Breaking News

TABARMAR KASHI Book 2 Page 66

 "HUGUMA*



_TABARMAR KASHI_*



Book 02 Page 66


Maji kamar bata a wajen,saidai tana ankare da komai, dr jarma da hankalinsa duka yake akan majin da duk wani motsi nata,ya dan waiwaya sashenta


"Shifa matsomin da wannan ruwan na gabanki na wanke hannuna" cokalin hannun hajiya mansura ne ya subuce ya fadi, ta watsa kallonta ga dr jarma. Alamu da dama suna mata nuni da yiwuwar faruwar was al'amura


"Meye hadinka da tsohuwar matarka da zata baka ruwan wanke hannu?,duk da nayi kara da alkunyar ciyar da abincin da na girka da hannuna ba tare da nayi qorafi ba"


"'Matarsa dai a karo na biyu ko?" Muryar hajiya qarama ta ratsa hargagin mansura. A gigice mansura ta waiwayo tana kallon fauziyya. Murmushin nan nata dake dauke da tarin ma'anoni ta jefeta dashi


"Af, nayi hanzarin shaida miki maganar da ba'a bakina ya kamata a jita ba ko?, to tunda dai na riga na fada bari na garasa miki.


"Ya isa fauziyya" Dr jarma ya dakatar da hajiya qarama a tsawace


"Da dai ka barni na qarasa yaaya" ta sake fadi tana sakin garamar dariyar da zaka dauka cikin tarin zallar nishadi take


"Da gaske ne abinda fauziyya take gayamin?" Hajiya mansura da tashi d'aya kamanninta suka juye saboda zallar tashin hankali ta furta


"Samu guri ki zauna muyi magana,wanann zaman bana hayaniya bane" dr jarma ya fada cikin nutsuwa da tsare gida


"Ban bugatar zama mahmud,amsa nake nema eh ko a'ah" ta fadi tana rige qugunta wutar bala'i da masifa tana ruruwa saman fuskarta.


Toufeeq da kansa ke duqe,tunda hayaniyar ta fara tashi kansa yake a qasa yana son hadiye nasa bacin ran sal a sannan ya daga kai yana kallon mansura,cikin kakkausar murya yace


"Malama ki zauna akace!!" Ya fada a dan tsawace da bacin rai, ita da hajiya garama din suna cikin sahun farko da a yanzun baisan me ya tsana kamarsu ba


"Karka sake magana toufeeq, ba huruminka bane" mai tace dashi tana tsare gida. Motsawa yayi alamun zai mige yabar wajen, don bayajin zai iya jurewa kallon mansurar tana yiwa Dr haka


"Koma ka zauna, matsala ce da ta shafi kowa da kowa"


Dr jarma ya fadi, sannan ya mayar da dubansa ga mansura


"Shifa matatace ta lalle uwar 'ya'yana,matar da duk duniya tayimin abinda ko.mahaifiyata iya abinda zata iya yimin kenan,wata gaddara da bansan meye silar faruwarta ba ta datse igiyar aurena da ita,na jima ina addu'a da bansan iya adadinta ba,a yanzun haka shifa na matsayin matata ta sunnah, an maida aurenmu a Algeria qarqashin jagorancin kawunta"


"Tabbas!" Hajiya garama ta rufe da fadin haka duk da bata jin ko mansurar tana jin dacin da takeji a zuciyarta akan dawowar maji gargashin igiyar auren dr jarma din.


Saidai a yanzun mansurar ce first target dinta, tanason ta nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane.


"Mahmud saidai kuwa ka zaba,ko ni ko shifa wallahi tallahi!" Ta furta tana buga table din gabanta


"'Maji kina gani fa!" Toufeeq ya fada yana yunqurin migewa cikin huci


"Koma ka zauna Muhammad!" Ta sake daka masa tsawa.


Da garfi ya koma ya zaune kan kujerar tasa. Säahar da ta tsorata da irin fushin da take gani kan fuskarsa ta laluba hannunsa cikin tafin hannunta. A hankali ya juyo ya zuba mata jajayen idanunsa, sai ta lumshe idanunta hadi da budesu ta kuma matse hannunsun guri guda, abinda ya kawo wani gwaggwaban gudun mawa,ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya can qasa yadda babu me jinsa yace


“can't take it moon"


"For maji's sake" ta maida masa a taqaice.


"Bazan tsaya doguwar magana ko bata bakina wajen gaya miki na san wacace ke, nasan irin zaman da nayi dake dukka shekarun da muka kwashe ba,amma ina me shaida miki na bar miki dukka dukiyata da kika dinga diba da kadan da kadan kina tarawa….amma kuma ina me farincikin shaida miki,NA ZABI SHIFA, NA ZABI SHIFA,NA ZABI SHIFA, don haka na sakeki saki daya,na sakeki saki biyu....”


"Dr!" Maji ta gwala kiran sunansa da garfi saboda ta fahimci me yake shirin qarasawa aikatawa,saidai kiran sunan nasa da tayi sam bai sakashi ya dakata ba sai daya kai inda yakeso yakai din


"Na sakeki saki uku ni Mahmud jarma, ku shaida" tsaf labiba dake zaune saman daya daga cikin kujerun dining din ta sulale tayi zaman dirshan qasan marbles din dake gurin ta saki wani irin kukan tashin hankali. Cikin izza da tagama da madaukakin farinciki haseena dake daura da ita ta waiwaya tana kallonta,sai taja kujerarta gefe tana tabe baki


"Su ungulu sai a shirya komawa gidan tsamiya ko?, abar masu abu da abunsu, banzar da akazo ci bata samu yadda akeso ba,sai a tashi aje gida". Maganganun haseenan sun sake jefa labiba cikin magurar tashin hankali, don me yasa mommyn zata bari har haka ta faru? me yasa zata janyo mata wanna babbar asarar?, gwara ita ta samu ta abinda ta samu,ta kuma tara abinda ta tara, amma ita fa?,ba toufeeq din, kuma bata tara komai ba.


Kai tsaye mansura ta juyo tana aje kallonta ga hajiya qarama, ta san shaidanci da shu'umancinta,lallai ita fa qulla wanna abun, dawowar shifa da kuma sakin da dr jarma yayi mata a yanzun, saidai batasan cewa har kanta da kanta ta ballowa ruwan ba


"Tabbas kin cika shu' uma,sannan na sake yarda ke kike aura masa mata ki kuma saketa a duk sanda kikaso kamar yadda kikayi igirari...... Mahmud" ta fadi tana waiwaya ga dr jarma. Yadda ta kira sunan nasa yaja hankalinsa


"Duk cutar da nayi maka ba zata kama gafar wadda fauziyya tayi maka ba,duk wani ha'inci da na aikata maka baiyi rabin rabin wanda jininka tayi maka ba. Ha'inci cin amana da ha'intar gauna tana kasnacewa me saugi ne akan ace makusancinka ne yayi maka, yau zan fito maka da ainihin wacece fauziyya da fuskarta da baka sani ba" sai ta tsugunna qasan table din.


Wata tsohuwar leda ta dauko da tasha qu|li ta fara kunceta. Kallon ledar kadai hajiya garama tayi hanakalinta yayi mugun tashi. Ashe!,har yanzu bata samu damar badda sahun wannan abun ba? ita kuwa ta yaya zata bari mansura tayi mata irin wannan tonon sililin a yau wanda yake dai dai da mutuwarta murus. A zabure. ta mige tana nuna mansura


"Qaryarki tasha qarya mansura,dama ashe da gaskene shi matsiyaci idan ka daukoshi daga rana zuwa inuwa yana hucewa burinsa na gaba shine yaga ya tunkudaka wannan ranar?, to kin makaro,duk wani sharrinki don ki shiga soyayya da fahimtar juna dake tsakanina da yayana da yaransa baki isa ki shiga tsakanin wannan hadin da ubangiji ba" murmushi me ciwo mansura ta fidda tana dakatawa daga bude ledar


"Ki bari na kammala fito da abinda ke ciki idan na gama nuna tawa shaidar kina iya musawa ko hajiya me gaskiya ) da amana?" . Koda Karen mahaukata ne ya cijeta ta yaya zata bari mansura ta kunce wannana ajiyar,sai ta maida dubanta ga dr mahmud wanda idanunsa yake a kansu yana kallonsu..


Kuka ta saki cikin salon da take amfani da shi a duk sanda takeson cimma wani buri nata akan yayan nata


"Dama na sani akwai mutane da yawa a duniya da basason suga kulawa cikin idanunka a kaina, to matarka da na yiwa halacci ashe tana ciki, kada ka saurareta yaaya,wallahi tallahi kome zata gabatar maka garya ne"


"Fauziyya!" Maji dake zaune tana karantar dukkan wani motsi na fauzivvan ta kirayi sunanta. Fitar sautin muryar maji da yadda ta kira sunan nata da wani irin amon sauti ya sakata waiwayowa ta kalleta


"Ki nutsu kinji fauziyya,ita gaskiya fure take ai bata

'ya'ya, gaskiya bata bugatar rantsuwa ko ay mata ado don a gawatata a idanun mutane a fidda ainihin kamanninta,tafi buqatar a qyaleta da zahirin kalarta...

...banga abun tashin hankali ba akan leda kawai

da ko budeta ba'a kai ga yi ba,ki dakata ta fadi duk abinda takeson ta fada din, ita gaskiya zatayi halinta da kanta" maganganun shifa sunyi dai dai da abinda Dr jarma yakeson fada,wanda tsabar mutuwar jiki ta hanashi furtasu. Haka kawai yaji jikinsa yayi wani mugun sanyi kamar babu laka a tare dashi.


"'Fauziyya kenan" mansura ta fadi tana ware ledar cikin karsashi da qwarin gwiwa.


Qulli biyu ne cikin ledar ta ajjiye qaramin ciki, sannan ta bude babbban. Wasu irin tarkace ne a ciki, wasu gananun tukwane da wasu tarin allurai da layoyi masu yawan gasken, sai ginin mutum mutumi guda biyu kowanne jilkinsa zagaye da allurar da layoyi da wasu gananun abubuwa kamar danyan nama yana wari wari.


Da mugun hanzari har tanayin taga taga kamar zata fadi hajiya qarama ta mige tana duban mansura, ilahirin jikinta da bakinta suna rawa. A ina mansura ta tono wanann tsimammen sirrin da ya dauki shekaru kusan talatin a binne?.


"Mansura!!!" Ta kirata da garfi, kiran da ya maido idanun kowa kanta. A take kuma kaicon yadda take qoqarin tonawa kanta a siri ya kamata,sai ta koma da baya ta zauna kafin irin da ta soma ji yana yawo da ita ya kwasheta ya zubar


Ko kallon inda hajiya garama mansura batayi ba gaban maji da Dr jarma ta turasu tana dubansu


"Wannan duka an shiryasu ne saboda ku,a raba tsakanin zucivarka da ta shifa,a raba tsakanin shifa da nadeeva Muhammad dake da gauna da qulafucin uwa a cire masa shifa daga zuciyarsa, sannan a mantar da shi uwarsa,saboda shi din namiji ne,yana da

power taurarinsa tun a wancan shekarun sun haska,sun nuna kuma shi din rayuwarsa na cike da arzigi me yalwa da ya ninka na mahaifinsa, fauziyya kuma ta shirya ita daya zata mori wannan arziqin, daga nasa har na ubansa sai wanda taga dama"


"Qarva kike mansura,garva ne wallahi " haiiya garama ta fada cikin hargagi tana nuna mansura da yatsa,duk da ciwon da kanta ya fara kamar zai rabe gida biyu.

Murmushi mansura ta sake mata tana jin farincikin yadda fauziyya ta soma birkicewa tana fita daga saitinta,alamu kuma suna nuna dukka dabarunta sun fara qwace mata.


"Saurin me kike fauziyya? idan duka kin musa wadan nan saboda daga ke sai malaminki kuka shirya shi,bakisan ina biye da kowanne taku naki ba,wannan ai baki isa ki garyatashi ba" ta fadi tana takawa dauke da qaramar ledar tana garasa budeta, sannan kanta tsaye ta isa ga tafkekiyar TV plasma din dake dining room din. A nutse ta jona komai, ta cire garamin memory card din ta soka shi a gefan tv din. Cikin qasa da second goma yayi loading ya hau,video clip guda daya ne akai, hajiya mansura ta daukj remote din tayi clicking akan video din.



_TURK'ASHI_*



Zafafabiyar

No comments