Breaking News

Kyalkyalin Kauna 32

 


EPISODE 3️⃣2️⃣




Please idan kina group 1, 2, 3, ko 4 kada kishiga 5 please BUT YOU CAN SHARE💃💃💃



https://chat.whatsapp.com/Izxc95b7WeW9ciRtgIvSXU



Dakin datake ciki yabude yashiga da ita yana kallon window dakin da drip daya gama zubewa akasa sannan ya zaunar da ita bakin gado, yawuce yarufo window yazo wajen drip din ya kalla sannan yajuyo yakalleta hada idanu sukayi dasauri tasauke kai kasa tana wasa da yatsunta cikin dan kakkausan murya yace “idan kikamin amai agidan nan anjima saikin lasheshi da kanki tunda kin iya zare drip” gyadamai kai tayi dasauri ba musu kaman yar karaman yarinya, juyawa yayi fuuuu haryakai wajen kofa ya tsaya yajuyo yakalleta yace “wat do you wanna eat”? Batare data dago kanta ba cikin yar kankanuwan muryanta mai dadi tace “tea” yanayin maganan ta yayi shima yace “tea” dasauri ta kalleshi watsa mata wani mugun kallo yayi yawuce yafita tareda bugo kofan, dan zaro idanu tayi saikuma tai murmushi sosai harta manta da damuwan datake ciki to metamai yake masifa kuma yanzu, murmushi kawai tayi ta kwanta kaman yar yarinya wlh har cikin ranta kawai she’s happy bamata san dalilin ba, “Maheer is soo cute” tafadi ahankali.


Yana fita kitchen yawuce still bai kalli Hajiya ba binshi kitchen tayi ganin hada tea yake kaman yanda yaga Hamad yayi jiya yasa fuu tafito tayi sama dakinta tashiga ta kulle tadauki wayanta takira Adamu ringing biyu yadaga tace “Adamu wai da gaske nizakama iskanci” ahankali yace “to baki nemeni ba” dasauri tace “kaga banda lokacin fada dakai wlh ina cikin damuwa Adamu” dasauri yace “menene babyta” ahankali ta zayyano mai komi ahaka yace “to mu kashe yarinyar mana Hajiya” dasauri tace “haba kazaci banyi tunanin bane, matsalan shine na kasheta CP will be on my baby neck for life, bazai taba barin Maheer ba saiyaga bayanshi aduniya saisa bazan haka ba, kawai dai sonake na duramata kwayan da saiya tattarata ba shiri yakaita gidansu gobe gudun karna kara bata wani abun, tausayin yarinyar yake sosai, kuma kasan I can’t call factory ko warehouse nasa akawomin zai sani, please kai kasamo mini wani abu kaji Adamu be fast zansan yanda zan na sace key dakin awurin shi” anatse Adamu yace “consider it done Hajiya” ya katse wayan ta tashi takara dawowa falo tana karkada kafa.




Tana kwance taji ana bude kofan dakin dasauri ta tashi tana kallon kofan deep down jitayi takosa taganshi, Dan taga yashigo dakin da tray wanda tea keciki da bread yakawo mata anatse yace “Oga yace akawo miki” bin Dan tayi da kallo daya ijiye komi agabanta ahankali tace “shiya hadamin tea”? Ita kanta batasan ya akayi tambayan yafito daga bakinta ba, dasauri Dan yakalleta sarai yaji tambayanta amman ahankali tace “mekika ce Miss?” Girgizamai kai tayi da sauri batare data dago kanta ba tama kasa magana hakan yasa Dan yajuya yafita daga dakin, kwanciya tayi dasauri akan gadon murya chan kasa tace “what’s wrong with me?” Dan gajeren tsaki taja ta lumshe idanunta tamaki kallon tea dan jitayi haushin tea takeji sabida tambayan datayi.

*****


Bangaren Baba

Baba tunda yafara aikin dan sanda baitaba shiga bakin ciki da damuwa irin wacce ya shiga kwanan nan ba, wato Pablo ya gwadamai cewa baida criminal mind and idan kanason ka kama criminal kaima you have to act like one, yasaki kayanshi yasaki direbobin shi amman basu saki Yasmeen ba sannan number tasu dip batakan network, yayi tracking number Yasmeen all he got from that was mekeke napep nan yabashi labarin yanda komi yafaru which Baba believe yakarbi jakan school na Yasmeen da wayan nata data bari a kekenshi dasuka dauketa.

Duk wani hanya da dabaru babu wanda baibiba baida any lead a case din, bazai karya ba Pablo kam yayi defeating nashi which kanshi yayi blaming, kafin yafara case din nan yakamata yasan waye shi Pablo Escobar din yasan wat he was getting kanshi into but no baiyi hakaba, baiyi protecting family nashi ba ta hanyar zuba yan sanda alayinsu da school na yaranshi all he was after was yakama Pablo and if he’s been honest to get recognition daga government as per dan sandan daya kama number one drug lord na africa gaba daya. Dukan table Baba yayi ya watsar da abubuwan kai yana wani kalan nishi yace “I will never never forgive you for this Pablo! Kama y’ata wani abu I swear by Allah saina wulakanta ka aduniya! Yasmeeen!” Baba yakira sunan Yasmeen ahankali yazauna akan kujera idanunshi sunyi jazur, duk idan yatuna har yanzu Yasmeen na hannunsu sai gabanshi yafadi rabon dayay wanka tun wanda yayi ranan Alhamis dazai tafi office, tun ranan da su Farida suka dawo gida har yau yakasa komawa gida dan baisan tayaya zai kalli mutanen gidan ba most especially Ammi dahar drip anhau samata inji Baffa dake yawan kiranshi yana tambayanshi progress, gashi tun yan layi basu san abinda ke faruwa ba har an soma sani dan daga school din su Farida news din yafara leaking yanzu few mutanen anguwan su ne basusan an dauke Yasmeen ba though ba asan asalin labarin ba amman dai ansan an dauke Yasmeen.

****



Tunda yabama Dan yakai mata tea yawuce study yazauna yay shiru tareda lumshe idanu. “what is wrong with me”? Ya tambayi kanshi dan tunanin Yasmeen kaman zai tsagamai kai, kalaman data fadimai sunmai katutu awuya yakasa mantasu, yakasa hadiyesu, su tsayamai sosai arai, tashi zaune yayi ahankali yabude kofan study din yafito kofan dakin da Yasmeen din take ciki ya kalla, ahankali yataka zuwa gaban dakin yay jim yana kallon kofan kaman yabude ya shiga yakeji yadaure yajuya wucewa yayi yafito yafita waje tsayawa yayi tareda kunna taba yana sha yana kallon makeken compound din nasu da tsuntsaye dake flying daidai lokacin wata mota tashigo gidan, kallo daya yama motan yadauke kai yawuce yay hanyar garden dan he wants to be alone, he wants to clear his head.



Adamu daya gama parking binshi da kallo yayi duk duniya baiga wanda ya tsana yake kuma adawa dashi kaman Pablo ba, he’s envying Pablo sosai, sometimes he wish inama he’s young he’s 32 kaman Pablo ba 46 din nan dayake ba, no be lie Pablo akwai kyau, ga brain, ga gayu, ga body, ga kudi shi baiga abinda Pablo baidashi ba har yanzu dole Hajiya ta mutu akanshi, bude motan yayi yafito yafara tafiya yawuce yashiga cikin gidan, Hajiya na zaune falo ta kumbura tai suntum yana ganinta yayi dariya yazo zai rungumeta wani kallo tamai da sauri ya tsaya hade rai tayi tace “bani sakona katafi bana mood na wasa” dan ijiyan zuciya ya sauke yana kallonta yaso koyaya ne tabarshi yadan da chaji amman yasan ko amafarki dan bata taba bari sunyi abu agidan nan ba koda Pablo bayanan, hannu yasa a aljihu yaciro wani dan kwalba karami ya dunkule hannunshi yabata yace “marfi daya ko ruwa ko drink” sa hannunta tayi ta karba tareda murmushi tace “jeka to nagode” juyawa Adamu yayi badan yasoba yawuce yatafi itakuma Hajiya tawuce sama da sauri dan yanzu ne perfect time yanda yatafi waje shan taban nan, dakinshi tashiga tawuce zuwa drawer spare keys na gidan, da kyar tagano key dakin dauka tayi tasauko tawuce kitchen gora tadauka na faro tabude ta daga kwalban gabaki dayan abin tajuye aruwa.


✨ KK✨




  ✍🏻M SHAKUR


No comments