Breaking News

Kanwar Maza Book 2 Page 10

 


Paid book ne, 500 ne via 00094


50228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*






Salati da salallami mutanen wurin suka fara yi, duk rashin imanin mutanen, idan suka so keta wa haddi, suna barin idon mutanen da su, amma yana nema ya keta ruma a gaban su.


Wasu kuwa gani suke ruma ita ta janyo wa kanta, tsananin ciwon da matar nan ke ji bai hanata jan jikinta zuwa in da suke ba, ta riƙe rigarsa tana kuka tana girgiza masa kai. Wani irin mari ya kwaɗa mata, da a take shatin yatsun sa suka bayyana a kan kuncinta.

Ɗaya daga cikinsu ya zo ya saka hannu ya dinga jan matar a ƙasa, ya wancakalar da ita a gefe.


Ya kuma danƙar skirt ɗin ruma, amma cikin ƙarfin hali ta riƙe.


Ji yayi an fincikoshi ta baya, an kwaÉ—a masa mari.

A gigice ya kalli wanda ya mare shi, barde ne wanda ruma ta bawa gyaÉ—a kuma yake kawo mata abinci wasu lokutan.


Wata irin ashar yayi masa, cikin ƙaraji ya ce "Me ka yi mata? Me na ce maka da aka kawo ta? Au har ka manta zaka karya yarjejeniyar?"


"Amma ai ka tsaya ka ji meyafaru kan kayi mini haka"


Cikin hasala barde ya ce "An maka É—in, wallahi da ka aikata abin da ka yi niyya, da sai na yi gunduwa-gunduwa da namanka a wurin nan" cikin huci ya nufi kan ruma, jikinta duk shaidar duka.


Ya ɗagota ya girgiza ta, ta buɗe ido ta kalleshi, a hankali ta fizge hannunta daga nasa ta mirgina ta kwanta a gefe, tana kallon matar nan, da take ta sauke numfashi da ƙyar, kamar sumammiya.


Bai sake ƙoƙarin taɓa ruma ba, ya ja ƙaton nan yayi gefe da shi yana yi masa magana.


Ruma ba ta sake bi ta kansu ba, a hankali ta mirgina, ta ƙarasa in da matar nan take kwance, tana numfarfashi, ruma ta ɗora hannunta a kan na matar, a hankali ta ji matar ta riƙe hannunta, ta sake matsawa jikin matar ita ma tana mayar da numfashi ba tare da wani ya tankawa wani a tsakanin ita da ita ba.


Dagaci kuwa tun da suka yi magana da dogo, a kan zai je ya bincika masa ruma, ya kira Aliyu ya sanar masa domin hankalinsu ya É—an kwanta, dan haka suka cigaba da dakon abin da dagacin zai ce masu, gashi Aliyu ya riga ya gaya musu yadda suka yi dagaci, dan haka mama kullum sai ta tambayi Aliyu, haryanzu dagaci bai yi magana ba?.


***

Kasancewa Adam ba a family house ya kwana ba, Kamar kullum bisa ga al'ada yana biyawa ya gaida Ammi, dan haka yau ma a cikin hanzari ya yake tafiya, ya ƙarasa sashinta.

A bedroom ya tarar da ita, sai dai saɓanin kodayaushe, ya tarar da fuskarta a haɗe, hakan ya tabattar masa da akwai damuwa.


Sai dai ya bari sun gama gaisawa, sannan ya ce "Allah ya baki yawan rai, lafiya na ga fuskar ki babu walwala?"


Ammi ta ce "A'a lafiya ƙalau, wambai ne ya bani saƙon cewa idan ka tashi daga aiki, yana nemanka" sak takawa yayi, ya dubi Ammi ya ce "Wani abu ne ya faru?"


"Ni ma ban sani ba, kawai dai ya ce yana nemanka?"


"Ko laifi na yi mass?" Adam ya sake tambaya.


"Ban sani ba takawa, ka je dai ka ji ko menene"


"Shikenan" ya faɗa a taƙaice, ya tashi ya ce "Na tafi".


"Allah ya tsare" Ammi ta faÉ—a ba tare da ta kalleshi ba.


Har ya kai bakin ƙofa Ammi ta ce "Adam!" Sai da tsigar jikinsa ta tashi, dan abu ne mai wahalar gaske ta kira sunansa haka kai tsaye.


Ya tsaya ya waiwayo ya kalli Ammi.


"Idan ka je wurinsa, ko me zai ce maka ban yadda ka tofa ko ka yi Æ™oÆ™arin kare kanka ba, ka bishi da to kawai" 

Ɗan shiru yayi yana nazari, akwai wata a ƙasa kenan, a zahiri kuma ya ce "To, in sha Allah".


A falo ya haÉ—u da Nusaiba, ta gaishe shi, bai iya amsawa ba sai jinjina mata kai kawai ya fice.


Yana tafe yana auna kashedin ammi da kiran da wambai yayi masa, saboda shi a yanzu tension ɗin da yake ciki ya ishe shi, ba sai an ƙara masa da wani ba.


Nusaiba ta shiga É—akin Ammi, ta tarar da ita zsune a gefen gado, ta yi shiru.


"Ammi" Nusai ta yi maganar kamar tana tsoron wani abu.


Ammi ta kalleta ta ce "Na'am ya aka yi?"


"Amma dai baki gaya wa takawa yadda kuka yi da wambai ba ko, kar ya hasala?"


Ammi ta girgiza kai ta ce "Ta yaya zan gaya masa, ni babban fatana idan ya je kiran da yake masa, Allah ya sa kar yayi masa irin cin mutuncin da yayi mini, kin san halin yayan naku da zuciyar tsiya babu lallai ya jure, dan ma na taushe shi kan ya tafi"


Jiki a sanyaye Nusaiba ta ce "Ammi ni fa gaba É—aya a maganganun da yayi, na kasa gane wane point yake son yayi magana a kai, sai kame-kame kawai yake yi yana faÉ—a na babu gaira babu dalili, ko dai Mummy ce ta je ta gaya masa wani abu?"


Ammi ta girgiza kai ta ce "Bana tunanin haka, kin san shi dai dama mutum ne mai zafi, a bar maganar kawai, 'yar auta ta ba ta tashi bane?"


"Eh bacci take yi, kin san exams suke shirin farawa".


Ammi ta jinjina kai, ta cigaba da jan carbinta.


****

Hatta masalattan unguwar su rumaisa, duk salla sai an yi addu'ar Allah ya bayyana rumaisa, saboda garkuwa da rumaisa abu ne da ya zo a bazata, kusan za a iya cewa ita ce yarinya ta farko da aka sace a unguwar, dan duk irin wannan abubuwan sai dai a ji su a nesa, amma yau gashi a cikin unguwa.


Kamar yadda dogo ya yi wa dagaci alƙawari, ya koma masa da maganar ruma.

Tun da dagaci ya ji dogo ne ya zo yake nemansa jiki na rawa ya tashi, ya fita tare da fatan Allah ya sa a dace a samu rumaisa.

Iya ma tashi tayi ta biyo bayansa, ya tsaya ya kalleta ya ce "Ke kuma ina zaki?"


Cikin rikicewa Iya ta ce "A ruÉ—e nake, ni dai mu je in ji me zai ce"


"Dan Allah ki koma, duk yadda muka yi da shi, idan na dawo zan sanar miki" da ƙyar ta yadda ta koma gida, amma ta ja ta tsaya a tsakar gida.


Cikin sauri ya fito ya iske dogo suka gaisa, cikin zaƙuwa ya ce "Ya ake ciki ka ganota?"


Dogo ya ce "Eh na ganota, tana rukunin su sha tara, sun ce ba zasu bayar da ita ba, ba sa buƙatar kuɗin fansarta, dan haka ku cigaba da addu'a, wannan yarinyar halinta zai iya sakawa su kasheta, halin na ta nema ya sanya suka ce ba zasu bayar da ita ba, dan haku ku cigaba da addu'a kawai." Daga haka dogo bai kuma ce masa komai ba ya yi tafiyarsa.


Dagaci kuwa ya tsaya ya dinga nanata Innalillahi wa Innalillahi raji'un.


Jiki a sanyaye ya koma cikin gidan, iya ta tare shi tana faÉ—in "Ya ake ciki, me suka ce maka?"


Yayi shiru ya kasa magana. "Dan Allah ka yi magana mana, menene ya ake ciki ya ganota? Sun faÉ—i me za a basu?"


Ya girgiza mata kai ya ce "Tana nan a raye, amma sun ce ba sa buƙatar kuɗin fansa, ita ɗin suke so, halinta ya saka suka ce ba zasu bayar da ita ba ta zama ta su"


"Wayyo Allah na shiga uku, yarinyar mutane ta salwanta a dalilinmu, na shiga uku na lalace".


"Meye haka ki ke yi kulu? Wannan ai rashin hankali ne".


"Ƙyaleni na yi rashin hankalin, har abada uwar 'yar nan ba zata mamta da ni da gwaggo ba na shiga uku, da na sani ban karɓi rumaisa ba, ban san haka zata faru ba, Allah ka shiga lamarin nan wayyo Allahna"


Haka dagaci yayi ta fama da iya tana kwarmato da É“urari.


****

Rana ce ta take a kan su ruma, a hankali ta ja jikinta da yake mata ciwo, ta tashi zaune, jikinta babu abin da yayi saura sai tsabar ƙarfin hali da taurin kai.

Da wannan ƙaton ta fara tozali yana hararata, ita ma hararar ta watsa masa, ta mayar da idonta kan matar nan, ta fara tattaɓata. A hankali matar ta buɗe ido, ta kalli ruma, tana ganin fuskar rumaisa ta yi murmushi. Ita ma ruma murmushin ta yi mata sannan ta ce "Tashi koma waccan bishiyar, nan rana ta tarar da mu".


Cikin ƙarfin hali ta ce wa ruma "Ba su yi miki komai ba ko?"


Ruma ta jinjina mata kai, da ƙyar matar ta tashi, da rarrafe suka canza wuri zuwa wata inuwa suka zauna.


"Yunwa ki ke ji ko?" Ruma tayi maganar tana kallon matar.


Ta girgiza wa ruma kai ta ce "A'a, ke nake so ma ki samu ki ci wani abu, baki da lafiya, dan Allah ki daina rigima kar su illata ki, ba zan ji daÉ—i ba".


Ruma ta ce "Mhmm ki daina damuwa da ni, ni na saba da kasada, sonake su kasheni na huta na gaji".


"A'a bana son a kashe ki, in sha Allah zaki fita lafiya ƙalau".


"Ban ga alamar hakan ba, gara na tunzurasu su kasheni na huta, suma su huta amma wallahi in dai suka barni a raye na din ga tayar wa da uban kowa hankali kenan".


Matar ta waro ido ta ce "Ke ba kya jin tsoro ne?"


"Taɓ, ai tsoro yayi yamma na yi gabas, ni fa ƙanwar maza ce guda bakwai, ko 'yan unguwarmu sun sanni, dan ma na daina dambe da maza, yayyena sun hanani, duk wata kasada idan na ɗauko in tafi ƙarfina su suke shigar mini, ni fa har wata 'ya na taɓa karyawa. Bindigogi ne fa kawai da su, to wallahi bana tsoron bindigar su kamar yadda nake tsoron mai sunan Baba".


"Waye haka kuma?"


Ruma ta gyara zamanta ta ce "Yayana ne, sunanshi umar, hmmm ina tsoron Allah ina tsoron sa, nifa bana jin tsoron mama kamar yadda nake tsoron sa, kin san idan nayi laifi baya tashi hukuntani, sai cikin dare ina tsaka da bacci zan ji ni a sama, in zata ko raina aka zare kin san ance idan mumini ya mutu, to sama ake yi da ransa, to sai na ji an watsoni tsakar gida, sannan nake gane ai ina duniya, hukuncin ma sunan Baba ne, idan ya haÉ—e rai ya tattare girarsa sai na ji kamar in zawo a tsaye". 


Duk da halin da suke ciki, bai hana matar yin murmushi ba, dan ba ƙaramin dariya ruma ta bata ba.

Ruma ma Murmushin ta yi ta ce "Mai sunan baba dodon marasa hankali in ji mama, idan ya sakani kama kunne a daren nan, to wallahi da asuba a zaune zan salla saboda azaba, mai sunan Baba ya iya punishment"


"Ni kuwa zan so na ga mai sunan Baban nan da ki ke tsoro fiye da bindiga".


"Kema idan ki ka ganshi sai ya baki tsoro, shi fa ba ya dariya, kullum fuskarsa a haÉ—e, wataran ko hararata yayi sai na kwana uku a nutse".


Dariya suka yi tare, ruma ta ce "To baki gaya mini sunanki ba, ina mijinki da 'yan gidanku?"


Matar ta yi murmushi ta ce "Suna na, sunana Aisha".


"Anty Aisha, ke a wani garin ki ke?"


"Zan gaya miki, yanzu jikina babu daÉ—i na bugu, yaron cikina sai juya wa yake".


Cikin damuwa ruma ta ce "Sannu, Allah ya sa su sake ki kan ki haihu, Allah ya sa ki amayo shi lafiya"


Cikin dariya ta ce "Me zan amayo?"


"Ɗan mana, ba ta baki ake yo aman jariri ba, haka mama ta ce mini, amma su fa akuyoyi to ta wurin kashin su suka haifo ɗa, daga yi wa mama tambaya ta ce idan na kuma wurinda akuya ta haihu sai ta zaneni" halin da Aisha ke ciki bai hanata yin dariya ba, ta riƙe cikinta, saboda dariyar ta ƙarfin hali ce.


"Ya naga kina dariya, ko ba ta nan ake haihuwar ba?"


"Ta nan ne mana, Allah ya sa na amayo shi lafiya".


Ruma ta ce "Amin, ina zuwa" daga haka ruma ta miƙe ta nufi mutumin nan ta je ta tsaya masa a ka, ya ɗago ya kalleta ya ce "Me kuma ki ke nema?"


"Abinci, yunwa muke ji"


Ɗagowa yayi yana ƙarewa ruma kallo, ita ma ƙyar ta ƙure shi da nata idanuwan.


Wata leda ya ɗauka ya wurga mata ya ce "Gashi nan shegiya mayya, mayuwanciya" ta durƙusa ta ɗauka ta ce "Koma me zaka ce na ji, na dai fi ƙarfin ka, ba yadda zaka yi da ni".


Tun mutanen wurin suna namakin ruma, har sun saba da halinta, kome zata yi sai dai ta ci duka, amma ban da haka ba wanda ya isa yayi mata wani abu.


Ta koma wurin Aisha ta zauna ta ce "Anty Aisha, tashi mu ci abinci" tayi maganar tana buÉ—e ledar.


Buredi ne a ciki da pure water.


"Matsiyata kullum daga gurasa sai buredi".


Aisha ta ce "Ruma dan Allah ki din ga shiru, kin ga baki da lafiya, kar su sake dukanki".


"Wai meyasa ki ka damu da ni haka ne? Dan Allah ki daina damuwa idan ba haka ba sai na koma baki haushi, haka nake, in dai ba gajiya zasu yi su kasheni ba, suna tare da wahala" ruma ta ƙarasa maganar tana miƙawa Aisha buredin a baki.


Murmushi ta yi ta karɓa, ba dan buredin na yi mata daɗi ba, sai dan rashin mafita.


****


Kwanaki kusan talatin kenan da sace ruma, babu wata tartibiyar magana a kan in da take ko yadda za a sameta, ga mama sai ciwo take a tsaye, ko ta sha maganin hawan jini, jinin baya sauka, ga ulcer ta yi mata mummunan kamu saboda rashin cin abinci.


Yanzu haka suna zaune duk sun kewayeta, amma babu iya cewa komai, sai ma ita ce cikin ƙarfin hali take musu faɗa, a kan rashin cin abinci.


Usman ya dubi Aliyu ya ce "Dan Allah ka sake kiran mijin iya, ka ce masa haryanzu muna jira bai ce mana komai ba, an samu an yi maganar da su kuwa?.


Usman bai yi musu ba, ya kira mijin iya, Abdallah ya ce "Ka saka mana a hansfree mu ji".


Aliyu ya saka wayar a hansfree, suka gaisa da mijin gwaggo sannan ya É—ora da cewa "Baba haryanzu ba ka ce mana komai ba, an gano a in da taken, ko kuma sun faÉ—i abin da za a basu?"


"Aliyu zancen ne babu daÉ—in ji, shi ya sanya na yi muku shiru".


"Sun kasheta ne?" Abdallah yayi maganar a kiÉ—ime.


"A'a, ba kasheta suka yi ba, wanda muka tura ɗin ya dawo ya sanar da ni cewa sun ce ba sa buƙatar komai ba zasu bayar da ita ba, halinta ya sanya za su riƙeta ko kuma a fansheta da 'yan mata biyar, duk iya ƙoƙarin da zan yi na yi abu ya faskara, sai dai mu cigaba da addu'a kawai".


Gaba É—aya aka rasa mai magana, sai mama da take ta "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ya sa ba taurin kan take yi musu ba, Allah ka kuÉ“utar mini da yarinyar nan ka tsare mini ita" tayi maganar tana kuka 


Abdallah ne ya rungume mama yana rarrashinta, yana goge mata hawaye.


***

Mintuna kusan talatin da takawa ya sanya aka yi masa iso wurin wambai, amma shiru bai fito ba gashi ya fara ƙoasawa da zaman, dan haka ya tashi da nufin ya tafi, dan akwai tarin ayyukan da suke gabansa ya yanke ya taho.


"Na sallameka ne zaka tafi, ko nima halin rashin É—a'ar zaka gwada mini?" Cak ya tsaya ya waiwayo ya kalli wambai da ya shigo falon, sanye da jallabiya ba tare da naÉ—i ba.


"A'a ranka ya daÉ—e, na zaci ba zaka samu fitowa ba, na baro ayyuka da yawa na taho" 


"Saboda ayyukan ka sun fi kirana muhimmanci ko, ashe abubuwan da ake gaya mini akan ka gaskiya ne ko Adamu?" Cikin mamaki Adam ya ke kallon wambai.


"Zaka nemi wuri ka zauna, ko kuma jera kafaÉ—a zamu yi sannan mu yi magana?"

Adam yayi ajiyar zuciya, ya samu wuri ya zauna a ƙasa yana tunanin laifin me yayi wa wambai haka har yake kiran sunansa haka.


"Dukkanin abin da ka ke yi ya sameni, kuma ka bani mamaki ka bani kunya, turbar da ka É—auko ba ita ce turabar da mahaifinka ya É—oraka a kai ba, dan haka ka shiga hankalinka idan ma uwarka ke zigaka kanka yake rawa gara ma tun wuri ka nutsu ka shiga hankalinka, kuma wallahi idan ba ka yi wasa ba, sarautar da kake jiran ba zata dawo gidanku ba, idan ma ta dawo É—in sai dai a bawa É—an uwaka tunda kai dai ba ka san abin da yake maka ciwo ba" maganar Ammi ce ta sanya shi yin shiru, gaba É—aya ya rasa a kan me Wambai yake yi masa faÉ—a tare da ci masa zarafi, shi ce masa yayi yana jiran a bashi sarauta ne?.


Nan da nan jijiyoyin kan Adam suka É—aga, saboda tsananin É“acin rai, haka tsohon nan ya saka Adam a gaba ya zage shi tsaf ba tare da wata tartibiyar hujja ba.


Sai da yayi mai isarsa sannan ya tafi gida, da ƙyar ya kai kansa gida, yana shiga sashen Ammi ya tara da su Fauziyya da Samha a falon Ammi.


Wucewa yayi ciki yana ta huci, Ammi da take zaune tare da su a falon ba ta tashi ba, ta basar da shi. Cike da gulma Fauziyya ta ce "Ammi meya sami takawa ne?"


Ammi da tun daga shigowar su Fauziyya shashenta ta san akwai wani abu a ƙasa, dan rabonta da su anfi wata guda, kawai ta basar ne.


Ammi ta ce "Babu komai, ina ga aiki ne yayi masa yawa kawai".


"Kin ga yadda idonsa yayi ja kuwa? Kamar ba shi da lafiya fa".


Iman ce daga kitchen ta wuce É—akinta, dan sam  a ta san abin da zai sanyata shiga shirgin su Fauziyya, tana zuwa ta tarar da takawa a tsaye a É—akinta, tamkar zai fashe, ya watsarwa mata da kayan kan mudubinta, sai karkarwa yake.


Yana jin motsin iman, ya buÉ—e jajayen idanunsa yana kallonta.


Girgiza masa kai ta shiga yi, amma ta kasa gaba ta kasa baya.


"Zo nan ya faÉ—a a kausashe".


"Dan Allah ka yi haƙuri, ba ni na ɓata maka rai ba" tayi maganar cikin rauni.


"A hayyacina nake iman, hannunki kawai zan riƙe".


Cikin rawar murya ta ce "Amma ba zaka yi mini komai ba?"


"Na rasa abin da zan riƙe, kaina zai tarwatse ne, help me just your hands" cikin tsoro ta nufe shi, ta ƙarasa nesa kaɗan da shi ya kama hannunta ya riƙe tamkar zai ɓallata.


Ihu ta ƙwala jin yadda ya murɗa mata hannu, haƙoransa sai karkarwa suke yi.


Sama-sama suka jiyo ihun iman, suka tashi suka nufi É—akin Iman.


Takawa suka tarar ya banƙare hannun Iman, hannu ɗaya kuma ya shaƙeta, rigar jikinta ta ɗage sai kokowa take da numfashi tana kakari.!!


No comments