Breaking News

TABARMAR KASHI Book 2 Page 65

 "HUGUMA*


*TABARMAR KASHI_*


Book 02 Page 65



Zucivarta kamar zata fado take takawa zuwa bedroom din Dr jarma din. Hankalinta na tashi idan duk second daya da zai shude idan tayi tunanin ko dai fauziyya ta sanya Dr jarma ya dawo da shifa dakint? tunda dai kalamanta hakan suke nunawa yana shirin faruwa. Kai ta girgiza, indai hakanne har abada ba ) zata taba yadda ta zauna da shifa ba, ba zata taba aminta wata mace ta shigo mata gidanta ba gidan data ciwa burika masu yawa,take kuma sanya ran ita daya ce macen da zata yiwa dr jarma takaba ta kuma karba tumunin takabar ita daya.



Fuskarsa cike da nishadi yake cire kayan jikinsa da zummar yin wanka,jya walwalar dake saman fuskarsa ya sake dasa mata matsananciyar fargaba "'Drya akayi na ganku tare da maji ne?, dama tare kukayi tafiyar?" Waiwayawa yayi ya dubeta yadda ta cake tana masa tambayar wadda tafi kama da titsiye. Kansa ya dan kawar yasan akwai dan rashin kyautatawa da yayi mata,a galla ya shaida mata koda ta waya ne zai maida aurensa


"'Me kikeson ii mansura?"


"Ka maida matarka ne?" Sake maida dubansa yayi a kanta


"Me kike ci na baka na zuba?, ki barni na watsa ruwa mana, ba tun muna can kika gayan kin shirya mana liyafa tare ba?" Kai ta jinjina masa kawai


• "Okay, bari na watsa ruwa na fito, saikiyi gogarin shaidawa kowa ya fito akan lokaci aci abincin tare. hakan dama va kamata lokaci lokaci a dinga yi, saboda vana kawo hadin kai da garin fahimtar juna" bata iya amsa masa ba har ya wuce zuwa bandakin,sai ta furzar da iska daga bakinta,ta dunqule hannunta ta daki dava tafin hannun nata, ta koma ta zauna ta kirayi daya daga cikin masu aikinta tace ta sake shaidawa kowa,amma sashen toufeeg a shaida musu ta waya. Ajiye wayar tayi gaba daya tana jin nutsuwa tana yin qaura daga gangar jikinta,duk yadda taso bawa kanta qwarin gwiwa da kwantarwa da kanta hankali abun ya faskara, sai ta bude wavarta ta hau shirya komai cikin shirin ko ta kwana koda

bugatar hakan zata taso.


Tun a hallway ya din bedrooms dinsu ya fara rage

mata kayan [ikinta,yana tsaye daga bayanta yayin data dogara dukkan wani garfi nata a jikinsa,cikin wani irin slow motion suke takawa shida ita,sadarwar skin to skin din dake a tsakaninsu tana rura wutar dake zukatansu gaba daya. Ta dauka yana isa qofar bedroom dinsa zal bude, sai taga bai tsaya ba har dai dava isa gaban full length mirror din dake bangon garshe na hallway din. Tar surarta da tashi suka bayyana a jikin madubin, tsananin kunya ta sanyata juyowa da sauri ta bawa madubin baya tana boye kanta a qirjinsa.


Wani galabaitaccen murmushi ya saki yana ci gaba da kallonta ta cikin madubin, yana jin yadda zuciyarsa ke sake laushi tana narkewa cikin soyayyarta. A nutse ya sanya lausasan tafukan hannunsa ya dago fuskarta yana kallon tsakiyar qwayar idanunta. Irin wanann kallon yana da bala'in tasiri cikin zukatan da jikkunansu su duka,musamman da suke kan irin wannan yanayin


"'Biyan bashi zanyi yau din,i hope you're ready?" Wani lallausan murmushi da tasan vana tarwatsa duk wata

nutsuwa tashi ta sakar masa,sanann tayi farrr da fararen idanunta da suka qara haske sosai,da zazzaqar muryarta tace dashi


"Babies sun shirya sada zumunci da abbynsu...

sassauta muryarta sosai


"Nima ummien babies din a shire nake,i crave for you since


"Shshshsh" ya furta yana murmushi hadi da dora yatsansa saman labbansa yana sakin murmushi


"I know,i can read it ta can gasan wadan nan fitinannun idanuwan" tabe baki tayi kamar me shirin sanya masa kuka


"You mean.....na zama fitinanniya fa?" Qaramar dariya ya saki


"Ba ke bace ai nasan laifin babies ne"


"Allah Allah nasan ni kake nufi" ta furta tana narke masa tare da dunqule hannunta ta daki qirjinsa. Hannu daya yasa ya dafe saitin zuciyarsa hadi da lumshe ido


"Ya salam ya Allah, maji zata illatani, bayan ban fara komai akan sonta ba,zo muje ki gani,na tabbatar hallway din nan yayi mana kadan" sai ya dauketa ya wuce nutsatsen bedroom din nan nasa dake da wani irin tattausan yanayi dake garawa zukata da feelings na masoya armashi.


Yadda a yau din ya susuce a kanta sai da abun ya bata mamaki ya kuma tsaye mata sosai a rai, don daga ita har shi din sun aminta da juna maqura,sai ya dinga jin kamar säahar din an sake sabunta masa ita ne,da ayar ta samu ta lallabashi ya shiga wanka itama ta wuce nata dakin don ta shiva,ranta da zuciyarta cike fal da mamakin sauyawarta,bata gajiya ko kadan da bugatuwa zuwa ga toufeeq din


"Allah yasa kici gaba da tabbata a haka koda bayan kin bani ajiyata ne" furucin da ya fada mata kenan a dazun yana gangame da ita.


Tsaf ta shirva cikin wani material me sulbi sosai

cream color da adon brown flowers da wani avalli a jiki.

Ta kusa mintuna ukun tana tsaye gaban madubi tana kallon kanta da kanta, bataga laifin toufeeq ba, dole ya sake haukacewa a kanta ya kuma sake manne mata, fuskarta ta aje wani kyau na musamman tayi mugu mugun yin fresh.Qaramin murmushi ta saki tana daukan wani siririn turarenta dake da wani sirrintaccen gamshi ta feshe jikinta da dashi sannan tasa wasu slippers masu taushi a gafarta da suka dace da kalar material din jikin nata.


Har ta juya ta dakata,ta dawo da bava tana duban cikinta. Har yanzu a shafe yake ga idanun mutane saidai idan ta sanya English wears ko kuma ta dora hannun nata saman mararta shine take iya jin tasawarsa. Ko a yanzun saman mararta ta dora hannun nata, ta shafi cikin a hankali, iva tudun nasa da takeii kadai vana saukar mata da wani irin farinciki me tarin yawa,qauna mara misaltuwa da ita kanta batasan adadinta ba akan cikin.


Yadda soyayyar mahaifinsu ke haukata a ranta, haka kullum rana takejin soyyayar 'yan tayin. Duk wannan abun kuma sai taga kamar toufeeq ya fita gaunarsu da nuna tsantsar kulawa. Kullum Allah shine da kullum sai yayi aqalla mintuna kusan hudu ko biyar kunnensa yana saman mararta wai yana gaisawa da biyunsa, hakanan kullum sai ya sanya tape ya auna tsaho da fadin cikin wai yaga sun qara girma?. Tun abun yana bata dariya harma ta riga data saba.


"I love you and your daddy so much"


"'Daddyn nasu shima yana masiliifar gaunar mamansu" taji an fada daga bayanta. Da hanzari ta juyo don bata tsammaci tsaiwarsa a gurin ba. Yana jingine da gofa hannuwansa goye a qirjinsa yana mata wani narkakken kallo. Sosai kunya ta kamata, batasan me yasa yakejin dadin yi mata labe yaji tace masa i love you ba, kunyar ta sanyata jan gefan mayafin boubou din tana sunne fuskarta a jiki.


Dukka hannuwansa va bude mata yana dariya


"Come-on babe bea, ba kalmar da yafi dadi a bakinki irin inji kince I LOVE YOU MY NUGGET the best name da nafiso bayan duk wani suna da za'a kirani da shi idan ka cire MUHAMMAD dina, taho taho" y fada yana sake ware mata hannuwansa.


Iya takun data iss gareshi kawai sun tafi da imaninsa,sanann ya sanya tana isa gareshi ya bata hotties kisses ssman fuskarta wuyanta da goshinta,ya tsugunna sukayi hirarsu da yaransa kamar yadda yake fada sannan ya riqe hannunta suka nufi main parlor na gidan kamar yadda aka sanar masa.


Kamar ma kowa su yake jira,don duk sun samu kowa cikin parlor din, maji na zaune gefe guda ita da nadeeya suna magana qasa qasa, fadeela na cinyar Dr jarma,hajiya qarama haseena na gefanta itama,hakama hajya mansura labiba na zaune daura da ita.


Kallo daya zaka yiwa kowa dake wajen kasan zukata na cike da abubuwa masu tarin vawa da zukatan kadai aka barwa sani akan su. Sallamarsu ta maida hankula a kansu,zukatan maji dr nadeeya da fadeela cike da farinciki da alfaharin ganinsu. Yayin da mansura labiba da hajiya qarama abubuwan da suke zakatansu sun banbanta da na juna.


Wani irin kallo na qurilla hajiya garama takebin säahar dashi, irin kallon da tunda suka je germany har suka dawo bata yi masa irinsa ba sai yau.


Qirjinta yayi wani mugun bugawa sanda sahar din ke kaiwa gasa tana musu barka da warhaka. Idanunta ta maida ta kulle tana fadin


""Na shiga uku" saboda tudun data hanga daga gasan mararta


"Yaushe tayi wani cikin har ya fito?, bayan a yanzun shine lokacin da zanyi kyakkyawan shirin cireta daga jarma family?, fita kuwa ta har abada? ba irin fitar da ameesha tayi ba tabar musu irin FADEELA?, ko dama qarya yakeyi mata toufeeq?, dama ba miscarriage tayi ba?" Wani mugun sarawa kanta yayi, har sai da takai hannunta da ya fara rawa ta dafe kanta tana sake kulle idanunta


"Relax.....relax mana fauziyya‚u are a strong woman" ta gayawa kanta da kanta, saita bude idanunta cike da qwarin gwiwa tana furzar da iska me zafi daga bakinta.


Kowa ya kama gurin zamansa,kamar yadda toufeed ke zaune kusa da säahar din, nadeeya da hajiya mansura ne suke serving, saidai shi din kuma ya kasa ya tsare. Bayajin zai iya barinta taci komai dake wajen, zuwa yanzu mutum uku ya yarda dasu akan säahar din. Maji cs ta farko sai nadeeya sai kuma baaba ramatu.


"Me zakici ne surukata?" Hajiya qarama dake fidda shu'umin murmushi ta tambayi sahar idanunta yana tsakanin fuska da cikin säahar. Motsawa kadan säahar tayi, bagin matar yana sake mamaye zuciyarta,taso ace wannan tambayar tayi mata ita ne lokacin da babu mutanen da takejin nauyi da ganin qimarsu a wajen, tabbas da ta bata cikakkiyar amsar da zata isar da

L sago, ba iya kanta kadai ba,har izuwa kunnuwan gadangarun 'yammatan dakeson shiga rayuwar toufeeq din nata.


"Karki damu da abinda zataci,ke dai ki lura da abinda zai iya zuwa gabanki" toufeeq ya bata amsar da wani irin qwarin gwiwa hadi da wani tsattsauran kallo cikin idanunsa. A hankali ta janye idanunta daga kansa gabanta yana faduwa,iya kallon da toufeea yakeyi mata a yau ya dasa gaqgarfan zargi a ranta


"Akwai abinda yake faruwa" ta bawa kanta amsa.

"Tabbas akwai ayar tambaya,tsahon shekaru sama da ashirin ban taba gain irin wannan kallon daga idanun Muhammad ba" ta sake jaddadawa kanta tana recalling abubuwan da suke faffaru tsahon satittikan da sukayita wucewa.



Zafafabiyar

No comments