Breaking News

Kaddararmu 3-4


 KADDARATA

      (OUR DESTINY)


                   3 _4


                      ✍️


Why !!! Jadeeda Why ? Afra tafada tana kuka ,hannu kawai Jadeeda  ta iya daga màta saboda  kukan dake cinta tana kokarin  rikeshi , batasan breaking a gabanta . 


Batareda ta kalleta ba, tace  Karki damu I will take care of myself okay ,ya Isa haka I will be alright, but promise me bazaki kuka ba  idan kika komai gida ba uhum yafada tana kallonta .

Girgiza kanta tai alamun bazatai màta Alkawari ba , Hakan na nufin saita yi kukan .

Tayaya kike tunanin hankalin zai kwanta bayan nasan kina Nan tareda this  monster Dakeda stood heart and you expect me to relax no that's impossible, tafada tana Dan turo bakinta tareda hade rai tana juyar da fuskarta daya barin   tareda  goge hawayen Dake zubo màta .


 Hakan datayi shi yasa jadeeda sakin  dan murmurshi tareda Komawa ta gabanta Daman tasan ma Bata bakinta take,  tayaya ma zaai Tayi tunanin afra zata  iya zama Kwana da kwanaki batareda ta gantaba  har Kuma hankalinta iya kwanciya tasan  Hakan ma Bazai taba yuwuwa ba ,A hankali ta dafata tana kallonta Sam taki bari su Hada Ido da ita , saboda fushin datake da ita am really sorry afra am going to miss ta whispering mata  , maimakon tabata Amsa kawai tafada jikinta tana Kuka , bubbuga bayanta tashiga yi , it's okay ya Isa haka kinji, gyada màta kanta kawai ta Kuma yi , don takasa magana Saboda da Kuka , kokarin   sake rumgumeta take taji an fizgota daga jikinta  Daya daga Cikin Yaransane yay hanyar kofa da ita , nan tashiga ihu tana kiran sunan jadeeda  tana kuka leave me alone tafada tana Kai masa duka tako Ina Amma kamar dutse , haka yajata tareda daurata kan kafadarsa yay waje da ita tana Kiran sunan jadeeda data tsaya Nan kamar status  tana kallonsu .Amma haka marasa imanin Nan yay  waje da ita   .


   jadeeda datai tsaye kamar wata status  takasa Gaba bare Baya tana kallonsu har Suka bace ma ganinta sanan ta juyo a hankali idanuwanta cikeda kwallah tana kallonsa , kan tai kasa da kanta tana sharar Hawaye na tausayin kanta da Yar uwarta .


Jin an rufe kofar yasata juyowa da sauri Kuma  Kallonsa Yana Nan a zaune hankalinsu a kwance kamar ma ba abunda yafaru illar seggeratte dinsa daya kunna , kallonsa take kamar  taga wata sabuwar halitta , su biyu ne kawai ita dashi , wani yawun takaici ta hadiye tareda danne kukan dake Shirin zuwan mata Wanda tun dazu take danneshi, har Kuma Lokacin Bata Daina Jin ihun afra Dake màta kuwa aka ba.


  tana Nan tsaye taji ansake Bude kofar, wanan Karan  ko gezo batai ba don haka Bata juyaba , she's ready for the worst , yadda take Jin zuciyarta a yanzu  ta kekashe dazaa Bata bindiga  ba abunda zai hanata harbe Wanan mutumin Dake gabanta saboda tsanar datake masa , tana Jin lokacin da wasu kartan mutanen suka sake shigowa , inda yake suka nufa cikin girmamawa , Batasan dai Mai yace masu ba tagadai sun nufota gadan gadan da sauri ta shiga matsawa da baya da baya tana kallonsu ganin Daya na kawo hannu zai tabata. 


"Don't touch me! ta fada tana daka masa tsawa ita kanta tai mamakin dakiyarta .

 

"Miss boss yace mutafi Dake gida  yafada Yana nuna mata hanyar kofa , ba yadda ta iya haka tana ji tana Gani  tabi bayansu ,Koda tazo fita Saida ta Kuma Kallon inda yake Yana Nan inda ta barshi Amma kallo wanan  bata isheshi ba .

    

Koda suka fito premises din wajen kowa harkar gabansa yake ba Wanda ya  takansu , mota suka shiga  Suka fita daga maaikatar .


Saida sukai tafiya Mai Nisa kan su karaso wata unguwa Mai masifar kyau ko Ina shiru kamar ba mutane , sai yan tsirarrun dake wucewa jefi jefi daga Gani ma GRA ce, Wani tangamemen gate suka nufa , horn Daya  aka Bude masu, sukasa kan motarsu  ciki.

  Wani sojane sanye da uniform ya Bude masu gate din .

 Tsayawa fadar tsaruwar gidan ma Bata lokaci ne gidane ya Hadu kamar bazaa mutu ba ,irin gidagen Nan ne da Ake nunasu a fina fina amerika sukai parking , Daya daga cikin Yaransa ne ya Bude mata kofar ta fito tana karema gidan kallo .

 

 "Get going taji muryar daya daga cikinsu hakanne yasata dawowa cikin hayyacinta ,tashiga bin bayansu batai masu gaddama ba Dan ta kulla Suma ba imanine dasuba kamar boss dinsu .  A gaban wani daki suka Tsaya , keys suka fito dashi itadai  kallonsu Kawai take da mamakin Nan inane suka kawota  before she could say a word sai Ji tai sun hankadata  cikin dakin kafin ta mike  suka sa keys da sauri suka rufe dakin , da sauri ta tashi hankalinta a tashe ta nufi kofar tana jijjigata tsoro fal cikin zuciyarta , the room was so dark da baka Iya ganin abunda ke gabanka  anan jikin kofar ta zauna tasa kuka tana bubbuga kofar su Bude mata Amma Ina sunyi tafiyarsu kamar yadda boss dinsu ya basu umurni .


  Hada Kai tai da gwiwarta tana kuka gwanin tausayi Wanan wacca irin rayuwace wanan inda mutum zai dauki mutum Dan uwansa yay treating dinsa kamar Dabba dan kawai yana takamarsa shi Mai kudi , shekarunta basufi ashirin da Biyu ba Amma shes going all true this miserable life , her dream , ambitious, joy ,hope everything has been shattered in the blink of an eye , Amma tasan all this is part of her Destiny .

 haka ta zauna awajen taita kuka ga zafi da dakin yake dashi daga jima  an jima baa amfani dashi tasan this is just the beginning of her Destiny.

koda ta gaji da kukan haka ta zauna  Nan tai shiru tareda zuba tagumi ba abunda take tunani sai Afra tasan yànzu haka tana can tana kuka , ba lallai yau ta iya cin abinci ba saboda sanin halin datake ciki , yau shine Rana ta farko dazata taba kwana Wani wajen batareda  Yaruwarta ba , A Nan kasan wajen ta kwanta tareda daura kanta kan hannunta tana share hawaye lokaci zuwa lokaci . ta kankame jikinta waje Daya saboda tsoro batasan duhu a rayuwarta ko kadan amma yau Wani mara Imani yanai mata azaba da duhu, dataji motsi saita firgita ta tashi zaune tana  waige waige dukda Bata iya ganin komai , a lokacin , da zaa gwada jininta , ta tabbata bakaramin Hawa zaiyi ba .


   A haka baccin wahala ya kwasheta awajen batareda saninta ba .

farkawa tai dakaran keys din dataji da sauri ta matsa dagà wajen tana mikewa tsaye don ganin Wanda zai shigo,  da sauri tàsà hañnunta saboda hasken daya haska Idanuwanta tajima a duhu ,  abinci aka turo mata kan asake rufe kofar kanta Karasa wajen akasa mukulli kamar wata prisoner.


kotakan Abincin batabi ba tashiga buga kofar da karfinta please let me out am scared of dark , Dan Allah ku budeni haka taita yi , Amma sukai biris da ita tana Jin footstep dinsu ,har Suka tafi suka barta Nan ,  Saida ta gaji Dan Kanta Ta zauna Nan kasa tana kuka.

  

haka ta yini tun safe Batasa komai a bakinta ba , tana nan yadda take tun safe , yunwa kuwa Kamar ta kasheta haka take ji , Dama lokacin dasuka fita kasuwa yima hajia rabi sayayya makociyarsu mutuniyar kirki dasuke zama wajenta tun bayan mutuwar babansu tana yin Abincin saidawa Bata taba haihuwa ba ,inda ta dauki  son duniya ta daura masu don ko lokacin da dangin mahaifinsu suka nemi tafiya dasu kauye ita taitai masu magiya harda kukanta tareda neman alfarman Subar mata su , su zauna a wajenta  har Lokacin da zasu kammala karatunsu inyaso sai su koma tunda sunyi nisa  , da kyar dai suka amince Amma da sharadin dasun kammala ko kwana Daya karsu Kara su dawo kauyen to a haka aka rabu .


  Suna cikin tafiya suka kulla da wata Mota baka Mai tint dake binsu a baya Nan suka Kara sauri suna Tafiya suna haiwayawa , Koda suka zo wata hanya daba mutane sosai suka kwasa a guje Amma sai mai motar yasha gabansu tareda cin birki hakanne yasasu tsayawa jikinsu yashiga rawa ganin Wani jibgegen mutum ya fito daga Cikin motar fuskar Nan tasa a hade ba Alamun rahma a tattare dashi ko kadan.

 Hannunsa yashiga nannadewa  kokarin magana jadeeda take dayan yafito Shima ta bangaren Mai zaman banza Hakan  da suka ganine ya daga masu hankali matuka . 


  Mai mukai maku ? Cewar jadeeda ganin Suna nufosu sukuma suna jada baya gashi ba hanyar guduwa hannunsu rike da juna,


"Get in the car !

 daya dagà cikinsu yafada yana daka masu tsawa , bazamu shiga ba saikun gaya mana inda zaku kaimu tafada cikin dakiya .

  murmurshi dayan yasaki Yana shafa gemunsa dayay masa die da kalan blue , Steve don't forget to blow off their head boss yace idan sukai mana taurin Kai hufff yay fito Yana nuna masa wuyansa , dariya ragowar sukasa dan haka Steve ya fiddo da pistol din Dake aljihun wandansa ta baya yay pointing dinsu dashi , aikuwa ba musu suka shige cikin motar suna kuka ganin bindiga muraran a gabansu .


       Cigaba 

kwanan ta biyu a dakin ba ci , Ba sha , haka Kuma kullum zaa a kawo mata abinci sau uku a Rana Amma ko tabasu batada alaman yi, sallah kawai ke tadata Shima da ruwan dasuke kawo mata , anan take alwalarta  datayi zata Koma inda take ta makure a wajen saukinta ma yanzu da haske ba kamar farkon zuwanta ba , ta tsine ma wanan mutumin yafi a kirga mutumin dako sunansa Bata taba sani ba , duk tabi tai laushi wanka kuwa baa maganarsa tun tana kuka har ta hakura ta zubawa sarautar Allah Ido.

     A bangaren afra kuwa har kofar gidansu suka kaita tana sauka suka taka motar da uban gudu suka bar wajen , akan Idon malam auwalu Abun yafaru da Sauri ya nufota nan yashiga jefo mata  tambayoyi Wanda ta kasa bashi Amsa illar kukan datake kamar zata shide , lafiya daga Ina take,  ina Yar uwarki suwaye suka saukeki. 


Ganin takasa magana Hakan yasashi janta cikin gidan Yana kwallawa hajia kira , Rabi ,Rabi kina Ina fito kiga iKon Allah ,ga afra ta dawo , da Sauri hajia tafito tana gyara zanenta Dake Shirin faduwa saboda tsabar rikicewa datai  malam tana Ina tafada tana rarraba idanuwa ...

batasan lokacin data dafe kirjinta ba ta kwalalo idanuwa,  Nan ta hau sallati tana tafa Hannu , afra daga Ina haka , Mai yasameki , tun dazu nake ta nemanku  , bakiga yadda hankalina ya tashiba ,Ina jadeeda kobata shigo bane ? Wai ya  kike kukane meyafaru tafada tana dafata ganin irin Kukan datake  , Nan tazauna dabas a kasa jikinta  sai  bari  yake takasa magana inbanda kukan Nan ba abunda take .

Ganin haka Yasa hajia daura hannu aka tareda rushewa da kuka , nashiga ukuna ni Rabi Ina Yar uwarki maiyasameta kibude Baki Dan Allah ki min bayani ko hankalina zai kwanta tafada tana share zufan dake tsattsafo mata a jiki .hakama malam auwalu Shima ya mugun tsurewa kaddai kashe Yarinyar Nan Akai Mai zasu cema danginsu yafada Yana zama Shima gefensu tareda cire hularsa yashiga firfita dashi 


Ganin hankalinsu ya tashi , afra tashiga Basu labarin abunda yafaru dasu bayan fitarsu zuwa kasuwa ai tunkan takarasa suke sallati suna sallallami barema hajia da hankalinta ya Tashi bakadan ba .

Gabadayansu suka zuba tagumi an rasa Wanda zaiyi magana a cikinsu hajia kuwa jitai cikinta na juyawa maizata cema iyayen yarinyar Nan da suka Bata Amana ko wata biyu cikakka baayiba ace Hakan tafaru , ai bashiri ta figi buta sai bayi saboda cikinta Dake juya Mata .

  A wanan ranan haka sukai ta rarashin afra saboda kukan datake abinci kuwa ko kallansa batai ba , lokacin da hajia ta tasata a gaba taci , ranan haka suka kwana cikin tashin hankali da zullumin yadda zasu bullowa alamarin .


Ganin tana neman halaka kanta yasata  mikewa da kyar ta janyo abinci da aka kawo mata tasamu ta cuccusa shi a bakinta batafi ci uku ba ,tabari don Ji take kamar zata amayo dashi .  haka ta hakura ta koma inda take ta Kuma kwanciya . 


Kwananta hudu a wanan dakin Wani yammaci taji ana Saka Dan mukulli ana kokàrin Bude kofar ko matsawa daga inda take Batai ba , don a tunanin ta masu kawo mata abincinne Amma ga mamakinta wasu mata tagani su uku Suna shigowa a hankali tashiga yunkurun tashi zaune , ta gabansu tadan manyanta Dan daga Gani zatayi irin shakaru hamsin din Nan sai Kuma na bayanta dabasu fi kamar irin talatin din Nan ba .

Babbar cikinsu ce ta tsaya tana kallonta na wasu yan mintuna kanta juya tana Kallon ragowar tai masu alama da hannu , Nan suka karaso gabanta jadeeda ta nuna masu , aikuwa suna zuwa suka dauketa kamar wata yarinya batare da sun barta ta taka da kafafuwanta ba ,Itama Kuma batai masu gardama ba saboda jikinta is very weak suka tsaida ita , Sanan suka fara Janta a hankali 

Zuwa Wani wajen daban , Basu tsaya ko Ina ba sai Wani daki, suna bude kofar suka wuce da ita toilet direct Wani kamshin strewberry ne yadaki hancinta dukda a halin datake ciki Saida ta lumshe idanuwanta Dan Allah yayita mai balain son kamshi .


" Strip ! Da farko Bata Gane Mai matar take nufi ba sai datace tube kayanki .


Aida sauri ta wartsake Jin Gane abunda  matar take nufi , sai lokacin ta Bude idanuwanta Ashe ruwa suka Tara mata cikin  jacuzzi ruwan kumfa Mai kamshin stewberry  Dake tashi a ciki.


Karki Bata mana lokaci kicire kayanki cewar wanan matar data Dan manyanta tasake maimaitawa  fuskarta ba Dariya ko kadan , Sanin cewa idan ma Bata cireba zasu cire Mata Dan Suma bataga alamun Imani  a tattare  dasu ba gara Kawai tayi abunda tace mata .


Saidai tunda take a rayuwarta Bata taba zama gaban wani Dan Adam tsirara ba Amma yau batada yadda zatai .

A hankali ta daga hannunta da nufin cire kayan wanan matan taima yaranta magana akan sucire mata tana Bata masu Lokaci , aikuwa suna zuwa suka yaje rigar gida biyu , 


Da sauri tasa Hannu tana kare jikinta , ita kanta kunyar kanta takeji bare Wani kwananta hudu ba wanka tanajin yadda take tsami bare su .

Daya dagà cikinsu ne ta dauko stool ta ajiye gaban jadeeda , sit tafada sai Kuma Daya Dake tsaye rikeda brush da paste.

No comments