Breaking News

Kaddararmu 31-32

 KADDARARMU

              ( OUR DESTINY)


                     31_32



                          ✍️

Kuka take muryarta har Wani  vibrating take  a cikin dakin yayinda  hawaye ke  zubow dàga idanta kamar an kwance fampo , gabadaya fuskarta ta damalmale da hawaye da magina   hankalinta a matukar tashe 


Duk laifinta ne , it's all her fault datasan Haka ne zai faru da Bata fita ba at first place , amma mahmud bai da laifi  he only called her ,  itace  duk ta jawo masa  shiga cikin wannan lamarin , kuma yanzu Gashinan  youngmaster Yana Bada umurnin a kamoshi , Banda uban bugun da sukai masa acan restaurant din  ,yànzu Kuma batasan Mai zasuyi masa ba . don haka bazata taba bari hakan yafaru ba.


Kalloñta Kawai yake without uttering a single word , wato dukda laifin datai masa har tana da Baki da Kuma  kwarin guiwar ya kyale saurayinta she's trying to  save him   .


Youngmaster thought to himself yana Kallonta ,  this is unbelievable , Wato 

tsananin son da take yiwa mutumin shi yasa take ganin Kamar zata Iya  komai domin ceto rayuwarsa ko?

Ok fine ! let's see yafada Yana Sakin Wani smirk akan fuskarsa .


" Take her to the basement " !  lock her up  and make sure bata ga haske ba , har sai nace kuyi hakan , yafada  Yana Bada umarni cikin  commanding tone  .


jadeeda najin haka  tashiga girgiza masa kai da sauri ,da  sauri trying to speak tareda mikewa tana yowa Inda yake ta gurfana a gabansa tareda hade hannayanta Biyu pleading for mercy.


No! no! please don't hurt him , Ina rokonka don Allah kar ka cutar da shi please young master he's sick , baida laifi  ba laifinsa bane , it's all my fault, ni yakamata Kai purnishing  bashi ba ,   Tafada shouting on top of her voice tana kuka kamar ranta zai fita .


Wani haushine yakuma turnike youngmaster baisan Lokacin Daya dakama guards Dinsa tsawa ba 


" Take her Out ! What are you waiting for?  Tafada Yana binsu da mugun Kallon Ganin sun tsaya cirko cirko  Suna kalloñta . 


Aikuwa kamar Jira suke suka yo kanta .


jadeeda kuwa najin haka ta dago tareda fara masa magiya  cikin kuka  screaming on top of her voice dukdà she's afraid of the darkroom dakin da aka fara kaita farkon zuwanta gidan bai daga mata hankali ba kamar kamo masa mahmud dayace suyi , idan har aka kawo shi batasan iya abunda zasuyi masa ba tunda zuciyarsu ba Imani ko kadan , Dan haka bazata bari Hakan yafaru ba , she would beg for mercy on his behalf dukdà youngmaster ba yafiya a rayuwarsa still she won't give up .


Dan haka da Sauri ta yunkura tareda karasawa gabansa tazube a gabansa kamar maineman gafara ko wacca ta gurfana a gaban sarki leaving an inch between them  tashiga  rokonsa kamar wani basarake .

 Don Allah youngmaster kaimin Rai  ina rokonka kada ka cutar da Mahmud baida  laifi , tafada tana fashewa da Kuka , ganin guards dinsa sun nufo inda take , ihu tasa lokacin da  suka Kai hannu da nufin dauketa  daga kasan dakeba , batasan lokacin data tashi da sauri ba tafada kansa tareda kamkameshi kamar zatashige Jikinsa tashiga Kuka , ko Ina a jikinta yana rawa cirko cirko sukai batareda sun karaso inda take ba suka tsaya suna kalloñta ,

please young master Kaimin duk abunda zakaimin but spare Mahmud tafada in between tears , tana Kuka yayinda kanta Ke kwance kan kirjinsa .


Wani Irin shock yakeji ajikinsa tun daga kansa yakejin Wani Abu na tafiya a jikinsa har kafansa , he hate what he's feeling da sauri ya hankada tai baya kamar zata Fadi  , Allah yaso da kujera a Wajen tai maintaining balance dinta  .


Ya daura idansa akan yaran nasa tareda daka masu tsawan datafi ta dazu .

" What the hell are you waiting for?


Hakanne yasasu riketa yayinda suka shiga janta tana kuka tana rok'onsa   karsu cutar da Mahmud , duk Wanan abunda take ko ajikinsa har lokacin ji yake kamar zuciyarsa zata raba kirjinsa tafito , saboda yadda take  tsananin tafasar dayake yayinda yake binta da kalloñ,  suna janta har ihun nata ya bace yay disappear into a distance  .


" Shit yafada Yana kaima table din duka  da hannunsa , dole ne ta kasance a kulle har zuwa lokacin dazai nemeta  

He didn't care about her ,  ko abunda  takeyi da rayuwarta , amma yanzu da take tare dashi  she must behave herself , dolene ta rabu da koma waye .

 

Koda sukaje basement din , jefata sukai  cikin duhun tareda bugo  kofar suka rufe ,  nan ta mik'e da sauri ta nufi k'ofar da gudu tana bugawa  da k'arfinta kamar zata ballah kofar ,


Get me out ! get me out of here please someone should help me ! tafada tana kururuwa ,amma sai  takun kafarsu dataji daga nesa alamun sunyi  nisa kuma Hakan ya tabbatar mata da sunyi tafiyarsu .


  she slumped to the floor crying .


yanzu yazatayi gashi yasa an kulleta a basement Kuma the place was so dark and no one to run for help , tafada tana hade kanta da gwiwa yayinda ta fashe da matsanancin kuka , what is he going to do to Mahmud , kill them ?


The thought of killing Mahmud pressed her chest da sauri ta dafe kirjinta tana Karanto duk aduar datazo Bakinta , saida tadan Sami nutsuwar bugawar da zuciyarta take ta mike da sauri tunawa da wayarta afrace kawaii zata iya taimaka mata ta shafa kofar tana jijjigata tareda kira ko Allah zaisa wani yaizo ta wajen koda bazasu Iya fitar da itaba subata Aron wayarsu  takira afra  , tace mata ta kira Mahmud and tell him to run for his life Saboda yaran young master are after him .


please youngmaster kill me instead I beg you tafada tana bubbuga kofar tare ihun wani ya taimaka mata , Amma abun haushin ihunta  banza dan bakowa Ake bari yazo wajen ba .


haka taitayi harta gaji Dan Kanta tareda zamewa kasa nan jikin kofar tana kuka .


Lokacin daya tashi daga kasan already guards din youngmaster sun tafi harda jadeeda , da sauri yafito da hanky dinsa  yana tare jinin dake zuba daga hancinsa dukda he dogded some of their blows Amma Saida yasami wasu minor bruises a jikinsa da fuskarsa , sai Lokacin mutanan Dake wajen suka kawo masa dauki yayinda wasu ke kallonsa cikin tausayawa .


Restaurant managern dinner yabashi first aid treatment kafin yabaro wajen , Koda yashiga motarsa Saida ya Kalli fuskarsa tajikin mirror lokaci guda harta tasa tayi suntum da ita , jikinshine yabashi tunda yashiga track din Marwan har yasa Akai masa haka Yasan he's coming for him very  soon .Dan haka he's leaving the city tunkan abun yazama worst .


Daga nan gida ya wuce Dama Kuma iyayensa sunsan da turashi Jos da Akai masa , da sauri yashige dakinsa Dan kar umminsa tagansa   ta tuhumaishi game da ciwon dake jikinsa saidai ya makaro dan Yana sa kafarsa cikin falon , bai kulla da ita dake zaune a faloñ ba , cikin sauri ya wuce dakinsa .


 kokàrin cire T shirt dinsa yake daya bace da jini aka turo kofar dakin or my God yafada yana rintse idonsa shikenan he's Doom ummi tashigo zata fara masa tambayoyi shikuma bayason tasan maike faruwa don hankalinta ba Karamin tashi zai ba .

  Maimakon yacire rigar kamar yadda yay Niya saiya maidata tareda wucewa straight inda kayansa suke duk Dan ummi ta dauka his busy ta fita daga dakin .


   Ummi Ashe kece yafada yana daukan travelling bag dinsa yahau zuba kaya a ciki.

  Eh ! nice da ka Dauka wah , tafada tana zama kan katifarsa , yanaga kanata diban kaya badai Tafiyar bace tataso ba ? , na dauka sai jibin kace zaka tafi .

Eh da jibi nai niyar tafiya ummi saidai an kiramu ana bukatar mu a wajen da gaggawa shiyasa  nai deciding natafi yau dinnan , yafada yana zuba  takalmansa ciki jakar , to ai shikenan Allah ya taimaka tafada tana mikewa wani irin dadine ne yakamashi Ganin zata Fita dagà dakin .

Saidai tana tashi wayarsa dake kusa daita   tafara ringing , harzata tashi saikuma ta dauka tana mika masa ganin his busy Kuma tana kusa da ita, ungo Kai wayarka ana kiranka tafada tana Mika masa .


  Kasa juyowa yay ya  karbi wayar. ungo  mana ? tasake fada  tana Mika masa wayar  hannunsa ya Miko Mata ta baya batareda yajuyo ba wai tabashi , tsayawa tai tana Kallonsa , cikin mamaki  Kai lafiyar ka kalau kuwa mai haka kakeyi tafada tana kallonsa batareda Tamika masa wayar ba , har Kiran yakatse , kajuyo ka karba mana ka tsaya kana  mikon hannu kamar wata saarka .


 Ganin ummi zatai masa wata fassaran daban yasashi juyowa a hankali jikinsa a sanyaye kansa na kallon kasa .....

Wayar Dake hannuntace  ta  subuce tafadi batareda tasani ba tahau sallati tana tafa hannu , Mai yasami fuskarka haka Mahmud tafada tana matsowa gabansa tareda shafa fuskar data kumbura tsabar naushin dayasha .

 Hatsari kaiyi ko meh ? ta Kuma jefo masa wata tambayar tana dudduba jikinsa .

   Dan Allah ummi ki kwantar da hankalinki ba Wani Abu bane serious it's just a minor accident yafada yana Juyawa Dan cire rigarsa tunda ta Gani theirs no need to hide anymore , yafada tareda fadawa cikin toilet Dan taking shower .


Nan da Nan sai gashi yafito still samun ummi yay a inda ya barta .

   Saida ya kammala shiryawa yakarasa kusa da ita tareda dafata don she's lost in thought, Dan firgigit tai tareda dawowa cikin nutsuwarta takalleshi , Dan Allah ummi ki kwantar da hankalinki ki min adua kawaii  shinafi bukata , time is running idan nakarasa I will give you a call zan kira Abba ma ko a hanya ne muyi sallama yafada Yana Bata side hug .


 Shikenan Mahmud Allah yakiyaye yakuma kareka Saidai naso ace kabari ko zuwa gobe ne katafi , saboda jikinka gara kaje asibiti a dubaka ....


Karki damu I will be ok , saimunyi waya kawai  yafada Yana Saba jakarsa, saboda sauri yake yafita Dan yasan ba karamin aikin Marwan muhd salis bane yasa a biyoshi har gida ba ,  ya fice daga dakin 

ba tare da ya jira amsar da ummi zata bashi ba ya fice daga gidan yashiga motarsa ​​bayan yasa kayansa a booth .


Yana shiga motar zai tayar kenan  saiga wata  bakar helux guda biyu suna shigowa  harabar gidan , with high speed , 

Shit yafada Yana kokàrin Fitowa daga motar  Amma Ina  wasu guards su uku suka fito daga Cikin motar tareda  nufowa inda yake  suka cimmasa  tareda fitowa dashi   daga cikin motarsa suka  tasa keyarsa zuwa tasu  motar , suka shiga , sanan suka  ja motar suka fice daga gidan.


Daure mahmud sukai  jikin kujera da isarsu gidan , hakama  idanuwansa Suma a  daure da guntun kyalle ,  bai San inda  suka kawo shi ba saidai yaji takun tafiya  da alamun ana nufowa  dakin .


kwatsam yaji an bude kofar aka shigo , yayinda yakejin takun na matsowa inda yake  inda mutumin ya tsaya Chak  a gabansa .


Mutumin bai ce masa  komai ba , hakama mutanen da ke cikin dakin, Mahmud zuciyarsa sai bugawa  take da karfi kamar  kirjinsa, zai fito , yayinda  kayan jikinsa ya jike da gumi  cike da  tsoro a ransa.


Youngmaster ba mutum ne mai tausayi ba , Kuma  ko kadan ba Imani a ransa Koda yay wanan tunanin a daidai lokacin aka cire masa kyalen da aka rufe masa Ido dashi Yana kokarin Bude idonsa yaji Wani hard blow a fuskarsa Wanda ya hade da jaws dinsa sending his face flying to the other side , Wani metallic taste yaji a lips dinsa and he knows that his jaws were broken .


Hannu youngmaster ya dagà masu Dan dakatar dasu dagà Kai masa Wani bugun Yana Kallonsa trying to ease the pressure on them saboda punch din dasuke masa .


" Kabani dalilinka daya nacewa why I shouldn't pop your head with this gun , yafada Yana Kallon bindigar dake hannunsa batareda ya Kalli direction din da Mahmud yake ba.


Mahmud Dake zaune har lokacin Bai dawo Daidai ba ya girgiza kansa Yana Kallon  jini daKe zuba dagà bakinsa yafadi kasa Tareda kujerar dasukai daureshi  Akai  .


Lokacin dayaji wanan word din daga Bakin attacker dinsa da sauri ya Bude idonsa tareda Kallon Wanda ke gabansa  , what ? Ma..r..wan yafada Yana Kallonsa  he recognize the man the demon  in flesh.


Yana  tsaye a gabansa rike da wata Yar karamar pistol a hannunsa kafin yay wani tunani sai Gani yay youngmaster yayi pointing dinsa da gun din .


Your time start now , you have only one chance Ka gayamin one valid reason that I shouldn't pop you skull ! yafada yayinda muryarsa ta karade dakin Yana aiming gun din akan Mahmud da heart dinsa ke beating fast fast as if to pomp out of his chest , yasan he need to think fast, coz this guy is crazy he can do anything stupid at this point with the gun pointing his head  , he has no option Yana son jadeeda sosai Amma Lokaci yayi dazai rabu da ita to save his life .


Bakinsa ya Bude Dake da jini yafara magana Yana karkarwa , because I ...I will leave her and go far away dagà garin Nan , will disappear and never return , zan tabbatar bazamu Kara haduwa ba , I will never ever contact her till my last breath , Dan haka spare my life don't kill me please yafada Yana shivering.

Finally Mahmud speak up yana rintse Idanuwansa yana  fatan wanan maganar daya fada is a valid reason not to be killed . Dan maganar gaskiya yasan da kyarne jadeeda ta dawo masa tunda tana Tareda Marwan he wish her the best in life Amma tabbass bazai iya hada kansa dashi ba .

 musamman yanzu Daya tabbatar da hatsabibancinsa ya wuce Inda yake tsammani , ya tabbata Idan har Bai rabu da itaba zai janyoma kansa da iyayensa balain da bamai fiddasu.


Dakin yay shiru for a moment yayinda har lokacin youngmaster na rike da gun din a hannunsa Daya saita kan Mahmud dashi , Idanuwansa sunyi jah dasu kamàr an zuba barkonu , sai guards dinsa Dake gefe suna Kallonsa tareda jiran command din boss din nasu , after few more second they heard a loud bang .


Youngmaster ne yasaki bullet din , take tsuntsayen Dake kan bishiya Suka tashi sama sun tsorata ,

Mahmud kuwa Dake daure rintse idonsa yay yana Jin kamàr ransa na barin gangar jikinsa yayinda yaki Bude idansa , waiting to die , Amma Kuma baiji Wani pain ba .


 He waited for few seconds kafin ya gwada Bude idonsa da sauri ya karasa Bude idonsa Yana Kallon youngmaster Dake maida gun din cikin case dinta .


Hakanne ya tabbatar masa Bai mutu ba da Ransa .

Sai Kuma ya sake juyawa as if looking for something Nan yaga bullet din jikin Bango inda ya fasa Bangon wato da kadan ya wuce kasan .


"He shot the wall! 

" I hope you stick to your words  if you ever come to her ,or if she sees your face I will wipe your whole family.


Kasa magana yay illah nodding Kansa Kurum dayay .


" Take him away ! Yafada Yana Bada command , da sauri Suka Daukeshi kamar Wani yaro suka fita dashi dagà dakin .


Immediately da fitarsu he fell to the chair .

" Me yasa har yànzu yake Jin ransa ba Dadi ne ? Why?

A hankali yake recalling abunda ya faru a wanan Ranan Koda ya tuno da wanan video da yake nuna Mahmud rumgume da jadeeda sai yaji ransa na masa daci .


But why is he angry with that , bama ta tunanin familynsa su ganta ba yake meh damuwarsa da wanan Mutumin daya ganta dashi , he dont care da irin rayuwar dazatai ko takeyi , Amma dolentane ta ajiyesu a gefe kafin rabuwarsu.


Tashi yay da sauri Jin yadda yake hada gumi ya sassauta daurin necktie dinsa tareda tashi tsaye daga kujerar dayake zaune ya shige daki , can saigashi da pack din cigar Nan yazubesu  a wajen Yana daukan Daya bayan Daya Yana busawar , da haka da haka yafarajin zuciyarsa tana sanyi .

No comments