Breaking News

Kanwar Maza Book 2 Page 9

 


Cikin ƙarfin hali da kuka, matar ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri, ku tau


saya mini halin da nake ciki, ku sallameni, ko dan halin da nake ciki, cikina saura kwanaki kaɗan na shiga wata tara, dan girman Allah ko nawa ku ke so ku kira gidanmu, za su baku ku sake ni".


"Ke ki rufe mana baki, ke zaki gaya mana abin da zamu yi?"


"Ba abin da zaku yi nake gaya muku ba, taimaka mini zaku yi, dan Allah ku duba halin da nake ciki"


Banza suka yi da ita suka cigaba da abin da ya dame su.


Ruma tana fama da kanta, amma sai bin matar take da kallo, ƙarshen tausayi matar ta bata. Galibin waɗanda aka ɗauko ruma da su, da waɗanda ta tarar an sallami wasu, wasu kuma an kashe su, sannan kuma kusan kullum akwai wanda mutanen za su kawo.


"Ki yi haƙuri ki daina kuka, ki yi addu'a" ruma tayi maganar cikin sanyin jiki.


Matar ta kalli ruma ta share hawayenta, ta ce "To, Allah ya kuɓutar da mu, sun kashe mini direbana ma, ya iyalinsa za su ji?" Tayi maganar cikin kuka.


Ruma a ranta ta ce "Lallai wannan 'yar gata ce, har direba ne da ke"


A haka dare yayi, matar nan na ta kuka, abinka da farar fata ta koma jawur saboda kuka.

Suna nan a  zube a wurin kamar shara, ga wata irin iska da ake yi mai sanyin gaske, ga yunwa na damun ruma ga ciwo, dare ya tsala ruma ta kwanta ta takure, saboda yadda sanyi ya takura mata. Matar nan kuwa tana zaune tana cigaba da aikin kuka, gaba ɗaya a tsorace take da wurin sai waige-waige take, ita ma tana sake dunƙule jikinta saboda sanyin da take ji.


Idon ruma biyu tana kallon matar, a hankali ta matsa kusa da ruma zata kwanta a ƙasa, saboda ta gaji da zaman ga ɗan cikinta ya dunƙule mata wuri guda, cikinta yayi mata babu daɗi, hannunta ne ya taɓa na ruma, ta ji yadda jikin ruma ya ɗau zafi sosai, ta sake kai hannunta goshin rumaisa ta ji kamar an kunna wuta. Ta ɗan jijjiga ruma amma ba ta motsa ba.

Ta cire ɗankwalin kanta ta rufawa ruma a jikinta, ta kwanta ta miƙe ƙafafuwanta, sai dai ba aje ko ina ba, matar ta fara tari da atishawa wanda hakan ba ya rasa nasaba da sanyin da yayi mata yawa.


***

Katafaren falo ne mai girman gaske, kai kace wata fadar ce, saboda girma da tsaruwar falon, Hajiya Jamila ce zaune a kan wani lallausan carfet a ƙasa, yayin da wani babban mutum ke zaune a kan kujera.


"Ina jinki Jamila, ina fatan dai ba wata matsalar ba ce?"


Ta sake duƙawa ta ce "Allah ya ja kwanan mai girman wambai, matsala kam ba za a rasata ba".


"To Ubangiji Allah ya warware mana, meke faruwa?"


"Allah ya taimake ka, tatsuniyar gizo dai ba ta wuce ƙoƙi, ƙarar giwa na kawo maka" sai kuma ta yi shiru.


Ya ce "Ina jinki".


"Allah ya baka yawan rai, na rasa gane in da ta dosa, ban san menene a ranta game da ni da yarana ba, 'ya'yanta ne manya, nawa ƙanana ko da kishi a tsakanin mu, ai bai kamata zumuncin yaranmu ya taɓu ba, shikenan ina son ganin su Nusaiba amma ba sa zuwa in da nake, shi kansa mai babban suna sai ya shafe wata bai taka in da nake ba, wataran tamkar zai dakeni, na rasa irin wannan abu. yaranmu ai abu ɗaya ne a ganina, amma sam yaran nan ban san kallon me suke yi mini ba, gaisuwa sai sun ga dama suke yi mini, mussaman wannan buzuwar yarinyar ni na gaji da irin wannan zaman da muke yi" ta ƙarasa maganar cikin damuwa.


Wambai ransa ya ɓaci ya ce "Shi takawan da kansa yake wannan rashin albarkar? Aikuwa albasa ba ta yi halin ruwa ba, haka ya canza hali? Har galadima mai ci yana batun zai yi murabus, mun fara tattaunawa a kan akwai yiwuwar a dawo muku da sarautarku, tun da ya kawo ƙarfi, kuma shi galadima babu lafiya, ina daf da kai maganar ga mai martaba, to a haka za a bashi mulkin yana wannan rashin ɗa'ar?"


Gaban Mummy ne ya faɗi, jin batun wambai na cewa za a dawo da sarauta gidansu a bawa Adam.


"Allah ya baka yawan rai, ni ba ziga ba, kuma ba wai ina kushewa bane ba, amma takawa ai ba zai iya jagoranci ba, ya fiye zafin zuciya da saurin fushi, abu kaɗan idan su Fauziyya suka yi masa ba ka ga cin mutunci ba, kuma kar ka manta bashi da cikakkiyar lafiya, larurar nan da yayi tun yana yaro haryanzu fa tana tashi, ai gara a bawa mahamud duk da shi ma da sauran ƙuruciya a kansa, ko a barwa Jabir kawai"


Cikin mamaki wambai ya ce "Kina nufin haryanzu takawa bai warke ba, amma ta ja bakinta tayi shiru balle a cigaba da nema masa magani? Meke damun Binta ne?"


"To ban sani ba idan ka shiga lamarin ko a samu mafita, amma takawa bai dace da sarautar nan ba ba zai iya ba, gara Mahmud amma Mahmud haryanzu hankalinsa da saura, ai gara a bawa Jabir, idan yayi murabus shine yakamata ya gaje shi"


Wambai ya ce "Wannan ba huruminki bane ba, sai abin da muka yanke, tashi kije zamu san abun yi".


Mummy ta duƙa ta ce "Allah ya baka yawan rai, a huta lafiya" ta tashi ta bar gidan.


***


Mai sunan Baba ne yayi rigingine yana kallon saman roofing, zuciyarsa sai bugawa take yi, yana ji a ransa da ya san direction ɗin da zai nufa ya tarar da in da aka kai ruma da sai yaje ko da zai mutu a can, babban fatansa kar a lalata rayuwar ruma, gashi tun yana buga waya ya ji ya ake ciki, har ya haƙura, dan babu wani labari mai daɗi an doshi sati na biyu.

A hankali ya tashi ya buɗe ƙofar ɗakin su ya fito tsakar gida, ya ga ƙwan ɗakin mama a kunne.

A hankali ya ƙarasa ya tsaya ta window ɗakinta ya leƙa, mama na zaune ta ɗaga hannayenta sama sai zubar da hawaye take yi.


Har ya shiga ɗakin ba ta sani ba, ga furar da ya kawo mata da magariba ko taɓawa ba ta yi ba.


Motsin da ta ji ne ya sanya tayi saurin goge hawayen ta ce "Babana ba ka yi bacci ba?" Ya zauna a gabanta ya ɗan kalleta ya ce "Ba ki sha furar ba, ki yi haƙuri ki daina zama da yunwa" ba ta iya ce masa komai ba sai kallonsa da take yi.

"In ɗauko miki kofi ki sha?" Yayi maganar a hankali.


Hawaye ne ya cika idonta, ya miƙa hannu ya ɗau kofin da ya kawo mata tun a lokacin, ya tsiyaya mata ya ce "Ki sha ko kaɗan ne"


"Ba zan iya ba, na san ruma ba ta sha kamar wannan ba, kar su lalata mini 'ya babana na fara karaya" tayi maganar tana rushewa da kuka.


Kamar zai yi kukan shima, ya dake duk da yadda zuciyarsa take masa zafi.


Ya kai hannu yana goge mata hawayen ya ce "Duk abin da ya sameta dama Allah ya rubuta mata faruwar hakan, amma addu'armu tana tare da ita a duk in da take, damuwar ki kawai ta isa ta ƙara mana zullumi, ki kwanta ki huta ki cigaba da yi mata addu'ar.


Haka ya lallaɓa mama ta kwanta, ba dan yana saka ran zata yi barci ba, sai dan fatan zuciyarta da ƙwaƙwalwarta su samu salama.


Ya tashi cikin sanyin jiki, ya tafi ɗakinsu, sai dai yana zuwa ya tarar da Huzaifa da Yasir sun haɗa kai da gwiwa suna ta uban kuka, Abubakar yana rarrashinsu, Abdallah ma ya haɗe kai da gwiwa usman kuwa ya zuba tagumi yana bin su da kallo, hannunsa riƙe da Alqur'ani, Aliyu ne kawai a kwance shima kuma ba bacci yake ba.


A hankali mai sunan Baba ya ja da baya, ya koma tsakar gida ya zauna, yama rasa ina zai saka kansa, shima da hali kukan zai yi, ya riga ya gama karaya.


Wayewar garin Allah, jikin ruma ya ƙara tsanani, sai rawar jiki take tana kwarara wani irin koren amai, ga kukan ciwon ciki da take yi duk ta fita hayyacinta.


Babu wanda ya damu da halin da take ciki, sai wannan matar, da a yanzu ba ta kanta take ba ta ruma take, saboda tausayin da take bata, sai sannu take yi mata, tun tana iya amsawa, har ta daina .


Cikin damuwa matar ta ce "Dan Allah bawan Allah ku taimaka ku kai yarinyar nan asibiti, kar ta mutu a haka, wallahi tana jin jiki sosai".


"Idan ta mutu meye naki? Ki ji da kanki mana uwar shishshigi" wani daga cikinsu ya bata amsa.


Cikin damuwa ta ce "Amma yarinya ce, dan Allah ku taimaka ko magani ku sai mata kar ta galabaita" banza suka yi mata suka cigaba da shaye-shayen su.


Kamar zata yi kuka, sai sannu take yi wa ruma tana dafa goshinta.


Ruma kuwa sai jujjuya kai take tana kiran sunan mama, duk ta fita kamar ta shekara tana ciwo.


Ko da rana ta ɗan ɗaga idon matar nan yayi ja, jikinta sai rawa yake saboda yunwa da take ji, ga ɗan cikinta sai motsi yake, ga mura da ta addaba mata, amma tafi tausayin halin da rumaisa take.



Mijin iya ne wato dagaci a tsaye a tare da wannan dogon mutumin da su ruma suka taɓa haɗuwa da shi.


"Dan Allah dogo ku taimaka dan zatin Allah ku sako yarinyar nan, ko ku faɗi abin da za a baku, ba 'yar garin nan bace ba, a mayar da ita hannun ahalinta wallahi marainiya ce".


Dogo ya ce "Ni ba 'yan ƙungiyar mu ne suka kawo farmaki ba, kuma dama yarinyar na ga kanta yana rawa, tun da aka kai wannan lokacin ba su ce muku komai ba, wataƙila sun kasheta".


Cikin kiɗima dattijon ya girgiza kai ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan girman Allah tun da baka tabattar ba ka duba mini, waɗanda suka sako suka dawo gida,  sun ce mana tana can a raye, dan girman Allah ka duba mini ka sanya baki a lamarin nan dan Allah"


"Ni ne zan saka bakin? Su sha tara ne fa suka yi aikin, ban maka wannan alƙawarin ba, zan dai je na duba maka ko tana nan"


Dagaci ya ce "To shikenan, hakan ma na gode sosai"


***


Mummy na barin gidan wambai ta tafi gidan aminiyarta Hajiya Lubabatu, domin fesa mata labarin da ta guntso a gidan wambai.

Sam labarin bai yi wa Hajiya Lubabatu daɗi ba.


Cikin hasala take cewa "Yanzu saboda tsabar wulaƙanci ace har yana shirin yin murabus amma ni ban sani ba".


"To da baki sani ba ni ba gashi na gaya miki ba, kuma shi yana can Germany ke kina nan ta ina zaki sani?"


"Amma shima wannan wamban ƙasurgumin munafuki ne"


Waro ido mummy tayi ta ce "Rufa mana asiri kar wani ya ji mana, ke ai ba a wannan yakamata ki mayar da hankali ba, wai yana tunanin idan yayi murabus Adam za'a dawo wa da sarauta, sai dai na gyara miki hanya, dan na kunno mus wuta daga shi har uwarsa, dan sai da na tabattar da na fusata shi sosai a kansu. Yanzu dai ki nemi Jabir ku tattauna a kai, ku yi duk iya ƙoƙari kar a rabaku da sarautar nan, Jabir ya gaji ubansa".


Hajiya Lubabatu ta ce "Ai faɗa ma ɓata baki ne, ai dan ubansa dole ya zo ya san abin yi, ya tare a gindin Adam sai ka ce ubansa".


"To wallahi ku san abun yi"


"Kar ki damu zaki ji ni" daga haka suka cigaba da hirarrakin su.


****

Kamar a bayi haka aka fara rabawa su ruma abinci, gurasa ɗaya da ruwa ɗaya, haka ake basu kullum, sai ranar da Allah ya kawo wannan mutumin, ya kan kawo mata abinci.

Wannan matar kuwa ko magana ta kasa saboda a wahale take, ji take kamar yunwa za ta kasheta.

Ko da aka bata gurasar nan ba ta tsaya komai ba, ta yi loma uku da ita, saboda azabar yunwar da take ji.


Ruma ta miƙa mata tata ta ce "Gashi ki ƙara da tawa ni na ƙoshi".


Matar ta girgiza kai ta ce "A'a, ke ce baki da lafiya, ki daure ki ci, sai ki ji ƙwarin jikinki" ruma ta girgiza mata kai alamar a'a.


Matar ta saka gefen zaninta, ta sharewa ruma gumin da ta fara yi, saboda zazzaɓin jikinta ya sauka.


Mutumin da ya tinkaro su, ruma ta tsaya ta zubawa ido, sarai ta gane shi, mutumin da ya tare su yana tambayar wacece ita?

Kenan duk rabin mutanen garin abu ɗaya suke yi kenan, satar mutane? Ta tanbayi kanta.


Suka gaisa da 'yan bindigar da suke wurin, ya yi musu magana da yaren da ruma ba ta iya ji.


Suka amsa masa, sannan ya shiga duba mutanen wurin, can ya nuno ruma, ya ce "Waccan ce".


Ƙaton da ya taɓa dukan ruma da bakin bindiga ya tashi ya je ya danƙo ruma, kamar an yi cinikin kaza za a sayar haka ya fizgota, cikin dakiya ta fizge hannunta tana haki.


"Bata da lafiya ka yi mata a hankali" cewar matar da haryanzu ruma ba ta san sunanta ba.


"Ke idan baki kiyayeni ba, da shiga abin da ba a saka ki ba, wannan cikin naki ba zai hana na keta miki haddi ba a gaban jama'a ba, ki shiga hankalinki" daga haka ya mayar da idonsa kan ruma ya ce "Wannan ka ce ko?"


Dogo ya ce "Eh ita, ya ce ku taimaka ku faɗi abin da za'a bayar ku bayar da ita"


Ya ƙyaƙyace da dariya ya ce "Ai wannan ta zama tamu, ba zamu bayar da ita ba, ta ce sai da a kashe ta a wurin nan, dan haka muma muna so,  su yi haƙuri su mance da ita, ko su fansheta da 'yan mata biyar, dan ni ba dan barde ya saka mini ido a kanta ba, da tuni ta zama yarinyata, kawai su je idan ubanta da sauransa yayi wani ƙoƙarin su haifi wata, wannan kuwa ba zamu bayar ba" yayi maganar yana ƙoƙarin rungumo ruma jikinsa.


Duk da yadda take a galaibaice, amma haka ta dunƙule hannu, ta ɗirka masa duka a ciki.

Sak suka yi gaba ɗaya suna kallonta, kamar wata zakanya, ta ja da baya ta dunƙule hannu "Wallahi idan ka kuma taɓani sai na yi maka duka, ni ba 'yar iska bace ba, wane irin azzalumai ne ku? Ba kwa tausayinmu? Muma fa mutane ne kamar ku, kar Allah ya sa ku sake ni, ku kasheni ka kasheni idan kai ɗan halak ne, ni a duniyar nan bana tsoron kowa sai Allah La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin" cikin tsananin ƙwarin gwiwa take maganar ga jikinta yana tsuma.


Ƙare mata kallo ya yi, dudu tsayinta bai fi cikinsa ba, ko a shekaru baya tunanin tayi sha huɗu, ko maza surrender suke idan suka shigo hannu amma yarinya ƙarama ta tsaya a gabansa tana wannan maganar.


"Dan Allah ka kashe yarinyar nan mu huta, sun hana a taɓata sun ƙi bari a saketa duk ta gallabi mutane, barde yana da matsala, kalli yadda take rashin mutunci fa" ɗaya daga cikin mutanen yayi maganar yana gyara bindigarsa tare da saita ta a kan ruma.


"Kai kuma ban saka da kai ba, idan kuma na kasa da kai to ka kwashe, kuma in sha Allah ba zaku gama da duniya lafiya ba, sai kun ga abun da Allah zai yi muku".


Murmushi ƙaton nan yayi cikin ƙarfin hali, da jin kunyar dizgin da ruma ta masa ya ce "Idan ka kasheta a yanzu ai ta ci bulus, bari in gwada mata tabon da zata tafi lahira da shi, yau ko ni ko barde amma sai na nunawa yarinyar nan iyakarta, ni ki ka ce zaki daka ko?"


Ruma ta sake gyara tsayuwa ta ce "Wallahi kana taɓani sai na ware ƙwanjina, na rama kai ka san wace ruma kuwa?"


Dogo kuwa kamar soko haka ya riƙe hannu yana kallon ikon Allah.


Cikin magiya da kuka matar nan ta fara "Dan girman Allah kayi haƙuri, kar ka yi mata wani abun zafin ciwo ne"


Ruma ta ce "Ba wani zafin ciwo, a hankalina nake, wallahi ya taɓani sai na rama, bana tsoron kowa a wurin nan"


Ya shammaci ruma ya danƙonta, zai fizge hijjabinta da yayi daƙal-daƙal saboda dauɗa, ta riƙe hijjabin ta shiga kai masa duka da hannu ɗaya tana wani gurnani da ihu kamar zakanya.


Ya saka kan bindiga ya ƙwala mata a ka, ihu ta yi ta durƙushe a wurin, sai ga jini ta hancinta.


Tasowa matar nan ta yi da ƙyar ta nufo su, sai dai kan ta ƙarasa ruma ta miƙe cikin tangaɗi ta saka hannu ta dintsi ƙasa da ciyayi, ta watsa masa a jikinsa, gaba ɗaya suka taso suka yo kan su.

Riƙe ruma matar ta yi ta shiga tsakiya, ta haɗa hannayenta biyu cikin magiya 🙏

Ba ta yi maganar ba ya hankaɗeta ƙasa, ta fasa ihu jin kamar a take ɗan cikinta zai faɗo, wani irin gigitaccen ciwo ya ɗaure mararta zuwa ƙafafuwanta.

Hankalin ruma ya koma kan matar, ta nufeta da sauri, amma mutumin nan ya kwarfeta, ya sanya bindiga ya dinga kwaɗa mata, yana takata da ƙafarsa, ihu take amma bakinta yaƙi mutuwa "Idan ka isa azzalumi ka kasheni, kuma in sha Allah yadda Allah ya kuɓutar da Annabi yunus a cikin kifi, ya kuɓutar da Annabi Ibrahim daga cikin wuta, sai Allah ya kuɓutar da mu, haka malamin mu ya ce mana mu yarda da Allah, in sha Allah zai saka mana" ya daka ya daka ya takata, ya sanya wani itace ya maka mata a baya. Wani irin ihu ta kuma yi, bakinta da hancinta na ta zubar da jini.

Tuni ta fara gani dishi-dishi, gadan gadan ya nufi ruma, ya durƙusa a kanta ya kama skirt ɗin jikinta ya fara ja.


No comments