Breaking News

Kyalkyalin Kauna 39

 


EPISODE 3️⃣9️⃣



KINA NEMAN INDA ZAKI SAYI GANGARIYAN ABAYA? Hadaddu na yan gayu?? Ga Maryam Abaya nan ku shiga group dinta.


‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V



Wani babban private asibiti ne yawanci turawa ne ma likitocin su Parking Hamad yayi yakalli Maheer yace “kadaisan ni bazan bika ciki ba” juyoda kanshi Maheer yayi yakalli Hamad din dan iskan tsaki yasaki baice komiba yabude kofar motan yafita, ganin rana yamai yawa yasa yadawo cikin motan, sun glasses din Hamad yasa hannu yadauka dasauri Hamad ya kalleshi, gira daya ya dagamai yafito bayan ya ijiye komi a motan yasa glass din yawuce ciki, binshi da kallo Hamad yayi saikuma yajuyo ya kalli papers din kasa hakuri yayi hannu yasa ya kwasa yashiga dubawa, lecturing job yasamu a FCE zai dinga koyar da general english ma all student na NCE1 irrespective of courses dasukeyi, shiru Hamad yayi kafin ahankali yakalli hotonshi dake jikin ID card din yace “what are you up to now”? Dan yasan Maheer, girman kai kadai bazai barshi ya koyarda kowa ba dudda brain bus ne Maheer akwai ilimi amman ina, and he definitely knows  cewa he’s not doing it for the money, and he is sure bawai harkan kwaya bane zaiyi a school dinba dan Maheer can never stood that low tunda Maheer yafara business din nan manyan mutane yake saidama kayayyakin shi, ko wannan ministry din daya shiga yasan wani babba yaje yagani, what are you up to Maheer? Hamad yay maganan ahankali kafin ya maida komi ya ijiye yay shiru yana tunani saikuma yabude kofa yafito koba komi rashin lafiya rashin lafiya ne so bari kawai yaje yamata Allah kara sauki.




Yana shiga cikin hospital din da Adamu yafara hada idanu dake tsaye dasu Nas, Wike dakuma Dan suna magana ganin Maheer yasa dukansu suka taho wajenshi banda Adamu daya dauke kai, hannunshi Nas ya kalla yace “meya sameka a hannu Pablo”? Dan yatsine fuska Maheer yayi batare daya basu amsa ba yace “tana ina”? Nunamai dakin Wike yayi yace “tana cikin chan dakin yanzun nan ma tasamu bacci she has been calling your name” wucewa yayi yana tafiya ahankali zuwa dakin ko kallon inda Adamu yake baiyiba shima haka Adamu baicemai uppan ba wanda dama haka suke all this while basama juna magana dan shi he’s not under Maheer kaman su Wike da Nas, he’s yaron Hajiya dan aikenta kaman yanda Hajiya tagayama Maheer da kowa saisa Maheer baida business dashi dan he only talks to mutanen dayakeda business dasu.



Ahankali Maheer yabude kofan dakin yashiga tana kwance akan gado bacci ya saceta ansa mata ruwa dakuma oxygen a hancinta dan jim yayi yana kallonta daganan kofa batare daya karasa cikin dakin ba kaman wanda ke tunanin shiga cikin dakin, motsi Hajiyan tayi kaman wacce taji ajikinta Maheer na wajen saikuma tabude idanunta tar tareda juyo da kanta dasauri jin kamshin Maheer, hada idanu tayi da Maheer dake tsaye wajen kofa ya rungume hannunshi a kirji yana kallonta, wani kalan zabura tayi ta tashi zaune kaman wacce ta zare tace “Pablo where have you been” ganin tana neman dirkowa daga saman gadon yasa yakarasa cikin dakin da dan sauri babu alamun wasa akan fuskanshi yace “ina zaki”? Hannunta tasa dasauri ta sauke oxyen na hancinta takai hannun nata dake rawa sosai tadaurasu akan kirjinta tana wani kalan jiniyan kuka kaman yarinya tace “Pablo yau 6days bansaka a idona ba, baka dauki wayana ba, baka duba messages dina ba, karabu dani ne da gaske”? Yanda take kukan sosai numfashi ke neman gagaranta hakan yasa yakai hannunshi ahankali yakama roban oxygen din zai maidamata a hanci yace “take this back” hannunshi tarike dasauri tana kallonshi ta girgizamai kai jikinta har rawa yake tace “you have to tell me first, karabu dani da gaske? Karabu dani Pablo?” Kaman wacce tazare haka ta dawo, dan lumshe idanunshi Maheer yayi ahankali kafin gently yabudesu yadaura akanta, dan daidaita muryanshi yayi yace “no” rungumeshi tayi tadaura kanta akan cikinshi hannayenta abayanshi tafashe da kuka sosai tace “thank you Pablo, thank you, nagod…” kukan datake yamafi karfinta, tace “wlh idan karabu dani zan iya rasa rayuwana, zan rasa raina I will be so shattered, just thought na I lost you yasa nai landing a hospital kaga kenan idan karabu dani I will die, you are the air I breath, Pablo baby u are my entire life, rayuwana ruhina gangan jikina komi nawa naka ne, wlh wlh bazan iya rayuwa babu kaiba, ina sonka, I love you Pablo, I love you so much kada ka kara fushi dani kaji, bazan kara bata maka rai ba wlh, baran karaba I love you baby” tai maganan tana mama hannuwanshi dasuke sake akasa takai kan bayanta dan shima ya kankameta ajikinshi, karbe hannunshi yayi dasauri tareda saukesu kasa, murya adan taushashe yace “sakeni ki kwanta you need some rest” girgixamai kai tayi dasauri tace “I don’t wanna ever let you go, 6-7days ban ganka ba I cannot just let you goo hakanan, lemme hold you sooo tight Pablo, my baby, I love y……” daidai tabude rinannun idanunta hada idanu tayi da Hamad dake tsaye jikin kofan kusan a kunnenshi tai all the maganganu, jin tai shiru yasa Maheer yadan tureta daga jikinshi tareda juyowa shima hada ido yayi da Hamad daya haderai sosai kaman baitaba dariya aduniya ba, bakin ciki yasa yaja wani mahaukacin tsaki yajuya tareda bugomusu kofa yafice abinshi da sauri shima Maheer yakarasa tureta daga jikinshi yakoma gefe tareda dauke kai yace “just lie down” kwanciya tayi ahankali batare datai musuba sai alokacin takalli hannun Maheer da bandage ke kai tace “what happened to hannunka”? Batare daya bata amsaba yakaraso gabanta dan dukawa yayi yasa hannunshi yaja oxygen din zai maidamata hanci dasauri tabude baki zatai magana hade fuska yayi adan zafafe yace “quiet!” Hadiye maganan tayi tareda gyadamai kai kaman yar yarinya maida mata oxygen din hancinta yayi ahankali yajuya zai fice karab yaji tarike hannunshi hakan yasa yajuyo ya kalleta girgixamai kai tayi hawaye na gangarowa daga gefen idanunta hakan yasa yay shiru saikuma yazauna abakin gadon ahankali batare daya karbe hannun ba, ijiyan zuciya ta sauke ko 2min ba’ayi ba baccin data dade batayiba yayi awon gaba da ita.

.

✨KK✨




    ✍🏻M SHAKUR


No comments