Breaking News

Kaddararmu 27-28

 KADDARARMU

             (OUR DESTINY)


                  27 _ 28

               


                        ✍️


Tana kallo har madam ta bacewa ganinta ,ko juyowa batai ba ,  Kodata  juya  wajen maids din dake wajen da Sauri sukai kasa da kansu ganin takamasu Suna kallonta kafin ko wacce ta maida hankalinta kan aikin datake   .


Maida kanta tai kan Flask din dake hannunta tasan Bata da wani choice illar ta Kai masa da kanta tunda taima grandma alkawarin bashi , gashi yànzu kusan karfe goma tasan by now yatafi office , don haka ta juya cikin Sauri dan kaiwa dakinsa tunawa datai Idan taje bayanan Yana office wata zuciyar ta gaya mata haka .

 All she needed was to go upstairs ta Bude dakin ta ajiye masa ai ba tsoran empty room dinsa take ba  , was she , tafada in her inner though tana tambayar Kanta trying to give herself courage saboda nervousness datake Ji , da Sauri ta wuce towards the stairs , Koda tazo floor dinsa her heart begin to pound .


 A bakin kofar dakin ta tsaya tana kokarin kawar da tsoran dayake ranta .

" Common jadeeda ki Bude ki shiga , you can do it , it's just an empty room , ba wani Abu ba,  ki nutsu tafada wa kanta .


gumi kuwa sai tsitsifo mata yake a hannunta  datake 

 rike da flask din ,da Sauri ta goge hannun jikin silky gown dinta tàredà Kai hannunnata dake rawa kan handle din kofar dakin ,  wata zuciyar kece mata tashiga kawai bakowa , it's just an empty room, what are you afraid of .


  Tunda tasan baya Nan sai batai knocking ba , instead tana Bude kofar tafada ciki tareda rufewa a hankali .

tsaye take jikin kofar tana studying dakin for a moment Kafin ta saki tsaki ,

Mts ! na batawa kaina lokaci ma Ashe bayanan nake ta wani Jin tsoro tafada tana karasa shiga cikin Falon towards the fridge da madam tace mata ta daura akai .

Ba kowa a dakin Amma batasan may yasa har Lokacin akwai tsoro tattareda ita ba kawai shes trying to give herself courage .


A hankali ta daura flask din kan fridge din tana kokarin juyawa idanta ya fada kan wani cabinet Dake kusa da firdge din , hakan Nan  taji tanason ganin meh a ciki ,Dan cute dashi , Inda  wata zuciyar tace mata tabude kawai tunda bayanan  taga menene a ciki , aikuwa without second thought ta Bude ,  Kodata Bude she could not believe what she is seeing ,  over twenty packs of pills, da Kuma kusan ten boxes of cigarettes ko budesu ma baayi ba .


Kasa matsawa tai daga wajen , saboda shock din data shiga kawai tsaye tayi a wajen tana kallon abubuwan Dake ciki harta manta da abunda ya kawota dakin  ma.


"Was he sick ? kokuma he's mentally sick ?

she wondered mai ke damun  mutum kamar Wanan dazai rinka Shan pills haka , da Sauri tashiga rufe cabinet tunawa da Abunda ya kawota , kafin ta juyo tana maida numfashi as she was about to leave har ta kusan kaiwa kofa, sai Kuma ta tsaya , ganin wasu Abu jikin wall din falonsa , Dan haka saita fasa tafiya wajen kofar instead she walked towards the falo , there were pictures of people hanging on the wall , a hankali tashiga tafiya harta Karasa inda hotunan suke , 

   Young master ne a hoton tareda wata mata dasuke balain kama da ita she was smiling, kyakkyawa da ita , duk yadda Akai Wanan mahaifiyarsa ce , saboda kamanin Dake tsakanin su ,

  dayan picture din Kuma Wani Mutum ne in his late forties Yana tsaye Shima kuma murmurshi yake .


picture na uku kuma yarinyace kamar yar shekara biyar tana rike da yartsanarta tana dariya tareda wanan matar da youngmaster da Kuma namijin a hoton suna Dariya hakanne zai tabbatar Maka da Cewa familyn sane .


Amma Ina suke ? tambayan data farayi ma kanta Kenan , meh yasa jiya Bata gansu ba a family house dinsu ba  , Kuma ba Wanda ya  ambace su , ko sun mutu ne ? gabanta ne ya fadi datai wanan tunanin,  tana Kuma kallon hoton .


To ko don mutuwa sukai shiyasa yake acting haka , that made him change into a monster could that made him become so cold .


Tana Nan tsaye gaban hotunan trying to figure out answer to her questions Taji budewar kofa tareda footsteps alamun ana shigowa cikin dakin , immediately tajuya inda takeji Karan tafiyar and her eyes widened ji take uwa kasa ta bude tafada ciki , from no where taga youngmaster yafito daga wata kofa , Dake ita ba Sanan kan wajen taiba daure yake  da towel a waist dinsa yayinda ya daura dan karamin kan wuyansa as he stepped out of the bathroom, sumar kansa a jike , there was a tattoo on his left  chest Wanda idan ba sosai ka kalleshi ba , bazama kasan akwai shiba .duk jikinsa a murmurde kamar Wani dan wrestling saboda tsabar workout din dayake Akai akai Sam baisan da mutum a dakin ba , gashin kansa yake gogewa da towel din dake hannusa .

 Jadeeda kuwa datai Mutuwar tsaye ta zama uwa mutum mutumi tana tsaye  tana kare masa  kallo kamar taga sabuwar  halitta sai kifkifta idanuwa take kamar wata mara gaskiya , gabadaya ta jike sharkaf da gumi ta rasa ma abunda zatai .


Saida ya gama goge sumarsa tsaf yajuyo da nufin kwance towel din dan a tunaninsa shi kaddaine a dakin , Wani irin zaro idanta tai tàredà kwalla Kara tana rufe idonta da tafin Hannunta yayinda ko Ina a jikinta yashiga  rawa saboda tsabar tashin hankalin data shiga tunda uwarta ta haifeta Bata taba ganin tsiraicin wani Babba ba , Dan haka ta tsorata matuka .


Da Sauri ya Maida towel din jikinsa yana kallon direction din dayaji ihun , shi kansa yayi mamakin ganinta a wajen meya kawota , what the hell is she doing a dakinsa batasan ya tsani shisshigi ba .


"What the hell are you doing here ? 

yafada his voice deeping   with anger but trying to control himself.so yake yasan who gave her the guts to come into  his floor batareda saninsa ba , ko ta dauka Nan din playground ne na Yara irinta  for her to come duk lokacin datake so ?


jadeeda dake tsaye Banda jikinta da ke rawa  ba abunda take datasan Yana Nan da tun farko Bata zo ba , Koma mai zai faru saidai yafaru tafada tanaiwa madam Allah ya Isa don Duk laifinta ne da Hakan Bai faru ba .


yànzu ya zatayi , me zata ce masa, ta Yaya zatai masa bayanin cewa camomile tea dinsa ne da grandma tabata takawa masa ta manta jiya Bata bashiba shine yànzu ta kawo Masa shi Nan daki  bayan kuma idan ya tambayeta Inda ta ajiye ba guri daya bane da Nan din Inda take  tsaye , itadai yau Allah ne kadaine zai fitar da ita .

Tasan kawai mutuwarta ce tazo kusa tana Kuma aduar yazama a less painful death.


you...ng mas...ter I ...can explain tafada tana daga hannunta sama ganin irin kallon dayake binta dashi 

Baice mata Komai ba , illar kallonta dayake ganin haka Tayi tunanin ya Bata permission din yin magana ne.


Na...manta ....ban bawa maids camomile tea dinka ba jiya , so...

so this morning nabawa madam takawo Maka , tacemin na kawo da kaina .

Wallahi danasan kana ciki bazan shigo ba , na dauka ko katafi office ne , I'm very sorry for bargging into your privacy.


I'll be on my way ! tafada da Sauri tana yin hanyar kofar amma muryar sace ta dakatar da ita ta tsaya kafin takai kofar .


" And  who asked you to leave?

cizon lower lips dinta tai as she stopped in her track .a hankali ta juyo tana Kallonsa , ko kadan fuskarsa ba wata alamun Dariya 

  Kasa tai da kanta kirjinta na bugawa very fast 

" what where you doing there ? ya kuma jefo mata tambayar , lokacin dayay taking step  zuwa gabanta his eyes fixed on hers .


Jadeeda data gama tsurewa ganin Yana matsowa Inda take tashiga Jan numfarshi kamar wata Mai asthma tareda matsawa baya , jitake kamar ta falfala da gudu  tabar masa part dinsa Amma Hakan bamai yuwuwa bane.


She couldn't breath well ganinsa a gabanta Yayinda numfarshinsa ke sauka akan fuskarta , rintse idont tai da karfi , batasan meyasa ba Amma she has start to feel sleepy in that serious situation.


" Kinada matsala da jinkine or are your lips  sealed?

Yafada Yana narrowing idansa as he asked in an irritating voice.


Wani yawu ta hadiye da kyar kana ganin wucewarsa yayinda ruwan gumi ke diga dagà jikinta , tasan cewa she's in a big trouble now .


"I'm sorry bayan na ajiye flask din sai naga wanan pictures din hanging on the wall sai  nazo na Kallah, tafada muryarta na rawa tasan Duk yadda taso fitar da kanta ba lallai ne ya kyalleta ba gwara ta fada masa gaskiya ta taimaki kanta . juyawa yay tareda bin falon  da kallo, yasan me take kallon , sanan ya Maida kanta .


" So have you satisfy your curiosity? 


Dan Allah kayi hakuri wallahi bazan sake shigo Maka waje ba Batareda saninka ba , idan kabarni natafi na Maka Alkawari Hakan bazai sake faruwa ba . Idan tafita da ranta Kenan bazata Kara shigowa wajen nan ba .no matter the consequences tafada ma kanta yayinda ta sunkuyar da Kanta kasa cikin tsoron hukuncin dazai yanke mata .


Kalloñta yake without saying a word ganin yadda jikinta ke trembling with fear , yasan idan ya biyewa zuciya he might end up locking her in the darkroom , but bai san maiyasa he couldn't bring himself to, ji yake kamar something is controlling his mind 

kan yarinyar Nan yasan shi ba Mutum bane dake daukan forgiveness or yay listening to plea din mutane ba , Amma he couldn't do anything to the lady  standing in front of him . 


Saida ya gama kallonta sanan ya juya Yana tafiya .


LEAVE! 

Yafada Yana tafiya Amma jadeeda Bata jishi Sosai ba Dan haka sai ta kuma tambayarsa , 


"Uhm?

I said get out of my site before I do anything stupid to you yafada screaming on top of his voice.


Aikan ya karasa itadai batasan ya Akai ba sai ganinta tai a dakinta , Nan tashiga maida numfashi kamar wacca tai tsare , hannunta tasa tana taba heart dinta dake beating Akai akai ,sannan ta lumshe idonta kafin ta fitar da iska ta bakinta a relief Allah nagode ma , that was close , da yànzu batasan abunda zai mata ba , lallai ta tsallake rigiya da Baya , Dan baKara tafada tana komawa inda gadonta yake ta zàuna har kuma Lokacin Bata dawo yadda take ba . Saida su binta suka shigone  tadan sake suna Hira har tasake gabadaya .


Kwana biyu da faruwar Hakan Wanda kullum take avoiding haduwarta da young master saitaga fitarsa take fitowa Dan ta daukama kanta Alkawarin kiyaye duk wani abunda zai Kara hadasu , kwasam saiga Kiran Mahmud , inda yake gaya mata he wants to see her , kwana biyu Baya Jin dadi , he misses her alot yaushe zatazo gida and so on , 

Tausayinsa ne yakamata sosai ita kanta Hakanne a wajenta Kuma tasan it's unfair for him to wait for her this long , Dan haka tai masa Alkawarin idan tasami time zata zo Amma bata tsaida Rana ba ,  Amma datazo zata kirasa a wayar da haka sukai sallama ta kashe wayar ,

   Tunani tafara ta yadda zata Fita dagà mansion dinnan Batareda ta sanar ma young master ba , don tana ganin haduwarta dashi is the last thing dazatai gara tanemi wata hanyar daban  .

Hakanan tundaga Ranan take sa Ido kan duk Wani fitar da young master zaiyi , Don tayi making up her mind she's going to sneak out of the mansion Batareda Sanin kowa ba .


A hankali ta matsar da curtains din tareda lekawa  , guards dinsa tagani a tsaye yayinda driver dinsa Ke gyara motar ,Hakan na nufin  jiran fitowar boss dinsa yake , 

" Yes tafada Wani Dadi na kamata if I could sneak out batareda Wani ya ganniba har Kuma na dawo Bazai taba sani ba ,There would never be a problem .


Matsala dayace idan aka kamani , tayama zan iya fita daga gate din Batareda Wani ya ganni ba ?


Suddenly Wani tunani yafado mata a Rai , tsaida idanta tayi kan motocinsa guda uku dake masa convey tana Wani tunani daban .


Wani murmushi ta saki Ganin tasamo hanya mai sauki dazata fita daga gidan , idan har motoci uku zai amfani dasu Hakan na nufin he's going to use only one car ragowar kuma guards dinsa ne zasu shiga , kenan inda Zata Sami Daman shiga motar karshe ba mai Ganinta idan tasamu tafita daga gidan then she would find her way as she thought to herself .


Murmurshi tayi tasan she's taking risk Amma it was a wonderful thought tafada tana daukan wayarta tareda zura hijabi kan doguwar rigarta sanan tafito daga dakin tasan at any moment young master zai iya fitowa .

Kodata fito saida  daidaita tafiyarta ganin guards din sun kalleta Lokacin data fito , dabara ce ta fado Mata , kawai sai tai hanyar garden.


Batasan iya Lokacin dazai dauka ba kafin ya fito Amma she has to be fast , da sauri ta tsuguna tana rarrafawa inda motar take Ganin sun juyar da kansu suna Kallon Wani direction daban Wani numfarshi ta sauke ganin sauran kadan wani guard ya ganta , a hankali  ta fara Jin footstep alamun wani na tahowa , makale jikinta tai jikin motar tana sa hannunta a bakinta gudun kar ajita , tsayawa yay a dan nesa da ita Yana Kallon hanyar garden din .

Kwalalo idanunta tai ganin Yana Shirin Juyowa barin datake , aduar tashiga karantowa duk wacca tazo bakinta , shikenan tasan kashinta ya bushe yau ,  sai yànzu take regretting wanañ shawara tata , Daidai Lokacin Daya daga cikinsu ya kwalla masa kira , wai Mai kakeyi ne anan ga boss Nan ya fito yafada Yana kallonsa.

 

Da sauri ya juyo yana tahowa I thought I saw something sainaga kamar mutum anan Wajen yafada Yana karasawa inda ragowar suke , Dariya suka sa masa kaidai kafiya Gane Gane waye zai shigo Gidan Nan under this tight security.

 

Wani gumi ta share Dan har ta saddakar an kamata , Allah ya taimake ta .da wanan daman tasamu suna magana ta Bude Kofar ahankali ,tareda kirga 


One 


Two 


Three 

Tashige ciki , Saida tashiga sanan tafara Maida numfarshi huh ! Finally my plan worked tafada tana Dariya Tareda labewa cikin motar sosai yadda ba wanda zai Iya ganinta . Amma batasan ta makaro ba , coz everything is been watched by someone.


Lokacin da Marwan ya gama dressing Ya Karasa jikin window dan ganin ko guards cars din where ready , ya gansu a Tsaye shi suke Jira harya juya  immediately Kuma saiya dawo saboda Wani Abu dayaga ya gifta a idonsa yana mai  sake kallon windon.


Ganinta yay tana kallon daya dàga cikin motocinsa kamar Wani Abu take gani a ciki , mamakine ya kamashi , he wonder what shes doing there  , Amma bari ya Tsaya yaga Iya Gudun ruwanta , ganinta  yay ta tsuguna  lokacin da daya dàga cikin guards dinsa yaxo wajen Amma Bai ganta ba , har yabar wajen , A hankali ya Kuma ganinta tana rarrafawa harta Bude last car din Dake wajen tashige Tareda maida Kofar a hankali .


He was shocked to his spine , what the hell is she doing ?


 ganin he could not find answers to questions sai ya fito kawai amma  idonsa nakan  motar ,


"Good morning boss ! aka fada daga bayansa

Daya dagà Cikin yaransa ne ke gaidashi ,as he approached the cars , daya daga cikin guards din ya taho da gudu tareda Bude masa kofar motar dake tsakiya , shiga ciki yay aka rufe masa kofar immediately suma guards din suka shiga motocinsu and they  drove out of the compound.


Jin tashin motar taji wani sanyi a ranta finally she's out  tafada tana Kara makalewa jikin kujerar sosai trying not to make any sound.


Daga inda take tana iya hango bishiyun dasuke wucewa .

A hankali tafara Jin motar na slowing alamun zata tsaya .


Idan mun Isa I want you to monitor that lady behind us ka bani feedback on inda zata , Mai zatai Sanan Karka bari ta ganka .


Guard din ya Amsa da yes boss Yana mamakin yaushe wata tashiga motar batareda sun ganta ba , kenan Hakan na nufin tai sneaking cikin motar kenan ko mai , yana son tambaya Amma yay keeping mute to himself.


  Wayarsa ya dauko daga cikin aljinhun sa yay dailing wata number, Sanan yakai kunnensa .


" Do not  lock the doors when you arrive 

Yes boss drivern 

Dake motar da jadeeda Ke ciki ya Amsa batareda ya tambayeshi dalili ba , ya kashe wayar.


Koda suka Isa company din guards dinsa  suka sauka dagà motarsu Tareda Bude masa ya fita .


A hankali ta leko da kanta tana murmurshi hangosa  datai shida yaransa Suna tafiya .


Wow this is the perfect way to go out of the mansion Batareda kowa ya sani ba , am very clever  she thought to herself .


 Sai Kuma ta juya da sauri tunawa datai wanna ne damanta na karshe ta fita daga cikin motar before she get caught wànan tunanin yafado mata .


"The Door ! tafada da sauri  hankalinta a tashi what if sun rufeta a ciki yaxatai , nan tashiga hada gumi , kwata kwata batai wanan tunanin ba kawai tunaninta tashiga ,nan da nan jikinta yafara rawa kamàr mazari , yayinda gumi ke tsatsafowa daga goshinta saboda tashin hankali . Adua tashiga Karantowa duk wacca tazo bakinta kawai Yi take yayinda takai Hannunta jikin handle din kofar tana rintse Idanuwanta ta Murda  a hankali , da sauri ta Bude idanta in shock ganin kofar a Bude take , Hamdala tashiga jerowa , Amma wanañ drivern wawane Tayaya zai bar kofar motarsa a Bude what if wani ya sace mota fah.


Da sauri ta fito daga Cikin motar tareda rufeta a hankali , 

" Muah I love you , you are a good car zan sayeki Idan nasami kudi sosai tafada blowing ma motar kiss murmushi kwance akan fuskarta .


Da sauri tajuya tareda Jan fuskar hijabinta to hide her identify tai hanyar dazai kaita gate batareda bata lokaci ba tafice daga Cikin company din, Wani sign of relief tai data ganta a waje , Inda tasami wata inuwa  nesa da company din taje ta tsaya , tunawa datai bata da kudi a jikinta kuma she's not sure kosu hajia suna gida and tsayuwarta a nan is not safe .

dan haka wayar Mahmud takira tareda Yi masa kwatancen Inda take , aikuwa yace tabashi minti biyar yana kusa zai karaso .

  Nan ta zauna tana tuninin rayuwa ,tasan cewa iyayen Mahmud ba wasu masu kudi bane sosai sunadai da rufin asiri dan mahaifinsa maaikacin gomnati ne , Shima kuma ba iya karatunsa ya tsaya ba , yana hadawa da business Dan har mota yake dashi ...

Horn Taji daga gefenta , da Sauri ta juya Mahmud ta Gani Yana sakar mata murmushi Kanta tashi har ya fito daga cikin motar Yana zuwa Inda take he hugged her so tight I'm so  happy to see you sweetheart  da Sauri ta tureshi  jikinta na rawa Mai haka Mahmud  tafada jikinta na bari , suna waje if  someone sees them  fah meh yakeson ace ,Nan da Nan ta hade rai Mahmud mai haka ko kamanta inada aure what if wani daga Cikin company din young master yaganmu , koshi Kansa  maikake son nace masa , and you know that is against our religion.


    Ok ok I'm really sorry wallahi tsaban farincikin ganinki ne yasani haka Amma bawai deliberately nai Hakan ba yafada yana shafa Kansa Ganin yadda tai kicin kicin da fuskarta .


Nace maki am very sorry Hakan Bazai taba faruwa ba .


Fine naji karka sake ?

Yes ma'am your wish  is my command yafada Yana mata bowing kamar saurauniya .

Dariya kawai tasa shiyasa takeson Mahmud Yana da saukin Kai  hakan kesa mutane susoshi .

 Motar ya Bude mata tashiga sanan ya zagaya Dayan barin yashiga tareda tada engine suka bar wajen .

No comments