Breaking News

Kanwar Maza Book 2 Page 30

 



Gudu yake sosai a kan titi, Bashir ya hau motarsa ya bi bayansa, amma ya kasa


cimmasa.

Ko da Adam ya ƙarasa gida, wani irin horn ya din ga yi kamar tashin hankali. A gigice masu tsaron ƙofar suka buɗe masa gate ya shiga da motar, ko da ya fito ko rufeta bai yi ba ya wuce sashin Ammi.


A can cikin gidan kuwa, bayan sallar isha'i, wata hadima ta shiga ta sanar da ammi cewar mummy na son ganinta.

Mamaki ne ya cika ammi, meya kawo mummy a wannan lokacin? Ba tare da wani ɓata lokaci ba, ta tashi ta fita falonta, ta tarar da mummyn tare da autarta ruƙayya.


Ta kalli ammi ta yi murmushi ta ce "Barka da warhaka giwar mata".


"Barkanki dai, kuna lafiya?"


"Alhamdilillah, ya kuma mu ka ji da wannan lamari da ya faru?"


Ammi ta amsa da "Alhamdilillah"


"To Allah ya jiƙanta da rahama"


"Amin ya rabb"


Mummy ta gyara zamanta ta ce "To, ni dai giwa idan wani abun na yi miki dan Allah ki yafe mini, ban san me na yi miki haka ba, ai ko ban samu shigowa ba, ya kyautu a ce kin aika mini jaririn na gani, nima jiakana ne, amma har su Fauziyya suka zo aka hanasu jaririn, yaran nan ko muna so ko ba ma so tsatsonsu É—aya fa, wannan abun babu in da zai kaimu, ni dai ki yafe mini, amma a bani yaron na ganshi"


Ammi ta É—an dubi mummy, kamar ba a wurin zaman makoki suka din ga yi da ita a gabanta suna yasar mata da maganganu ba, ta basar ta ce "Bari a kawo shi ki ganshi" tayi maganar ba tare da ta tanka wancan maganganun da ta yi da fari ba.


Iman ce ta ɗauko sabir, ta kawo wa mummy shi, ta sanya hannu ta karɓe shi, tana wani irin murmushi ta ce "Tubarkallah masha Allah, wannan yayi wayo sosai, sai dai ni kasa gane ma da wa yake kama a tsakanin aishar da takawa"


Ammi kawai ta kalleta ba ta ce komai ba.


"To wane sunan aka saka masa?"


"Mahmud, ana kiransa sabir".


Da sauri Mummy ta kalli Ammi ta ce "Mahmud kuma? Sunan Mahmud ya ci kenan?"


Ammi ta ce "Eh, sunansa ya mayar masa"


Mummy za ta yi magana, Adam ya faɗo ɗakin kamar wanda ya ƙwato a hannun miyagu.


Tun a falon ya fara ɓalle rigarsa, saboda wani irin gumi da yake yi, ƙafafuwansa kamar ba zasu iya ɗaukarsa ba.


A gigice ammi ta tashi ta bi shi tana kiran sunansa, sai dai bai iya tsayawa ba, Mummy ma tashin ta yi ta bi bayansu, tana tambayar ko lafiya.


Kan gadon ammi ya haye, jikinsa ya fara wannan mazarin, kamar wanda ake bugawa gangi.


A gigice ammi ta ce "Iman, É—auko maganinsa maza"


Da hanzari iman ta fita ta bar É—akin, ammi Cikin damuwa ta ce "Takawa meyafaru ne? Meyake damunka?" Bai amsa mata ba, sai runtse idanuwansa da ya yi.


Iman ta dawo da jarkar maganin da ake shafa masa, ta buɗe ta tsiyayo, ta fara ƙoƙarin shafa masa, amma ya juya kansa ya ce "Kar ki shafa mini, a hayyacina nake, jikina zai daina rawar ne, ku lulluɓeni" duk yadda ammi ta so shafa masa ƙin yarda ya yi, sai lulluɓe shi da aka yi.


Bin maganin da kallo Mummy ta din ga yi, sannan ta ce "Wai giwa harzuwa wani lokacin zaki bar yaron nan ya cigaba da rayuwa da wannan larurar ba tare da kin nema masa magani ba?" 


"Ina iya ƙoƙarina, Allah ne bai kawo ƙarshen abun ba"


"To kina zaune Allah za kawo ƙarshen lamarin, shi meye wannan ɗin da ake shafa masa?" Ganin ammi ba ta bata amsa ba ya sanya iman cewa "Magani ne"


"Miƙo mini na gani" ta yi maganar tana tsare iman da ido, iman ta ɗauka ta miƙa mata, ta karɓi jarkar ta din ga jujjuyata, tana nazartar meye a ciki, amma ta kasa ganewa, ta ajiye robar ta ce "Shikenan, ga wannan yaron, amma akwai buƙatar ki miƙe tsaye fiye da da, ko kuma ya dauwwama cikin nakasa" kamar dai ɗazu, a yanzun ma ba ta samu amsa daga ammin ba.


Bashir kuwa tun da ya ga Adam ya ɓace masa, ya haƙura ya koma, dan bashi da tabbacin in da zai nufa ya bi adam ɗin, kuma ya kira shi bai ɗaga wayarsa ba.


***

Rumaisa kuwa zazzage kayanta ta yi da aka bata, na wurin Ammi da na turaki. Turmi biyar ammi ta bata na atamfar tare da turare mai ƙamshin gaske.

Turaki kuma ya sanya an cika mata ledoji da kayan dubulan, da uban kilishi fal da soyayyen naman kaza, sai kuma turaruka, ga kuma nono mai kyau kusan galan guda da man shanu. Ruma ta din ga yashe baki tana murna.


Mama ta ce "Eh dole ki yi murna mana, a dalilinsa kin samu iyayensa sun yi miki sha tara ta arziki ke kuma kina yi wa É—an su rashin mutunci"


Ruma a ranta ta ce "Hmm mama ba zaki gane bane ba, baki san girman laifin da mutumin nan yayi mini ba, sai na tabattar masa da abun da na gaya masa ai" mama ta yi ta mita, amma ruma ta yi shiru ba ta ce komai ba, sai ma tunanin gobe in Allah ya kaimu za ta koma makaranta abun da ba ta so.


Sai da ta zo kwanciya barcci, sannan wata irin kewar sabir ta sake kamata, ta rungume fulonta, ta rintse idonta, ta din ga hango fuskarsa yana kallonta yana lumshe idonsa.

Kamar an kunnawa zuciyarta wuta, haka ta din ga jin wata irin ƙishirwar son sake ganin sabir, tamkar ta yi tsuntsuwa ta tashi. Ta sake rintse idonta, tana sake tuna yadda take kwana gata sabir a asibiti, ganinsa da ta yi yau ta sake jin du rintsi duk wuya sai an bata ɗan ta.

Haka kurum ta hau kuka, tana sake jin tsana da haushin adam a zuciyarta, a ganinta duk shi ya ƙulla a ƙwace sabir a hanata shi.


Cikin ikon Allah, takawa ya farfaÉ—o gaba É—aya, ammi ta saka shi a gaba ta din ga tambayarsa a kan meyafaru har ya shiga wannan yanayin.


Ya ɓoye yaƙi gayawa ammi dalili, ya ce mata bakomai, kamar kullum ta din ga yi masa nasiha tare da fatan Allah ya bashi lafiya da mafita a kan lamuransa.


Washegari da safe rumaisa kamar ta saka kuka, mai sunan baba ya kafa ya tsare, ya sanya rumaisa a gaba ta shirya cikin uniform É—in ta da suka sha guga, kamar ta fashe saboda takaici, ba ta son makarantar nan, ya sakata a gaba ya tafi kaita makaranta.


A ofishin shugaban makarantar ma, sake jajantawa rumaisa abun da ya sameta malamai suka yi, suka yi mata barka da dawowa tare da fatan Allah ya sanya ta nutsu zamanta a hannun Æ´an bindiga ya zame mata darasi.

Gaba daya hankalinta ba ya kansu, tunaninnta kawai yadda za ta ga sabir, mai sunan baba ya gama clearing É—in abun da yakamata, aka ce ta tafi aji, amma ajin baya zata koma saboda an riga an yi mata nisa a karatu.


"Kaii repeating aka yi mini, kenan ba zan yi candy da wuri ba, taɓ wallahi ba..." Gum ta rufe bakinta ba ta ƙarasa maganar ba, saboda kallon da mai sunan baba yayi mata, tana ji tana gani aka mayar da ita ajin baya.


A ranta ta ce 'Wallahi ba zan zauna a ajin baya ba, sai a zata ma daÆ™iÆ™anci ne ya saka aka yi mata repeating" 


Da aka fita break, Æ´an ajinsu da suka yi gaba, suka din ga tsalle suna murna, rumaisa ta dawo.


Sam ta ƙi shiga sabgar kowa, ta ɗau littafinta ta din ga zana hoton sabir a bayan litattafan ta. Har aka tashi ba ta san me aka yi ba.


Da ta koma gida mama tana ta murna, tana tambayarta ya aka yi a makarantar?


Rai a É“ace ruma ta ce "saboda tsabar tsanar da mai sunan baba yayi mini, ya sa aka yi mini repeating, wallahi ba zan zauna a ajin nan ba, ni ajin yan candy ma zan koma" ganin rumaisa za ta É“ata rai, ya sanya ta shareta.


Can rumaisa ta kuma cewa "Mama dan Allah in anjima, ki ce yasir ya rakani gidan su hauwwaliya na duba ƙafarta"


Mama ta ce "Kuma kin yi tunani mai kyau, kya je ki gaishe su, su ga kin warware sosai, amma sai gobe in Allah ya kaimu"


"Dan Allah mama in je yau"


"Goben in Allah ya kaimu ma sai na ce ba zaki je ba"


"To ki yi haƙuri, Allah ya kaimu goben".


Adam kuwa gaba ɗaya wunin ranar bai fita ba, ya san dole Jabir zai zo nemasa, ya bar saƙon ko jabir ya zo, a bashi haƙuri ba zai iya ganin kowa ba.

Ya kulle kansa a ɗaki, ya kunna wayarsa ya hau social media, ya ga yadda labari ya baza ko in, ga tarin kiran waya da saƙonni daga ƴan jarida, mutane sai comments suke kala-kala.

Ganin wayar na neman caza masa kai, ya sanya yayi jifa da wayar, gaba ɗaya ya ji ya rasa ƙwarin gwiwar da zai sake fuskantar duniya, da ƙudurinsa na son kawo ƙarshen yi wa ƙasa da harkar tsaro ɓarna. Ya ji ya rasa ƙwarin gwiwar bincikar waɗanda suka yi garkuwa da matarsa.


Sai da Ammi ta yi da gaske, sannan ya buÉ—e É—akinsa, har ya samu ya ci abinci, amma bai gaya mata abun da yake faruwa ba, saboda kar ya sake É—aga mata hankali.



Rumaisa yau ji take yi kamar salla, saboda yau zata kuma zuwa ta gano Sabir, dan a yanzu babu abun da yake faranta mata rai sama da haka.

Yau da rumaisa ta je makaranta, ƙin zama ta yi a ajin da aka kaita, ta tafi ajinsu ta yi zamant, ta ce ba ta ga wanda ya isa yayi mata repeating ba, sai dai a gaji a koreta daga makaranta gaba ɗaya, wanda da za ayi mata haka da shi ta fi so, dan ita ba ƙaunar makarantar take yi ba.



Mai martaba a yau da kansa ya dira a gidan su takawa, wanda hakan ya sa gidan ya cika maƙil da hadimai, da jami'an tsaro, masu kaiwa suna komowa, tun daga farkon titin har cikin gidan.

Bai sauka a ko ina ba, sai a sashen Ammi.

Mummy na jin labarin zuwan mai marataba, ta tarkato yaranta ta bazamo sashin ammi, da sunan zuwa kwasar gaisuwa a wurin mai martaba sarki.


Ƙafa da ƙafa ya zo ya yi wa Adam ta'aziyyar mutuwar aisha, sakamakon baya gari lokacin da abun ya faru.


Mai martaba ya numfasa ya ce "Turaki yayi mana bayanin komai yadda al'amarin ya faru, sai dai bai kamata a ɓoyewa duniya gaskiyar abun da ya faru ba, maƙiya za su iya amfani da wannan damar, wurin cutar da kai, kamar yadda zancen ya fasu har wata gidan jarida suka wallafa, kuma ba zai wuce saboda ƙoƙarin da ake yi wa ƙasa ba, ya sanya miyagu ke ta ƙoƙarin bayyana laifinka, amma ayi haƙuri a daure, a cigaba da abun da ake yi kar a fasa Allah zai shiga lamarin"


Adam ya risuna ya ce "In sha Allah, muna fatan mai martaba ya cigaba da sanya mu a addu'a".


"Addu'a kullum cikin yi muku ake, kuma ko dan albarkacin mu babu wani abu da wani zai iya yi ya cutar da ku a kan gaskiya a ƙasar nan, a cigaba da ƙoƙari. Ita kuma 'yar mu Allah ya jiƙanta ya raya mini wannan kyakykyawan jikan nawa" yayi maganar yana shafa kan Sabir da yake hannunsa.


Mummy ta risuna tana "Allah ya taimaki mai martaba, mun gode da wannan karamci, Ubangiji Allah ya ƙara girma da ɗaukaka ya ƙara maka lafiya da nisan kwana"


"An gaisheki amaryar Galadima, , ƴar malam kin ƙi halin malam, mai martaba ya amsa kuma yana godiya" wani irin takaici ne ya kama mummy, jin yadda hadimin mai martaba ya amsa mata.


Aka karÉ“i jaririn aka miÆ™awa ammi, shamaki ya dubi ammi ya ce "Mai martaba ya bawa jariri gidaje guda biyu, ya bashi dawakai guda uku, sannan mai martaba ya yi umarnin a  gina masallaci sadaka ga mahaifiyarsa. Sannan idan ya shekara uku a duniya mai martaba ya ce a kai shi umara"


Nan dogarai suka É—auka da "Godiya yake mai martaba, godiya yake Allah ya baka yawan nasara. Mai bayarwa da dama hagu ba ta sani ba"


Takawa ma risinawa yayi, suna yi wa mai martaba godiya.

Dogaransa suka kare shi ya tashi tsaye, har zai fita ya hangi iman a gefe a zaune.


Ya ce "Ahhh giwa, wannan buzuwar ƴar ta ki tana nan dama, ko da yake an ce mini bafullatana ce? ta daina zuwar mana, Allah ya jiƙan mai babban ɗaki, lokacin da muka kai mata ziyara a Saudiyya kan ta rasu, take tambayar ina wannan buzuwar ƴar ta giwar Galadima, a lokacin bamu sani ba ko kuna tare ko kin mayar da ita, mai babban ɗaki tana sonta"


Ammi ta yi murmushi ta ce "A'a muna tare mai martaba, ai tun da kuka saka baki a kan maganar nan, muke tare da ita"


"Allah sarki, baki fuskanci wani abu ba binta, wataƙila albarkacin yarinyar nan ne Allah ya kawo muku yaron nan cikin aminci, Ubangiji Allah ya yi jagora, Allah ya raya mana su baki ɗaya"


Ammi ta amsa da amin mai martaba.


Ba ƙaramin ƙulewa Mummy ta yi ba, yadda mai martaba ya mayar da hankali a kan yaran ammi, har da agola, amma ita ko kanta bai bi ba.


Mai martaba na tafiya, mummy ta fice fuuuuu ta bar sashin ita da su Fauziyya.


Bayan fitar su Ammi ta ce "Iman, mun yi laifi fa daina zuwa gidan mai martaba da ki ka yi, balle ki je gaishe shi,  kin ga har ya magantu, Allah sarki mai babban É—aki, lokacin kina Æ™arama rigingimun da aka yi ta yi a kan ki,  cewa ta yi sai na bata ke, na din ga kuka, ita tsaya mini a kan riÆ™onki".


Iman ta ce "Ammi tsoron zuwa gidan nake, fulanin yola ta hana ni zuwa, saboda yarima Hashim, kin san ai abun da aka yi mini su da Mummy"

Ammi ta ce "Na ji, kar ki yi kuka, jikina na bani mijinki mutum ne na gani na faÉ—a, karki damu autata"


Kunya ce ta kama Iman, Nusaiba ta ce "To ni fa, ko ita kaÉ—ai ake yi wa Addu'a"


"Ke dai nusaiba baki da girma sai na jikinki, kishi ki ke iman É—in?"


"To shikenan ma, ni na yi zuciya" Nusaiba ta tashi za ta fita, iman ta tashi ta bita da gudu tana yi mata dariya.


Ammi ta mayar da hankali a kan adam, da fuskarsa sam babu walwala, ta dube shi a tsanake ta ce "Mai martaba yake magana a kai ne, na ji yana cewa an yi amfani da gaskiyar abun da ya faru ana sukarka, meyafaru?"


Yayi ajiyar zuciya ya ce "Wata gidan jarida ne suka yi posting a social media, cewar aisha ta mutu a hannun 'yan bindiga, ko kuma ni na kasheta na yi tsafi da gangar jikinta tun da ba aga gawarta ba ma"


"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, adam waye ya aikata wannan abun? Waye ya fitar da wannan zancen har da sharri haka?"


"Nima ban sani ba, ɗazu na ɗauko wayata a mota, kira daban-daban da saƙonni daga ƴan jaridu, suna buƙatar wai na ce wani abu a kan lamarin na kashe wayar ma gaba ɗaya".


Ammi ta dafe kai, ta rasa me ma za ta ce ko ta yi? Abubuwa kullum sake rikicewa suke yi.


Da la'asar yasir ba dan yana so ba, ya saka rumaisa a gaba zai kaita cikin gari, suna tafe yana mita, sai da suka je titi, sannan rumaisa ta ce "Dan Allah Yasir taimakona zaka yi"


"Taimakon me?"


"Dan Allah gidan su sabir zaka rakani na je na ganshi" wani mugun kallo ya yi mata ya ce "Ba zani ba, yaushe ki ka je ki ka ganshi? Ba zani ba ba nan muka yi da mama ba".


Riƙe hannunsa ruma ta yi ta fara kuka "Dan Allah yasir, wallahi na kasa bacci jiya, ba zamu daɗe ba dan girman Allah" ganin tana kuka ya sanya jikinsa yin sanyi.


"Kin yarda zaki wanke mini uniform, ki É—aukar mini jakata zuwa islamiyyar"


Da sauri ta ce "Eh wallahi na yarda"


"Shikenan mu je, saura idan buƙatar ki ta biya, ki yi mini rashin kunya".


"Ai ba ma zan yi ba"


Ya tarar musu abun hawa, suka hau suka tafi.


Suna tafe yasir yana danna waya, can ya ce "Kaii"


Ruma ta ce "Menene?"


"Wani labari na gani, ke dama baban sabir É—in nan shi ne Adam Sharif Galadima?"


"Wai wannan mai tona asirin mutanen, ba wani nan ba shi ne ba"


"Dan ubanki ƙarya zan yi miki?"


Rumaisa ta ce "Taɓ, ba shi bane ba, shi wannan yana abun arziki ne?"


Yasir ya ce "Ke ba wannan ba, wani labari aka wallafa wai, ya sayar da matarsa yayi tsafi da gangar jikinta, kuma jaririn da aka ce nasa ne, ƙarya ne rainawa mutane hankali ake"


Wani takaici ne ya turnuƙe rumaisa ta ce "In ji uban wa?"


'oho, wani gidan jarida ne suka wallafa"


Rumaisa ta ce "To rubuta musu ka ce ƙarya suke yi, wannan yaron nice nan na zo da shi"


Yasir ya ajiye wayar ya ce "A'a ba ruwana"


Rumaisa ta ce "Zan yi waya katsina a kawo mini wayata ni na rubuta, wannan ai sharri ne"


"Ke dalla rufewa mutane baki, zaki saka na ƙi rakakin wallahi"


Ta riƙe bakinta ta ce "Na daina in sha Allah"


Da haka suka ƙarasa gidan su Adam, rumaisa har da ɗan tsalle za su je ta ga Sabir.


Sai dai rumaisa ta yi ta mamakin ganin layin duk kashin dawakai, duk da abun mamaki bane, amma yanayin wurin ya nuna an yi wani sha'ani a wurin.


Yanzu babu wanda yake yi wa rumaisa shamaki da shiga sashen ammi, sai dai ta jira ta ce wurin ammi suka zo, ak shiga da su sashen Ammi.


Ko da ammi ta ga rumaisa sai da mamaki ya kama ta, shekaranjiya rumaisan ta zo, yau ma kuma gata.

Ammi ta É“oye mamakinta, ta yi musu maraba, a nutse Yasir yake gaida Ammi, rumaisa kuwa ko gaisawar ba ayi ba, ta koma kusa da ammi ta É—au Sabir.


Shi kansa takawa kallon rumaisan take, wannan nacin na ta ya fara yawa.


"Rumaisa ya mamanki"


"Tana lafiya ƙalau" ta ƙarasa maganar tana jujjuya sabir da yake bacci, wai sai ya tashi ya ganta.


Hakan kuwa aka yi sai da sabir ya buɗe ido yana miƙa, wasa rumaisa ta yi masa, ya geɓare baki ya fara murmushi.


"Laaa kun ga, yayi mini dariya, Yasir kalli yana yi mini dariya, ya gane ni, sabir ummanka ce rumaisa ka gane ni ko?"


Ammi ta ce "Ikon Allah, ko bacci bai fiye dariya ba, lallai ya ganeki, ke ya fara yi wa dariya".


"Kaii dama kewarsa ce ke damuna, na yi ta mafarkinsa, na cewa mama a rakani mandawari na duba Æ´ar uwarmu Hauwwaliya, na cewa yasir dan Allah ya rakoni na ga sabir É—ina"


Ammi kallonta take tana murmushi, tana jin daÉ—in yadda sabir ke yi wa rumaisa murmushi.


"Rumaisa baku gaisa da baban sabir ba" ruma ta É—ago ta kalleshi ta ce "Ni ma bai kulani ba, yauwwa ammi wai da gaske shi yake shayar da shi?"


"Shi wa?"

Rumaisa ta nuna Adam ta ce "Haka ya ce mini, wai idan aka bani sabir bani da abun da zan shayar da shi, na ce masa ana bashi madara, wai ba a bashi madara shine yake bashi abun da ake bawa jarirai wai ni idan an bani sabir me zan bashi?"


Paid book ne ₦500 via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*




Dariya ce ta kuwa kufcewa ammi, ta ce "A'a rumaisa wannan maganar dai taku ce ba tawa ba"


Takawa dai ko kallonta bai yi ba, dan ya fuskanci yarinyar ba ta da kunya sam.


"Amma dai ammi ai ni ban taɓa ganin maza suna shayarwa ba, shi kuma ya ce mini haka, kuma dai na ga shima ƙirjinsa babu komai"


Ammi rasa amsar da za ta bawa rumaisa ta yi, can sai hankalin rumaisa ya É—auke daga kan maganar.


"Ammi" ta faÉ—a a hankali.


"Na'am umman sabir"


Rumaisa ta washe baki ta ce "Wayyo daɗi, ammi na ji daɗi, Allah ya amsa dukkanin buƙatinki, na fili da na ɓoye ya biya miki buƙatunki na alkhairi, na ji daɗi da ki ka kirani umman sabir"


"Amin rumaisa, in dai kin ji daɗi, ina son ki din ga saka baban sabir a addu'a, Allah ya biya masa buƙatunsa".


"To ammi, ai saboda ke zan yi masa addu'a ba dan halinsa ba"


"Subhanallah, meye da halin nasa?"


"Ba ki ga yadda ya tsaneni ba? Hmm baki san halinsa ba ne"


Wani ƙarfin hali sai rumaisa, mace da ɗan ta, amma tana faɗin ba ta san halinsa ba ne.


Ammi ta ce "Rumaisa takawa mutumin kirki ne, fiye da yadda ki ke tunani, kawai mutum ne mara son hayaniya da shiga sabgar mutane".


"To ni dai saboda ke zan yi masa addu'a kawai"


"Yauwwa rumaisa, maƙiya sun saka shi a gaba, wai cewa aka yi shi ya kashe aisha ya yi tsafi da gawarta, kuma sabir ba ɗan sa bane ba"


Ruma ta waro ido ta ce "Wai dama da gaske yasir yake, muna tafiya a hanya ya gaya mini, Innalillahi kam bala'i, to shi kuma yayi shiru" ta yi maganar tana ƙare masa kallo.


Sai kuma ta sake cewa "To shine yayi kuka da aka faÉ—i haka? Na ga kamar idonsa yayi ja?".


"A'a ba kuka ya yi ba, addu'a dai zaki din ga yi masa"


Ruma ta ce "Taɓ, ammi kin san wani abu?".


Ammi ta ce "A'a".


"Nifa wallahi dan mutanen duniya sun tsaneni suna yi mini sharri, in dai Allah yana so na shikenan, kin ganni a unguwarmu ce mini ake ƙanwar maza, wai idan na yi tsokana yayyena suna tare mini, eh wataran suna tare mini, idan aka koma gida kuma su hukuntani, har gida aka je aka cewa mama wai bani da tarbiyya, tun da ƴan unguwarmu suka yi mini tambarin rashin ji na daina jin nauyin kowa. Idan na yi musu abun arziki ba a zuwa a gayawa mama ko yayyena, da na yi rashin ji, za su zo su faɗa. Ni kuwa tun da na gane haka na daina saurarawa kowa, idan na yi tsokana ta ko a zaneni, ko.....


Jin zancen nata ba kai ba gindi ya sanya yasir cewa "Bari mu tashi mu tafi".


Ammi ta girgiza masa kai, ta ce "Baka ga hira muke yi ba, ina jinki umman sabir"


Ta sake gyara zama ta ce "Tun da na fuskanci ƴan unguwar nan ba sa yaba mini a kan abun arziki, ya sanya na zauna a kan kalmar rashin ji, idan aka ce na yi abu bana jin shakkar in ce na yi ko kasheni za ayi, idan ban yi ba komai za ayi mini ba zance na yi ba. Allah kaɗai nake tsoro shi ya halicceni kuma jin tsoronsa dole ne. Wallahi ammi a kan gaskiyata sai da a kasheni, kin san bala'in da na gani a hannun 'yan bindiga kuwa? Hmmm ai wallahi idan nice shi, zan kalli duk wanda ya ce na kashe matata na ce na kasheta idan kana da alaƙa da ita ka nemi shaida ka kaini kotu.

Ba dai baba mai farin rawani ne baban Anty Aisha ba, kuma ya ce mini ya san baban sabir ba zai cutar da anty aisha ba, to wallahi sai na kalli uban kowa na ce masa na yi ɗin. Ai su yadda na fuskanci mutane, idan suka yi maka ƙage, ka yi ƙoƙarin kare kanka, to zasu yi ƙoƙarin su ga sun sake binciko wani laifin saboda zasu gane ka tsorata, yaya usy ya ce mini, na koyi rayuwa nikaɗai a lokacin da babu wanda zai taya ni ƙwatar ƴancina, sannan na fuskanci abun da yake bani tsoro, aikuwa na ɗauka, ai tunda na gane ƴan unguwa sun gane lagona su kai ƙarata gida mama tayi mini faɗa na fetsare, ka kai ƙarata gobe na yi maka abun ya fi na jiya, idan ka kawo ƙarata aka tambayeni na yi in ce eh, zaɓi ya rage a kasheni ko a barni da rai.

Wallahi ammi idan ya ce wa masu cewa ya kasheta yayi ɗin, ya gani idan za a cigaba da takura masa, duk wanda ya damu ya kai ƙara, ko kuma tun da ɗan sanda ne ya kamosu ya yanke musu hukunci, su faɗi yadda aka yi suka san kasheta ya yi, ko kuma ya kullesu ba rannan wata haka ta yi ba, wannan kwamishiniyar ba aka ce wani ya ɓata suna ba, aka kai su gidan yari, ko decoration of character ko me ake cewa oho dai".


Duk da damuwar da adam yake ciki, sai da ya tattara hankalinsa yana sauraron rumaisa, duk da ba kallon in da take yake yi ba. Shi wasu lokutan har tsoro take bashi, ta wani fannin maganganunta a kan gaskiya suke, da maganar hankali da shirme haka take kwaɓa kayan ta.


Ammi ta ce "Waii, rumaisa an gaisheki, ban taɓa ganin yarinya irinki ba, ke kuwa ya ƴan bindiga suka iya zama da ke?"


Ruma ta yi murmushi ta ce "Haka suka zauna da ni, amma na ci ubana ba ƙarya ammi. Ni fa tun da ga kano aka ɗaukemu da ƴan bindiga, har kaza suka sai mini da na ce ina jin yunwa, suka nuna mini wata jaka, cike da bullet, har da bindigogi, shugabansu ne fa ya zo in da aka yi garkuwa da mu, ya sakeni ni da sabir, shi wanda ya sai mini kaza, ammi garin da na je, idan ka yi noma ba zaka taɓa ba sai ƴan bindiga sun yi maka izini, ni na je na ɗauki masara aka je aka gayawa mai gari, da nake a gidansa.


Da aka yi garkuwa da ni, baki ji abubuwan da suka faɗa a gabana ba, na ce idan na kuɓuta sai na faɗa suka ce kona faɗa a banza, la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin, na yi ta karanta musu, ba ƙaƙƙautawa sai Allah ya kawo mini anty aisha, daga baya kuma muka kuɓuta ni da sabir"


Ammi ta yi wata irin ajiyar zuciya ta ce "Amma abun da mamaki, wannan wane gari ne haka?"


Rumaisa ta É—aga kai ta kalli adam, sannan ta ce "Na manta sunan garin"


Adam tambayoyi ne fal a ransa, amma girman kai ya hana ya tambayi rumaisa, gashi ammi ta fara taɓo abubuwa masu muhimmanci, amma rumaisan ta kauce taƙi magana.


Ruma ta yi wa sabir kiss, ta miƙawa ammi shi ta ce "Ammi, bari mu tafi, kar mu yi dare ba mu je gidansu Hauwwaliya ba".


Ammi ta ce "To madalla, Allah ya tsare dan Allah ku gaida mamanku, ku jira bari na baku kuÉ—in mota".


Ruma ta ce "A'a muna da kuÉ—i, na ga kaya na gode sosai da sosai, baba mai farin rawani ma, ya bani kaya har da kayan gara masu daÉ—i da zuma da nono, da kilishi na gode sosai"


Ammi ta takura ruma, ta basu dubu biyar suka tafi.


Bayan tafiyarsu ammi ta kalli takawa ta ce "Adam, dan Allah ne ka fuskanta game da yarinyar nan, ji yadda take magana kamar ana karanta mata?"


"Ni banga komai ba sai shirme da rashin nutsuwa a tare da ita".


Ammi ta ce "No, maganganunta abun dubawa ne, a duk lokacin da duniya ta nemi juya maka baya, ka kama Allah ka nuna musu zaka iya rayuwa kai kaɗai, kar ka yi ƙoƙarin lallai sai an yadda da kai"


Ya numfasa ya ce "Ammi wannan shirmenta ne kawai na ƙuruciya, da rashin sanin ciwon kanta, yaushe ta zo duniyar balle ta san me duniyar ke ciki, tana tunani ne a iya ƴar ƙaramar duniyar ƙwaƙwalwarta, bari na tafi masallaci ".


Ammi ta ce "Shikenan Allah ya taimaka".


Sai dai maganganun rumaisa suka cigaba sa shiga suna fita a cikin kwanyarsa, kamar maganganun ta na bisa turba.


Rumaisa sai da suka je gidansu Hauwwaliya, ƙafar Hauwwaliya ta yi kyau sosai, suka din ga murna da ganin rumaisa, ana yin sallar magariba, Yasir ya tasata a gaba suka tafi gida.

A hanya yasir ya yi ta yi wa rumaisa faÉ—a a kan tsinannen surutunta yayi yawa, ko a jikinta tun da muradinta ya cika.


Bayan sallar magariba, Adam da kansa ya je gidansu Jabir, ya tarar da shi da Jamil suna tare.

Jabir ya ce "Ka gama jan ajin ka neme ni kena?"


"Jan ajin me fa?"


"Ai ka fini sani, ka ce zamu haɗu amma na yi ta kiran wayoyinki ka ƙi ɗagawa"


Adam ya ce "Ba ƙin ɗagawa na yi ba, kaɗaici nake buƙata ne, abubuwa sun sha kaina da yawa".


Jamil ya ce "Ai kai dama yanzu sai ana yi maka uzuri"


"Hmm baku ga abun da yake ta yawo a social media ba, game da mutuwar aisha? Wai yanzu rahoton cikin gidana shine labarin yaÉ—awa a media dan a É“ata mini suna"


Jamil ya ce "Ni kaina abun ya girgiza ni, na rasa yadda aka yi maganar nan ta fita a haka, tun É—azu ni da Jabir abun da muke tattaunawa kenan, yadda za a shawo kan matsalar nan, amma ya kake gani, me ka shirya gayawa duniya domin wanke kanka?"


"Ba ni da isasshen lokacin da zan ɓata wurin ƙoƙarin wanke kaina a idon duniya, ina da abubuwan yi da yawa a gabana, kuma ba za a kawar da hankalina a kan abubuwan da na sanya a gaba ba, duk wanda yake ganin yana da wani ƙorafi, ko son tuhumata a kan mutuwar matata, idan yana da shaida ya kaini kotu" yayi maganar yana jin kamar za ayi masa kallon wawa abun da ya faɗa.


Jabir ya waro ido ya ce "Yanzu kana nufin haka zaka zuba ido a cigaba da É“ata maka suna?"


"Idan sun gaji zasu daina, idan kuma basu gaji ba zasu cigaba, idan na cigaba da ƙoƙarin wanke kaina, za su cigaba da ƙoƙarin kaini ƙasa, idan na tsaya a kan ƙafata na cigaba da karɓar duk abun da za'a ce kaina, wataran gaskiya zata yi halinta"


Jamil ya ce "Amma kana ganin hakan mafita ce adam? Duk abun da ya shafeka ya shafi masarautar garin nan ne fa kai tsaye"


Adam ya ce "In da nake godewa Allah kenan, atleast masarautar nan wani immunity ne a gareni"


Su da suka san Adam da saka abu a rai, da shiga damuwa sun yi mamakin yadda yau ya nuna halin ko in kula da wannan lamarin.


Jabir ya ce "To, bari mu ga zuwa yaushe wannan mafitar taka za ta kawo sauyi ga lamarin nan, amma a ganina kamar kasada ce hakan, Allah ya yi mana jagora"


Adam ya amsa da Amin, ya miƙe ya ce "Bari zan shiga gari na ga Bashir, gobe in Allah ya kaimu zai bar gari, ina da muhimman abubuwan da zamu tattauna".


Jamil ma tashi yayi ya ce "bari nima na gangara gida, na gaida Alhaji, sannan na wuce gida sai sa safenku".


Jabir ya ce "To Allah ya bamu alkhairi"


Kamar yadda Jamil ya faÉ—a, gida ya wuce ya je ha gaida mama da turaki, sannan yayi aniyar tafiya gidansa, Samha ce ta bi yo shi, tana kiran sunansa.

Ya tsaya yana jiran isowarta, ko sa ta ƙaraso, hannunsa ta ja ta ce "Mu je motarka mu yi magana" bai musa mata ba suka wuce motarsa, suka shiga.

Shiru ne ya É—an ratsa, daga bisani ya É—an numfasa ya ce "Ina jinki"


Ba tare da ta kalleshi ba ta ce "A duniya bayan mama bani da wani kamarka yaya jamil, mama ta kasa fahimta ta, ban sani ba ko kai zaka fahimceni, domin kuwa kaine dai-dai da zamanin da muke ciki"


Jamil ya ce "Haka ne, ina saurarenki".


"Yaya jamil game da takawa ne"


Ya dubeta ya ce "Takawa again, me kuma ya faru?".


"Maganar nan ce dai ta shekarun baya, tun da Aisha ta mutu ina son maye gurbinta, na so na je wurin baba da kaina, amma sai na ga rashin dacewar hakan, ka taimaka yaya kai kaÉ—ai zaka fahimci halin da nake ciki"


"Wai ke samha ba zaki ƙyal adam ba kamar baki da zuciya? Duk cikin tarin samarinki babu wanda zaki fitar ki aura sai shi dai?"


Kamar ta fashe da kuka ta ce "Da zan iya cire shi daga zuciyata da tuni na yi, dan Allah ka taimakeni yaya jamil"


Jamil ya É—an yi shiru sannan ya ce "Zan fara yi wa adam É—in maganar na ji mai zace"


Da sauri ta ce 'A'a dan Allah kar ka gaya masa yanzu, turaki zaka fara yi wa zancen"


"To amma kin san magana yanzu ba zata yiwu ba, tun da haryanzu ana cikin alhinin mutuwar nan"


"Ohhj God, to sai zuwa yaushe kenan?"


'dole ki yi haƙuri, lokaci ya ɗan tura kaɗan"


"To shikenan na gode, ina saurarenka ka gaida gida " ya jinjina mata kai, ita kuma ta buÉ—e motar ta fita, tana jin a jikinta kamar a wannan karon za ayi nasara.



Kamar wutar daji, haka Zancen mutuwar aisha, ya cigaba da zaga gidan jaridu, da kuma kafafen watsa labarai, yayin da ta ɓangarensa yaƙi cewa kowa komai, kuma yaƙi magana da kowane ɗan jarida.

A yau babu tsammani, mai girma turaki ya karɓi baƙuncin wambai da misalin ƙarfe tara na dare.

Turaki yayi mamakin ganin ɗan uwan nasa a wannan lokacin, amma ya ɓoye mamakinsa, ya karɓe shi.


Wambai ya ce "Na san zaka yi mamakin ganina a wannan lokaci, sai da ba komai ne ya kawoni ba, illa zuwa in sake tabattar da abun da kunnuwana suke jiye mini, kuma ka yi burus, ba ka ce da ni komai ba"


Cikin rashin fahimta, turaki ya ce "Meke nan kake nufi?"


"Maganar rasuwar Æ´ar wurinka aisha mana, ko kai ba ka jin jita-jitar da ke ta yawo a kan mutuwarta?"


Turaki yayi murmushi ya ce "Alhamdilillah, da kai da kanka ka ce jita-jita ne, nima haka nan na tsinci zancen"


"Turaki na zuwa na yi domin mu yi wasan barkwanci ba, gaskiyar lamari zaka sanar mini, gaba É—aya mutuncin masarauta na nema ya zube, martaba da kimar gidanmu adam na ta cigaba da rusata sa shi da uwarsa, wannan wane irin abu ne?"


Turaki ya girgiza kai ya ce "Na san mai ɗakina ce ta je ta gaya maka wasu abubuwan, maganar da ke yawo a gari, tabbas aisha ta mutu a hannun 'yan bindiga, amma ba adam ne sila ba, ko ya kasheta ya sha jininta ba kamar yadda maƙiya ke ta kwarmato, kuma yarinyar da aka tsaresu tare ta zo da yaron wurin aisha".


"Turaki kana nufin goya masa baya wurin ɓoye laifinsa, dan me za a ce a ƙasar waje ta mutu a ɓoye gaskiya, wannan banzan aikin da yake yi na shishshigi ga manyan ƙasar nan da kawo ƙarshensu, ai gashi shi zasu kawo ƙarshensa, ko iya wannan labarin an yi mana mummunan tambari, a ce an samu babbar zuriya kamar ta mu da ƙarya. Dan haka dole a hukunta adam, sai ya yi wa duniya bayanin yadda matarsa ta mutu domin wanke ahalinmu daga mummunan zargin tsafi da kisan kai, ga uwa uba ayar tambaya a kan yaron da ake ce nasa ne, na baku awanni arba'in da takwas, idan har bai yi abun da na ce ba, matakin da zan ɗauka a kan sa ba zai yi muku daɗi ba.

Kai banda tsabar rashin sanin ciwon kai, kamar ba Æ´arka ba wane irin abu ne haka?"


Turaki ya ce "Da Adam da A'isha, duk tsatso É—aya ne, kuma Æ´aÆ´anmu ne, dukkansu.....


Bai ƙarasa ba, wambai ya ɗaga masa hannu tare da faɗin. "Ba nasiha nake buƙata ko tunatarwa ba, martabar ahalinmu da sarautarmu nake ƙoƙarin karewa, dan haka ayi abun da muka umarta, ko a ga ba dai-dai ba"


Turaki yayi ajiyar zuciya, ya bi wambai da kallo, da ya tashi fuuuu ya fice.


Yayi ajiyar zuciya yana jin wani irin matsanancin tausayin Adam.


Duk wannan kumfar bakin da wambai yayi, ya biyo bayan ziga da kuma famfon da Mummy ta je har gida ta yi masa tare da taimakon hajiya sauda, shi kuma kamar kullum ya hau kai ya zauna ba tare da bincike ba.


Rumaisa har islamiyya ta koma, in da malamai da ɗalibai suka din ga yi mata barka da arziki na kuɓutowa daga hannun ƴan bindiga, sai dai a wannan karon ma, duk yadda ƴan bugun ciki, suka so ta basu labarin abun da ya faru da ita ƙi ta yi, wasu har suna cewa rumaisa ta koma saliha.

Bayan tashi daga islamiyya, ta wuce gidansu habiba, dan tun da ta dawo ba ta je gidan su habiba, suka rungume juna suna tsalle a tsakar gida.

Daga bisani suka zauna suka hau hira, mamansu habiba ta zubo musu É—an wake, suka kewaye suna ci suna hira.


"Ruma ina yaya Aliyu ne?"


Ruma ta kalleta ta ce "Meyasa ki ke nemansa?".


"A'a, tun a asibitin nan ban kuma ganinsa ba"


"To meye haÉ—inki da shi, to idan son sa ki ke yi, zaki dinga sai mini kayan daÉ—i kina bani"


Waro ido habiba ta yi ta ce "Astagfirullah, dan Allah ruma ki daina yi mini haka, baki san kirkin da ya yi mini ba lokacin da nake zuwa gidanku da ki ka É“ata, mai sunan baba yayi ta hararata, shi yake rarrshina ya dawo da ni gida".


Ruma ta kwashe da dariya, ta ce "Allah sarki habibata, kamar ba nan muke kwasar dambe da ke ba, ke ni shawara zaki bani ma"


"Shawarar me" habiba ta yi maganar tana suÉ—e hannunta.


"Mutumin nan da ya ƙwace mini jaririna, wai ya zan yi da shi ne in karɓo ɗana?"


"Wai ƙwace jaririn suka yi gaba ɗaya to saboda me?"


"Saboda wulaƙanci mana, kullum da tunanin yaron nan nake kwana nake tashi, babarsa fa cewa ta yi ta bar mini shi, amma ya ƙwace mini shi. Habiba kin san in da kotu take? Ƙararsa zan je na kai, ba dama an ce zulai ta kai ƙara kotu alƙali ya bata ɗan ta ba, to nima kotu zan kai shi".


Habiba ta É—an yi shiru ta ce "Tsoro nake ji ruma, kin san ba a wasa a kotu"


"Na sani, ai ba wasa zamu je ba, ƙara zamu kai".


Habiba ta ce "To, a unguwar su babanmu akwai kotu, dama za ayi sauka a gidan, sai ki zo mu je".


Ruma ta yi murmushi ta ce"Amma na ji daɗi habiba, Allah ya kaimu in sha Allah sai an bani ɗa na, bari na tafi gida" ta miƙe suka fita tsakar gida suka wanke hannu, ta yi wa maman Habiba sallama sannan ta tafi gida.


Idan har da wanda za'a zarga a kan mutuwar aisha, to ba kowa bane ba face ni mahaifinta, domin ni na ɓoye ainihin abun da ya faru, adam ba matsafi ba ne, bai kashe aisha ba, kuma bai yi tsafi da gangar jikinta ba, a madadinsa, ina mai baiwa al'umma haƙuri na ɓoye haƙiƙanin gaskiyar abun da ya faru.


Mummy ta yi jifa da wayar hannun ta, bayan kammala karanta abun da turaki ya sanar da Æ´an jarida, ya wanke adam.


Ayshercool.

No comments