Breaking News

Kyalkyalin Kauna 38

 


EPISODE 3️⃣8️⃣






Jama’a ina sababbin amare da matan aure dasuke so su koyi abubuwan da basusan da akwaisu daba, M shakur dinku is back again with another banging class na MATAN AURE dazan fara muku next month dazaran nagama wannan novel din na KYALKYALIN KAUNA💃💃💃


Classes namu asabar da lahadi ne na tsawon wata daya wato 4 good weekend classes kenan.

Ki shigo class dina lemme teach you how to catch your husband a hannu ba kayan mata ba magani tsabagen iyawa kawai da kwarewa a harkan oza room🥰

Registration is 1k

Chat me up idan kinason shiga wannan class din nawa.

wa.me/+2347012181461


https://vm.tiktok.com/ZM2DAkuct/




Bayan 7 days.


Tun bayan ranan da aka sakota bata kara leka daidai da kofar gida ba, su Farida sunyi resuming school itakuma Baba yace gobe ne zata fara fita, Maman Intee tazo sau biyu ta gaidata dan Baba cewa yayi adinga gayama kowa rashin lafiya tayi saisa tazo ta dubata sannan ta aikamata dasu abinci da snacks Allah Allah kawai take taji sauki dan kaman Yasmeen ne cinikin ta dan rabonta datai ciniki sosai tunda tadaina zuwa shagon, Allah yasama hannuwan yarinyar albarka duk abincin dazata dafa a shagon to sai yayi sold out.


Sosai Yasmeen ta danne damuwan dake ranta amman ita kawai tasan meke damunta duk tarufe ido Maheer take gani, mafarkinshi kullu yaumin saita ganshi acikin mafarki, tunaninshi kamshin turaren shi, kayan da akai kidnapping nata dasu dudda an wanke amman har yau har gobe kamshin turaren Maheer suke she is just remembering everything about him, Ammi dake tsaye agaban dakin tadade tana kallonta yanda taga tana tunani hakan yasa takarasa shigo dakin ganin inuwan mutum yasa tadago kanta dasauri takalli Ammi zama kusada ita Ammi tayi kan gadonsu tace “menene Yasmeen tunanin mekike”? Kanta ta girgixa dasauri tace “bakomi Ammi” dan murmushi Ammi tayi kafin tadaga hannunta tashafa gashinta da aka tsife aka wanke akai parking anjima mai kitso zatazo tamata kitso Ammi tace “kin gaji da zaman gida ke kadai ko? Kowa yatafi school yabarki ke kadai agida ba boko ba islamiyya ba shagon Maman Intee”? Ahankali ta gyadama Ammi kai, murmushi Ammi tayi tace “karki damu gobe Thursday Baban ki yace gobe zakiyi resuming, je dauko littatafan ki nabiya miki Allah dai yasa ba’ayi wani abu nai mahimmaci ya wuce ki ba” tashi Yasmeen tayi ahankali tasauka dagakan gadon tawuce tadauko jaka she’s just wishing ko sau dayane takara ganin Pablo..

*****



Ahankali Hamad ke tuki amotan nashi yana kallon hanya, saikuma yajuyo yadan kallo Maheer dake zaune gefenshi hannunshi rikeda wasu papers dawani ID card anatse yace “Maheer waye wanchan mutumin daka hadu dashi?” Dan dago kanshi Maheer yayi yama Hamad wani matsiyacin kallo kafin cikeda isgilanci yace “client” jinjina kai Hamad yayi yace “meka shiga kayi a ministry na education? Kafito tareda mutumin nan da papers din nan a hannu what is business dinka da FCE dawanan ID card din na lecturer ga hoton ka ajiki” dan murmushi kadan Maheer yasaki yace “me ruwanka da harkana kodan kaga nace ka kaini” cikin fushi Hamad yaci burki yakalleshi yace “wlh darajan hannun naka dayaji ciwo kaci kaima kasan wlh saidai katuko kanka bazan taba kaika inda zakai harkokin ka na banza ba” yatsine fuska Maheer yayi baice komi ba yadauke kai tsayawa Hamad yayi yana kallonshi yace “I don’t know what deal dinka is da FCE yanzu, I just hope ba shirin lunching kwayoyi kake a school dinba” wani irin juyowa Maheer yayi yazubamai manyan idanunshi irin na repeat abinda kace, hannu Hamad yabude yace “to me kakeso nace dan nagama cracking brain dina bansan uban abinda zakaje yi a FCE amatsayin malami ba mugama abinda zaka koyar” Hamad yay maganan yana daukan ID card din yakalla sannan yadago kai yakalli Maheer daya dauke kai yana kallo waje yace “english zaka koyar, kaida ka karanta pharmacy ubanme yakaika koyar da English at this point kafara bani tsoro dan connections din nan naka duk wasu Cabals na garin nan ka sansu sabida kaine head of all the cabals kaika sa……..” tsayar da maganan yayi ganin wayan Maheer na ringing dan kallon wayan Maheer yayi ganin Dan ne yasa yayi picking tareda danna speaker dan baida karfin kai wayan kunnenshi shikuma Hamad yatada motan yacigaba da tafiya.


Cikeda damuwa Dan yace “Sir where are you?” Dan shiru Maheer yayi dan he just sense something is wrong daga tambayan hakan yasa yace “what happen?” Cikeda damuwa Dan yace “yanzun nan Nas yakira yace all of them sunata kiranka number ka baya tafiya, anyi rushing Boss to hospital anyi admitting nata wai bama tasan waye ke kanta ba tanata kiran sunanka” “mtswwwww…” Hamad yaja wani  mugun tsaki dayasa Maheer yajuyo yakalleshi Hamad ya wankamai side harara batare daya kalleshi ba, yakai kusan 3min baice komiba kafin chan yace “which hospital”? Dasauri Dan yace “U.S Hospital” dan jim yayi kafin chan yace “ok” katse wayan Dan yayi, dan dagokai Maheer yayi Hamad dake kallonshi ta gefen ido yana tuki yace “don’t even ask me to take you there kaima kasan anything daya danganci Matar nan that ruin your life banso” dan lumshe idanu Maheer yayi baisake cewa komi ba, kallonshi Hamad yayi saikuma yaji wani iri tsaki yasakeja badan yaso ba yayi kwana da motar suka dauki hanyar hospital din, dan murmushi kadan Maheer yayi batare daya bude idanunshi ba.

No comments