau gobe batajin zata manta da kalan kamshin nan ba dawani kalan sauri ta dago kanta ta jujjuya gefenta kaman wani abu take nema saikuma chan kaman ance ta kalli chan stage gaban aji ido da ido tayi da Maheer dake tsaye yasa wani dark blue suit idunshi sanye da glasses bakake amman tasan ita yake kallo, yayi mahaukacin kyau kaman ba dan Nigeria ba, gently yakai hannunshi yazare glasses na idanun nashi yana kallonta still faduwa gabanta ya mugunyi dasauri tadafa table, almost cikakkun 2mins yayi yana kallonta kafin yajaye idanunshi daga kanta yadan kalli student din tareda sakin little smile yace “good morning student I’m Maheer M Maheer your new English master” wani kalan tafi ajin yadauka dan he’s so charismatic kanajin yanda yake turenci kasan ba’a nigeria yay karatu ba ga kyau ga pink lips ga gayu ga tsayi, kowa kallonshi yake both maza da mata babu kyafta idanu.


Dan kallon Yasmeen yayi sannan yadauki marker yajuya to the board kawai yarubuta C.A dasauri ajin yadauki yan kananun magana kala kala.

“Write an Eassay about yourself” 15mins 20mark ya ijiye marker tareda juyowa yana kallon yan ajin da kowa yashiga yago paper banda Yasmeen dake kallonshi, yarinyar dake kusada ita ne ta taba Yasmeen firgigit Yasmeen ta kalleta yarinyar tace “ke bazakiyi test din bane 15min fa yabayar kin tsaya kina kallon sabon malamin kaman baki taba ganin namiji mai kyau irinshi ba” Gyadamata kai Yasmeen tayi tama rude tabude jakanta tadauko long note ta fallo ta ijiye tadauki pen sannan takalli allo tahada essay tafadi tasan me Essay zata iya amman spellings dinne, ahankali tafara rubutun tana tunani dan dago kanta tayi suka hada idanu yana kallonta sauke kanta tayi kasa dasauri tacigaba. 15mins daidai suka dauka yace “time up” hakan yasa kowa yadago ya kalleshi, anatse yace “at the end of the class zakuzo individually to my office kuyi submitting, now let’s talk about Essay” yashiga lecturing nasu kan Essay duk Yasmeen na kallonshi takasa yarda shine a school nasu tunda take tafara school din nan bata taba gane karatu kaman na yau ba, is as if yana bayanin yana bude kanta ne yana juyema ta yana shiga, 12:30 yagama dasu yawuce yafita, class rep yatashi yace “by 1 za’aje ayi submitting” kowa fito da nashi yayi yacigaba da yi wasu na gyare gyare 1 nayi aka fita kusan su 200 aka tafi office nashi classrep namusu jagora, Dan ke tsaye agaban office din dayake kulle yay dressing kaman wani dalibi, one by one ake submitting to Dan saiya kalla yace you can go, Yasmeen sai kallon Dan take saida yakarbi nata sannan yakalleta yace “what is this kika rubuta haka? Take jeki bama Sir da kanki” yay maganan yana bude office, kallon Dan tayi some mutanen yan department nasu dasuka santa sukahau dariya kasa kasa sabida sunsan yanda batada kokari, miyau tahadiye tareda sauke ijiyan zuciya gabanta na mugun faduwa ahankali tawuce tashiga office din Dan yamaida kofan yarufe office ne mai shegen kyau, akan table taga Maheer zaune yazuba mata idanu kaman he’s seeing her for the first time in life, daganan ta tsaya tareda mikamai paper kirjinta na bugawa, binta da kallo yayi zuwa paper datake bashi sannan ya sauko daga kan table din yafara takowa zuwa wajenta yana tafiya one one, kasa jure yanda takeji tayi dawani kalan sauri tajuya zatai kofa dagudu wani kalan fizgota yayi da bala’in karfi tajuyo tafado jikinshi adan zuciye ya mannata abango yana gabanta.


✨KK✨



EPISODE 4️⃣3️⃣


No comments