Breaking News

Kanwar Maza Book 2 Page 12

 



Cigaba da tunkaro su ruma suka yi, ruma kuma ta tattara hankalinta ta ga me za ayi.

Suna zuwa suka


kewaye su rumaisa, ɗaya daga cikin su ya sanya hannu zai ɗaga Aisha, amma ruma ta saka hannu ta kare, ta ce 'Wai me zaka yi mata? Matar aure ce fa yaya zaka taɓa ta?".


"Ke, ni ki ke yi wa wannan maganar?" Ya kuma kai hannu zai janyo Aisha, amma ruma ta riƙe hannunsa. Jin hayaniya ya sanya Aisha motsawa a hankali ta buɗe idonta, ta kalli mutanen da ke tsaye a kanta, ta yinƙura da ƙyar ta tashi zaune ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un Lafiya?"


A karo na uku, mutumin ya kai hannu ya danƙi Aisha, ya fara janta, ruma kuma ta miƙe zata bi bayansa, ɗaya daga cikinsu ya danƙo ruma, yayi jifa da ita a gefe ya saita ta da bindiga.


Da sauri sha tara ya ce "A'a kar ka kuskura ka yi mata wani abu, akwai yarjejeniya tsakaninmu da ƙungiyar su barde, mun yi yarjejeniya a kanta, muddin wani abu ya sameta zamu yaƙi juna, babu ruwanku da ita, zan riƙe muku ita, dan ba zata yarda ta bari ku yi aikinku ba".


Yayi maganar tare da ƙarasawa ya danƙo ruma, aikuwa ta hau bori, tana kiran Anty Aisha, Aisha kuwa ta kasa magana, sai miƙawa ruma hannu take yi, mutumin nan kuwa babu imani sai janta yake yi.


Cikin gigita ruma ta ce "Dalla ka cikani, suwaye su me zasu yi mata?"


Sha tara ya ce "Ke a shegen shishshigin ki, zaki jawa kanki abun da ba shikenan ba" kan ruma ta kuma yin wata maganar, sha tara ya watsa wa ruma wani abu a fuska, ta silalale a wurin nan, tana gani sama-sama.


***

"Uwani ki buÉ—e kunnenki da kyau ki ji ni, bana son a wannan karon a samu wata matsala, ki yi mini aikin nan yadda yakamata"


Baba uwani ta risuna ta ce "In Allah ya yarda ba zan bari a samu wani kuskure ba uwar É—akina".


"Yauwwa, aikin da na saka ki ki ka kasa, Fauziyya ta yi mini rabin aikin, dan haka ƙarashe ne zaki yi yanzu, Fauziyya ta tabattar mini da ta gano in da maganin nan yake, yana ɗakin iman, a cikin drowern mudubinta, dan haka duk yadda zaki yi, ki samo mukulli ki buɗe wardrobe ɗin nan, ki ɗauko mini, akwai wani aiki da za ayi mini, wanda lallai sai da shi".


Baba uwani ta É—an yi shiru tana nazarin yadda za ta É—au wannan kasadar.


"Ya ki ka yi shiru ko ba zaki yi ba?"


"Wace ni? Ki ƙaddara an gama wannan aikin uwar ɗakina, zan yi da iznin Allah".


"Ai na zata ba zaki yi bane, sai kuma abu na biyu, wata jita-jita nake son ki yaɗa mini a gidan nan, na san daga nan har masarauta kowa zai ji, dan duk wani mufurci ku hadimai kun iya shi. Ina son ki je ki yayata cewar, Adam ya yi shaye-shaye ya bugu ya tashi yinƙurin yi wa iman fyaɗe!"


Ras! Gaban baba uwani ya faÉ—i, ta gyara zamanta ta ce "Uwar É—akina, fyaÉ—e kuma?"


"Eh, ko baki ji ba?"


"Allah ya baki yawan rai, na ji zan kuma aiwatar"


A wulaƙance "Mummy ta ce "Tashi ki je"


Jiki a sanyaye baba uwani ta tashi ta bar É—akin.


A hanyar komawa sashinsu ta haɗu da baba sabuwa, sabuwa ta ƙure uwani da ido, uwani ta ce "Lafiya ki ke yi mini wannan kallon haka?"


"Lafiya lau, kawai ina tunanin ranar da dubunki ta cika ya zaki yi? Baiwar Allah can ta yarda da ke ta baki amanar kanta da ta 'ya'yanta kina ci, duk wahalar da take yi miki"


A fusace baba uwani ta ce "To ina ruwanki, bana son saka ido fa, wallahi idan ba ki yi wasa ba, sai na gaya mata ta É—au mataki a kan ta".


"Wallahi ki ka gaya mata, kan ta É—au mataki a kaina zan É—auka a kanku, dan sai na ja abun da za'a É—auremu duka, dan nima na san sirrinta tana sakani aiki, ni idan nayi mata babu laifi, dama hadimarta ce ni, ke kuwa fa? Ki dai ji tsoron Allah wallahi" ba ta jira me baba uwani za ta ce ba, ta tafi ta bar wurin.


Hajiya Jamila ɗawisu sarkin ado, sukari ba ka yi farin banza ba, gugar ƙarfe sha kwaramniya. Haka hadimanta suka shiga jera mata kirari, sai dai babu wanda ta kula ta cigaba da takunta ɗai-ɗai ta nufi sashin Ammi.


Ammi kuwa na zaune ita da Adam a É—akinta, yana zaune a gabanta ya sunkuyar da kansa, sai dai duk ya rame, cikin nutsuwa da tawakalli Ammi ke yi masa nasiha.

"Har kullum Adam ba zan gaji jadadda maka batun yin addu'a ba, addu'a na da muhimmanci a rayuwarka, tun da na haifeka a cikin jarrabawa ka ke, ko in ce muke, ka ƙara haƙuri wannan ma zamu cinyeta da yardar Allah, ka yi haƙuri ka jure, na sani akwai ciwo amma ka sani, jarrabawa alamar soyayya Allah ce ga bawansa, kullum cikin Addu'a nake maka, har abada maƙiyanka fadawanka ne, waɗanda ka sani da wanda ba ka sani ba, Allah zai ije maka su in dai har kana Addu'a, ni dai fatana ka rage zafin zuciya adam, babu in da zuciya zata kai ka, ka din ga haƙuri da yanayin da duk zaka tsinci kan ka" wata hadimar Ammi ce ta nemi izini ta shiga, ta sanarwa da Ammi zuwan Mummy.


Sai da gaban Ammi ya faɗi, ba ta ƙaunar abin da zai haɗata da Mummy, dan ba ƙaramin fargaba take shiga ba, ƙarfin Addu'a ne yake sanya ta iya riƙe kanta.

Jiki a sanyaye ta tashi ta fita falo, ta tarar da Mummy a zaune a falon tana yi wa iman magana, sai dai ba ta kai ga jin abin da take cewa iman É—in ba ta yi shiru.


Ita kanta iman ba ƙaramin tsoron Mummy take ji ba, saboda haɗuwarsu babu daɗi sam, ta tsaneta sosai da sosai.


Fuskar iman Ammi ta kalla, ta san akwai wani abu da Mummy ta gaya mata, da ya sanya Iman shiga ruɗi, dan fuskar iman kullum idan ba murmushi ba, to tabbas shagwaɓa, amma sai ta ga iman a razane.


Mummy kuwa na ganin Ammi ta faÉ—aÉ—a murmushin ta, ta risuna ta ce "Allah ya taimaki giwa, barka da fitowa".


Ammi ta nemi wuri ta zauna, ta ce "Barkan ki dai, kuna lafiya?"


"Eh to, mun gode Allah sai dai ba na ce lau ba, yara babu wanda yake zuwa, duk sun ɗauke ƙafarsu".


"Kin san yanayin makaranta, ba sa samun zama shi ne kawai".


Mummy ta yi murmushi ta ce "Haka ne, dama yara ne suka zo mini da batun rashin lafiyar takawa, na ce bari na zo na yi masa sannu, Allah ya bashi lafiya, amma gaskiya yakamata ki tashi ki nema masa magani, shi da ake sanya ran ya gaji mahaifinsa, amma ya din ga abu kamar mahaukaci, gaba É—aya zance ya cika masarauta har kunnen manya".


Kalmar mahaukacin da ta kira Adam da shi, ba ƙaramin dukan Ammi ya yi ba.


Amma ta maze ta ce "Ai shi lamari irin wannan, duk maganin da zaka nema, lafiya ta Allah ce, idan ka miƙa masa lamarinka kuma, sai ya kawo maka mafita, tun da shi ya halicci kowa".


Mummy ta ɗan kaɗa ƙafa ta ce "Haka ne, akwai wasu ɗabi'unki da suke burgeni, wanda har nake koyi da su, ƙarfin hali da yarda da kai, bari mu gani idan yana da rabon warkewa, Allah ya bashi lafiya, na barki lafiya uwar masu jiran gado" ta miƙe tana wani irin shu'umin murmushi.


Kan iman Ammi ta mayar da idonta ta ce "Iman, me ta ce miki ne?"


Iman ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Bakomai Ammi, tambayata take ya jikin Takawa" Ammi tayi shiru, dan ta san iman ƙarya tayi mata, ba ta takura sai ta ji ba, saboda kar ta ji abin da zai ƙara bata haushi.


***

A hankali ruma ta buÉ—e idonta, ta ji kanta kamar ba nata ba, yayi mata wani irin nauyi har yana nema ya rinjayeta, daga kwance nan ma jiri take yi.

Shiru ta yi tana ƙoƙarin tuna abin da ya faru, kan abun da aka watsa mata ya ɗauketa, ta tuna yadda ta ga ana jan Aisha, da ta ja ta tsaya saboda cikinta, ɗaya daga cikinsu wani ya tsinketa da mari, har sai da ta durƙushe saboda gigicewa, ɗaya daga cikinsu ya takata da ƙafarsa, ta saki ihu daga haka ruma ba ta san meya kuma faruwa ba.

A gigice ruma ta tashi, sai dai ta cigaba da tangaɗi, saboda abun bai saketa ba, Aisha ta hango a zaune jingine da bishiyar da suke kwana a ƙasanta da daddare.

Ruma ta nufeta, amma ta kasa sauri, da ta yi ƙoƙarin yin sauri, sai ta ji tana ƙoƙarin faɗuwa.

Tana zuwa ta tarar da Aisha a zaune, idonta É—aya ya tara jini, fuskarta duk a kumbure, zaninta kuma na farin leshi, ya rine da jini, sai haki take yi.


"Anty Aisha menene? Me suka yi miki?" Ruma ta yi maganar da ƙyar.


Alama ta yi wa ruma da ta ƙaraso kusa da ita, ruma ta ƙarasa a hankali ta zauna a kusa da ita. Aisha ta miƙa hannu ta riƙo na ruma, ta ɗora a kan cikinta sannan ta ce "Rumaisa, takani suka yi a cikina, kin ji babyna ba ya motsi" tayi maganar tana fashewa da kuka.

Kuka ruma ta saka ta ce "Suwaye su? Me ki ka yi musu?"


"Ban sani ba, sun ce ba dan su karɓi kuɗin fansa suka ɗaukoni ba, dan su tozarta ni ne, ki yi mini Addu'a dan Allah, Allah ya sa babyna yana raye, na fara jin jiri, na zubar da jini da yawa".


Ruma ta rasa abun yi, ta rungume Aisha suna kuka.


"Zaki iya tashi a rakaki wurin da zaki wanke jikinki?"


Barde yayi maganar yana kallon Aisha.


Ruma ta ce "Ba ta so, mugwaye azzalumai, marasa imani, me ta yi muku?"


Barde ya ce "ke! Ki daina ganin ina ɗaga miki ƙafa, wannan matar ba an ɗaukota ne dan ayi garkuwa da ita ba, mutanen da suka zo ɗazu su suka yi garkuwa da ita".


"Wallahi ba zata je ba, ba ta so salon ku kuma yi mata wani abun"


"Shikenan, kun huta".


Aisha ta ce "Rumaisa ki yi sallolin da suka wuce ki, sai ki sakamu a addu'a"


Ruma tayi taimama, ta miƙe ta kabarta salla, dan Anty Aisha ce ta koya mata yadda ake yin taimama, farillanta, da sunnoninta.


Da ta idar da sallar ma kusa da Aisha ta koma ta zauna, tana ta jera mata sannu.


****


Ammi na zaune a kan sallaya tana lazumi, Baba uwani ta faÉ—o dakinta a hargitse, da har sai da Ammi ta tsorata.


"Tuba nake ranki ya daɗe, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana, tuba nake ki yafe ni, na faɗo miki ɗaki babu neman iso, wani abu na jiyo da ya girgiza ni, na ga bai kamata na rufe miki ba".


Cikin mamaki Ammi ta ce "Ke kuwa menene haka?"


"Allah ya baki yawan rai, kin san zance a cikin masarauta ba ya rufuwa, ban sani ba ko a hadiman sashin nan ne da basu san meke faruwa ba, ni kin san tun yaranki na ƙanana muke tare da ke, wani zance na ji yo da ya ɗaga mini hankali na ce dole na sanar miki".


"Ina jinki, meyafaru?"


"Kin San rashin lafiyar nan ta takawa ba kowa ya san yana fama da ita ba, to jita-jita ta yaɗa gari wai shaye-shaye yake yi, yayi mankas yayi yinƙurin yi wa iman fyaɗe!"


Ras! Zuciyar Ammi ta yi wata irin mummunar bugawa, shaye-shaye ga kuma kalmar fyaÉ—e da aka jinginawa yaranta.


A kiÉ—ime ta ce "Uwani, a ina ki ka jiyo wannan mummunan zancen?"


"Hadiman gidan turaki na ji suna faÉ—a, ammma suma wai-wai suke yi ".


"Kenan Samha ce ta je ta faÉ—i wannan maganar?"


Cikin inda-inda uwani ta ce "Amm...a..a'a ba na tunanin hakan, ban dai san yadda a kai zancen ya fasu a haka ba" Ammi ta ja wani irin numfashi ta ce "Shine, jeki kawai" daga haka ta kasa tofa komai, saboda tsananin tashin hankali.


***

ÆŠan barcin da ya saci mama tana daga zaune, ta ji daÉ—insa sosai, dan dama ba iya baccin take yi ba. Aliyu yana zaune ya na yi mata ninkin kaya, mai sunan Baba kuma yana gyara socket É—in É—akin.

A gigice mama ta farka daga baccin, ta miƙe tsaye zata fita, cikin zafin nama mai sunan baba ya tashi ya riƙota yana faɗin "Ina zaki je ne?"


"Rumaisa ce a waje tana ƙwanƙwasa ƙofa zan je na buɗe mata ne".


"Haba, amma ya aka yi mu bamu ji bugun ba, ba kowa fa".


"Kai umar ka sakeni, tana ƙofar gida tana bugawa, sai kuka take ni na ganta, kuma na ji bugun". Umar zai iya ƙirga sau nawa mama ta kira sunansa da wayonsa.


Ya kwantar da murya ya ce "Mama, yau kuma umar ba baba ko mai sunan baba ba? Cewa fa ki ka yi kin ganta a waje tana kuka? Ta yaya ki ka ganta? bacci fa ki ke yi mafarki ne ba gaske ba?"


Sai kuma jikin mama yayi sanyi ta fashe da kuka ta ce "yi haƙuri babana, na zaci gaske ne, yi haƙuri na yi maka tsawa".


Aliyu ya ce  "Mama, tun da ki ka fara mafarkin ruma a Æ™ofar gida tana buga gida, in sha Allah ta kusa dawowa, ina jin hakan a jikina, baki ga Adduoin fa da ake yi mata ba".


Mama tayi murmushi ta ce "Ashe kai ma kana jin za ta dawo, na zaci nikaÉ—ai nake ji, dan dai kar in dameku ne, ina ma san ranar da zata dawo".


Mai sunan Baba ya girgiza kai ya ce "Shikenan, dama lokacin shan maganinki yayi, zauna in baki ki sha ki kwanta ki huta, Allah ya dawo mana da ita lafiya, ya tsare mana ita a duk in da take".


Kamar ƙaranar yarinya mama ta ce "Kai ma kana kewarta ko babana?"


"Mama ƙanwata ce fa, duk halinta jininmu ɗaya ina kewarta, zauna to" haka ya zaunar da mama da ƙyar, ya bata magani, dan mama har likitan ƙwaƙwalwa liktanta ya bada shawar ta gani, saboda depression na neman kamata.


***

Tamkar ciwo jira yake dare yayi, ciwo ya tayar wa Aisha, sai dai ta daure ta ƙi nunawa saboda kar ruma ta tayar da hankalinta.


Ruma da hannunta ke kan cikin Aisha, ita kuma ta riƙe hannun ruma, ruma na kwance lamo ba bacci take ba, can ruma ta ce "Laaa, Anty Aisha wallahi jaririnki ya motsa, baki ji ba?"


Da ƙyar ta yi murmushi ta ce "Na ji ruma, yana raye Allah ya sa ina da rabon ganinsa".


"Amin, bari in yi musu magana su kai ki asibiti "


Ta riƙe ruma ta ce "Ƙyalesu, ba zasu kai ni ba, na ji sauƙi ki zauna mu yi hira"


Ruma ta ce "Ni bana son hirar, so nake na ga kin koma kamar da"


Cikin dakiya ta din ga yi wa ruma hira, tana sakata dariya, amma a ƙasanta kuwa jini ne yake zuba sosai.


Jin tana cigaba da numfashi da ƙyar, ya sanya ruma ta tashi, ta tafi wurin 'yan bindigar nan ta ce "Dan Allah sha tara ku kai ta Asibiti, bata da lafiya sosai wallahi"


Duk da duhu ne, ya kunna fitila ya haske in da Aisha take, sai jujjuya kai take, zaninta yayi sharkaf da jini.


A aljihunsa ya sanya hannu, ya ciro wayarsa, ya kira wata lamba.


"Oga, matar nan fa kar ta mace mana, ya ake ciki azo a fita da ita ko zuwa wayewar gari ne"

Ruma ta kasa kunne, sai dai ba ta jiyo me na cikin wayar yake cewa ba. Sha tara ya kashe wayar ya ce "Da safe za a kaita asibitin, tafi ki kwanta"


Ruma ta tashi ta koma wurin Aisha, tana gaya mata ai da safe zaa kaita asibiti.


Aisha ta jinjina kai, ruma ta ce "Anty Aisha, wai daga ina jinin nan yake fitowa, ko fitsarinsa ki ke yi ne?"


"A'a ruma, amma dan Allah matso in din ga jinki a kusa da ni, jiri nake ji".


Ruma ta matsa ba tare da ƙyamar jinin ba, ta rungume Aisha.


"Rumaisa ina É—an kwalina da na baki?"


"Yana ƙunguna na ɗaure shi, na baki ne?"


Ta ce "Yauwwa sannunki baby rumaisa, ina ƙaunarki sosai"


Ruma da kuka take ta ce "Nima ina sonki sosai Anty Aisha".


"Idan na haifi mace sunanki zan saka mata, idan namiji ne kuma sunan wannan abokin naki da ya taɓa miki ƙirji, ya ma ki ka ce sunansa?" Ta yi maganar cike da zolaya, da son kunna ruma.


Aikuwa ruma ta ce "Wallahi ba za'a saka masa sunansa ba, ke me yayi miki zafi, zaki saka sunan É—an iska, ba gara a saka sunan Barde ba, tun da dai yana bamu abinci"


Ta yi dariya ta ce "To a saka mai sunan Baba"


Ruma ta ce "Kaii, ban baki wannan shawarar ba, faÉ—ansa kaÉ—ai ya isheki".


Aisha tayi wa ruma wani irin riƙo tana nishi, sannan ta ce "Kawo kunnenki ki ji wata magana".



AYSHERCOOL.

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*


*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* 

*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* 

*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*


*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*


👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*


*1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje* 


*2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* 


*3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* 


*4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin* 


*5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*


*6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* 


*7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*


*8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* 


*9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*


*10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* 


*11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* 


*12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje* 


*13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*

*14.  Supplement na whitening/glowing skin*


*15.  Supplement for Acne, dark spots remover*


*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*


*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*


Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*


No comments