Breaking News

Kaddararmu 9-10

 KADDARARMU

                 (OUR DESTINY)


                        9_10

   


                          ✍️

A bangaren afra kuwa kullum batada aiki sai kuka tun hajia na rarrasheta har Suka zuba mata , inda malam auwalu yaje can companyn yafi a kirga Amma aka hanashi shiga ba yadda zasu haka suka hakura , suka zubawa sarautar Allah Ido ,

jadeeda data  Maida  wajen window wajen zamanta  ta zauna  tana kallon waje daga Cikin dakin da aka dawo da ita , yànzu basa  takura mata bakamar fakon zuwan taba, Dan kamar yadda madam Tafada a ranan aka kawo mata kayayyakin sauwanta  masu uban yawa kama dagà takalma , turarririka , nighties , komai da komai da akasan ya mace zata bukata haka aka jibge matasu hatta pad catoon biyar aka loda Mata Kuma duk lokacin dazata ci abinci , rose daya daga Cikin Yaran Madam zata zo tai mata jagora zuwa dining taci abincin tana Tsaye a kanta ,  data gama Kuma zata sakota a gaba su dawo dakin ta kulleta da key .

 

A Yauma tana zaune tana  kallon katon katafaren gidan da Kuma abunda ke wakana ciki.

 Wani mai aikin lambu ne ke yanke flowers din da sukayi cicciko  tareda levelling dinsu Yana yi Yana Waka daga Gani Yana Jin dadin aikinsa matuka , sai daga can gefensa Kuma  wasu maids ne su uku sanye da uniform zaune a karkashin bishiyar dabino  daya bawa wajen inuwar suna hirarsu suna Dariya daga Gani hirarsu suke akan abunda ya shafesu yayinda kamshin kasa ke Tashi , alamun hadari dake tasowa , wanan yanayin ne  ke  dauke mata  damuwar datake ciki ga Kuma kukan tsuntsaye Dake tashi sosai take Jin Dadin yanayin .

Bakamar farkon zuwanta ba , she was so panic da  Bata tsaya Karema gidan Kallo ba , yau kusan kwananta biyar da aka chanza mata daki , da alama Nan da aka kawota will be where she would be staying for now ,  matsalarta dayace afra , batasan halin datake ciki ba .

The estate was a very large one akwai  three gate guarding the estate ko Wani mighty gate,  akwai Guards kusan ashirin sanye da uniform na militry , who kept watch day and night , estate din Yana dauke da three mansion and the young master lived in the estate heart shine Inda aka kawo jadeeda .


A Cikin mansion din dayake zama Yana dauke da hawa uku first floor maaikatan gidan ne ke zama , na biyun kuwa ba kowa , na karshen ne  young master wato  ke zama a Ciki  shi kadai .


  Tun bayan fitowarta daga  dark room din Nan ta dauka a ranan zata hadu dashi shiyasa Bata iya Tayi bacci ba saboda fargaban datake ciki , dataji an taba kofa saita Tashi cikin tsoro a tunaninta ko shine ,tun tana sa ran ganinsa a ranan  har bàcci ya kwasheta  batasani ba sai washegari , haka Nan ma taita zuba Ido cikin fargaba Amma Shiru ba abunda yafaru har yau datakai kwana Biyar a gidan bataga young master ba kamar yadda taji maids din gidan nafada , da haka tasaki jikinta Amma tasan definitely dole su hadu wataran tunda zamansa take .


Tayi zurfi cikin tunani; all of a sudden taga everyone started running , da sauri ta tashi daga jikin windon gabanta na faduwa Anya kuwa lafiya ? Mai yasa taga kowa na gudu , shi Kansa garderner da gudu yakwasa she wondered if they hard been attacked , da sauri ta matsa daga gun, dressing mirror Dake wajen ta hau turawa da kyar tana hada gumi tasashi jikin kofar , dukda a rufe kofar take hankalinta Bai kwanta ba .

Dawowa tai wajen windon da sauri  then she found out that no one was there , ko kare Babu a wajen ,Karan tahowar motoci taji,  Kara lekawa tai yadda Zata Iya Gani sosai and she show a train of cars suna shigowa cikin mansion din a jera wato convey with high speed, bazata iya kawo sunayan irin motocin datake Gani ba Amma daga ganinsu zakasan they're all expensive cars , they are five in numbers all black, Koda shigowarsu Cikin mansion din  suka rage gudun dasuke Kafin su tsaya a  main entrance din shiga gidan , a tare the doors of the four cars open wasu Murda Murdan body guards ne  suka fito Tareda  tunkarar  gudan motar dake gabansu Wadda baa Bude ba da Sauri.

jadeeda ta tsaida idonta don ganin wanan Wani hamshakin ne Yazo da kowa yake guda haka , bata gama wanan tunaninta ba taga fitowarsa daga Cikin motar , da Sauri ta matsa baya tareda dafe kirjinta saboda bugawan dayake non stop , The Young master tafada bakinta na bari,  nan tashiga karanto duk aduar datazo Bakinta jikinta ko Ina na rawa don tasan haduwarsu ba alkairi bane .


Magana yakema  bodyguards dinsa suka daga Kai a tare Alama amsawa Yana kokarin juyowa direction din datake tai Maza tasaki curtains din gudun ma karya ganta . kamar ko yasan da mutum a wajen ya tsaida idonsa kam batareda ya dauke ba , he thought he sees something sai Kuma Karan wayarsa ya dauke Masa hankali  ya juya tareda daukan  wayar .


Zama tai kan gadon Ta zuba uban tagumi tarasa Mai yake màta Dadi dukda a tsorace take dashi  why does she always have this feeling nacewa abunda  ke zuciyarshi bashine a ransaba, yànzu dai jibishi lokacin dayake ma guard dinsa magana ba Wanan hargagin , he looks normal daga nesa ba Wanan dark eyes  din , the terror in them duk baka hangosu , he looks Charming and breathtaking Amma fa daga nesa Amma idan ya matso kusa you would see the monster who he was .


 Koda ya gama wayar sake juyowa yay trying to figure out something jikinshi nabashi kamar someone is watching him and then he found the curtains . 


Wucewa yay cikin mansion din Yayinda suke take masa Baya . maaikatansa sai kwasar  gaisuwa suke , Amma  haka ya wuce batareda ya Amsawa kowanan su ba dama sun Saba da wanan halin nasa  .


Haka ta zauna jiki a sanyaye , tana fargaban what will happen next tunda wanan demon din ya dawo .

Bata Wani Dade da fitowa daga wanka ba tana cikin shafa mai , saiga wanan maid din dake zuwa kiranta cin abinci rose tashigo  idan kin  Kamala  food is ready tafada tana jiran fitowarta , Kai kawai ta daga mata ta dauki  doguwar rigarta kawai ta zumbula tareda daura mayafin abaya a kanta suka fito tare.

 Ba Wani mai yawa abincin taci ba , saboda yadda takejinta , jiki a sanyaye  tamike don tunda taga Taga young master Dinnan takejinta Wani iri .


Kodata koma dakin ma brush kawai tai tareda chanza rigar jikinta ta haukan gadon ta Kwanta tana tunanin abunda zai sameta .


Afra ce tafado mata a Rai Allah sarki ko Mai take yànzu tafada tana share hawayen daya  zubo mata , she hasn't spoke to her sister tun ranan da aka sata darkroom wayanan mutanen sun kwace wayarta gashi ko ganinsu Bata Kuma yi ba , don haka batasan Taya zata Sami wayarta ba , bare takira wayar hajia  taji ya afra takare da ragowar mutane Dake bin mahaifinsu kudi kosun wanye lafiya , tana Nan kwance har bàcci ya dauketa batareda tasani ba .


Ko minti talatin bataiba taji ana unlocking kofar , da sauri ta mike zaune tana murza idanuwanta tareda kallon Kofar cikin fargaba .

Baccin Dake idonta tuni ya washe ganin madam a gabanta su uku kamar dai lokacin dasuka fara zuwa , Dama tataba Jin wasu maid dasuka zo wucewa ta windon dakin datake suna Gulman Madam akan itace wacca boss ya yadda da ita a gidan ba mutuncine da ita ba taji suna fada don haka ba abun mamaki bane idan aka ce she's as wicked as her boss zata yadda .


 Tana zuwa hannunta ta kama tahau janta kamar wata kayan wanki Saida suka je kofar toilet taja ta tsaya , da kallo ta bisu , heart dinta na beating very fast sai lokacin hankalinta yakai kan Daya daga cikinsu Dake rike da Wani basket dauke da kayan sawa , gaban tane yashiga bugawa da sauri da sauri kamar zuciyarta zata Faso kirjinta ta fito haka takeji , she need no explanation kan  abunda take zargi, idan ko hakane tashiga uku yazatayi .


" Go take your " tafada not caring to explain why they came .


Jadeeda da bakinta ke bari amma takasa magana ta Kalli madam muryarta na shaking tace .


I....I just took my  Bath she tried to explain to her looking very scared .


Am sure you don't want me to repeat myself cewar madam tana hade girarta , da sauri tai  kasa da kanta tareda shigewa cikin toilet din da kallon tausayi ragowar suka bita dashi gata yarinya da ita kyakkyawa komai yahadata da young master basu sani ba, don shi mutum ne da baida Imani ko kadan . 


Wanan Karan da kanta tai komai Amma madam na tsaye a kanta tana nuna Mata abubuwan da zatayi amfani dasu dasuke kan varnity table duk Saida tasata  amfani dasu , Daya daga cikinsu madam tasa tashafa mata wasu mayuka a gashinta masu balain kamshi aka busar mata dashi suka sakeshi haka .


Dan light makeup sukai mata a fuskarta Wanda ya dada fidda kyawunta , kayan madam ta karba tareda Mika mata su .


" Put those on  and follow me" 


 tafada tana juyawa , kayan tabi da kallo wasu shegun night wears ne , very transparent pure white sai tasamanta dazata daura akai ta Dade a tsaye a Wajen tana tunanin Saka wayannan kayan tunawa da cewa fa shidin ba mijinta bane akan Wani dalili zatasama wani Kato kayan dazai bayyana jikinta sai kace matarsa .... Jin motsin madam batasan lokacin data zura rigar ba Jin tana kokarin shigowa tafito da sauri har suna kusan yin gware .


 Binta tai da kallo tun daga sama har kasa sai wani rurrufe jikinta take  coz she's not comfortable with it.


Perfect " let's get going we are running out of time tafada tana juyawa bin bayanta tai tana share hawayen takaici .


Haka tabi bayan madam suka fito daga wanan bangaren wata hanya daban suka bi , tunda Suka doshi wajen Wani sanyi sanyi da kamshin furani ke  tashi a wajen saboda  gardern din Dake wajen wanda aka kawatashi. sosai wajen ya dauki hankalinta haka tazama kamar wata Yar kauye ko Ina fitulune ke Bada Wani walwal ta bagan swimming poll dinshi wajen ya mugun daukan hankalinta sosai har batasan Lokacin data tsaya tana kallo ba , Jin alamun ba tafiyar Mutum a bayanta yasata juyowa Taga Maiya tsaidata . hangota tai nesa da ita tana kallo , Wani haushine ya kama madam batasan lokacin data daka mata Wani tsawa ba ganin Zata bata mata lokaci , da saurita takaraso inda madam ke tsaye rike da kugu tana hura hanci kokinsan young master Yana chan Yana jiran mu kika tsaya salon ki bata masa lokaci? Am...so....kanta karasa madam ta damki hannunta da karfi Saida tasaki Kara hhhh,  tashiga Janta da karfi cikin mugunta Dama gatanan shirgegiya da ita gudu gudu sauri sauri haka jadeeda ta rinka binta har tana tuntube Amma hakan baisa taji tausayinta ba yayinda rigarta  samanta  ke flying tana Jan kasa kamar wacce take fadowa daga sama Basu tsaya ko Ina ba sai part din young master.

    Wow wajen Nan ba karamin haduwa yay ba , everything is looking so natural the , decorations, furnitures settings komai da komai looks different from the second floor , the third floor was monochrome  _ black and white they were black paintings everywhere , wajen shiru kamar ba Wanda yake rayuwa a ciki , har eco na footsteps dinsu  sukeji , suddenly taga madam taja burki ta tsaya gaban Wata katuwar kofa da Akai mata ado da golden colour .

Itadai jadeeda Binta Kawai take da Kallo.


A hankali tashiga knocking Saida tai Hakan kusan sau hudu kan a Amsa masu daga ciki 


"Come in" 

 Bàzàta taba manta wanan muryar ba it's impossible to scrape the sound from her memory , tura kofa madam tai tana shigewa gaba , yayin da jadeeda ke biye da ita hankalinta a tashe.


As expected, dakin Shima anyi Masa paint black and white da zanunnuka daban daban jikin wall din , black curtains , mini falo in the room ,yayinda a tsakiyar dakin akwai king size bed , duk Wanan kallon acikin Yan muntina kalilan taisu .


Idanuwanta ne suka fada kan young master dake zaune kan couch beside  the east , he's eyes were glued at hers as he inhale his cigar Yana zuba tokar cikin ash tray din Dake gabansa. Ga Kuma wasu additional five pack of the cigarettes dako  tabasu ba aiba gabansa  .


"She's here " young master:

 madam tafada fuskar nan a hade ba wasa a tattare da ita , akwai bambamci yànzu da lokacin datake yima maids dinsu magana , anan shi looks calm with respect .


Har Lokacin baice mata komai ba illar buga cigar dinshi da yayi jikin ash tray din yadda tokan zai zuba ciki , he didn't say a word , Dan durkusa masa Madam tai kafin tajuya tafice daga dakin ya rage daga ita saishi su kaddai suka rage .


Remote ya dauka tareda danna bottons din Nan kofar tashiga rufewa da kanta .

Bam karar rufuwar kofar ne Yasa jadeeda juyawa a tsorace itadai harga Allah tsoran mutumin Nan take , ji take Kamar ta zura a guje tabi bayan madam Kamar yadda suka zo, Amma ba Hali yarufe kofar.


Tanajin yadda gumi ke tsasstsafo mata a goshi tundaga kanta har kafarta , tunda Suka shigo baiyi magana ba , hakama bayan fitar madam illar Wani Karan cigar daya sake dauka dake   gabansa ya kunnata yashiga busawa Yana busar hayakin ta Baki ta hanci cikin kwarewa  .


Dago Kansa yay Yana Kallonta she looks terrified daga ganinta dama,  who wasn't scared of him .


Shiru bakajin Komai sai sanyin acn Dake tashi har Kuma Lokacin Bai cemata uffan ba , his dark eyes kept keen on her  body , kamar Wanda ya sami Tsuntsu zai kashe.

Wutan Dake dakin Mai haske ce don haka tana iya ganinsa Sosai , he looks tremendous angry da alama yana neman Wanda zai huce haushinsa Akai .


Finally he speaks, 


"come !! " 


his voice was so close yafada Yana cigaba da Shan abarsa kamar ma bashi yay magana ba .


Da kamar  bazata jeba Sai Kuma ta daga kafafuwunta ta karasa inda yake a hankali ta tsaya dagà nesa batareda ta karasa ba tana Jin  zuciyarta kamar zata buga saboda tsoro ,

Hannayanta duka biyun rikeda gefe da gefen rigarta ta rike gam  gudun kar ya Fadi , Saida ya kalleta nawasu yan mintuna kan yace .


"Take off your clothes"

No comments