Breaking News

Kaddararmu 19-20

 KADDARARMU

             (OUR DESTINY)


                       19_20



                           ✍️


for regular update pay 500 into this acct 0013350361 Fatima muhd sagir jaiz bank saiki turo shedar payment ta wanan number 08062352006.

 


Hannu ya daga na nufin shafa kansa ya dakata Lokacin da yaji muryar young master.


" Just tell me abunda Kake so nama , but don't turn your back at me .

Shafa kansa yay Yana Jin Wani Dadi daya lullubeshi , I knew it , yasan Marwan is good at heart Kawai his forcing himself to be this way .

  

Dagoshi yay ,  Amma saiyaki kallonsa , wani tausayinsa ne yakamashi that's my boy Yafada yana rumgumeshi , nasan bazaka taba fishi da granpa dinka ba , kasan Mai yasa? yafada Yana kallonsa , Bai Jira amsarsa ba yace because you love me so much da har kake gudun bacin  raina , am proud of you . Very much proud of you yafada Yana bugun kafadarsa tareda dagoshi ya zauna kan kujera .


Kasa yay da Kansa duk Yana sauraran abunda yake fada , 

About the marriage I will .....


Dakatar dash granpa yay , aurenka   da yarinyar I want you to accept it with good faith , I want both to  you live happy  Ina son ganin haka kafin nabar duniya , promise me zakai Hakan yafada muryarsa na breaking .

Hannunsa ya daura Kanna Kakansa ba abunda yake bashi tsoro irin granpa yay masa zancen mutuwa .

  "I will do as you wish ! Shine abunda Kawai yafada , sai Kuma ya Mike I'm leaving.

  Murmurshi Kawai granpa yay Dan yasan abunda ya Bata masa Rai , Dama Kuma yayi hakane sanin weakpoint dinsa , ta Nan yake kamasa a hannu.


Idan har da gaske kake Ina son naga chanji , I want to see you change , and promise me next zuwan da zakai Zaka zo da yarinyar Taga Yanuwanka oky , yafada Yana kallonsa , nodding masa Kai Kawai yay  tareda sa Kai yafice daga falon . Girgiza Kai Kawai Yana mamakin irin wanan Hali na Marwan .


Koda ya dawo mansion kobi takan jadeeda Bai ba , da so yay yana dawowa yay mata Rashin mutunci Amma magannan granpa ne ya dakatar dashi .


Haka aka Kuma diban kwanaki Yana gidan yana harkokinsa , A bikin binta taji dawowarsa inda taita zuba Ido kozai nemeta Amma Shiru , tun tana zuba Ido harta watsar , kullum da sassafe yake fitowa yay jogging sai yay one hour sanan zai koma ciki , Wani Lokacin Kuma saidai Taga fitarsa .


Kwatsam Mahmud yakirata after a long time , akan yadawo gari and yanason zuwa  wajenta .

  Dama akan gado take batasan Lokacin data Sako tashiga zagaye dakin .

 Bana Nan yànzu tafada muryarta na rawa Amma mu bari gobe insha Allah .


Ok then Amma dai kisani Wanan Karan da zafina na dawo , inason iyaye sushigo maganar.


Wani irin kululu taji cikinta yayi , Banda Inallilahi ba abunda take Wanan Wani irin abune ana cikin Wanan sai ga wani, dole su hadu da Mahmoud face to face suyi magana ta yadda zai fahimceta , haka Nan sukai Sallama , a ranan haka tayini  Jikinta a sanyaye .

  

  Washegari  kodata tashi da safe part din youngmaster taje  tana jiran fitowarsa ,   Dama Kuma kamar yadda su binta suka sheda mata 8:00 yake fita office Dan haka cikin shirinta na wata Malaysian gown ta yane kanta da mayafin taje ,

  yau sati guda kenan da daura aurensu , wanda take ganinsa as cover to her Bata Wani damu ba .

So take taje gidan gashi ya kafa mata dokan she could not leave unless she told him , shiyasa yanzun ma tazo  . dukda she's not interested in seeing him often , amma ba yadda ta iya dole Saida saninsa zata samu tafita daga estate din nan saboda tsaron dake gidan .


A Nan Wajen kasan staircase dinsa ta zauna tana tareda fadawa cikin dogon tunani .

 

A hankali tafara Jin footsteps coming towards her , her heart starts to beat da sauri da sauri , as his  steps approached , koyaya ne  Yana da Wani irin kwarjini da yake dashi , Dan haka tana tsoran mai reply dinsa zai kasance .


As he walk quitely suddenly saiyaga mutum a zaune , Saida ya matso kusa ya kulla dacewa yarinyar Nan ce , yayi mamakin ganinta a Wajen  because no one dares to step in his path duk lokacin dayake gida . he wondered who gave her the audacity to come here.


 Dauke Idonsa yay daga kanta, she Bazai iyà tuna last time Daya daura idonsa Kanta ba , Yana mai cigaba da saukowa daga stairs din Amma lokacin dayake kokarin wuceta , he heard her voice.


MA...R..WAN ! Chak ya dakata  da Tafiyar dayake ya tsaya batareda ya juyoba he was surprised and speechless to hear this rat call him by his  name .


Da sauri ta kwalalo idanta Jin kwabar datai .


  A hankali ya juyo looking straight into her eye , bakintane yafara rawa , batasan Wani karambanin bane yasata kiransa da sunan sa ba ,

  I'm ... really sorry youngmaster I... please forgive me Tama rasa Mai Zatace masa .

 Har Lokacin Bai dauke idonsa daga kanta ba , so she really got  the nerves to call him by his name , ganin kallon dayake binta dashi ne  yasata tuna abunda ya kawota .


 I want to leave the estate , can I go ? Juyawa yay Yafara tafiya kawai sai Jin muryarta yay a bayansa pleassse tafada tana Dan Jan please .

 

"No !

yafada dan sai yànzu ya tuna da granpa dayace masa Yana son yakawota family house for dinner tonight.


 "Get ready by 6:00pm we will be out for dinner! yafada Yana barin wajen , Baki Tasaki a wajen tana bin bayansa da Kallo harya bacce ma Ganinta , what sort of a man is this ita tana masa maganan zataje gidansu , shi kuma Yana Bata command din tashirya zasu fita , wai they are going out for a dinner, Wani dinner perhaps  he's taking her to meet his family , hannunta kawai ta ware a sama irin don't know din nan tareda girgiza kanta sanan tafice daga part dinsa .


Daki ta Koma ganin Bata da abun Yi yasata debo littatafan hausan  dasu maris suka kawo mata Dan daibe kewa tashiga dubawa danta daukar ma kanta Alkawarin cire duk Wani Abu dazaisa ta shiga damuwa har waadin zaman ta yakare a gidan .

Sosai littafin datake karantawa ya dauki hankalinta sosai mai suna ukubar soyayya Wanda mallakin usainat salisu , har batasan lokaci yatafi ba .saida taji cikinta Yafara kukan yunwa tukunna  ta tuba da Batai breakfast ba saboda daukin zuwa gida datasa a ranta .


Mts tai Tsaki tareda ajiye littafin  kan side drower Tareda mikewa tsaye wayarta dake gefenta ta dauka tàna duba time , karfe goma tagani nasafe , tasan yànzu duk inda young master yake yayi Nisa Bazai dawo yànzu ba , Dan haka da sauri ta Bude curtains din dakin tana lekawa saboda wani tunani   daya fado mata a Rai . 


Mayafinta tadauka cikin sauri sai wayarta dake  rike a hannunta  ta Bude dakin tafita da sauri , daidai lokacin datake kokarin Saka kafarta waje taji muryar madam daga bayanta , rintsa idanta tai tana adua kanta juyo da sauri tana kallonta Yayinda  gabanta ke faduwa , but she tried to pretend calm.

 

" where are you going to miss ? Ina fatan young master yasan da fitarki ?


Tafada tana tsareta da kallo .


Yes ...ya...yasani I told him myself before he let for work tafada tana adur Allah yasa tabarta , saida ta tsaya tana kallonta kamàr wacca Bata yadda da abunda tafada ba sai Kuma tace , 

 " you can go ! Wani sign of relief jadeeda  taji a ranta but I will call the guards to go with you , dam dam kirjinta ya buga lokacin dataji abunda madam tafada .

 Ok , sure ,  nagode tafada tana yake .

Koda isarta gidan tai kicibis da afra dake  Shirin fita school , Jadeeda afra tafada cikin mamaki meyafaru ? Why are you this early tafada tana satar kallon guards din datazo dasu .


  Do you have time ? tafada tana kallonta  gyada mata kanta tai , inada lectures 12 zan shiga Amma  inada sauran one hour , ok let go inside muyi magana tafada tana kama Hannunta suka shiga cikin gidan .

Saida suka zàuna tukunna  ta dago tana kallonta wai mai yafarune , you're making me feel scared .


Afra he's coming  today ! wa kenan ? I didn't get you who is coming  ? ta tambaya tana kallonta cikin Rashin fahimta .


"Mahmoud! Mahmoud is coming today , mai zan gaya masa ? 

Baki afra tasaki tana kallon jadeeda how did you know  he's coming  ? munyi waya dashi Nan tagaya mata yadda sukai dashi  .


Amma dakin Sani Baki zoba Hakan zai iya zama matsala , koki gaya masa through the phone nasan Mahmud  will understand you better .


No ! maganar Nan Bata waya bace afra zuwan Danayi shine daidai saboda inason mu hadu face to face na gaya masa komai yadda zai fahimta batareda Wani yarigani sanar masa ba .


Toh Amma na dauka ya daina contacting dinki but how...why ba dawoba lokacin sai yànzu da abun ya lalace .


Nima bansani ba , bansan maiyasa yazo lokacin da komai ya dagulemin ba , everything is in a mess tafada tana Maida kanta kan sofa , ita kanta afra she's confused batasan Mai next step dazasu dauka ba .


Yànzu Mai abunyi tafada tana kallon jadeeda data lumshe idanuwanta.


I think Kawai zan sanar masa da gaskiyan abunda Ake Ciki , tunda wanan auren it's just a fake marriage, Nan da five months zan dawo sai muyi auren mu,  tafada tana sakin Wani iskar as a sign of relief escaping from her lips .


Amma kinsan Mai let me tell you a secret that man is a gay ,


What !! afra tafada da sauri  tana tashi zaune tareda  zaro idanuwanta cikin shock tana kallon jadeeda .


Wait a minute inko hakane that means baya bukatar wata mistress coz he's not interested in women .


Exactly! a yadda maganar  tazo kenan ,  mutane da Dama suna zarginsa  da gay , wanan maganan ita tasa Kakansa Samo masa macce ya aura but he refused , so according to rumurs da wanan zancen gay din nasa yafito shine yake using Dina to silence everyone  ta yadda Kakansa zai dauka sharri Ake masa .


gyada Kai afra tai sanan takuma jefa mata wata tambayàr , 

So Idan har hakane maganar  then  mai yasa da farko yace maki you shouldn't die before the five months a conditions din Daya baki.


Wani tarine ya turnike jadeeda da sauri ta tashi daga kan sofa ta dauki ruwan dake ajiye kan drawer tana Sha .  sannu afra tahau Yi mata tana bubbuga bayanta kan tarin yalafa .

  Sorry , it's ok, wanan duk ba Wani Abu bane , duk cikin  barazanarsa ce ,watakila Yana  referring to Wahalar dazaimin ne a  gidansane .


  Dafata afra tai for some minutes sanan tace shikenan ,  jadeeda but nidai Abunda nakeso dake you have to be very careful and stay alert kinsan mutumin Nan is a demon .


  Insha Allah I will do as you say uhum ! tafada tana Jan check dinta a hankali tareda sakar mata murmushi.

  ok , I will be on my way tafada tana mikewa tareda sakala Jakarta , mikewa tai Itama tana bata side hug , take care ok ? tafada tana kallonta .

 I will , idan Zaki fita saiki Sakala  mana key din jikin windon can tafada tana juyawa Dan barin gidan , har waje ta Rakata sanan ta dawo ciki.


Bayan tafiyan afra jadeeda ta Ciro wayarta dagà Cikin purse dinta tashiga gwada layin ,  Mahmud daidai lokacin da kiransa ke shigowa kamar hadin baki , her heart pounded  against her ribcage tana kallon sunan Mahmoud din dake yawo jikin screen dinsa  , tunani take ta dauka,  kota kashe   har lokacin da wayar ta katse . 

Wani Kiranne yasake shigowa  she took in a deep breath kanta dauki wayar .


He..llo tafada tana tunanin ta yadda zata fara Wani conversation dashi 

 Da dane Mahmud yakirata saitafi kowa farinciki she would be shouting over the roof with joy .

 Amma bayan hello din datafada , shiru tai bata Kuma cewa Komai ba , hakanne yasa Mahmud tunani ko Bata  kan layin ne , then he spoke.


 Hello Jadeeda are you there ? ya tambaya  cikin cool voice dinsa Wanda kesa heart dinta melting cikin kaunarsa  , idanuwanta ta rufe yayinda takejin Wani irin sonsa na fizgarta she missed his voice so much , da sauri ta Bude idanta kamar Wanda aka mintsina lokacin da gabanta ya buga tunawa datai yànzu tana auren wani dukda Bata dauki auren a bakin Komai ba .

 

Hello Mahmud I missed you ? tafada tears dropping from her eyes .Baby maiyake faruwa please kigayamin am worried .

Yafada Jin Muryarta na rawa .


No Mahmud Wanan maganar Bata waya bace idan kana Kusa kazo muyi maganar  ina gida , there is something I want to tell you .

 Ok bani like five minutes haka zan karaso gidan , okay I love you , I love you too , tafada tana kashe wayar .


Tayi making up din mind dinta it's better ta sanar masa gaskia kar yaji zancan a Wani wajen , Nan taita safa da Marwa a cikin gidan tana duba agogo Allah Allah take yazo kar youngmaster Yasan Bata dawoba tunawa datai da dinner dayace zasu fita 6:00 pm.

   Da sauri ta dauki mayafinta tasaka tareda karasawa wajen kofar Jin tsayuwar mota a Kofar gidansu , 

 Cike take da fargàba tana tunanin yadda zai reacting idan yaji wanan maganar  , would he end it with her ko Kuma zai jirata tafito suyi auren su kamar yadda suka tsara tun farko .


 Her heart squeeze lokacin datai wanan tunanin na zai iya rabuwa da ita , tasan ba Karamin shock zata fada ba ,Bata sani ba ko zata iya handling shock din dazata shiga ba.

Kwankwasa kofar da Akai ne yasata dawowa daga duniyar tunanin data tafi , da sauri ta nufi kofar  , Saida tai taking breath canta Bude kofar .


Yana Tsaye bakin kofar matashine Shima Mai jini a jika , Mai matsakaicin tsayi baida jiki sosai ba laifi kyakkyawa ne , shine mutum na farko Daya fara sace mata zuciya , sun Hadu dashi first day of her school inda tana tafiya Bata lura dashi ba , sukai karo takardun Dake hannunta suka tarwatse a kasa hakama nasa , 

Sorry tace masa tana kokarin tattare takardun Dake Kasa , ya tsuguna yana tayata , saida suka gama tsaf ya Mika mata tareda Bata hakuri itama ta Mika masa na hannunta tana bashi hakuri kan sukai sallama kowa ya wuce department dinsa .

  Saidata zauna suna lectures ta Bude handout dinta kenan Dan karantawa idanta ya fada kan sunan Mahmud Dake rubuce kan handout din , gabantane ya Fadi tashiga duba papers din , tareda tunanin Ina ta samesu kan a hankali ta tuna da gayan dasukai karo .


Shima a nasa bangaren Koda ya shiga theater dinsu ya ajiye takardun gaban wani abokinsa dake zaune yana gaisawa da sauran yaji muryar Abdullah , jadeeda abubakar Idris Chak ya tsaya dagà mikama Ibrahim hannu ya juyo da sauri Yana  kallon Abdullah dake masa Dariya tareda  shakiyancin wai yaushe yakoma macce , nan  ragowar suka dauka Suma suna dariyar , kayan ya dauka da sauri yashiga  dubawa tabbas wayanan takardun banasa bane na yarinyar datai bumping into him ce dazu , fizge papers din yayi tareda rolling dinsu yasanya a aljihunsa  saboda dariyar dasuke masa , hakane yasashi fita daga theater din tareda komawa inda suka hadu kozai ganta yasan dole tana bukatarsu , ba mamaki itama tanata nemansa , kamar ko tasani, sai gata Itama inda suka hada suna kallon kallo, atare suka ce papers saikuma suka Sanya dariya , I'm really sorry na dauki papers dinki without knowing yafada yana Mika mata , thank you tafada Itama ta Mika masa nasa tareda cewa same here , fuskarta dauke da murmurshi,  thanks yace mata Shima .

   Harta juya zata tafi taji muryarsa daga bayanta , " can we be friends?

  Da sauri tajuyo tana kallonsa , ganin Yana Miko Mata hannun alamun hand shake  fuskarta dauke da mamakin .


Oops sorry yafada Yana Sauke hannunsa kasa sunan Mahmud suleiman from medical department final year student , sai lokacin tasakar masa murmushi nikuma sunana jadeeda abubakar Idris from English dept , wow nice name yafada Yana maimaita sunan , wanan shine alakarsu da Mahmud Wanda a hankali ya rikide ya koma soyayya zallah , dukda ankawo masa tsegumin mahaifinta Dan caca ne Hakan baisa ya janye dagà soyayyar dayake mata ba .

        Cigaban labari

Jadeeda yakuma Kiran sunanta ganin she's lost in thought , as if she not happy  seeing him after a long time.

Da sauri ta kalleshi Anya kuwa kinyi murna da ganina ? Yafada Cikin barkwanci ni sainaga ma kamar kin Kara kiba kinyi Wani fresh , da alama kin manta dani yafada Yana kashe Mata Ido .


 Dan murmushi tasakar Masa yeah Kai Kuma you have thinned alot tafada tana matsa masa dan yashigo ciki , dariya Yasa sanan yake tambayarta da su wanene mutanen Daya Gani a Waje ,yafada Yana nuna mata inda yaran young master sukai parking motarsu .


  Not again tafada cikinta  na kartawa  lokacin data tuno da  yaran young master Dake waje suna jiranta  , Cike da fargàban karsu ganta  da Mahmud.


Dan smile  tai tareda ce masa , let's go in first ! I'll explain tafada tana Bude masa kofar sosai .


Haka dai yashiga Yana tunanin mutanen daya Gani a Waje , 

" Sit please jadeeda tafada bayan ta ajiye masu fararan rubber chairs guda biyu ,

 Thanks yafada Yana zama a Kai  .


Wai Ina baba ,? Ina afra Banga kowa ba , yafada with a smile on his face , don baba mutuminsa ne , mutum ne Mai barkwanci Kuma tasu taxo Daya .

Sai lokacin ta tuna Ashe baisan baba ya rasu ba , 

Maimakon ta bashi Amsar tambayar Dayay mata sai cewa tai tana zuwa bari takawo masa ruwa da abinci Dan hajia na ajiye masu abinci Kanta tafi shago , tasan he must be hungry tafada tana juyawa .


 No please dawo ki zauna , nafison Ina Ganinki Kusa dani , bana tareda wata yunwa tunda nai Ido biyu dake nake jina a koshe yafada Yana smiling.


Saidata dawo ta zauna sanan ta kalleshi , Mahmud we need to talk , akwai Abunda nakeson gaya Maka .


Yes I'm all ears Ina sauraranki yafada Yana zama serious

Nan da nan idanuwanta suka ciko da hawaye , da sauri ya gyara zamansa tareda tsai da idonsa kanta Dan sanin taka maiman Abunda ke damunta .


Allah yay ma baba rasuwa tafada tana kokarin hana kanta kuka .

 Kalloñta yake trying to see if she's telling the truth kan yace .


Nasan da wasa kike  , you like joking alot amma nasan Wanan is expecptional , Taya zakice baba ya rasu  yafada Yana girgiza kai.


I'm serious , baba ya mutu , his gone , gone forever.

Da sauri ya kalleta there is no joke a muryarta Hakan na nufin da gaske take kenan .


What...what did you just  say 


Yadda yayi ne yasa jadeeda fashewa da kuka Kamar lokacin akace mata baba ya mutu.


Bashikenan ba , bayan Mutuwar baba na Kuma shiga Wani shock din , kallonta yake don Jin mai zata ce masa .


  Saida ta dauki dogon lokaci tana tunanin Kalmar dazata gaya masa , tana murza hannunta, kan  dakyar tai forcing maganar Fitowa daga bakinta .


  I....got married , Dam ya dago yana Kallonta tareda zuba mata Ido ...

No comments