Breaking News

Kanwar Maza Book 1 Page 18

 



Sarai ya ji abin da ruma ta ce, amma ya share kawai ya tafi, dan idan ka biye mata babu abin da zai hana ta saka maka hawan jini.



Sai a lokacin ta samu zarafin dirarwa wainar da mama ta yi, ta fara ci ta na ajiyar zuciya, dan a kwanaki ukun nan Allah kaÉ—ai ya san tsananin damuwar da ta shiga.


Yasir ya ce "Na so auren nan aka yi miki, mu ga ta tsiya, kowa ma ya huta da halinki"


"Ta Allah ba taka ba, bakinka ya sari É—anyen kashi, na asuba mai tururi"


Mama ta ce "Meye haka, ki na cin abinci kina zancen ƙazanta"


"To mama ba sune suke tsokanata ba"


"Ina ruwanki da su, wato har kin samu kanki za ki É—ora daga in da ki ka tsaya ko?".


Ta girgiza kai ta ce "A'a, ai na shiryu ba zan ƙara ba"


"Kima cigaba, wallahi kin san idan ya zuciya da halinki, zai aikata abun  da ya ce"


Sallamar Abubakar da suka ji ne, ya sanya ruma yin wani zillo, ta daka tsalle ta yi waje, maƙalƙale shi tayi tana murmushi tana faɗin "Oyoyo yaya"


"Amarya ba kya laifi, kar dai har an É—aura auren ban samu É—aurin auren ba?"


Ta É“ata fuska ta ce "Yaya har da kai ko?"


"A'a, nima fa kirana aka yi a waya, aka ce mini yau É—aurin aure"


Waiwaya ta yi, ta kalli mai sunan Baba da ya shimfiÉ—a tabarma ya baje litattafai yana dubawa, ta kalli Abubakar, ta kai bakinta kunnensa ta ce "Wallahi hussaininka ya É—au hakkina, ba dan yayana bane ba ko? Hmmm"


Ya kalli mai sunan Baba ya yi murmushi ya ce "Kai, a wani dalilin ya sa ka É—aga mana hankali haka fisabilillahi?" Ko É—agowa bai yi ba, balle ya kallesu. Ruma ta kama hannunsa suka shiga É—akin mama.


Mama ta ce "Ta barka ka ƙaraso in ganka kenan? Na ga ta je ta tsareka da zance, kamar ba yanzu ta gama kuka da neman taimako ba"


Abubakar ya yi murmushi, ya zauna ya ce "Sannu da gida Hajiya mama, uwar 'yan maza da 'yar budurwa, na sameku lafiya?"


Mama ta yi murmushi ta ce "Lafiya lau Alhamdilillah, amma ba ka da lafiya ne?"


Ya É—an kalli jikinsa sannan ya ce "Me ki ka gani?"


"To ai ganinka nayi wuri-wuri duk ka rame Saddiƙu"


Ya shafi sumar kansa da taru sosai ya ce "Mama wannan karatun namu, ai ba sauƙi ne da shi ba, pressure ce kawai, ruma zubo mini abinci" miƙewa ruma ta yi, ta fita ta kawo masa kulolin abincin ta dire masa, ta zauna ta saka shi a gaba, tana ta zuba masa surutu, mama kuwa kallon yadda yake zira abincin nan yake babu ji babu gani, kai da ganin yadda yake cin abincin ka san akwai yunwa a tare da shi, ba dai ta ce komai ba suka cigaba da hira.


Da la'asar shi da mai sunan Baba suka tafi masallaci, bayan sun dawo kuma suka zauna a tsakar gida suna hira.

Ruma so take ta zauna da Yaya Abubakar, ta yi masa hira sosai dan ya fi kowa tsayawa ya saurareta, amma ta ga hankalinsa yana kan É—an uwansa.

Ganin ta zauna daga nesa tana ta kallonsu, ya sanya yaya Abubakar cewa "Ruma, É—auko comb ki zo mu yi tsifa, na ga kitson kanki ya tsufa" ta jinjina masa kai, ta shiga É—aki ta É—auko comb da kibiya ta kawo masa, ta zauna a kusa da shi, tana yi tana kallon fuskar Umar, dan kar ya hantareta ko ya koreta.

Yaya Abubakar ya karɓi kayan tsifar, ya kwantar da kanta a kan cinyarsa, ya fara tsfefe mata kai.

Rai a haɗe mai sunan Baba ya ce "Amma dai ka san bana son ƙazanta ko?"


"Ƙazantar me kuma?"


"Dan me zaka zo kusa da ni kana aikin gashi, ko ƙyanƙyami ba ka ji"


Abubakar ya yi murmushi ya ce "Kayi karatunka ka ƙyalemu mu yi tsifar mu" a hankali ruma ta fara lumshe ido, bacci yana ɗibarta, cikin gyangyaɗinta ta ji Abubakar yana cewa mai sunan Baba "Ka ga ƙoshin nan da na yi cikina har wani ciwo yake yi"


Mai sunan Baba ya kalle shi ya ce "Kamar yaya, da ba ka ƙoshi ne?"


"Wallahi Akhi rabona da Abinci kusan kwana biyu yau, a ƙafa fa na taho tasha, na samu mota na taho gida shi ma daga tasha na ninko, Allah ya haɗani da wani ɗan unguwar nan ya goyoni a babur"


Cikin mamaki Umar ya ce "Garin yaya?"


"Wallahi kamfanin 'yan chinan da muke yiwa aiki ne suka koremu, suka kawo mutanensu. Ni kuma na ga ban aiko da komai gidan nan ba, ta yaya zan bugo na faɗi matsala, na sayar da wayata na sai ƙarama ina ta fama, gashi mun kusa exam, shiyasa ban zo gida ba, shekaranjiya garrin kwaki na ci ko jiƙawa ban yi ba, na wahala a semester nan wallahi"


Umar yayi tsaki ya ce "Akhi kana da matsala, amma ko baka gaya wa mama ba, ni mai ya hana ka gaya mini, sai ka je ka kashe kan ka da yunwa, idan ba abinci ta yaya karatu zai yiwu?"


"Kai ba fa ban gaya maka ne dan ka yi mini masifa ba, ko nima ƙaninka ne?. Na tafi na barku kuma kuna ta fama da yadda zaku yi, ni ban muku ba, kuma na ɗoro muku matsala, gashi na yiwa yarinyar nan alƙawarin sabuwar jakar makaranta ban samu saya mata ba, har kunyarta nake ji wallahi".


Mai sunan Baba ya numfasa ya ce "Dole mu din ga gaya wa juna matsalolinmu, watarana sai labari, ni kaina abubuwan sai a hankali, na saya wa yarinyar nan sabuwar katifa kusan dubu talatin,  ta ta ta lalace, da so nake na sauya mata makaranta, makarantar gwamnatin nan ba ta iya komai, an ce mini registration dubu Arba'in, duk term kuma dubu Ashirin da biyar, gashi muma an yi mana Æ™arin kuÉ—in makaranta, ga komai ya yi tsada, rayuwar Æ™asar nan sai dai Allah ya sassauta mana, ina jin su Huzaifa ma suna zancen zasu yi sauka, suma kusan dubu sittin ake nema su biyu, ga garin a tsaye yake cak, sai dai Allah ya iya mana kawai, ita kanta mama ba Æ™aramin Æ™oÆ™ari take ba, yakamata ace zuwa yanzu ta fara hutawa, ta sha wahala domin mu rayu mu zama mutane".


Abubakar ya ce "Haka ne, amma komai lokaci ne, daga cikin godiyar da nake yiwa Allah shi ne kasancewar dukkaninmu Allah sa babu wani wanda yake fita ya É—auko mata magana a waje, ko ba komai hankalinta a kwance yake "


"Sai wannan abar" mai sunan Baba yayi maganar yana nuna ruma, da tayi pretending kamar bacci take.


"Ba wani É—aukar magana, guda nawa take"


"Kai ba zaka gane ba, da ta je ta karya 'yar mutane a makaranta, sai da aka kusa korarta, har wurin 'yan sanda aka kaita"


Abubakar ya waro ido ya ce "Autar"


"Hmm kai ba ka nan, ba ka san wainar da ake toyawa ba kawai, wannan yarinyar ba ta da kai sam, kullum cikin nemo magana take ana ta abin da za a ci"


"To a daina faÉ—a, gara ayi ta mata addu'a "


Mai sunan Baba ya ce "Ai Addu'ar ce kamar ba ta kamata, duk gidan nan babu mai ibada kamar mama, kuma babu wanda zai yi mata addu'a ta karɓu sama da wadda take mata, amma haryanzu shiru, kullum rashin jin ta gaba yake yi, ni tausayi take bani wasu lokutan, tana da zaɓe-zaɓen abinci, and we can't provide what she wants, kuma ba ta san babu ba, sai ta zauna tana kuka, wai an bata kunu ba suga, ko ba za ta ci tuwo ba, could you imagine?"


Abubakar yayi murmushi ya ce"Allah dai ya yassare mana, in sha Allah za su huta, ita da mama"


Ruma da ta yi bakamm ta na jin su, wani irin tausayinsu ne ya kama ta, wato duk wannan zare idon da hantarar da mai sunan Baba yake yi mata, yana son ta har yana tausayinta haka.


Tana wannan tunane-tunanen har baccin gaske ya yi awon gaba da ita, sai magariba ta tashi, Yaya Abubakar ya tsefe mata kai tas ya taje, dama ya saba yi mata tsifa idan har yana gari.


Duk in da suka gilma sai tayi ta kallonsu cike da jin tausayinsu, tabbas tun da ta buɗi ido a duniya, yayyen nan na ta maza kowa ƙoƙarinsa ya ga ya kawo abin da za a rufa kai asiri, haka mama kullum cikin faɗi tashi take.

Ta zubo abincin dare ta zauna tana kallon yadda kowa ke ta walwala kamar ba su da wata damuwa, ta zubawa su Mai sunan Baba ido, da suka zuba Abinci kwano É—aya, tausayin Abubakar ya kamata, da tuna yadda yake gaya wa É—an uwansa ya kwan biyu bai ci abinci ba, kuma ya sha garri ba ruwa balle suga, kuma ba wanda ya gayawa.

Ta kalli Abincin gabanta, Usman ya sayo kifi ya ɗora mata a kan abinci, kifin da shi bai ci ba, bai kuma bawa kowa ba sai ita, gefe ga ƙullin lemon fata da Aliyu ya shigo da shi, shi ma bai sha ba ita ya bawa.

A hankali ta ture abincin, ta shiga ɗaki ta zauna tayi shiru, sai kuka wani irin ƙauna da tausayin yayyen nata ya kamata.


Babu tsammani ta ga mama ta hasketa da fitila.


"Kukan me ki ke yi a duhu haka, ga abincin ki ba ki ci ba?"


Da sauri ta girgiza kai ta ce "Ba kuka nake ba"


"To me ki ke yi idan ba kuka ba, ƙarya nake kenan?"


"A'a mama ni fa ba kuka nake yi ba"


"To meya hana ki cin abinci ki ka dawo É—aki ki na kuka?"


Ta girgiza kai ta ce "ba komai"


"Wai ba ance miki batun auren nan wasa bane ba, shi ne ki ka cigaba da takura kanki, ba zaki tashi ki je ki ci abincin ba?"


"Ba magana ake yi miki ba, ko sai na zo kan ki?" Ta jiyo muryar Yaya Umar daga tsakar gida. Jiki na rawa ta taso ta fito.


Cikin haÉ—e rai ya ce "zauna ki cinye abincin nan, sai wani ciwon ya kama ki ki cazawa mutane"


Ƙoƙarin kai abincin bakinta take, amma ta kasa kuka ya kuma ƙwace mata.


Aliyu ne ya dubeta ya ce "Ko Abincin ne ba kya so, ki ke yiwa mutane kuka? Me zaki ci?"


"A'a zan ci"


"To kukan me ki ke yi?"


"Ku ƙyaleni dan Allah, na ƙoshi ne" tayi maganar tana share hawaye.


Abubakar ya ce "Ikon Allah, taso dawo nan kusa da ni, zo ki saka hannu mu ci namu abincin tare" ba ta son ɓata masa rai, dan haka ta tashi ta je kusa da shi ta zauna, ya dinga ɗebo abincin yana bata a baki tana karɓa yana rarrashinta ba tare da sanin dalilin kukan nata ba, sai dai ba rarrashin da yake yi mata ne ya sanya ta yi shiru ba, hararar da mai sunan Baba ya jefeta da ita ne, ta sanyata haɗiye kukan da take yi.


Haka ya dinga lallaɓa ruma, da kansa ya gyara mata wurin da zata kwanta, ya saka mata net, har da yi mata addu'a, hakan ya ƙara sanya tsananin tausayinsa a ranta.

Sai da ya tabattar ta ɗan nutsu, sannan ya tashi ya fita, Mai sunan baba kuwa sai tsaki yake yi, yana hararar Abubakar, ya san da ya yi wani yinƙuri na yiwa ruma tsawa, zasu yi faɗa.


Mama har ta manta da batun ruma, ta na shirin kwanciya, ta sake jin sheshsheƙar ruman a cikin net ɗinta.


Mama ta kuma haskta da fitila ta ce "Ke dan ubanki fito daga cikin net É—in nan, ki zo ki gaya mini abin da aka yi miki?"


Ruma tayi saurin goge fuskarta tayi kamar bacci take yi.


A hasale mama ta ce "Ba zaki fito ba sai na zo?" Ruma ta janyo jikinta ta fito, ta zo gaban mama ta zauna, amma ta kasa magana.


"Gaya mini menene kuma? Ko wani ne yayi miki wani abun?"


Ruma ta girgiza kai, "to kukan me ki ke yi wa mutane, ki gaya mini ko na leƙa na kira miki dodon naki"


"Kiyi haƙuri, zan gaya miki amma kar ki ce na gaya miki"


Mama ta ce "Ina jinki" nan ruma ta kwashe komai ta gaya wa mama, sannan ta ɗora da cewa "Mama Allah ya bamu kuɗi, ya horewa su Yaya ya sa kar su daina zuwa makaranta, kuma ni ba sai an canza mini makaranta ba, Allah ya bamu kuɗi su daina shan wahala, yayana ya kwana biyu bai ci abinci ba mama, wai an kore shi daga kamfani bai gaya miki ba" ta ƙarasa maganar tana kuka.


Jikin mama yayi sanyi ainun, duk wauta sa rashin tunani irin na ruma ashe ta na da hankali wasu lokutan, biri ya yi kama da mutum, Abubakar ya rame amam yaƙi gaya mata meke faruwa.


Mama ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ruma, kin ga wannan yana ɗaya daga dalilan da yasa nake miki faɗa a kan nutsuwa, ke gaki a gida amma sai abin da ki ke so shi zaki ci, kin ga yadda suke ta wahala da ƙoƙarin faranta mana, dan Allah ki daina rashin ji kin ji, ki yi ta yi muku addu'a, nima ina yi, yanzu ki je ki kwanta, gobe in Allah ya kaimu kin san zaki tahfiz". Ruma ta jima ta kwanta, sai dai bayan kwanciyarta mama ta kasa barci, sai tunanin yadda za ta ɓullowa al'amuran.


*****

Kirarin da É—aya daga cikin hadiman Ammi ke ta rangaÉ—awa ne, wadda suke kira da Baba uwani, ya tabattar wa da su Iman da ke zazzaune a falo, takawa zai shigo, nan suka din ga kintsawa, ban da Iman da ta rashe a jikin Ammi, suna hira.

Sai dai Adam tare da Jabir suka shigo, hakan ya sanya Iman jan mayafi ta rufe kan ta.

Cikin girmamawa suka gaida Ammi, Jabir ya kalli Iman ya ce "Ke ba ki san girma ya zo ba ne?, Look at you, you are now a big girl duk kin bi kin danne mana Ammi"


"To idan ba ta danne ni ba wa zata danne? Ƙyaleta 'yar auta ce ai"


Jabir ya yi wani murmushi sannan ya ce "Ammi, biyo takawa na yi, na kawo miki ƙararsa, ko ke zai ji maganar ki"


Adam ya harari Jabir, amma Jabir ya maze ya cigaba da magana.


"Ammi kin san halin ƙasarmu sarai, kin san yadda abubuwa ke gudana, duk da kasancewar sa shima wani ne, amma gaba da gabanta ta yaya zai sako Senator wakili da mutanensa a gaba, ai duk wanda ya kwana ya tashi, ya san mutane ne masu ɗaurin gindi, dan me zai tsananta?"


Ammi ta ɗan numfasa ta ce "Ban ƙi ta taka ba Jabir, amma abin nan na ga duk sabgar aikinku ce, ni ba komai nake ganewa ba, amma nima ina yawan yi masa magana a kan ya san in da zai din ga kai kansa"


"Yanzu haka Ammi, wai akwa ibom zai je, na rasa abin da zai kai shi wata akwa ibom"


Ammi ta kalli takawa, da ya kashingiÉ—a ya lumshe ido, kamar ba a kansa ake tattaunawa ba, ta yi murmushi ta ce "Rabu da shi Jabir, zan yi magana da shi"


"Ai gara dai Ammi" ya mayar da kallonsa kan Iman ya ce "Iman, É—an sama mini abin sha mai sanyi mana, zan je garden in É—an yi wani aiki"


Haushi ne ya kama Iman, ga masu aiki amma bai saka kowa aikin ba sai ita, ga Ammi a zaune balle ta ce ba zata yi ba.

Haka ta tashi ta tafi kitchen dan haÉ—a masa wani abun.


Adam kuwa É—akinsa ya wuce, ya je ya nemi wuri ya kwanta, dan ya ji kansa ya fara yi masa ciwo, tun wayewar garin yau.


A garden ta tarar da Jabir, tun da ta ɓullo ya kafeta da idanunsa, da hakan sai da ya ƙona mata rai, ta yi tsaki.

Tana zuwa ta dire masa jug da kofi, za ta juya.

"ÆŠan tsaya mana" ta tsaya cak, sannan ta waiwayo ta kalle shi.


"A tunaninki haka kawai na ce ki zo ki sameni a garden, magana zamu yi".


Cikin yanayinta mai kama da shagwaɓa ta ce "Ni uncle J karatu fa zan yi, ina da exams"


Tashi yayi ya zagaya kusa da ita yana kallonta.


"Maganata ba ta da muhimmanci kenan?"


Ta É—an ja da baya ta ce "To ina jin ka"


"Iman me na yi miki ne ki ka tsaneni, ki ke guduna kwanan nan?" Shiru ta yi ba ta bashi amsa ba. Sai gani yayi kamar ta É—an razana tana kallon wuri É—aya.


Waiwaya ya yi domin ya ga mai take kallo, Mahmud ya gani a tsaye yana kallonta, gaba É—aya ta ruÉ—e.


"Zo nan" Mahmud ya faÉ—a cikin isa yana kallonta.


Jabir ya ce "Kamar yaya ta zo, haka ake yi?"


"Ban saka da kai ba, kar ka É“ata mini rai"


Jiki na tsuma, Iman ta sunkuyar da kai ta nufi in da Mahmud ya ke.


"Amma Mahmud kamar ba ka ikon nuna wa iman wannan isar, tun da dai ba wani abu a tsakanin ku"


"Jabir, kafi kowa sanin waye ni, idan ba ka kiyayeni ba, za a ji kaina da kai, ba ruwana da abin da ku ka laɓe a lambu kuna yi, abin da ya dameni shi zan yi"


Waro ido Iman ta yi, jin abin da Mahmud ya faɗa, sai dai ko kusa ba ta ga fuskar da zata kare kanta ba, haka zalika ba ta da zaɓin da ya wuce ta bi umarnin Mahmud.


Ya tasata a gaba har sashin su na Mummy, da Mummy da Fuziyya da ruƙayya duk suna falon sai kuma Samha da dama tun tasowarta kusan kullum tana gidan su.


"On your knees" yayi maganar cikin tsawa. Cikin mamaki iman ta yi abin da ya ce, tana son jin laifin da ta yi.


"Ke saboda baki da mutunci, Mummy ta aika a kiraki amma ki ce ba zaki zo ba aiki ki ke yi wa Ammi, Mummy sa'arki ce?"


Cikin rashin fahimta iman ta ce "Ni kuma? Wallahi ba wanda ya zo ya kirani"


Mummy ta ce "Au iman ruƙayya ƙarya za ta yi miki kenan, ai da ka ƙyaleta, dama ta daɗe tana nuna mini ba ni na haifeta ba, dama ba wani abun ne ya sa na ce a kirata ba, dogwayen riguna ne na saya musu, nace ta zo ta karɓi nata".


"Wallahi Mummy ban haɗu da Ruƙayya ba jiya, ruƙayya a ina muka haɗu?"


Ruƙayya ta ce "Ni zaki rainawa hankali, kina falo fa kina kallo a lokacin ki ka ce mini ba zaki zo ba"


Samha ta girgiza kai ta ce "Yaya Mahmud, ta ina zaka yi tsammanin tarbiyya a wurin 'yar da ba jinin sarauta ba, 'yar karere 'yar riƙo"


Haka suka din ga jifan iman da miyagun maganganu.


Tun da ta taso, ta buɗi ido a gidan Galadima, take fuskantar ƙalubale sharri gami da makircin hajiya Jamila wato Mummy, makira ce ta gaske.

Suka ƙare mata cin mutunci, Fauziyya ta watso mata dogwayen rigunan a jiki, Mahmud ya ce ta yi godiya ta ɗauka ta bar sashen.

Ba yadda ta iya, ta aikata abin da ya ce ta tashi ta fita gwiwa a sanyaye.


Mummy tayi murmushi, a ranta ta ce bari mu gani, yarinyar nan zata gayawa wancan mahaukacin ne ya zo yayi hayagaga ko kuwa? Idan har ya zo yayi mana tashin hankali, zan tabattarwa da Samha akwai alaƙa a tsakanin iman da Adam, ko kuma in cigaba da amfani da wannan damar, wurin rura wutar ƙiyayya tsakanin Mahmud da shi, ina baƙantawa matar nan.


*****

Mama tayi ta faÉ—i tashi, ta tarawa Abubakar kayan abinci na komawa makaranta, wanda sam shi bai san ma tana yi ba, tun da ya dawo yake ta buga-buga yana tara É—an abin da zai tafi da shi, ranar da zai koma mama ta tambaye shi babu wata matsala, ya ce mata eh ai yana da komai.

Mama ta yi murmushi, ta nuna masa watto bagco ta ce ya É—auko, ya duba. Ya É—auko ya duba, kayan abinci ne da ta tara masa.


Ya ce "Mama na gaya miki fa ina da komai, Meyasa zaki takura kan ki?"


"A'a ni ban takura kaina ba, Ubangiji Allah ya bada sa'a ya taimaka" yayi ta yiwa mama godiya, mai sunan Baba ya raka shi tasha, ya bashi dubu biyar, amma sai da suka kai ruwa rana Sannan ya karɓa.


Ruma ce ta fito daga wanka, ta tsaya a gaban mudubi daga ita sai pant, tana kallon kanta.

Mama ta kalleta ta ce "Meye haka ne ki ke tsaye tsirara ki nemi kaya ki saka"


Ruma ta juyo ta kalli mama cikin damuwa ta ce "Mama kalleni"


"Na ganki meyafaru?"


"To ba abin da ki ka gani?"


"Ni banga komai ba"


"Mama wai baki ga ƙirjina kamar ya kumbura ba?"


Mama tayi murmushi ta ce "Na gani"


"Mama to ya kike dariya, ba alamomin ciwon Cancer bane?"


Mama ta ce "A'uzubil'ahi, ba wannan bane ƙirga dangi ki ka fara"


Cikin rashin fahimta ruma ta ce "Wane dangin na ƙirga, ni ina zan iya ƙirga danginmu?"


"Ba wannan ake nufi ba, girma ki ka fara zaki zama budurwa, fitowa za su yi"


Ruma ta haÉ—e rai ta ce "Ni bana son su fito"


Mama tayi dariya ta ce 'Saboda me?"


"Da nace ina son su fito a daina ce mini ƙwaila, Yaya Aliyu ya ce gara na yi zamana a haka, ai suma basu da shi"


"To ke namiji ce, da zaki zauna a haka nan gaba da kanki zaki zo kina nema daga baya, ke da a da ki ka ce zaki sayo na sayarwa ki saka"


"To ai yanzu na fasa, gara kar ya fito, idan ya fito fa ba zan din ga yawo ba riga ba"


Mama ta ƙarewa ruma kallo, alamomin girma duk sun fara bayyana a jikinta, mama ta numfasa ta ce "Yanzun ma ai na hanaki yawo babu riga"


Ruma ta É—au vest É—in ta ta saka, ta ce "Mama kalli fa, kalli yadda vest É—in fa tayi mini, to wai tsayi zai cigaba da yi? Ko kuwa?"


"Nima ban sani ba, sai ki bari in sun fito, sai ki ga yadda za su yi, ki dai kula da kanki, ban da wasan banza da maza ko mace, duk wanda yayi miki wasan banza ko ya kai hannunsa jikinki, idan kin zo ki gaya mini, wannan wurin ba wurin wasa bane, gaba É—aya jikinki ma al'aura ne abin alkintawa ne".


"Ni mutum ya taÉ“ani ma, ba sai na sumar da shi ba" 


"Ni dai bana son rashin hankali, ki kula da kanki, zuwa gaba in ga mai yakamata ayi, idan rigar mama yakamata a saya, sai a sayo ki farawa sakawa".


Ruma ta ce "Taɓ, haka kurum a din ga yi mini kallon 'yar iska"


Mama zata yi magana, usman  yayi sallama ya shigo, ba ta amsa sallamar ba ta ce "Yaya usy, kalleni me ka gani?"


Ya ce "A ina?"


"Au dan ubanki gaya masa zaki kin fara nono, ni yau na ga ta kaina, Innalillahi wa Innalillahi raji'un" 

Jin abin da mama ta ce ya sanya Usman ja da baya ya bar É—akin.


(Masu nema daga farko, ku din ga dubawa watpad ko arewabooks)


Ayshercool

08081012143

[01/08, 5:33 pm] JAKADIYAR AREWA:                 Æ˜ANWAR MAZA

                 


*Na Aisha Adam (Ayshercool)*


MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES



No comments