Breaking News

Kanwar Maza Book 2 Page 5

 Ayshercool.



*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*



Ba ta ji ko ɗar ba da ta yi maganar, ta ɗau abubuwan da ta saya, mutumin nan ya bi ruma da kallo, har zata fita daga shagon ya ce "Ƙawata yaushe zan zo kano na kawo miki ziyara, in ga Kanon da ake cewa ta fi garinmu kyau?"


Murmushi ta yi ta ce "Idan ka zo kano ka ce wurina ka zo sai yayyena sun naÉ—a maka na jaki ni ma su karairayani, cewa za su yi kai saurayina ne, amma dai Kano tana da kyau sosai, sai watarana É—an uwanmu"


Ta yi waje, su lawisa suka bita kamar munafukai.


Jerin babura ne suka din ga shigowa cikin kasuwar ko ta ko ina, suna É—aukar mutanen nan masu rufaffiyar fuska suna barin cikin kasuwar.


Ruma ta ce "Zaliha wai wannan mutanen idan suka idan su ka bar nan ina suke tafiya a kan bauran nan?"


Jiki a sanyaye zaliha ta ce "Cikin daji suke tafiya, ruma mutumin nan fa na cikin rumfar nan shima fa sune, É—an uwansu ne" waro ido ruma ta yi ta ce "Haba dai? Amma nake hira da shi?".


"Shiyasa ake ce miki ki iya bakinki, kin zage sai zuba ki ke har da cewa zaki gaya wa 'yan sanda".


"To ba gara a gaya wa 'yan sandan ba, tun da ku tsoronsu ku ke ba za ku iya ba, ai taimakonku zan yi, ke nifa DPO É—in unguwarmu ma ya sanni, tun da na karya wata yarinya ya sanni, dan haka sai na je na gaya masa".


Lawisa ta ce "Ke waye ya ce miki aikin 'yan sanda ne?, sojoji ma fa ake turowa, amma haryanzu abu ya gagara mu samu tsaro "


Tunawa ta yi da batun da aka yi, na da sanin wasu daga jami'an tsaro ake zirga-zirga da makamai amma ba yadda suka iya.


Ƙarar wani abu ruma ta ji, da bata taɓa jin sauti irinsa ba, sai gani tayi mutane suna gudu, mutumin da yake tafiya a kusa da su ya faɗi cikin jini.

Aka buÉ—ewa mutanen kasuwar wuta. Tuni ta nemi su lawisa ta rasa sun arta, ita kuwa ta kasa gudun, ta kasa gaba ta kasa baya, sai rungume kayan sayayyar ta da tayi tana rarraba ido, mutane sai faÉ—uwa suke cikin jini.


Ji ta yi an kama hannunta an ja ta da gudu, an bi ta bayan kasuwar da ita, ba ta san ko waye ba, sai da suka bar cikin kasuwar, sannan suka tsaya.

Mutumin da ya zauna a rumfar mai awo ne, sai dai shima a wannan karon fuskarsa a rufe take, da kayansa da kuma muryarsa ta gane shi ya ce mata "Yi sauri ki bar wurin nan, ki tafi gida" daga haka ya juya ya barta.


Ikon Allah ne ya kai ruma gida, dan ba ta taɓa ganin tashin hankali kamar wannan ba, mutane kwance a cikin jini an kashe su.


Ko da ta je gidan babu kowa, ta zube kayan hannunta a tsakar gida ta zauna, ta yi shiru tana cigaba da jiyo ƙarar harbe-harbe sama-sama.


Ta yi kusan mintuna ashirin, sai ga iya da su lawisa sun shigo, da alama ita suka tafi nema.

A gigice iya ta ƙaraso in da ruma take tana faɗin "Rumaisa babu abin da ya sameki ko? Bari gobe in Allah ya kaimu da sassafe azo a mayar da ke, mutanen nan sun sake waiwayo mu, ina fatan babu abin da suka yi miki"


Ta kalli jikinta, ba abin da ya sameta sai dai jini duk ya taɓata. Iya ta saka ruma ta yi wanka ta canza kaya.


Sai dai ruma ta kasa magana, dan ta tsorata da abin da ta gani, gawar mutane kwance a cikin jini.


Da ƙyar ta iya cin abinci, ta nemi wuri ta kwanta, sai dai bacci ya gagari ruma sai tsananin zurfin tunani.


Ruma tana jiyo iya da sauran mutan gidan, suna mayar da zance da irin É“arnar da aka yi a harin na yau, a nan ta ji irin masifu da tashin hankalin da suka fuskanta a baya, wanda haryanzu suna kai.


Tun da Allah ya sa ruma ta buɗi ido, ba ta taɓa ganin tashin hankali kamar wannan ba.


****

Takawa jiki yayi kyau, ya daina jin abin da yake ji, ya cigaba da sabgoginsa a Abuja, sai dai duk yadda ya so ya gama abin da yake ya dawo kano abu ya gagara.

Tattaunawa ce ta musamman suka yi, ita ma tattaunawar sai dare suka yi ta, sai bayan sha biyun dare sannan suka gama, ya fito zai tafi masaukinsa, dan ko direban bai nema ba yau.


Ya biya wani restaurant ya ci abinci, sannan ya nufi makwanci. Tun safiyar yau yake fama da fargaba da ya rasa dalilinta. Yana tsaka da tuƙi gabansa yayi wata irin mummunar faɗuwa gabansa ya faɗi, ƙirjinsa yayi wani irin bugawa da sai da burki ya kusa ƙwace masa a tsakiyar titi. Da ƙyar yayi parkinh ya kifa kansa a kan sitiyari, ya dafe ƙirjinsa sa hannu ɗaya, yana jin yadda zuciyarsa ke tsananta bugu.


***

Gari yayi tsit kamar an yi ruwa an shanye, duk wannan balahira da ta faru har aka yi aka gama, babu jami'in tsaro ko ɗaya da ya bayyana a wurin, sai da ƙura ta lafa waɗanda aka karkashe wa 'yan uwa, suka je suka ɗebo gawarwaki, aka yi musu sutura ana jiran gari ya waye a sallacesu, wasu gawarwakin ma ba a samu ɗebo su ba saboda tsoro.


Dare ya tsala sosai, farin wata ya haske gari, ko ƙwaƙwƙwaran motsin wani abu ba ka ji, ciki har da ƙwari.


Idanunta tarwai, babu alamar bacci zai ɗauketa ko da kuwa ɓarawo ne. Daga can ƙasa-ƙasa ta fara jiyo jiniyar babura suna kusantowa. Ta runtse idanunta tana hango yadda a abubuwa suka faru ɗazu a kasuwa, sai dai ƙarar baburan suka cigaba da kusantowa yana cika mata kunne.


Hannu ta saka ta toshe kunnuwanta, tare da sake rintse idanuwanta. Dan ƙarar baburan na sake hasko mata abun da ya faru

Ba ta san iya adadin lokacin da ta kwashe a haka ba, ta sauke hannuwanta, iface-iface ta din ga jiyowa ana salatuttuka, hayaniya ta yi yawa a ilahirin kewayen gidan.


Muryar mijin iya ta jiyo yana faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, mutanen nan sun sake dawowa, mai kuma suke nema da mu? Me suke buƙata?"


Iya ma cikin kuka take salati tana "Allah kana gani, Allah bamu da wani gata sai kai, Allah ka duba mu".


Wani irin ihu da gurnani kunnuwan ruma suka jiyo mata, kai daga jin ihun ka san wadda take yi a cikin masifa take.


Muryar wani magidanci suka ji yana ta magiya "Dan girman Allah ku yi mini rai, 'ya ta dan Allah ku rufa mini asiri" 


Ƙarar harbi suka ji, daga nan basu sake jin muryar mutumin ba, sai kuka da ihun yarinyar. Wadda ruma sukan yi wasa tare.


Gaba ɗaya kururuwar mata da hargowar mutanen ta karaɗe ƙauyen, haɗi da harbe-harben bindiga.


Kan iya suyi wani yunƙuri, wasu irin zaratan maza su kusan huɗu sun afko cikin gidan.


Mijin iya ya tsaya ƙyam, babu tsoro a tare da shi ya ce 'Haka muka yi da ku? Kun saɓa alƙawari mun yi duk abin da kuke so, amma bamu tsira ba, so kuke lallai sai mun fita mun bar muku garin, idan mun fita ina kuke son mu je?"


Cikin tsawa wani ya ce "Ba tuna mana alÆ™awari muka zo ka yi ba, aiki muka fito yi, kai ku kama shi ku É—aure mana shi" aikuwa suka kama dattijon suka yi masa É—aurin huhun goro, suka rufe masa baki,  sannan suka afko cikin É—akin.


Lawisa da zaliha sai kyarma suke yi, ruma kuwa tayi zuruu da ido, tana ganin sarautar Allah, abin da take ji a radion mama yau gashi a zahiri ba labari ba.


Hargitse kayan É—akin suka shiga yi, wasu kuma suka zaga suka kwance garken dabbobin da ake kiwo a gidan, suka yi waje da su.


Ɗaya daga cikin su, ya zo ya danƙi ruma ya fara janta.


Cikin kururuwa iya take faɗin "Ka yi wa Allah da ma'aikinsa ka ƙyale yarinyar nan, baƙuwace 'yar amana ce, dan Allah karku cutar da ita".


"Kai wuce da ita" ɗayan yayi umarni cikin tsawa. Iya ta yinƙura zata yi magana, ɗayan ya saka bakin bindiga ya buga mata a ka ta zube a ƙasa sumammiya.


Ruma ta zura silifas É—in ta, É—ayan yayi waje da ita yana janta. Ko da suka fita ko waiwayowa ba sa yi, su Zaliha sai kuka suke suna kiran ruma, amma suka ce idan suka kuma magana sai sun harbesu.


Ko da suka fita tuni duk sun tattara waÉ—anda zasu tafi da su, a cikin daren suka ingiza su zuwa cikin daji, ciki har da ruma.


Tafiya suke tamkar suna kaɗa dabbobi, an tattaro mata manya da ƙanana sai maza 'yan tsirari.


Tafiya suke a tsananin duhu, ba tare da sun san in da suke sanya ƙafafuwansu ba, ruma ganin abin take kamar a mafarki.


Tun suna tafiya ruma tana saka ran tafiya za ta ƙare, har ta sare ta fara galabaita ta gaji tiƙis, dan haka ta ja ta yi burki ta durƙusa tana hutawa.


Cikin tsawa wani ya ce "Ke! Tashi ki wuce mu tafi"


"Na gaji wallahi, ba zan iya tafiya ba"


"Ba zaki iya tafiya ba? Tashi kan na É—auke kanki da harsashi"


"Wai ya ka ke so na yi, ba ka ga ni yarinya bace ba, wallahi sai dai ku kasheni, nace na gaji ni wallahi ban taɓa ganin bala'i irin wannan ba"


"Dalla kasheta mu wuce, ba zata É“ata mana lokaci ba" cewar É—aya daga cikinsu.


"Tsaya in zauna daga nan, sai ku harbeni, ina zan iya wannan wahalar, Allah yasa idan na mutu na je a sa'a, na san mama za ta mini Addu'a" tayi maganar tana zama.


WaÉ—anda suke kan babura ne suka iso, wani yayi parking ya ce "Tsayuwar me kuke yi ne?, ku wuce mana".


"Oga wai ta gaji, shine ta samu wuri zauna ta ce mu harbeta"


Hasketa na kan babur É—in ya yi da fitila, ta saka hannu ta kare fuskarta tana mucincina ido, saboda hasken fitilar.


"Ke 'yar gidan waye a garin nan?" Ya tambayeta.


"Nifa ba 'yar garin nan bace, ziyara kawai na zo, gwaggo ta yaudareni aka kawo ni nan, wai sai zamu koma makaranta zata mayar da ni gida "


"Taso ki hau mu ƙarasa" yayi maganar yana nuna mata babur ɗin da yake kai.


Babu musu ko wani abu ta kama babur ta É—ane, ya ja suka tafi.


Aka cigaba da kaɗa sauran a ƙafa, tamkar shanu, a iya sanin ruma ita dai kawai sun yi tafiya mai nisan gaske, kafin su ƙaraso wani ƙaton wuri, bayan wani dutse tsakiyar daji sosai da sosai.

Wasu mutanen suka tarar riƙe da manyan makamai, ga wasu mutanen da aka kama duk a zube a ƙasa a zazzaune kamar fursunoni.


Ya karkata babur É—in ya ce wa ruma ta saukko.


Ta cimimiye shi sannan ta sauka, tana kallon wurin, sai dai duk da hasken farin watan ba kowa take iya ganewa ba.

ÆŠaga kai tayi ta kalli mutumin da ya kawota a babur. Da kayan jikinsa ta gane shi, mutumin É—azu da duka haÉ—u a kasuwa.

Cikin mamaki ta ce "Kaii, kai ne?"


Ya sanya yatsansa a kan leɓensa ya ce "Shhhhhh, wuce ki nemi wuri ki zauna"


Ta ƙarewa wurin kallo, sannan ta kalleshi "Wai a nan zan kwana? Akwai sanyi fa, kuma a wannan filin babu abin rufa ba katifa?"


Wani daga cikinsu ya gyara bindigarsa cikin tsawa ya ce "Zo ki wuce, au ke daÉ—i ma ki ke nema, zaki gane kuskurenki kuwa".


Ba ta motsa ba ta sake duban wanda ya kawota, ya jinjina mata kai ya ce "Wuce ki zauna"


A hankali ta ja ƙafarta ta wuce ta zauna a in da aka nuna mata, wani irin sanyi take ji har cikin ƙashinta, ga bishiyoyin wurin sai rausayawa suke yi, ƙafafuwanta duk sun yi tsami ga ƙaya da ta taka.


Wasu daga mutanen suka koma gefe, suka kunna sigari suna sha.


"Allah mai iko, yau kuma nan Allah ya kawo ni" ta takure jikinta tayi shiru, da yanzu tana gida kusa da mama, mama tana lulluɓeta.


***

Da ƙyar Adam ya iya kai kansa hotel ɗin da yake, bai tsaya ko ina ba sai ɗakinsa, ya je ya buɗe ya kwanta a ruf da ciki, yana ta maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un.


Cikin wani abu mai kama da bacci da kuma gizo, yake jin sheshsheƙar kukan ruma, kamar dai kowane lokaci itan dai yake gani tana kuka.


Haka ya wanzu a wannan yanayin, da shi kansa bai iya tantance wane iri bane ba.

Alarm É—in wayarsa ne ya buga, alamar asuba ta yi, hakan  ne ya sanya ya farka da kalmar shahada a bakinsa.


Ya tashi zaune ya ɗan yi shiru yana tunani, shi dai tun da Allah ya sanya ya taso da ƙuruciyarsa bai taɓa cikakkiyar lafiya ba, daga wannan sai wannan, bai taɓa tunanin zai kawo i yanzu ma a raye ba.


Ya yanke shawarar idan ya koma kano, zai kuma neman ruma ya ji meye matsalar sa da ita, da ta hana shi sukuni irin haka.


***

Har gari yayi haske, waɗanda aka ɗauko su ruma tare da su ba su ƙaraso ba, ruma ta kalli wani tsaye da bindiga ta ce masa "Zan yi sallar asuba".


"To waye ya hanaki?"


"Ban gane ba, zan yi fitsari ne in yi alwala, a bani abin salla"


"Duk ciki waye ki ka ga yayi salla a nan, kar in sake jin bakin ki".


Wani dattijo ya ce "Yarinya sai dai ki yi taimama ki juya ki kalli gabasa ki yi salla, amma babu mai baki wani ruwan alwala a nan" tsananin mamaki ya cika ƙwaƙwalwar ruma, ita haryanzu ma ba ta san dalilin da ya sanya a ka kawota nan ba.


Shawarar tsohon ta bi, ita kanta taimamar ba ta iya ba, haka nan ta batsaltsalata, ta yi salla.


Gari yayi haske sosai, sai ga waɗancan sun ƙaraso a mugun galabaice, wasu ƙafa sai jini take saboda taka ƙayoyi, wasu sai haki suke yi suna kuka, haka suma aka zube su a wurin gaba ɗaya.


Matan da suke ciki sai koke-koke suke, wani ƙato baƙi daga cikinsu yayi musu wata razananniyar ƙara "Ku rufe mana baki, ko tarwatsa ƙwaƙwalenku da harsashe".


Ruma tayi zurruu da ido tana kallon mutumin.


"Ke kuma na yi kama da ubanki ne da ki ke kallona?"


Jin maganar ruma tayi a sama ba daÉ—in ji.


"A'a meya kawo zancen ubana kuma, ubana ko da ban san shi ba, yafi ka kyau" tayi maganar cikin ƙunƙuni.


"Me ki ke cewa?" Yayi maganar yana yo wa kan ruma.


Tayi shiru ta sunkuyar da kai.


Babu wanda ya sake bi ta kansu, aka bar su a wurin nan.


****

Gidan iya kuwa sai da gari ya waye maƙwabta suka shigo, aka yayyafawa iya ruwa, aka tafi da ita Asibiti da ita da mijinta, su lawisa kuwa sai koke-koke suke yi.

Maƙwabtansu kuwa an yi wa yarinyar gidan fyade an kashe babanta an tafi da matar gidan. Nan da nan labari ya cika gari.


Babu shiri gwaggo ta shirya ta sanya lawalli ya goyata a babur ya kaita garin su iya. A nan ta iske cewar an yi garkuwa da rumaisa. A take ita ma ta yanke jiki ta faÉ—i, ita ma aka yi asibiti da ita.


Iya tuni ta farka, gwaggo kuwa da ƙyar ta farfaɗo, tunda ta farko take koke-koke tana faɗin "Na shiga uku me zance wa uwar yarinyar nan, da na sani na basu 'yar su, ƙaunar yarinyar nan ya sanya na riƙeta, da na san haka zata faru, da na barshi ya tafi da ita. Ni yanzu ina zan saka kaina"


Sai da ma'aikatan wurin suka taru suka yi ta rarrashin gwaggo suna bata haƙuri, amma cewa take "Ni dama tawan suka ɗauka suka bar 'yar mutane, bawan Allah baƙuwace 'yar wa na ce, ban san me zasu yi mata da suka tafi da ita, Allah ka fitar da yarinyar nan ni Shafa'atu ina zan saka kaina, ta ina zan yi wa uwar yarinyar nan bayani?"


Likitan ya ce "Ai uwar yarinyar na tabattar musulma ce, kuma tayi imani da ƙaddara, dan haka ko a gabanta ne za a iya sace yarinyar "


Girgiza kai gwaggo ta yi ta ce "Ba zaka gane ba"


A social media Abubakar ya fara ganin abin da ya faru, kuma ya san da batun an kai ruma katsina, ƙauyen da iya take, duk da yana makaranta.

Ba shiri ya kira Aliyu a waya ya sanar masa da a kan lallai ya bincika, su ji ya ruma take, sannan su gaggauta zuwa su É—aukota.


Usman ma ya gani, dan haka a burkice ya ja Aliyu yake nuna masa abinda ya gani.


Aliyu ya ce "Yanzun nan Yaya yayi mini magana a waya, ina son na kirasu a waya amma tsoro nake ji, babban tashin hankalina kar mai sunan Baba ya ji balle mama, dama ya ce gobe in Allah ya kaimu zai je ya É—auko ruma".


Usman ya ce "Ka ga ba wannan ba, ka kiras lawalli a waya ka tambayeshi yaya rumaisa take?"


Aliyu ya girgiza kai ya ce "Usman gabana faÉ—uwa yake yi fa, ance an karkashe wasu an tafi da wasu, kai dai ka kirasu"


Usman ya kira wayar lawalli, amma taƙi shiga, dan haka ya kira ta ɗanlami babban ɗan gwaggo, dan tabattar da abin da yake faruwa.


Sai da ta kusa katsewa sannan É—anlami ya É—aga wayar.


Ba tare da sun gaisa ba, cikin zaƙuwa Usman ya ce "Yaya ɗan lami, ya ake ciki ne? Na ji 'yan ta'adda sun kai hari garin su Iya, ya ake ciki ya ya ina ruma?"


Yaya É—anlami ya ce "Wallahi kuwa, dan kaga gwaggo ma tana gadon asibiti, Baba kawai aka sallamo"


Aliyu ya karɓe wayar ya ce "To Allah ya kyauta, ya ya rumaisa, gobe in Allah ya kaimu yaya umar zai zo ya ɗauketa ya taho da ita, dan Allah a ɗaukota daga garin nan kan ya zo".


"Aliyu sai dai fa mu tsananta addu'a, an samu matsala 'yan bindiga sun tafi da rumaisa!!!"


"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, me ka ke cewa ne...?"


Usman ya girgiza Aliyu ya ce "Me ya ce maka ne?"


Kan Aliyu yayi magana, suka ga mai sunan Baba a tsaye yana kallonsu, Allah kaÉ—ai ya san iya adadin lokacin da ya shafe a tsaye yana jin su ba tare sun sani ba.


No comments