Breaking News

Kaddararmu 21-22

 KADDARARMU

                ( OUR DESTINY)

;


                       21_22

For regular update pay 500 into this acct 0013350361 Fatima muhd sagir jaiz bank saiki turo shedar payment ta wanan number 08062352006.


                           ✍️

Kallonta yake he's beyond  shock,  bai gama fita daga shock din mahaifinta datace ya rasuba , yake Jin wanan maganar datai mugun daga masa hankali da Kuma firgitarwa  .

Nan yay tsai da idansa Yana kallonta kamar status , yakasa yadda da abunda take fada , kallonta kawai yake kamar Wanda yau Yafara ganinta he can't believe he's ears kodai kunnensa ne basu jiye masa daidai ba.


  " what do you mean yafada still  idonsa a  kanta  .

"Talk to me ! Jadeeda ban Gane 

 kinyi aure ba , ko Dan na dade banyi contacting Dinki ba , shine kike cemin kinyi aure , I can't believe you're telling me this Idan ma wasa kike min I don't like it,yafada Yana girgiza Kansa in disbelief.


No ! Mahmud ba haka bane don't say such thing tafada tana kokarin kare kanta ganin Yana kokarin misunderstanding  dinta .

Toh idan bahaka ba ,what do you mean by telling me you got married to someone else yafada ransa na tafarfasa muryarsa har wani  rawa take saboda yadda yakejin zuciyarsa kamar zata fito , bai contacting nata ba for some months saboda final exams din daya rikeshi ,a kuma ranan daya gama ya tattara ya dawo kafin lokacin  graduation dinsu  shine zatace masa tayi aure this is  rediculous , his totally broken .


My father owed many people muryarta takatse shi dàga zancen xucin dayake , Kuma daya daga cikinsu shine Marwan muhd salis , tadan dakata da magana  tana kallonsa tana jiran Jin Mai zata ce saboda tasan yasan youngmaster tunda ba karamin mutum bane .


kina nufin he owed his boss too , Wanda yace baida mutunci ko kadan ? yafada Yana kallonta Dan yasan baba Yana aiki karkashin Marwan .


Nodding kanta tai , yes , ya ari makudan kudade a wajensa and used it for gambling ya dauka idan yaci kudin zaiyi doubling but luck wasn't on his site bayan wasan it  turns out to be negative .


And he dead of shock ganin yadda yay asaran  kudin  lokaci guda .bayan Nan boss dinsa yay finding out everything that happened inda Yasa mutanensa taremu a hanya suka kaimu har office dinsa Nan dai ta labarta masa Abunda yafaru har zamanta a gidan kafin dagà baya a daura masu aure .


  And the fact that you don't have feelings for me kika amince da conditions dinsa , yafada kishi nacinsa , Inda kin kirani kin fada mun maganar kudin this could not have happened dan nemo Duk Inda kudi yake abashi , but now everything is ruined yafada yana dukan couch din da hannunsa .


Ba yadda na iya Mahmud kudin nan ba karamin kudi baba ya Karba ba millions of naira Kuma bazanso na daura Maka nauyi ba , despite that nasa kana karatu ,Kuma  bazan iya barin afra tashiga wanan Halin danake ciki ba ,   I can't , wanan aure I  promise you , nothing will happen saboda kwata kwata baida interest akan  mace.


hhhh and you believe that right? yafada Yana Kallonta a dage ,  look jadeeda , mutumin Nan nataba ganinsa a tv  baimin kama da abunda Ake fada ba , it's just a rumurs yafada with so much anger a muryarsa .


Am serious he's just using me to distract his grandfather Amma lokacin Daya daibar min nacika zamu rabu and we will be together.


Shiru yay mata batareda yace mata Komai ba , hankalinta bakaramin tashi yay ba , look Mahmud just give me five months I will be free inshallah and we wilI be back together I promise .


Saida ya dauki lokaci kamar bazai magana ba , kan yace five months Amma daga shi ba Kari , deal ?

 Yess deal ! na yadda  tafada tana masa smiling shima ya na maida mata .


Now ji yadda kika batamin wanan beautiful face din naki da hawaye Dariya Kawai tasa masa.

  He loves her so much that he could not afford to lose her , kallonta yake yayin da take Dariya he loves everything about her , and want to see her always happy , zai iya sacrificing farincikinsa domin ta if that will make her happy , don haka he will wait for her har zuwa lokacin dazata fito daga gidan suyi aure .


Ganin irin kallon dayake binta dashine yasata Dakatawa da Dariyar da take , what ? Why  are you staring tafada tana smiling this time around , 

Blowing mata kiss yay I love you yay whispering , langwane kanta tayi yayinda idanuwanta ke Tara hawaye  I  know  Mahmud , And I love you too , tafada starting to get emotional .


 please jadeeda karki manta da alkawarinmu keep to your promise and we will be back together ok , 

 Dan  zan iya jiranki i will wait for you har zuwa lokacin dazaki rabu dashi .

 

Nodding kanta tai immediately tears dropping from her eyes , I love you yasake  fada yana sakar mata murmurshi tareda Mika mata hanky Dan share hawayenta .


Batai musu ba , takarba tana goge fuskarta duk  yana kallonta .


Saida ta nutse ta kalleshi Mai yasa baka kirani ba  Wanan tsawon lokacin?


Dariya Yasa yasan Dama saita tambayeshi Kuma yasan yay mata laifi

I'm sorry , Ina rubuta exams ne , shiyasa kika jini shiru , Amma yànzu nagama , Kuma kinsan mai ? yafada Yana kallonta , girgiza masa kai tai tana turo bakinta ina gamawa ko Sallama ban tsaya yima friends Dina ba  nataho saboda Nayi Missing dinki sosai .


Harararsa tai cikin wasa nasanka da dadin Baki , munyi wata guda fa baka kirani ba , you made me get so  worried na dauka ko wani abun ne yasameka . Nan dai sukai har hirarsu na soyyaya kan yai mata sallama yatafi .


 Saida ta Kara minti uku kanta fito bayan ta kulle masu Gidan , kallonta suke suspiciously batareda sunce mata komai ba Bude kofar baya tai tashiga cikin motar fuskarta a hade .


Bayan isar su wata koda ta kalli Inda suke ajiye motocinsu ganin sun ragu Hakane ya tabbatar mata da young master Bai dawo ba har lokacin Wani sign of relief taji , Dama batasan su hadu .


Miss ! madam tanason ganinki wata maid tai mata magana Lokacin datake  saukowa daga Cikin motar ,  da Sauri ta karasa saukowa lokacin data tuna young master yace zasu fita anjima yace ta shirya 6:00 zasu fita .


Dan haka tabi bayanta zuwa kiran da madam ke Mata , a zaune tasameta a sitting room , immediately tana ganin jadeeda tashigo tamike tsaye tareda cemata follow me tai commanding dinta  .Batai mata musu ba tabi bayanta a hankali suna Tafiya .


Dakinta suka shiga she could barely recognize it saboda kayan da aka loda kan gadon , gefe guda kuma jakukuna ne da takalma hadaddu sai jewelries cikin Wani boxes , sai mutum biyu  dake tsaye cikin dakin dabata taba ganinsu ba mace da namiji  tunda tazo Gidan da Alama Baki ne .


Jin Karan rufe kofar ne yasasu juyowa suna kallonta  , namijin ne ya kalli madam

 " is she the one ? namijin yafada Yana wani lankwashewa kamar Macce yay ma gashinsa Wani style gyada masa Kai kawai madam tayi tana nunama jadeeda kujerar da zata zauna Ganin gadon ba waje saboda kayan Dake Kai , kafin ta maida Kanta kan mutane Dake tsaye a dakin  wayanan sune wayanda zasu shiryaki saboda fitar da zakuyi keda youngmaster, I will be waiting for you outside tafada tana ficewa daga dakin , Saida ta rufe kofar sanan jadeeda ta Kalli inda suke tsaye .


   Kallon namijin tasake Yi kamar Wani Dan daudu sai Wani fari yake da Ido irin wanda ya kware da aikinsa din nan ,batasan lokacin data saki asharba a zuciyarta  Amma sunma Raina mata hankali in da tadauki abunda sukai mata yànzu bazata dauka ba , Sam bàzàta bari Wani Kato  ya Kai hannunsa kan fuskarta ba da sunan makeup ba wallahi duk abunda zai faru .


Gud day sweetheart, taji muryarsa  I'm a makeup artist and she's a fashion designer muna Daya daga Cikin wayanda ake jidasu a wanan kasa tamu, it's my  pleasure  meeting you .


Kut ay tunda Wanan mai kama da Dan daudun yafara magana take kallonsa kamar tasami television , da sauri ta kalleshi tana mai danja dabaya ganin Yana Miko Mata hannu alamun handshake , hannun ta kallah da Kyau yay Wani irin yellow yellow da Wani Kore alamun Yana bleeching yayinda Nan take Taji zuciyarta yafara yashi saboda aman dataji Yana Taso Mata , 


We are running out of time for the makeup..... Yafada Yana janyo kit din aikinsa .da sauri ta daga masa hannu, 

Tsayawa yay Yana kallonta don Bai fahimci abunda take nufi ba , look , I think there's no need for that the designer is ok please tafada tana hade rai .

 But miss our boss want you to look your best today , kina bukatar mu mubiyun, kallon  datake masa ne yasa Jikinsa yin sanyi I'm sorry yafada sauri yana sadda Kansa kasa .


   Don't worry ka ajiyemin kits din I will do that myself , gyada Kansa kawai yay sanan yajuya yafice daga dakin badan yaso ba , don baisan matsayinta wajen young master ba , Yana tsoron karya fiya zakalkalewa , don bakaramin kudi aka sakar masa ba , don yay mata Kwalliya ba .


Kallon fashion designer tai dake tsaye gefenta , da sauri ta sunkuyar da Kanta ganin takamata tana satar kallonta .

 I will take shower sainazo mu shirya , ok ma'am tafada cikin biyayya tareda Dan matsa mata Dan ta wuce .


Koda tai wankan tafito Saida ya dauketa kusan thirty minutes tana kalkale fuskarta Dama makeup ba Saban Abu bane a Wajenta Nan da Nan sai gata tafito kamar ba ita ba , idan ba kallonta saika dauka ba ita bace ,  sosai tai kyau .

 Rigunane guda biyar akan gadonta lokacin data kai idonta kan gadon, da sauri designer ta karasa kan gadon  Tareda  dauko mata daya daga ciki tana nuna Mata , let's start with this tafada tana Mika Mata rigar , karba tai  tashige bathroom din ta gwada wow it looks nice on her black gown ce har kasa take jah saidai ta matseta sosai , Koda tafito haka taita kodata  dan rigar tai mata Kyau sosai ,madam data shigo dakin da nufin taima jadeeda magana  akan Koran samual makeup artist din da aka dauko mata takanas don yi mata Kwalliya and she was like wow jadeeda tai matukar mata Kyau saika dauka ko Wani artist dinne yay mata Kwalliya  , don haka saita share tareda kodata cikin kayan  , ta  karbi ta biyun pink Itama tasaka Koda tasaka Itama ta mata Kyau matuka , tana fitowa madam dake rike da dayar red ta Mika mata shima , try this I know you would look perfect on it ,  ita har ta fara gàjiya Amma haka ta koma ta Sako rigar .

  

Wow you look good in this dress it looks good on you madam ma takara ,aikuwa dai haka sukaita kodata  sanan  aka daura mata Wani turban a Kai , daya shiga da kayan sosai take daukan Ido kamar wata bride , suka Bata jewelries tasa sai Kuma  Wani flat shoe dashima fadar kudinsa ma Bata lokaci ne saboda kyansa kana ganinsa kasan Mai balain tsada ne. 


Wayar madam ce tafara Kara da alama kiranta Ake tana ganin number ta dauka da sauri cikin nutsuwa tareda girmamawa , amsawa take da yes sir , ok , right away tafada tana kashe wayar .


Kallonta madam tai I will be back in a jeffy tafada tana Bude kofar don fita the girlish man came in , Yana kallon jadeeda tun daga sama har kasa Dake gaban mirror tana kallon kanta ta yadda Tayi kyau kamar yadda Suke fada saidai batai murna daya kasance wanan evil man din taima Kwalliyar Nan ba , how she wish Mahmud ne , she would be more happier.


Tafi Taji daga bayanta don a tunanin ta su biyu ne a dakin tunda madam tafita , Da sauri tajuyo tana kallon girlish man din nan wato  makeup artist da aka kawo mata , wow , wow you're looking stunning and beautiful in that dress .


Thank you tafada with a faint smile ,

 Juyowa  tai  tareda Dan tattare rigar . kofar aka Kuma budewa again madam ce , Inda ta Kalli jadeeda , 

"ki fito young master na jiranki! 

Wani numfashi taja  a hankali tana Mai shakar fita dashi tanajin Wani nervousness  wanan shine karo na farko dazasu zauna waje daya dashi dan  haka akwai wanan tsoron a tattare da ita .


Haka suka fito daga dakin inda take Tafiya a hankali Saboda rigarta Dake Jan Kasa tana gudun karta Fadi Dan bawai Saba sa irin wanan Kayan tai ba , Wanda Hakan zaisa ka Dauka yanga take   .


Yana Nan tsaye Jikin wata black lamborghini Aventador yabada bayansa , Yana sanye cikin wasu kaya da suka kasance sky blue kamar kullum rigar ta matseshi tareda Wani black jeans , ta kulla Yana son irin wanan shigar , tsaye yake Yana wayar baisan ma da isowarsu ba Saida yajuyo dan gyara tsayuwarsa nan idansa ya Sauka kanta tana tahowa kamar wacce ke tsoran taka Kasa hannunta rike da rigarta ba karamin kyau tai a Kayan ba , maganar  da nacikin wayar yay masa  ne shiya  dawo dashi daga tunanin Daya tafi  , da sauri ya Maida hankalinsa Kan  wayar dayake tareda ya dauke idonsa daga  kallon barin datake , Yana mai cigaba da wayarsa Kamar Bai ganta ba .


  Heart dinta ne ke beating very fast as she approached him Dan tunda Taga sun hada Ido takejinta Wani uncomfortable  tana Tafiya kafarta na hardewa kamar yau tafara Tafiya  don haka tai kasa da kanta tana cigaba da tafiya towards direction din dayake .


Wayar yake but he's mind is telling him ya dago ya Kuma kallonta so he watched her approach,batareda yadauke Ido saba ,his eyes tranfixed , unable to pull away , Amma tana Shirin dagowa yay Maza ya Kauda Kansa Yana kallon  elsewhere, maimakon haka ma saiya Bude motar immediately yashige ciki driver seat Hakan na nufin shi zai driving kenan , da sauri guard din dake  tsaye gefensa yay Maza ya zagaya dayan side din tareda Budewa jadeeda Kofar .

Dan murmushi tasaki tareda ce masa thank you , sanan tashiga Wani kamshine ya dakeshi saboda turaren datai amfani dashi , Wanda ya hade da nasa Dana motar Suka Bada Wani Kalan kamshi daban Mai sace zuciya ,Saida tashiga sanan ta  dagama su madam Hannu kan ya rufe mata Kofar and they zoomed off not saying a word to her.

 Wani cool  music ne ke tashi a hankali cikin motar ,yayinda ta rike  Purse dinta  kam a hannunta 

tana mamakin yau Kuma shida Kansa ke driving, komai na cikin motar is black a zuciyarta tace she ko komai yasa yakeson black ,  komai nasa  black ne ? Baki kamar Wani devilish soul , tana mamakin yadda mutum yake Jin Kansa secured da wanan kallan so much around him .


Ganin ba Abunda zatai tashiga kirga trees din dasuke wucewa a hanya tana Neman Abunda zai dauke mata hankalin coz she's suffering air in the car .


Suddenly taga yay pulling over tareda  gangarawa gefen titi kafin ya tsaida motar Chak , da sauri tashiga kallon wajen ganin ba gidaje sai  bishiyu da little grasses .juyawa tai don ganin Ina yakawota tare Kuma mamakin Meyasa ya kawota wajen Nan da daddaren Nan suka tsaya ?


Light din motar ya kunna tareda juyowa Yana fuskantanta , Wanan shine karo nafarko dayake kare mata Kallo sosai to his satisfaction she was so beautiful and innocent, da sauri kamar Wanda aka mintsina ya hade rai his gesture made him come back to his senses  immediately yay pushing wanan Tunanin a Ransa .

Shi mutum ne Wanda ya tsani irin wayanan thoughts din yasha ganin kyawawan mata so there  is nothing special about her.


I'm taking you to my extended family Taji muryarsa Dan haka not all of them are nice , ba kowa Zaki kula ba , yafada Yana dakatawa .


"Now here are the conditions!

Idan muka je gidan inason ki acting kamar we're into each other do you understand yafada Yana tsareta da idanuwansa , saboda yasan this is  the only wai  da zai nunama granpa dinsa  yaji maganarsa ta yadda zai yadda dashi  .


A hankali tashiga nodding masa Kanta ,  ganin yadda ya tsareta da idanuwansa , a ranta kuwa tana tunanin yadda Zata iya acting into each other with a demon like him amma ba yadda ta iya haka tai nodding kanta .


Saida ya tsaya kamar Wani mai Tunani kan ya dauko tab dinsa yashiga hoton farko na granpa ne , ya tsaya akansa my grandfather and this is my grandmother yafada bayan yayi swiping across the screen .


Wanan itace Antyna  da mijinta my father's sister , you should be nice to them , bayan wayanan mutane Dana nuna maki duk Wanda kika Gani karki masa magana without my permission understood ? Nan ma nodding masa Kai Kawai tai , he stared at her for a moment kafin ya tada engine suka hau hanya .


Itadai gabadayanta she's confused Taya zai nuna mata mutum hudu kawai  batareda taga na iyayensa ba , where there his enemies tafada tana tambayar kanta batareda tasami amsar tambayarta ba .

 Jitake kamar ta tambayeshi Amma ta bar ma kanta question din sai Wani lokacin. Basuyi kusancin dazatai masa tambaya Makamancin wanan ba .


Tayi Nisa a tunaninta Taga yayi slowing down hakanne yasata dagowa dan Ganin Ina suka zo ,

No comments