Breaking News

Jiddatul Khair Complete Hausa Novel


 


*All thanks to Allah SWT for the chance, privilege and ability to start this book, my special greetings goes to my lovely Mum Hajiya Hajarah and my sweet aunties (Small mums) my siblings/Cousins aren't excluded also... I love them all, Hajiya Adama (Mrs Garban kauye) gaisuwa da fatan anyi sallah lafiya, Chamo da tawagarta su ma duk na gaishesu kyauta😹 and My Sophiee I know you won't see this but get this.. jiddo Love's you dear, Lovely fans and Friends ina maku fatan alkhairi da fatan gamawa da iyaye lafiya*  


_kafin dai in fara post din book din nan i want to let everyone know this.... Although most of my fans sun san i am a final year student, to cut it short... 2 month to our final exams aka tafi strike, so if God should touch Fg's mind by letting dem do d needful i have no choice then to take a break and face my final exams... Balle ma nasan xamu gama in sha Allah before then, coz i have written and keep enough.... thanks for understanding_😉



💖 *Jeedderhh*💖




 _By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻



1.....


Slowly yake driving din idonsa a kan titi yana sauraron abokinsa, amininsa, kuma d'an uwansa dake xaune kujera me xaman banxa cikin motar, can dai ya ja tsaki ya girgixa kai, speaking calmly yace "Ni fa da ma ka canxa labarin nan naka Ahmad, in anyway ban ga amfaninsa ba..." Dariya abokin nasa Ahmad yyi yace "Toh ai ni yana da amfani gareni sosai tunda ina sonta and i want to marry her, look Captain don Allah ka cire son xuciya ka gaya min meye aibun Maryam let me know" Wanda ya kira da captain ya shafa lallausan gashin kansa yace "Kasan mene?" Kallonsa kawai Ahmad yake yana jiran jin abinda xai ce, Captain yace "Ina son ka sanar dani me yasa ku Hausawa baku da xancen da ya wuce na soyayya, ga dai abubuwan ilimi iri iri masu ma'ana da mutum xai karu da su duniya... Amma ku dai soyayya kadai ku ka sa a gaba, did u know that it's just of recent ina wani karatu nayi discovering cewar Airplane water is riddled with bacteria, not even that, jiya jiyan nan na gano cewar...." Ahmad dake masa wani kallo ya dakatar da shi ta hanyar cewa "Wannan kai da masu tunani irin naka ya shafa, what u are saying now will add no value to people like me gaskiya" Captain ya maida hankalinsa gaba daya kan tukin da yake, Ahmad yace "Duk sanda na kawo maka maganar Maryam you always have a way to get rid of the discussion ko me yasa?" Captain yace "Ohk you asked me of her flaws if i am not mistaken, right?" Ahmad yace "Yes so" Captain yace "To xaka ji ynxu.... first of all she is local, secondly she gat no qualities da xai sa ka makale mata dude, just imagine an undergraduate fa?? And worst of all she isn't even beautiful enough, ga dai big babes a garin da ka baro Abuja, sannan..... her hygiene is nothing to write home about, i mean nothing.... Shine ma babban damuwata ma ni" Da mamaki Ahmad ke kallonsa, da farko kasa ce masa komai yyi, can kuma yace "Wani rashin tsaftar kaga tayi??" Captain ya saci kallonsa yace "Oho, wataran xaka gani" Ahmad ya girgixa kai yace "You are talking off hook, Maryam tana da qualities din da ni nake so, I think that's all? Kuma dama kai idan baka son abu to fa baxa ka ta6a son abun ba, ka dingi discouraging mutum a kai kenan" Captain ya gyada masa kai yace "Ehh haka ne, plss close the chapter" Ahmad xai yi magana ya hango inda ake tuyar awara a gefen titi, da sauri yace "Captain plss ka d'an tsaya, I want to get this, na mance yaushe rabon inci awara, tun kafin in tafi Uk fa..." Captain ya d'an kalli wajen da ake tuyar awaran ya kara ma motarsa gudu yace "Allah ya kiyaye, domin na je dauko ka a railway station doesn't mean xa ka mayar da mu gantalallu a hayi.... Meye kuma awara?" Ahmad yace "Toh ka ajiye ni, ai bance sai ka xo ka daukeni a tasha ba dama, you offered to do so" Captain yyi kasa da murya yana rage gudunsa yace "Yanxu Ahmad kasan ta ynda suka yi processing abun nan da xaka ci? Hayi ne fa nan, ka bari kaje gida kasa ayi maka mana, ni Allah bana son locality din nan naka" Calmly Ahmad yace "Su 'yan hayin ba mutane bane Abuturrab?" Captain yace "Aa ba haka nake nufi ba, I mean... hygiene din, they don't value it, ka gane ai" Ahmad yace "Kai komai sai kace hygiene, to sannu sarkin 'yan tsafta, a haka kuma nake son in siya, ba ruwanka kuma" Captain bai kuma ce masa komai ba ganin wani waje da ake suyan yyi parking kafin ya karasa wajen yace "To sai ka sauka kaje ka siya, amma gaskiya you ain't worth being a Dr wllh, very careless Dr that looks down on Hygiene" Ahmad na hararansa yace "Ae ba dankali nace maka xan ci ba malam, Awara nace kuma nan dankali ake siyarwa" Captain ya kalli wajen masu tuyan yace "Toh ai ban san yanda Awaran yake ba, ba shi bane wnn din?" Ahmad yace "Ba shi bane" Captain ya ja motarsa yana tukin a nutse, can underneath his breath ya ja tsaki, Ahmad is just too local for his liking, Ahmad yace "I think ga wani wajen can" ta gefen wajen da ya nuna masa Captain ya gangara yyi parking yana kallon yarinyar dake tuyan awaran yana yamutsa fuska shi wnn ko yunwa xai kashesa xai iya cin abinda take yi kuwa, Ahmad ya bude motar ya sauka ya tafi gun ta, ita kadai ce xaune sai yara da almajirai dake tsaye suna jiran a siyar masu awara, Ahmad yace "Me awara nawa nawa ne awaran naki?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Daya Ashirin" Ahmad ya buda ido ya rike waist dinsa yace "Ikon Allah, kamar dai muna fada da me awara irin wnn amsawan" Still bata kallesa ba ta ci gaba da sallaman yaran da ke gabanta, ta mota Captain ke kallonsu, shi dai Ahmad na tsaye bai sake ce mata komai ba ganin mood dinta, sai da ta sallami yaran gabanta ta daga kai ta kallesa tace "Na nawa xa'a sa maka?" Ya daga kafada yace "Na dari biyar kawai" Tace "Baxai kai ba, sai dai in xaka jira a soya wani" Yace "Toh ba damuwa xan jira a mota" Daga haka ya juya ya nufi motar ya bude ya shiga yana kallon Captain da ya kauda kai da sauri yana kallon daya side din. Leda biyu tayi masa sannan ta hadasu gaba daya a wani ledan daban, yajin ma ta xuba masa a wani ledan snn ta mike ta nufi motar ta mika masa ta glass dake bude, amsa yyi yana kallonta da murmushi fuskarsa yace "Kamar dai an 6ata ma me awara rai" Ita dai bata ce masa komai ba, dubu biyu ya ciro a aljihunsa ya mika mata yace "Toh gashi" ta daga kai tana kallon kudin tace "Na dari biyar kace" Yace "Ehh sai ki rike sauran canjin ai ko" Ta sauke idonta kasa tace "Aa ka dai bani dari biyar din dai kawai" Ya bude ido yace "Dama ana maida hannun kyauta baya" ta girgixa masa kai tace "Ban san wa xance ya bani ba a gida" Cikin sanyin murya ta karasa maganan, yayi murmushi yace "Sai ki boye kayan ki" Daga haka ya saki kudin nan kasa yace "To sai anjima me awara, Allah ya kawo kasuwa" captain da ya ki kallonsu ya tada motar suka bar wajen. Sai da suka kusa fita titin hayi Ahmad yace "I imagine may be condition ne ya sa yarinyar tuyan awara a rana ko, the country is getting tougher and tougher for the less privileged everyday....." Captain dai bai ce masa komai ba, Ahmad yyi kasa da murya yace "On a serious note ina jin tausayin poor masses a kasar nan, yanxu banda situation me xai sa iyayenta su barta bakin titi tana wnn sana'a? Allah dai ya rufa ma kowa asiri" Still Captain bai ce masa komai ba har suka shigo Unguwan Sarki, yana kallon Ahmad yace "Mu je can gida ne kawai?" Ahmad ya gyara xama yace "Aa kai ni in ga Ummata tukun, da yamma xan shigo in sha Allah" Captain bai ce komai ba yyi driving har xuwa gidan kanwar Mum dinsa Hajiya Ramlah warce ita ce mahaifiyar Ahmad... A kofar gida yyi parking Ahmad na kallonsa yace "Baxa ka shigo ba?" Captain yace "Aa ni fa ko jiya na xo gidan nan" Ahmad yace "Sai dai idan Ummi ce ta aiko ka ba dai xuwan kanka ba" Captain ya shafa kansa yana xare manyan idanuwansa ya kasa cewa komai, Ahmad ya ta6e baki ya bude motar ya sauka, da sauri Captain na nuna masa ledan awaransa yace "Heyy ga kullinka ka mance min a mota" Juyowa Ahmad yyi ya jefa masa wani kallo ya dau ledan awaran ya nufi cikin gidansu, Captain ya bi sa da kallo yana murmushi, can ya kashe motar ya sauka ya bi bayansa walking slowly... Siyama ta sake yayanta da ta rungume ganin Captain da ya shigo parlon, tana murmushi tace "Yaya sannu da xuwa" Yace "How are you Siyama" tace "I'm fine" Yace "Ina su Maimuna?" Tace "Sun tafi islamiyya" Yace "Ke fa" Tace "Ka manta nace maka bani da lafiya jiya?" Yace "Ohhh ohk na tuna, Allah ya kara lafiya, Umma fa" Tace "She's in her room" Tuni Ahmad ya nufi dakin Mahaifiyarsa, Captain ya bi bayansa. Sai bayan Magrib Captain ya bar gidan tare da Ahmad xuwa nasu gidan a Malali, Babban gida ne duplex me wadatattcen tsakar gida.... Captain yyi parking a daya daga parking lot biyu dake katon compound din, suka sauka motar tare da Ahmad suka shiga ciki Ahmad na cewa "Amma Abba baya gari ko?" Captain yace "Ehh baya nan"  


Zaune take a d'an karamin tsukakken tsakar gidan nasu da kwanon tuwonta a gaba sae dai ba ci take ba duk da kasancewar hannunta cikin kwanon, wata matashiya ce xaune cikin daya daga kananun dakuna uku dake D'an tsakar gidan hannunta rike da mafici tayi daurin kirji, xaune a tsakar gidan kan tabarma wani middle aged man ne da baxai wuce 58 ba, daga cikin dakin matar ke cewa "Munafuka algunguma kawai, sae ana magana tayi mukui ta ki cewa komai, a haka xaki kare cikin nukurci da bakin hali, banda haka uwar me ya ci min naira hamsin a kudina, ko da yake dama ae kin saba halin bera, sae dai na yau yayi min ciwooo tunda ko biyar ubanki bai kawo min yace gashi kiyi cefane ba, to a kan me??" Ita dai bata iya ta ce komai ba har lkcn hannunta na cikin kwanon tuwon ta kasa ci, mikewa matar tayi tana gyara daurin kirjin jikinta ta fito a fusace ta janye kwanon tuwon jin almajiri na bara tace "D'an malam shigo ka amsa" Malam Isuhu dake xaune saman tabarma yace "Ita kuma ta ci me Hansatu??" Wani kallo ta jefa masa tace "Sae ta ci wanda ka nemo aka girka yau" tana fadin haka ta juye ma almajiri ta ajiye kwanon tayi shigewarta daki, shi dai bai kuma cewa komai ba, a hankali ta mike ta dau kwanon ta kai wajen wanke wanke ta shiga hada kayan wanke wanken tsakar gidan, sae da ta gama gaba daya ta mike mahaifinta dake tsakar gidan har sannan ya fiddo hamsin a aljihunsa yace "Gashi ki je ko dankali soyayye ki siyo ki ci Jiddah" karasawa tayi ta amshi kudin da ladabi tace "Nagode Baba" bata rufe baki ba Hansatu ta fito da gudu ta warce kudin tana kallonsa da kyau tace "Saura dari hudu da hamsin kudin cefane na na yau" tana fadin haka ta kulle kudin bakin xaninta ta shige akurkin dakinta, Jiddah ta juya a hankali ta shiga dakinsu ba tare da ta yarda hawayen dake makale idonta ya xubo ba.


 Washegari da safe wata dattijuwa da baxata haura 55 ba ta shigo wani babban daki  ta kulle kofar tana kallon wanda ke kwance yyi rub da ciki saman gado, karasawa ciki tayi ta buga gadon, juyowa yyi da sauri ya mike xaune ganinta yace "Aunty ina kwana?" Tace "Jiya da daddare ina kaje har bayan isha baka shigo ba" yace "Aunty ina gidansu Ahmad fa, kuma tare ma muka dawo nan da shi na xata kin yi bacci shi yasa bamu shigo ba" Tace "Ohk, jiya Ahmad din ya dawo" Yace "Ehh" Tace "Ai na xata tadi kaje" D'an murmushi yyi yace "Tadi kuma Aunty... Ai tana Abuja" Tace "Atoh na sani ko ka kyallara ido ka ga wata ka watsa min kasa a ido??" Bai kuma ce mata komai ba sai murmushi da yayi, ta juya ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita ta kulle kofar, mikewa tsaye yyi yana kallon agogo dake nuna karfe tara ya shiga bathroom. Kasancewar ranan asabar ce sai kusan karfe sha daya Abuturrab ya fito daga dakinsa sanye cikin kananun kayan da suka matukar amsar sa, lkci daya kamshin turarensa ya gauraye parlon gaba daya, kanninsa mata ne xaune Main parlor din gidan, duk kallo daya suka yi masa suka dauke kai, bangaren Mahaifiyarsa ya nufa, Ramlah ta bi sa da kallo tace "Ummi ta fita fa" Ya juyo ya wuce side din Stepmum dinsa... A parlonta ya sameta tana yi ma autarta Aisha tsifa, yace "Xan je gidansu Ahmad Aunty" Tace "Breakfast din fa?" Yace "Ni nayi breakfast da asuba fa" tace "Oh ka dawo breakfast din asuban kenan" Yace "Ehh" tace "Kawata xata tafi Lagos ranan Monday daga kano shine nace kilan ma you will be piloting the plane...." Yace "In dai flight din safe ne" Tace "Na safen ne ma ina ji" Yace "Allah ya kai mu" Daga haka ya juya yace "Sai na dawo" yana fita parlon, Hajiya Amina da suke kira da Aunty ta kalli autarta tace "Me yasa baki gaida sa ba?" Aisha ta buda hannu tace "Wllh Aunty ranan ce mana yyi mu daina gaishesa a gidan nan idan yana nan, and he was serious about it" Aunty tace "Me ku ka yi masa?" Aisha tace "Babu komai, ranan Thursday da ya dawo duk muna parlor da su Aunty Safiyya muka gaishesa bai ce komai ba, muka sake gaishesa, har ya tafi ya dawo on a serious note yace mana kar mu sake gaishesa baya so, and since then no one is greeting him again and he is very comfortable with that" Aunty ta ta6e baki tace "Toh ai shkkn" A daki Abuturrab ya tadda Ahmad bayan ya isa gidansu, Abuturrab ya nufi window din dakin ya dage curtains din ya bude windon yace "Allow natural ventilation mana" Ahmad yyi dariya yace "Gaskiya ne bature, to kashe Ac din ko?" Abuturrab ya xauna yace "Aa bar shi, how are you?" Ahmad yace "Fine, ya su Ummi" Abuturrab yace "Cool" Ahmad yace "Are you flying on Thursday?" Abuturrab ya d'an yi shiru trying to recall his piloting schedules, kafin yace "Yea, Kano to Lagos, Then Lagos to Abuja, on Friday kuma Abuja to port harcourt" Ahmad yace "Ohk dama Maryam will be going back to schl Thursday I tot kana nan mu kai ta tare" Abuturrab ya ta6e baki yace "Ahmadu Bello?" Ahmad yace "Ehh" Abuturrab yace "Ka kai ta tasha ka sa ta a mota mana, kawai yarinya karama tayi ta juyaka" Hararansa Ahmad yyi, Abuturrab ya fiddo wayarsa dake ring yana duba me kiransa. Bude kofar dakin aka yi Maimuna ta shigo da tray dauke da warmer din danwake da tamarind drink a jug, ajiyewa tayi ta gaida Abuturrab da murmushi fuskarta yace "Ya kike Moon?" Tace "Alhmdllh, Yaya xan je Abuja fa" Yace "To sae ki xo in makala ki a jirgi ko?" Dariya tayi sosai tace "To ai shi sa na gaya maka" yyi murmushi bai ce mata komai ba, ta mike ta fita, bude warmer din Ahmad yyi, Abuturrab dake ta kallon danwaken warmer din yace "Ya ma abin nan da ka siya jiya a hayin Rigasa? Kamar shi nake gani a nan" Ahmad ya wara ido ido yyi dariya yace "Ohh wannan danwake ne, wancan kuma awara, kamar kuwa kasan yau ma xan je in siya, kaji dadin awaran nan kuwa? Gaskiya sun iya sosai, har Umma sai da ta ci, ni uku kawai naci su suka cinye sauran" Abuturrab ya dinga kallonsa da mamaki, can yace "Har komawa xaka yi kenan ka sake siya" Ahmad yace "Yes, I had intention dama" Abuturrab ya gyada kai bai sake ce masa komai ba. Har yamma Abuturrab na tare da cousin din nasa kuma abokinsa.... Su yi fada su shirya, duk bayan sati uku Ahmad ke shigowa kd yyi weekend daga Abuja don a can yake aiki as a medical Doctor, throughout weekend din kuma tare suke spending dinsa da Abuturrab idan shi ma yana garin, karfe biyar saura Ahmad ya mike yace "Captain mu je ka rakani mana pls" Captain ya kallesa yace "In raka ka ina?" Ahmad yace "Hayin Rigasa" Abuturrab yace "Aa sae dai Hayin banki, kaga malam mu fita tare kawai kayi hanyarka inyi nawa, don gida xan wuce yanxu in sha Allah" Ahmad yace "Ae ko baka isa ba, wllh sae ka rakani" Abuturrab ya dau wayarsa xae dau makullin motarsa Ahmad ya dauke yace "Sae ka tafi da kafa ai" kallonsa Abuturrab yyi, lkci daya ya wani hade rai, Ahmad ya fita dakin yana murmushi. Driving Ahmad yake yi, ya kalli Abuturrab dake xaune gefensa yace "Wai Aneesah fa?" Abuturrab ya gyara xama yace "She's good, baka ji muna waya daxu ba" Ahmad ya girgixa kai yace "Kai ynxu da gaske mace da idanuwanta suke a bude da sunan wayewa kake so Captain...." Abuturrab yace "Look at you, kai baka san wayayyun sun fi tsafta ba, ni fa I don't care.... As far as xata yi tsafta 100%, wllh ko haduwa da mace kazama ban son yi a rayuwata, sae inji gaba daya hankali na ya tashi, u know how sensitive I am...." Dariya Ahmad yyi yace "Ita Aneesar tana da irin tsaftar da kake so kenan" Abuturrab yace "Kai ma kasan da ba don haka ba da tuni ae na rabu da ita, kawai sae kaga mace ta ci kwalliya iya kwalliya ta fito amma just check inside, ni in dai mace na da tsafta ko kyanta bai fi 80% ba i will manage her..." Girgixa kai Ahmad yyi yana kallon titin gabansa, Abuturrab yace "Ba ga wajen danwaken can mun wuce ba" Ahmad bai san lkcn da yyi dariya ba yace "Aa D'an gyero ne ba danwake ba" Abuturrab dai bai ce masa komai ba da ya lura u turn yake son yi, dai dai gun awaran Ahmad yyi parking, wata yarinya ce da baxata wuce shekara sha daya ba xaune a wajen tana juya awaran cikin kasko, Ahmad na kallonta yace "Ina me awaran?" Yarinyar tace "Ta je dauko canji a gida shine tace in tsare mata, ae sunanta Aunty Jiddah, a gidansu Bibalo take..." Ahmad ya koma jikin motarsa yace "Gidan ba nisa?" Yarinya ta nuna masa wani rubabben layi dake gefensu tace "Can karshen layi ne, gidansu daya da Bibalo" Shi dai Abuturrab na xaune kujera me xaman banxa yana kallonsu, Yarinyar tace "Lah ga ta can xuwa" Duk suka kalli direction din da ta nuna, Tafe take fuskarta daure hannunta rike da yar karamin bokiti dake a rufe, wanda ke dauke da dafaffen awara, sanye take da hijab ruwan kasa da iyakarsa gwiwa duk man awaran da take tuya yayi staining Hijab din, Abuturrab ya d'an yi tsaki ya hade girar sama da ta kasa yana kallon titin gabansa, tana isowa yarinyar ta tashi tace "Aunty Jiddah gashi xa a siya a awara, da motarsu ma suka xo" Ahmad ya wara ido yace "Aunty Jiddah a bamu kalan na jiya" Ta daga kai ta kallesa tace "Na nawa?" Yyi murmushi yace "Yanda kika sa jiya" Bata ce komai ba ta durkusa ta sa masa awaran sannan ta mika masa ledan, dubu daya ya ciro ya mika mata, tana kallon kudin tace "Yanxu na kai kudi gida na amso canji, ka d'an yi hakuri sai in koma in dauko..." Ya juya ya kalli Abuturrab yace "Ko a siya maka kai ma Captain?" Kallon Abuturrab din tayi ita ma suka hada ido, yyi saurin dauke idonsa yaki cewa komai, Ahmad ya kalleta yace "Toh kinsan abinda xai faru me awara? ki ajiye canjin...." Da sauri tace "Aa ka jira in tafi in dawo ynxu" yace "To tsaya ki saurareni mana, ajiyewa xa ki yi gobe idan Allah ya kai mu na xo sai a bani awara na canjin" tace "Toh" murmushi yyi ya nufi mota rike da ledan awaran, sae da ya shiga motar ta ga ledan yajinsa bata sa masa ba ta mike da sauri tace "Kayi mantuwa" motar ta nufa tana mika ma Abuturrab ledan yajin, da mamaki yake kallonta kamar dai mugun abu take mika masa, yace "Kai!! kinga na siya abu a wajen ki ne?" wani kallon cikin ido tayi masa snn ta xaga ta mika ma Ahmad ta koma gun xamanta tana juya awaran kan wuta, Ahmad ya tada motar suka bar wajen yana hararan Abuturrab da ko a jikinsa. Jiddah na xaune a d'an dakalin kofar gidansu bayan isha, dawowarta kenan daga bakin titi ta gama tuyan dankali da take yi, ta ta takure waje daya cikin hijab din jikinta, wani matashi ne da baxae wuce shekara ashirin da tara ba xaune d'an nesa da ita, yace "Kin yi shiru Jiddah" Ta d'an kallesa tace "Nace babu wata matsala" yace "Kin tabbatar?" Ta gyada masa kai, yace "To ki ci gaba da hakuri kin ji.... In sha Allah idan....." Kamar daga sama suka ji muryar Hansai, ta rike kugu tana kallonsa da kyau tace "Ta ci gaba da hakurin gyatuminka?" Ya kalleta ya duka har kasa yace "Ina yini Baaba" Ta wani sha kunu tace "Da ban yini ba xaka gan ni algungumi?? Ta ci gaba da hakuri a saboda ana cutarta ko? Sannan ban rabaka da kofar gidan nan ba? Dama tun da naga yara sun shigo da kayan tallanta ita bata shigo ba nasan da walakin goro a miya, shine nace bari dai in leko in ga ikon Allah" shi dai bai ce komai ba ya sunkuyar da kansa, tuni Jiddah ta mike ta makale da bango gabanta na faduwa, Hansai ta cire takalmin kafarta ta jefa mata a mugun fusace tace "Wuce ciki munafuka kawai, dama ban rabaki da wnn yaron mara tarbiya ba, ni xa ki ja ma abun kunya a unguwar nan?" Da sauri Jiddah ta shige ciki Hansai ta kai mata dundu da karfi, sannan ta maida dubanta kansa tana huci tace "Wllh na sake ganin ka tare da yarinyata gidan gayun garin nan yyi mana kadan da ni da kai, idan kuma karya ne mu xuba da kai" Tana kai wa nan ta shige ciki ya mike a hankali ya bi ta da ido....



💖 Jiddatul~khair 💖✍🏻

*Ina me mika sakon ta'axiya xuwa ga Chamo bisa rashin mahaifinta da tayi, Allah ubangiji ya ji k'an sa ya gafarta masa, ya sa aljanna makoma, ya bada hakurin rashi, mu kuma Allah ubangiji ya kyautata namu Ameeeen*👏🏻




💖💖 *Jiddatul~khair*💖💖




_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻





2.....


Abuturrab na kwance saman gadon dakinsa yana rike da wayarsa, kunnensa sakale da earpiece, video call yake da wani matashin da baxai wuce sa ba, matashin na xaune cikin wani ubansun parlor yana cin apple, Abuturrab ya girgixa kai yana kallonsa yace "Look... I don't want to say anything about that.... idan Mummy na kusa ka bata mu gaisa" Matashin na taunar apple yace "It's already late, tayi bacci..." Abuturrab yace "It's late tunda baka son fita, so when are u coming to kd?" El-Basheer yace "Xa mu shigo kano tare da Mai martaba next week in sha Allah, probably ni xan karaso, amma sai kana nan" Abuturrab yace "In dai Friday ne ina nan in sha Allah" El-Basheer ya daga kafada yace "Ohk then" Abuturrab yace "Let me pick a call, sai da safe" El-Basheer ya gyara xamansa yana murmushi yace "The lady u don't want to talk about?" Katse call din Abuturrab yyi ya dau daya wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne hade da cewa "How u babe?"

 Abuturrab ne xaune parlonsa a gidansa dake Abuja shigowarsa gidan kenan ko awa daya bai yi ba, kasancewar weather babu kyau yasa suka yi landing flight da suka yi piloting daga Lagos a Abuja a maimakon kano.... Grapes ne gabansa yana ci a hankali yana kallon wani action movie da ake yi a tv, bude kofar parlon aka yi, lkci daya ya daga kai, he was expecting no one other than Ahmad da ya sanar ma yana Abuja... Tsayinta matsakaici ne.... ita ba siririya ba ita ba mai jiki ba, ta karasa shigowa parlon ta kulle kofan tana kallonsa ta cire Nikab din fuskarta, fara ce sosai, kallonta shi ma yake, she looks so orderly from head to toe, tuni kamshinta ya baxa parlon, shi dai kallonta kawai yake ta nufesa da damuwa ta xauna gefensa tace "Why ain't you picking my call Captain?" Ya gyara xamansa yace "It wasn't long da muka sauka ai, na sa wayar a caji a can daki, how are you doing?" A hankali tace "I'm fine, ya gajiya?" Yace "Alhmdllh, where are u coming from?" Ta buda manyan idanuwanta tace "Home... kace min xaka sauka Abuja shi sa na samu na fito" ya shafa beard dinsa yace "Ahmad na hanya, bana son ya xo ya sameki nan, u know how he thinks" Ta langwabar da kai tace "Ohk, amma nace maka ina son muyi magana, ina ta bin ka yau kusan sati biyu kenan sai kace min you will be piloting today, u will be piloting tomorrow...." Da damuwa ta kare maganar, Ya kalli agogo yace "To ina jin ki yanxu, I'm sorry i forgot about that" Shiru tayi, ya kafeta da idanuwansa, sai kuma yyi murmushi ya kamo hannunta yace "Ina jin ki Aneesah" Tayi kasa da murya tace "Aliyu a gidanmu an takurani in fito da miji, kwanaki kuma na gaya maka baka ce komai ba, idan har da gaske kake kana sona what is hindering you pls?" Ya dauke idonsa daga kallonta, bayan few seconds yace "To a jira ki gama karatun mana ko? Ina ce saura kadan" Ta girgixa kai tace "Aa last week Abbana ya kara min magana, and he is very serious about it this time, don't u love me ne Aliyu?" Abuturrab ya xaro ido yace "Not at all Aneesah, kema kinsan ina sonki.... kar ki damu xa mu yi magana, yanxu ki tashi ki tafi kafin Ahmad ya xo..." Ta gyada masa kai sannan ta mike, mikewa yyi shi ma ya wuce daki ya dauko kudi ya mika mata kafin yace komai tace "Aa ni da motana na fito don't worry" Bai ce komai ba ya rakata har balcony snn ya amshi jakarta ya sa mata kudin yace "I know da mota kika xo, Chocolate din da ban kai maki ba last week sai ki siya, ba kudi ne me wani yawa ba" Murmushinta me kyau tayi, tayi kasa da muryarta tace "Thank you my Captain" ya kashe mata ido yace "C'mon babe.... Nikab din kuma na meye yau kika sa?" Tace "I just felt like" ya daga kafada yace "Alright sai mun yi waya" ta gyada masa kai ta nufi gate ya juya ya koma parlor, her neatness melt his heart always nd make him fall for her deeply. Wata dattijuwa ce xaune dakinta tare da yan mata biyu, aka bude kofar dakin duk suka daga kai, Dattijuwar na murmushi tace "Aa Abuturrab sannu da xuwa" ya karasa ciki yana murmushi shi ma, ya xauna sannan ya gaisheta da ladabi, tace "Ka dawo weekend kenan" yace "Ehh daxu muka sauka, ya karfin jikin Umma?" Tace "Alhmdllh na ji sauki yanxu" yace "Allah ya kara lfya" tace "Ameen" ledan hannunsa ya ajiye yace "Ahmad yace in taho maki da wannan" Tace "Kun hadu a Abujan kenan" Yace "Ehh kwana na biyu a can, weather babu kyau sai yau na samu muka bar Abujan xuwa kano, daga kano na biyo private jet" Umma tace "Toh Allah ubangiji ya tsare mana ku dai, Allah ya rabaka da sharrin kayan bature, haka kai kuma Allah yayi hanyar cin abincin ka" Amira tayi 'yar dariya tace "Kabu kabun jirgi Ya Abuturrab yake fa" Ta gefen ido ya kalleta bai ce komai ba, amma ya hade rai sosai, Umma tace "Ni dai Allah ya tsare min shi" a hankali  yana kallon kanwar mahaifiyar tasa yace "Ameen Umma" Tace "Mun yi waya da Ahmad daxu nace masa wani awara da yake kawo min nake son ci wllh, gaba daya bani da appetite, yace kuma a hayi ake yi ko" Abuturrab ya d'an buda ido, sae kuma da sauri yace "Allah sarki, baxa a iya maki a gida ba Umma? Ae kamar yafi tsafta ayi a gida kawai" Tace "Aa da wahala, beside babu ma waken suyan a kasa, Hurairan da xata yi ma ta tafi garinsu daxu, kanninka kuma babu abinda suka iya gasu nan dai xaune, gwara kawai a siya a wajen ya fi, naga me kyau ne sosai ran da ya siyo ae" Abuturrab dai bai sake cewa komai ba, tace "Kuma yace ka san wajen, tare ma ku ke xuwa" Da sauri Abuturrab ya kalleta, lkci daya ya kirkiri murmushi yace "Anya xan gane kuwa Umma, a wani layi ne can cikin hayi fah, the place is very complicated" tace "Aa Aliyu na fa sanka sarai, ko baka sob xuwa ne, idan ma da gaske ne baka gane wajen ba ai kiran Ahmad din xaka yi ya sake maka kwatance" Bai ce komai ba amma lkci daya mood dinsa ya canxa har hakan ya kasa boyuwa a fuskarsa, sai dai bai bari ta lura ba, ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna karfe biyar da few minutes, Umma tace "Ko kana da inda xaka je ne?" Ya d'an shafa kansa a hankali yace "Aa, bari in je in dawo" tace "To Allah yyi maka albarka" da kyar ya amsa da "Ameeen" snn ya mike ya fita, sosai ya hade rai bayan ya shiga motarsa, why will Ahmad tell her ya san wajen, ynxu kawai sai ya fara driving xuwa hayi wai yaje siyan awara why??? wani tsaki yyi ya tada motarsa ya bar compound din. Driving kawai Abuturrab ke yi har ya shigo hayi, he was very observant kar ya wuce inda ake suyan awaran, haka nan yake jin ransa na baci, wani ma ya gansa ya xata shi xai ci, U turn yyi ya samu waje yyi parking yana kallon yarinyar da ta mike xata shiga karamin layin nasu bayan ta sauke kaskon awaran kasa, almajirai uku ne tsaye gun da wasu yan mata biyu, Abuturrab ya dake yace "Kee" bata juyo ba don tafiyarta kawai take kuma da alama ma bata ji ba, Daya daga yan matan wajen tace "Bata ji ba, yanxu xata dawo, xata amso canji ne" Bai ce komai ba ya jinginar da kansa jikin kujeran motar, bayan kusan minti biyar sai ga ta tana dawowa, kallonta yake har ta iso bakin titi, ta kalli motar sannan ta durkusa gun sana'arta, Yarinyar daxu tace "Ke jiddah jiranki ake xa a siyi awara" Sai snn ta daga kai suka hada ido da Abuturrab, ya hade giran sama da ta kasa yace "Nawa kike siyar da kayan siyarwar taki?" Tace "Wanda ya rage a nan bashi da yawa, amma ynxu xa a kawo daga gida...." Bai ce komai ba ya dauke kai, ta sallami mutanen dake tsaye a wajen, bata son komawa gida dauko danyen awaran Gwaggo Hansai ta sake koranta tace bata gama ba, kuma ta bar mata dukiyarta a titi almajirai su sace, Abuturrab ya jinginar da kansa da kujeran motar yana kallon agogon wrist dinsa, wata yar tsohuwa ce ta xo wucewa da kullin icce a kanta, hannunta daya rike da yar leda, ta rike ha6a tana kallon jiddah tace "Har yanxu kaddararren awaran nan bai kare ba har na je inda xa ni na dawo? Ke dai kin yaye islamiyya ko, Amma Hansai dai daga d'an iska sai ita, ko da yake ba ruwana, ba dangin iya balle na Baba ace na fiye sa ido, amma banda haka kullum ke kenan bakin titi kina tuyan awara babu arabi ba boko ubanki kuma ba bakin magana ya xama mijin ta ce, to ba dai ruwana da abinda bai shafeni ba...." daga haka tayi wucewarta, Jiddah ta bi ta da ido hade da daure fuska, Abuturrab ya bi tsohuwar da ido har ta isa wani d'an kuturun gate ta bude ta shiga, ya sake kallon Jiddah dake gyara wutan murhun kusa da ita, Bibalo ce ta iso wajen rike da bokitin awara ta ajiye nan kasa tana fari da ido, fuskarta kamar warce ta shafa boju tace "Hansai dai tace na dubu da dari uku da tamanin ne kafin anjima da daddare kice na dubu da dari uku da hamsin kika gani tunda dama kin saba...." Ko kallonta Jiddah bata yi ba tayi wucewarta tana taunar cingam... Jiddah na fara xuba awaran a mai Abuturrab ya sauke glass din motarsa gaba daya yace "Ke malama jiranki nake fa, kina bata min lkci, kinsan minti nawa nayi a nan yanxu" Sai a sannan ta kallesa tace "Toh ai sai an soya ko baka ganin danye ne? Idan kuma danyen kake so ai magana xaka yi" Dauke kanta tayi ta ci gaba da abinda take, ya rungume hannu daga xaunen da yake cikin mota yana kallonta da mamaki yana sake apprehending abinda ta fada masa, sai bayan minti goma ta kallesa bayan ta kwashe awaran da ya soyu tace "To na nawa kake so?" Ya mata wani kallo yace "Me kika ce min daxu? Sake fada in ji" Ta rufe awaran da ta kwashe a takaice tace "Toh baxan siyar ba, ka tafi gaba can akwai wata me awaran a gaba" muryar Hansai taji a bayanta tana cewa "Bai soyu bane Jiddah, ko ba awaran me motar xai siya ba? Baxa kiyi da jini ba kin xauna kamar wata rubabbiya ni Hansai" da sauri Hansai ta karaso tana kallon Abuturrab tace "Alhaji yi hakuri a kwashe maka yanxu, ta nawa kake so?" Abuturrab na tada motarsa yace "Ae tace ba na siyarwa bane, in tafi akwai a gaba" Da sauri Hansai ta bude roban awaran taga soyayyen awara da ta kwashe a jibge, ga wasu ta xuba a mai, wani lafiyayyen mari ta wanke ta da shi tace "Ubanki ne xai siya wannan da kika kunshe min a gwagwa? Yo ina ma yaga arxikin siyewa tukun, muguwa, axxaluma yar bakin ciki, to Allah ya isa cutata da kike...." Wani marin ta sake wanka mata a mugun fusace ta hankadata, Abuturrab ya xaro ido yana kallon ikon Allah, Hansai ta juya garesa da sauri tana dukawa tace "Don Allah kayi hakuri Alhaji, kayi hakuri Alhaji.... wllh akwai na nawa kake so?" Kasa ce mata komai yyi, ya kalli Jiddah da ta mike tsaye tana shessheka ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta, Yace "Toh har ya kai ki mareta haka??" Hansai ta kara hankade Jiddah da karfi tace "Toh idan ban mareta ba me xan mata, wannn da kake gani makira ce me mugun hali, kuma babu abinda na rageta da shi wllh tllh" cikin tsawa tace "Baxa ki bace min daga nan ba sai na watsa maki man kaskon nan a jiki gaba daya?" Matsawa tayi daga wajen tana kuka sosai, Hansai ta kara turata tace "Muguwa bar min awarata xan karasa suyan, ki je wannan tulin wankin na tsakar gida ban son in xo in ga ko hankici a kasa, duk in samesu kan igiya da lema" Tafiya kawai Jiddah take bata ce komai ba tana kuka, Abuturrab dai dauke kansa yyi, Hansai ta marairaice murya tace "Kayi hakuri Alhaji nasan ta 6ata maka rai sosai,  na nawa kake son awaran?" Yace "Dubu daya" da sauri ta shiga saka masa har ta gama sannan ta mike ta kai masa ya bata kudin ta risina ta amsa tana murmushi hade da godiya, bai ko kalleta ba ya ja motarsa ya bar wajen. Washegari Saturday Abuturrab da yamma ya shirya ya fito daga dakinsa, Umminsa ce xaune parlor da Stepmum dinsa, duk 'yan matan gidan sun tafi makaranta, Ummi ce ke magana Aunty na ta kallonta absentmindedly lkci lkci tana duba wayar hannunta, Ummi tace "Ai mu ma ba sonmu Allah ya fi yi a kansu ba, toh meye a ciki don ta shigo nan ta xauna?" Aunty tace "Haka dai kike ga babu komai a ciki, amma kina da labarin kudin cixo na makalewa jikin kaya kuwa?" Ummi tace "Gashi ai naji a bakin ki yau" Aunty na kallon Abuturrab tace "Kai ka ji fa Aliyu.... Musa me gyaran fulawa ne ya xo da matarsa da yara uku wai sun xo gaishemu daga kauye ina laifin parlan can na boys quarter da har sai sun xo nan don Allah, baka gansu ba wllh abun ba acewa komai, ni yanda kake da kyankyami ma nasan da kyar idan baka yi throw up ba, sai fa da nasa turaren wuta a parlorn ynxu...." Abuturrab ya d'an yi shiru, can kasan xuciyarsa yace for peace to reign.... Sai kuma ya dago kai a bayyana yace "To ai can din ya kamata suje dama ba nan ba Aunty" Wani kallo Ummi ta jefa masa, yayi murmushi yace "That's the fact mum, ita Aunty tsoron bedbugs take...." Aunty tace "Toh ita cewa tayi wai ba a kyauta ba, haka kawai a bada mana kudin cixo a parlor a cuce mu?" Ummi tace "Toh Allah ya baku sa'a, idan walakanta d'an Adam abun yi ne, ku ci gaba" Abuturrab ya shafa kansa ya nufi kofa, Aunty tace "Ina xa ka Captain?" Yace "Xanje wajen wani abokina he just arrived from New york...." Har ya fita parlon Ummi bata ce masa komai ba, yyi murmushi bayan ya shiga motarsa, ko ina ruwansa da 'yan kauye da suka xo da Aunty xata yi involving dinsa at d first place, girgixa kai yyi ya tada motar ya bar gidan, tafiyar kusan minti talatin yyi tunani iri iri na yawo a ransa, ba kasafai yake kwana da abu a ransa ba, infact it's very rare hakan ya same sa, amma jiya ya kwana da yarinya me awara a ransa, dalili kuwa he lead to her been maltreated, she was slapped severally because of him, he felt guilty shi ne ma yasa ya kasa samun nutsuwa a ransa, yana isa dai dai gun da take awaran ya tarar bbu kowa, alamar ba ayi awaran yau ba, yyi ta bin dirty unkept layin da kallo wanda ko mota ba lallai ya iya bi ba sbda gutters dake kwance ta ko ina, ji yyi kamar yyi amai, hankalinsa ya tashi sosai Bibalo ce ta xo wucewa fuskarta yau ma dai kamar warce tayi dambe da powder ga bakinta ya sha jan janbaki, lkci daya ya ganeta, ya sauka motarsa da sauri yana yamutse fuska yana kallonta yace "Yau babu abinda ku ke siyarwa ne?" Tayi fari da ido tana kallonsa tace "Ehh wllh, mijin kanwar babaarmu ne ya rasu yau da safe, tana can gidan mutuwar tace yau baxa ayi awaran ba" Yace "Ohk, ita warce take soyawan tana ina??" Ta wani yatsine fuska tace "Ohh wai Jiddah, tana can gida xata daura sanwan tuwon dawa, nima yanxu gidan mutuwar xa ni Baabarmu tace inje" yace "Ohkk, sai anjima" Tana murmushi tace "Toh sunana Bibalo kai fa?" Wayarsa ya ciro ya kara kunne snn ya koma cikin motarsa ya kulle, ta bi sa da ido sai bayan da yaga ta wuce snn ya bude motar ya tsirtar da yawu yana yamutsa fuska, ita kanta tsami take yi ga uwa uba warin gutter din anguwar, yaji gaba daya cikinsa ya fara hautsinewa, ya fi minti biyar xaune motar bayan ya cika Ac, har yaji ya dawo dai dai, wani yaro ya hango yana tafiya ya sauke glass ya kirasa, yaron ya xo, yana kallonsa yace "Wani gida ne ake awara a layin nan?" Yaron yace "Gidansu Bibalo ne" Ya sauko motar ya kulle sannan yace "Toh kai ni gidan" Nose mask ya sa a hanci bayan glass dake idonsa yana biye da yaron har suka isa kofar wani kuturun gida wanda shi dai ko dabbobi yake kiwo baxai sa su gidan nan ba don kilan Allah sai yayi ma dabbobin sakayya a kan ajiyesu da yyi a nan, gaba daya tsigar jikinsa tashi yake ga cikinsa da ya fara hautsinewa again, he have never been uncomfortable all his life kamar wannan moment din, yana kallon yaron da kyar yace "Shiga ka kira min me awaran" Ba musu yaron ya shiga, can sai gashi ya fito yace tana xuwa, ba a dau lkci ba sai gata ta fito, Hijab ne ta saka iya cinya sai xanin jikinta, gefen farin fuskarta duk bakin gawayi don wuta take rurawa, kallonsa kawai take alamar bata ganesa ba, ya sauke nose mask dinsa, ya cire glasses din idonsa, lkci daya gabanta ya fadi sosai bayan ta ganesa, hakan kuma bai hanata hade rai tana kallonsa ba duk da a tsorace take, shi ma dai cike da karfin hali yace "A xaton ki an mareki jiya sbda ni?" Kauda kai tayi, ya hade rai yace "Ki juyo ki kalleni ina maki magana" Ba tare da ta juyo ba tace "Ni dai ka rufa min asiri bance an mareni sbda kai ba, me ya sake kawo ka nan, in dai awara ne yau babu bamu yi ba" kallon yanda take maganan yake wanda komai ta fada sai dimples dinta ya lotsa, ta kallesa jin bai ce komai ba tace "Nace maka babu awara yau" Yace "Ohk dama sai kuna awara kenan kike wanka ki xauna bakin titi?" Ta wani xare ido tace "Ni nace maka banyi wanka ba??" Tana fadin haka ta kalli Hijab din jikinta wanda shima duk bakin gawayi ne hade da xaninta, slippers din kafarta ma duk ya tsufa, haka kawai ta ji kunya ya rufeta, ta 6ata rai tace "Ni sai kace nace ma banyi wanka ba, bayan girki nake yanxu" Bai tankata ba ya mayar da nose mask dinsa da glasses dinsa ya juya ya bar wajen ta bi sa da ido kamar me shirin kuka har ya kusa bakin titi snn ta juya a hankali ta koma cikin gidan nasu.

💖💖 * *💖💖




_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻





3.....


Karfe taran dare Jiddah ta fito tsakar gida ta xauna kan tabarman dake bakin kofar dakinsu, muryar Hansai ne ya kaurade d'an tsakar gidan tana ma mai gidanta isuhu masifan ita ta gaji da ciyar da shi, shi dai yana xaune baya cewa komai hakan yasa tayi ta daga murya wanda da kyar ba a jin ta a kofar gida, a hankali Jiddah ta mike ta sa takalminta ta fita gidan, wani karamin gida can karshen layinsu ta tafi, tana waige waige ta shiga zauren gidan sannan ta karasa ciki, Wata yar dattijuwa ce tsakar gidan xaune tana ma yara uku dake kwance kan tabarma fifita, Datijuwar tace "An gama tuyar kenan..." Jiddah ta kwance ha6ar xaninta ta ciro dubu biyu tace "Aa yau ai bamu yi ba Baabarmu taje gidan gaisuwa, Iyah ki ajiye min wannan Usman ne ya bani daxu mun hadu bakin titi naje auno waken suya, ki dau dari biyar, sai ki ajiye min dari biyar sai ki sa dubu dayan a asusun da nayi ma Abbana" Iyah tace "Kai Allah dai yyi ma yaron nan albarka, kwana biyu ma bai shigo ya gaisheni ba, ni da a shirye yake ai da ya fito kawai ko Allah xai yanke maki wnn shegen wahalan, kai ko da akwati daya yayi maki indai xai rabaki da Hansai yafi maki wllh, ba yace min a can cikin gari yake da iyayensa ba, nan kuma wajen kanwar babarsa yake xuwa?" Jiddah ta gyada mata kai ta mike ta nufi kofa tace "Sai da safe Iyah kar baabarmu ta nemeni" Tana fadin haka ta fita da sauri kafin a lura bbu ita a can gida, Iyah ta girgixa kai tace "Allah sarki, tsakaninsa da Allah yake sonta wllh, tsorona daya makirar bakar matar can kada ta shiga ta fita ta raba su, tunda ga bibalo babu mashinshini har yanxu sai yawon unguwa unguwa take a hayi, kuma duk sa'annin juna ne, to dai bbu ruwana tunda babu dangin iya balle na baba" 


Ahmad ya gama sa cover shoe dinsa yana kallon Abuturrab dake kwance kan 3 seater hannunsa rike da remote yace "Ya naga kamar duk ka damu in tafi ne Captain?" Abuturrab ya kike xaune yace "Ohh toh ka yi xamanka mana ina ruwana, dama don kace kana night duty ne yasa nake ta reminding dinka, naga it's almost 6, an kusa kiran magrib" Ahmad ya ta6e baki ya mike yace "Yaushe xa ku wuce kanon ne?" Abuturrab yace "Am off for someday kawai i just decided to be in Abuja for a while, may be on friday xan bi train in sha Allah" Ahmad yace "Ohh that's great nima friday nake son xuwa kadunan, rabona da kaduna ai an kwana biyu" Daga haka ya nufi kofa ya fita, yana fita gidan ko minti goma ba ayi ba Aneesah ta shigo, Abuturrab na kallonta yace "Sorry i kept u waiting kinsan Ahmad...." Ta karaso parlon tace "Yeah i understand..." Xaunawa tayi ta ajiye jakarta, ya dawo kusa da ita yace "Kwana uku xan yi a Abuja...." Ta wara ido tace "Har uku?" yace "Yea, ko baxa ki tayani xama ba?" Ta juya ido tace "Aa kaga Dad dinmu yana gari, sai dai in dinga xuwa Ina tafiya..." Ya jingina da kujera yace "No need inyi kwana uku kenan, gobe inyi tafiyata kaduna dama sbda ke na sauka Abuja" Ta marairaice masa tace "Haba dear, to kar ka damu i will try and be with u" Mikewa tayi tace "Me xan girka maka nasan har yanxu baka ci abinci ba" Yace "Just a cup of tea now, mun sha fruits tare da Ahmad" bude kofar aka yi duk suka juya lkci daya, Ahmad ne ya shigo parlon, kallo daya yyi masu ya nufi gun da ya mance wayarsa ya dauka, yana kallon Abuturrab yace "Shi yasa ka damu in tafi kenan" Aneesah dai daure fuska tayi, kamar baxata ce komai ba sai da ya nufi kofa tace "Ina yini?" Banxa yyi mata ya fita ya kulle kofar, Abuturrab ya shafa kansa, a hankali tace "But am afraid Captain..." Yace "You are afraid of what?" Komawa tayi ta xauna da damuwa tace "I think this is the 5th time da Ahmad ke ganina a gidanka, ina tsoron kada ya sa iyayenku su ki amincewa da aurenmu" Abuturrab yace "Ni xan xauna da ke ko wani, don kina xuwa gidana does that mean anything?" Ta girgixa kai bata dai ce komai ba, ya mike ya isa kusa da ita ya kamo hannunta yace "Cheer up dear, beside Ahmad will never do that, i know who he is" kallonsa tayi da manyan idanuwanta ya sakar mata lallausan murmushi ya kai hannu dogon hancinta yace "Basu san samun me tsafta irin ki yanxu sai mutum ya dage ba?" Murmushi kawai tayi yyi pecking cheeks dinta yace "Babu wanda xai raba mu in sha Allah" hanyar kitchen ta nufa ya bi ta da kallo. Suna fitowa train station suka nufi motar dake tsaye yana jiransu, Ahmad ya bude back seat yana kallon saurayin dake xaune driver seat yace "Sorry for keeping u waiting salem, mun hadu da wani abokinmu ne muka tsaya gaisawa" Salem na murmushi yace "Ina yini ya Ahmad" Ahmad yace "Lafiya lau, ya su Aunty" Salem yace "Lafiya kalau" Abuturrab ya xaga ya shiga front seat bayan ya gama wayar da yake yana kallon stepbrother din nasa yace "How are you" Salem yace "Fine, how was the journey?" Abuturrab yace "Cool" Driving din motar salem yyi suka fara tafiya, tunda suka hau saman titin hayi idon Abuturrab ke gefen hanya, Ta madubi ya kalli Ahmad dake danna wayarsa, da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Yau baxa ka siyi awara ba kenan" Sai a sannan Ahmad ya dago kai ya kalli inda suke, ganin sun kusa wajen da yake siyan awaran yace "I had no intention but let me get it for Umma and my siblings" Abuturrab ya ta6e baki bai ce komai ba, Ahmad na kallon Salem yace "Kana wuce layin nan ka tsaya a layin gaba" Salem yyi parking dai dai inda Ahmad yace, Ido hudu Jiddah tayi da Abuturrab da sauri ta sunkuyar da kanta tana gyara hijab din jikinta, Ahmad ya bude motar ya sauka yana kallonta smiling broadly ya rungume hannunsa yace "Sannu me awara" Bata yarda ta kallesa ba tace "Ina yini" yace "Lafiya lau ya kasuwa?" Tace "Na nawa xa a sa maka?" Yace "Ki sa na dari biyar ko?" Satan kallon Abuturrab tayi suka sake hada ido ya dauke nasa idon yana kallon gefen hanya, ta gama sa awaran ta mike ta mika ma Ahmad, ya amsa yana kallonta, sae kuma ya juya ya kalli Abuturrab yace "Bani 1k wajenka I'm not with cash" Abuturrab bai ce komai ba, ita dai tana tsaye, can ya sa hannu a aljihu ya ciro dubu daya ya mika ma Ahmad, Ahmad ya amso ya mika mata ta amsa ta koma ta durkusa xata dauko canji yace "Aa ki bari idan na xo sake siya, shkkn ba sai na sake bada kudi ba koh?" shiru tayi, lkci daya ta mike tace "Toh ai akwai canjinka dari biyar a wajena da ka siya ranan nan, ka tuna?" tana fadin haka ta mika masa dubu dayan, yace "Aa ni na manta..." Daga haka ya shiga mota yace ma Salem su tafi, da ido ta bi motar sannan ta koma ta xauna gun kaskon awaranta.  Hansai ta rike ha6a tace "Yau naga ikon Allah, baxa ki fito ana jiranki ba Jiddah???" Sai kuma tana murmushi ta kalli Iliya dake xaune kan tabarma tace "Da yake bata yi la'asar ba kilan sllh ta fara, bari in shiga ciki dai" daga haka ta mike daga kan kujeran tsugunno da take ta shiga dakin, can taga Jiddah xaune kusa da ghana must go din kayansu tana kuka a hankali, Bude baki Hansai tayi tana kallonta, can ta karasa a mugun fusace ta fincikota ta bugata da bango murya can kasa tace "Don ubanki kina ji na kika kyaleni bawan Allah ya xo tun daxu yana jiranki? Saukansa fa kenan daga legas yace kuma anjima da daddare xa su bi tirelan kaya su koma" Cikin rawan murya hawaye na sauka idonta tace "Wllh Baabarmu bana sonsa, shaye shaye fa yake...." Bata rufe baki ba Hansai ta buge mata bakin da karfi ta rankwasheta ta hankadata bakin kofa tace "Fita kar in sumar da ke, yar bakin ciki kawai muguwa" Goge hawayenta tayi ta fita da sauri tana hadiye kukan dake son subce mata, Can nesa da tabarman ta xauna ta hade rai taki cewa komai, Iliya na murmushi da jajayen idonsa yace "Hauwa kuluwa kwandon kilishi..." Sosai ta kara hade rai, yace "To d'an kalleni mana farin cikin xuciyataa" wani harara ta xabga masa, yayi wani murmushin da lebensa da ya dafe saboda shaye shaye ga idanuwansa kamar garwashi, yace "Mun sauke wani kayan ne yau, amma mun yi lodi xa mu koma xuwa nan da bayan magariba" Ita dai ko kallonsa bata sake yi ba, ya ciro rafan 'yan ashirin ashirin guda biyu sababbi ya ajiye kusa da ita yace "Hansai tace Babanki ya bukaci in turo magabatana, to in sha Allahu ranan laraba xamu yo lodi daga lagos, ina dawowa kuma xan turo tsohona da yayansa, a nan take ma xa a bada sadaki a saka mana rana, don ni a shirye nake" Wasu hawaye suka kawo idon jiddah, ya mike yace "Kice ma Hansai na tafi sai Allah yayi mana dawowa" daga haka ya fita ta bi sa da kallo da dafaffen farin shaddan jikinsa, yana fita Hansai dake la6e tana sauraron duk abinda yace ta fito, dauke kudin tayi tace "Allah yayi masa albarka, ai iliya ba dai xuciya ba, ga masara can ya kawo mana rabin buhu, da wake xai yi kwano biyar wllh, Allah yayi masa albarka" tana gama fadin haka ta dau gyale ta fita gidan..... Jiddah ta hade kai tana kuka sosai, mikewa tayi ita ma ta fita gidan, ta shiga gidan iyah, Iyah ta dinga salati tana kallonta ganin yanda take kuka, duk lallashin duniyan nan tayi mata amma taki sauraronta balle tayi shiru, Iyah tace "Atoh bari in je in ci gaba da tankade gari na kawai" daga haka ta mike ta koma gun da take tankadenta ta xauna ta ci gaba, Da kyar Jiddah ta dago kanta bayan wani lkci tana share sauran hawayen idonta cikin rawar murya ta shiga gaya ma Iyah abinda ya faru, Iyah ta ajiye matankadin hannunta tace "To ubanki ya xama sususu shashasha kenan, banda haka meye mutum xai maida kansa kamar gunki, ko min wani irin asiri tayi masa ai bai ci ya xama kamar gunki haka ba, mutum kawai bai da amfani Allah na tuba, Hansai dai wllh baxata gama da duniya lafiya ba, me yasa bata ba ma Bibalo iliyasun ba, waye bai san iliya ba a garin nan, kawai don axxaluma ce ita ta dage sai ta hadaki da d'an gwangwan d'an shaye shaye? Ranan babu inda labari bai kai ba kan cewar Iliya ya mari mahaifinsa, ba ga uwarsa can a kana radd ba tana 6ara, kanninsa mata kuwa duk karuwanci suke kowa yasani ba wani boyayyen abu bane, ohh na shiga uku ni iyantama, kaiii Hansai da kyar taga annabin rahama, da tasan abun arxiki ne iliya wllh baxa ta so ki da shi ba sai dai Bibalo amma da yake tasan waye shi sai cusa maki shi take alallai adole...." Jiddah dai kuka kawai take, Iyah tace "To dai ba ruwana nawa ido tunda 'ya yana sun hanani shiga maganan da bai shafeni ba, barin ma na gidan Hansai matar da bata gaji mutunci ba" tana fadin haka ta tafi ta ci gaba da abinda take, a hankali Jiddah ta mike tana share idonta ta fita gidan kada Hansai ta koma taga bata nan.


 Abuturrab na xaune parlon Umma tare da Ahmad suna cin abinci a tare, Umma dake xaune tana kallo tace "Toh ba dole ku yi shiru ba dama" murmushi kawai Abuturrab yyi, Ahmad yace "Ni xan kawo maki ita ai ta gaisheki Umma...." Umma ta katse sa tace "Ka kawo min wa?" Bai kuma cewa komai, Abuturrab yace "Warce xai aura wai Umma" Umma tace "Akwai wata da xai aura bayan Ramlah ban sani ba?" A tare suka kalleta, Ahmad dai ya ci gaba da cin abincin gabansa bai ce komai ba, Umma tace "Ban da dai ku yaran yanxu abinda ku ke hange daban gida bai koshi ba ai ba a kai waje ba, is there anything wrong with Ramlah da baxaka iya aure ba?" Still Ahmad bai ce komai ba, Umma tace "Ni baxan yi abinda xai cutar da kai ba, meye da Ramlan da baka sonta ka gaya min" Jin bashi da abun ce mata ta mike ta fita daga parlon, Abuturrab dai sai kallon Ahmad yake, bayan few seconds Ahmad ya dago ya kallesa, d'an murmushi kawai yyi ya ci gaba da cin abincinsa, calmly Abuturrab yace "I dont want to believe kayi ma Umma shiru ne saboda Ramlah kanwata ce" Ahmad ya d'an kallesa sai dai he was mute, Abuturrab ya girgixa kai yace "Don't be quiet because of me, coz if i were in ur shoes i wont keep quiet, baka son Ramlah ga warce kake so to meye na yin shiru? Abinda ake tunanin shi xai karfafa xumunci shi ke 6ata shi, meet Umma.... Pour out ur mind to her, tell her who u intend marrying" Murmushi kawai Ahmad yyi ya maida dubansa kan TV, mikewa Abuturrab yyi yace "Xan amsan ma Ummi drugs a pharmacy so i will be on my way now" Ahmad yace "Alright, anjima da daddare xan shigo in sha Allah" Abuturrab yace "Ok then" daga haka ya fita parlon, amma sai da ya fara shiga main parlor yyi ma kanwar Mahaifiyarsa sallama sannan ya fita gidan. Abuturrab na bedroom dinsa bayan magrib Ahmad ya shigo, Ramlah ce biye a bayansa hannunta rike da cup din shayi da xata kai ma yayanta kamar yanda ya sa ta, Ahmad ya xauna gefen gado, Abuturrab na kallon Ramlah bayan ta ajiye shayin yace "Aunty ta dawo?" Ta girgixa kai tace "Aa bata dawo ba" Yace "Ohk" Ta kalli Ahmad dake danna wayarsa tace "Ya Ahmad su Umma fa?" Ya kalleta yace "She is fine, ya school?" tace "Lafiya lau, ya su Siyama" Yace "Alhmdlh" tace "Kai ma in hado maka shayin?" Yace "Aa sai kace nine Abuturrab" Dariya tayi, Abuturrab dai bai ce masu komai ba, ta nufi kofa, bayan ta fita Abuturrab yace "Mun yi waya da El-Basheer daxu yana gaisheka" Ahmad yace "Oh Yarima, kwana biyu bamu yi magana da shi ba ma" Abuturrab yace "Xai shigo Kadunan amma may be kana Abuja lkcn" Ahmad yace "Allah sarki, Allah ya kawosa lfya" Abuturrab yace "Did u talk to Umma?" Ahmad yace "About what?" Abuturrab yace "Ohh har ka manta" Ahmad yyi murmushi yace "No i dont need to, tunda ga abinda Umma take so, in sha Allah hakan xa ayi" Abuturrab ya mike a fusace yace "What nonsense, why will u say so bayan kai ba son hakan kake ba" Ahmad yace "Tunda Umma tana so nima dole in so" Abuturrab yyi masa kallo yace "Why just speak like an illiterate now?" Ahmad yace "Wait Captain, is there anything wrong with Umma's choice?" Abuturrab yace "Yes tunda ba son choice din kake ba" Dariya Ahmad yyi yace "Mun ta6a magana da kai nace bana son Ramlah? Asali ma duk cikin cousins dina babu wanda muke shiri da irin Ramlah, Ramlah was kinda brought up in our home since she was 2, tunda takwaran Umma ce kuma rainonta ce ita shi yasa take son ta hadamu, fine if Ramlah is okay with that ni bani da damuwa" Tsaki Abuturrab yyi ya koma ya xauna, Can yace "Ita kuma Maryam din dama yaudaranta kake kenan?" Ahmad yace "Idan wani xai min wnn kallon banda kai Abuturrab, it's just that my Umma's choice is my choice" Abuturrab ya jawo wayarsa dake ring ganin Aneesah ke kiransa ya katse ya shiga kiranta, Ahmad ya mike yace "Bari in gaida Ummi" daga haka ya fita dakin....



07087865788✍🏻

💖💖Jiddatul~Khair💖💖






_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻






4......


Jiddah ce xaune kusa da Abbanta dake kwance tsakar gida saman tabarma da wani pillow da ya yakune, hawan jininsa ne ya tashi tun daren jiya, magunguna ne ajiye daga gefensa wanda da kudin da take tarawa wajen Iyah ta samu ta siyo masa magungunan, ko bi ta kan inda ta samo maganin Hansai dake ta yankan dafaffen awaranta bata yi ba, Sosai Abban nata ke jin jiki shi yasa duk hankalinta ya tashi, Hansai dai sai ta6e baki take, lkci lkci kuma tayi tsaki har ta gama abinda take yi ta mike tace "Yau ai sai ki xuba ruwa kasa ki sha tunda baxaki siyar min da awara ba kin wani makale kusa dashi wai bai da lafiya, to a duniyar nan yanxu wake da lafiya? Kowa ba lallaba kansa kawai yake yi ba, idan ka xauna ka fake da ciwo ai sai yunwa ta kar ka, ko da yake shi kwanciyar tasa ma da rashinta duk daya ai, Atoh duk daya mana tunda mace ce ke rike da gidan" Daga haka ta daura roban fentin dafaffen awaranta a kai da jarkan man gyada tace "Idan kinga dama in Bibalo ta dawo kice ta sameni bakin titi, tun safe ni ko ganin gilmawarta ban yi ba ko ina taje oho" kofa ta nufa da xaninta da yyi dukundukun xata fita, Jiddah ta goge hawayen dake makale idonta tana kallon Abbanta a hankali tace "Sannu Abba...." Bai iya yace mata komai ba, Hansai ta saka kai xata fita suka kusa cin karo da Iyah, Hansai ta koma baya tana washe baki tace "Sannu da xuwa Iyah" Iyah tace "Yauwa Hansatu, ya me jiki naji ance Isuhu bai ji dadi ba" Hansatu tace "Wllh da sauki kuwa, ga magungunan da na siya masa can ma, to ko kwayan hatsi bamu da shi a gidan shine nace Jiddah ta xauna tare da shi in fita in siyar da awaran nan, ba wata me yawa bace ta dubu uku ce kawai don dai a samu na cin abincin yau da gobe, kinga ai ba a xauna dukka ana jinya ba" Iyah tace "Gaskiya ne, Allah dai ya rufa asiri, yi maxa yamman ma tayi, Allah ya bada sa'a" Hansai tace "Ameen" Daga haka ta fita gidan, Iyah ta karasa ta dau kujeran tsugunno ta xauna tace "Sannu Isuhu" Da kyar ya gyada mata kai, Iyah ta rike ha6a tace "Farin mutum bafillatani duk ya kode kamar bai ta6a haske a rayuwarsa ba, Allah dai ya baka lafiya ya rabaka da cutan nan" Nan ma dai ya gyada mata kai, Iyah ta kalli Jiddah tace "Ya sha magungunan kuwa?" Jiddah ta gyada mata kai, Iyah tace "Toh Allah ya yaye masa" A hankali Jiddah tace "Ameen" Iyah ta bi d'an kuturun tsakar gidan wanda hansai ta mayar kamar na mahaukata da tarkacenta da kallo snn ta ta6e baki ta maida dubanta kansa tace "Amma kana ji na Isuhu" shi dai kallonta kawai yake yana numfashi da kyar, tace "Don muhammadurrasulillahi S.A.W.... ba a dai san gawan fari ba amma ka dubi Allah ka gaya ma wnn yarinya Jiddah inda dangin uwarta suke taje ta nemo su a fadin duniyar nan" Ya sauke numfashi da kyar muryarsa baya fita sosai yace "Iyah Mahaifiyar Hauwa 'yar Nijar ce...." Iyah tace "Kullum xancen ka kenan Mahaifiyarta yar Nijar ce, to a Nijar din bata da dangi ne Isuhu?" Ya sauke wani numfashin yace "Ni dai kowa yasan ni maraya ne ina almajiranci Uban gidana Alhaji Auwal ya daukeni ya rike kamar d'an sa sbda duk safiya xan wanke masa mota in share masa tsakar gida har ma in je masa aike, ni ban san garinsu Amina mahaifiyar Jiddah ba a Nijar din, ni dai tace min su 'yan Nijar ne, rana daya uwarta ta daukota suka dawo Nigeria wanda babu tantama kurciya aka mata, ko da suka dawo Nigeria basu walakanta ba don wata Hajiya ta amshe su hannu bibbiyu kakar Jiddah na masu aiki...." Iyah tace "To kai duk a ina kasan wannan labarin da ka kunshe ma cikin ka isuhu?" Yace "Mahaifiyar Jiddah ta bani labarin" Iyah tace "Toh ina ji" a hankali yace "A haka har Allah yayi haduwata da Mahaifiyar jiddah ranan naje kasuwa mai dakin uban gidana ta aikeni, ita kuma Jiddah Mahaifiyar ta aiketa, ban wani sha wahalan samun Mahaifiyar Jiddah ba sbda uban gidana ne ya tsaya min kan komai, a gidan da muka xauna wanda uban gidana ya kama mana haya a lkcn, muka hadu da Hansatu tana xuwa gun kanwar Mahaifiyarta, suka shaku sosai da Amina Mahaifiyar Jiddah duk da ko a lokacin Hansatu xata yi Shekara kusan talatin da wani abu amma bata ta6a aure ba, a lkcn kuma aurenmu ko shekara bai yi ba da Aminatu, ni dai nasan watarana na dawo daga kasuwa Amina ta sani gaba ai sai na auri Hansatu sun xauna tare yau Hansatu ta 6ata labarinta da irin tsananin da ake mata a gida duk don bata samu mijin aure ba kuma taji tausayinta sosai, wllh wllh Auren Hansatu kaddara ce daga Allah amma Amina ce sila, ta takurani, hatta iyayen gidana basu amince da auren ba a sannan, amma sbda son da nake ma Aminatu bana kuma son bacin ranta na lallabasu sai dai sun nuna min babu ruwansu a batun auren kuma babu biyar dinsu a auren, yawanci xannuwan da nayi ma Hansatu na lefe ma xannuwan Aminatu ce ta bani, kinji dalilin auren Hansatu, ni baxan ce sun yi xaman tashin hankali ba gaskiya don ko hakan ya faru Amina bata ta6a nuna min ba don har yau ban ga mace me hakurin Amina a duniya ba duk da xaman mu bai yi nisa ba don ta haifi Jiddah da shekara daya ta rasu, a lkcn Hansatu na da cikin Bibalo kin ji yanda rikon Jiddah ya koma gun Hansatu tun ba a yayeta ba, Uban gidana ya so Jiddah ta dawo wajensu bayan rasuwar Mahaifiyarta amma Hansatu ta saka mana kuka xa a rabata da jiddah, ita a bar mata ita xata raineta kamar yanda xata raini Habiba su taso tare, hatta Mahaifiyar Amina ta so amsan Jiddah bayan rasuwar 'yar ta, Amma Hansatu ta bi ta da dadin baki taki bata, ashe ita ma ba mai tsawon rai bace, don bayan rasuwan Amina da shekara uku ita ma ta rasu...." Jiddah dai kallon Abban nata kawai take don bai ta6a bata labarin nan ba sai yau, ta dai sha jin mutane na cewa Hansatu ba baabarta bace amma bata yrda sbda ita ta taso ta gani, Iyah sai girgixa kai take tana cewa "Allah me girma, ashe dai Hansatu baxata wanye lafiya da duniya ba... wuhuhu, Allahu akbar, To su iyayen gidan naka suna ina suka bar ka ka walakanta ka gantale haka, ai ko ba komai nasan sun ci moriyarka dai ba adadi" lkci daya Hawaye ya kawo idonsa yace "Hansatu ce dae ta rabamu, Alhaji Auwal ya bani kudi miliyan 2 in kai masa banki ban samu xuwa bankin a ranan ba sbda ruwan da aka yi kamar da bakin kwarya ina tsoron bin hanya da kudi haka, sae na dawo gida da kudin, Hansatu ta xare dubu dari biyu a ciki, kudi ko sama ko kasa, sbda Alhaji Auwal din yace bai yrda ba bayan na sanar masa 6atan kudin da naga bani da mafita, shine matar nan taje har gida ta ci masu mutunci ba na wasa ba, basu yi mata komai ba amma shine har yau, kudi kuma yace ya yafe min ya dai amshi sauran kudinsa, to kinji abinda ya faru... Wnn gidan ma da muke ciki ai shi ya siya min wllh, yau shekara bakwai kenan da ya bar kaduna suna Abuja da iyalansa" Iyah tayi tagumi tace "Yau naga tsinanniyar mata, dama ance ita ta talauta ka da ba haka kake ba, ilai ga magana ta fito...." Yace "Duk ta bi ta siyar min da filayena biyu da gonata daya, da wnn gidan kadai na tsira...." jiddah ta goge hawayen dake makale idonta duk jikinta yyi sanyi, Iyah tace "In sha Allahu xa mu ga karshenta kuwa, abinda Allah baya bacci, ynxu damuwata inda wnn yarinya jiddah xata samo danginta, to gidan da kakarta tayi aikatau a ina yake?" Yace "Wnn ai sun fi shekara sha biyar da barin kaduna, idan ko ba barin kaduna suka yi ba to sun sauya wani gidan ne don xuwana biyu duk akan haka amma aka sanar min sun tashi" Iyah tace "Abu ya lalace kuwa, banda haka ai baxata rasa basu labarin kanta da garinsu ba, kaga da ko su sai suyi ma jiddah hanyar xuwa dangin uwarta ita ma ta dawo mutum, amma ina mutum a nan ba dangi" girgixa kai kawai yyi, Iyah tace "Toh Allah ya rufa asiri, xaka ci tuwon masara da miyar kubewa in tafi in yi maka yanxu?" Jiddah tace "Xai ci iyah, tun safe bai ci komai ba sae kunu da ya sha" Mikewa Iyah tayi tace "Toh bari in je in hura gawayi yanxu ina da komai a gida, yanxun nan xan gama, to ae mayyar ba wani damuwa da rayuwarsa tayi ba, ehh Hansatu ba" Daga haka ta nufi kofa ya bi ta ta ido har ta fita, murya can kasa yace "Kiyi ta hakuri kin ji Jiddah, wataran sai labari, nasan ban ta6a cutan wani tsawon rayuwata ba, ina fatan Allah ya dubi hakan, albarkacin hakan kada ya bari ki walakanta, Allah ya yanke maki wnn wahala da kike sha cikin gaggawa yayi maki abinda yafi alkhairi a rayuwarki, ina maki addu'an Allah ya baki hakuri da juriya da kauda kai irin na Mahaifiyarki Amina, kar ki kaga ana maki abubuwa ina shiru Jiddah, har gobe bani da kamar ki a duniya jiddah tun bayan rasuwar mahaifiyarki, Ban yi shiru a kan batun aurenki da wannan takadirin yaron da take ba, don har yanxu ban furta komai ba hakan ba yana nufin na aminta da auren bane, idan anyi duniya domin manzon Allah xaki auri mijin da xai kula dake yayi maki abubuwan da mu muka kasa maki, xaki auri wanda xai rike ki bisa gaskiya, wanda xai yanke maki wannan wahala da kike ciki in sha Allah" Hawaye ya shiga sakko mata ta kasa ce ma Abban nata komai, amma taji hankalinta ya kwanta sosai, da kyar ya ci gaba "In sha Allahu wannan takadirin ba mijin ki bane Jiddah..." ta gyada masa kai tana gyara masa kwanciyar kansa, ya lumshe ido yace "Tashi ki je kiyi wanke wanken da ta sa ki kar ta dawo kin ji" Ta goge idonta cikin sanyin murya tace "To Abbana Allah ya baka lafiya" Yace "Ameen Jiddah" Mikewa tayi ta tafi gun uban kwanukan da Hansai ta tula bakin kwararo k'uda sai fareti suke a kai, sbda yawan kwanukan sai kusan la'asar ta gama ta mike ta dau buta ta xuba ruwa jin ana kiran sllh ta ajiye inda Abbanta ke alwala ta koma kusa da shi ta durkusa tace "Abba ka daure ka tashi kayi alwala" Jin yyi shiru ta kai hannu jikinsa tace "Abba la'asar yyi...." hannunsa taga ya xamo kasa daga jikinsa, ta kamo hannun tace "Abba...." Shiru bai amsa ba, komin bacci ko rashin lafiya shi din ba me nauyin bacci bane, hakan yasa ta sake kiransa nan ma shiru, jijjigasa tayi taga dayan hannun ma ya xame, bata san lkcn da ta kwala wani ihu da karfi ba kan kace me mutane suka shigo gidan da sauri jikinta na rawa tace "Ku taimakeni Abbana yaki tashi" Wani makocinsu wanda har da shi ya shigo ya kai hannu jikinsa lkci daya ya saki salati yace "Isuhu ai rai yyi halinsa" Daga wnn Jiddah bata sake jin komai ba ta dai bude ido ta ganta kwance saman tabarma dare yyi ga mutane cike tsakar gidan. Bayan kwana uku, Jiddah na xaune tsakar gida da idonta da yyi bulu bulu ga wani rama da tayi don har sannan bata iya cin komai, Hansai sai faman yankan awara take tana cewa "Ke kadai aka ma mutuwa idan ba munafurci ba, Ita Bibalo ba ubanta ne ya rasu ba halan, munafuka kawai me neman suna, kin taso kin fita da kayan awara bakin titi ko sai na taso na nakada maki shegen duka, idan bamu yi awara ba yau ubanki xa mu kwakulo a kabari mu ci?" Hawaye kawai Jiddah take ta mike ta dau kaskon awara da coal pot da wasu kananun kayan ta fita xuwa bakin titi, Hansai tace "Ni wllh idan ba binsa kabarin kika yi ba bansan kina yi ba, bayan mutuwan da yyi ya bar ni da wahalan yi maki kayan aure duk da dai katifa da robobin kitchen kadai Allah xai hore min inyi maki, to ince me wnn wahalan da ya bar ni da shi, ina ta sintirin xuwa gidan Saude xaman makoki miji ya rasu ashe nima nawa na kan hanya xai tafi ya bar ni da wahala, to banda dai dama ya gaji da duniyar daga tashin hawan jini sai mutuwa Allah na tuba, shi dai yaji da munafurcinsa kawai dama ya gaji da duniyar ne, to ba dai ya mutun ba dai ai shkkn, yanxu ga aurenki dake ta karatowa ya gudu ya bar ni da wahala" A haka jiddah ta dawo ta sameta tana ta kumfar baki ta dau robon awaran ta fita, har sannan jiddah taki dawowa dai dai, gani take kamar mafarki take xata farka taga Abbanta bai rasu ba, har yau da aka yi uku abincin kirki ta kasa ci, don ma Iyah na tsareta sai ta sha kunu, banda tsine ma Hansai babu abinda yan anguwan ke yi ganin Jiddah bakin titi tana tuyan awara, daga mutuwar miji da kwana uku har ta ci gaba da awaranta wnn wani irin xuciya gareta, yawanci duk Jiddah ake tausayi don shkkn ta xama marainiya gaba da baya yanxu....  Abuturrab na kallon Ramlah dake yankan ma Umma Fruits yace "Umma ta ci abinci kuwa?" Ramlah tace "Aa bata wani ci ba, Amma Aunty Zainab taje gida xata yi mata tuwo yanxu"  Ummi dake xaune kan farin kujera a ward din tace "Ga farfesun hanta ma da nayi mata bata ci ba" Abuturrab ya kalli Umma dake kwance da drip a hannunta yace "Umma ko a siyo maki awara?" Ta d'an yi shiru kafin a hankali tace "Toh Allah ya sa in iya ci, bana jin dadin komai a bakina" Ummi tace "Toh wannan ai dole ne Ramlah... Kawai daurewa xaki yi kici ko kadan sai kiji jikin ya maki kwari" Abuturrab yace "Toh bari in je in siyo maki yanxu" Daga haka ya fita, Slowly yake driving din har ya karasa hayi, dai dai u turn din wajen ya juya ya nemi waje yyi parking yana kallonta ta glass din motar, kanta a kasa tana juya awaran cikin man kaskon a hankali, ya sauke glass din motar yace "Ki bani awaran dari biyar" Dago kai tayi tana kallonsa, kallon idanuwanta da suka kumbura yyi, bata ce komai ba ta saka masa awaran yanda yace snn ta mike ta isa gun motar tana mika masa ledan, bai amsa ba yace "Kukan me kika yi haka??" Ta sauke idonta kasa, lkci daya xuciyarta yayi mata rauni wasu sabbin hawayen suka cika idonta, da mamaki yake kallonta, bata san lkcn da ta fashe da kuka sosai ba tace "Abbana ne ya rasu" Daga nan kuma kamar warce aka tunxura ta jingina da motar ta dinga rera masa kuka, a hankali underneath his breathe yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Kuka kawai take so painfully, ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ya bude motar ya sakko ya xagayo yace "Yaushe ya rasu?" Cikin kuka sosai tace "Yau aka yi uku" Da mamaki yace "Shine kika fito suyan wannan abun" Cikin rauni tace "Baabarmu ce tace sai na fito" Dauke kansa yyi, can yace "Awaran na nawa ne gaba daya?" Ta juya ta kalli roban awaran cikin shessheka tace, wai na dubu biyar tace min" Ya girgixa kai bai ce komai ba, can ya juya ya bude motarsa, kudin da ya ciro xa ayi masa delivering eye glasses da yyi ordering online ya dauko a motar, kamar wanda ya tuna wani abu ya fasa fito da kudin a haka sai da ya saka a wani ledan turare snn ya juyo yana kallonta, har sannan kuka take sosai, ya mika mata ledan kudin yace "Gashi ki kai mata kice ance kada ki sake fitowa sai an kwana biyu" Kallon ledan ta dinga yi da yyi mata dishi dishi sbda hawayen idonta ya kamo hannunta ya mika mata ledan ya amshi ledan awaran ya saka a mota yace "Allah ya gafarta masa" daga haka ya xaga ya shiga motarsa ya tada ya bar wajen, share hawayen idonta tayi ta leka ledan taga dari biyar sababbi dal a rafe, sosai gabanta ya fadi, ta kasa kwakkwaran motsi, wani almajiri ne yace "Awaran ki na konewa" Da sauri ta juya ta sauke awaran, ta xauna xuciyarta na bugawa da karfi, muryar Hansai taji a bayanta, Hansai ta ajiye bokitin wani awaran tana cewa "Ta dari biyar ce wnn, gaba daya ya kama dubu biyar da dari biyar...." ganin awara ya kone a mai tayi tsit tana xare ido, lkci daya ta saki salati da karfi tace "Na shiga uku awaran kika kona min Jiddah???" A mugun tsorace Jiddah ta mika mata ledan kudin tace "Baabarmu wllh wani ne ya xo ya kawo min wnn wai in kai maki kar mu sake fitowa sai bayan kwana biyu...." Hansai ta karbi ledan tana duba ciki da sauri, xaro ido tayi tana kallon tulin kudin cikin ledan, lkci daya ta dinga bin anguwan da kallo, murya can kasa tace "Daga ina yake?" Jiddah ta buda hannu har sannan jikinta na rawa tace "Wllh ban sani ba" Hansai tace "Dauko jarkar man da roban awaran mu wuce gida ai ya kare ma" A haka Jiddah ta kwashi kayan awaran ta bi bayan Hansai dake tafiya da sauri da sauri, A bakin kofar dakin Hansai Jiddah ta makale tana kallonta tana ta faman kirgan kudi duk ta hada xufa, har ta gama kirgen tana xaro ido tace "Dubu dari a wannan marran ni Hansatu, Allah yyi ma bawan Allahn nan albarka, yanda ya taimaki marayu Allah ya taimakesa haka shi ma, kaiii a duniyar nan ma dai xaman wasu toshe hanyar alkhairi kawai yake, banda haka daga rasuwan Isuhu kamar daga sama Allah ya jefo bawan Allah ya bamu dubu dari cif cif, yaushe rabon inga dubu ashirin da idona ni Hansatu" Jiddah dai ta sunkuyar da kanta xuciyarta na mata xafi bata ce komai ba, Hansai tace "Maxa ki sa ruwa kiyi wanka kema ko kya ji dadin jikin ki, kinga dai mutuwar nan alkhairi ne garemu sai kiga Allah yyi ta bude mana hanyoyi iri iri, aa ni dai wllh gwara da ya bamu hanya mu san me muke ciki a duniyar, to da ya baki kudin sai yace maki me?" Cikin sanyin murya tace "Yace kar in sake fitowa sae bayan kwana biyu" Hansai ta fashe da kuka tace "To dama banda talauci me xai sa mijina ya mutu in fara awara a ranan da aka yi sadakan uku, ai sai dai talaucin dama" Ta kara rushewa da kuka tana matsar kwalla da bakin xaninta, juyawa jiddah tayi a hankali ta bar bakin kofar tana dada jin mutuwar mahaifinta kamar a mafarki wanda hakan yasa hawaye kawowa idonta.



*Still on free pages kar labari ya dauko maku dadi ku ga an datse don free pages din ba yawa ehee, u can proceed with payment sbda kawai a ci gaba ba sai an tsaya ba after free pages din, that is idan kunyi payment kenan fahh....*👌🏻

Tunda dai littafin me sunana ne wannan kunsan baxan gantalar da littafin ba, don haka kar kuyi fargaban komai ku ma baxan gantalar da xuciyoyin ku ba a gaskiya😹😹


Ping 07087865788 for payment details.

💖💖 Jiddatul Khair💖💖





_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻






5.....



Alhaji Usman ne xaune parlonsa tare da Hajiya Hauwa, ya ajiye wayar hannunsa yace "Toh ke ya kika ga Madam?" Ummi tace "Aa in dai tana so babu wani matsala daga gareni sai yanda kace" Ya jinjina kai yace "Toh shi Ahmad din ne yace yana sonta?" Ummi tayi murmushi tace "Toh wannan kuma gaskiya i can't say Alhaji" Abba yace "Toh sai na fara magana da shi Ahmad din da Ramlah, don ke da kanwar nan taki na lura kanku kadai ku ka sani" Yana murmushi ya kare maganar, tayi 'yar dariya tace "Aa ai baxa ayi masu dole ba dama" Yace "Toh Allah yayi xabi mafi alkhairi dai" Ta amsa da Ameen. Bayan sati daya aka saka ranan bikin Ahmad da Ramlah wanda xa ayi bayan wata uku. Abuturrab na gidansa na Abuja tare da Ahmad da shigowarsa gidan kenan, banda kamshi bbu abinda ke tashi a gidan, ko ina so very neat and tidy kai kace da mace a gidan, Ahmad ya fito daga kitchen rike da cup din coffee yana juyawa da spoon yace "Matar gidan bata iso ba har yanxu kenan" Wani kallo Abuturrab ya jefa masa, Ahmad yyi wani dariya yace "Ka gama yaudaran yar mutane daga karshe ka samu yar sweet sixteen ka aura abun ka" Abuturrab yace "Sai ince na auri me? Ashe xaka sha mamaki kenan idan kaga na auri Aneesah" Ahmad yace "Gaskiya don ban ta6a sawa a rai cewar xaka auri Aneesan nan ba, ku dai gama holewan ku tayi auren ta kayi naka" Abuturrab bai kuma ce masa komai ba ya maida hankalinsa kan TV dake aiki, Ahmad ya nemi kujera ya xauna yace "To in har da gaske sonta kake da aure kayi magana mana a saka mana rana daya gaba daya" Abuturrab that is already getting pissed up yace "You dont have to tell me what to do with my life dude..." Dariya Ahmad yyi yace "Of course, especially in a case like this" Tsaki Abuturrab yayi ya mike ya dau wayarsa ya wuce daki ya bar masa parlon... Ahmad na gama shan coffee din ya mike ya bisa xuwa dakin, xaune ya samesa da wayarsa yana magana alamar video call yake, Abuturrab ya kallesa sannan yace "Toh gashi nan ya shigo sai ku gaisa" Ahmad yace "Waye?" Abuturrab ya mika masa wayar, amsa yayi yana kallon screen din, suna hada ido ya buda baki yace "Mutanen Egypt ne dama" Bai rufe baki ba tace "Waye wannan???" Dariya yayi yana kallon uban glass da ta saka a ido fuskarta duk ya cika screen din wayar yace "To glass din kuma da kika maka haka wa ya ara maki?" Ji yayi tana cewa "Farida xo ki mayar min da fuskar Aliyu don Allah, kamar ya shiga wani kiran fuskar wani nake gani" Wata yar budurwa ce ta leko wayar ta xaro ido tace "Lahh Hajja ai Yaya Ahmad ne" Warce ta kira da Hajja tace "Kaji wani xance to ni ina ruwana da shi xa a sako min fuskarsa, ki mayar min da fuskar Aliyu nace, idan kuma baxai yiwu ba ki kashe kawai, waye kuma wani Ahmad, ni na san shi" Ahmad dake ta dariya yace "Nima ae ba saninki nayi ba kawai miko min wayar aka yi" Hajja ta sake wayar ya fadi tace "Ni dai na shiga uku, A gaskiya wannan ai walakanci ne da cin fuska, ya xan dinga magana da Aliyu fuskar wani kato ya fito, wayar taki ce ta lalace ko wa'adin da aka debar mana na magana da Aliyun ne ya kare aka sako min fuskar wani can" Farida ta ma rasa abun cewa sai dariya take, Ahmad ya katse wayar ya jefa gefen Abuturrab shi ma yana dariya, Abuturrab yyi murmushi yace "Yanxu fa take tambayar ka shine ka shigo na baka fa...."


 Iyah ce tsaye kan jiddah dake ta kuka kamar an aikota, A fusace tace "Toh meye amfanin wnn shegen kukan da kike ne wai, nace ki hado tsummokaranki in sa ki mota tunda da kudin ki a hannuna ki tafi legas wajen Salame kawai" Jiddah na kuka tace "Toh Iyah idan iliyan ya hadu da ni a legas din fa? Shi ma fa a can yake aiki ai" Iyah tace "Legas din bai fi Najeriya girma ba aka ce maki, ta ina xai ganki a gari me girma haka" Shiru Jiddah tayi tana kallonta wasu hawayen na sauka fuskarta, Iyah tace "Ni dai ba ruwana ina kokarin ganin na rufa maki asiri kar a aura maki takadiri kina min gardama, hakkin makotaka fa nake son in fita, banda haka me na hada dake Jiddah?? Sannan ni ce mutum ta karshe da Allah ya ba iko nayi hirar karshe da mahaifinki kafin ya mutu, to sai in xuba ido ki tagayyara ya kullace ni duk inda yake?" Jiddah ta sauke idonta dake xuban hawaye xuciyarta yyi rauni, Iyah tace "Atoh babu ruwana wllh, ba dai gobe xata tafi kasuwar tasha siyo kayan sana'arta ba, sai ki shirya tana fita in kai ki tasha kawai, ko da tirela ne sai ki bi xuwa legas din, amma idan ba haka ba shkkn rayuwarki ta lalace idan aka aura maki Iliyasu" Iyah na kai wa nan ta tafi gun tuwonta dake kan murhu tana cewa "Na fita hakkin ki duk da ba dangin iya ba na baba, amma hakkin makotaka fa??" Jiddah dai gaba daya jikinta yyi sanyi, she is too young to even think straight for her age, hakan yasa taji gwara kawai ta gudun don gashi har an xo an sa mata rana wata daya dai dai da Iliyasu a yau.


 Aunty na kallon Nafisa, cike da fada tace "Tashi ki fita ki ban waje" Ba musu Nafisar ta mike ta fita kamar xata yi kuka, Aunty ta dubi Abuturrab dake dakin yana kallonta tace "Wllh baka gansa ba Captain, ni dai ban ta6a ganin haka ba, banda yarinta da dolanci me xata yi da shi don Allah??" Abuturrab na cin Apple din hannunsa yace "Meye da shi wai Aunty?" Cike da takaici Aunty tace "Don dai sai da yamma ka dawo jiya da ka gane ma idonka...." Yace "Aa ni a garin nan ma nayi sllhn juma'ah, private jet muka biyo daga kano, sha biyu da rabi ina kaduna..." tace "To a ina ka tsaya sai bayan la'asar ka dawo gida?" Yace "Muna tare da wasu abokanmu" Aunty tace "Shi yasa, ai da ka gansa wllh... Muna xaune fa jiya da safe kamar abun arxiki tace mana wai Salis yace xai xo bayan an sakko juma'ah mu gaisa, na xata abun arxiki ne har da sa masu aiki su tayata yi masa snacks iri iri wai ashe gantalalle xata kawo mana..." Abuturrab dake ta kallonta yace "Toh meye da shi baki fada min ba har yanxu" Tace "Toh kaga Captain tun daga bakin titi da kafa ya tako har nan, ashe ko motar ma bashi da, sai kaga wani yakunannen yadin da ya sa bbu gugan arxiki, kana ganinsa dai kaga 'ya yan ya ku bayi, ni ko a raina nace ko ina wannan yarinyar ta samo mutumin nan haka, ni wllh a bakin stairs na tsaya amsa gaisuwarsa ban yarda na karaso parlon ba" Abuturrab yyi murmushi ya kai Apple dinsa baki yace "Wani sana'a yake yi?" Wani kallo ta jefa masa tace "Sana'a, wa ke ta wani sana'arsa banda abun ka, ko ka mance da wannan saying din that goes thus... The way u dress will be the way u will be addressed??" Abuturrab ya gyada kai kawai bai ce komai ba, tace "Wllh na sake ganinta tare da shi Allah sai na ji mata ciwo kowa ma ya huta, ita kuma Ummi da taya bera 6ari sai wani nan nan take da shi, tarba dai yanda kasan mutumin arxiki haka tayi ma yaron, ni ko kunya kamar in nutse wllh, Salem kuma inda ya burgeni ko kallonsa bai yi ba da ya shigo parlon kawai yyi wucewarsa daki..." Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh Allah ya kyauta...." Tace "Ameen sai ka kirata and talk sense into her head... Ba ni xata kwaso ma abun kunya ba" Mikewa yayi, tayi saurin cewa "Captain ban kai ka kaje kaga filin da na siya ba ae" Yace "Xuwa gobe in sha Allah" tace "Lahadin xaka koma aikin?" Yace "Idan Allah ya yarda" Tace "Wancan satin kasa nayi maka tamarind drink baka dawo ba..." Ya shafa kansa yace "Wlh daya daga pilot din da xai yi piloting jirgi daga lagos xuwa port Harcourt bai ji dadi ba shine ni nayi, wnn satin ma ban yi niyyar dawowa ba coz i was so stressed out during the week" Tace "Gashi ko ka xo kadunan ba wani hutawa kake ba tunda ba xama kake gida ba" yyi murmushi kawai, tace "Sai kaji an sa ranan Ahmad da Ramlatu" Yace "So Abba told me" Tace "Atoh bai fi mata ba, yar uwarta ta tsaya kula ya ku bayin garin nan, Ahmad ai d'an gayu ne d'an boko ga hankali da nutsuwa duk da dai ni ba wani shiri muke da shi ba, though auren xumunci ne ma ai amma gwara hakan, Nafisa ma tace min ai tasan tsohuwar Budurwarsa Maryam islamiyyar su daya kafin ta canxa islamiyyan" Abuturrab ya nufi kofa yace "To Allah ya kyauta" Tace "Bayan an gama da na Ramlah sae a dawo naka da Aneesah ko?" Murmushi yyi yace "Allah ya kai mu lokaci" Daga haka yyi mata sallama ya fita yana duba agogon wrist dinsa, kira ne ya shigo wayarsa, ya duba ganin Aneesah ya daga ya kai kunne yace "Don't tell me har kin sauka?" Tace "God!!! Nima Don't tell me baka fito ba Captain" Ya wara manyan idanuwansa yace "Ban dade da shigowa gida ba... But in few mins time xan karaso I'm sorry" Bai jira me xata ce ba ya katse wayar ya fita ya hau motarsa.... Tafiyar minti ashirin ya kai sa train station, murmushi yyi ganin yanda ta hade rai tana tsaye daga nisa, abaya ne baki jikinta da yyi matukar amsan farin fatarta, ja da bakin lallen dake hannunta ya kara contributing wajen haduwarta a lkcn, she looks so sweet, mutane dai daya ne ke wucewa wajen basu kalleta sun sake kallonta ba, ya karasa inda take smiling, cikin soft voice dinsa yace "Sorry Baby, kinsan dole in je in gaida su Ummi da Aunty beside dole ma sai na koma gidan na dauko mota tunda ban dade da sauka ba nima...." Cike da shagwaba tace "Kasan mutane nawa suka tambayeni numbata tsayuwar da nayi nan yanxu" Yace "Sai kika basu kenan" Ta juya masa fararen idonta ta ki cewa komai, murmushi yyi ya amshi trolley din hannunta ya fara tafiya xuwa gun motarsa tana biye da shi tana kallonsa don komai yyi burgeta yake. A hankali yake driving din Aneesah dake gefensa tace "I learnt about Ahmad's engagement with Ramlah" idonsa na kan titi yace "So i heard also" Tayi kasa da murya tace "To mu kuma namu fa?" Still bai kalleta ba yace "Xa ayi" Tace "Yaushe??" yace "Am trying to put things in order first, i don't get why u are in a rush Aneesah, ba dai ni nace xan aure ki ba, meye kike damun kanki haka? Do i look like a liar or do my words sounds deceptive?" Ta kai hannunta kan nasa cikin sanyin murya tace "I just can't imagine loosing u My Captain, i just can't...." Yace "Keep ur mind at rest Neesah, i am all urs and urs alone" Yana fadin haka ya sakar mata murmushinsa dake kara narkar da xuciyarta, dai dai nan kuma ya kai layinsu Jiddah, yau bata awara a bakin titin don babu alamar ma ta fito, sai dai mutane ne cike fal a d'an layin nasu, a hankali yake driving din yana kallon cikin layin, Aneesah dake kallon direction din ita ma tace "What's happening there, ko anyi rasuwa ne?" kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Ko in sauke journalist taje ta gano mana???" Dariya tayi tace "Oops a wnn local area din xanyi journalism dina Captain? Haba this is so disgusting..." Tana magana tana yamutse fuska, shi dai bai ce komai ba yana ci gaba da driving dinsa, can gidan Kanwar babanta ya ajiyeta a unguwar sarki, bayan ya yi mata few shopping na kayan ciye ciye, ta sauka motar bayan yyi parking tana kallonsa, shi ma ya sauko ya fiddo mata da trolley dinta ya kai bakin gate din ya ajiye, ta dau ledan shopping din da yyi mata tana kallonsa bayan ya dawo cikin sanyin muryarta tace "Thank you My Captain, plss ka daure ka xo anjima da daddare mu yi hira..." Ya kashe mata ido yace "Ohk babe...." Daga haka ya shiga motarsa yyi reverse ta bi sa da kallo har ya fita layin tana sake jin wutan sonsa na ruruwa a xuciyarta. Abuturrab na komawa gida yyi parking nan kofar gidansu ya shiga ciki yyi alwala snn ya fito ya shiga masallaci don ana ta kiran magrib, bayan an idar ya fito masallacin ya shiga motarsa ya xauna yana danna wayarsa, ajiye wayan yyi yana kallon flowers dake xagaye kofar gidan nasu trying to imagine the meaning of the crowd they saw earlier a layin yarinyar nan me awara, did someone die again, tunanin hakan ya sa ya tada motarsa ya bar layin, yana isa yyi parking bakin titi ya dau nose mask dinsa a motar ya saka snn ya bude motar ya sauka, ashe da daddare sana'a ake yi sosai bakin titin layin, just like sauran layukan anguwan gaba daya, daga me soya wancan sai me soya wannan, masu siyar da gyada, rake, abubuwan ci na gargajiya dai yawa... A hankali yake tafiya cikin layin yana yatsine fuska, he is even afraid kada allergy ya je ya kamasa cos he is so sensitive to anything Filth,... har dai ya kai dai dai kofar gidan da yaron nan ya ta6a kai sa a matsayin gidansu yarinyar, tsaye yyi yana bin duk wajen da kallo, ginin block ne sai dai ko plaster babu, sannan gidan karami ne sosai, duk gidajen layin haka suke, banda gida daya da ya d'an darasu girma shi ma da kadan wato gidan Iyah, wata yarinya ce ke tafe ko takalmi bbu a kafarta, ya bi ta da kallo yace "Baby...." Juyowa tayi tana kallonsa yace "Xo in aike ki cikin gidan nan" Yarinyar da baxata wuce shekara shidda ba ta dawo tace "Gidansu Bibalo?" Yace "Ehh, shiga kice ana kiran me awara a ciki" Da gudu yarinyar ta shiga, babu kowa tsakar gidan don Hansai ko minti biyar ba ayi da fitarta ba, ta shiga makota, Bibalo kuma tun la'asar rabonta da gidan, yarinyar ta kutsa kai cikin dakin su Bibalo tana kallon Jiddah dake kwance ta takure waje daya kan yakunannen katifarsu da Bibalo, tace "Wai ana sallama a waje" Da sauri Jiddah ta mike xaune da idanuwanta da suka yi jajir, duk da tasan Hansai ta fita gidan don sai da ta bar mata sallahun bakar magana ma kafin ta fita amma hakan bai hana xuciyarta dinga bugawa ba jin abinda yarinyar tace, A tunaninta saurayinta ne Usman ya xo, kilan ya ji abinda ke faruwa ne, da kyar dai ta lallaba ta mike ta cire Hijab din jikinta ta dau wankakke dake a linke ta saka, sanyi take ji sosai don xaxxabi ne jikinta, ta fito dakin ta sa takalminta tana tafiya kamar iska xai kadeta ta fito kofar gidan, babu haske sosai wajen hakan yasa ta dinga kallon mutumin dake tsaye da fararen kaya ya juya baya, gani tayi ba Usman bane don wnn yafi Usman tsayi, ta bi layin da kallo tana kara tsoron kada Hansai ta dawo ta tarda ita a waje bayan an yi mata iyaka da wajen daga daxu da yamma, da kyar tace "Wa kake nema?" Sai a snn ya juyo ya sauke mask din fuskarsa yana kallonta, ta xaro ido tsoronta ya tsananta, haka xaxxabinta ma taji yana neman fin na da, don sanyi sosai ya dinga shigarta, kallonta ya shiga yi daga sama har kasa, rasa abin cewa tayi daga karshe ta jingina da bangon gidan, still looking at her yace "Baki da lafiya ne?" Ta gyada masa kai, lkci daya hawaye ya kawo idonta, bin layin ya sake yi da kallo, can yace "Baki sha magani ba?" Hawayen dake makale idonta ya silalo kasa ta girgixa masa kai tace "Babu maganin" yace "Ke da waye a cikin gidan?" Tace "Ni kadai ce, Baabarmu ta fita yanxu" Shiru yyi kamar me naxari sai kuma ya kalli inda motarsa yake yace "Akwai asibiti a nan anguwar?" Ta gyada masa kai tana nuna masa tace "A layin can gaba" Yace "Mu je" Da mamaki take kallonsa tace "Ina?" Ya wani hade rai yace "Mu tafi can din nace" ta marairaice cikin rawar murya tace "Baabarmu tace idan na sake fitowa ko nan bakin kofa sai ta kasheni wllh" Shiru yyi na few seconds kafin yace "Saboda me?" Tana share hawayen da ya ki tsaya mata tace "An sa min rana" Daga sama har kasa ya sake kallonta snn yace "Da wa?" Ta fashe da kuka tace "Da iliya" tana fadin haka kamar an tunxurata ta dinga rera kuka, yace "Ohk, amma bai san baki da lafiya bane bai kawo maki magani ba" Bata basa amsa ba sai kukan da take yi sosai, yace "Mu je" ganin ta ki motsawa ya daure fuska sosai yace "Ke kinsan daga inda nake?" Ta shiga goge idonta bata ce komai ba, yace "Mu tafi nace" A hankali ta fara goge idonta, ganin ya fara tafiya ta bi bayansa gabanta na faduwa tana waige waige har suka kusa bakin titi ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta don duk maxaunin bakin titin nan babu wanda bai santa ba, ya bude mata back seat, xuciyarta ya dinga bugawa da karfi ta tsaya tana kallonsa, ya sauke nose mask dinsa yace "Kina 6ata min lkci" A hankali tace "Baabarmu xata....." Wani kallo yyi mata yace "Nace ki shiga malama" shiga motar tayi a tsorace, ya rufe sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar, sai da ya hau saman titi yace "Ina asibitin yake?" Layi uku dake gaba da nasu ta nuna masa ya shiga layin suna isa yaga irin asibitin yyi parking yana kare ma wajen kallo, kafin yace "Nan din ne asibitin?" Kai kawai ta gyada masa, ya ja tsaki ya tada motarsa yayi reverse ya bar wajen, ta dinga kallonsa gabanta na faduwa, wani asibiti a cikin gari ya kai ta, yana parking haraban asibitin ba tare da ya juya gareta ba yace "Sauka" kalle kallen motar ta dinga yi alamar bata ma san ta ina xata bude ba, ya sauka ya xagayo ya bude motar, sauka tayi ya rufe motarsa, ganin yanda ta tsaya ya dake yace "Mu je" he sounds so pissed off, Ba musu ta bi bayansa har cikin asibitin, nan take ya yankar mata kati, ba a dau lkci ba nurse din ta sanar masa xa su iya shiga gun likita, yana daga xaune ya nuna mata office din likitan yace ta shiga ta gaya masa duk abinda ke damunta, Jiddah ta mike gabanta na faduwa tana kallonsa a hankali tace "Ai tsoro nake ji" ya hade rai a d'an tsawace yace "Tsoron likitan sbda xai cinye ki?" Sunkuyar da kanta tayi, yace "Juya ki shiga" a hankali ta juya ta nufi office din likitan da ya nuna mata, kamar me tsoron kofar ta murda ta shiga, sai a sannan ya mike ya bi bayanta xuwa cikin office din, tana xaune ta takure waje daya likitan na cewa ta kwantar da hankalinta ta nutsu, ganin ya shigo sai taji hankalinta ya kwanta, ya ja kujera ya xauna suka gaisa da likitan, likitan na kallonta yace "Me ke damun ki?" Cikin sanyin murya tace "Kai na ke min ciwo, ina jin xaxxabi, kuma ina ganin jiri...." Mikewa yayi ya dawo kusa da ita yana duba idonta da wani d'an abu kamar fitila a hannunsa, Abuturrab dai na xaune yana dubansu har likitan ya gama gwaje gwajensa snn ya koma ya xauna yana kallon Abuturrab yace "Xa ayi mata test, though symptoms din na malaria ne, but it's good ayi test din sannan kuma .... Is she ur sister?" Abuturrab ya d'an kalleta sannan a hankali yace "Yea" Likitan yace "Me ke damunta haka, yar yarinya da ita na ga Bp dinta ya hau" sake kallonta Abuturrab yyi, likitan na kallonta yace "Kina da damuwa ne 'yan mata, idan ma baxa ki gaya ma d'an uwanki ba ni ki gaya min" Sunkuyar da kanta tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta, Abuturrab yace "Dont worry Dr i will talk to her about that, ynxu dai idan ba damuwa kawai a hada mata drugs if there is need for injection ayi mata ba sai an yi mata test din ba cos i guess it will take up to 40mins kafin result din ya fito mu kuma a kan hanya muke" Likitan yace "Toh shkkn babu damuwa" daga haka ya fara rubuce rubuce yana gamawa ya mika ma Abuturrab ya amsa snn ya mike yyi masa godiya, ganin har sannan bata mike ba yace "Mu je" Mikewa tayi yana gaba tana biye da shi har suka fita office din, wajen bada allura Abuturrab ya ga abinda bai ta6a gani ba, don kememe taki yarda ta dinga rusa masu kuka a asibitin tana rokansu, hakan yasa ya koma office din likitan yasa ya rubuta magunguna kawai gaba daya ya biya bill din sannan suka fita asibitin, har sannan shesshekan kuka take, ya bude front seat ya hade rai yana kallonta a hankali ta shiga ya kulle sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver, sai da suka fita asibitin yace "Kin ci abinci?" Girgixa masa kai tayi tace "Baabarmu ta ba almajiri nawa" Ya dinga nanata sunan da ta kira a ransa, wai Baabarta, girgixa kai yyi cikin ransa still yace ba dai baabarki ba, gidan wani cin abinci ya tsaya ya siya mata abinci sai malt guda biyu da bottle water, yana shigowa motar ya ajiye mata, kallon ledan ta dinga yi, can ta bude ta ciro malts din ta ajiye gefe tace "Ban iya sha ba" Yace "Sai me?" Tayi shiru bata ce komai ba, yace "Tambayarki nake" a hankali tace "Ban iya shan lemo ba ni" Bai kuma ce mata komai ba, sai da suka shigo titin hayi yace "Taron me naga aka yi a layinku daxu da yamma?" Shiru tayi sai kuma ta kallesa a hankali tace "Baabarmu ce take dukana" Da mamaki yace "Saboda me?" Ta share hawayen da ya kawo idonta tace "Dama Iyah ce tace xata sa ni a motar tirela in gudu legas don kar a min aure da Iliya, shine sai na gaya ma wata kawata da muke xuwa makarantar dare tare da ita da, don gobe Iyah tace xata kai ni tasha, sai kawata taje ta gaya ma baabarta shine baabarta ta xo ta gaya ma Baabarmu, shine Baabarmu ta dinga dukana wai xata kasheni, duk aka taru a layin...." Tana kai wa nan ta fashe da kuka, Shi dai sauraronta kawai yake yi, bayan few seconds yace "Wacece Ita warce tace xata sa ki mota ki tafi lagos?" Cikin rawar murya tace "Wata tsohuwa ce a layinmu ana ce mata Iyah...." Ya kalleta yace "Har yanxu xa ki tafi lagos din kenan don kar a maki auren?" Ta girgixa masa kai hawaye na sauka idonta tace "Aa baxan je ba amma xan kashe kai na" Bai ta6a expecting jin hakan daga bakinta ba, yyi parking yana kallonta da mamaki yace "Xa ki kashe kanki?" Ta gyada masa kai, yace "Da me xaki kashe kan naki?" Cikin rawar murya tace "Piya piya xan siya in sha" Bai san lkcn da ya bude baki ba yana kallonta ganin she is so damn serious, da wani expression yake kallonta ganin she is truly depressed and frustrated, tana goge hawayen dake xuba idonta tace "Dama ae Abbana ma ya tafi ya bar ni, ba sai in bi sa ba" ya kwantar da murya yace "Amma kina xuwa islamiyya kuwa?" Ta girgixa masa kai a hankali tace "Na daina tun da dadewa, tun sanda muka fara sana'a" Yace "Toh saboda xa a maki aure kike son kashe kanki?" Ta gyada masa kai, sai kuma ta hade kanta da gwiwa ta fashe da matsanancin kuka tace "Shaye shaye fa iliya ke yi, kuma har kwaya yana sha shine Babarmu take son in auresa...." Kallonta kawai yake, can yace "To wa kika ta6a ganin ya kashe kansa sbda xa ayi masa aure da wanda baya so?" Tana shessheka tace "Akwai wata ma ai ta kashe kanta a nan hayi" yace "Shine ke ma xaki kashe kanki?" Ta gyada masa kai, yace "Toh duk sanda kika shirya ki min magana ni da kaina xan kawo maki piya piyan, kin ji ni?" Ta dago tana kallonsa tace "Toh ai ni na shirya" yace "Yaushe?" Da kyar tace "Yau da daddare nake son in sha" yace "Aa kinga ni sai yau na sani, ki bari ko xuwa jibi xan kawo maki" tana shessheka sae kuma ta sakar masa kuka tace "Yayi min nisa" Yace "Ya sunanki?" Tana kallonsa da hawaye idanuwanta tace "Jiddah" Ya d'an yi shiru, bayan few seconds yace "Jiddah.... shekaranki nawa??" Cikin sanyin murya tace "Babaarmu tace sha bakwai" yace "Toh ki jira sai na kawo maki da kaina, kar ki kuskura ki siya da kanki, kin ji me nace maki?" Ta gyada masa kai kawai, yace "Ki yi min alkawari xa ki jirani" Tace "Nayi" yace "Kina komawa gida ynxu ki ci abinci ki sha maganin ki ai nurse din ta nuna maki ynda xa ki sha" Ta gyada masa kai, tada motar yyi ya ci gaba da driving dinsa gaba daya yana kara naxarin xancenta.



07087865788✍🏻

💖💖 *Jiddatul Khair*💖💖





_By Khaleesat Haiydar_✍🏻







6.....


Suna kusa layinsu cikin sanyin murya tace "Toh me xan ce ma Baabarmu idan ta dawo, wllh har dukana xata yi" Bai ce komai ba yyi parking d'an nesa da layin snn ya d'an kalleta yace "Amma ba Baabar da ta haife ki ba ko..." Ta girgixa masa kai a hankali tace "Abbana yace ita ta rasu tun ina yar karama" ganin hawaye idonta ya dauke kai bayan few seconds yace "Allah ya gafarta mata" Ta sunkuyar da kanta ta amsa da Ameen, yace "Sai kice mata saurayin da xaki aura ne ya xo kika fito" Ta marairaice tace "Ai yana legas bai dawo ba" Yace "Kwanaki da na baki kudi ki bata don kar ki sake fitowa bakin titi, kin sake fitowa?" Ta girgixa kai tace "Aa bamu sake yin awaran ba sai shekaranjiya ta fara" bai ce komai ba ya tada motarsa ganin ya fara tafiya ta kallesa da sauri tace "Ina kuma xaka kai ni?" Bai bata amsa ba ganin wani shago da ake cire kudi ta Pos ya tsaya sannan ya sauka motar, without taking much time ya dawo ya shiga motar.... Dai dai layin nasu ya sake parking ya ciro kudi a aljihu yace "Gashi ki kai mata yanxu ma" Kallon kudin ta dinga yi, sannan ta kallesa tace "Ince wa?" Yace "Kice wani ya bata" Amsan kudin tayi gabanta na faduwa, yace "Me nace kiyi idan kin koma gida yanxu?" tace "Kace in bata wai in ji wani" Yace "Kafin wannan" Ta d'an yi shiru sannan tace "Kace in ci abinci in sha magani" Ya d'an daure fuska yace "To sauka" yana fadin haka ya bude mata motar ba tare da ya yarda ya ta6a ta ba, ta sauka, yace "Kulle min mota" Ba musu tayi yanda yace sannan yayi wucewarsa without looking at her, sai a sannan bugun xuciyarta ya tsananta, ta fara tafiya a hankali xuwa cikin layinsu, ta fi minti biyu bakin xaurensu ta kasa shiga, daga karshe ta kutsa kai ciki, tuni hawaye ya fara sauka idonta tana jiran jin saukan duka, sai dai me... Har sannan Hansai bata dawo ba balle Bibalo, gidan babu kowa, dakinsu ta shiga duk da akwai wutan nepa amma kamar ko da yaushe wutan is very low, xaunawa tayi ta ajiye ledan hannunta sannan ta boye kudin cikin ghana must go dinta, a hankali ta bude take away din abincin ta ga shinkafa da katon kaza, ta xaro ido, ita yaushe rabon da ta ci shinkafa balle wata kaza, shinkafa sai suyi kusan sati uku ma basu ci ba daga tuwon masara sai taliya 'yar Hausa ko garin rogo, Kaza kuma dama ranan sllh ne kadai Hansai ke bata kai da kafafuwan ko kuma wuya, yau kuma ga kaza kato a gabanta har da shinkafa, kasa cin abincin tayi tana ta kallonsa, tunawa da tayi Hansai na iya dawowa yanxu ko Bibalo yasa ta xaro ido, a hankali ta fara cin abincin, sbda a tsorace take ta kasa nutsuwa ta ci abincin, ta dai ci wanda xata iya ci, jin almajiri na bara ta mike da sauri ta fita da abincin da ta kunshe a ledansa ta mika ma almajirin ta dawo ciki, ta fi minti daya tana kallon magungunan, kafin ta fito da su tana kallo, ganinsu kadai taji xuciyarta ya fara tashi ta mayar da su da sauri ta cusa a ghana must go, duk ciwon da xata yi bata shan ko d'an paracetamol da Abbanta ke siyo mata lkcn da yake da rai, Hansai kuma ko kasheta ciwo xai yi bata ta6a cewa ta sha magani, muryar Bibalo ta ji tana kiran Uwarta tun daga bakin Zaure hakan yasa ta boye goran ruwan da ta sha ta rage, snn ta kwanta ta rufe idonta. Washegari da asuba jiddah ta kasa tashi kamar yanda ta saba, duk karfe biyar dama take tashi ta fita ta debo ruwa a borehole ta cika jarkunan tsakar gidan da ma bokiti, ganin gari ya fara haske Hansai ta leko dakin tace "Yau naga walakanci, Jiddah kece kwance har yanxu baki fito ba, uban wa xai debo ruwan yau? Bibalo me ciwon kirji ko ni xan fita debo ruwan?" Bibalo dake kwance tana bacci ta gyara kwanciyarta hade da rufe har fuskarta da xanin gadonsu, Jiddah ta dago da kyar muryata na rawa tace "Baabarmu kaina ke min ciwo sosai, idan na tashi juwa nake gani" Hansai tace "To a rayuwar nan yanxu waye baya fama da ciwon kai, ko digon ruwan alwala fa babu a gidan nan, ni kike son in fita in debo ko Bibalo da ba cikakkiyar lafiya gareta ba" Jiddah dai bata ce komai ba, Hansai tace "Ai ko daurewa xa ki yi ki mike ki debo ko bokiti uku ne, gida idan babu ruwa ai ba magana" Daga haka ta juya ta fita tana cewa "Idan ma xaki rufa ka kanki asiri ga bishiyar gwanda da mangwara can ki tsinko ganyayyekin su ki hura icce ki dafa ki sha kiyi wanka don sile na baxanyi amfani da shi wajen siyo maki magani ba" Da kyar jiddah ta mike tana dafa bango ta fita, ta dau bokiti, d'an makotansu ne ya taimaka ya kawo mata ruwan har kai uku gidan, ta dawo da kyar ko tafiyan bata iyawa ta shige daki ta kwanta ko ina na jikinta na mata ciwo... Har karfe goma na safe tana kwance, Hansai ta shigo dakin cike da masifa sosai tace "Ke ni fa babu ruwana ki tashi kiyi ta kanki ki tsinko abinda nace ki dafa uban waye xaki daura ma wahala bayan na ciyar da ke da nake yi" Jiddah ta mike ko ina na jikinta na rawa sbda sanyi, tace "Xan yi" tana magana ta jawo ghana must go dinta ta fiddo kudin jiya ta mika ma Hansai tace "Jiya wani ya kawo wai a baki" Hansai ta xaro ido tana kallon kudin ta karba tace "wani kuma? A ina kika gansa?" Tace "Aikawa yayi in xo, ina xuwa yace in baki" Hansai ta xauna gefen gado ta fashe da kuka tace "Amma gaskiya isuhu ya tare mana abubuwa da yawa a duniyar nan sanda yake raye, to da ya baki sai yace me??" Jiddah ta koma ta kwanta tana fidda numfashi da kyar tace "Cewa yyi in baki kawai" Shiru Hansai tayi tana kirga kudin har ta gama taga dubu talatin cif, ta kalli Jiddah da sauri tace "Ko dai mutumin da ya ta6a baki kwanaki ki kawo min kada mu fito sana'a?" Jiddah ta gyada mata kai, Hansai tace "Toh don girman Allah duk ranan da ya sake dawowa kice masa ya shigo in masa godiya" Jiddah bata iya ta bata amsa ba, Hansai ta mike murna fal cikinta tana murmushi ta nufi kofa tana cewa "In dai haka ne duk wani nawa amma banda Bibalo ya mutu a duniyar nan mana, daga mutuwa sai billowan alkhairi ta ko ina? Ashe dama akwai sauran mutanen kirki a duniya ban sani ba" Jiddah ta bi ta da kallo hawaye me xafi na sauka idonta. 


Ummi na kallon Abuturrab tace "Ina kuma xaka da yamman nan kana ganin hadari?" Yace "Aa ni ba nisa xan yi ba, nan governor road xan je" tace "Ahmad din har ya tafi ne?" Yace "Aa tare xa mu fita da shi amma xai dawo" Tace "Toh Allah ya tsare, ka siyo min tsire while coming back" Yace "Alright, in sha Allah" Daga haka ya fita dakin nata ya dawo main parlor, Ahmad na xaune yana jiran sa, Ganinsa ya mike ya nufi kofa, bin bayansa Abuturrab yyi wayarsa ya fara ring, dubawa yyi yaga Aunty ke kiransa, ya daga ya kai kunne, wara ido yyi yace "Aunty yanxu ai xan dawo..." Murmushi yyi yana kallon wayar don har ta katse, juyawa yyi ya koma bangare Stepmum din tasa, Ahmad ya ta6e baki, a parlonta ya sameta, yace "Ba nisa fa xanyi Aunty" ta hade rai tace "Shine ni  baxa ka min sallama ba amma ai naga ka shiga gun uwarka?" Yace "Toh kiyi hakuri" Yana fadin haka ya jefa ma stepsis dinsa dake xaune parlon wani kallo sanin ita xata gaya mata, Aunty tace "Toh me Ummin tace maka da ta kira ka?" Yace "Nothing kawai tace in taho mata da tsire while coming back" Tace "Toh nima ka taho min da tsiren" yyi murmushi yace "Toh" Daga haka yace "Sai na dawo" ya fita dakin. Yana driving ya d'an kalli Ahmad dake danna wayarsa yace "A ina xaka sauka?" Ahmad ya kallesa yace "Kai ina xa ka???" Abuturrab yace "Bakin ruwa, nan by pass" Da mamaki Ahmad yace "Me zaka je yi a bakin ruwa Captain?" Ya gyara xama yace "Xan amshi sako gun wani frnd dina ne, he is coming from Abuja kuma kano xai wuce, so yace min ya shigo kd yanxu mu hadu by pass in amshi sakon" Ahmad yace "Ohk, drop me home" Abuturrab ya nufi gidansu yyi parking bakin gate, Ahmad ya sauka yace "Sunday din xaka tafi kano?" Abuturrab yace "In sha Allah" Ahmad yace "Alright... Sai da safe" Daga haka ya shiga ciki, Abuturrab yayi reverse ya bar layin. Abuturrab ya fi minti goma tsaye a kan hanya bayan ya iso bakin ruwa, jinginar da kansa yyi jikin kujeran da yake xaune yana tunanin wanda ya sani wanda bai yi aure ba that he can do anything possible to see him married to this girl that is ready and wanting to kill her self, driver din Abbansa ko wata uku ba ayi da yyi aure ba, who again? Wani senior cleaner ne a Airport din kano ya fado masa, Guy din na da hankali... a Diploma holder, ga shi da mutunta mutane, Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya ganin ya kusa samun solution, and he will try all possible means sai Mu'axxam ya auri yarinyar nan, wani ajiyar xuciyar ya sake saukewa na relieve, driving ya ci gaba da yi, yana isa u-turn ya dau hanyar Hayi, kamar ko da yaushe parking yyi a bakin layin yana kallon cikin layin, nose mask dinsa ya saka da glasses din ido sannan ya sauka motar ya fara tafiya, calmly yake tafiyar har ya isa kofar gidan, wani yaro ya tura ya kira masa jiddah cikin gidan, Hansai na xaune tsakar gida tana cin shinkafa da wake da mai da yaji da salak wanda rabon da su ci shinkafar tun rasuwan Mai gidan nata, tana kallon yaron tace "Lawali daga ina haka?" Yace "Wani ke kiran jiddah a waje" Hansai tace "Jiddah kuma?" Jiddah dake kwance xaxxabi ya ci karfinta ta bude jajayen idanuwanta da sauri gabanta yyi wani mugun faduwa ta mike xaune, Hansai ta kakkabe guntun shinkafar hannunta a samiran cinyarta tace "Waye shi? Kuma daga ina?" Yaron yace "Wani dogo ne ya sa gilashi da takunkumi a hanci, ya sa fararen kaya" Hansai ta mike da sauri tana leka dakinsu Jiddah tace "Ke tashi, kaddai me kawo min kudin nan ne?" Jiddah ta mike tsaye da kyar jikinta na rawa tace "Ban sani ba" Hansai tace "To ai kuwa daurewa xa kiyi ki tashi ki saka hijabi ki fita ki ga waye, kika sani ko shi din ne wani kudin ya kawo yau ma" Kasa ci gaba da tsayuwa tayi duk ynda ta so yin hakan, Hansai tace "Yau naga tsiya, baxa ki daure ki tashi ba kamar ba mace ba Jiddah??" Jiddah ta dafa gadon ta kara daurewa ta tashi, Hansai ta warware Hijab dinta dake ajiye a linke kan jaka ta mika mata tace "Sa ki fita maxa maxa ki ga waye" da kanta ta sa mata hijab din, jiddah ta fita dakin, Hansai ta xauna gefen gado tana addu'an Allah ya sa shi din ne, kuma wani kudin xai bada yau ma, jiddah na fita kofar gidan ya juyo yana kallonta, durkusawa tayi nan kasa ta kasa ci gaba da tsayuwa, ya dinga mata wani kallo yace "Jikin bai maki sauki ba?"  hawaye ya shiga sauka idonta, kana ganinta kasan tana jin jiki, yace "Kin sha magungunan nan kuwa?" Kin cewa komai tayi, Ya hade rai da d'an tsawa yace "Tambayar ki nake" Ta fashe da kuka a hankali ta kara jingina da bango tace "Ni amai xanyi idan na sha" Da mamaki ya dinga kallonta, Hansai dai na ta tsaye tsakar gida tana jiran ganin shigowar jiddah, jin shiru shiru ta nufo xauren cikin sanda tana leko waje, hada ido suka yi da Abuturrab, ta sunkuyar da kanta da sauri tana d'an kame kame tace "Sannu da xuwa Alhaji.... Ae da ta fito maka da tabarma ko" kallonta kawai Abuturrab ke yi daga sama har kasa, can yace "ina wuni" Hansai ta rutsuna tace "Lafiya lau Alhaji, sannu da xuwa, ko xaka shigo daga ciki...." Yana kallon jiddah yace "Ya mai jikin?" Hansai ta marairaice tace "Wllh da sauki kenan xa a ce, kuma fa ta sha magunguna amma shiru har yanxu" yace "Toh bari mu je asibiti" Hansai tace "Kai Alhaji da dai a je chemist kar hidiman yyi yawa, ga chemist can bayan mu" yace "Aa xa a je asibitin kawai" Hansai tace "Toh shkkn Alhaji, daure ki tashi Jiddan Mama, sannu... Ga dai ana shan maganin kamar ba a sha" tana fadin haka ta dagota, Abuturrab na kallon Hansai yace "Motata na bakin titi" Hansai ta kwance dankwalin kanta ta rufe jikinta da shi tace "Toh bari mu je can din" tana rike da jiddah suka isa bakin titin ya bude back seat ta saka jiddah ciki, mutanen layin sae kallonsu suke, Abuturrab na kallonta yace "Ina 'yar uwarta mu tafi tare" Hansai tace "Au wai Bibalo, ai kuwa bata anguwar nan yanxu haka, ko in shiga mu je ni?" Ya kalleta daga sama har kasa sannan yace "Yanxu xa mu dawo in sha Allah, ba sai kin je ba" tace "Atoh dama ae bai ma kamata in bi ku ba, toh Allah ya kiyaye Alhaji, a dawo lafiya" xagawa yyi ya shiga driver seat ya tada motar ya bar wajen Hansai sai washe baki take tana daga masa hannu, sai kuma ta hade rai tana kallon 'yan layin da suka xuba mata ido da kallo tace "To wai lafiya wannan shegen kallo haka??" Tsaki ta ja ta juya ta fara wucewa tana cewa "Jama'ah baxa su ji da talaucin da yyi masu katutu ba sai shegen sa ido da neman abun fade, to d'an uwanmu ne daga Habuja sai kowa yyi ta kansa haka kuma" Abuturrab na hawan saman titi ya kalli Jiddah ta madubi yace "Wato baki sha maganin jiya ba??" Shiru tayi bata ce komai ba, ya hade rai yace "Ki bude baki kiyi min magana ina tambayarki" kai kawai ta gyada masa, yace "Me yasa baki sha ba?" Kamar xata yi kuka tace "Nace maka amai xan yi idan na sha" Yace "To xa mu je su maki alluran yanxu ai" Ta mike xaune da kyar tace "Aa ni bana son allura" Wani kallo ya wurga mata, tayi shiru bata sake cewa komai ba.... Sai kusan karfe taran dare Abuturrab ya dawo da ita bakin layin nasu, yau ma da ledan take away din abincin da ya siya mata, ya sauko motar ya xaga ya bude mata side din da take xaune, da kyar ta sauko motar da wasu ledan magungunan daban da aka kara bata a asibitin da ledan abinci, ya rufe motarsa, har ya xaga xai shiga maxaunin driver ya sa hannu aljihu ya ciro dubu goma ya dawo ya bata yace "Sai ki ba Baabar taku" daga haka ya shiga motar yayi wucewarsa, da kyar ta dinga jan kafa har ta isa gida, Hansai na xaune da Bibalo dake cin abinci, ganin ta shigo Hansai ta mike a xabure tace "Me ya baki?" Jiddah ta mika mata duk ledojin hannunta da kudin sannan ta xauna nan bakin kofa ta jingina da bango kanta na juya mata, Hansai ta kirga kudin ganin dubu goma ne tace "Toh ya baxai bani dubu goma ba bayan kudi ya kare a shegun magungunanki, munafuka kawai, ciwo kalilan duk ta bi ta langwabe ma mutane kamar kyanwa, kuma da ganin asibitin me tsada xai kai ki, to Allah ya isa wllh...." Kallonta kawai Jiddah ke yi, Hansai ta ja tsaki ta shiga fiddo magungunan a fusace tana kyabe baki, can ta watsa mata su tace "Abun takaicin ma asaran kudinsa kawai yyi, ke din ce xaki sha ma mutane magani" watsa mata ledan magungunan tayi gaba daya sannan ta bude dayan ledan ganin shinkafa da dunkulelen kaza ta murmusa tace "Allah sarki bawan Allah" Tuni Bibalo ta tura kwanon gabanta ta dawo kusa da uwarta, Hansai tace "Toh bai saka da lemo ba sai ruwan gora?" Jiddah dai bata ce komai ba, Hansai da Bibalo suka shiga cin abincin kamar mayunwata, sai da suka kusa cinyewa ta kallo jiddah tace "Au, to ai ba mu sam mata ba" kwanon abincin da Bibalo ke ci ta jawo, tana kallon guntun shinkafar da Bibala ta rage ta debi na take away din loma biyu ta yarfa a kai, sannan ta dau tsoka me K'ashi, sai da ta ta66atar ta kwaye tsokan sannan ta saka k'ashin a kwanon ta tura ma Jiddah tace "Gashi kema" Jiddah dai bata ce komai ba, suka cinye nama da abincin tass sannan Hansai ta maka uban gyatsa ta mike ta shige daki tana cewa "Bibalo ke da yar yabi sai ku bibbi gobe ku kai cingam da sweet din sa ranan da aka yi, har yau ba a ba jama'a ba" Bibalo ta mike ta bi bayan uwarta tana cewa "Yo ai cingam din kwali daya ya rage..." Jiddah ta jingina da bango hawaye ya kawo idonta a hankali tace "Kuma bai kawo min piya piyan ba" Washegari lahadi Abuturrab ya fito gida misalin karfe sha daya na safe, Waya ne kare kunnensa yana driving a hankali don bai fita layinsu ba, girgixa kai yyi yace "No kai dai ka samu adaidaita ni na riga da na fito da mota, sai ka fadi inda xan sameka" Murmushi yayi bayan few seconds yace "Okay then, tunda kasan hospital din ba sai ka tafi ba" Yana fadin haka ya katse wayar hannunsa. Dai dai inda suka yi xai dau Ahmad yyi parking yana jiransa, bayan kusan minti goma Ahmad ya iso wajen da adaidaita ya shiga motar yana kallon Abuturrab yace "Amma ba yau xaka bar kaduna ba Captain" Abuturrab yace "probably.... Akwai abinda xan yi yau din" Ahmad yace "Ni train xan bi in sha Allah yau xan koma Abuja..." Abuturrab bai ce komai ba har suka isa wani hospital domin duba wani frnd dinsu da aka yi admitting, fruits iri iri suka siya masa a hanyarsu ta xuwa wajen, suna shiga ward din da yake suka tarar da abokansu hudu su ma sun xo dubiya, bayan an gaisa, wani frnd dinsu Umar na kallon Abuturrab cike da tsokana yace "Captain ko dai a hayin rigasa kake gini ne? Or probably neman aure...." Da mamaki Abuturrab ke kallonsa har ma da sauran abokansu, Ahmad yayi dariya yace "Haka yace maka Umar?" Umar ya gyara xamansa yace "To for the past 4 days kullum sai na ga motarsa a hayi" Abuturrab ya xaro ido yace "Ni kuwa?" Umar yace "Kai mana, yawanci kana ta daya side din nake ganinka, kai akwai ranan da ma na kiraka ina jin ka bar wayar a mota and u didn't even follow my miss call" Abuturrab yace "Subhanallah on a serious note ban lura ba...." Umar yace "To airport xa a bude mana a hayi ne kullum muke ganin Captain a can" Murmushin yake kawai Abuturrab yyi yana kallon Nasir dake kwance da drip a hannunsa yace "Barrister guda a gadon hospital, so how are u feeling now?" Nasir ya jefa masa wani kallo yace "Kai ma baka wuce a kwantar da kai gadon asibitin ba ai" Dariya kawai Abuturrab yyi, sun fi minti ashirin a dakin suna labarin duniya, daga karshe Ahmad ya sanar masu xa su koma bayan sun ma Nasir addu'an samun lfya, a tare suka fito da Umar daga ward din don shi ma wucewa xai yi, Abuturrab ya d'an kalli Ahmad dake bayansa suna magana da wani abokinsu da ya fito rakasu, ya kalli Umar da har ya kusa fita reception din hospital, ya kara pace dinsa har ya isa gunsa yace "Kai me kake xuwa yi hayi har kake ganina?" Umar yyi murmushi yace "A can fa Mahaifiyata take, so kusan kullum nakan je can din" Abuturrab yace "Ohhh Allah sarki..." Umar yace "To kai wajen wa kake xuwa?" Abuturrab ya d'an shafa kansa ya saci kallon Ahmad dake tahowa yace "Aboki nayi nima a can din" daga haka ya fiddo wayarsa ya d'an yi gaba kamar xai yi answering call don bai son Umar ya ci gaba da maganan gaban Ahmad. Abuturrab yana kallon Ahmad bayan sun hau saman titi yace "Gida xan sauke ka?" Ahmad yace "Yeah..." Driving kawai Abuturrab ke yi, Ahmad dake kallonsa yace "Wajen wa kake xuwa a hayi Captain?" Abuturrab ya kallesa da sauri cos the question came unexpected, ya dake yace "Ka yarda da Umar kenan, he was just pulling my leg idan ba dai a train station ba ya gan ni wa gareni a hayi da xanje? Wa na sani a hayi? Kawai dai idan mun hadu dole sai ya tsokane ni ne..." Ahmad na gyara xama yace "To na sani ko budurwa kayi a can baka sanar min ba kake boye min, ai idan tayi tsami ma ji" Wani kallo Abuturrab ya jefa masa yace "In rasa inda xanyi budurwa sai anguwar nan???" Ahmad na kallonsa da mamaki yace "Meye da su 'yan anguwan, ba mutane bane su din? Or sai da aka halicceka specially sannan aka halicce su aka ce maka? What's wrong with u Abuturrab? Why do u sometimes behave like...." Abuturrab yace "Illiterate right?" Ahmad yace "Of course" Abuturrab yace "Fine, but do not forget everyone is entitled to his or her opinion, ra'ayinka daban ra'ayina daban, kai xaka iya budurwa a can infact har ma ka aureta ku xauna a can din, it's ur opinion, ni kuma last thing da baxanyi ba kenan a rayuwata, and this is my opinion, so stay entitled to urs, and i stay entitle to mine also" Ahmad yace "Baxa ka iya aure a can ba sbda kafi su a wajen Allah ko??" Abuturrab yyi masa wani shegen kallo yace "Wai Ahmad ance maka ni kai ne?? Ni fa ina da class ina da taste, as in i am far beyond that ka daina yi min irin wannan maganan bana so wllh" Ahmad yyi d'an murmushi bai kuma ce masa komai ba, Abuturrab yyi tsaki yace "Haka kawai sai kace kowa sai ya bi ra'ayinka, kai mace ko min kazantarta da locality dinta xaka iya aurenta ku xauna lafiya, ni kuwa it's a big No for me, bana walakanta 'yan adam kai shaida ne, sannan kasan ko kai baka kaini tausayin d'an Adam ba, idan naga mutum na cikin damuwa ko wani yanayi more especially mace ina bakin kokarin ganin nayi duk abinda xan iya yi ko a ina ne kuwa, even with my last card i can help, amma sai ka dinga hadani da su kana wasu maganganu marasu ma'ana" Ahmad bai kuma ce masa komai ba har suka iso gidansu, Abuturrab yyi parking, Ahmad ya juya yana kallonsa still bai ce komai ba ya bude motar ya sauka ya rufe masa motarsa, tsaki Abuturrab yyi, yyi reverse ya bar layin kallon agogonsa dake nuna masa sha biyu da rabi yyi ya nufi gida kawai....



07087865788....✍🏻 Almost done with free pages

💖💖 *Jiddatul Khair*💖💖





_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻






7.....


Fitowa Hansai tayi tsakar gida jin ana sallama, ganin aminyarta Zulai ta ce "Aa ashe Zulai ce, shigo daga ciki mana" Zulai tace "Ina ta addu'ar Allah ya sa in sameki wllh" Hansai tayi dariya tace "Ai ko kin ci sa'a, don yanxu haka shiri nake xan fita kasuwar tasha in saro kayan sana'ata" Zulai ta rike ha6a tace "Kin fara wani sana'ar ne banda awara?" Hansai tayi shewa tace "Ai ni na kwan biyu ma banyi awarar ba, amma kilan idan na fita yau dai in siyo har da waken suyan, yanxu su maggi, kubewa, kuka, daddawa... Kai duk dai mahadin miya da kika sani nake siyarwa, ko kwana hudu ban yi da farawa ba, sannan ina sa ran fara dillalanci kwanan nan" Zulai dake ta kallonta tace "Ikon Allahhh..." Hansai ta shiga d'an dakinta tana murmushi, Zulai na biye da ita a baya, bayan sun xauna Zulai tace "To ina yaran?" Hansai tace "Bibalo yanxun nan ta shiga makota, Ita kuma warcan gantalalliyar na can kwance wai ba lafiya" Zulai tace "To Hansai wani labari dai nake ji a gari, shine nace bari dai in sa6o gyale in taho..." Hansai ta gyara xama tana kallonta tace "Me ke faruwa? Wani labarin kika ji?" Zulai tayi kasa da murya tace "Yawo ake da ke wai bayan an kawo gaisuwan wannan yarinya jiddah har an saka rana kina turata gun wani me katuwar mota kullum sai ya xo kofar gidan nan, meye gaskiyan lamarin nan?" Hansai ta saki salati tana tafe hannu tayi mici mici da ido tace "Amma dai Allah ya tsine ma duk wani me sa ido a duniya, da yaushe da yaushe na turata gun me mota? Yau naga lalacewa, Jiya ne fa bata da lafiya shine ya siyo mata magunguna, kai ni Hansatu jama'a basu da gadonka amma suna da gadon maganarka..." Zulai tace "To waye shi me motar ma dai tukun" Hansai na huci ta lafto wani uban ashar tace "Duk wanda ya fasa sa min ido bai haifu cikin uwarsa ba a garin nan, tunda isuhu ya rasuwa wani shege ne ya ta6a kawo min kwayar masara balle shinkafa ko man kulli yace gashi ki ci kanki Hansai?? kawai sai don bawan Allah ya ga muna cikin matsatsi da yanayin rayuwa yana xuwa yana taimaka mana domin Allah sai a sa mana ido a hau mana bakin ciki da hassada a anguwa? Ni wllh ji nake kamar in siyar da gidan nan in bar gantalallen anguwar nan ko xan samu ci gaba" Zulai tace "Ke ni duk ba wannan ba tsoho ne mutumin nan ko yaro?" Hansai ta ja tsaki tana gyara xama tana huci tace "D'an yaro ne fa Zulai, ina jin ma saurayi ne bai ta6a aure ba, baki gansa ba bawan Allah wllh...." Zulai tace "Gun jiddar yake xuwa?" Hansai ta kalleta da sauri tace "Waye kuma jiddah? ita a wa xai xo wajenta? kema dai da wani xance wllh, xuwa fa yake idan yaga tana tuyar awara bakin titi ya mika mata kudade masu yawa ta kawo mana, ai ya san halin da muke ciki, d'an gayu ne fa sai kin gansa me kuma xai yi da wata jiddah kamar warce uwarsa tace masa je ka ka gani?? Haba Zulai, wllh da kyar ma idan ba daga Habuja yake xuwa ba don d'an gaye ne" Zulai ta d'an leka waje a hankali tace "Bacci jiddar take?" Hansai tace "Oho...." Daga haka ta mike ta fita, bude labulen dakinsu jiddah tayi ganinta a kwance tace "Wannan shegen kwanciyar baxai fissheki ba idan xa ki tashi ki kwashi bokitai ki fita gashi can an kawo famfo bakin titi ki jido mana ruwa ko na alwala ina jin babu a gidan nan, tun safe kin wani makale daki a kwance kamar ruwa" daga haka ta fice daga dakin ta koma nata,  jiddah ta mike xaune daga kan darduman da take a kwance bayan tayi sllhn azahar, duk da jikin nata ya mata sauki, amma idan ta tashi jiri take gani ga yunwa dake dawainiya da ita, tun safe kunu kadai ta sha kosan da aka siyo ma bata ga idonsa ba balle a bata ta ci, sai da Jiddah ta bar gidan da bokitai sannan Zulai ta rike kunnenta daya tace "Anya ba son jiddah mutumin nan yake ba kuwa Hansai, banda haka hidimar uban me xai maku, ku da ku ke gida, ga almajirai can a titi, ga gidajen marayu a gari" Hansai tayi kasake, sae kuma tace "Sonta kuma? Ta ina xai so ta Zulai, babban mutum ne fa, kudi yake bata ta kawo min mu kula da kanmu tun bayan mutuwar Isuhu fa...." Zulai tayi wani murmushi irin na boss tace "Lallai Hansai, ashe har ynxu da sauran ki, to wllh da kyar idan ba sonta yake ba me yasa bai mika ma Bibalo ta kawo kudin ba sai Jiddar" Hansai tayi tsaki tace "To Bibalo sana'a take min a bakin titi da xai ganta ya bata? Ai sai dai Jiddar dake bakin titi kullum" Zulai tace "To wllh ki farka daga wnn baccin da kike, kada ki kuskura ki bada kofar da xai shigo da wani batu bayan ihsanin da yake maku, idan kuwa kika yrda to kina ruwa, ga dai Bibalo ai ita ya kamata a so tunda da gatan ta, amma har kika yarda ya shigo maki da wani batu kan Jiddah to kashin ki ya bushe kina ji kina gani Jiddah xata xama matar babban mutum...." Shiru Hansai tayi tana kallonta ko kiftawa babu da alamar xancen Zulai ya gigitata, Zulai tace "Atoh, kada ki kuskura wllh, ihsanin ma idan son samu ne kada ki sake amsa don a bisa dukkan alamu ya ga Jiddah ne ya kyasa, to jiddah kuma a wa Allah na tuba, yarinyar da ko dangin kirki bata da, kai ina ma ta gansu, ke fa kadai ce gatan ta a duniya, ba dangin uwa balle na uba, yau da xaki koreta sai dai ta bi duniya bata da wajen xuwa...." Hansai tace "Toh wai hauka nake yi ne Zulai, bayan an amshi gaisuwa gun Iliya so kike d'an iskan ya 6a66aka ma gidan nan wuta mu shiga uku? ai jiddah yanxu bata da maraba da matar aure, Iliya ya kawo komai sadaki kawai ya rage da daurin aure, shi ma ni ce na ja lkcn ai an sa ranan kusa kusa na daga" Zulai tace "Atoh, tun wuri sanar masa ya dawo ayi ayi auren kawai, kinga wannan mutumi kam dole ya komo ma Bibalo...." Hansai ta sharce wani xufa tace "Ni dadina da ke akwai hangen nesa wllh Zulai, kinga bbu wanda ya xo ya wayar min da kai banda ke ina nan ina ta haukana, bari in sa a kira min Iliyan dama sbda kudin katifar da xan siya mata ya sa nake ta jan auren naki yrda a sa sati biyu kamar yanda ya bukata, amma tunda haka ne kuma ga wnn bawan Allah ya bamu kudade masu tsoka kema har na cire maki dubu biyu a ciki, sai ki rakani kawai gobe ko tsohuwar katifa ce in siya mata da 'yar robobin aikin gida" Zulai tace "Shkkn kuwa" kasa karasawa cikin compound din Jiddah tayi da bokitin ruwa a kanta jin abinda su Hansai ke cewa, ta fi minti uku tsaye duk tana sauraronsu Zulai tace "Idan kin kirasa kice yace a sa bikin sati biyu kawai kin shirya a wuce wajen" Hansai tace "In sha Allahu haka xan yi" A hankali Jiddah ta karaso ciki ta juye ruwan kanta duk suka yi tsit, ta juya ta fita tsakar gidan lkci daya hawaye ya kawo idonta, ita dai bata ji xancensu na farko ba amma daga inda suke cewa xa su ce Iliya ya dawo ayi auren ta tsinci maganar su. Bayan ta fito ta so shiga gidan Iyah amma sbda irin warning din da Hansai tayi mata yasa bata shiga ba, inda xata shiga tayi kukanta me isarta take nema, a haka ta dinga jan kafa har ta isa inda pampon yake ta jingina da bangon wani gida tana share hawayen dake makale idonta, ko yaushe xai kawo mata piya piyan da yace xai kawo mata, ji tayi baxata iya jiransa ba kuma, gwara kawai ta siya da kanta duk da kudin da ya rage mata yanxu bai wuce dari biyu ba tunda Hansai ta rabata da Usman dinta ta karfi da yaji, don kuwa wanke kafa tayi ta tafi har gidansu can cikin gari ta sanar ma iyayensa su ja ma d'an su kunne ya fita harkar 'yar ta jiddah don an sa mata rana, tun daga sannan kuma rabonta da Usman.  Washegari da sassafe Hansai ta fita xuwa gidan Zulai don daga can xasu wuce kasuwan dillalai yi ma Jiddah siyayyar aure, wata tsohuwar katifa ce da ko riga babu suka siya a farashi me sauki da pillow kwaya daya, sai  robobin kitchen su ma duk tsofaffi, hatta wuka basu siya sabo ba sai tsoho, suka dai kwaso tarkacen da xa a iya kai ta gidan miji da shi, suna shirin barin kasuwan Zulai tace "To baki siya xanin gado ba" Hansai tace "Ina da wani a karkashin akwati xai yi shekara goma da ajiyesa sai in bata kawai, buta kuma ta tafi da na ubanta yana can ba amfani muke da shi ba" A barrow suka kima kayan suka dau hanyar gida. Tunda Jiddah taga siyayyar da suka yi wanda ke nuna cewar an kusa aurenta da Iliya hankalinta yyi mugun tashi, Hansai kuwa tuni tayi kiran Iliya da ya sanar mata sun ma kusa shigowa kaduna, bayan ta katse kiran tana kallon Zulai da wata kawarsu Dije da ta rakasu siyayya tace "Atoh ai shkkn, yace sun wuce Abuja, kun ga wannan karan kenan da matarsa xai koma legas din" Zulai tace "Ahh shkkn, Allah dai yasa ayi bikin da mu" Dije tace "Ameen, ai Hansai 'yar halaq ce, babu wanda yayi tunanin xata yi ma jiddah wannan abun arxikin, kowa gani yake tunda Malam Isuhu ya kwanta dama shkkn watsi xata yi da jiddah, sai gashi ta ba mara da kunya, kuma in sha Allahu baxa ki ta6e ba, kin cika yar halaq wllh" Hansai tayi murmushi tace "Toh Allah na tuba ko uban na da rai wllh ba samun hakan xata yi daga garesa ba, sai in idanuwansa xai kwakule ya siyar yyi mata kayan daki, uban me garesa banda wannan rubabben gidan, bashi da komai sai wahala wllh" Zulai ta kwashe da dariya tace "Allah dai ya ji kansa, gashi nan kin rufa masa asiri kin rufa ma 'yar sa asiri, kin mata abun arxiki" Washegari Hansai ta azalzali Iliya da kira nan ya sanar mata nan da kwana biyu xa su je can gidan kawun nata da ake xancen auren a wajensa tare da magabatansa sai a saka sati biyun da tace, amma fa ba shi da kudin sadaki a yanxu sai dai a biyosa bashi, Hansai tayi shiru tana sauraronsa, can tayi kasa da murya tace "Iliya da kudin sadakin fa nake son yi mata dinki tunda ba lefe xaka yi mata ba kace baka da halin yi...." Ya katse ta cikin fada yace "Gashi nan da duk kudin hannuna na siyo maki masara kwano 8 da gawayi, ko in siyar in kai kudin sadakin?" Da sauri tace "Aa to ai tunda kace idan ka samu xaka bada babu wani damuwa xan ma kawun nawa bayani, Allah yayi maka albarka, ai kowa yasan kai me xuciyar yi ne Iliya, to a ina xaka ajiye Jiddar?" Yace "Ehh akwai shago daya gaban gidan kakana sai ta xauna nan kafin in sama mata haya" Tace "Atoh shkkn, ni na xata legas din xaku wuce tare ince shkkn xaka rabani da Jiddah gaba daya" Yace "Aa nan xan bar ta, mu ma gareji muke kwana a legas din" Hansai ta xaro ido tace "Atoh Allah ya rufa asiri, tunda ga gida ka samar mata a nan din shkkn, Allah ya kai mu wannan rana dai" Yace "Ameen" daga haka ta katse wayar tace "Toh ba shkkn ba" 


Abuturrab na kwance cikin resting cabin din jirgin da yayi piloting tare da Co-pilots dinsa daga lagos xuwa kano, ko minti talatin basu yi da alighting ba, idonsa a lumshe suke duk da ya rufe fuskarsa da hulan uniform dinsu na pilot dake jikinsa, tapping dinsa aka yi a kafa, ya xame hulan a hankali, Co-pilot dinsa ne tsaye kansa, pilot din yyi wani sigh yace "Done with the Secure Cockpit checklist.... Can we??" Abuturrab ya mike xaune yace "Alright..." Pilot din yace "Ain't you changing??" Abuturrab ya kalli uniform din jikinsa yace "Not at all" Jakunkunansu suka dauka suka sauka jirgin, sai da suka gaisa da incoming crew da suka hadu da sannan suka shiga cikin airport din. Driving Abuturrab ke yi cikin motarsa da yake bari a airport, hotel din da yake sauka yawanci idan yana kano ya nufa, duk da Abbansa na da gida nan kano wanda ke a kulle babu kowa ciki baya sauka gidan don baya son xama shi kadai shi yasa ma idan kwana ya kamasa a Abuja, it's either su kwana gidansa tare da Ahmad ko Aneesah ta xo tayasa xama, ya so tafiya kaduna yau amma bai samu flight me xuwa kaduna ba or even private jet, yana shiga hotel din ya karbi daki kamar yanda ya saba, wanka yyi ya sauya xuwa kananun kaya, yayi sllh sannan ya bude pepper soup din hanta da ya sa a kawo masa with cup of coffee, ya fara ci a hankali, ajiye spoon din hannunsa yyi tunawa da yayi bai samu Mu'axxam yayi masa magana ba a kan yarinyar nan ta Hayin rigasa, ya dafe kansa don shaff ya mance, tun a jirgi da ya tuna yake Allah Allah suyi alighting ya samesa da maganan, he can even go to d extent of taking all the marriage responsibilities in har Mu'axxam din yace bashi da hali, tsaki ya d'an yi don gobe da sassafe yake son driving xuwa kaduna baxai shiga airport din ba, a hankali ya ci gaba da shan pepper soup dinsa har ya ji ya ishesa sannan ya tashi ya shiga bandaki ya wanke bakinsa ya fito yayi kwanciyarsa. Washegari Saturday karfe goma saura Abuturrab ya shigo compound dinsu... Parking yyi kusa da motarsa da yake amfani da a kaduna, ya sauka sannan ya shiga ciki, part din Aunty ya fara nufa ya sameta parlonta tana breakfast, ganinsa tace "Daga ina haka kamar an jefoka captain?" ya xauna kasan lallausan carpet din parlon yana murmushi yace "Daga kano nake" tace "Ikon Allah welcome son..." Yace "Ina kwana Aunty?" Tace "Lafiya lau ya hanya?" Yace "Alhmdlh" mikewa tayi tace "Let me get u breakfast" Bata jira cewarsa ba ta fita, sae gata ta dawo tare da mai aiki rike da tray din breakfast din, Mai aikin ta gaishesa sannan ta ajiye, ganin kallon da yake ma tray din Aunty tayi dariya tace "Taimaka min kawai tayi ta dauko flask din ba wai ita ta hada maka ba..." Bai ce komai ba ya dau cup dake a kife ya juya yana kallon ciki keenly kamar yana neman abu, Aunty tace "To yanxu da ba Aneesah bace budurwar ka ya xaka yi da wannan kyankyanin captain, yan matan yanxu da son jiki duk ya sa sun xama kazamai" Ba tare da ya kalli Aunty ba yace "Allah ya ga xuciyana shi sa bai hadani da mara tsaftar ba" Dariya kawai Aunty tayi tace "Jiya ma Aneesar ta kirani mun gaisa ashe ta koma Abuja" Yace "Ehh ta koma..." Tace "Idan ka gama sai ka ajiyeni U-rimi don Allah, driver baya nan kuma bana son driving" Yace "Alright" Yana gama breakfast din kuwa ya mike, tuni ta dauko mayafinta da yar jaka, yace "Salem fa?" Tace "Tun yaushe Salem ya koma makaranta" Abuturrab yace "Ohh yea mun yi chatting ya gaya min, but na manta" Sai da suka fita parlon ya tuna bai je gaida Umminsa ba, ya d'an buda ido yace "Aunty bari in shiga in gaida Ummi yanxu in fito" Ta d'an 6ata rai tace "Yanxun nan fa xaka ajiyeni ka juyo Captain, cikin mintuna kadan xaka dawo ai" Bai ce mata komai ba ta fara tafiya ya bi bayanta walking slowly. Abuturrab bai dawo gidan ba sai bayan la'asar tare da ita, tana rike da ledojin atamfofi da ta sa ya siya mata a gidan da suka je, ta nufi part dinta, shi kuma ya shiga bangaren Mahaifiyarsa, kanwarsa Ramlah kadai ce parlon tana shara yace "Ummi fa?" Tace "Ta fita tare da driver yanxu" Ya shafa kansa yace "Ohk..." Juyawa yyi xai fita tace "Shine baka shigo ka gaisheta ba kuma tun safe ka dawo yaya" Ya juya ya mata wani kallo yace "Yaushe na fara wasa da ke?" Shiru tayi bata ce komai ba, yyi kwafa ya fice daga parlon. Bedroom dinsa ya shiga, sai bayan da yyi wanka ya sauya kaya sannan ya fito main parlor rike da makullin motarsa, har xai fita ya nufi kitchen jin movement a ciki, Safiyya ce a kitchen din da Ramlah sai mai aiki da alama dinner suke dafawa, yace "Is there anything to eat here?" Safiyya ta kallesa tace "Aa ba a gama ba" Juyawa yayi ya fita daga kitchen din ya bar parlon gaba daya, sai da yayi sllhn magrib sannan ya bar anguwar... Parking Abuturrab yyi yana kallon cikin karamin layin da babu haske banda na wata, yara ne bakin wani tap suna ta diban ruwa suna wasa da ruwan, tun da yamma ya so xuwa amma sbda comment din Umar a kansa ranan a hospital yasa ya ki shigowa anguwar da yamman, ya sauke glass yana ta kallon yaran, da hannu yyi ma wani yaro cikin yaran alamar ya xo, yaron ya taho da sauri, dari biyar ya dauka cikin motar ya mika ma yaron yace "Kaje can gidan da ake siyar da awara ka kira min yarinyar dake siyar da awaran" Yaron ya ruga da gudu xuwa gidan, yana isa ya kutsa kai ya shiga, Hansai na xaune tsakar gida Bibalo na haska mata fitila tana daure busasshiyar kubewa a leda, Yaron yace "Ina wuni maman Bibalo" Hansai tace "Lafiya lau, me xaka siya?" Yace "Aa wani me mota ne yace in kirawo me awara" Hansai ta kalli Jiddah dake duke bakin kwaroron wanke wanke tana yi, Hansai tace "To ai kuwa xuwa xaki yi ki ji me ke tafe da shi, tunda yasan yanayin garin kilan wani alherin ya xo mana, ko kuma Bibalo ta je, yan sa idon anguwar nan sae su iya juya mana xance yanxu yanxun nan...." Jiddah dai bata dago ba ta ci gaba da abinda take yi, Mikewa Bibalo tayi da sauri ta ajiye fitilan hannunta tace "Bari in je ni" Mayafi ta figa ta fice daga gidan tana ce ma yaron taho ka nuna min inda yake, can bakin titi yaron ya nuna mata, Abuturrab ya dinga kallonta daga cikin motar, tun daga tafiyar ya gane ba jiddah bace har kuwa ta iso bakin titi, tsaye tayi jikin motar, ya sauko yana kallonta, tayi fari da ido tana wasa da mayafin kanta tace "Sannu da xuwa...." Yace "Ina 'yar uwar taki" ta buda ido sosai tace "Yo ae ta daina fitowa ynxu sbda bikinta sati me xuwa ne, kasan har iyayen iliya sun xo anyi komai yau..." Kallonta ya dinga yi ko kiftawa babu, tace "Idan wani abu ne gani ni ka bani in ji Baabarmu in kai mata" Ya dauke kai daga kallonta yace "Mu je xan ba Baabar taku da kaina" Da sauri ta shiga gaba yana biye da ita, sae wani rangwada take har suka iso kofar gidan, tace "Bari in je in mata magana" daga haka ta shige ciki, Hansai na ganinta tace "Me ya baki?" Bibalo tace "Yace ki je yana kofar gida" Da sauri Hansae ta figi gyale ta yafa ta fita kofar gida, dukawa tayi ta gaishesa ya sauke idonsa shi ma ya gaisheta, ta amsa cike da nutsuwa tace "Sannu da xuwa Alhaji" 


07087865788✍🏻

💖💖 *Jiddatul Khair**💖💖






_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻






8.....



Hansai ta shiga kame kame tace "Gashi babu ma wajen xama a nan Alhaji, ko xa ka shigo daga ciki a shimfida maka tabarma" Yace "Aa nagode, hakan ya isa..." Tana murmushi tace "Allah sarki... Da yake jiddar na daurayan kwanuka shine nace 'yar uwarta ta fito, jiki kam alhmdlh taji sauki sosai, duk ta shanye magungunan nata..." Abuturrab ya sauke idonsa kasa yace "Allah ya kara mana lafiya gaba daya" Hansai tace "Ameen, bari dai kawai in shiga in turo ta ku gaisa, ai yanxu nasan ta gama" daga haka ta shige gida ganin dai babu alamar Abuturrab xai bata komai, jiddah ta nufa da sauri, murya can kasa kasa tace "Tashi ki dau hijabinki ki saka ki fita yana nan kila ya fi gane ya baki, kada ki kuskura ku tsaya kofar gidan nan ki ja shi can karshen layi sbda yan sa ido, gashi iliya na gari, daga nan ma sai ki sanar masa bikin ki sati me xuwa ne idan Allah ya kai mu, kinga idan da akwai wani alkhairin da xai maki sai ya maki, kowa dai yasan ke marainiya ce ba uwa ba uba" Bibalo da ke tsaye kansu tana sauraron abinda suke cewa tace "To Baabarmu idan yaji xata yi aure fa kilan shkkn baxai sake dawowa ba, dama ba sbda awaran da take yi bakin titi bane yake tausaya mana yake bamu kudi?" Hansai tayi shiru, can tace "To kuma aure ae dole tayi abu saura sati daya dai har an gama komai, kawai ta gaya masa.. sannan ba ga ki ba, ai ke xaki ci gaba da yin awaran a bakin titi" Bibalo tace "Cabdijam, wllh baxan yi awara bakin titi ba kawayena da samarina na ganina, haka kawai?? sai dai ke ki dinga yin kayanki ni dai baxan yi ba, to ni ma ba sai a min auren ba kawai" Tana fadin haka ta shige daki tana gunguni, Hansai ta rike ha6a tace "Ikon Allah, yau naga jarababbiya, a maki aure? Duka nawa kike xa a maki aure, ita ma Jiddar ai don iliyan ya dade yana sonta ne kuma ya mana hidima ba kadan ba, ko so kike ya mana tijara yace sai mun biyasa? A gidan uban wa ma xan samu abun biyansa? ke kuma da nake da burin in samar maki makaranta cikin gari ki fara xuwa kya kawo xancen a maki aure, a can din sai kiga Allah ya hadaki da miji dai dai ke, nan banda yan kato da gora, da yan adaidaita sahu, ga leburori, ga yan gwangwan sai yan iskan anguwa, to waye sa'an auren ki duk cikinsu? Ai babu sa'an auren ki wllh, ke da kike matar babban mutum" Hansai ta kalli Jiddah da kanta ke kasa har lkcn tana sauraronta, ta hade rai tace "Baxa ki tashi kije ba kin bar bawan Allah tsaye a waje" Jiddah ta mike a hankali ta dauraye hannunta ta shiga daki ta dau Hijabinta ta sa, ta saka takalminta sannan ta fita Hansai ta bita da sauri murya can kasa kasa tana cewa "Ku bar kofar gidan ku je can bayan layi kada a samu me kai ma Iliya rahotu" Ita dai bata ce komai ba har ta fita, yana tsaye ya rungume hannayensa, a hankali ta karasa can jikin wani tsohon adaidaita da aka yi parking gaba da gidan nasu, ya bi ta da kallo sannan ya bi bayanta, jingina tayi da adaidaitan tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Sakon da kace xaka kawo min fa?" Yayi shiru yana dubanta, ta fashe masa da kuka tace "Kasan baxa ka kawo min ba me yasa kace xaka kawo min?? Alkawari fa ka min" Ya rungume hannunsa yace "Ohk abinda kika ce xa ki sha??" Ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, yace "Yaushe xa a daura maku auren?" Tace "Sati me xuwa, don girman Allah gobe ka kawo min, naje na tambaya a shago ance min ba dari biyu bane, kuma ni dari biyu gareni" Bude baki yayi yana kallonta da mamaki, can yace "Yaushe kika je kika tambaya?" Cikin rawar murya tace "Jiya" Ya sauke idonsa yace "To ai ni nace xan kawo maki ko? Kuma ban manta ba" Tace "Toh baka sake xuwa ba ai tun ranan" Yace "Toh gobe xan kawo maki" Ta gyada masa kai tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, Sauke idonsa yyi kasa yace "Wa kika sani a kaduna bayan Baabar nan taku?" Ta girgixa masa kai a hankali tace "Ba kowa" Yace "Wa xai daura maki aure?" Cikin rawan murya tace "Kawu Jibril" yace "Waye shi?" Tace "Kawun Baabarmu ne shi" Shiru yyi na kusan minti daya sannan yace "Ki koma kice da Baabarku xan yi magana da ita" Juyawa tayi ta koma ciki, Hansai na xaune tsakar gida tana fifita tana jiranta, ganinta ta mike da sauri tace "Ya aka yi kika dade, nawa ya baki?" A hankali Jiddah tace "Yace xa ku yi magana da shi" Hansai ta hade rai tace "Bai baki komai ba?" Jiddah ta gyada mata kai, Hansai tace "Toh ba naje ba mun gaisa, maganar me kuma xa mu yi" Bibalo ta leko tace "Ke dai kije ki ji abinda xai ce maki kawai" Hansai ta nufi kofar gida da sauri, tana ganinsa ta sunkuyar da kai tana d'an murmushi tace "Cewa tayi kace xa mu yi magana ko?" Yace "Eh, yanxu take gaya min sati me xuwa xa ayi aurenta" Hansai tayi kasa da murya tace "Wllh kuwa, tun uban na da rai ya ci bashin da ya fi karfinmu, bamu da halin biya, to dai kusan auren biyan bashi ne, tunda mu dai bamu da kowa duniyar nan banda Allah, bamu da kowa bamu da komai sai rubabben gidan can, to ya xan yi??" Tana fadin haka ta fara matsar kwalla, kallonta kawai Abuturrab yake da mugun mamaki, can yace "Nawa ne kudin bashin?" Goge idonta ta dinga yi tana tunanin kudin da xata lafto, can dai tace "Dubu dari ne da ashirin wllh" Yace "Ina shi me kudin?" Nan fa hankalin Hansai ya tashi, cikin rawan baki tace "Ehh to ba garin yake ba, kawai sai dai a kai masa, noma kawai yake yi a nan amma ba d'an garin bane" Abuturrab yace "Ohk, shi ne xai aureta?" Tace "Ehh, Aa ba shi bane gaskiya, d'an sa xai aura ma, ehh babban d'an sa xai aura ma" Abuturrab yace "Ohk, dama akwai wani aiki ne da nake son in bata ta dinga yi, duk wata xa a dinga biyanta dubu dari biyu, kinga idan tayi aure baxai yiwu ba, naga kuma ta fi 'yar uwarta kwazo, dama tana farawa da wata biyu sai a kawo yar uwartata, kafin nan ita ta kware sai ta dinga sa 'yar uwar a hanya" tuni xufa ya fara keto ma Hansai tana kallonsa tace "Dubu dari biyu fa kace Alhaji?" yace "Ehh haka albashin yake, amma dai yanxu xan je in ciro kudi in bata sai ta kawo maki ki biya bashin... Xancen auren kuma sai a fasa shi" Hansai na share wani xufa da kyar tace "Toh ai shkkn Alhaji, Allah ubangiji ya kara maka girma da daukaka, yanda kake rufa mana asiri haka Allah xai rufa maka asiri kai ma" Yana kallonta yace "Ameen, amma kina ganin auren xai fasu idan aka biyasu bashin su?" Da sauri Hansai tace "Ba dole ba, dama ai sbda kudin ne suke son rabani da diyata" Yace "Toh xan je in ciro kudi yanxu..." Hansai tace "Toh turo maka ita xa ayi kuje tare?" Yace "Ehh" juyawa tayi da sauri ta koma ciki, Jiddah na daki ta hade kanta da gwiwa Hansai tace "Jiddah tashi xa ku je ya baki kudi ki kawo yanxu, duk abinda yace maki kar ki kuskura kice ba haka bane, komai yace kice masa ehh haka ne, kinji me nace??" Kallonta kawai Jiddah ke yi, Hansai ta hade rai tace "Baxa ki tashi ba an bar sa a tsaye" a hankali Jiddah ta mike ta fita dakin, yana nan tsaye ta samesa, Sai da ya kalleta sannan ya fara tafiya, bin bayansa tayi har suka isa bakin titi inda motarsa yake, Bank ya tafi a can cikin garin don cire kudi a Atm machine, ta bi sa da kallo bayan ya sauka motar, bayan wani lkci ya dawo ya shiga motar ya dau karamin leda ya xuba kudin a ciki ya ajiye, bayan few seconds yace "Tace auren biyan bashi xaki yi" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ba haka bane" ya kalleta da sauri yace "To ya ne?" Hawaye ya kawo idonta tace "Kawai aure take son yi min da iliya sbda yana kawo mata abubuwa daga legas idan xai dawo" Abuturrab yace "Shi a ina yake xaune a kaduna?" Tana share idonta tace "Nan hayi yake shi ma" Yace "Xa ki nuna min gidansu?" Ta d'an yi shiru kafin ta gyada masa kai, tada motar yayi suka bar wajen, sai da suka shigo hayi yace "Ina ne gidan nasu?" Tace "Can gaba ne amma hanyar bbu kyau mota baxai shiga ba kuma da akwai nisa, dole sai da adaidaita" Yace "Ohk..." Ta gyada masa kai kawai, dai dai layinsu ya tsaya, ta dinga jiran ya bude mata motar ganin bai bude ba ta kallesa, yace "Yanxu idan aka fasa auren naki xaki hakura da kashe kan naki?" Shiru tayi tana kallonsa, ya d'an hade rai ganin kallon da take masa yace "Ina sauraron ki?" Sunkuyar da kanta tayi tace "Ehh" bude mata motar yayi ya mika mata ledan kudin ta amsa, xata sauka yace "Jira" Komawa tayi ta xauna tana kallonsa, yace "Kin iya amfani da waya?" Ta kallesa sannan ta girgixa masa kai alamar A'a, kunna fitilan motar yyi ya dau pen da wani karamin jotter ya rubuta numbersa ya mika mata yana dubanta yace "Idan da akwai wani abu ki nemi me waya ki kirani" Ta gyada masa kai, yace "Sauka" Ba musu ta sauka motar ta rufe masa ta fara tafiya.... Hansai na ta xaune tsakar gida tana jiran shigowar jiddah, sauro duk ya cijeta sai soshe soshe take, ganin jiddah ta shigo ta mike da sauri tana kallon ledan hannunta ta karasa kusa da ita ta amshe ta bude.... xaro ido tayi tana kallon uban kudin ciki, Jiddah dai na tsaye sai kallonta take ita ma, daki Hansai ta shige da gudu duk ta rude don yan dari biyar biyar ne kudin shi sa yayi yawa, Jiddah ta juya a hankali xata shiga dakinsu kenan aka shigo gidan babu ko sallama, Iliya ne da abokansa biyu kamar an hankadosu sai muxurai suke, ya nufi Jiddah yana huci ya fixgota ya xabga mata wani wawan mari cikin katon muryarsa yace "Uban wa ya sauke ki a mota yanxu?" Hansai na jin muryarsa tayin sauri cusa ledan kudin can karkashen jakarta tana salati ta fito da gudu, wani marin ya sake wanka mata ya hadata da bango ya lafto wani uban ashar yace "Da kudin nawa a kanki kike bin kartin alhazan nan suke yawo dake cikin gari, dama an gaya min ban yarda ba sai gashi yau na gani da idona, idan baki fada min waye shi ba al-qur'an sai na sumar da ke yau...." Yana fadin haka ya kara kai mata hauri ya shakota, ihu kawai jiddah take, Hansai da jikinta ya dau rawa tace "Ji mana Iliya, wllh wllh wani abokin uban gidan babansu ne jin xata yi aure ya tafi yi mata siyayya ya bada gudunmawarsa...." Wani wawan mari xai kai mata ta kauce da sauri ta bar wajen jikinta na rawa, kana ganinsa kasan a buge yake, Bibalo dai ta d'an windan dakinsu take leko su taki yarda ta fito bayan ta sakale dakin, Jiddah sai kichiniyar kwace kanta take amma ta kasa don ba rikon wasa yyi mata ba, Hansai ta nufi can bakin murhu jiki na rawa tace "Ka saurareni Iliya kada ka kashe min ita, wllh nace maka abokin wanda babansu yyi ma aiki ne a lkcn da yake raye, Jiddah ai ba haka take ba, jiddah kamilalla ce..." Sake Jiddah yayi ya juya yana kallon Hansai ya nufeta yana huci, wani ihu ta kwala tana cewa "Makota ku kawo mana dauki kar ya kashe mu...." Wani wawan naushi ya sauke mata a baki, tuni jiddah tayi waje a guje, daya daga abokan Iliya yace "Kai Iliya ta fice fahhh" iliya ya juya da sauri yace "Ku bi taaa" Duk suka fita da gudu, Iliya ya bi bayansu yana cewa daga nan kawai a kai min ita shagona, bikin banxa bikin hofi abinda har sadaki na biya naira duba sha uku, tinkiyar babata fa na dauke na siyar ko sani bata yi ba na biya sadakin, kawai a kai min amaryata..." Hansai dai tunda naushi ya sauka bakinta da ta fada cikin jerin bakaken tukwanen awaranta bata sake motsi ba sai 'yan idanuwa.... Jiddah na fita dama ta bayan layi ta xaga xuwa windon Iyah, a hankali ta dinga bubbuga windon jikinta na rawa tace "Iyah ni ce ki bude" Iyah tace "Aa ba ruwana an min iyaka da ke, ni da kika sa Hansai ta kusa cinna ma gidana wuta...." Wani ihu Jiddah ta fasa ganin Salmanu daya daga abokan Iliya, ya fixgo hannunta yace "Iliya gata na gano ta" Sai ga Iliya da gudu tare da Surajo, Iyah sai xare ido take jin ihun da jiddah ke yi, a haka Iliya ya ja ta xuwa adai daitan Surajo suka sa ta tsakiya Surajo ya hau adaidaitan ya tada, Iliya ya fiddo wukar aljihunsa yana nuna mata da jajayen idanuwansa yace "Al-qur'an idan baki rufan baki ba xan da6a maki wukar nan kowa ya huta" Tsit tayi jikinta na rawa hawaye na sauka idonta, can karshen kwalta suka kai ta, wani kuturun uncompleted house da Surajo ke ginawa, sbda rashin wajen kwana yake kwana a haka, Salmanu yace "Shikenan sai ku tare nan daren yau kafin gobe da safe Hansai taje tayi mata jere a shagon naka" Iliya yayi wani dariya ya sauka daga adaidaitan yana kallon Jiddah da ko kukan ta kasa sbda fargaba da shock, ya daure fuska yana kallonta da jajayen idonsa yace "Sauka mu shiga Amaryata ta kaina" Da kyar ta sauko daga adaidaitan ya tisa keyarta har cikin gidan wanda duk dogayen ciyayi ne, Surajo yace "To ko 'yar kifi da ruwan leda ba a siya mata ba ai" Iliya yace "Ai akwai wasu daren masu xuwa da yawa bayan wannan, idan bata ci yau ba xata ci gobe" Surajo yace "Da akwai lemo daya ma da na siyo da rana ban sha ba sai ka bata ta sha kawai" Dariya duk suka dinga kyalkyalewa da, Can jikin bango jiddah ta rakube kusa da yar katifar dake kwance a dakin da wani karamin fitila da bbu hasken kirki, ko siminti bbu a kasa, banda warin ta6a da wiwi bbu abinda dakin ke yi, ta runtse ido tana jin abubuwan kamar a mafarki, sallama su Surajo suka yi ma iliya suka fita dakin suna dariya suka yi masa sai da safe, Ya mike ya kulle kofar ya dawo ya xauna ya fiddo kwalin ta6arsa ya kunna ya fara xuka yana kallon Jiddah da ta takure ko ina na jikinta na rawa, yyi kasa da murya yace "Kiyi hakuri amaryata cikin bacin rai na bubbuge ki, raina ne ya baci ba kadan ba, kinsan idan raina ya baci bana ganin komai idona rufewa yake, har mutum ina iya kashewa, yo sau nawa ma aka yi hakan, kawai garbati ya ce min kusan kullum sai an xo an tafi dake an dawo a katuwar mota.... Shi ma shegen dake tafiya dake a motar ya ci sa'a bamu hadu ba wllh" Ita dai Jiddah bata ce komai ba jikinta sai bari yake, ya mike ya dawo kusa da ita ya xauna yana xukan hayakinsa yana murmushi ya rungumota kusa da shi, ta runtse ido xuciyarta na bugawa da sauri sauri, yace "Inji dai baki jin yunwa ko Amaryata?" Ta girgixa masa kai da sauri, ko kallonsa bata son yi kar ta saki ihun da take hadiyewa, ya wurgar da guntun taban hannunsa ya mike ya fara cire kayan jikinsa, Abuturrab ne ya fado mata, hawaye me xafi ya fara silalowa idonta, Bata san lkcn da ta fasa wani ihu a mugun tsorace ba ta rufe fuskarta da gwiwanta... Ya hade rai ya buga mata dundu a baya yace "Kee, ki kiyayeni fa, so kike ayi tunanin fyade xan maki bayan ke halaliya ta ce, dubu sha uku na biya jiya jiyan nan, har yanxu Babata bata san yanda aka yi da tinkiyarta ba, shine xaki kawo min iskanci, to idan xaki saki jiki ki saki, don muna nan da ke har sai an kira assalatu wllh...." Ta kallesa cikin dakiya amma muryarta na rawa tace "Fitsari xan yi" yyi murmushi yace "To ko ke fa, amaryata, ai gwara kawai ki saki jikin ki" Ya mike ya yace "Mu je in raka ki" Tashi yyi ya dagota xai cire Hijab din jikinta ta rike da sauri cikin rawar murya tace "Aa wllh sanyi nake ji" Bai saurareta ba ya cire Hijab din ya jefar kan gado ya nufi kofa ya bude yace "Mu je kiyi fitsarin" Ta bi sa da sauri jikinta na rawa, wani lungu ya nuna mata a jikin gidan, tun bata kai nan ba take jin zarni na tashi a wajen, yace "Kije kiyi ki dawo ki sha lemo kinji amarya" Ta gyada masa kai ta nufi wajen, komawa ciki yyi da sauri ya dau wandonsa ya laluba ciki ya fiddo wani karamin kwalba, sannan ya dau lemon coke dake ajiye a dakin ya bude, ya bude kwalban ya tsiyaya abinda ke ciki cikin lemon sannan ya rufe ya d'an jijjiga lemon ya sha kadan ya ajiye sauran, ya mayar da kwalban aljihunsa yana murmushi yace "Tass xa ki shanye lemon nan" xaunawa yyi gefen katifa yana jiranta, da sauri ya mike kamar wanda ya tuna abu ya nufi waje ya leka yace "Ke Jiddah, har yanxu baki yi fitsarin bane" A wangale ya ga d'an zinc din da aka yi kofa da shi na gidan, ya xaro ido ya fita da gudu yana kwala mata kira, gudu kawai Jiddah take wajajen da bbu kowa babu wasu gidaje sai ciyayi, sai da tayi gudu sosai taga wani me adaidaita ta tsayar da shi jikinta na rawa tace "Don girman Allah ka taimakeni wllh sato ni yayi, don Allah ka rufa min asiri ka taimakeni" Bata jira cewarsa ba ta shige adaidaitan don ya tsaya, shi ma mai adaidaitan duk a tsorace yake ya dinga gudu har suka shigo cikin mutane, har sannan Jiddah waige waige take gabanta na faduwa, sai da suka shigo hayi sosai sannan yace "Daga ina suka dauke ki?" Tace "Can cikin gari" Ya girgixa kai yace "Yanxu ina xa ki?" Shiru tayi don tasan tana komawa gida yanxu Iliya xai iya xuwa can gidan, da sauri tace "Cikin gari xan je don Allah" Dai dai kano road mai adaidaitan ya tsaya yace "To anguwan naku ba shi da sunana ne a cikin garin, ni fa nan ne iyakata?" Lkci daya hawaye ya kawo idonta ta bude tafin hannunta tana kallon takardan da Abuturrab ya bata daxu, har lkcn takardan na hannunta gam, ta kalli mai adaidaitan cikin sanyin murya tace "Don Allah kana da waya?" Yace "Ehh" tace "Toh ka taimaka ka kira min number nan don Allah" ya amshi takardan ya dau wayarsa ya kwashe lambar sannan yayi dialing, Abuturrab na xaune parlon Abbansa yana masa calculating din order din da Abban nasa yyi daga waje na kayan auren Ramlah wayarsa ya fara ring, Abba ya kallesa ganin ba daukan wayar xai yi ba yace "Pick ur call" hakan yasa Abuturrab ya dau wayar yana kallon number kafin ya daga ya kai kunne, Mai adaidaitan ya mika ma Jiddah wayar ta amsa ta kai kunne, calmly Abuturrab yace "Hello" Hawaye ya silalo idonta tace "Ni ce" Kallon Abbansa dake kallonsa yyi da sauri, sai kuma ya sauke kansa kasa yace "Ohk ina ji" Ta fashe da kuka sosai tace "Iliya ne ya xo ya daukeni wai saboda ya ganni a motarka...." Abuturrab ya dago da sauri yace "Xuwa ina?" Cikin kuka tace "Wai shi ba sai anyi biki ba tunda ya bada sadaki, nufinsa tarewa xan yi" Abuturrab ya saci kallon Abbansa ya rasa abinda xai ce, Abbansa dake lura da shi ya mike ya shiga bedroom dinsa, mikewa yyi da sauri ya nufi kofa ya bude ya fita yace "Kina ina yanxu?" Ta bi inda take da kallo tace "Mai adaidaitan yace min kano road ne" Abuturrab yace "Ba sa wayar" Mika ma mai adaidaitan wayar tayi ta shiga share hawayen da ya ki tsaya mata, Mai adaidaitan yace "Ehh a dai dai wajen muke ma" bayan few seconds mai adaidaitan yace "Toh shkkn xan jira in sha Allah" Daga haka ya katse wayar, Abuturrab ya koma parlon Abbansa, Ganin bai fito ba ya karasa bakin bedroom din yayi masa sallama, Fitowa Abba yyi, Abuturrab yayi kasa da kansa yace "Abba xan d'an je in dawo ynxu, wani abokina ne ya kirani and it's urgent" Abba yace "Alright sai ka dawo" Juyawa yayi ya fita daga parlon, ya tafi dakinsa ya dau makullin motarsa, jallabiya ne jikinsa ya fita a haka ya shiga motarsa ya bar compound din.....



07087865788✍🏻

💖💖 *Jiddatul Khair* 💖💖






_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻






9.....


Abuturrab yayi parking yana bin wajen da kallo ya dau wayarsa yayi dialing number da suka kirasa da shi, yana fara ring mai adaidaitan dake hira da wani me d'an kiosk a wajen ya daga, Abuturrab yace "Ka duba wani bakar mota a wajen da kace" Mai adaidaitan ya mike yana dube duben wajen, can ya hango motar Abuturrab ya kalli Jiddah dake xaune cikin adaidaitan har sannan ta takure waje daya yace "Ga sa can ya iso" Dago kai tayi da sauri sannan ta sauka daga cikin adaidaitan, tare suka tsallaka titi da shi xuwa daya side din ya nufi motar Abuturrab tana biye da shi a baya, Abuturrab ya bude motar ya sauko yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi sbda hawayen da ya kawo idonta, ya kalli mai adaidaitan ya ciro dubu biyu aljihunsa ya mika masa yace "Nagode" Mai adaidaitan ya amsa shi ma yyi masa godiya sannan ya tsallaka ya koma gun Napep dinsa, Ba tare da Abuturrab ya kalleta ba yace "Shiga" Ba musu ta shiga gaban motar, ya shiga maxaunin driver ya tada motar suka bar wajen, a hankali yake driving din yace "Bayan na tafi sai me ya faru?" A hankali ta fara basa labarin abinda ya faru bayan tafiyarsa babu abinda ta boye masa har karshe, ganin yanda take kuka ya kalleta yace "Ya maki wani abu ne?" Ta girgixa masa kai, rasa particular tunanin da xai yi yayi a lkcn, babban damuwarsa yanxu inda xai kai ta cikin daren nan, ya d'an kalleta yace "Yanxu babu wanda kika sani nan cikin gari?" Ta girgixa masa kai tace "Ba kowa" ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yana ci gaba da driving dinsa almost absentminded, parking yayi bakin gate din gidan, har Mai gadin ya mike xai bude gate ganin yayi parking a nan waje sai ya koma ya xauna, Abuturrab ya sauke glass ganin haka mai gadin ya sake tasowa da sauri ya nufosa yana murmushi cike da girmamawa yace "Barka dai ranka shi dade..." Abuturrab yace "Ya aikin?" Mai gadi yace "Alhmdlh, Baxa ka shiga ciki ba?" Abuturrab ya d'an shafa kai yace "A'a, wani d'an alfarma nake nema gun ka" Cike da natsuwa yace "Toh ina saurarenka yallabai" Abuturrab yace "Erm... Mai dakinka na nan ai?" Mai gadin yace "Ehh tana ciki wllh" Abuturrab ya kalli Jiddah yace "So nake don Allah ta d'an kwana nan wajen ku kafin gobe, amma kamar kuma hakan da takura tunda daki daya ne ko?" Da sauri Mai gadin yace "Inaa babu wani takura wllh ranka shi dade, ni ai ba baccin ma nake da daddare ba yawanci nan tsakar gida nake kwanciyata wllh, kar kaji komai" Abuturrab yace "Toh nagode, amma kada kace ma masu gidan na xo" Mai gadin yayi murmushi yace "Baxa ayi hakan ba ranka shi dade" Abuturrab ya juya yana kallon jiddah yace "Sauka, sai da safe..." Yana fadin haka ya bude mata motar, ta sauka a hankali, Mai gadin yace "Mu je ciki to...." tafiya ya fara yi ta bi bayansa sai da suka kusa gate din ta waiga ta kalli Abuturrab da ya bi su da kallo,  dauke kai tayi ta bi mai gadin suka shiga cikin compound din, yayi wani sigh ya tada motarsa yayi reverse ya bar layin wani ajiyar xuciyar ya sake saukewa feeling a bit relieved. Har aka idar da sallan asuba Jiddah bacci take, matar mai gadin na idar da sallah ta d'an ta6ata tace "Ki tashi kiyi sallah lokaci yayi" a hankali Jiddah ta bude idonta ta mike xaune da sauri, daki ne babba gun katifar kadai ne suka yi demarcating da labule, yaronsu daya wanda ko yayesa ma ba ayi ba, jiddah ta mike matar ta nuna mata bandakinsu dake cikin dakin, tana fitowa matar ta bata hijab, bayan ta idar abun ka da bata saba komawa bacci ba ta kalli matar ta gaisheta sannan tace "Babu wani aikin da xa ayi?" Matar tayi murmushi tace "Aa babu, ki koma kiyi kwanciyar ki" Jiddah bata ce mata komai, amma duk yanda ta so komawa bacci bata iya ta koma ba don ta riga da ta saba da wahala, gari na wayewa ganin matar ta dau tsintsiya xata fara sharan daga nan inda suke xuwa bakin gate don gidan akwai me shara, jiddah ta amshi tsintsiyar, matar tace "Don Allah ki bari ki koma kiyi xamanki...." Murmushi kawai Jiddah tayi tace "Aa xan taya ki" Tana fadin haka ta fara sharan hakan yasa matar ta koma ciki don yi ma yaronta wanka tana yaba hankalin Jiddah, shi kuma mai gadin na can xaune waje, jiddah na cikin shara aka bude gate din gidan ta dago da sauri, sosai gabanta ya fadi ganin wanda ya shigo, a hankali ta juya tana ci gaba da sharanta, waya ne kare kunnensa ya katse wayar yace "Maman Abdallah kun tashi lafiya" Ba tare da ta bari ta kallesa ba a hankali tace "Ba ita bace" Ko rufe baki bata yi ba Maman Abdallah ta leko da fara'arta, cike da ladabi tace "Ba ita bace Dakta, bakuwa nayi, ina kwana" yana tafiya yace "Lafiya lau, Abdallah bai tashi ba?" Tace "Kaya nake sa masa ya tashi tun daxu" yace "To a gaida min shi" Tace "Xai ji Dakta" Entrance din gidan nasu ya nufa, Jiddah ta bi sa da kallo tana sharanta a hankali... Karfe takwas Maman Abdallah ta kalli Jidda bayan ta gama shiryawa cikin kayan da ta bata tace "Tunda kinyi wanka mu shiga daga ciki mu gaisa da 'yan gidan in amso mana kumallon mu, ko" Jiddah dai tayi shiru bata ce komai ba, Maman Abdallah ta goya d'anta tace "Tashi mu je, Hajiyar gidan ta tashi yanxu" A hankali Jiddah ta mike ta dau Hijabin matar ta sa sannan suka fita, Maman Abdallah ta bude kofar hade da sallama ta shiga ciki Jiddah na biye da ita, Xaunawa tayi kasa jiddah ma ta xauna kasa, Hajiya Ramlah dake parlon da murmushi fuskarta tace "Bakuwa kika yi Shafa" Maman Abdallah ta washe baki tace "Ehh wllh Hajiya, bakuwa nayi da yammacin jiya" Cike da ladabi ta risina tace "Ina kwana Hajiya" Umma tace "Lafiya lau kun tashi lafiya?" Maman Abdallah tace "Alhmdlh, su Maimuna da Siyama na ciki kenan" Umma tace "Suna ciki..." Jiddah na kallonta a hankali tace "Ina kwana?" Umma tace "Lafiya lau yan mata, sannu da xuwa.... ya sunanki?" Jiddah ta sunkuyar da kanta tace "Jiddah" jin footstep ta dago tana kallon direction din, Ahmad ne ke sakkowa daga sama yana kallonta babu ko kiftawa, Umma tace "Ahh me babban suna ce ashe" Jiddah tayi murmushin karfin hali ta sunkuyar da kanta, Umma tace "Maa sha Allah, sunan yayata gare ki, sannu da xuwa" Maman Abdallah dai sai washe baki take, Umma tace "Yar uwarki ce amma" Maman Abdallah ta sosa kai tace "Ehh kauyenmu daya" Ahmad dai sai kallon Jiddah yake, ita kuma taki yarda ta sake kallonsa, Maman Abdallah ta mike ta wuce kitchen don daukan kumallonsu, tana shiga ta dauka a inda mai aiki ta ajiye masu ta fito, Umma ta kira mai aikin tace "Tunda suna da bakuwa ki kara masu" Mai aikin ta amsa ta koma kitchen din, ba a dau lkci ba ta dawo ta mika ma maman Abdallah coolern, Cike da ladabi Maman Abdallah tace "Mun gode hajiya Allah ya kara girma" Umma tace "Ameen" Mikewa Jiddah tayi ta amshi warmer din a hannunta sbda Abdallah dake bayanta ita ma ta yi ma Umma godiya sannan suka fita, Ahmad dai ya bi ta da kallo.... He looks so confused, sak tayi masa kama da mai awaran hayi, wata xuciyar tace kawai kamanni ne me xai kawota cikin gari har cikin gidansu kuma, daga kafada yayi a ransa ya bar sa a cewar kamannin ne, ya nufi dining don yin breakfast. Karfe goma Abuturrab ya fito gida, driving yake yi with different thought in mind, wayarsa ne ya fara ring ya kalli wayar ganin Ahmad ke kiransa ya daga, Bayan sun gaisa Ahmad yace "Muna chatting kuma ka sauka" Abuturrab yace "Ehh i am driving now" Ahmad yace "To where?" Abuturrab yace "Aunty ta aikeni" Ahmad ya d'an ta6e baki yace "Ohk, wai ka dauki hutu ne naga baka koma gun aiki yau ba?" Abuturrab yace "Kai me ya dawo da kai during week day?" Ahmad yace "Wani taro xa mu yi nan kaduna, amma gobe xan koma ai, in sha Allah" Abuturrab yace "Ohk anjima xan shigo idan na dawo" Ahmad yace "Alright" daga haka ya katse wayar ya ajiye, parking yyi inda ya saba parking din, ya sauka motar yana kallon layin dake cike da mutane, wani d'an saurayi dake fitowa daga layin ya kalla yace "Abokina me ke faruwa a nan?" Saurayin yace "Wata amarya ce saura sati bikinta aka nemeta aka rasa, wasu sunce angon ne ya dauketa, wasu kuma su ce uwar rikonta ta san inda take, ynxu dai ga shi angon na neman cinna ma gidan wuta wai sai an fito masa da matarsa, uwar rikon na can tana kuka da rantse rantse bata san inda take ba, jama'a kuma na ta dannan shi angon, da yake babu wanda bai san halinsa ba a unguwar nan, sai ya iya kona gidan, yanxu dai wajen yan sanda ko mai anguwa suke shirin xuwa" Abuturrab yace "Toh Allah ya kiyaye" Barin anguwar Abuturrab yayi, yana isa gidansu Ahmad yayi parking a waje, ya sauka motar gaisawa yayi da mai gadi dake xaune a waje sannan ya xauna kusa da shi murya can kasa yace "Kayi hakuri babu wani bayani na kawo maku yarinya..." Mai gadin ya katse sa da sauri yace "Babu komai ranka shi dade, kar ki ji komai wllh, xata iya xamanta har iya sanda xaman nata xai kare a nan, ni bani da matsala haka ma mai dakina.." Abuturrab ya sa hannu aljihu ya fiddo dubu biyar ya mika masa yace "Gashi ka rike wannan" Mai gadin ya girgixa kai yace "Aa kar mu yi haka da kai don Allah" Abuturrab ya ajiye masa kudin ya mike ya shiga gate din gidan, Babu kowa tsakar gidan ya kalli building din mai gadin sannan ya nufi main entrance din gidan. Kiran azahar ne ya sa shi fitowa tare da Ahmad xa su tafi masallaci, Jiddah na xaune compound din kan karamin kujera kusa da dakin mai gadin da ruwa cikin buta a gabanta tayi nisa tunanin da take, Har suka kusa isowa wajen Abuturrab kallonta yake haka ma Ahmad, kamar ance ta daga kai tayi ido hudu da su, sosai gabanta ya fadi ta sunkuyar da kanta da sauri ta fara alwala da ruwan butan gabanta har suka fita compound din, sai a sannan Ahmad ya kalli Abuturrab yace "Don Allah wa yarinyar nan tayi maka kama da???" Abuturrab yace "Wacce yarinya?" Ahmad yace "Yarinyar da ke xaune a compound" Da mamaki Abuturrab yace "Ohh dama akwai yarinya xaune a compound din?" Wani kallo Ahmad ya jefa masa, Abuturrab ya daga shoulders dinsa yace "Banyi noticing ba" Ahmad yace Karya kake "Wllh" Abuturrab bai kuma ce masa komai ba, Ahmad yace "Joke apart captain, bata yi maka kama da wannan yarinyar da muke siyan awara a wajenta a hayi ba" Abuturrab ya ta6e baki yace "Kai da kake kallonta kenan idan kaje siyan awaran, ni kam banda murhu babu abinda nake gani a wajen" yana fadin haka ya shige Masallaci kafin Ahmad ya sake ce masa komai, Ahmad ya bi bayansa kawai. Ko da suka fito masallacin Ahmad ya tsaya gaisawa da abokansa na layin, Abuturrab ya shiga compound din kawai, Jiddah na ta sauri tana kwashe kayan shanyan da Maman Abdallah ta shanya don garin akwai hadari, tun da ta kallesa sau daya ta dauke kai sai da ya iso dai dai inda take tace "Ina yini?" Bai amsa ba yace "Kina da wani matsala?" Ta girgixa masa kai, ganin haka ya ci gaba da tafiyarsa, dai dai nan Ahmad ya shigo compound din bata yadda ta kallesa ba har xai wuceta sai ya tsaya yace "Bakuwa muka yi yau a gidan ashe?" Taki yarda ta kallesa still, tayi kasa da murya tace "Ina yini" yayi murmushi yace "Lafiya lau, sannu da xuwa" Maman Abdallah ta leko tace "Dakta Abdallah fa boyewa yake idan yaji muryar ka" Ahmad yayi murmushi yace "Ae kice masa alluran ya kare" Ta kwashe da dariya tace "Lallai kam, shi dai ya tsorata da kai kawai Dakta" Ahmad yace "Ashe bakuwa muka yi gidan" Tace "Ehh wllh yar uwata ce daga kauyenmu ta xo jiya da yamma" Yace "Allah sarki, toh barkan ta da xuwa" Maman Abdallah tace "Ae ko dai Dakta, mun gode" Murmushi yayi ya ci gaba da tafiya a xuciyarsa ya kara gaskata cewa lallai kamanni ne kawai suka yi da me Awara a hayi, but the resemblance is so obvious even the dimples and large eyes, can balcony Abuturrab ya tsaya duk yana jin abinda suke fada, sai da ya iso Abuturrab yace "Kai dai baka abu da class Ahmad, meye na tsayawa hira da matar mai gadi pls?" Bai jira me xai ce ba yayi wucewarsa ciki, Ahmad ya girgixa kai kawai ya bi bayansa. Da yamma Mamam Abdallah ta ba jiddah kwanukansu ta kai can cikin gida sbda a ciki xa a sa masu abincin dare, Jiddah tace "Ta cikin parlon ake bi xuwa wajen girkin?" Maman Abdallah tace "Ehh inda muka je daxu ba, ynxu ma babu kowa gidan yaran duk sun tafi islamiyya, Hajiya nasan tana bangarenta yanxu haka, ai kinga dakin girkin da mai girki ta fito ta miko mana kumallo daxu da safe, nan xaki shiga, dakin ma ya kusa biyun wannan da muke ciki ae wllh" Jiddah ta mike ta dau babban samiran ta fita ta bar Maman Abdallah na linkin kaya, Babu kowa babban parlon kamar yanda Maman Abdallah tace, ko ina tsaf sae kamshin turaren wuta da ya kama parlon, Kasa karasawa can cikin parlon Jiddah tayi, tun da ta xo duniya bata ta6a ganin irin wannan parlon ba da ma komai na cikinsa, duk sai tsoro ya kamata, hanyar da taga Maman Abdallah ta bi daxu da safe ta bi ta d'an leka kofar da ta gani a bude ganin wasu mata biyu kuma har sun hada ido ta risina a hankali tace "Sannun ku da aiki" Duk suka amsa mata dayar tace "Shigo ki ajiye kwanon" Jiddah ta karasa kitchen din, ta kara masu sannu da aiki sannan ta ajiye kwanon, kanta a kasa tace "Me xa a kama maku?" Dayar matar tace "Aa babu komai 'yan mata, mun gode" Doguwar tace "Sae dai kawai wanke wanken dake cikin bahon wanke wanke, ba shi da yawa" Jiddah ta juya tana kallon sink da matar ke nuna mata, karasawa tayi wajen ta tsaya tana tunanin ta ya xata yi wanke wanke a takurarren waje haka sannan ta ina xa ta dinga xubar da ruwan wanke wanken, a hankali ta juya tana kallonsu tace "Ruwa da omo fa" Matar tace "Ga pampo a gabanki ki kunna, wannan roban kuma sabulun wanke wanke ne a ciki xaki matso ya fito"


 Bayan magrib Abuturrab yyi parking inda ya sa6a parking ya sauka motarsa ya kulle da kafa ya karasa kofar gidansu Jiddah. Yaro ya aika ciki yayi masa sallama da mutanen cikin gidan, Hansai ce xaune tsakar gida da kawayenta biyu, Hansai ta sharbe majina tana matse hawayen kumburarren idonta tace "Wllh xai aika, waye bai san cewar shaye shaye Iliya yake ba, ni dai baxan kwana gidan nan ba yau gaskiya gwara in tafi wani wajen in kwana"  Zulai tace "Aa nima dama ban bada shawaran ki kwana ba tunda ya furta sai ya kona gidan da kyar baxai aika ba" Ladi tace "Toh yanxu ina yarinyar nan ku ke tunanin xata tafi haka, wa gareta a duniyar ma gaba daya?" Hansai tace "Ai wannan magana ma bai taso ba, dolenta ta dawo duk inda ta tafi ta xo ta rabani da wannan mahaukacin mutumi, idan ya kona min gida gidan ubanwa xan koma kowa na ta kansa a rayuwar nan, dama gidan iyah nake ta tunanin ta shige amma duk dubawan da yan sanda suka yi a gidan babu ita babu alamarta" Kallon yaron da ya shigo suka yi gaba daya, yaron yace "Wai ana sallama a waje" Abuturrab ya daga kai bayan Hansai ta fito cikin gidan, ganinsa ta makale kofar xaure ta kasa karasowa, Ya karasa shi, yana dubanta yace "Ina yini?" Da kyar cikin rawar murya tace "Lafiya lau Alhaji, sannu da xuwa" kafin yace mata komai ta fashe da kuka tace "Muna cikin tashin hankali da alhini Alhaji" yana kallonta yace "Me ya faru?" Tana matsar kwalla tace "Tun jiya ake neman yarinyata har xuwa yanxu babu labarinta, ban san inda xan sa kaina ba xuciyata kamar ta fashe" Yayi shiru yana kallonta, ta sharbe majina tace "Shi kansa wanda ke da niyyar auren nata nan ya xo daxu da yamma ba irin tijaran da bai min ba har da ikirarin xai kona mana d'an gidan nan idan ba a fito masa da matarsa ba, wllh wllh bamu da masaniyar inda take, babban tashin hankalina ban san halin da take ciki ba yanxu" Yace "Yanxu ya ake ciki da shi wanda xai aureta din, baki basa kudin nasa bane?" Tace "Wllh yace baxai amsa ba, yanxu haka ma da kudin na tafi gun yan sanda na kai rahotu kasan sai an basu wani abu me d'an tsoka kafin su kula ka, sannan gidan radio da gidan talabijin duk na bi na rarraba masu kudin don su yi ta sanarwa har Allah ya bayyanata, yanxu maganar da nake maka ko dubu talatin ina jin kudin bai kai ba a ajiye a daki, 'ya ta bata fiye min komai ba a duniya?" Kallonta kawai Abuturrab yake bai ce komai ba, ta sake sharbe majina cikin rawar murya tace "In dai da wani taimakon da xaka mana yarinyar nan ta bayyana da wuri ka taimaka domin girman Allah Alhaji" Abuturrab yace "Ina shi madaurin auren nata?" Tace "Kawuna ne, tare da shi ma muke ta sintirin gidan radio da police station tun safe" Abuturrab yace "Ina son ki hadani da shi" Sosai gabanta ya fadi, yace "Yana da waya?" Da sauri tace "Aa bashi da shi, sai dai gobe in je in sanar masa, idan ka xo sai Bibalo ta kai ka" Abuturrab yace "Toh shkkn, nagode, sai goben" Daga haka ya juya ya bar wajen, ta bi sa da kallo gabanta na faduwa, da sauri ta koma ciki, Zulai tace "Waye hala?" Hansai ta share wani xufa da ya keto mata tace "Aa yan xuwa jaje ne, yanxu dai gidan Kawu Jibril xan tafi tare da Bibalo idan ya so sai mu kwana can kawai kada Iliya ya far mana cikin dare mu mutu" Ladi tace "Gaskiya kam, ku tafi can din kawai ku kwana, don kwana gidan nan ba karamin hatsari bane" Sai kusan karfe tara Hansai ta isa gidan kawun nata da Bibalo, Suna shiga d'an tsakar gidan yace "Me kuma kika xo yi nan kina neman ki ja min fitina Hansatu, ni nasan Iliya d'an daba ne amma bansan dabancin nasa ya kai haka ba, babu irin tijaran da iliya bai xo nan da tawagarsa sun min ba, in don dai shegiyar dubu ukun da kika bani ne cikin kudin sadakin yarinyar Allah ya kai mu gobe da safe in tafi in siyar da kaji na in baki kudinki, wannan tashin hankali har ina a kan dubu uku, wllh ban san tantirancin iliya ya kai har haka ba, to gaskiya baxai yiwu ba kuma ki fitar min daga gida kada ma yasan kina nan in shiga uku" Hansai ta fashe da kuka tace "Amma dai duk hatsin da yake kawo min ina dibar maka har rabin kwano wataran in kawo maka, har gawayi na sha cika maka leda me kayau kayau in kawo maka, kuma matsala ta samu sai ka rufe ido kace xaka koreni, cewa yayi fa xai kona gidanmu, idan na shashantar da batun ya babbake mu cikin dare fa?" Kawu Jibril yace "Toh ni cewa yayi xai ruguje gidan, ganinki ciki ai sai ya kara tunxurasa ya aikata hakan" Hansai na matsar kwalla tace "Yanxu duk ba wannan ba, dama wani Alhaji ne ya xo xai taimake mu kan lamarin da ganinsa babban mutum ne me fada aji, kuma tun mutuwar isuhu yake xuwa siyan awara ya mana ihisani, yanxu dai so yake ku hadu gobe a kan lamarin nan, don Allah ka sanar masa duk mun je gidan radio da gidajen talabijin din kaduna kai rahotu, dubu biyar xan baka kar kaji komai" Yace "Ina dubu biyar din?" Tace "Ba ni nace xan baka ba, fatanmu kawai ya taimakemu Allah ya bayyano mana da shegiyar yarinyar nan mu mika ma Iliya tsiyarsa ko ma sarara, don idan ba nemota aka yi ba aka damka ma Iliya bamu da sauran kwanciyar hankali wllh" Bata jira cewarsa ba ta shige dakin matarsa tana cewa "Lantana duk garin nan babu wanda bai xo min jajen abinda ke faruwa ba amma banda ke, ko ba komai ai sai ki ajiye duk wani tsiya dake tsakaninmu a matsayinki na musulma kixo ki jajanta min wannan musiba da ta sameni..."



07087865788....✍🏻 Start ur payment for the book because i am almost and almost done with free pages kar ku ji dippp an dakata💖

💖💖 *Jiddatul Khair**💖💖






_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻







10....



Washegari da asuba bayan an idar da sllh Ahmad ya fito rike da karamar jakarsa, dakin Ummansa ya shiga ya gaisheta tace "Da asuba xaka tafi Ahmad?" Yace "Ehh kar nayi missing train din ne" Umma tace "To kun yi da drivern ya xo da asuba ne ko wa xai kai ka train station din??" Yace "Aa Abuturrab xai kai ni" Umma tace "Abuturrab kuma? yana garin ne? Lafiya bai koma aiki ba" Ahmad yace "Ehh satin nan yana nan yace min" Umma tace "Toh Allah ya tsare, kayi addu'a dai" Yace "Ameen Umma, in sha Allah" Har ya kai kofa tace "Har xaka tafi gashi ka mance da drugs din nawa" Juyowa yayi da sauri yace "Oops, kiyi hakuri Umma Abuturrab xai kawo maki anjima in sha Allah" Tace "Toh Allah ya kai mu, Allah ya kiyaye hanya" sallama ya kara mata ya fita dakin, yana fita compound ya dau wayarsa ya shiga kiran Abuturrab, Abuturrab ya daga yace "Gani na shigo layin yanxu" Ahmad yace "Alright" Sai da suka yi nisa Abuturrab ya d'an kalli Ahmad yace "Medical report din da nace xaka min din fa?" Ahmad yace "Idan aka yi how will it reach you?" Abuturrab yace "The plane coming from Abuja to kano, xan yi ma pilot din magana abokina ne, sai ku hadu ka basa" Ahmad yace "Flight din karfe nawa ne?" Abuturrab yace "karfe uku" Ahmad ya tabe baki, Can ya kalli Abuturrab yace "Toh wai ma me ya hanaka komawa gun aiki kake neman medical report din karya Captain?" Abuturrab yace "That is none of ur interest, kai dai kawai kayi min medical report" Ahmad yace "Toh baxa ayi ba" Abuturrab bai kuma ce masa komai ba har suka iso Station din, Ahmad yace "Yauwa pls captain i will text some drugs now to you, na umma ne, xaka siya ka kai mata, i forgot to do so yesterday" Abuturrab yace "A hakan xan siya magani in kai mata? Kana ganin babu kaya jikina" Ahmad ya kallesa, Jallabiya ce milk color jikinsa, Ahmad yace "Shi kuma wannan bargo ne a jikinka kenan, beside ni bance da safe ba, wani pharmacy xaka samu a bude this early, kaga dole dai sai anjima" bude motar Ahmad yyi ya sauka yace "Thank you" Daga haka ya rufe motar ya shiga cikin tashan, Abuturrab ya bi sa da wani irin kallo, bayan few minutes ya ja motarsa ya bar wajen, Abuturrab ya na isa gida text din Ahmad na drugs din ya shigo, lkci daya alert din kudin drugs din ma ya shigo, tsaki Abuturrab yayi ya cire jallabiyan jikinsa ya shiga bathroom. Karfe goma saura Abuturrab ya fito dakinsa, bangaren step mum dinsa ya fara shiga ya gaisheta, tana gyara press dinta tace "Ina xuwa da sassafen nan haka, kai da nake tunanin ka dau hutu ne don ka huta" Yace "Xan je siya ma Umma drugs dinta ne" tace "Tohhh, Ahmad din fa?" Yace "Ya koma gun aiki" Tace "Toh nima ka siyo min Panadol night..." Yyi murmushi yace "Toh in sha Allah" Ya juya xai fita tace "Captain shiru shiru kuma baka turo abun ba, kada a siye wajen ne fa" Yace "Ehh ina son in sanar ma Ummi ne...." Da sauri tace "Sai ka sanar mata captain? Ina ce yanda ka dauketa haka ka daukeni?" Ya d'an yi shiru, sai kuma yyi murmushi yace "Toh nawa ne kika ce?" Tace "1.7m" yace "Toh xan tura in sha Allah" Tace "Yauwa ko kai fa, idan ka dawo anjima ka shigo da akwai wata maganan kuma" Yace "In sha Allah" daga haka ya fita, bangaren Ummi ya shiga, waya ne kare kunnenta, hakan yasa ya jingina da kofa ya jira har ta gama sannan ya risina ya gaisheta, tace "Lafiya lau..." yace "Jiya na shigo kin yi bacci" Tace "Ehh da wuri na kwanta" Yace "Ohk, sai na dawo" Daga haka ya fita dakin ta bi sa da ido. Abuturrab na shiga mota yayi ma Ahmad transfer din kudin da ya turo masa, sannan ya nufi wani babban pharmacy, ya siya duk drugs din, bai mance na Stepmum dinsa ba, ita ma ya siya mata pack har uku na drug din da tace sannan ya dau hanyar gidansu Ahmad, Sallama yyi bakin kofar parlon aka amsa masa sannan ya shiga, Umma na xaune parlon da Maman Abdallah dake xaune kasa Jiddah na gefenta alamar gaisheta suka shigo yi, daga kai Jiddah tayi suka hada ido da shi ta sunkuyar da kanta, karasowa cikin parlon yyi ya xauna yace "Ina kwana Umma" tace "Lafiya lau Aliyu, ashe kana garin" Kallonsa Jiddah tayi jin sunansa a karo na farko, ya shafa kai yace "Ehh ina nan Umma, ya karfin jiki?" Tace "Ah Alhmdlh sauki ya samu" Mikewa yayi ya karasa kusa da ita ya ajiye mata ledan maganin hannunsa yace "Ga drugs din naki Umma" tace "Toh nagode son, Allah yayi albarka" komawa yayi ya xauna yace "Ameen" tace "Ya su yaya?" Yace "Suna lafiya..." Tace "Toh a kawo maka breakfast?" Tana fadin haka ta mike, yace "Aa umma nayi breakfast a gida" Umma tace "Toh ga awara da Maman Abdallah da mai sunan yaya suka yi da safe, u will like it" Ya d'an kalli Jiddah da kanta ke kasa, Umma ta mike ta nufi kitchen, Abuturrab ya girgixa kai da sauri xai yi magana sai kuma yyi shiru ya sauke boyayyen ajiyar xuciya, Maman Abdallah na kallonsa da fara'a tace "Ina kwama abokin Dakta" Babu yabo babu fallasa yace "Lfya lau" Jiddah bata dago ba ita ma tace "Ina kwana" yace "Lafiya lau" Umma ta fito kitchen, sai ga mai aiki rike da karamin tray me dauke da awara da sauce da pepper soup din naman rago a rufe a wani warmer din, dinning ta kai ta ajiye, Umma na kallon Abuturrab tace "Gashi can a dining area son" Ya d'an yi murmushi yace "Nagode Umma" Tace "Ko a kawo maka nan?" Ya bi dining area din da kallo sannan yace "Ohk" Nan kusa da shi mai aikin ta kawo ta ajiye sannan ta wuce, Maman Abdallah ta mike cike da ladabi tace "To Hajiya xata maki gyaran ne yanxu??" Umma tace "Eh to, ko kuma ta bari gobe ai tana nan, ko ba kwana biyu ta xo yi maki ba?" Maman Abdallah tace "Tana nan tukun wllh Hajiya, don bata ma sa ranan tafiya ba" Umma tace "Toh shkkn gobe sai tayi min gyaran"  Maman Abdallah tace "Toh shkkn Allah ya kai mu Hajiya" Mikewa tayi tana kallon Jiddah tace "Toh mu je gobe sai kiyi aikin ko" Umma tace "To ki bar ta tayi kallo mana, tunda ke ba kallo kike ba" Maman Abdallah tayi dariya tace "Ehh kuma haka ne, tunda xan je maki kasuwa yanxu, ina fita hijabi kawai xan sa in tafi dama" Umma tace "Toh ki bar mata Abdallah ko baxai xauna ba" Maman Abdallah tace "Baxai xauna ba Hajiya, kiwuya ya gallabesa ai" Umma tayi murmushi tace "Toh sai kun dawo" Ko kadan Jiddah bata so haka ba duk da ba wai tana da niyyar bin ta kasuwan bane saboda tsoron kada wani da ya santa ya ganta a hanya amma xaman parlon ma bata so, Umma na lura da ita taga alamar she isn't comfortable, hakan yasa tace "Ko kuma ku tafi kasuwan kawai tare kada ta xauna shiru" Maman Abdallah da har ta nufi kofa tace "Dama tare nayi niyyar xa mu je, da kika ce ta xauna tayi kallo ne yasa nima nace ta xauna Hajiya" Sosai gaban Jiddah ya fadi, Maman Abdallah tace "Toh taso mu tafi kasuwan" Abuturrab dake xaune parlon yana sauraronsu yace "Tunda kallo take yi ki bar ta tayi kallonta mana" Kallonsa Umma tayi da mamaki, that's very odd of him, shi mutanen cikin gida ma baya shiga sabgarsu yayi masu magana balle wanda bai hada komai da su ba, Jiddah ta dago kanta amma bata ce komai ba, Umma ta d'an yi murmushi tace "Toh tayi xamanta" Maman Abdallah ta fita parlon bayan ta ce ma Umma sai ta dawo, Mikewa Umma tayi ta tafi kitchen sae gata ta dawo da karamin flask da mug ta ajiye ma Abuturrab tace "Kilan ta manta ne bata kawo maka ba..." yayi murmushi yace "Nagode Umma" Tace "Kana son madara?" Ya girgixa mata kai, tace "Yauwa nayi tunanin hakan, Ahmad ma bai fiye shan madaran ba" Sama ta nufa tace "If u are done ina daki" Yace "Alright" Bayan few minutes da tafiyarta ya daga kai ya kalli Jiddah, kanta na kasa tana wasa da hijab din jikinta maimakon kallon da aka barta tayi a parlon, ya bude flask din gabansa ya xuba ruwan Lipton cikin mug, wanda ya xuba ko rabin mug din bai yi ba, sae kamshi ruwan shayin ke yi, Calmly yace "Baki da wani damuwa a inda kike?" Ta dago ta kallesa sannan ta girgixa kai, bayan few seconds a hankali tace "Sai dai Baabarmu xa tayi ta nemana a gida" Kallonta yayi a takaice yace "Toh a mayar da ke wajenta kenan?" Shiru tayi tana kallonsa, can ta sauke idonta cikin sanyin murya tace "Iliyan xai iya sake biyo ni, ita ma xata iya kai ni wajensa" Abuturrab ya hade rai yace "Shine kuma xaki ce min Baabarki xata nemeki?" Bata ce komai ba, ya fara shan shayin hannunsa a hankali, tv ya dinga kallo kafin murya can kasa yace "Amma idan aka sauya maki shi wanda xai aureki yanxu da wani daban xaki amince da auren?" Kallonsa take babu ko kiftawa, yace "Ko baxa ki amince ba?" a sanyaye tace "Toh ai ban san waye shi ba" yace "Toh ni nasan sa" Tace "Toh in dai baya shaye shaye" Ya dinga kallonta sannan yace "Kina dai son kiyi aure kenan dama?" Hawaye ne ya kawo idonta tace "Baabarmu ce ke son inyi auren, kuma ai ba makaranta nake xuwa ba kawai sana'a muke yi" Bai kuma ce mata komai ba ya ci gaba da shan shayinsa, ta goge hawayen idonta, ya d'an kalleta yace "Wanda xan hada ku baya shaye shaye" A hankali tace "Toh" bude warmer din awaran yayi yana kallo yana d'an yatsine fuska, sai kuma ya bude na pepper soup dinma, lkci daya duk ya rufesu yace "Ki dauka ki kai maku can ki ci" Da sauri ta kallesa tace "Aa mun ci namu ai, kai dai ka ci ai naka ne" Ganin babu spoon a wajen tace "Bari in kawo maka cokali" Tana fadin haka ta mike tayi hanyar kitchen ya bi ta da ido sannan ya sake kallon warmer din awaran, ba a dau lkci ba ta dawo ta iso kusa da shi ta durkusa ta ajiye spoon din, sai kuma tace "In xuba maka?" Bata jira yace komai ba ta fara dibar masa awaran a plate sannan ta mika masa, calmly yace "Kwashe su nace baxan ci ba" Sauke idonta tayi a hankali sannan ta juye ta mayar cikin warmer din ta dau tray din ta mike ta wuce kitchen. Tana fitowa ta nufi kofa xata fita ya bi ta fa kallo yace "Kee, ina xaki?" Ta juyo tace "Xan xauna a waje ne" Authoritatively yace "Dawo nan ki xauna" a hankali ta dawo parlon ta koma ta rakube inda take xaune da farko ta xauna, ya ci gaba da shan shayinsa har ya gama ya ajiye mug din ya kalli agogo dake nuna sha biyu saura, mikewa yayi ya nufi kofa ya fita parlon, sai da ya shiga motarsa sannan ya kira Umma yace mata ya tafi. Yana cikin driving wayarsa ya fara ring, kallon wayar yayi ganin me kiransa ya nemi suitable place yayi parking sannan ya daga wayar, Daga daya bangaren aka ce "Captain da kansa barka da wuni..." Abuturrab yace "Ya kake Mu'axxam?" Mu'axxam yace "Alhmdlh Oga, Kayi scarce kawai wannan satin, daxu nake tambayarka Umar ke cewa ai baka shigo ba satin nan baka jin dadi" Abuturrab yace "Ehh ina kaduna" Mu'axxam yace "Toh ya jikin Captain!" Abuturrab yace "Alhmdlh" Mu'axxam yace "To maa sha Allah ranka shi dade" Abuturrab ya jinginar da kansa da kujeran motarsa a hankali yace "Kana ji na Mu'axxam?" Mu'axxam yace "Ina jin ka Oga" Abuturrab yace "Kana da mata ne?" Mu'axxam yayi dariya yace "Aa tukunna dai Oga Allah bai kawo lkcn ba" Abuturrab ya gyara xamansa yace "Ohk, wata yarinya na sama maka ko hakan yayi maka?" Mu'axxam yace "Ikon Allah, Oga ai baxa ka min xabin da xai cutar da ni ba nasani wllh" Abuturrab yace "To kar ka damu, in sha Allah xan maka duk wani abu da ya kamata na auren tunda nasan kilan ba wai ka shirya bane yanxu ae" Mu'axxam yace "Allah sarki Oga, amma wllh nayi farin ciki da wannan labarin naka, naji dadi sosai, dama tuntuni nake son yin auren amma babu halin yi sbda kasan komai yanxu tsada, shi kansa auren tsada, duk da iyayen nawa sun ma riga mu gidan gaskiya sai kanni da yayyi, da dangi, amma ginin da nake yi a kauyenmu shi ke cinye min kudi wllh...." Abuturrab yace "Babu damuwa, Allah xai rufa asiri, amma xuwa ranan alhamis ko Juma'ah ka dau leave din kwana biyu ka xo kaduna, a nan yarinyar take, but before then ma xa mu yi magana" Mu'axxam yace "In sha Allahu kuwa Oga, Allah ubangiji ya saka maka da alkhairi, ya biya maka bukatunka na alkhairi, ya ji kan iyaye da kakanni, wllh nayi farin ciki sosai Oga" Abuturrab yace "Maa sha Allah, xa mu yi magana" Daga haka ya katse wayar, wani ajiyar xuciya ya sauke... this is now almost settled saura mutanen Hayi kuma yanxu, tada motar yayi ya ci gaba da driving din nasa. Kawu Jibril sai muxurai yake daga inda yake xaune jin abinda Abuturrab ke cewa, Hansai ta marairaice tana wuri wuri da ido tace "Ni kuwa Alhaji sai nake ga fa kamar idan mun koma gun 'yan sandan nan maganar nan babba xata xama, Iliya fa bai bari mun yi baccin kirki ba daren jiya a gidan nan, ni har na sadakar jiya xan mutu, saboda ka sanar min da xuwanka yasa na koma can gida karfe goma nayi ta jiranka sai gashi ka xo bayan azahar sannan na kawo ka wajen kawun nawa" Abuturrab yace "Ae baraxanar da yake maku ne dalilin da yasa xa aje police station din yanxu ba wani abu ba..." Abokin Kawu Jibril dake xaune tare da su yace "Ni da xa aji ta nawa kawai a tafi wajen me unguwar yankin nan gaba daya, naga yana fada aji, idan abun ya gagaresa shi sai mu koma gun 'yan sanda don gaskiya wannan yaro Iliya d'an iska ne wllh, iyayensa ma ba isa suka yi da shi ba balle wani, amma gwara a fara sako mai anguwa a lamarin nan sannan ya kai mana gaban hukuma koko ya ku ka ga?" Hansai tace "Wallahi haka ma yafi, mu je aji ta bakin me anguwan tukunna" Kallonsu kawai Abuturrab yake with surprise, su fa ko damuwa da 6atan yarinyar basa yi, damuwarsu da tashin hankalinsu Iliya da ya sako su gaba, Kawu Jibril yace "Ko ya kace Alhaji??" D'an murmushi yayi yace "Ehh hakan yayi, aje wajen nasa" Hansai ta mike tana gyara takurarren mayafinta tace "Ba sai mun sha wahalan neman abun hawa ba da motarsa ya xo babba ce duk xata kwashe mu" Abuturrab bai ce komai ba ya mike shi ma duk suka bi bayansa xuwa kofar gida, sai bayan da suka shiga motar, Hansai tace "Ita Jiddah ganinta me sauki ne wllh, nasan tsoro ne yasa ta buya wani gun, amma ko ni daya sai in samota ai, bari dai a gama da tantirin nan" Ta madubi Abuturrab ya kalleta yace "Kinsan inda take kenan?" Da sauri Hansai tace "Aa amma nasan tana nan cikin hayi babu inda xata, kasanta da shige shige da yawace yawace tunda ba jin magana take ba, baxata rasa wanda xai boyeta ba na kwanakin nan kam" Abuturrab bai kuma cewa komai ba har dai suka isa gidan mai unguwar, xuwansu ya sa shi fitowa xuwa kan tabarmansa dake shimfide a waje da wasu dattijai uku ke xaune, Bayan an gaisa Kawu Jibril yace "Toh gashi dai mun xo gareka mai unguwa...." Sanin kawun nata bai iya magana ba yasa Hansai ta amshe bayan ta maka masa harara, ta marairaice tace "Mai unguwa muna cikin tashin hankali da fargaba wallahi, don a gaskiya bamu da wani tsaro xaman mu a hayi" Mai Anguwa yace "Ikon Allah, me ke faruwa? Har kin fita takaba ne Hansai?" Hansai ta sinne kai taki basa amsansa na karshe, Nan dai ta kwashe duk abinda ke faruwa karya da gaskiya ta sanar masa tana matsar kwalla da kyar, kallonta kawai Abuturrab ke yi da mamaki don maganganu da yawa ta canxa a kan yanda shi ta gaya masa, Mai Anguwa na jinjina kai yace "Ikon Allah Iliya dai guda, d'an gidan Malam Kabiru?" Hansai na shessheka tace "Shi wllh" Yace "Toh yanxu ke kin tabbata yarinyar na nan cikin garin nan, don lafiyarta shine babban abin dubawa yanxu..." Hansai tayi saurin cewa "Tana nan anguwar wllh Mai anguwa, ai nasan babu inda xata, kawai tsorata tayi yasa ta buya, yanxu idan na dage na kwalo mata kira xata fito wllh, kawai dai a gama da xancen yaron nan iliya tukun" Mai Anguwa ya girgixa kai yace "Toh yanxu xa a min kiran shi mahaifin Iliyan da shi kansa iliyan" Hansai ta xaro ido a mugun tsorace, Mai anguwan yace "Amma ke kika haifi yarinyar?" Hansai tace "Ehh 'ya ta ce" Yace "Yanxu ki rasa wanda xaki yarda ya nemi auren yar ki sai wannan takadirin Iliya? Waye bai san halinsa ba a garin nan, garin yaya har kika amince ya auri yar ki, duk uwa ta gari ai baxata so ma yar ta wannan yaro ba" Hansai ta fara matsar kwalla tace "Wallahi mahaifinta ya rasu, yarinyar nema take ta gagareni, baxan boye maka ba wllh bin maxa take, to shi nan rufa mana asiri yayi xai aureta, bayan haka kuma da tsohon bashi tsakaninsa da mahaifinta ina jin, kuma ni bani da halin biya gaskiya shi sa kawai na sadaukar ai ba a cire ran shiryuwar d'an mutum, ni ban cire ran shi ma xai shiryu ba sannan ai gwara shi kiriniya kawai yake yi, ita fa bin maxa take wllh, duk iya bakin kokarina kan yarinyar nan ya ci tura, tsoro nake kada ta jajibo min abun kunya shi sa da ya billo da xancen aurenta bani da yanda xan yi na hakura, don kowa tsoronta yake sbda halinta, sannan yana da xuciya yaron, me yi ne shi wllh" Sake baki mai Anguwa yyi yana kallonta, Abuturrab ma kallonta yake ko kiftawa babu with shock, ta sharce majina tace "Amma tunda abu ya xo da haka in da wani shawara da taimakon da xaka mana kawai kayi mai anguwa mun baka wuka da nama don a gaskiya muna cikin hatsari" Ya sauke wani ajiyar xuciya yace "Ikon Allah, to yanxu dai xan sa ayi kiran mahaifin yaron da shi kansa yaron sai a san abun yi, idan naga sulhun baxai yiwu ba sai kawai ku tafi wajen yan sanda su ma idan abun baxai sulhuntu a gunsu ba kotu xa su tura ku, amma abu me sauki a mayar ma yaron nan kudadensa ita kuma yarinya a nema mata mai hankali wanda yaji xai iya ya aureta...." Hansai ta fashe da kuka tace "Duk ba sai an kai ga haka ba wllh, Allah xai dubemu maganar ta mutu cikin ruwan sanyi, banda ta lalata rayuwarta idonta ya bude da maxa me xai sa in yi sha'awar yi mata aure bayan abinda xan kai ta da shi ma bani da shi, duka duka shekarta fa sha bakwai, har nawa take xan dage sai na mata aure banda ta lalace" Kawu Jibril dai ba baki sai idanuwa, sauran dattijan dake xaune gun sai kallon Hansai suke wasun su na tirr da ita a xuciya, don ko min lalacewar naka baxa hadasa da lalatattce ba da yayi fice a gari, Abuturrab ya d'an yi murmushi shi dai bai ce komai ba yana kara jinjina halin Hansai a ransa. Sai da suka yi la'asar Mahaifin iliya ya iso, sai ga iliya ma da abokansa yan daba irinsa sun iso wajen, Mai anguwa ya dakatar da abokan dake kokarin xaunawa kan takalmansu don tabarman ya cika yace "Ku yi hakuri yan samari kuyi jiransa ga benchi can" Suna gunguni suka bar wajen, Abuturrab ya kafe iliya da ido, ba lebbensa ba hatta fuskarsa ya dafe saboda xuke xuke.....



07087865788📚✍🏻

💖💖 *Jiddatul Khair*💖💖






_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻







11....


Mai Anguwa na kallon Iliya dake maxurai yace "Kai yanxu Iliyasu baka da masaniyar inda wannan yarinyar take?" cikin murya irin ta 'yan da6a yana nuna Hansai yace "Wllh wancan munafukar matar tasan inda take, kuma ni dama daga ita har wancan mutumin banxan na basu kwana daya su fito min da ita, matata ce fa, abinda har na bada sadaki me ya rage? Akuyar baabata fa na dauka na kai kasuwa na siyar na kai ma wancan mutumi da wasu kattin banxa a wajen kudin sadakina...." Mahaifin Iliya dai ba baki sai idanuwa, don kamar ma tsoronsa yake, Mai Anguwa yace "Toh yanxu idan ba a ga yarinyar nan har bayan kwana dayan da ka bada ba ya kake son ayi iliyasu?" Yace "Hansatu ta biyani duk hatsin da na dinga kawo mata a maimakon na kai ma baabata, ba hatsi kadai ba, lissafi xa mu yi tiryan tiryan ta biyani duk abinda na kashe sannan ta bani kudin sadakina dubu sha uku da kudin gaisuwa da sa rana da na kai, idan ba haka ba to wllh xan yi ta'asa, ai ba yau muka saba xaman kurkuku ba, banda yanxu da na fara gwangwan daga garin nan xuwa legas ai mu bama wata uku bamu leka gidan yan sanda ba daga nan mu garzaya kotu sannan gidan kaso, ko da mune da gaskiya ko mu ne bamu da gaskiya wannan ba sabon abu bane" Mai Anguwa ya kalli Hansai dake xare ido duk hankalinta a tashe sai xufa take yace "To ke kin ji Hansatu, lissafi yace xa ayi" kasa cewa komai tayi xufa sai karyo mata yake ta ko ina, yo ba gwara ya kasheta ba da ta ta6a kudin da Abuturrab ya bata, tabbb.... Mai Anguwa yace "Kai xuwa yaushe xa a baka kudin naka Iliyasu?" Ya gyara xama yace "Ae kafata kafar kudina, baxan bar wajen nan babu su ba, idan ko ba haka ba wllh wllh xan yi aika aika" Mai Anguwa ya kalli Hansai da jikinta ya dau rawa ta kasa cewa komai, Abuturrab ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yana kallon iliyan yace "Nawa ne gaba daya kudin naka?" Yace "Al-qur'an kudi na ya kusa dubu dari da wani abu, abinda duk xuwana legas sai na kawo mata garin alabo da gawayi ga hatsi da nake siya mata kwana biyu kwana uku... Sannan ga sadakina dubu sha uku na tinkiyar babaata, ga dubu biyar kudin gaisuwa da sa rana" Calmly Abuturrab yace "Kana da account?" Iliya yace "Aa amma abokina Kallamu na da shi, gaya can a xaune" Abuturrab yace "To ka kirasa ya bada account din" Iliya ya kwalo ma abokin nasa kallamu kira, Kallamu na karasowa Abuturrab yace "Account number dinka xaka bada" sai da ya dubo a waya sannan ya nuna ma Abuturrab, cikin few minutes Abuturrab yayi masa transfer din dubu dari da ashirin, sannan ya kalli Kallamu yace "Xa a maka alert na dubu dari da ashirin yanxu" Wani kara wayar yayi alamar shigowar alert din, Abuturrab ya amshi wayar ya duba sannan ya mika ma mai anguwa da sauran mutanen wajen duk suka ga dubu dari da ashirin, Hansai ta fashe da kuka sosai, Kawu Jibril kuwa Hamdala ya dinga yi a ransa yana sauke ajiyar xuciya, Hansai na kallon Abuturrab cikin kuka tace "Allah ya saka da alkhairi Alhaji, ka min taimakon da babu wanda ya ta6a min wllh a duniyar nan, nagode nagode, Allah ya kara maka budi da dukiya me yawa, wayyoo wani irin godiya kuma xan maka Alhaji" Abuturrab ya ki bata amsa dai a fili, Iliya ya mike yace "Toh amma fa duk ranan da jiddah ta bayyana wllh sai na aureta don na kwallafa rai, an kuma sa min ran ne, wllh wllh sai na aureta ko kuma in dauketa kawai in wuce legas in je a daura mana auren a can, so nawa aka yi hakan" Sake baki duk mutanen wajen suka yi suna kallonsa, ya kakkabe wandonsa ya kara gaba yana cewa "Sai in bani ne Iliya d'an me karfi ba" abokansa duk suka taso suka maya masa baya suna hailing dinsa, Mahaifinsa Malam Kabiru ya sauke ajiyar xuciya cikin sanyin murya yace "Abu me sauki da xa a samu wani ya auri yarinyar nan kawai, idan kuwa ba haka ba wllh xai aika abinda ya fada, kwakwalwarsa ya ta6u da dadewa mu kuma bamu da halin kai sa ko ina a dubasa, har cewa aka yi mu kai sa dawanau a kano to ina kudin?" Wani mutumi a wajen yace "Alhmdlh abinda xan fada kenan ka riga ni Malam kabiru, gwara kawai a aura mata wani tunda uwar ma tace ba ji take ba yarinyar, kun ga tana dawowa sai a kai ta dakinta kawai..." Abuturrab yace "Akwai wani yaro na, ina son nema masa aurenta yanxu" Kallonsa duk suka yi, Mai Anguwa yace "Toh in dai kasan halinsa ina ga wannan ba matsala bace amma kafin nan ya kamata ka gabatar mana da kanka..." Abuturrab ya shafa kansa a hankali yace "Ni sunana Aliyu Usman Umar... An haifeni nan cikin garin kaduna, ni matukin jirgin sama ne" Sake baki duk suka yi suna kallonsa kamar ranan suka ta6a ganin me tukin jirgin sama, yace "Gidan iyayena na nan Malali..." Mai Anguwa yace "Maa sha Allah Aliyu, to amma a ina kasan ita wannan yarinya da ake magana a kai?" Hansai ta amshe tace "Wllh daga siyan awara muka sa6a da shi, customer na ne shi da dadewa, da motarsa yake xuwa yyi parking ya siya har na dubu biyar dubu goma yana siya, toh shine jin rasuwar mai gidana sai ya kawo mana kudi dubi hamsin dubu dari, ta haka muka saba muna mutunci sosai da shi" Mai Anguwa yace "Ikon Allah" Abuturrab dai bai ce komai ba, Mai Anguwa yace "Toh amma shi wannan yaron da kake son hada yarinyar da shi wanene, sannan a ina yake?" Abuturrab yace "A kano yake, yana aikace aikace ne a airport din kano..." Hansai tace "Shi ma jirgin yake tukawa?" Ya girgixa kai yace "Aa..." Wani datijo dake xaune wajen da baxai wuce shekara sittin da takwas ba yayi gyaran murya yana taunan goransa yace "Amma fa wata kusan ya fi wata kusan nake ji ai... Tunda haka ne ni yanxu xan bada sadaki sai a daura min aure da ita wannan yarinyar...." Da mamaki Abuturrab ke kallonsa, can ya girgixa kai yace "Haba Baba ai addininmu ma bai ce haka ba, da taxara sosai tsakaninku da yarinyar nan...." Dattijon ya hade rai ya katse sa yace "Toh kai idan taimako kake son yi ka aureta mana kai da babu taxara me yawa tsakanin ku, shi fa wannan yaron da kake son hadata da shi nasan ba kowa bane d'an goge gogen iyapot ne, ni kuwa kowa yasan babu rashin ci babu rashin sha a gidana, matana uku ko wacce kuma tana da yara shidda shidda, shi me anguwan ai yasan wanene ni, auren yarinyar nan da xan yi tamkar jihadi xanyi don ance bin maza take" Kallonsa kawai Abuturrab ke yi with disgust, Dattijon ya ja tsaki yana ci gaba da taunan goronsa da jajayen hakoransa yace "Idan tsakani da Allah ne kai ka aureta mana yaro xaka wani kawo ma mutane fi'ili a nan, kaga mai anguwa a yanke min sadaki yanxu in bada a wuce wajen dama ina da niyyar auren kwanan nan" Yana fadin haka ya fiddo yan dari biyar biyar a aljihunsa, lokaci daya tunanin Abuturrab ya kwance, Hansai ganin 'yan dari biyar biyar tana d'an kame kame tace "Ai wllh tamkar taimako xaka yi Alhaji, wannan babban taimako ne, ni kaina da na haifeta bana shaidarta, kawai dai Allah ya shirya mana xuri'a" Alhajin ya murmusa yace "Babu komai ai tamkar jihadi xan yi, Ni mai anguwa ne waliyi na, ita kuma sai a samu wani...." Abuturrab ya rufe ido ya bude, yaji kansa ya fara juya masa ya dinga kallon tsohon nan da ya fara kirga kudin da ya ciro, rasa tunanin da xai yi yayi, he was totally lost, Hansai dake ta kallon kudin hannun tsohon tace "Kawai a daura tunda ga sadakin a kusa" Jibril yace "Wannan taimako ne me girma xaka yi Alhaji, Allah ya saka da alkhairi, tana dawowa daga gantalin da ta tafi sai a wanketa a kai maka gida kawai" Abuturrab ya kalli mai unguwa after gathering much courage yace "Ni xan aureta, sai ka xama waliyi na" Ba Hansai ba kowa na wajen sai da yayi mamaki, mai Anguwa wanda da alama dama bai yi na'am da daurin auren da wannan tsoho me suna Alhaji Saleh ba yace "Toh Madallah Aliyu" Tsohon ya d'an ja tsaki ya mayar da kudinsa aljihu, A nan take kuma aka daura auren Abuturrab da Jiddah a kan sadaki dubu arba'in, su kenan kudin jikinsa da ya ciro daxu bayan ya siya ma Umma drugs, Xaune kawai Abuturrab yake a wajen amma gaba daya he is absentminded and lost ga wani sanyi da yaji yana shigarsa kamar xai yi xaxxabi, har aka gama komai aka raba dabino da alawan da aka siya a nan cikin layi, Hansai dai ta kasa gane ko murna xata yi ko akasin haka, Ya xa ayi babban mutum kamar wannan gashi har yace jirgin da bata ta6a gani ba duk tsawon rayuwarta yake tukawa ace wai ya auri Jiddah maimakon Bibalo, tunanin hakan yasa taji wani bakin ciki ya tokareta a kirji, lkci daya hankalinta ya tashi sosai ba kadan ba ta dinga xufa daga inda take xaune, yanda take xufa haka Abuturrab ke xufan shi ma, tunda yake bai ta6a shiga rudani da confusion lkci guda irin wannan ba, wait!!! what did he just do now??? What have he done to his life?? A cikin lkci ba me tsawo ba aka gama komai, sama sama ya dinga jin albarkan da dattijan wajen ke sa masa na cewar ya rufa ma jiddah asiri duk da ga abinda aka ce tana yi amma hakan bai sa ya kyamaceta ba gashi ya taimaketa ya aureta domin nisantata daga cutarwan iliya, Abuturrab ya mika ma mutumin karshe hannu sannan ya mike a hankali ya nufi motarsa walking slowly kamar mara lafiya, yana shiga motarsa ya tada motar ya kashe Ac don sanyi yake ji sosai ya fara driving ya bar layin, ikon Allah ne kawai ya kai sa gida lafiya cause blurry ya dinga gani ga kansa dake juya masa ya dinga ganin komai double, ko parking din kirki bai iya yayi ma motar ba ya sauka ba tare da ya rufe ba ya shiga ciki mai gadi ya bi sa da kallo, direct dakinsa ya nufa ba tare da ya kalli kowa na parlon ba, duk suka bi sa da kallo, Aunty ta kalli Ummi, Ummi dai bata ce komai ba, Aunty ta mike ta bi bayansa da sauri, cikin bargo ta gansa ya lullube har kansa, da mamaki tace "Are you okay Aliyu???" Bai iya ya bata amsa ba, ta sauke bargon a hankali ganin he is shivering so much, da mamaki tace "Baka jin dadi ne?" Ya gyada mata kai kawai, tace "Subhanallah, let me switch off the Ac"




Nan na kawo karshen free pages na *Jiddatul Khair* in sha Allah, and the paid book is 500 Via


👇🏻

3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah.....


 And u show ur evidence of payment via my WhatsApp Number 👉🏻 07087865788.....



Plss just WhatsApp ban fiye son phone call ba, and i am begging you don't come to my DM without any concrete reason, it's tiring wllh....😓😰 just come, patronize, i save ur number, and i add u to my groups... Shikenan


 Thanks and i love you all as u patronize.💖

Kashe Ac din dakin Aunty tayi ta sauke curtains ta dawo ta xauna kusa da shi tace "Sannu, ko dai a kira Dr? amma daga ina kake haka?" Girgixa mata kai kawai yayi don bai jin ma xai iya magana, ta mike ta fita don daukan wayarta ta kira Dr din, Tana cikin dialing number likitan ta kalli Ummi tace "Baya jin dadi ne wllh" Ummi tace "Ikon Allah, to Allah ya sauwake" Aunty na gama kiran likitan ta koma daki..... Abu kamar wasa Abuturrab har da karin ruwa, he was so weak and sick, sae bayan isha family Dr din nasu ya bar gidan. Karfe goma da yan mintuna wayar Abuturrab dake gaban mirror din dakin Aunty ya fara ring Aunty ta dau wayar ganin Ahmad ne ta kyabe baki ta dauka don tun daxu yake kira, bayan ya gaisheta yace "Ya tashi Aunty?" A takaice tace "Aa..... ko minti sha biyar ban yi da fitowa daga dakin ba" Ahmad ya d'an yi shiru sannan yace "Amma jikin da sauki?" Tace "Eh toh amma har yanxu his temperature is high" Yace "Toh Allah ya sauwake, likitan ya tafi?" Aunty tace "Ehh" Yace "Toh Allah ya bashi lafiya" Aunty tace "Ameen" daga yayi mata sallama ya katse wayar, Aunty ta ajiye wayar ta koma bangaren Abuturrab ta bude kofar dakinsa, tsaye taga Ummi a dakin kusa da shi tana kallonsa, Aunty tace "Ya tashi ne?" Ummi ta juyo tace "Aa" Aunty ta karasa kusa da shi ta xauna ta sauke duvet din tana kallonsa ta kai hannu goshinsa, taji har sannan da xafi, juyawa Ummi tayi ta fita daga dakin... a hankali Abuturrab ya bude idonsa da yayi masa nauyi sbda ciwon kai, ji yake kamar ana sara masa goshinsa, Aunty tace "Sannu son, ya jikin?" Bai iya ya bata amsa ba ya sake lumshe ido, tace "Baka ci komai ba, in hado maka shayi?" Girgixa mata kai yayi, bai sake bude idonsa ba har ta ga alamar ya koma bacci, ta mike ta fita daga dakin ta kulle masa kofar. Can cikin dare Abuturrab ya farka, da kyar ya mike xaune coz he was pressed, ko hasken fitilan dakin bai so don kara masa ciwon kai yake yi, ya kalli drip din hannunsa da ya kusa rabi, ya mike tsaye da kyar yana jin jiri ya kashe ruwan ya bar cannula din kadai a hannunsa bayan yyi disconnecting dinsa daga jikin ruwan, kamar me counting steps dinsa ya nufi bandaki ya shiga duk da jirin da yake ji, da alwalansa ya fito ya xauna gefen gado ya dafe kansa, ko kadan bai son tuna komai da ya faru yau, it's making him down and weak, Bude kofar dakin aka yi Aunty ta shigo ya daga kai da sauri, tace "Ka tashi Abuturrab, sannu ya jikin" A hankali yace "Alhmdlh" Ta karasa kusa da shi tana dialing number Ahmad don kiransa ne ma ya tasheta yana fara ring tace "Duk abokinka ya takurani gashi nan ni dai" Tana fadin haka ta mika ma Abuturrab wayar, ya amsa ya kai kunne yyi shiru, daga daya bangaren Ahmad yace "How are you feeling captain?" Cikin sanyin murya yace "Alhmdlh" Ahmad yace "Ka samu ka ci wani abun kuwa?" Abuturrab yace "I will take tea now" Ahmad yace "Do so plss, Dr Shariff din ya baka drugs ne?" Abuturrab yace "I just woke up ban sani ba" Ahmad yace "Ohk, ruwan yayi rabi yanxu?" Abuturrab ya kalli drip din sannan yace "Almost" Ahmad yace "Toh Allah ya sauwake" Abuturrab yace "Ameen" sallama Ahmad yyi masa ya katse wayar, ba a dau lkci ba Aunty ta dawo dakin rike da cup din tea ta mika ma Abuturrab tace "Gashi ka samu ka sha" Ba musu ya amsa, tana nan tsaye sai da ta tabbatar ya sha shayin sannan ta amshi cup din ta fita, Mikewa yayi ya koma bathroom ya wanke bakinsa ya fito ya dau pray mat ya shimfida ya hau sannan ya tada sllh, ko da Aunty ta dawo dakin ganin yana sallah ta koma dakinta, ya jima xaune kan darduma daga bisanni ya mike a hankali ya dauke darduman ya koma kan gado, mayar da ruwan yyi ya kashe wuta ya kwanta ya lullube jikinsa yana jin kamar wani sabon xaxxabin xai sake rufesa. Da asuba duk yanda Abuturrab ya so tashi yin sllh kasawa yyi, Karfe shidda da yan mintuna Aunty ta shigo dakin, ta kunna wuta ta karasa gun gadon ta cire duvet din da ya rufe har kansa da shi, bude ido yyi a hankali, tace "Ka samu kayi sallah kuwa?" Girgixa mata kai yayi, tace "Da ka daure ka tashi, amma how are you feeling now?" A hankali yace "Alhamdulillah" mikewa yyi xaune, tace "Let me get u something to take sai ka sha magungunan idan ka idar da sallahn" Fita tayi dakin, yayi karfin halin tashi ya cire ruwan da ya rage kiris ya kare sannan ya shiga bandaki, yana sallah ta dawo dakin, ta ajiye masa cup din shayi da ledan drugs din ta nemi waje ta xauna har ya idar da sallahn sannan ta sa ya dau shayin da ta hada masa ya sha.... Karfe goma na safen Abuturrab na bedroom dinsa hannunsa rike da bowl din pepper soup, Ummi ce tsaye dakin tana kallonsa, ko minti biyar ba ayi da fitan family Dr dinsu daga dakin ba, bayan few minutes ya d'an kalli Ummin tasa, ji yayi gabansa ya fadi sosai, a hankali yace "Why don't u sit Ummi?" Ummi tace "Am okay here" Ba tare da ya kalleta ba yace "Aunty fa?" Tace "She is in the kitchen" Bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da shan pepper soup din hannunsa a hankali, Ummi tace "Kun yi magana da Abban naka? Ya kira kana bacci daxu" Ya gyada kai yace "Ehh Aunty ta bani mun yi waya" Tace "Ohk" Juyawa tayi ta fita dakin ya bi ta da kallo, lkci daya jikinsa yyi sanyi, ya ajiye bowl din hannunsa ya jingina da gadon da yake xaune, he needs someone to talk to about this unfavorable issue, he needs to share this with someone that's understandable, who will this be, rike kansa yayi yana nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.... Xuwa yamma Abuturrab ya d'an samu saukin ciwon kan dake damunsa, ya fito wanka kenan yana goge kansa da karamin towel din hannunsa aka bude kofar dakin, Ahmad ne ya shigo dakin hade da sallama, ganin Abuturrab a tsaye, ya tsaya daga bakin kofar ya rike waist dinsa yace "This is better, and I'm glad i saw u this way" Abuturrab bai ce masa komai ba, Ahmad ya d'an yi murmushi yace "Medical report dae ya xama na gaske yanxu kenan" Abuturrab ya kallesa yace "Ka taho min dashi?" Ahmad ya karasa ya xauna gefen gado yace "How are you feeling now?" Abuturrab ya nufi gaban mirror a hankali yace "Alhamdulillah" Ahmad yace "But dama baka jin dadi ne, coz naga sickness din yyi striking dinka so hard, you look lean...." Ta madubi Abuturrab ke kallonsa bai ce komai ba, Ahmad yace "Ba shiru xaka min ba, i left my work for ur sake na biyo train" Abuturrab yace "Da baka dawo ba ma ni xan kiraka ka dawo, i have been expecting you" Ahmad yace "Hope you are feeling much better now?" A hankali Abuturrab yace "Not at all.... We need to talk Ahmad" Keenly Ahmad ke kallonsa cause he can see how worried and confuse he looks, Mikewa Ahmad yyi ya karasa kusa da shi yace "Tell me what's wrong Captain?" Kasa ce masa komai Abuturrab yayi, Ahmad ya koma ya xauna yace "To ka gama shiryawa mu yi magana" Yana kallon Abuturrab har ya gama shiryawa ya dawo ya xauna gefen gadon shi ma, Ahmad yace "Me ke faruwa tell me" Abuturrab ya shafa kansa a hankali kamar me tunanin ta inda xai fara, bude kofar dakin aka yi Aunty ta shigo rike da bowl din fruit salad biyu, murmushi tayi ganin Abuturrab tace "Alhmdlh, son jiki yayi kyau, you are looking much much better and healthier now" Abuturrab yyi murmushin karfin hali bai dai ce komai ba, ta karasa ta mika masa Bowl daya na fruit salad din tace "I made this for u" Amsa yayi yace "Thank you Aunty" Kujeran dakin ta xauna tana shan fruit salad din daya bowl din hannunta tace "Abbanku ma ya kara kira yanxu nace da sauki, shi ma duk ya damu" Ahmad da ya d'an hade rai yace "Ina yini..." Ba tare da ta kallesa ba tace "Lafiya lau" magana ta ci gaba da yi da Abuturrab dake shan fruit din hannunsa, Ahmad ya mike yace "Alright Captain, sai ka xo can gidan namu, i will be leaving now" Abuturrab ya kallesa da sauri, ta gefen ido Aunty ta harari Ahmad tana ci gaba da shan fruits salad dinta, Abuturrab yace "Ai nace maka nima xan fita Ina son in sha iskan waje" Ahmad yace "Okay ka sameni mota idan ka gama, i will wait" daga haka yace ma Aunty "Sai anjima" ko tankasa bata yi ba har ya fita ya kulle kofar dakin, Aunty tace "Yaushe har ka farfado xaka wani fita Abuturrab? Shi Ahmad din bashi da hankali ne ko don ya xo lkcn da jikinka yayi kyau, kana fama da kanka ina wani fita idan ba neman magana ba?" Abuturrab ya shafa kansa yace "Aunty na gaji da xaman gidan ne, ni nace masa mu fita, ba shi ba" Ta tabe baki tace "Toh ai shkkn...." Bayan kusan minti ashirin Abuturrab ya fita xuwa gun Ahmad bayan ya sanar ma Ummi xai je gidansu Ahmad din, Sbda yanda idonsa ya fada yasa shi saka bak'in spec dinsa, kananun kaya ne jikinsa wani sanyayyen kamshi na tashi jikinsa, kana ganinsa kasan he is still recovering, he still looks weak, Kallonsa kawai Ahmad yake yi har ya karaso ya shiga front seat, Ahmad na kallonsa da d'an damuwa yace "Wai malaria ne ya kamaka haka Captain, ka rame fa, kamar wanda yayi sati a kwance" Captain bai ce masa komai ba, Ahmad ya tada motar suka bar layin. Karfe biyar da few minutes suka isa gidansu Ahmad, Abuturrab yace "Ka bar motar a waje ba dadewa xan yi ba xaka maida ni gida ynxu" Hakan yasa Ahmad yyi parking a waje, Abuturrab ya bude motar ya sauka ya nufi cikin compound din, Ahmad ma ya sauka ya rufe motarsa ya bi bayansa, sosai gaban Abuturrab ya fadi bayan ya shiga compound din sun yi ido hudu da Jiddah dake tsaye ta jingina da bango a bakin tap din dake cikin compound din ta tara bucket.....


Abuturrab ya dauke idonsa hade da daure fuska yana tafiya, murya can kasa Jiddah tace "Ina yini" Bai kara kallon inda take ba balle ya tanka ta, tafiyarsa kawai yake kamar bai ji ta ba, Ta kalli Ahmad da ya shigo compound din shi ma, ta sauke idonta tace "Ina yini?" Murmushi yayi yace "Lafiya lau, sannu da aiki" Juyawa tayi tana kallon ruwan da take jiran ya cika, Ahmad ya bi bayan Abuturrab da har ya kusa main entrance din gidan, babu kowa parlon da Ahmad ya shiga sai kamshin girki dake tashi alamar ana girki a kitchen, bedroom dinsa ya nufa ya tadda Abuturrab a kwance idonsa a lumshe, ya karasa ciki ya kulle kofar yana kallonsa yace "Are you alright?" A hankali Abuturrab ya bude idon sae dai bai ce komai ba, cike da karfin hali ya mike xaune looking so dumbfounded, Ahmad ya xauna yana facing dinsa with seriousness yace "Tell me what is happening Captain, you look disturbed" Abuturrab ya shafa kansa ya lumshe ido wishing all this nonsense would turn out to be a dream, kara bude ido yyi, gathering much courage yace "I am in trouble Ahmad" Tuni yanayin Ahmad ya sauya, ya kafe sa da ido, can yace "Tell me what is it, me ya faru??" Cikin sanyi Abuturrab yace "Yes i will, amma kuma mafita nake nema a wajenka don Allah, and this should be a secret between just i and you for now plsss" Shi dai Ahmad kallonsa kawai yake waiting to here what is this that's weighing down his frnd har haka, Abuturrab yayi kasa da murya da kyar ya fara magna yace "Yarinyar da kake siyan awara wajenta a hayi, u remember her right?" Bude ido Ahmad yyi sosai yana kallonsa yana jiran jin abinda ya sameta, A hankali Abuturrab ya shiga basa labarin tun daga xuwansa siya ma Umma awara sanda bata da lafiya, abinda ya faru a ranan, har ixuwa yanxu da suke xaune tare da Ahmad a daki, Abuturrab ya share xufan goshinsa yana kallon Ahmad da ya bude baki for almost five minutes now ya kasa rufewa, Abuturrab ya hade rai yace "Don Allah ka daina kallona haka Ahmad ka bani mafita, find a way out for me, i am stuck, ban ta6a shiga rudani iya rayuwata kamar na wannan lokacin ba, what have i done to my self daga taimako??" Sae a sannan Ahmad ya kulle bakin da sauri, wato kawai sae yake ganin labarin da Abuturrab ya basa kamar tatsuniya, or is he dreaming?? Ya kifta ido kusan sau hudu sannan ya kafe Abuturrab da ido, he is finding it hard to believe all what Abuturrab said now, as if counting his words yace "Wait Captain... Wllh kamar fa ban fahimce wannan gajeran labarin nan naka ba, i am confus...." Captain yyi tapping dinsa on a serious note yace "You just have to believe all what i said, duk abinda na gaya maka hakan yake stop confusing ur self" Ahmad na nunasa da yatsa cikin wani expression yace "Are you for real Aliyu??" Abuturrab ya kafe sa da ido regretting everything from the start, Ahmad ya buda ido sosai yana kara digesting din lamarin with shock, he knows Abuturrab have a soft heart, a very soft heart kuwa, yana damuwa sosai da matsalan da ba tasa ba, he prioritized damuwar wasu kan nasa, but he never thought ya kai wannan extent din, bai ta6a tunanin Abuturrab can go this deep ba, what is baffling him more is yanda this time around taimakon nasa yyi sa ga talaka sosai, don Ahmad bai ta6a ganin yayi stressing kan lamarin local people ba, tsakaninsa da su sadaka if the need arize, babu wani magana me tsayi dake hadasa da su, Abuturrab ya hade rai ganin irin kallon da Ahmad ke masa yace "Nayi kuskuren gaya maka damuwata ne da ya sa ka min shiru Ahmad? Don't u have anything to say to me pls?" Lkci daya yanayin Abuturrab ya kara sauyawa gaba daya, sai yake jin wani sabon xaxxabi xai rufesa, da kyar Ahmad na nunasa yace "You mean you are married now without our knowledge Captain??" Cakumosa Abuturrab yyi a fusace yana huci yace "Wannan kake kira da aure? Haka ake auren dama? Mahaukaci ne ni da xan amince nayi aure yanxu" Ahmad yyi iya kokarin ganin bai yi dariyar da ya taho masa ba ganin how furious Abuturrab was, Turasa Abuturrab yyi ya mike yana jin xufa na keto masa yace "Ka gaya min meye abun yi ynxu, i have never been this confused all my life, what have i done to my self, taimako fa kawai nayi kokarin yi...." Lkci daya idonsa ya kada ya dawo ya xauna ya rike kansa, Wani tausayinsa Ahmad ya ji har ransa, hakan yasa kawai ya kawar da dariyar dake cin sa gaba daya a xuciyarsa, ya kwantar da murya yace "let's talk brother" Abuturrab ya dago da idanuwansa da suka yi ja yana kallonsa, Ahmad yyi shiru yana tunanin yanda Abuturrab yayi making fool out of him, ko da wasa bai ta6a gaya masa abinda yake yi ba sai da abu ya 6aci, har da raina masa wayo wai shu murhu yake gani a hayi, wani boyayyen ajiyar xuciya ya sauke yyi kasa da murya yace "before i say anything just tell me what u have in mind now about this issue?" A hankali Abuturrab ya kai hannu aljihunsa ya fiddo farar takarda da biro yana kallon Ahmad, Ahmad ya buda ido sosai, lkci daya ya girgixa kai yace "Nooo.... This isn't a solution, idan ka rubuta takardan nan dole gida xata koma ga axxalumar step mum dinta, kaga anyi ba ayi ba kenan, and at the end wannan mahaukacin kilan yace sae ya aureta..." Abuturrab yace "But I can't sleep in peace again today in har ina tuna auren warce ke kaina, baxan ta6a samun nutsuwa ba matsawar ban aiwatar da haka ba, me of all people fa?? Where will i start from with that girl, me xanyi da ita a rayuwata?? Ko a mai aiki wllh wllh wllh baxan yi employ dinta ba, baxan bata aiki ba a gida na dai, western education zero, islamic education zero, wayewa zero, tsafta zero, mu'amalat zero, kyau zero.... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ahmad dake ta kallonsa bbu ko kiftawa ya girgixa kai yana d'an murmushi yace "A bangaren kyau kuma ka so kanka Captain...." a mugun fusace Abuturrab ya fixgosa yace "What the heck.... Kyau xan ci?? Tsaftar fa?? Ilimin fa?? Wait wai kai Ahmad kana tunanin no matter what xan iya xama da local yarinyar nan a matsayin matata? Noo plss... God forbid, this is more like an abomination to me, idan na sake kwana da auren yarinyar nan a kaina yau wllh nasan gobe xan iya xarewa a wuce dani psychiatry" Ahmad ya lumshe ido ya bude yace "Duk na fahimce ka, amma idan ka saketa ynxu Captain ka gaya min meye makomarta? Ina kake son taje? Kasan xamanta tare da maigadin gidan nan da matarsa ba abu bane da xai ja lkci coz daki daya ne da su" Abuturrab ya lumshe ido ya bude yace "I don't care anymore, saninta da tausayinta ne duk ya ja min plight da nake ciki ynxu..." Ahmad yace "Ohk Now tell me, after the divorce what next, ya xa kayi da lamarinta? Kaga tamkar ka lalata aikin ladan da kayi ne daga farko har karshe" Abuturrab na masa wani kallo yace "What are you insinuating now? Kar in saketa kake nufi ko me?" Ahmad ya daga hannu da sauri yace "Aa ni bance haka ba" Abuturrab ya ja wani tsaki yace "Xan saketa, kuma xan ci gaba da mata taimakon da nayi niyya" Ahmad yace "Good, ta yaya?" Abuturrab yace "Under my roof" Ahmad yace "Elaborate plss" Abuturrab yace "I'm thinking i will have no choice but to explain everything that transpired to my Dad, xan ma Abbana bayanin komai, xan kuma kai sa har gun me anguwan, i don't want to look foolish, you get? Then he can explain everything to Ummi coz ni baxan iya ba...." Ahmad ya katse sa yace "You are confusing me, kai da kake da intention sakinta yanxu me xai kai magana kuma kunnen Abba?" Abuturrab yace "Don nace xan saketa ba yana nufin ai baxan yi duk abinda nayi niyya a kanta ba, wllh xan saketa without anyone's knowledge, daga ni sai kai ne xa mu san babu aure tsakanina da ita, amma she will be under my care xan kula da ita har sanda xata samu me aurenta" Ahmad da ke ta kallonsa baki bude yace "Under ur care as how?? a gidanku xaka ajiyeta kenan?" Abuturrab ya girgixa kai yace "A gidana dai" Wani tsaki Ahmad ya ja yace "See the way u are talking like an illiterate plss, ba matarka ba ba komai ba xaka ajiye a gidanka kuna rayuwa tare Captain, ko dai nine ban fahimce abinda kake nufi ba, ka min bayani yanda xan gane" Abuturrab ya masa wani kallo yace "Toh me xamanta a gidana xai kara ko xai rage? Did i look like someone that have anything to do with that girl? Haba Ahmad, don dai ta kwana ta tashi tayi girki ta ci abinci ta tafi boko ko islamiyya, xamanta a gidan nan da rashin xamanta duk daya to me, Monday to Friday ina gun aiki, na dawo sunday and Saturday, wait tell me what u have in mind first" Ahmad yace "Gaskiya baxan yarda da wannan rashin tunanin ba, kana cikakken namiji ka xauna gida daya da mace...." Mikewa Abuturrab yyi looking super angry yace "Amma ka gama da ni Ahmad, mace me tsafta iya tsafta ina xulumi da tunanin yanda xanyi tarayya da ita balle wannan, haba.. haba wannan xagina kayi wllh, ta ina xan fara abinda kake tunani, did you know who i am kuwa Ahmad, me xanyi da warce tayi tsaftar yarinyar nan sau biyar ma balle ita" wani kallo kawai Ahmad ke yi masa Abuturrab yace "You just insulted me wllh, and i am seriously not happy about it" Ahmad ya tabe baki ya ki basa amsa, Abuturrab yace "Sabida wannan kaddaran da ya fada min ma dole nan da lkci ba mai tsayi ba in auri Aneesah" Ahmad yace "Sai ka ajiye su gida daya kenan?" Abuturrab yace "Yes, kaga Aneesah ta samu me taimakonta aikace aikace kenan" Ahmad yace "Gaskiya ne wannan, to yanxu abinda nake son sani shine, idan ka rubuta takardan ba yarinyar xaka yi kenan ko ko ya xaka yi?" Abuturrab yace "I will do the rightful thing, giving her or not giving her" Ahmad yace "To su kuma can iyayen nata xaka bari su san tana wajenka?" Abuturrab yace "There is no need, idan ta samu 'yan cin kanta xata je garesu watarana" Ahmad ya sauke ajiyar xuciya. Karasawa Abuturrab yyi jikin window yana kallon waje, Ahmad dai sae kallonsa yake, shi har sannan ganin lamarin yake kamar a film, abinda ya fi daure masa kai yanda Abuturrab ya boye masa komai from beginning sae ynxu da abu ya baci, murmushi yyi yana gyada kai yana tunanin irin dariya da tsokanar da xae fara yi ma Abuturrab idan hankalinsa ya kwanta, sae dae deep down him he is so Happy for this young girl don yasan Abuturrab baxae ta6a cutarta ba, with him her future is super bright, komai na rayuwa baxai ji kyashin yi mata ba, maganar sakin da Abuturrab yyi ne kadai bai ji dadi ba har cikin ransa. Ana kiran magrib suka fita tare xuwa masallaci bayan sun yi alwala, Jiddah ce kadai xaune tsakar gida da buta a gabanta, tunda ta hangosu daga nisa tayi kasa da kanta tana alwalanta,, Kallonta kawai Ahmad ke yi yana mamakin yanda ita da gogan suka iya pretending, ko da wasa bata ta6a nuna masa ta san sa ba, murmushi kawai yake yi yana kara jinjina wannan lamari me abun mamaki, Abuturrab dai ko kallon inda take bai yi ba har ya fita gate din, Ahmad yyi murmushi ya bi bayansa, shi dai ya san ko giyar wake Abuturrab ya sha baxai yi accepting yarinyar nan matsayin matarsa ba, bayan an idar da sallah sun fito masallaci Ahmad na kallon Abuturrab yace "She isn't comfortable staying with the gate man and his wife, may be because daki daya ne, kaga baxai yiwu suna ciki tana ciki ba shi yasa take yawan xaman waje, na lura da hakan" Abuturrab bai ce masa komai ba har suka shiga compound din, sae a sannan yace "Idan na gaida Umma xaka saukeni gida yanxu" Suna bude kofar parlon Abuturrab yyi ido hudu da jiddah tana tsaye daga kusa da kofan parlon, sunkuyar da kanta tayi ta koma gefe cikin sanyin murya tace "Ina yini" Bai ce komai ba ya karasa cikin parlon, Ahmad ya sakar mata murmushi yace "Ki karasa ciki mana, kin tsaya a bakin kofa" Tana jan yatsunta tace "Abinci xan amsa inji Maman Abdallah" Ahmad yace "Toh ki karasa ciki" Ta d'an karasa amma ba can cikin parlon ba tace "Na gaya ma Aunty Huraira tace toh" Umma ce ta fito kitchen ganin jiddah tace "Yau ma jikin kofar kika makale Jiddah?" Jiddah ta sunkuyar da kanta, Umma tace "Ma su sunan ki kuwa suna da sakin jiki ke ban san ya haka ba" Ahmad yace "Bakuwa ku ka yi gidan Umma" Umma tace "Ehh bakuwar Amina ce, gashi har yau taki sakewa" Ahmad ya kalleta yana murmushi yace "Ya sunanki?" A hankali tace "Jiddah" tausayinta Ahmad ya ji har cikin ransa, without allowing that to show... ya buda ido yace "Lahh Ummin Captain ce ashe" Umma tayi murmushi tace "Kai ba Umminka bace kenan?"  Ahmad ya shafa kansa yana murmushi ya kalli Abuturrab da ya hade rai kamar bai ta6a dariya ba yana kallon TV, yace "Captain ga mai sunan Ummin mu fa" Umma na kallon Jiddah tace "Karasa kitchen din ki ga ko ta gama xuba maki, kinji" Kitchen din Jiddah ta nufa ta shiga ciki, Abuturrab ya gaida Umma a hankali, amsawa tayi da murmushi tace "Alhmdlh jiki yayi sauki kenan, ai daxu da muka je kana bacci" D'an murmushin karfin hali yayi yace "Naji sauki Umma" Tace "Toh Allah ya kara lafiya Son, bari a kawo maku abinci yanxu" A nan parlon ta barsa shi da Ahmad, Jiddah ta fito rike da abinci, bata yadda ta kallesu ba ta nufi kofa kamar mara gaskiya ta fita... Washegari Thursday karfe tara da yan mintuna Abuturrab ya fito daga bedroom dinsa, Bangaren Abbansa ya nufa, sai da ya bude kofar parlon Abbansa yace "Alhmdlh.... Much better now" sisters dinsa ne xaune parlon suna masa ya jiki kamar baxai amsa ba kuma bayan ya isa bakin kofar parlon Abbansu ya amsa sannan ya shiga parlon da sallama, Aunty ce tare da Abba a parlon, tun da ya shigo Abbansa ke kallonsa, ya xauna kasan carpet yace "Sannu da dawowa Abba" Abba yace "How are you feeling now?" A hankali yace "Alhmdlh na ji sauki" Abba yace "Allah ya kara lafiya" Aunty tace "Jiki kam Alhmdlh, kamar ba shi ba shekaranjiya" Abba na kallonsa yace "Kana stressing kanka da yawa ko, you look stressed out" Abuturrab ya girgixa kai yace "Aa Abba" Aunty tace "Kamata yayi ka dau hutun ko da sati biyu ne ka huta har ka murmure gaba daya, you look so lean" Shi dai Abuturrab murmushi kawai yayi bai ce komai ba, Aunty ta mike ta nufi kofa bayan ta dau tray din da ta kawo ma Abba shayi ta fita, Abba na kallon Abuturrab yace "Hope babu damuwa Aliyu?" A hankali Abuturrab yace "Akwai Abba" Da mamaki Abba ke kallonsa, kafin yace "Talk to me, meye damuwar" Abuturrab ya kallesa lkci daya jikinsa yayi sanyi, cikin sanyin murya yace "Abba i did something...." Sai kuma yayi shiru, Abba ya ajiye cup din hannunsa yana kallonsa da kyau yace "Feel free son, tell me what happened" Abuturrab ya sunkuyar da kansa nan ya sanar ma Abbansa komai tun daga farko, bai boye masa komai ba, Abba couldn't stop looking at him da wani expression da shi kansa ya kasa fahimta, Abuturrab ya xauna kan kneels dinsa a hankali feeling so remorseful yace "Kayi hakuri Abba, i neva thought things will turn out that way da ban yi komai gaban kaina ba, ban san haka lamarin xai kasance ba, i am sorry father, I don't know if this means failing you, kayi hakuri Abba..." Abba ya dafa shoulder dinsa ya sauke ajiyar xuciya amma kuma ya rasa ma abinda xai ce masa, da alama ya girgixa sosai da batun shi ma, Abuturrab yace "Xan iya kai ka gun mai anguwan ma so u can believe me 100%, ban ta6a xaton haka abubuwan xa su tafi ba da ban yi ba" Abba ya kara sauke wani ajiyar xuciya yace "Ikon Allah, to Allah ubangiji ya sa hakan shine mafi alkhairi gare ka Aliyu, but this is astounding..." Abuturrab yayi shiru bai ce komai ba, Abba ya dinga pondering kan lamarin, sai yake ganin abun kamar a mafarki, his son getting married babu shi, babu yan uwansa, infact unprepared marriage, hakan bai ta6a faruwa a xuri'arsu ba kaf" Abuturrab ya katse ma Abba tunaninsa ta hanyar cewa "Amma xan saketa Abba" Da sauri Abba ya kallesa yace "Why? Ba saboda ka taimaketa ka aikata hakan ba, xaka saketa saboda me kuma?" Da mamaki Abuturrab ke kallon Abbansa, can yace "Abba amma ai ni baxan iya xama da ita as a wife ba, i just can't Abba, she is not my class" Abba ya dinga kallonsa, Can ya girgixa kai yace "Dole hakan xaka xauna da ita kuwa, before making the decision of marrying her ai ya kamata ka fara naxarin ko xaka iya xama da ita din as wife or not, ka saki yarinya for what reason, i thought it's ur decision? Ko ka dau aure abun wasa ne, ka xata film ku ka yi acting a wajen ranan, ko kuma wasan yara ku ka yi?" Abuturrab ya marairaice hankalinsa a mugun tashe yace "Abba wllh kawai don in taimaketa a wannan moment din ne yasa na amince da auren ba wani abu ba, naga xa ayi ruining rayuwarta ne yasa na amince Abba, amma kuma nayi niyyar sakinta ai bayan daura auren" Abba na masa wani kallo on a serious note yace "Erase that harebrained idea right away, babu wani sakinta da xaka yi, tunda har aka daura auren shaidu duk sun shaida ka bada sadaki, babu wani abinda ya rage illa kayi accepting fact din ka tare da matarka, kada in sake jin ka yi xancen saki, ba drama ko film din Hausa kuka yi acting ba a wajen" Da mugun mamaki Abuturrab ke kallon Abban nasa baki bude, sanin arguing further won't favor him yasa yayi shiru, but deep down him yasan in har yana son ci gaba da rayuwarsa yanda yake yi a da to sai ya datse igiyar yarinyar nan a kansa, idan bai saketa ba he will never have peace of mind, he might even turn a Sadist, sakinta kuma da xai yi babu wanda xai bari ya sani, they will stay in the same roof but not as husband and wife, muryar Abbansa ya ji yana cewa "Sai ka karasa gyara gidanka na nan garin ku tare, i will call all my brothers and inform them what happened, since u chose this for ur self" Abuturrab ya ji kamar yayi kuka sanin in har cousins da frnds dinsa suka ga cewar wannan yarinyar ce matarsa ai tasa ta kare kuma, he don't even want to imagine how they will make jest of him and even laugh at him, yayi narai narai da ido ya marairaice yace "Abba don girman Allah ba sai ka gaya ma kowa wannan abun ba pls I'm begging you Dad" Dariya ya kusa ba ma Abban nasa ganin yanda ya marairaice, wanda he couldn't help it but laugh, duk da kasancewarsa musulmin kwarai sannan dattijon kwarai ne kadai ya sa ya saduda yayi give up da wannan auren na d'an sa, amma banda haka shi da kansa xai iya sa Abuturrab ya saketa don har cikin ransa bai ji dadin wannan lamarin ba, Lkci daya idanuwan Abuturrab suka kada sosai ya kife kansa da kujera, Abbansa yaji tausayinsa ba kadan ba yana murmushi yyi patting shoulder dinsa cikin kwantar da murya yace "Abu me kyau kayi my son, and i am proud of you, Allah kadai ya san ladanka, kar ka damu it shall be well, Allah yayi maka albarka, and kada ka sake tunanin sakinta a ranka shine xai yi helping matters, ka xauna da ita tunda ka aureta, you won't regret it in sha Allah coz you've got a good heart, nasan wataran xaka yi alfahari da ita...." Da sauri Abuturrab ya dago ya kalli Abbansa da jajayen idonsa, ji yayi xaxxabi na neman kara rufesa, amma tunawa da yayi xai saketa ba tare da sanin kowa ba sai ya ji hankalinsa ya d'an kwanta, Abba yace "Xuwa yaushe xata tare din yanxu?" Abuturrab ya kalli Abbansa a sanyaye, Abba yace "Let me talk to ur mothers about it first, i hope they won't be disturb much..." Wayarsa ya dauka ya shiga kiran matan nasa, Abuturrab gabansa ya dinga faduwa don bai san yanda Umminsa da Aunty su kuma xa su dau lamarin nan ba, ba a dau lkci ba duk suka shigo, Abuturrab ya kalli Abbansa a hankali yace "Can i excuse my self sir..." Abba yace "Sure dear" Mikewa yayi ya nufi kofa walking slowly, Ummi ta bi sa da kallo, tun a shekaranjiya ta san abu na damunsa yana cin sa har cikin ransa, though tasan da kyar ya gaya mata koma meye da ya shafesa sai dai kishiyarta amma wannan karan ta lura ita din ma bai gaya ma ba, hakan yasa abun ya dameta sosai tun daga jiya bata da nutsuwa, don duk da baya gaya mata sabgarsa in dai xai gaya ma Auntyn da sauki, ko ba komai ita ma tana basa shawaran..... Aunty da ta bi sa da kallo tace "Alhaji ko ya gaya maka damuwarsa, tun safe nake fama da shi yace min ba komai, kuma nasan ba gaskiya bane, and this is so unlike him" Abba ya d'an sauke ajiyar xuciya yace "Kiran da nayi maku kenan yanxu" Duk suka maida hankali kan Abba don jin damuwar Abuturrab din. 




*Tohm Khaleesat Haiydar dai bata Allah ya isa kuma baxata fara ba a kan littafin Jiddatul Khair, sannan nasan ni baxan iya hana fitar book din nan ba, kawai dai idan xaka yi ma kanka adalci if u should come across this book, keep it in mind that ba free book bane, littafin kudi ne, if u are willing to read just make ur payment ka sha karatunka ba wani shakku a ranka, and bana tunanin u will regret paying and reading this book in sha Allah....*✍🏻


_And i really appreciate my lovely fans patronage..... na samu sabbin fans da yawa da suka yi patronizing Jeedahh kuma naji dadin haka... Ina godiya da maku fatan alkhairi_ 🥰



The book is 500 via 3276052019

Fcmb

Hauwa Bello Jiddah... And u show ur evidence of payment via

 07087865788.... 


Thank you.😇

Mikewa Aunty tayi bayan Abba ya kai aya cikin tashin hankali tace "Ban gane ba Alhaji?? Are you for real? Shi Abuturrab din ne yaje ya daura ma kansa aure without our knowledge????" Abba yayi murmushin karfin hali yace "Dama mutum ya ta6a daura ma kansa aure, we just have to accept it Hafsah, it doesn't make sense though, to amma ya muka iya da lamarin ubangiji, Allah ya riga da ya tsara hakan" Ummi kallonsu kawai take ko kiftawa babu, wanda da alama duk ta fi su shiga shock din, Aunty ta dage hannu biyu sama tana girgixa kai da karfi tace "No wayyy, mu ba gantalallu bane gaskiya, yanda aka daura auren haka xai saketa wllh wllh, me xai yi da yar hayi, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yar hayi fa kace Alhaji?? To na rantse da Allah baxai yiwu ba" Wani kallo Abba ya dinga yi mata har tayi shiru tana huci kafin yace "Ja xa ki yi da lamarin ubangiji??" Aunty ta dalla masa wani harara ta nufi kofa rai bace tana cewa "Allah ya kiyaye, wllh sae ya saki wannan yarinya dai, banda fitinarsa ma ina shi ina shiga tsabgan talakawa mutan anguwan nan balle har wannan mummunan kaddararran ya fada masa, wllh saki kamar yayi sa...." sai kuma ta fashe da kuka ta fice ta rufe kofan, Abba ya kalli Ummi bayan kusan minti biyu da fitan Aunty jin taki cewa komai yace "Kinyi shiru Hauwa" Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh me xance, jin abun nake kamar a mafarki ai, an ta6a aure haka dama Yallabai?" Abba yace "Gashi nan dai d'an ki yayi, kinsan babu abinda taimako baya sa mutum yyi, to kinga inda nasa taimakon yayi leading dinsa to" Ummi ta girgixa kai tace "Toh yanxu meye abun yi Yallabai? Wannan ai ba abun ayi shiru bane ayi ta kiran taimako, wani irin aure ne wannan kamar a wasan kwaikwayo" Abba yace "Meye kuwa abun yi banda ya tare da ita yarinyar, ai an riga da an daura aure, kuma lamarin aure ba lamarin wasa bane" Da mamaki Ummi ke kallonsa tace "Kana nufin haka xai yi rayuwa da ita? Ya tare da ita fa kace" Abba yace "Kwarai, tunda har an daura auren, ai yanxu matarsa ce ita din, ko ke wani shawara xaki bada a nan?" Ta girgixa kai tace "Haba Alhaji, a ina aka ta6a irin wannan auren, ni dai tunda nake ban ta6a jin irinsa ba ma, me xa muce ma 'yan uwa da abokan arxiki, me xa ace ma Hajja, ya kake ga xata dau lamarin nan? shi Abuturrab din shaye shaye ya fara da xai kai kansa ga irin wannan taimakon? Ba gwara ma ace yau kawota yayi gidan nan ba yace mana ga ta, ai babu wanda xai hanata xama gidan nan idan anyi bincike an gano gaskiyar lamarin, kuma baxa mu ki riketa ba, idan ma wani ya ki ni baxan ki ba ka sani" Abba yace "A takaice kema dai kin goyi bayan ya saki yarinyar kenan" Ummi tace "Toh idan bai saketa ba me xai yi, ai sakin kadai ne best solution a nan, ko a garin ga6a ga6a ba a irin wannan auren Yallabai" Abba yace "Toh duk kun yi kokari, amma ku sani auren nan bbu fashi tunda ba wani ya dau sadakin ya kai masa ba, da kansa ya aikata duk abinda ya aikata gaban kansa ba tare da ya duba cewa yana da iyaye da magabata ba, to don me xa ace sai yayi saki, tunda har ya amince aka daura masa aure da ita wllh dole ya amince ya xauna da ita, ba dai taimakonta yake son yi ba, gata nan sai ya taimaketa har karshen rayuwarta, nan gaba sai kiga ba shi ba har ke sai kiyi alfahari da ita a matsayin matar d'an ki, sannan a rayuwar nan there is reason for everything, Allah ya riga ya tsara hakan to mu a su wa da xa mu ce tsarin bai yi ba??" Mikewa Ummi tayi bata sake sauraronsa ba ta fice daga parlon, ya daga kafada yace "Yanda bai maku dadi ba nima lamarin bai min dadi ba ko kadan, but who am i to ask why tunda haka Allah ya tsara???" Aunty ce tsaye kan Abuturrab inda take shiga ba nan take fita ba duk ta hada xufa kai kace tayi wani tafkeken asara ne a rayuwarta, ko Salem ne yayi abinda Abuturrab yayi iyakan abinda xata yi masa kenan take ma Abuturrab, Abuturrab dai na xaune gefen gado ya rike kansa da yyi masa nauyi duk yana sauraronta ga wani bugawa da xuciyarsa yake, he just hate himself completely for this foolish mistake he made, me yasa bai yi duk wannan tunanin ba kafin ya aikata wannan shirmen, me yasa bai yi reasoning abinda xai biyo baya ba yayi abinda yayi?? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da kyar ya dago kai yana kallon Stepmum din tasa da idanuwansa da suka kada cikin sanyin murya yace "Wllh xan saketa Aunty, ba da dadewa ba kuma xan yi hakan, ni ko ba ace in saketa ba ma dama ba sa'ar aurena bace dole xan saketa" Aunty na huci tace "Toh uban me kake jira har yanxu? Mu xaka kwaso ma abun kunya a dinga nuna gidanmu a gari, wllh baxai yiwu ba ko almajiri baxa ayi masa irin wannan auren da kaje kayi ma kanka ba, aikin banxa kawai, ko yar cikin gari wllh wllh kafi karfinta balle yar kauyen hayi, to sai ta shigo gidan mu gani ai...." Tana fadin haka sai ta saki kuka ta fice daga dakin. Abuturrab ya dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a xuciyarsa, what has he done with his life, he wish he could wake up and see that all this is nothing but a dream, mikewa yayi a hankali ya karasa kofar dakinsa ya sa makulli don ma kar ta sake dawowa sannan ya dawo ya xauna ya dafe kansa hade da lumshe ido yana kiran Allah a ransa. Bayan azahar Abuturrab ya dau makullin motarsa ya fito daki, tun safe bai fito ba sai yanxu da yaje masallaci yayi sallah ya dawo, yana shigowa parlor ganin kallon da siblings dinsa ke masa yasan sun samu labarin kenan su ma, bai kuma kallonsu ba har ya fice daga gidan, ya hau motarsa ya bar gidan, gidansu Ahmad ya nufa, ko kallon matar mai gadi dake gaishesa bai yi ba ya nufi entrance din gidan, a yanxu dai komai haushi yake basa, underneath his breathe yayi sallama ya shiga parlon, Huraira ce da Siyama parlon, su ma bai sake kallon inda suke ba balle ya amsa gaisuwarsu, dai dai nan Ahmad ya fito daga wani daki dake nan parlon, ganin Abuturrab yace "I was planning on calling you now, welcome... Duk kayi scarce yau" Abuturrab bai ce komai ba ya nufi dakin Ahmad, Ahmad ya bi bayansa yana murmushi a ransa yana cewa the latest ango in town, xaune ya tadda shi gefen gado, Ahmad ya tsaya bakin kofa yana kallonsa yace "Ya ake ciki yanxu, hope it went well??" Abuturrab yace "Kamar yanda na fada, no much problem from Dad, but aunty took the matter tooo personal, Aunty tayi misunderstanding komai" Ahmad ya masa wani kallo yace "And so what? How about Ummi? Though she is here, daxu ta xo" Abuturrab ya xaro ido yace "Kana nufin Ummi na gidan nan?" Ahmad yace "Yea tana dakin Umma" Abuturrab ya lumshe ido ya bude, gaba daya abun duniya ya ishesa yanxu fisabilillah baxai farka yaga duk wannan abun mafarki bane, Ahmad yace "Amma Ummi tayi maka magana ne?" Abuturrab ya girgixa kai yace "Bata ce min komai ba har yanxu" Ahmad yace "Ka kwantar da hankalinka komai ya xo da sauki tunda Abba ya fahimce ka" Abuturrab yace "Ya fahimce ni?? Ai ni da abinda Abba ke ce min yanxu gwara ma ace bai fahimceni ba kwata kwata, Did you know that he is forbidden me from divorcing her?? Ce min yayi fa baxan saketa ba" Ahmad har xai ce dai dai kenan amma don kar ya sake provoking din d'an uwan nasa yayi fuskan mamaki yace "Toh fah, kar ka saketa kuma??" Abuturrab ya d'an ja tsaki a fusace fuskar nan tasa a murtuke, Can ya dago ya kalli Ahmad yace "Toh me Ummi ta xo ce ma Umma ynxu?" Ahmad yace "Don't know.... And least i forget, Jiddah bata da lafiya fa" Daga kai Abuturrab yayi yana kallonsa, Ahmad yace "Yea, ina mata karin ruwa, shine kaga na fito dakin dake parlor da ka shigo yanxu" Abuturrab dai bai ce komai ba, Ahmad yace "Dakin mai gadin baxa a rasa sauro ba, it's malaria symptoms...." Abuturrab na kallonsa yace "Kayi mata test ne? She just finished treating malaria few weeks ago" Ahmad yace "Yea it's possible she is reinfected" Abuturrab bai sake cewa komai ba, Ahmad ya juya yace "Mu je ka dubata" Abuturrab yace "It's not necessary" kallonsa Ahmad yayi yana ciro wayarsa dake ring a aljihunsa yaga Umma ke kiransa, ya kalli Abuturrab  yace "Hmm Umma is calling" Daga kiran yayi ya kai kunne, bayan few seconds yace "Toh" daga haka ya katse kiran yana kallon Abuturrab yace "She's calling me to her room now" Yana fadin haka ya fita dakin ya tafi bangaren Ummar tasa, tana xaune bedroom dinta tare da yayarta ko wannensu fuska babu annuri, Ahmad yyi kasa da kai ya xauna nan kasa yace "Gani Umma" Umma na kallonsa strictly tace "Ahmad wacce yarinya ce Abuturrab yaje ya aura without acknowledging how stupid that will be?? Yanxu kana matsayin d'an uwansa ka yi shiru ka barsa ya aikata abinda ya aikata Ahmad??" Ahmad yayi kasa da kai a hankali yace "Wllh i knew nothing about that Umma, i swear to God ban san komai ba..." Umma ta daka masa tsawa tace "You are lying, ya xaka ce baka san komai a kai ba, akwai wani abu da Aliyu ke boye maka?" ya kalleta da sauri yace "Billah abinda ya sanar da ni jiya ne kadai nasani game da lamarin nan, a jiya nima nasan abinda ya aikata Umma" Umma tace "Me ya sanar da kai jiyan?" Ya sauke kansa yace "Umma nima he didn't tell me all, but he is around now, yana dakina" Umma tace "Abuturrab na gidan nan????" Ahmad yace "Ehh yanxu ya shigo" Umma tace "Call him" Mikewa Ahmad yayi ya fita dakin.... Abuturrab ya mike da sauri bayan Ahmad ya sanar masa kiran Umma yace "Me yasa xaka ce ina gidan nan Ahmad for God sake?" Ahmad ya daga shoulder yace "i didn't say so, kawai kirana tayi tace i should call u, kilan ko su siyama ne suka gaya mata ka xo, aikena kayi da xanje in ce masu ka xo?" Abuturrab ya wani hade rai yana jin kamar ya dau car key dinsa ya bar gidan, but he just can't, babu yanda ya iya haka ya fita dakin Walking slowly, Ahmad na biye da shi yana d'an murmushi, kasa ya xauna shi ma bayan ya shiga dakin Umma, tunda suka hada ido da Umminsa bai sake yarda hakan ya faru ba, ita ma small mum din tasa ya ki yarda su hada ido, su kuwa sai kallonsa suke kamar ranan suka fara ganinsa, Calmly Umma tace "Abuturrab, who is this lady that u went and tied the not with.. without the knowledge of ur parent??" Abuturrab kansa na kasa a hankali yace "I'm sorry Umma, i never knew it will happen this way, wllh it's not intentional..." Ta dakatar da shi a fusace tace "Malam tambayarka nake wace yarinya ce?? Ba wani xance can ba" Abuturrab kamar baxai ce komai ba sai kuma cikin sanyin murya yace "Tana gidan nan Umma" Ba Umma ba har Ummi bude ido tayi sosai tana kallonsa with shock, can suka kalli juna, Ahmad dai na tsaye bakin kofa ya rungume hannu, Umma na masa wani irin kallo tace "Wani gidan?" Abuturrab yace "Nan gidan?" Da wani expression Umma na kokarin calming kanta tace "Wacece ita?" Abuturrab ya kasa bata amsa, Umma ta kalli Ahmad, ya sauke idonsa murya can kasa yace "Yarinyar dake gun matar mai gadi yanxu" Umma ta xaro ido tace "Ban gane ba, wacce yarinya kenan?" Ahmad yace "Me sunan Ummi" Bude baki Umma tayi tana kallonsu gaba daya, Ummi dai duk sun gama confusing dinta sae bin su da kallo take, Cikin tsawa Umma tace "Baxa ku min bayani ba yanda xan gane???" Abuturrab ya dago yace "Ita ce Umma, da abun ya faru ne shine na kawota nan gun matar mai gadin gidan nan" Salati Umma ta saki har da tafe hannu tace "Kana nufin bakuwar nan Jiddah???" A hankali Abuturrab ya gyada mata kai yana kallonta da manyan idanuwansa, Umma ta hangame baki ta dinga kallon Abuturrab with shock, can ta kalli yayarta dake kallon ikon Allah tace "Yaya wai kinji yarinyar da mu ka shiga daki daxu a downstairs kika duba da jiki..." Ummi sai kallon Abuturrab take ko kiftawa babu, ya sunkuyar da kansa cikin sanyin murya yace "Ku yi hakuri Umma, i don't know d words to use in asking for forgiveness, I'm truly sorry for all this, wllh it's not intentional, Allah ne ya kaddaro min haka, amma in sha Allah nace xan saketa" Umma dake ta kallon yayarta da ta jinginar da kanta da gado ta kasa cewa komai, Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "This is serious, Abuturrab? Why?? Why Abuturrab, dama ashe kai ka haifi kanka??" Kallonta kawai yake ruefully... ta girgixa kai feeling so disappointed tace "I am disappointed at u Aliyu, ka bani mamaki" Shi dai bai iya yace komai ba, Tace "Yanxu ita Jiddar ta sani? I mean tasan da wannan auren?" Ya girgixa kai yace "Bata san komai dake faruwa ba har yanxu.... And xaki iya samunta ki tambayeta ta gaya maki duk abinda ya faru da dalilin kawota gidan nan da nayi, sannan ni a lkcn da na kawota gidan nan ba a daura auren ba wllh" Umma was totally lost of words balle kuma Ummi da sai binsu kawai take da kallo, Umma tace "Daga bakin ka nake son jin labarin abinda ya faru ba ita ba" Abuturrab ya lumshe ido ya bude babu musu ya shiga bata labarin abinda ya faru tun daga farko ita ma bai boye mata komai ba har xuwa sanda aka daura masa aure da Jiddah, da tafin hannunsa ya rufe fuskarsa cikin breaking voice yace "Plss Umma ku daina ganin laifina, i only tried to help ne ban san haka abun xai kasance daga karshe ba, kice Ummi tayi hakuri ta yafe min wllh xan saketa na dau ma kaina wannan alkawarin, ban yi hakan don in bakanta maku ba Umma..." Umma ta rasa abinda xata ce tausayinsa ya cikata, cikin sanyin murya Ummi tace "Aa ni baka min komai ba, Allah ubangiji ya sa mu dace" Umma ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ta na kallonsa tace "Tashi kaje Abuturrab" Mikewa yayi ya juya ya fita dakin Ahmad ya bi bayansa, Umma na kallon Yayarta tace "Kiji wani babban lamari na ubangiji yaya, yanxu ke me kike ga xa ayi kan lamarin? What next?" Ummi ta sauke ajiyar xuciya a fili tace "Ban san me xance ba Ramlah" Bayan la'asar Abuturrab na fitowa masallaci tare da Ahmad, Ahmad yace "Ka shiga ka duba yarinyar nan pls, she was very sick yesterday night fa" Captain na kallonsa yace "Me dubata da rashin dubata xai kara mana ni da kai pls? Kai dai ba kana dubata ba me yasa xaka damu ni sai na dubata" Ahmad bai kulasa ba ya tsaya gaisawa da wani frnd dinsa a kofar gidan, Abuturrab ya shiga compound din walking slowly, babu kowa parlon ya kalli dakin da yaga Ahmad ya fito daxu da ya xo, kamar xai wuce sai kuma ya nufi dakin ya bude kofar a hankali ya shiga ya kulle sannan ya juyo yana kallonta, tana kwance saman gadon dakin drip a hannunta jin budewan kofa ya sa ta bude ido, ganinsa ta mike xaune da sauri, kana ganinta kasan she is very sick don har ta rame, lebbenta yayi ja, ya kalli drip din da har yayi rabi, da kyar tace "Ina yini" Bai yarda ya kalleta ba idonsa na kan drip din cikin calm voice dinsa yace "Ya jikin?" A hankali tace "Da sauki" Bai kuma cewa komai ba, bayan few seconds ya d'an saci kallonta suka hada ido, da sauri ta sauke idonta, ya d'an hade rai, bude kofar dakin aka yi ya juya da sauri, Ummi da Umma ne bakin kofar, he wish hakan bai faru ba, ya ji kamar kasa ya bude ya shige kawai ya huta, kasa kallonsu yayi, Ummi dai sai kallonsa take ta karasa cikin dakin tare da kanwarta, Jiddah ta sunkuyar da kanta don sun gaisa daxu, Umma na kallonta tace "Ya jikin?" Tana jan fingers dinta tace "Da sauki Umma" Ummi dai sai kallon Jiddah take, Juyawa Abuturrab yyi xai fita amma ya kasa ce ma Umma ta basa hanya ita kuma ta ki basa hanyar, Ummi tace "Sannu Allah yakara lafiya" Jiddah na kallonta tace "Ameen" Umma tace "Kin sha shayin kuwa daxu?" Jiddah ta gyada mata kai, Umma tace "Toh Allah ya sauwake" Daga haka ta kalli Captain tace "Meet me before leaving...." Shi dai bai dago kansa ba, Tana fadin haka ta fita Ummi ta bi bayanta, sai a sannan Abuturrab ya daga kai ya bi su da kallo, Umma ta kulle kofan, still yayi bakin kofar, can ya d'an kalli Jiddah, kallonsa take ita ma, suna hada ido tayi light smile tace "Kun yi kama da warce ke kusa da Umma" ya hade rai ya juya ya bude kofan ya fice ya kulle. Sai da Abuturrab ya tabbatar Umminsa ta bar gidan sannan ya koma dakin Umma, Kallonsa take xai xauna kasa ta nuna masa kujera ya mike ya koma saman kujeran tana kallonsa, cikin sanyin murya yace "Gani Umma" Tace "Tell me now son, what do u have in mind a kan wannan auren da kaje kayi ma kanka?" Ya girgixa kai yace "Taimakonta kawai nake son yi ba wani abu ba, but ban san things will turn out this way ba da ban fara ba..." Umma tace "So what's ur next plan now?" Ya shafa kansa yace "Umma sakinta xanyi, since yanxu kun san abinda ya faru sai ta xauna nan ko kuma wajen Ummi, i know Ummi won't say no" Umma dai kallonsa kawai take, can tace "Toh kilan hakan kadai ne mafita gareka, amma can su iyayen nata da suka baka aurenta fa?" Ya girgixa kai yace "Ba mutanen kwarai bane, ko da xata xauna da ke ko Ummi to babu ita babu su, ita din marainiya ce, she is staying with just her Stepmum, tace min iyayenta sun rasu, I don't know of relatives amma da da akwai baxa su bari tana wahalan da take ba a gun Kishiyar Baabarta, beside that baxa su bari a aura mata shi wanda aka yi niyyar aura mata da farko ba, don duk anguwar babu wanda bai san tout bane shi, amma sbda yana ba ita stepmom din nata abun duniya wanda bai kai ya kawo ba shine take son aura mata shi, sannan tana da 'ya ita ma sa'arta fa" Umma dake ta sauraronsa ta girgixa kai cike da tausayin Jiddah tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...." Yayi kasa da murya yace "Ita ce me yin awaran da muke siyo maki a hayi, Ahmad yasanta... But bai ta6a sanin ina xuwa gunta a can hayin ba har sai da wannan abun ya faru" Umma ta buda ido tace "Ikon Allah, Allah sarki rayuwa, yanxu abinda nake so da kai shine you talk to her about all what happened tunda kace bata sani ba, ka sanar mata komai" Da sauri Abuturrab ya kalleta, ta gyada masa kai tace "Yes she needs to know kafin ma kayi sakin da kake cewa, after that kuma idan nan din xata xauna to, in kuma gun Yaya xata xauna shkkn" a hankali Abuturrab yace "Toh shkkn Umma, nagode" Umma tace "Amma ba yau xaka sanar mata ba tunda bata da lafiya, gobe ka xo we are hoping she will get much better sai kayi mata bayanin komai" Abuturrab yace "In sha Allah Umma" Tace "Maa sha Allah, you can go, Allah yayi maka albarka" Yace "Ameen" mikewa yayi ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya, tun bayan faruwan wannan lamarin sai yanxu ya ji magana da ya sa masa relieve a xuciya, he is happy Umminsa bata dauki wannan batun personal ba, just like his dad and small mum, but Aunty, wani sigh yayi yana tunanin yanda xasu yi da ita idan ya koma gida anjima....



The book Jiddatul Khair is 500 via 3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah.... And u show ur evidence of payment via 07087865788... Do justice to ur self by subscribing before reading...






*mg's skincare*


Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩

Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️

Shin kinafama da

Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?

Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫

Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind

Bridal kit:18k

Beauty kit:11k

Student package:7k

Herbal whitening soap:3k

Chat

 08062991549

07046881166

07067210195

Call 08064532391

Facebook: mg's skincare

Instagram:glow_with_mgs

Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝

Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩

Then @mgs skincare gat you covered 💯

Now is time to glow😍

Pamper ur skin🦵

Shine like bride👰🏻♀

Glow🧖♀️


💯 tested nd trusted🤝

Guarantee



Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166

Ko da Abuturrab ya koma gida bai bari stepmom dinsa ta san ya dawo ba don bai ma dawo da motarsa ba a gidansu Ahmad ya barsa, Ahmad yayi dropping dinsa kofar gida a nasa motar ya koma, yana shiga bedroom dinsa ya sa makulli hade da sauke ajiyar xuciya, wanka yayi ya sauya xuwa pajamas dinsa ya xauna gefen gado, yana son shan shayi but baya son fita duk da ko ya fita din kanninsa xai saka still, wayarsa ya jawo ya shiga dialing number din Ramlah, tana dagawa yace "Make me a cup of tea, an omelette with just two eggs" Bai jira cewarta ba ya katse wayan, ba a dau lkci ba Ramlah tayi knocking bakin kofar dakinsa, ya mike ya isa kofan ya bude ya bata hanya ta shigo, ajiye plate din hannunta na kwai dake rufe tayi da cup din shayin tana kallonsa tace "Yaya...." yace "Goodnight Ramlah" Shiru tayi sai kuma ta juya ta nufi kofa kafin ta fita yace "Thank you" Ta sake juyowa ta kallesa ta marairaice tace "Amma yaya me yasa....." Hade rai yayi yace "Fita!!" Fita tayi ta kulle masa kofar ya karasa ya sa key. Washegari Friday Abuturrab na dawowa masallaci da asuba ya shiga bangaren Umminsa, da da ne bangaren stepmom dinsa xai fara shiga, kansa a kasa ya gaida Ummi ta amsa, a hankali ya soma bata hakuri, tace "It's okay, ae kun gama magana da Hajiya Ramlah ko?" Ya gyada mata kai tace "Toh maa sha Allah" Yace "Amma Ummi don Allah kiyi ma Abba magana naji yana cewa baxan saketa ba..." Ummi tace "I don't know... But seriously he is not to decide that for you, you just ignore him" Abuturrab bai ce komai ba, can yace "Toh shkkn Ummi" mikewa yayi ya fita dakin ya koma nasa, a masallaci ma dodging din mahaifin nasa ya dinga yi har ya shigo gida basu hadu ba. As early as 10 Abuturrab ya bar gidan ya tafi gidansu Ahmad, bayan ya gaisa da Umma dake parlor ya tafi dakin Ahmad, Ahmad na shiryawa ya samesa, Ahmad na murmushi yace "Welcome latest ango" Abuturrab yayi still ya dinga masa wani kallo, Dariya Ahmad yayi yace "Yanxu dai cikin ruwan sanyin kullum sai ka xo gidan nan ko?" Abuturrab bai tanka sa ba ya tafi ya xauna, Ahmad ya gama shiryawa yace "She's getting better, jikin da sauki yau sosai" Nan ma Abuturrab ya sharesa, bai san shi abinda ya kawosa daban ba, Mikewa kawai yayi ya fita daki hoping Umma ta bar parlon yanxu, Ahmad ya bi sa da kallo yana murmushi, luckily ya tadda babu kowa a parlor ya karasa dakin da Jiddah take ya bude hade da sallama murya can ciki, tana xaune saman gado da wani drip din a hannunta ga pepper soup da Umma ta sa ayi mata, Huraira da Maman Abdallah ne dakin suna ta hira, ita dai sai dai tayi murmushi, ganin Abuturrab duk suka gaishesa, bai san suna ciki ba da baxai fara shigowa directly ba, ya amsa without looking at them, Jiddah ta kallesa tace "Ina yini?" Ita ma bai kalleta ba yace "Lafiya" Ahmad ne ya karaso dakin ya shiga ciki yana kallon jiddah yace "Alhmdlh jiki yayi kyau sosai ko Ummi?" Ta d'an yi murmushi amma bata ce komai ba, shi dai Abuturrab na tsaye, Ahmad ya kalli su Huraira da basu da niyyar fita a tunaninsu kawai dubata suka shigowa yi, yana murmushi yace "Maman Abdallah da Aunty Huraira a bamu waje mu duba patient pls" Duk suka mike, Huraira tace "Toh bari mu fita" Bayan sun fita dakin Abuturrab ya karasa gun window ya tsaya Ahmad dai sai kallonsa yake, Can yayi murmushi ya kalli Jiddah yace "Kin sha maganin ai ko?" Ta gyada masa kai tace "Eh" yace "Toh Allah ya kara lafiya" Tace "Ameen" Ya juya yace "Bari in kawo maki na karshen.." Daga haka ya juya ya nufi kofa ta bi sa da ido har ya fita ya kulle kofar, sunkuyar da kanta tayi, Abuturrab ya d'an kalleta, he don't even know where to start from, hada ido suka yi ya rungume hannunsa yace "Ya jikin?" Tace "Naji sauki" Ya d'an yi jim kafin yace "Iyayenki sun daura maki aure..." Da sauri Jiddah ta daga kai ta kallesa, yaki yarda su hada ido ya ci gaba yace "Amma ba da mutumin nan ba" Kallonsa kawai Jiddah take ko kiftawa babu, ya shafa kansa yace "Amma shi wanda aka daura maki auren da shi xai sake ki, sai ki ci gaba da xama a nan wajen Umma ko gidanmu wajen Ummina, amma fa sai kin amince babu ke babu Baabar nan taku don ba sonki take ba, kuma baxata ta6a sonki ba, neman kudi take da ke" Cikin sanyin murya Jiddah tace "Toh da wa aka daura min auren??" Yace "Fada maki ba amfani xai yi gareki ba, kawai dai abinda na sani xai sake ki, sai kiyi xaman ki a nan ko kuma ki xauna gidanmu, ki fara karatu islamiyya da boko, kinsan wacece ke, kinsan daga inda kike, kawai na shiga rayuwarki ne ba don komai ba sai don in taimakeki in samar maki yan cin ki, idan ba don haka ba, ni bana shiga abinda bai shafeni ba...." Kallonsa kawai Jiddah dai take a sanyaye, lkci daya hawaye ya kawo idonta, a hankali tace "Jiya Umma da daddare ta shigo ta tambayeni in gaya mata gaskiyan wacece ni, kuma ya aka yi na xo gidan nan" Cikin rawar murya ta ci gaba tace "Ni kuma baxan iya mata karya ba" Abuturrab na kallonta yace "Kin dai gaya mata ko?" Ta gyada masa kai yace "Good, xuwa gobe duk inda kika ce xa ki xauna nan xa a kai ki, ko gidanmu ko nan" A hankali tace "Toh idan na xauna nan xaka dinga xuwa?" Kallonta yake da kyau, ya hade girar sama da ta kasa yace "In xo in yi maki me??" Kasa cewa komai tayi tana wasa da fingers dinta, yace "Ae ba lallai ki gan ni ba, ki ma daina min kallon sani daga yanxu, ki kama Umma da su Siyama ki rike sosai, they will like you, ni ba lallai a shekara ma kike ganina ba" Kai kawai ta gyada masa hawaye cike idonta, yace "Sai ki tsaya kiyi karatu da kyau domin al'umma da wa enda suke tare dake suyi alfahari dake..." Nan ma ta gyada masa kai kawai, yace "Allah ya kara lafiya" Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita dakin, hawayen da bata san dalilinsa ba ya dinga sauka idonta, Abuturrab ya amshi medical report dinsa wajen Ahmad kawai ya bar gidan coz baya tunanin har ya koma aiki da akwai abinda xai sake dawo da shi gidan, he now felt relieved, yaji baya tare da duk wani damuwa. Da yammacin ranan Abuturrab dake bedroom dinsa ya dau wayarsa dake ring, ganin number Abbansa yaji gabansa ya fadi sosai, dagawa yayi ya kai kunne hade da sallama, Daga daya bangaren Abba yace "Ka sameni parlona ynxu" Kafin yace komai Abba ya katse kiran, lumshe ido yayi ya bude, bayan few minutes ya mike a hankali still holding to his phone ya nufi kofa ya fita, a main parlor suka ci karo da Aunty, yayi kasa da kai yace "Ina yini Aunty" Ko kallonsa bata yi ba balle ta amsa shi tayi wucewarta, ya bi ta da kallon gefen ido sannan ya ci gaba da tafiya xuwa parlon Abbansa cikin sanyin jiki, a hankali yayi sallama sannan ya shiga, sosai gabansa ya fadi ganin Abbansa da brothers dinsa biyu, a sanyaye ya karasa shiga cikin parlon ya xauna kasa sannan ya gaishesu, uncles din nasa suka amsa, ya kalli Abba amma bai ce komai ba, Alhaji Lawal yayan Abbansa ne yace "Mun ji abinda ke faruwa Aliyu, ko kuma ince mun ji abinda ya faru" kasa cewa komai Abuturrab yayi, Alhaji Ibrahim kanin Abbansa yace "What u did is something very good but ba ta yanda ya kamata kayi ba kayi, kada ka manta ba kai ka haifi kanka ba, kana da iyaye, no matter what ya kamata ka nemi consent dinsu, ya kamata ka basu girmansu su san abinda kake ciki, ba sae da abu ya kwabe ba....." Daga kafada yayi yace "Anyway, wannan duk maida hannun agogo baya ne, tunda abinda ya faru ya riga da ya faru, sae dai a tari na gaba" Abuturrab bai iya yace masu komai ba, Alhaji Lawal yace "So what next now? Yarinyar tana ina?" A hankali yace "Tana gidan Umma" Alhaji Lawal yace "Wacece Umma?" Abba yace "Kanwar Hajiya Hauwa" Alhaji Lawal yace "Ohkk, am asking what ur next action is now" Abuturrab ya sunkuyar da kai yace "Abba sakinta xanyi sai ta yi xamanta tayi karatu that was my intention dama" Alhaji Lawal yace "Ka saketa a saboda me?" Abuturrab ya kallesa ya marairaice yace "Abba dama wllh niyyata kenan, ai baxai yiwu inyi aure iyayena basu sani ba, ni kawai na amince na aureta ne sbda kubutar da ita daga hannun matar babanta, amma ai ni baxan iya aurenta ba" Alhaji Lawal yace "Wannan ba magana bane Aliyu, ka aureta, ka aureta kenan, babu wani kwaskwarima, Allah ubangiji ya baku xaman lafiya, kada ka sake tunanin sakinta, kaddararku da ita ne a haka" Bude baki Abuturrab yayi yana kallonsa without knowing cewar yayi hakan, Alhaji Ibrahim ya gyada kai yace "Hakuri xaka yi son, ka xauna tare da ita, ka cike ladanka, ai Allah ya ga xuciyarka, idan ka saketa baka kyauta mata ba, akwai hikima cikin auren nan...." Abuturrab ji yayi kamar ya fara masu kuka gaba daya, Abba ya sauke ajiyar xuciya yace "Dama ni nace baxai saketa ba, cikin weekend din nan ya dauketa su tare, ai ba wani ya jawosa ya aura masa ita ba, sai yayi hakuri ya rungumi kaddara" Abuturrab was lost of words amma ganin musa masu baxai yi masa amfani ba yayi shiru duk yana sauraronsu, sai dai xufa kawai yake yi, to lkcn da ma xai saketa din sani xa su yi? Tunanin hakan ya saukar masa da relieve, Muryar Alhaji Lawal yaji yana cewa "Gobe asabar ka tare kawai da matarka, Allah ya sanya alkhairi, not too long sai ku shirya da ita ku tafi gaida mai martaba a bauchi" Abuturrab bai samu courage din ce masu komai ba, but he is boiling inside, dama taimako na iya xama fitina da tashin hankali haka bai sani ba??? Alhaji Ibrahim yace "Sai a kira Hajiya Hauwa ita ma aji ta bakinta tunda tana da right a kansa ko?" Abba ya dau waya ya kira Ummi, har da Aunty, Abuturrab ya ji dadi da Abba ya kira har Aunty don yasan she will stand for him, ba a dau lkci ba suka shigo parlon, duk suka yi ma 'yan uwan mijin nasu sannu da xama don tun xuwansu gidan suka gaisa, Alhaji Lawal ne yayi masu bayanin shawaran da suka yanke, Ummi dai ta kasa cewa komai, ita babban tashin hankalinta asalin yarinyar nan ba wai tana kin auren bane, ba a san wacece ita ba gashi yace uwarta da ubanta sun rasu sai kishiyar uwar, Aunty ta mike tana girgixa kai cikin tashin hankali tace "Haba fisabilillah, an ta6a aure dole ne? Tunda yace bai so, yayi auren nan ne kawai don taimako to a barsa ya datse wannan kaddararren auren mana, ai ya gama taimakon da yayi niyya, to meye kuma xa ayi ta cusa masa yarinya kamar ku ka aura masa ita, wannan ai kamar neman suna ne ku ke yi, banda haka wllh ko mahaukaci baxai amince da irin wannan auren ba,  yarinyar da bata da asali ku ke burin d'an ku ya xauna da?" Alhaji Ibrahim yace "Ke kinje kinyi bincike kinga bata da asali Hafsah?" A fusace tace "Banda yanxu da na kawo maganan asalin ai babu wanda ya damu da hakan, haka kawai xaku yi ma yaro dole kuce sai ya xauna da yarinya yana ce maku baya so?" Alhaji Lawal na kallonta da kyau yace "Tunda ni ko d'an uwana ko Ibrahim babu wanda ya ja Abuturrab ya kai sa aka daura masa aure he just have to dance to his music, ko yaki ko ya so haka xai hakura ya xauna da yarinyar, mu ba kananun mutane bane, yanda bai yi shawara da mu ba yaje yayi abu gaban kansa bai isa yace yanxu ma xai juya mu ba, Allah ya basu xaman lafiya" Abba ya gyada kai cikin gamsuwa, Aunty na masu wani kallo gaba daya tace "Ai ko baxan ta6a xuba ido Abuturrab ya cutu ba in dai ina numfashi..." Daga haka ta fice daga parlon fuuu, Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh Allah yayi abinda ya fi alkhairi, ya sa mu dace" Alhaji Lawal yace "Ameen Hauwa" ta mike ta fita parlon ita ma, Abuturrab dai kansa na kasa, Abba na kallonsa da kyau yace "Kafin gobe kayi duk abinda xaka yi a gidan nan ka tare da matarka, kamar yanda Alhaji Lawal ya fada maka, idan an kwana biyu kuma ka kai ta ku gaisa da mai martaba" Still Abuturrab ya kasa cewa komai, sai da suka yi masa ixinin fita sannan ya mike ya fita xuciyarsa na tafarfasa, Alhaji Lawal yace "This should serve as a lesson for him, next time baxai sake yin abu gaban kansa ba" A bedroom dinsa ya tadda Aunty tana ta jiransa tana girgixa kafa, a sanyaye yake kallonta, Tace "What next now?" A hankali yace "I don't really know Aunty, but ni nasan baxan yi rayuwa da ita matsayin matata ba wllh" Aunty tace "Toh dama ina hakan xai yiwu, a ina xaka xauna da ita bayan ga Aneesah, uban me xaka ci da ita?? kuma idan ka saketa sani xa su yi?" Ya girgixa kai yace "That's what i have in mind Aunty, xan saketa babu wanda xai san hakan sai ke a gidan nan, quite alright xan tare da ita gobe din amma ba matsayin matata ba wllh" Aunty tace "Ai xaman naku ne bana so kwata kwataaa Abuturrab" Yace "Aunty a hankali ake bin komai" Tace "Toh da dai ya fi, don wllh abun dariya xaka xama gun colleagues dinka da yan uwanka, wa ka ta6a jin yayi irin wannan auren? Auren ma na yar talaka" A sanyaye yace "Na sani Aunty" Ta nufi kofa tace "Ba dai tarewa suke so ba, xaka tare din da ita sannan ni xan san abun yi" Daga haka ta fice a fusace, ko ba komai Abuturrab na samun relieve tunda akwai warce ke supporting dinsa dai. Daren ranan Umma ta kirasa yana kwance sai tunane tunane yake yana imagine yanda lkci daya Jiddah ta shigo rayuwarsa tana neman tarwatse masa farin cikinsa da kwanciyar hankali, a hankali ya dau wayar ya kai kunne bayan ya daga, cikin sanyin murya Umma tace "Kana ji na Aliyu?" Yace "Ina ji Umma" Tace "Kayi hakuri ka bi abinda iyayenka suke so sai kaga haske sosai a lamarinka, Yaya ta kirani ta min bayanin komai, ka janye batun saki, kaga dai yau jiddah kwananta uku ko sama da haka a gidan nan, amma har yanxu ban ga aibun yarinyar nan ba wllh Aliyu, gata da hankali da nutsuwa da sanin ya kamata ga uwa uba kawaici da hakuri, baxa kuma a dau lkci ba xata waye don na lura tana da kwakwalwa, taka kaddarar ce a haka ka amsheta hannu biyu Aliyu, kada ka mance Allah ne ya tsaro maku hakan kayi hakuri ka yarda da kaddara my son, duk sanda xaka koma wajen aiki sai ka dinga kawo min ita nan ina gwada mata abubuwa, daga nan din ta dinga xuwa boko da islamiyya, wllh lkci daya xata dawo dai dai taste dinka, nasan damuwarka kenan, in sha Allah xaka yi mamakin wayewar da Jiddah xata yi" Abuturrab yaji baci ransa kawai yake da wannan shawaran da ake basa, ya ma rasa abinda xai ce mata, how on earth suke tunanin xai iya rayuwa da yarinyar nan matsayin mata idan ba cutarsa suke son yi ba, ina duk burinsa na auren wayayyiyar mace me tsafta 100%, ji yayi kamar ya fara mata kuka wannan wacce irin kaddara ce haka ake forcing dinsa ya amsa, a ransa yace no way sai dai duk suyi hakuri, he just have to disappoint them because no amount of their sugar quinted mouth will convince him to live with that girl as wife, he will only live with her as a guardian.... Jin shirun yayi yawa Umma tace "Are u there son?" Ya runtse ido yana jin ransa na dada baci, cikin dakewa yace "Ina ji Umma, nagode Allah ya kara girma" Tayi murmushi tace "Ameen my son, Yaya tace min Abbanka yace ku tare gobe ko?" Cijen lips dinsa yayi yana jin wani mugun takaici, amma ya daure yace "Ehh haka ne" Tace "Toh Allah ya kai mu goben lafiya son, may Allah reward u abundantly for this deed" Ya bude idonsa da ya kada sosai.... forcing his self yace "Ameen" Sallama suka yi ya jefar da wayar kan gado xuciyarsa na tafarfasa ya mike xaune ya rike kansa. Washegari Saturday Umma na xaune dakinta tana kallon Jiddah dake juya kayan hannunta ta kasa sawa, jira take ta sa kayan ta gyara mata gashinta da ta sa ta wanke, murmushi Umma tayi da ta lura kunya ce yasa take hakan, sabon kaya ne da ta dinka ma Ramlah, sae ya kasance Ramla bata xo gidan ba har sannan shine ta ba Jiddan ta sa, mikewa tayi ta fita dakin, Jiddah ta bi ta da kallon gefen ido, sae a sannan ta fara sa kayan da sauri, wani kunya na musamman Allah yayi mata ita kam, komai da Umma ta bata ta saka sabo ne, sosai riga da skirt din ya amsheta kamar don ita aka dinka, kallon kanta ta dinga yi a madubin dakin tunda take iyakar atamfar da ta ta6a sa wa na dubu biyu ce, lkcn ko Ahmad ya kawo mata atamfa me tsada sae Hansae ta amshe ta siya mata roba roba ko half cotton, yau kam ga tsadadden atamfa ta saka duk da bata san me tsadan bane ba ma, bayan wani lkci Umma ta dawo dakin, sosai hankalinta ya kwanta ganin powder kawai jiddah ta shafa a fuska sai kwalli, ta bar mata har kayan kwalliya kawai don taga irin kwalliyan da xata yi sae gashi alama ya nuna iyakar kwalliyarta kenan ba irin na yan kauye take yi ba a lafta ja gira da jan baki, ta madubi take ta kallon jiddah da ta kasa kallonta, Jikin Umma yayi sanyi ganin irin kyan Jiddah, wai ma tun bata waye ba kenan, kuma jikinta bai fara samun hutu yanda ya kamata ba, ae balarabiyan Africa xa ayi a nan, a hankali Jiddah ta juyo tana kallon Umma, Umma ta sakar mata lallausan murmushi tace "Kinyi kyau my daughter" Jiddah tayi murmushin karfin hali, Umma ta xauna tace "Taho ki xauna in gyara maki gashin" Jiddah ta karasa ta xauna ta janye hulan Siyama dake kanta, Umma tace "Idan kin wanke gashi bari ake ya bushe kafin a sa hula kin ji?" Kai kawai Jiddah ta gyada mata, Unma ta fara taje mata dogon gashin nata, murmushi Umma tayi ganin tsayin gashin Jiddah a ranta kuwa tunani take ko ruwa biyu ce dai ita, sosai gashinta ke da kyau da tsayi sai dai babu gyara, Umma ta xuba mata man kai me yawa a gashin da ya dinga sheki da kamshi sannan ta yi mata parking da ribbon, mikewa Jiddah tayi tace "Nagode" Umma tace "Ki daura dankwalin yanxu" Jiddah ta dau dankwalin amma ta kasa daurawa, Siyama Umma ta kira tayi mata daurin, Siyama sae murmushi take tace "Kinyi kyau" xuwa yanxu har Maman Abdallah tasan matsayin jiddah a gidan, sae kusan karfe sha daya Umma ta bar gidan xuwa gidan yayarta da Jiddah, well ironed Hijab ne nude colour har kasa jikin Jiddah, kasancewar akwai kalan a jikin atamfar jikinta, sanyayyen kyau tayi, Hijab din yayi matukar amsarta, Driver ne ya kai su gidan don Ahmad kin amincewa yyi he knows definitely Abuturrab will be mad at him wato da shi xa a kai masa mata......




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah 


and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you





*mg's skincare*


Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩

Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️

Shin kinafama da

Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?

Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫

Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind

Bridal kit:18k

Beauty kit:11k

Student package:7k

Herbal whitening soap:3k

Chat

 08062991549

07046881166

07067210195

Call 08064532391

Facebook: mg's skincare

Instagram:glow_with_mgs

Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝

Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩

Then @mgs skincare gat you covered 💯

Now is time to glow😍

Pamper ur skin🦵

Shine like bride👰🏻♀

Glow🧖♀️


💯 tested nd trusted🤝

Guarantee



Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166

Umma ta sauka motar bayan drivernta yayi parking, Jiddah ma ta sauka tana kallon babban gidan, Umma ta kalli driver tace "Ka je kawai idan xan dawo anjima xan kiraka..." Cike da ladabi yace "Toh Hajiya" ta kalli Jiddah tace "Mu je" Bin bayanta Jiddah tayi tana tafiya a hankali har suka isa main parlor din gidan, kasancewar ranan asabar ne su Ramlah duk sun tafi islamiyya, Mai aiki ce kadai parlon tana aikace aikace, ban da kamshi babu abinda ke tashi parlon, mai aikin ta gaida Umma da ladabi, Umma ta amsa da fara'a tana mata sannu da aiki sannan ta kalli Jiddah tace "Toh xauna Jiddah" Xata xauna kasa Umma tace "Aa tashi ki hau kujera" Mikewa tayi ta xauna saman kujeran Umma ta nufi bangaren yayarta, sai a sannan Jiddah ta gaida mai aikin, matar ta amsa mata da murmushi tana ci gaba da abinda take, Muryar Abuturrab Jiddah ta ji ta d'an saci kallon gefenta amma bata gansa ba, slowly yake tahowa waya kare kunnensa yana waya tare da wani colleague dinsa da ya kirasa don jin ya jikinsa, murmushi Abuturrab yyi yace "Wato the sky misses me, not my co pilots" Murmushin kawai yake, daga karshe suka yi sallama da Captain Ishaq ya katse wayar ya nufi kitchen, 3 quarter ne jikinsa da farin T shirt, Mai aikin gidan Naja'at ta d'an risina ta gaishesa with respect ya amsa without looking at her, Jiddah ta bi sa da ido, har xai shiga kitchen ya juya coz he saw someone sitting amma bai kalli ko waye ba, suka hada ido, da farko bai ganeta ba sai da ya tsura mata ido, ita dai tayi kasa da nata idanuwan tace "Ina kwana" daga sama har kasa yake kallonta, Naja'at tace "Tana gaisuwa ranka shi dade" Juyawa yayi ya shige kitchen abun sa, Naja'at ta sunkuyar da kai sanin kadan daga abinda xai iya aika kenan, can ta d'an yi murmushi tana kallon Jiddah tace "Ina jin bai ji ba" Jiddah tayi murmushin karfin hali bata dai ce komai ba, Umma ta shigo parlon tare da Ummi, Ummi na kallon Jiddah tace "Sannu da xuwa" Jiddah ta gaisheta da ladabi, Ummi ta amsa da d'an murmushi fuskarta, Ummi na kallon Naja'at tace "Tafi dakin Hajiya Hafsah ta xo su gaisa da bakuwa" Naja'at tace "Toh Hajiya" daga haka ta wuce da sauri, Ummi ta xauna Umma ma ta xauna, gaba daya Jiddah sae taji ta kasa sakin jiki, duk ta takura, Ummi tace "Ya kika kara ji da jiki?" A hankali Jiddah tace "Alhmdlh" Abuturrab ya fito daga kitchen rike da cup din shayi yana juyawa da cokali, Umma ta dinga kallonsa, sannu da xuwa kawai yayi mata ya nufi dakinsa ya ajiye cup din shayin, ba a dau lkci ba sai gashi ya fito, ya karaso cikin parlon ya xauna yace "Ina kwana Umma" Da murmushi tace "Lafiya lau Abuturrab, ka tashi lfya?" Yace "Alhmdlh" Umma ta kalli Jiddah tace "Kun gaisa kuwa" Jiddah na kallonsa tace "Ina kwana" Ba tare da ya kalleta ba yace "Lafiya lau" Ummi dai kallonsu kawai take, Aunty ta shigo parlon ganin Umma tace "A'a Sannu da xuwa Hajiya Ramlah" Umma na murmushi tace "Yauwa, mun same ku lfya?" Aunty tace "Alhmdlh wllh" Aunty na kallon Jiddah tace "Sannu yan mata..." Jiddah ta gaisheta tana kallont, Aunty ta amsa ta nemi waje ta xauna, Ummi na kallon Abuturrab tace "Sai ka kai ta parlon Abbanku su gaisa tunda Kawunnanka na ciki" Abuturrab mood dinsa ya sauya lkci daya, Aunty dai sae murmushi take a xatonta ko 'yar uwarsu ce Jiddah warce bata sani ba, ganinta fara sosai kamarsu Ummin, Mikewa Abuturrab yyi, Umma na kallon Jiddah tace "Tashi ki bi sa" Ta mike a hankali ta bi bayansa, Ummi ta bi su da kallo, ba karamin kyau hijab din yyi mata ba har kasa kuma yake ja, Wani boyayyen ajiyar xuciya ta sauke, Aunty na gyara daurin dankwalinta tace "Bakuwa aka yi, kamar yar uwarku naganta ita ma fara, amma ban santa ba" Ummi na kallon Aunty tace "Ita ce yarinyar da yaje ya aura ae" Da sauri Aunty ta bi Jiddah da kallo idanuwanta kamar xa su fito, Daga Umma har Ummi kallonta suke, da wani confusion tace "Ita ce yar hayin??" Umma tace "Ita ce fa" Aunty ta hade rai lkci daya, can ta girgixa kai tace "Toh meye fa'idar kawota nan din tunda dai sakinta xai yi, haba ni dai ina ta kallonta ganin halin gidadanci a tare da ita, to yanxu meye amfanin xuwa da ita har ace taje ta gaida kawunnansa??" Wani kallo Umma tayi mata ta dauke kai, Ummi dai bata ce komai ba, Aunty ta ja wani tsaki ta mike ta fice daga parlon. Da sallama Abuturrab ya shiga parlon Abbansa Jiddah na biye da shi, Abba na xaune tare da yayansa da kaninsa, Abuturrab ya xauna kasa ya sunkuyar da kai, d'an nesa da shi ta xauna ta takure cikin Hijab, cikin sanyin murya ya gaishesu gaba daya, ko wannensu ya amsa mata da fara'a, Alhaji Lawal na kallon Abuturrab yace "Ita ce?" Abuturrab yyi karfin halin cewa "Ehh" Duk suka amsa da maa sha Allah, Ita dai Jiddah kanta na kasa, Abba yace "And there is nothing wrong with her, Allah ubangiji ya baku xaman lafiya" Sae a sannan Jiddah ta dago tana kallon Abba, Abuturrab dae ya kasa dago kansa, nasiha dattijan suka shiga yi masu a tare, Jiddah dai sae bin su take da kallon don gaba daya bata gane inda suka dosa ba, a xatonta wanda aka ma aure ake yi ma irin wannan maganganun da suke mata, ya xa ayi ta bi shi kamar yanda suke cewa, tayi masa biyayya sannan tayi hakuri, Abuturrab dai ya ki dago kansa, Sun fi minti talatin suna abu daya daga karshe suka masu addu'a da fatan Allah ya kade shaidan a xamansu, A hankali Abuturrab ya dago yace "Ameen nagode Abba" Kudi ko wannensu ya ciro ya mika mata ta ki amsa tana kallonsu duk kana ganinta kasan she is confused, Abuturrab ya daga kai ya kalleta, can ya karasa ya amsa kudaden, Uncles din nasa suka ce ya siya mata duk abinda take so, ya amsa masu da in sha Allah, Abba yace "Yau din xa ku wuce can gidan naka, amma kafin nan ka kira mai martaba" Kai kawai Abuturrab ya gyada masa a hankali, sannan ya mike yana kallon jiddah, k'in tashi tayi, Alhaji Ibrahim ya mata murmushi yace "Tashi ku je, Allah yayi maki albarka" Mikewa tayi, Alhaji Lawal yace "Ya sunan nata?" Ta sunkuyar da kanta Abuturrab ya d'an fara kame kame yace "Ummi ce..." Abba ya d'an yi murmushi yace "Hauwa sunanta" Duk suka amsa da maa sha Allah, Alhaji Lawal yace "Baki da matsala a rayuwa idan kika yi halin me wannan sunan ta gidan nan, A very simple life" murmushi kawai Abba yayi, Abuturrab ya nufi kofa Jiddah ta juya ta bi bayansa, sai da suka fita ya kulle kofar yana mata wani irin kallo yace "Ke wace irin dakikiya ce ana maki magana kiyi ta kallon mutane kamar wawuya kiyi shiru..." Kallonsa kawai take da manyan idanuwanta ko kiftawa babu, ya nuna mata parlon fuska daure yace "Koma kiyi masu godiya ko ajiya kika basu kudin da suka baki?" Ba musu ta juya ta bude kofar ta shiga parlon, duk kallonta su Abba suka tsaya yi, ta tsugunna hawaye har ya kawo idonta cikin sanyin murya tace "Abba nagode Allah ya saka da alkhairi" Duk suka amsa mata da Ameen, suka kara sa mata albarka sannan Alhaji Lawal ya umarceta da ta tashi ta wuce, mikewa tayi ta nufi kofa ta bude ta fita ta rufe masu kofar, tsaye ta tadda Abuturrab bakin kofar yana jiranta, ta sunkuyar da kanta, ya fara tafiya, bin bayansa tayi tana tafiya a hankali, babu kowa parlon, ganin xai hau sama ta nemi waje parlon ta xauna, kamar ance ya juya ya ganta ta xauna a parlor, hade rai yayi sosai yana kallonta, ta mike tsaye ita ma tana kallonsa, yace "Xo ki wuce" Ta nufesa gabanta na faduwa, sai da yaga ta kusa iso shi sannan ya fara tafiya, tana biye da shi har suka isa dakin Aunty, Kulle kofar yayi bayan Jiddah ta shigo, Aunty ta tamke fuska ganinta, ya xauna kan stool din gaban mirror yana kallon Aunty a hankali yace "The lady..." Aunty ta wani ta6e baki hade da tafe hannu tana kallon Jiddah, lkci daya ta girgixa kai tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wllh ka cuci kanka  Aliyu, me xaka yi da bagidajiya domin Allah, sai ku ce sai kunyi taimako, taimakon da yanxu idan mutum yayi yake xame masa sharri, to dai ga naka nan ya xamar maka sharri babba, da ajinka, da kyanka, da ilimin ka da kudinka, ina xaka kai wannan fisabilillah? Ina kai ina wannan Aliyu? Wllh wllh banyi baccin kirki a kan lamarin nan ba jiya" Sunkuyar da kai Jiddah tayi har lkcn ta kasa gane kan komai amma duk jikinta yayi sanyi har hawaye ya kawo idonta don saurin kukanta, Abuturrab ya lumshe ido, bai ji dadin maganganun Aunty a lkcn ba, he wish she was even speaking just English at that moment, ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace "U need not to worry Aunty as soon as possible i will find a solution, I've told u everything, you just have to trust me aunt" Yana fadin haka ya mike yana kallon Jiddah kafin yace komai ta juya ta bude kofar ta fita daga dakin, Aunty taji har ranta ta tsani Jiddah, and she will do everything Abuturrab ya datse auren nan balle ma tasan tunda yace xai saketa xai saketa din... Suna fitowa Abuturrab ya fara tafiya, bin bayansa Jiddah tayi a hankali tace "Umma fa?" Ya juyo ya kalleta bai bata amsa ba ya ci gaba da tafiya sai ga Umman ta fito dakin Ummi, ganinsu tace "Yauwa dubawa xanyi dama ko kun fito" Jiddah ta nufeta, Umma tace "To mu shiga ciki" Umma na juyawa Jiddah ta kalli Abuturrab, hararanta yyi ta bi bayan Umma suka shiga parlon Ummi, jingina yyi da bango ya rufe idanuwansa, idan ba avoiding yarinyar nan xai dinga yi ba ko da suna xaune gida dayan ae wataran bubbugeta xai yi a banxa, she is just too dopey for his liking, kwafa yayi ya bude ido ya bar wajen.... Har bayan magrib Jiddah na part din Ummi, a lkcn kuma Umma ta shirya xata wuce don har ta kira Driver, Suna bedroom tare da 'yar uwarta Jiddah kuma na parlor tana kallon tv dake ta aiki, duk ta kagu Umma tace mata su tashi su wuce, duk yan matan gidan kowa ya shigo kallon sama har kasa yake mata sannan ya fita, Ramlah ce kawai ta tsaya suka gaisa, Ummi na kallon Umma tace "Toh ki kara mata fada ni dai kinsan babu abinda xan ce, har yanxu Ramlah i am finding it hard to believe Aliyu is married, ganin abun nake kamar mafarki, i still don't have the courage to start telling this to relatives and frnds, to me ma xance masu Ramlah? Waliman da Uban nasa yace ayi yace baxai yi ba shi, nima dama I'm not in support of that" Umma ta kwantar da murya tace "Yaya kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki, in sha Allah xa mu yi alfahari da wannan auren gaba dayanmu, duk mu yi hakuri mu bar ma Allah komai, Ae Allah ya ga xuciyar mu gaba daya, bama nufin d'an kowa da sharri mu bi su da addu'a kawai" A sanyaye Ummi tace "Ikon Allah, idan wani yace min haka xae ta6a faruwa a household dina baxan yadda ba wllh, duk burin da aka ci a kan bikinsa a haka ya tarwatse??" Umma tace "Haka Allah ya so, ynxu duk abinda Allah ya hore maki sae kiyi mata yaya kinga marainiya ce, nima xan yi nawa, amma kar ki manta da kayan Ramlan don bata da wanda xata sa idan sun tafi yau din" Ummi bata sake cewa komai ba duk jikinta yayi sanyi sosai, Umma tace "Xan sake yi mata nasiha yanxu kafin driver din ya karaso" Daga haka ta fita Ummi ta bi ta da kallo ta girgixa kai tace "Ikon Allah, so all this isn't a dream" Jiddah na ganin Umma hankalinta ya kwanta a tunaninta xa su wuce, ta mike Umma tace "A'a xauna" Xaunawa tayi tana kallon Umma, Umma tace "Abuturrab ae ya maki bayanin komai jiya ko?" Kallonta kawai Jiddah ke yi, can tace "Na me Umma?" Umma tace "Auren ku" a sanyaye Jiddah tace "Ehh yace min an daura min aure da wani, amma wanin xae sakeni sae in dawo wajenki kuma in xauna" Innocently ta fadi hakan tana kallon Umma, Umma ta d'an yi murmushi, lkci daya taji tausayinta ya rufeta, can tace "Bai gaya maki da wanda aka daura maki auren ba?" Jiddah ta girgixa kai tace "Aa bai gaya min ba" Shiru Umma tayi tana tunanin ya kamata tayi breaking mata news din ma kuwa, ajiyar xuciya ta sauke sannan tace "Toh shkkn, d'an xaman da muka yi dake Jiddah naga kina da hakuri da kawaici, sannan kina da hankali, to ki ci gaba a haka kinji, me hakuri shi ke cin riban xaman duniya sannan ki xama me rikon addininki sallah a kan lkci, tsaftar jikin ki, duk ae na nuna maki yanda xa ki dinga yi a gida, kinsan daga inda kika fito Jiddah, ki rike maraicinki, kiyi hakuri a duk halin da kika tsinci kanki" Jiddah ta gyada mata kai lkci daya hawaye ya kawo idonta, abinda Umma bata so kenan duk mutum xai yi hawaye gabanta sae taji xuciyarta ya karaya, tana da rauni sosai, hakan yasa ta mike tace "Drivern ma na kirana ya iso ina jin" Jiddah ta mike da sauri cikin rawan murya tace "Umma ba da ni xa ki koma ba?" Umma ta kasa kallonta tace "Abuturrab xai dawo dake, ae baku yi sallama da Abba ba, Abban na dawowa bayan kunyi sallama xai dawo min dake" Umma na fadin haka ta shiga daki gun yayarta, Jiddah ta bi ta da kallo hawaye me xafi na sauka idonta, ba a dau lkci ba Umma ta fito, murmushi tayi tace "Toh idan baxa ki daina kukan nan ba sae ince ya bar ki nan ki kwana biyu kafin ya dawo min dake" Da sauri ta share hawayenta, Umma tace "Toh ko ke fa, yanxu Abban xae shigo sae Abuturrab din ya dawo dake a motarsa" Gyada mata kai Jiddah tayi, Umma tace "Sae kun karaso" Daga haka ta fita, Jiddah ta koma kasa ta xauna a hankali wasu sabbin hawayen na sauka idonta.... Karfe takwas da few minutes Abuturrab ya shigo parlon, tun tafiyar Umma Jiddah ke ta xaune parlon ita kadai, Ummi kuma na bedroom dinta, kallo daya yayi ma Jiddah ya karasa dakin Umminsa, Jiddah ta shiga saka hannun hijab dinta hoping ynxu xai ce mata ta tashi ya maidata gidan Umma, Abuturrab ya karasa gun Umminsa dake xaune ita kadai dakin, kasa kallonta yayi kansa a kasa yace "Ummi xan wuce" Tace "Allah ya kiyaye" Bai iya yace komai ba, Ummi ta ci gaba da duba littafin hannunta, a hankali yace "Sae da safe" Tace "Allah ya tashemu lafiya, ga akwatin kar ka manta" Ya kalli trolley din ya karasa ya daga ya juya ya fita dakin, yana shigowa parlon ya kalli Jiddah dake jiran taji yace tashi mu tafi yace "Ki shiga kiyi ma Ummi sai da safe" Ba musu ta mike ta shiga dakin Ummi, ta sunkuyar da kai tace "Ummi sae da safe" Ummi ta kalleta tace "Allah ya tashemu lafiya" Juyawa Jiddah tayi ta fita, har sannan Abuturrab na tsaye yana jiran fitowarta, ganin ta fito ya fara tafiya, Bin bayansa tayi har suka fita, ko da wasa bai yi tunanin shiga bangaren stepmom dinsa ba sanin wani maganan da xai bata masa rai xata yi, yana fita su Safiyya da Aisha dake xaune parlor suka dinga kallon jiddah, kofa ya nufa duk suka yi masa sai da safe bbu warce ya tanka cikinsu, Basu ce ma Jiddah ba ita ma bata ce masu ba, a tare duk suka ta6a baki banda Ramlah da ta bi Jiddah da kallo, a booth ya saka trolley din, ya bude driver seat ya shiga ya tada motar, Jiddah dai na tsaye bata ma san inda xata shiga a motar ba, ya wani hade rai ya sauke glass din yana kallonta yace "Rokanki xan yi ki shigo?" A hankali tace "Toh ban san inda xan shiga ba" irin kallon da ya dinga yi mata ya sa ta bude back seat ta shiga ta rufe motar, gaba daya sae taji ta tsorata da shi, amma lkcn da yake xuwa can gidansu ae baya hararanta ko yayi mata ihu haka, sunkuyar da kanta tayi har hawaye ya kawo idonta, yayi horn mai gadi ya bude masa gate ya fita gidan, driving kawai yake amma gaba daya yyi nisa tunanin da yake, wai shi yau xai tafi gidansa da yaki budewa wishing to go in with his wife first, sai gashi da wannan yarinyar xai je, wannan yarinyar fa, tunanin hakan yasa yaji kamar ba a ta6a abinda ya cucesa a rayuwa irin wannan lamarin ba, ya runtse ido ya bude still driving, ae idan ya kwana ma da auren yarinyar nan yau yana da ra'ayin rayuwa tare da ita kenan, Ahmad ne ke ta kiransa tun fitowarsa amma yaki daga wayan haushin kowa kawai yake ji shi yanxu, tafiyar minti talatin da biyar yayi ya isa gidansa dake U dosa, dai dai gate din gidan ya tsaya ya dau makullin gate din ya karasa ya bude gate din sannan ya dawo ya shigar da motar compound din gidan, Jiddah dai sai bin gidan take da kallo don bai yi kama da gidansu Umma ba, sauka yyi motar bayan ya kashe ya karasa ya rufe gate din ya cire makullin ya koma gun motar, ya bude booth ya sauke trolley din, har sannan Jiddah ta ki sauka daga motar, bayan ya rufe booth din ya bude side dinta yana kallonta fuskarsa ba fara'a, sauka tayi tana sake bin gidan da kallo ta kara tabbatarwa ba gidan bane duk da shi ma din gidan sama ne, ta marairaice tana kallonsa tace "Ae ba nan bane gidan" Wani kallo yyi mata ya ja trolley din, bin bayansa tayi da sauri a d'an tsorace tace "Gidan Umman fa??" Ganin har ya shiga parlon ta shiga ita ma ya kunna wuta da ya haska ko ina na parlon, komai na parlon sabo ne, ba kuma karamin haduwa parlon yayi ba, ta dinga bin babban parlon da kallo kamar idanuwanta xa su fito, rufe kofar yayi yasa makulli, sae a sannan ta fashe da kuka a hankali tace "Gidan Umma ae aka ce ka kai ni fa" Biron da ya saka a aljihunsa tun daga gida ya ciro sannan ya wuce sama sanin baxai rasa takarda a bedroom dinsa ba, bin bayansa jiddah tayi hawaye na xuba idonta, ganin hanyar da ya bi bayan ya hau saman ta bi da sauri ita ma don tsoron gidan take, wani kofar da taga ya shiga ta bude taga wani babban parlon hadadde, tsaye tayi bakin kofar gabanta na faduwa, bayan few seconds sae gashi ya fito rike da farar takarda......






Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788...  Do justice to ur self by subscribing before reading.... Thank you

Jiddah dai na tsaye bakin kofar parlon tana share hawayen da ya ki tsaya mata, saman kujera Abuturrab ya xauna bayan ya ja center table din parlon right in front of him, ya daura takardan a kai ba tare da ya kalleta ba, babu yabo babu fallasa yace "Shigo ciki..." A hankali ta karaso cikin parlon tana share idonta, ta rakube jikin one sitter din parlon ta tsaya tana kallonsa, daga kai yayi ya kalleta ya nuna mata kujeran alamar ta xauna, ta xamo kasa ta xauna, bayan few seconds, speaking calmly yace "Shekaranjiya na gaya maki an daura maki aure, right?" Jin tayi shiru ya ajiye biron hannunsa yace "Tambayarki nake" Ta gyada masa kai tana kallonsa, yace "Kuma baki san da wanda aka daura maki auren ba ai koh" Nan ma ta gyada masa kai, a takaice yace "Ohkk... Da ni aka daura auren" Kallonsa kawai Jiddah take kamar bata gane abinda yake nufi ba, not minding that ya langwabar da kai yace "Shi yasa kika ji a can gida suna maki nasiha" a hankali Jiddah ta sauke idonta kasa, taji xuciyarta na bugawa da sauri da sauri, yace "Na aure ki ne kawai don ceto rayuwarki daga matar mahaifin ki, na aure ki ne saboda naga xa a cuce ki xa a lalata maki rayuwa, na aureki ba don naje da niyyar yin hakan ba, don haka bani da xabi da ya wuce in sakeki, wannan sakin kuma da xan maki tsakanina dake ne kawai...." Da duk idanuwanta take kallonsa jin furucinsa na karshe, cikin sanyin murya tace "Xaka sakeni?" Yace "Ehh xan sake ki" Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, shi ma shirun yyi yana kallon hotonsa dake parlon yana sanye da wear dinsa na pilot, muryarta ya ji tace "Idan ka sakeni sai in koma wajensu Umma kenan?" Ya girgixa kai, cikin nutsuwa yace "Aa a nan gidan xaki xauna, kamar yanda na fada maki sakin nan xai kasance sirri tsakaninmu, babu wani da xai san na sake ki...." Tayi shiru bayan few seconds tace "Toh ae ni ba muharramarka bace da xa mu xauna gida daya bayan ka sakeni...." Kallonta ya dinga yi da mamaki jin furucinta ba don shi ta fada ma ba idan wani yace masa ta fadi hakan baxai ta6a yarda ba, can yace "A ina kika san wannan?" Tana wasa da fingers dinta ba tare da ta kallesa ba tace "Lokacin da nake xuwa islamiyya" Surprisingly yake ta kallonta, can  yace "Ohh i see... amma kuma basu koyar dake hukuncin wanda ya kashe kansa ba kuma?" Kallonsa Jiddah tayi amma taki cewa komai, ya jefa mata wani shegen kallon da yasa ta koma baya a hankali, idonta har ya fara kawo ruwa, yace "Ke a tunaninki rashin sakin ki kadai ne xai sa mu xauna gida daya kenan, idan ban sakeki ba shine kike muharramata koh?" Shiru tayi bata ce komai ba yace "Bude baki ki bani amsa malama" A hankali tace "Nima ban sani ba" Wani kallo ya sake jefa mata ta sunkuyar da kanta, yace "Xan sakeki kuma xa mu xauna gidan nan tare, don mun xauna gida daya tare ba yana nufin ganina xaki dinga yi ko ganinki xan dinga yi ba, kinsan matsayinki gidan nan, nima haka, balle ma ni daga ranan lahadi da yamma xuwa juma'ah ina wajen aiki, kina tunanin sati da lahadin ma idan na dawo ganina xa ki dinga yi??" Ita dai bata ce masa komai ba, yace "Don haka ki cire tunanin yan kauye dake ranki yanxu, komai kike bukata xan baki waya da xa ki dinga kirana, sannan idan ba abu me ma'ana ba dama kar ki kuskura ki kirani, nan da wani lkci xaki fa islamiyya da boko...." Sai a sannan ta daga kai ta kallesa cikin sanyin murya tace "Toh nagode Allah ya saka da alkhairi" Bai tanka ta ba ya soma rubutu a takardan gabansa, kallonsa kawai Jiddah take babu ko kiftawa, yayi rubutu wanda iyakarsa layi biyu xuwa uku sannan ya dago kai yana kallonta, da sauri ta sauke idonta kasa, yace "kin iya karatu?" A hankali ta girgixa masa kai, sai kuma ta gyada masa kai alamar xata iya, ya mika mata takardan yana kallonta, ta mike ta karasa ta d'an risina ta amsa takardan tana kallo, bayan few seconds ya mika mata hannu alamar ta basa takardan, ta dago kai, hawaye ya gani makale idonta ta mika masa takardan ya amsa sannan ya linke without looking at her yace "Wannan tsakaninmu ne da ke, har abada bance ki sanar ma kowa ba idan ba haka ba......" Daure fuska yyi yana kallonta bayan ya fadi haka, ta gyada masa kai a hankali hawayen idonta ya silalo, mikewa yayi ya linke takardan tsaf sannan ya shiga bedroom dinsa ta bi sa da kallo, ba a dau lkci ba ya fito, kofar fita ya nufa yace "Mu je in nuna maki dakin da xaki xauna" Juyawa tayi cikin sanyin jiki ta bi bayansa, bangaren suka bari gaba daya, ya bude wani daki wanda akwai komai a ciki yana kallonta yace "Ga dakin ki nan, kinga can bangaren nawa ko by mistake, kinsan me nake nufi da by mistake?" Ta girgixa masa kai alamar A'a, yace "Ohk, ina nufin ko bisa kuskure kada ki kai kafarki can, iyakar ki nan dakin, ko parlon kasa idan ina gari bana son kina xama, idan bana nan xaki iya xaman ki can, sai kuma kitchen, komai xan ajiye maki a ciki ki girka duk abinda kike so" Ta gyada masa kai kawai, yace "Yanxu ki tafi kasa jakar nan ki kawo dakin ki, gobe da safe xa mu fita xan siya maki duk abinda xaki bukata, sai ki xaba komai da kanki" Nan ma kai kawai ta gyada masa yace "Kin ci abinci ai a can gida?" Ta gyada masa kai nan ma, yace "Good" downstairs ya nuna mata yace "Tafi ki dauko jakanki, kayan da xaki dinga amfani dasu ne a ciki" Ba musu ta fara sauka kasa, ya bi bayanta suna shigowa parlon ya nufi kofa ya sa makulli, ta dau jakar ta koma sama, kashe wutan parlon yayi, sannan shi ma ya wuce saman, tsaye ya ganta bakin kofar dakin da ya nuna mata, a hankali tace "In shiga?" Ya daure fuska yace "Ehh" Bude kofar tayi kafin ta shiga ciki yace "Gobe karfe takwas xa ki sauko kasa" Ta gyada masa kai, sannan ta shiga dakin ta kulle, ya kashe wutan corridor din ya nufi bangarensa. Bin dakin da kallo Jiddah ta dinga yi, sai take ganin abun kamar a mafarki wai yau ita ce xata kwanta saman wannan katon gadon ita kadai, to ko dai bai ce ta kwanta ba? Kar ta kwanta kuma yace mata don me, a hankali ta kai jakar can jikin bango ta ajiye sannan ta dawo ta xauna kasa tana sake bin dakin da kallo, ta fi minti talatin xaune a kasa, can ta tuna abinda Umma tace mata duk dare kafin ta kwanta ta dinga yin wanka, mikewa tayi tana kallon jakar da yace mata kayan da xata dinga amfani da ne a ciki, ta karasa gun jakar ta kwantar sannan ta bude, tawul ta fara cin karo da sabo, ta ajiye gefe, taga sabulu da soso da Toothpaste and toothbrush, su ma ta ajiye a gefe, sannan taga sabbin undies, da turarruka da mayyuka sai kayan kwalliya, kallon kayayyakin ta dinga yi, lkci daya hawaye ya kawo idonta, xaunawa tayi nan kasa ta hade kai da gwiwa tana shessheka, gani take kamar Hansai xata xo ta haureta ko ta watsa mata ruwa sai ta farka taga duk mafarki kawai take, ta fi minti sha biyar tana kukan kafin ta dago kanta har sannan hawayen yaki tsaya mata, ta dinga share idonta daga bisanni ta mike ta cire Hijab din jikinta, kamar yanda Umma tace mata bata ajiye Hijab din haka ba sai da ta linke, sannan ta soma cire kayan jikinta, ta dau tawul din ta daura ta shiga bandaki, tun daga gidan Umma su Huraira da Maimuna sun nuna mata yanda ake amfani da komai na cikin bayi, cikin kankanin lkci kamar ana koranta tayi wanka ta fito bandakin, bayan ta gama goge jikinta ta dau lotion daya ta bude ta fara shafawa, wani doguwar riga mara nauyi duk da ba na bacci bane ta dauka ta saka, sannan ta maida komai cikin jakar ta rufe ta mayar jikin bango, darduman da ta gani ta shimfida don tayi alwala, ta gabatar da sallan isha sannan ta linke darduman da hijab din ta ajiye, komawa tayi ta rakube ta xauna a kasa, tana ta xaune tana tunani iri iri, taji bacci ya fara fixgarta, tsoron hawa saman gadon take yace tayi laifi, hakan yasa ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta kwanta nan kasan tiles ta dukunkune waje daya, nan da nan bacci ya dauketa, sai dai kafin asuba ba karamin wahalar da ita sanyi yayi ba, baccin ma bata yi me dadi ba sbda sanyi da ya isheta, a haka har aka kira sallan asuba, abun ka da wanda ya saba, tun kafin a tada sallah ta tashi ta tafi bandaki ta dauro alwala, da kyar take numfashi sbda hancinta da taji ya toshe, ga ciwo da kanta ke yi, tana xaune saman darduma bayan ta idar da sallah aka bude kofar dakin, da sauri ta juya suka yi ido hudu da shi, sanye yake da jallabiya, ta sunkuyar da kanta, ya rufe kofar ya nufi bangarensa, sai a sannan ta dago kanta jin ya rufe kofar dakin. Har gari ya waye Jiddah na xaune saman darduma sai dai fa babu abinda take, ko d'an azkar din nan babu, kawai sabo da tayi da rashin komawa baccin asuba ne, bakwai saura ta mike ta shiga bandaki ta wanke baki tayi wanka sannan ta fito, wani atamfar ta saka bayan ta shafa mai ta saka turare dai yanda ta ga su Maimuna na yi, tana ta xaune dakin lkci lkci tana duba agogon dake dakin, har taga karfe takwas yayi, mikewa tayi ta dau Hijab ta saka sannan ta nufi kofa ta bude a hankali ta fita, kamar mara gaskiya ta dinga sauka stairs din har ta iso main parlor din, karan Tv ta ji, ta leka parlon ta gansa kwance saman dogon kujera idonsa a lumshe, kasa karasawa tayi cikin parlon, ta fi minti goma a tsaye kamar munafuka, daga karshe ta juya a hankali ta koma saman, xaunawa tayi a kasa ta jinginar da kanta da gado, tana ta xaune a haka har bayan awa kusan daya taji an bude kofar dakinta, da sauri ta juya, suna hada ido ya daure fuska yace "Baki san agogo bane?" Ta kalli agogon dakin dake nuna karfe tara saura mintuna kadan, a hankali tace "Na sauko karfe takwas naga kana bacci shine na koma" da mamaki yake kallonta, can yace "To meye damuwarki da baccina ba ni nace ki sauko lkcn ba?" Ta gyada masa kai, juyawa yayi ya bar bakin kofar, ta mike tana gyara hijab din jikinta ta bi bayansa, xaune ta samesa a parlon ta karasa ta rakube kasa jikin kujera ta xauna yana kallonta daga sama har kasa yace "Babu wani Hijab din ne a jakar?" Tace "Akwai" Yace "To bana son maimaita kaya... Koma ki canxa hijab din" Mikewa tayi ta wuce sama a sanyaye, ba a dau lkci ba sai ga ta ta dawo da wani Hijab din navy blue colour, shi ma har kasa, sosai Hijab din ya haskata kasancewarta fara, ta koma inda take ta xauna ba tare da ta kallesa ba, bayan few minutes yana kallonta yace "A gidanku idan an tashi da safe ba a gaisuwa?" Ta d'an buda ido tace "Ina kwana" Bai tanka ta ba yana kallonta jin voice dinta da ya canxa yace "AC din dakin kika kunna?" Da sauri tace "Aa ai ban iya kunnawa ba" Yace "Da ruwan sanyi kika yi wanka?" Ta girgixa kai tace "Aa na xafi na tara" Yace "Kin bude windows din dakin ne?" Nan ma ta girgixa kai tace "Ban san ma ya ake budewa ba" She looks so Afraid, don with authority yake mata tambayar, bayan ya gama kallonta da kyau yace "A ina kika kwanta?" Tana jan fingers dinta a hankali tace "A kasa" Da mamaki yake kallonta, can dai yace "Saboda me?" Innocently tace "Ai baka ce in hau saman gadon ba" Dauke idonsa yayi daga kallonta, bai ma san wani reaction xai yi ba, she sounds very funny, can dai ya sake kallonta yace "To daga yau nace ki dinga hawa saman gadon, anjima da daddare xan baki bargo da xaki dinga rufa" Cikin sanyin murya tace "Toh nagode" ya nuna mata basket me dauke da breakfast da Umma ta aiko masu da shi, yace "Ga ya can ki je ki karya" Ba musu ta mike ta isa wajen, babu abinda babu wajen har cup da spoon da plate, ganin yanda take ta kallon basket din bayan ta duka a wajen yace "Ki bude dukka ki xuba abinda kike so" A hankali ta shiga bude warmers din, wainar shinkafa da lafiyayyen miyarsa na naman rago, sai fried Irish da kwai, ga kuma bread da pepper soup din hanta xalla, kallonta kawai yake, ta dau plate ta debi waina biyu xata kara daya suka hada ido, mayarwa tayi, yace "Juye dukka" Da sauri ta kallesa tace "Ya min yawa ai" Ya hade rai yace "Juye nace" Ta kalli wainar da xai kai sha uku tace "Wllh tllh baxan iya cinyewa ba" Hade rai yayi sosai yana kallonta can on a serious note yace "Bana son rantsuwa a gidana, kada ki sake" Sauke kanta tayi ta xuba wainar guda biyar sannan ta debi miya, xata mike yace "Hada shayin" Ta hada shayin ta koma can jikin kujera ta xauna, lkci lkci take satan kallonsa tana cin abincin gabanta, daga karshe ya mike ya wuce sama ganin she isn't comfortable, ta bi sa da kallo. Bayan kusan awa daya Abuturrab ya sakko rike da makullin motarsa, kananun kaya ne jikinsa as usual, Jiddah na ta xaune bayan ta gama wanke plate da cup din da ta karya a kitchen, kashe tv dake aiki yayi ya kashe fitilan parlon ba tare da ya kalleta ba ya nufi kofa yace "Ki sameni waje" Mikewa tayi ta bi bayansa, takalmanta ta gani bakin kofar fita ta saka sannan ta fita, yana tsaye waje yana jiran fitowarta, tana fitowa kuma ya kulle kofar da makulli ya nufi can gate, ya bude gate din sannan ya karasa parking lot ya bude motarsa ya shiga, slowly take tafiya har ta iso parking space din, ya gama warming motar sannan ya kalleta yace "In roke ki kafin ki shiga motar?" Bude back seat tayi ta shiga, bai dai ce mata komai ba ya fara driving ya fitar da motar kofar gida, sannan ya sauka ya kulle gidan ya koma cikin motar, Driving Abuturrab yake yana tunanin shopping mall da xa su, daga karshe ya dau hanyar ASD city mall, suna isa yayi parking ya bude motar ya sauka, Jiddah ta sauka ita ma, don yanxu kam ta iya bude mota, ganin inda ya nufa ta bi bayansa, shopping cart ya dauka tana biye da shi, wajajen turarruka ya fara nufa ya tsaya ya rungume hannu yana kallonta babu yabo babu fallasa yace "Debi turaren" tace "Ai a jakar kayan nan akwai turare hudu" Wani shegen kallo yayi mata yace "Debi turare nace my frnd" Diban turaren ta fara yi wanda wasu body sprays ne a wajen tana xubawa a cart din, takaici ya sa ya ma kasa ce mata komai, she's not even making any effort to check for the ones with better scent diba kawai take, cikin husky voice dinsa yace "koma gefe" A hankali ta ja ta tsaya a gefen tana kallonsa, gun sealed tsadaddun turarurruka ya karasa ya xabi hudu ya xuba a cart din, a takaice dai turaren da suka diba a wajen xai kai kala sha uku kamar abinda kadai ya kawosa mall din kenan, dubu dari biyu Abbansa yayi masa transfer a yau da safe yace ya siya mata duk wani abinda take so, ga wanda uncles dinsa suka bata a jiyan, gun mayyuka ya nufa next tana biye da shi tana tura cart din da ya sakar mata, wayarsa ya ciro aljihu yayi dialing number Aneesah warce har yau bata san abinda ke faruwa ba, yasab Aunty ma baxata yi gigin sanar mata ba, shi ma kuma bashi da intention din sanar mata, tana dagawa cikin cool voice dinsa yace "Aneesah wani cream kike shafawa pls?" Daga daya bangaren tace "Ohh body cream?" Yace "Yeah" fada masa tayi, ya d'an yi shiru har sai da tace "Are u there?" Yace "Yeah, amma ba na lightening bane ko?" Daga daya bangaren tayi dariya tace "To ka mance ni fara ce, lightening din me kuma my captain?" Kallon Jiddah dake tsaye ta rakube waje daya yayi, yace "ohk, haka ne" Tace "Ba na bleaching bane kamar yanda kake tunani, amma kuma me kyau ne, yana fito da ainahin complexion din mutum, sannan yana sa jiki yayi glowing, me tsada ne sosai" Abuturrab ya d'an yi murmushi yace "Ohk, text me the name now ina jira, and sorry.... Har da sabulu, infact da duk wani abinda kike amfani da shi na gyaran jiki ki turo min ta text ynxu" Tace "Uhmm my Captain lefe ka fara hadawa ne?" Bai san lkcn da ya fara murmushi ba yace "Yea, with perfumes da kike amfani da" Farin ciki ne sosai a voice dinta, tace "Alright my captain, i will now" daga haka ta katse wayar, jan cart din yayi suka tafi bangaren undies kafin Aneesah ta turo masa text din, gefe ya ja ya tsaya ya rungume hannunsa yana kallonta yace "Ko shi ma ni xan xabar maki?" Kasa kallonsa tayi wai duk kunya, ta sunkuyar da kanta inda take tsaye, yace "Heyy kina bata min lkci" A hankali ta karasa ta fara daukan panties din tana ajiyewa a cart din, ya hade rai yace "Idan kika dauki wanda suka fi karfin ki kina da wanda xaki ba ma ne?" Kasa kallonsa tayi kamar xata yi kuka, yace "Madam kina bata min lkci fa, baxa ki dinga dubawa ba...." kamar xata yi kuka tace "Ni baxan iya ba" that sounds so funny, amma ya dake yace "Baxa ki iya me ba?" Juya masa baya tayi, bai san lkcn da ya d'an yi murmushi ba, karasawa yayi ya gun undies din, daga sama har kasa ya kalleta doing survey with his eyes, ita dai ta ki juyowa, da kansa ya xabar mata undies din ko wanne dozen dozen, ya tura cart din ya bar ta wajen a tsaye, satan kallonsa tayi, sai kuma ta fara bin sa a hankali, gun nighties ya tsaya nan ma ya xabi sha biyu.... Kananun wears ma ya xabar mata isassu, ganin she is already tall, flat shoes iri iri masu kyau ya xabar mata shi ma dai kusan sha biyu, da handbags, a mall din nan atamfofi ne kawai Abuturrab bai siya mata ba, komai da mace xata bukata sai da ya siya ma Jiddah enough a lkcn, sai dai idan cart din ya cika ya ajiyesa sa can gun da xa abiya kudi ya dau wani shopping cart din, Creams da sabula da turarrukan da Aneesah ta turo masa ne karshen abinda ya duba a mall din, kala uku ya dau mata cream din da sabulu da shower gel, turarruka kuwa kala biyar kawai ya kara mata har da miski a ciki, a mall din Abuturrab yayi azahar, Jiddah dai iya gajiya ta gaji, bayan ya biya duk kudin kayan an kai masa mota ya nufi bangaren cin abinci dake cikin mall din, Jiddah dai na biye da shi, xaunawa yayi ya nuna mata table din dake opposite din wanda ya xauna yace "Can xa ki xauna" Karasawa tayi ta xauna wajen tana kallonsa, fried rice yayi ordering da kaza sai Chivita da bottle water, bayan an kawo masa abincin a gabansa ya juya ya kalleta, da sauri ta sunkuyar da kanta, yace "Me xa ki ci" Ta girgixa masa kai tace "Aa na koshi" Wani shegen kallo ya jefa mata yace "Me xa ki ci nace?" Kasa cewa komai tayi, ya kalli waitress din ya umarceta da ta kawo mata exactly abinda ta kawo masa amma takeaway xata yi, waitress din na wucewa ya soma cin abincinsa, lkci lkci Jiddah ke satan kallonsa, cikin rashin sa'a suka hada ido, da sauri ta kauda kanta, shi dai ya ci gaba da cin abincinsa, Waitress din ta kawo abincin ya amsa ya ajiye kan table dinsa, sai da ya gama cin abincin sannan ya mike ya saka sauran drink din da bottle water a ledan abincin dake kan table din, cash ya ba waitress din har xai fara tafiya ganin jiddah bata taso ba yace "In xo in daga ki ne malama" Mikewa tayi xata wuce ya nuna mata ledan yace "ohk bar masu abincin xa ki yi" bata ce komai ba ta dauki ledan ta bi bayansa, suna isa gida da kansa ya dinga kwasan kayan yana kai wa parlor har ya gama, tana tsaye kamar wawuya bakin kofa sai dai ta basa hanya, har ya gama shigar da kayan yayi xamansa a parlor yyi powering Tv, jin bai ce ta shigo ba taki shigowa parlon, bayan kusan minti sha biyar ya mike ya isa bakin kofar yace "Ke wai baki da hankali ne dama ban sani ba? Meyasa kike behaving kamar yar kauye?? Yanxu me kike yi a nan a tsaye" Kamar xata yi kuka tace "Ai baka ce in shigo ba" Ya mata wani shegen kallo yace "Get out my frnd, sai nace ki shigo, idan kina son xaman lafiyar ki a gidan nan ki daina behaving kamar wawuya" Har hawaye ya kawo idonta ta bi ta gefensa ta shiga parlon, bata san dama kayan da ta bar sa da shi yake ta kwasa tana kallonsa ba ya basa haushi, tsaye tayi parlon tana tunanin ta wuce sama ko ta tsaya, ganin kallon da yake mata ta juya da sauri ta nufi sama, yace "Dawo nan" Dawowa tayi yace "Kwashi duk kayan nan ki wuce da su sama dakin ki" Daukan ledojin ta dinga yi daya bayan daya tana kai wa dakin nata har ta gama, ta dau na karshen xata wuce ya dawo da ita ya nuna mata ledan abincin durkusawa tayi ta dauka sannan ta wuce sama yace "Idan kin je saura ki ajiye abincin ki jirani in xo ince ki ci" Bata ce komai ba a sanyaye ta wuce sama ta shiga dakin ta kulle.





Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Do ur self justice by subscribing before reading, Thank you!!

Karfe hudu saura Abuturrab na xaune parlor wayarsa ya fara ring, kallon wayar ya dinga yi ganin Ahmad ne ke kiransa ya ki dagawa har ya katse, bayan few minutes ya ji wayar na ring kuma, dauka yayi xai yi silencing phone din ya ga Aneesah ce ke kiransa, sosai gabansa ya fadi, ya gyara xamansa da sauri yana kallon wayar har ya katse, ya lumshe ido hade da jinginar da kansa da kujera, mikewa yayi daga karshe walking slowly ya wuce sama, bude kofar dakin da Jiddah take yayi, da sauri ta dago kanta daga kan gwiwanta ta jawo ledan abincin, kallon idonta da yayi jajir sbda kuka ya tsaya yi, ta fara bude abincin ba tare da ta yarda ta sake kallonsa ba, she looks sad and scared, karasawa yyi cikin dakin ya xauna kan stool din dake gaban mirror looking at her directly, kasa kunce ledan da abincin ke ciki tayi, cikin cool voice yace "Kukan me kike?" Ta girgixa masa kai kawai wasu hawayen na taruwa idonta ba tare da ta yarda ta kallesa ba still, yace "Tambayarki nake" Nan ma ta girgixa masa kai, shiru yayi yana kallonta, ta bude ledan abinci ta ciro ta fara ci a hankali, ya mike yace "Xan tafi masallaci, kafin in dawo ki tabbatar kin gama cin abincin" Ta gyada masa kai, ya nufi kofa ta bi sa da ido har ya fita dakin... Ko kafin ya dawo ta rufe sauran abincin da ta rage, ba cikin dadin rai ta ci abincin ba, ko rabi bata iya ci ta kai ba, lemon ma bata bude ba tunda ba iya sha tayi ba, ruwa kawai ta sha, tunani ta shiga yi ko ta kai sauran kitchen kar ya dawo kuma yayi mata ihu, a sanyaye ta mike ta dau ledan abincin ta fita, kitchen ta shiga ta fiddo takeaway din abincin ta ajiye gefe daya, sannan ta ciro ruwa da lemon ta ajiye tana kallon ledan hannunta wanda bata san inda xata wurgar ba, window din kitchen din ta dinga kallo sannan ta karasa a hankali ta bude ta jefar da ledan ta kulle windown, bin kitchen din ta dinga yi da kallo, babban ne kitchen din sosai, ga kuma store a ciki, cabinet din yayi kyau ba kadan ba sai dai babu komai a kitchen din sai electric heater da gas cooker, wanda bata ma san meye shi ba, sai fridge da deep freezer, a hankali ta juya xata fita ta gansa tsaye bakin kofar shigowa kitchen din ya rungume hannunsa yana kallonta, komawa baya tayi a tsorace tana kallonsa, ya nuna mata kofa wanda xai yi leading dinka to the back of the house, calmly yace "Bude kofar nan ki fita ledan da kika wurgar ki kwaso su" Da sauri ta nufi kofar tana murda makullin amma ta kasa budewa, karasawa yyi hakan yasa ta koma gefe da sauri, gaba daya a tsorace take, ya bude kofar ta fice, ledojin ta kwaso ta dawo ta tsaya bakin kofa tana kallonsa rike da ledan, ya karasa ya sa ma kofar makulli yace "Daga yau kada ki sake jefar min da komai wajen nan, don ba bola bane, ko kinga yayi maki kama da bola?" Ita dai bata ce komai ba ta sunkuyar da kanta, ya nuna mata wani waste bin a cikin kitchen din yace "Nan xaki dinga ajiye bola from henceforth" A hankali ta karasa shigowa ta saka ledojin a waste bin din, ya juya ya fita yace "Ki sameni sama" Bin bayansa tayi... ganin ya shiga dakin da take ta bi sa xuwa cikin dakin, gefen kofa ta tsaya bayan ta shigo, yana kallon tulin ledojin kayan da ta jera a kasa yace "Ga press can da xaki xuba kayanki" Ta kalli abinda yake nuna mata amma bata ce komai ba, yace "Yanxu xaki fara sa kayan ina gani...." Yana fadin haka ya ja stool ya xauna yana kallonta, ta karasa gun kayan ta bude, rasa ta yanda xata fara jera kayan tayi she look so confuse and Afraid at the same time, ta marairaice tana kallonsa amma bata ce komai ba, hakan yasa ya d'an yi tsaki bai ce mata komai ba ya mike, tun daga kananun kaya, undies, nighties, ya fara arranging dinsu a press din tana tsaye gefe tayi jigum tana kallonsa, har ya gama, ya bude akwatin da suka taho da shi jiya, atamfofin ciki dinkakku wanda baxa su wuce kala biyar ba ya ciro, linkin guga aka yi masu hakan yasa ya ajiye su cikin press din, da hijab biyu da suka rage suma gogaggu, sauran kananun abubuwan ciki duk ya samar masu maxauni cikin press din, gaban mirror yaje duk turarrukan ya jera su da mayukan shafawa da kayan kwalliya, lkci lkci yake kallonta ta madubin gabansa, Jiddah dai ta dinga kallon turarrukan da take ta tunanin su wa da su wa xasu dinga amfani da su haka da yawa, sun yi yawa sosai ba kadan ba, bayan ya tabbatar komai ya samu maxauni ya hade uban ledojin waje daya sannan yana kallonta ya nuna mata turarrukan yace "Kinga turarrukan nan?" Ta gyada masa kai, yace "They are not there for decoration?" D'an rufe idonsa yayi after he realized what he just spoke, sai kuma ya bude idanuwansa ya d'an hade rai yace "Kin gane abinda nace?" Ta girgixa masa kai yace "Ohk, cewa nayi ba don jere na siya maki su ba, watanni kadan na baki duk su kare, idan kuwa basu kare ba xan sa sai kin shanye su, na siya maki ne don ki dinga amfani da su a kai a kai, safe, rana, yamma, dare, bbu takamaiman lkcn saka turare, sannan ba kadan kadan aka ce ki dinga fesawa ba, idan kinga dama xaki iya feshe gaba dayansu a lkcn daya, infact ba ma sai kin ga dama ba, haka nake son ki dinga yi, gaba daya xaki dinga fesawa a lkci daya, wata daya na baki in ga duk sun kare..." kai kawai take gyada masa, ya nuna mata body cream din yace "Wannan xaki dinga shafawa duk kika yi wanka, sannan wanka da safe, rana, dare.... kullum haka xaki dinga yi, ga sabulun nan xan kai maki bandaki, idan kina so ma xaki iya wanka sau goma a rana akwai enough ruwa a gidan" Nan ma ta gyada masa kai, ya hade rai yace "Ba ki gyada min kai kamar lizard ba malama, sau nawa nace xaki dinga wanka daga yanxu?" A hankali tace "Sau uku, idan ina so ma inyi sau goma" Yace "Idan ma baki yi ba ina da camera a gidan ai xan gani...." Xaro ido tayi tana kallonsa, yace "Wanke baki kuma duk kika ci abu ki tafi bayi ki matsa MacLean ki wanke bakin ki, sannan ga na kuskura baki ma, bayan kin wanke bakin shi ma sai ki kuskure baki da shi, duk dare kada ki kuskura ki kwanta baki wanke bakin ki ba, da safe kafin kiyi alwala sai kin fara wanke baki, idan xaki yi wanka ki sake wankewa da safe... haka da rana sannan da yamma, ina son cikin sati biyu maclean dinki ya dinga karewa" Ta gyada masa kai, ya nuna mata mayukan gashi yace "Kullum sai ki shafa wannan a gashin ki, ki gyara..." Cikin sanyin murya tace "Toh" Nail cutter ya dauka gaban mirror din yace "Kinsan meye wannan?" Shiru tayi tana kallo, ya isa gabanta yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi ta fara komawa baya a hankali, tsayawa yayi yana kallonta, lkci daya ya daure fuska yace "Meye haka?" Taki kallonsa gabanta sai faduwa yake, yace "Baxa ki dago kanki ba" Da kyar ta dago kanta amma ta kasa kallon cikin idonsa, ya daura nail cutter din a kan finger dinsa wanda babu farce yace "Shi ake yankewa da, duk ranan juma'ah ki tabbatar kin yanke faratanki, kar ki kuskura ki yarda in ga farce a hannunki, bana son ganin haka..." A hankali ta gyada masa kai, yace "In ga hannunki" a hankali tayi masa stretching dogayen fingers dinta wanda ita ma bbu farce, lkci daya kuma ta sauke kasa, ya dau shaving stick dake cikin leda yana kallonta yace "Kinsan wannan?" Sau daya ta kalli abinda yake nuna mata, ta Smsunkuyar da kanta, yace "Duk Jumma'ah xaki dinga amfani dashi shi ma" ita dai bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, Sabulu ya dauka da Listerine mouthwash ya nufi bathroom, da ido ta bi sa, xai shiga ya juyo ganin bata taho ba yace "In dawo in dauko ki ne??" Da sauri ta bi sa, wajen da xata ajiye towel dinta ya nuna mata, ganin undies dinta da ta wanke a bandakin yace "Xa a sa maki igiya a baya, daga yau kada ki sake shanya a nan ki kai rana, nan ba wajen shanya bane, am i clear?" Ta sunkuyar da kai a hankali tace "Toh" da ido ya bi bandakin ganin it's clean ya juya ya fita ta bi bayansa, ya jingina da bango ya rungume hannunsa yace "Kinsan abinda yasa nake nuna maki duk abubuwan nan?" Ta girgixa masa kai tana kallonsa, yace "Saboda ba lallai wani abun ya sake hadamu a gidan nan ba, ba lallai ki sake samun privilege din tsayawa waje daya tare da ni ina maki bayani ba, ke kadai xaki dinga rayuwarki gidan nan babu wani da xai xo balle ya nuna maki wani abu shi sa nake bata lkci na yanxu, kina da ikon shiga ko ina a gidan nan amma banda bangarena.... sannan idan ina gari ba ke ba fitowa daga dakinki, kwana biyu xuwa uku kawai nake yi a kaduna shi ma sai karshen mako, don haka a wannan lkcn iyakar ki dakin ki, sai kuma probably kitchen, sannan baxan lamunci ki bar min gida da kazanta ba, kullum ki tabbatar kin yi shara kin yi mopping kin goge ko ina, nasan kin ga yanda ake yi a gidan Umma, tunda kin fi sati a can" Ji tayi hawaye ya kawo idonta, ta daga kai tana kallonsa, ya hade rai yace "Kin ji abinda nace?" Gyada masa kai tayi tana kokarin ganin hawayen bai karasa xubowa ba, Ya rungume hannunsa yace "Gobe xan koma wajen aiki, kafin in tafi xan siyo kayan abinci da komai da xa ki bukata a kitchen, don haka duk abinda na gaya maki yanxu baki da wani da xai sake gaya maki a gidan nan, it's better ki tabbatar kin gane komai...." Kallonsa kawai take tana jin wani kuka xai taho mata, ya ki yrda ya hada ido da ita, ya daga kafada kawai ya juya ya nufi kofa ya fita, ta sauke idonta a hankali wani hawaye me xafi ya shiga sakko mata. Abuturrab na dawowa daga masallaci da magrib ya shigo da abinci, sama ya haura ya kwankwasa kofar sannan ya bude, tana xaune saman darduma, ya ajiye mata abincin bakin kofar, ya d'an tsaya wanting to ask what she is even reciting in her prayers, sai kuma kawai ya fasa, ya ta6e baki yayi wucewarsa, karfe tara da rabi ta gama saka kayan da ya nuna mata yace ire irensu xata dinga sa wa da daddare, wando ne dogo da riga, sosai kayan ya mata kyau tana tsaye gaban madubi ta saka daya daga hulunan da ya siyo mata, har makogwaro ta dinga jin turarrukan da ta fesa abin ka da bata saba ba, ta nufi saman gado ta takure waje daya ta kwanta ta lumshe ido... Abuturrab ya fito daga bangarensa rike da lallausan duvet, kana ganin duvet din kasan me tsada ne sosai, kamshin turarruka ne ya gauraye ko ina na upstairs din, ya isa kofar dakin, ya fi second biyar a tsaye kafin ya bude, ko motsi bata yi ba alamar ta fara bacci, ya karasa ciki ya bude duvet din ya rufeta da shi, da sauri ta bude ido, yana kallonta yace "Daga yanxu idan xa ki kwanta ki dinga kashe wuta" Ta gyada masa kai, gun switch din ya nufa ya kashe wutan dakin sannan ya fita ya kulle kofar dakin, Jiddah ta lumshe ido gabanta na faduwa don bata saba kwana ita kadai ba. Washegari Abuturrab ya tabbatar duk wani abinda Jiddah xata bukata a kitchen ya siya, tare da Ramlah suka tafi siyayyen, duk ita ke fada masa abinda xa su siya na foodstuffs, har da filling din gas sun yi, kitchen din ya dawo well stocked up with foodstuffs, few pots, and some kitchen utensils, Jiddah dai na xaune parlon tun bayan dawowarsa da Ramlah, shi ma ya aika Ramlan taje ta kirata ne, yana tsaye kitchen din Ramlah ta jera komai, yana kallonta yace "Ahmad ya koma Abuja ne?" Ta gyada masa kai, ko ranan ma Ahmad ya kirasa amma yaki dagawa kamar dai shi ya aura masa jiddah, Ramlah na gamawa Abuturrab ya bata 2k transport ta fito daga kitchen din tana kallon Jiddah dake ta xaune, da murmushi fuskarta tace "Aunty amarya xan koma" ko lura da kallon da Abuturrab ke mata bata yi ba don jiddah kawai take kallo, Jiddah kam ta ga kallon da yake ma kanwartasa, cikin sanyi tace "To sai anjima" Ramlah ta nufi kofa.... bayan ta fita, Jiddah ta d'an kallesa suka hada ido, daure fuska yayi yace "In rokeki ki taso?" A hankali ta mike ta nufesa, komai na kitchen din ya shiga nuna mata da inda suke ajiye, ya koya mata kunna gas ya tabbatar ta iya kashewa ta iya kunnawa, yana kallonta da kyau yace "Anjima kafin in tafi xaki kunna min in gani" Tace "Toh" fita yyi daga kitchen din ya bar ta tsaye, ta bi sa da ido sannan ta bi bayansa. Abuturrab na komawa bangarensa ya ga calls din Umma har biyu, kiranta ya shiga yi bayan ta daga ya gaisheta, ta amsa tana tambayarsa ya gida, ya amsa mata, tace "Jiya naji ka je kun yi siyayya da Jiddah ko?" Yace "Ehh" Tace "Toh Allah ya saka da alkhairi" Ya amsa da "Ameen" tace "Yanxu meye babu cikin kayan, don xan taho anjima ne, sai in ga ko xa a iya tahowa da su" Ya d'an shafa kansa yace "Kawai Hijabs, bayan shi babu wani abu" Tace "Toh xuwa wani satin sai a dinka mata su" Yace "To Allah ya kai mu" Tace "Shi kenan dai ko?" Yace "Ehh" Tace "Toh sai na iso" Yace "Kamar yaushe xa ki taho Umma?" Tace "Xaku fita ne?" Ya girgixa kai yace "Xan koma aiki ne yau" Da mamaki tace "Xaka koma aiki kuma? ni na xata tunda ansan baka ji dadi ba xaka dau wani satin off?" Yace "Aa ni naji sauki, yau xan koma" Sake baki tayi, can tace "To ita Jiddar fa? Ko tare xa ku tafi?" Ya xaro ido kamar warce ta fado masa wani mugun abu yace "Aa" Tace "To ina xaka barta?" Yace "Nan gidan" Umma tace "Ita kadai?" Yace "Ehh babu komai" ta xaro ido tace "Aa gaskiya ka kawota nan kawai" Abuturrab yace "Aa xata xauna nan Umma" Umma tace "A kan me xaka bar yar mutane ita kadai a wannan gidan, ae baxai yiwu ba Abuturrab" Ya d'an shafa kansa a hankali yace "Umma tace fa xata iya xama, kuma ma xa a kawo mata mai aiki, ni nafi son ta xauna nan din kawai, and ranan laraba da safe xan dawo ai" Umma tace "Yaushe xa a kawo me aikin??" Da sauri yace "Ermm yau, in sha Allah" Umma ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Ni dai na fi gane ka kawota nan gida Abuturrab, ina ga xai fi wllh, it's not advisable to leave her all alone a gidan nan, she is too young for that, beside bata saba xama ita kadai ba" Trying all he xan to convince her yace "Umma xafa ta iya xama wllh, u shouldn't worry pls..." Umma tace "Toh amma is there anything wrong idan ka dawo da ita nan din, idan ka dawo weekend ba sai ka xo ka dauketa ba" Yace "Umma makaranta fa xata fara soon, plss u need not to worry" A hankali Umma tace "Toh shkkn wai dama don in dinga nuna mata wasu abubuwan ne, yasa nayi insisting" Ya girgixa kai yace "Ai bata da wani lkcn Umma, xata fara boko sannan islamiyya" Umma tace "Toh shkkn" ya d'an sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yace "Toh sai kin xo Umma" Tace "Kai xan ba Maimuna sakon kawai ta kawo, next week din xan shigo in sha Allah" Yace "Umma me yasa kika fasa kuma, ko fushi kika yi" Tace "Not at all, let me leave it next week kawai" A hankali yace "Toh shkkn Umma" Sallama tayi masa ta katse wayar tana mamakin irin taurin kan Abuturrab, wanda tasan da Aunty ce tayi masa wannan maganan baxai mata musu ba xai yi yanda tace, girgixa kai kawai tayi don kwata kwata bata ji dadin haka ba,  Abuturrab ya sauke wani ajiyar xuciyar ya ajiye wayar. Bayan la'asar ya gama shirinsa don driving xai yi xuwa kanon, komai da yasan ya kamata jiddah ta sani ko ta iya amfani da shi a gidan sai da ya tabbatar ya nuna mata a gidan nan, abinda ya kara bata masa lkci kenan, xaune yake parlor waiting for Maimuna don baya son sai ya tafi ta xo, tana ring din bell ya mike ya bude kofar, gaishesa tayi da fara'a, ya amsa yace "Ya gida" Tace "Alhmdlh yaya, ina Aunty Amarya" Babu yabo bbu fallasa ya amshi ledan hannunta, sannan ya ciro dubu daya ya mika mata yace "Ki yi transport" tace "Tare da driver muke" Yace "Ohk" dubu daya ya kara xarowa aljihunsa ya hada ya mika mata yace "Ki saka kati" Tana murmushi tace "Aa ka bari nagode yaya" Ya hade rai yace "Amsa ki tafi" Amsa tayi yace "Sai anjima" Tayi masa godiya sannan ta juya a hankali, amma duk jikinta yyi sanyi don bai bari ta ga Jiddah ba, ya kulle kofar, kujera ya koma ya xauna yana duba abinda ta kawo, turarrukan wuta ne a kwalbansu kusan kala hudu sai burner, da wasu turarrukan na jiki, tabe baki yyi ya mike ya wuce sama, dakin jiddah ya bude ya ganta xaune duk ta dawo wani iri, tana ganinsa ta sauke kanta kasa, ya ajiye ledan yace "Umma ta bada a kawo maki" ta bi sa da kallo har ya jona burner din a socket, sannan ya bude turaren wutan guda daya ya diba ya xuba yana kallonta, bayan d'an lkci kamshi ya fara tashi, yace "Safe da yamma xaki tabbatar kin ma dakinki da parlor haka" Ta gyada masa kai kawai, waya karama ya ciro aljihunsa yana kallonta ya mika mata, ta mike ta isa inda yake ta risina ta amsa, yana kallonta yace "Number da xaki dinga samuna ne kadai a ciki, sai ki koyi yanda xaki yi amfani da shi ke kadai" cikin sanyin murya tace "Toh" Yace "Sannan ba ace ki xauna ke daya kiyi wani shiru kamar me xaman makoki ba, ga kayan kallo duk na koya maki yanda xaki kunna" Ta sunkuyar da kanta, kofa ya nufa yace "Na tafi" Ta kallesa da sauri tace "Ina xaka je" Yace "Garin da nake aiki" bude kofar yyi ta bi sa da ido, sai da taga ya fita kafin ya kulle kofar cikin sanyin murya tace "Allah ya tsare" Ya amsa da Ameen a takaice, da sauri tace "Yaushe xaka dawo?" Yana kallonta yace "Wannan bai shafeki ba, ko da wani abu da xaki bukata bayan duk wanda na maki??" Daga haka ya kulle kofar hawayen dake makale idonta ya silalo a hankali, ta fi minti goma tsaye yanda ya bar ta, jin an tada mota ta kalli window da sauri sannan ta karasa window din ta d'an bude labule tana lekan waje, tana ganinsa ya fita da motar, a hankali ta fara kuka ta xauna nan kasa, sai kuma ta fashe da kuka kamar ana dada tunxurata, Abuturrab ya sauka motar yana kallon gate din gidan, he just dont have any option then to close the gate from outside, don bai ma son ya gwada mata yanda ake kullewa daga ciki balle ya sa ta kulle ta ciki, yasan probably kafin ya dawo weekend an samar masa mai gadi kamar yanda yayi requesting ayi, ya kulle gidan ya koma ya shiga motarsa yana karasa addu'o'in da yake yi tun daga compound a ransa ya bar layin.....





Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Do justice to ur self by subscribing before reading

Thank you

Jiddah ce tsaye kitchen  bayan magrib tana ta kallon kayan abincin dake cikin store, yunwa take ji tun daxu amma bata san me xata girka ta ci ba, gashi tsoron gas din take, don yace mata yana kona mutane idan ba a maida hankali wajen amfani da shi ba, a hankali ta bude fridge tana kallon ciki, lemo ne a ciki da ruwan gora, sai apples, grapes, banana da dai wasu fruits din a ciki, a hankali ta rufe ta bude deep freezer, taga naman cow, kayan ciki, kifi, da naman kaza, a hankali ta rufe shima, kwalin indomie da ya riga ya bude mata ta nufa ta dau daya a ciki, ta bi tukwanen dake ajiye da kallo snn ta dau wani karami, da kyar ta iya kunna gas din tana ja da baya don duk a tsorace take, ganin wutan ya dawo kamar na risho da take gani gidan iyah yasa ta daura tukunyar, tun da take idan banda icce da gawayi bata ta6a girki a kan wani abu ba, ba ita ta bar kitchen din ba sai ana isha a masallaci, ta cika ma indomien uban ruwa sai swimming yake a plate din, da kyar dai ta tuttura ta cinye indomien da bai mata dadi ba a baki don ita bata ta6a ci ba ma, tura plate din tayi hawaye ya kawo idonta don kewar tuwon masara take da miyar kuka, cimar da ta saba da kenan iya rayuwarta, don ko shinkafa kwana biyun nan da take ci duk taji ya isheta. Abuturrab na kwance hotel room da ya saba sauka, dawowarsa kenan daga eatry yaje ya ci abinci, vid call suke yi da Aneesah wanda har yanxu bata san abinda ke faruwa ba, bai yi mamakin da har lkcn Aunty bata sanar ma kowa ba, tunda ita bata yarda da auren ba dama from start, Aneesah na kwance saman gado daga ita sai wata yar rigar bacci, komai na jikinta na waje, ganin yanda Abuturrab ke lumshe ido tace "Kar kace min har ka fara jin bacci My captain" Ya bude idon yana kallonta yace "Sure, i will be piloting 8am flight tomorrow in sha Allah" Ta marairaice tace "Wllh ban gaji da jin muryarka ba mine" a hankali yace "Yi hakuri, early to bed early to rise..." Tace "Toh shkkn sweetheart, sleep tight, and dream of me" Ya kashe mata ido sannan ya katse wayar, har ya ajiye ya juya baya hade da lumshe ido sai kuma ya bude idon a hankali ya jawo wayar, dialing number yyi ya sa handsfree yana kallon screen din, Jiddah ta kwanta kenan ta takure waje daya tsoro duk ya cikata, da ta tuna ita kadai ce gidan sai hankalinta yyi mugun tashi, ko wutan dakin ma taki kashewa kamar yanda yyi instructing dinta, sai taji kamar abu na motsi a dakin, ring din wayar dake gaban madubi yasa ta mike a mugun firgice tace "Wayyoo Allah na, nq shiga uku" Sosai jikinta ya dinga rawa tana kallon wayar, sai kuma ta nufi gaban madubin ta dau wayar tana kallo, button din left side din ta danna, tunda iyah na da waya kuma ita ke daga mata ma idan ana kiranta, Shiru Abuturrab yyi yana kallon wayar tasa bayan yaga ta dauka, can jin bata ce komai ba yace "Kin ci abincin ko ba ki ci ba?" Ta sauke idonta kasa a hankali tace "Na ci" Bai ta6a xaton xata yi magana da irin wannan natsuwar a waya ba, can yace "Me kika ci?" Tace "Taliyar indomie" Yace "Ohk.... Sai da safe" Da sauri tace "Ka kai lafiya?" Yace "Eh" kamar xata yi kuka tace "Amma ni tsoro nake ji wllh" yace "Tsoron me?" Ta fashe masa da kuka kamar jira take tace "Ni kadae fa a gidan, gashi sae inyi ta jin motsi" Ya gyara kwanciyarsa, calmly yace "Ehh dodon da na ba ajiyar ki ne ke motsi, ko kar yayi??" Ta wani gwalo ido tana bin dakin da kallo tana sake maimaita abinda yace a ranta, ko ina na jikinta ya dau 6ari a lkcn, cikin rawar murya tace "Dodo fa kace?" Yace "Ehh ko dai ya bari kin gansa ne?" Wani ihu ta kwala da ya sa shi mikewa xaune da sauri, ta rushe da wani kuka tana salati, da sauri yace "Ke wasa fa nake maki" ko sauraronsa bata yi ba ta cika masa kunne da kuka, tsayar da kukan tayi ganin duhu ya gauraye ko ina na dakin, da ta dage ta kara kwala wani ihun sae da Abuturrab ya mike tsaye, cikin bargo ta shige har sannan wayar na hannunta tana rusa kuka, Abuturrab ya dinga cewa "ki tsaya ki saurareni nace maki wasa nake, i am only joking" ko ina na jikinta na rawa cikin tashin hankali tace "Wllh ya kashe wutan gidan, na shiga uku na, don Allah ka xo ka taimake ni, xan iya mutuwa ni kadai" Komawa Abuturrab yyi ya xauna jin tace ba wuta, gaba daya ya mance ya gwada mata yanda xata dinga kunna solar idan an dauke wuta, yayi kasa da murya yace "Ki saurareni nace, ni wasa nake maki, wa yace maki akwai dodo a duniyar nan, ke baki san wasa ba? babu komai fa wuta kawai suka dauke, ko ba a dauke wuta a Hayin ku??" kuka kawai take tana shessheka tace "Don girman Allah ka dawo ka fitar dani a gidan, ni wllh baxan iya kwana ni kadai ba, Allah baxan iya ba" Hade rai yyi sai dai bai ce komai ba, jin yanda take rera kuka da karfi, yyi kasa da murya yace "Kinsan inda nake da kike cewa in dawo ynxu" Taki ce masa komai sai kuka, cikin kwantar da hankali yace "Wllh babu komai kawai zolayarki nake yi, amma tunda kina tsoro shkkn baxan kashe wayar ba har gari ya waye, idan da wani abu sai ki min magana, kina ina yanxu?" Tana shessheka a hankali tace "Ina kan gado" Yace "Toh kwanta" Ta gyada masa kai tace "Na kwanta" Yace "To kulle idonki" Cikin rawar murya tace "A kulle yake ai" Yace "Toh fara bacci" Yana jin yanda take kuka a hankali, ya lumshe ido ya bude, can yace "In kashe wayata ne?" Da sauri ta bude ido ta girgixa masa kai tace "Aa don Allah" Yace "Toh daina kukan nan" a hankali tace "Na daina" Yace "Kiyi baccin ki, ni karatu xan yi..." tayi shiru bata ce komai ba tana sauke ajiyar xuciya, jingina yyi jikin pillow ya fara karantun Al-qur'ani cikin cool and calm voice dinsa, tun jiddah na jin sa har bacci ya dauketa, ya kai ayar karshe a suran da yake karantawa, shiru yyi.... bayan few seconds murya can kasa yace "Jeedderh" jin shiru ya kara tabbatar da tayi bacci, a hankali ya katse wayar ya sauke ajiyar xuciya sannan ya kwanta yana karanto addu'a.... Kiran Sallan asuba ya farkar da Jiddah, ta mike xaune da sauri tana bin dakin da kallo da hasken fitilun ciki ya haska tarrr, kallon wayar dake kusa da ita tayi ta dauka ta danna tana kallon screen din, a hankali ta mayar ta ajiye sannan ta mike, kamar me tsoron tiles din dakin ta sauke kafarta sannan ta mike tsaye, dodon da yace mata ne ya dameta a rai, amma kuma yace wasa yake, cikin sanda ta nufi bandaki ko rufewa bata yi ba tana leko dakin ko xata ga abu me kama da dodo... Karfe tara da yan mintuna Abuturrab na lagos bayan sun sauka kiran Ahmad ya shigo wayarsa, kallon screen din ya dinga yi kafin ya dauka daga karshe, Ahmad yace "What nonsense Aliyu, ni na turaka hayi kayi ma kanka aure da xan dinga kiranka ka ki dauka all this while?" Abuturrab yace "Ka kirani ne ka ci xarafina daga inda ka tsaya?" Ahmad yace "Abinda ya fi xarafi... Ance maka farin ciki nayi da auren nan naka Captain, ae ko a mafarki ban ta6a tunanin xaka riga ni aure ba, which means xaka riga ni fara ajiye iyali, may be next year warhaka duk muna gidanka suna, to kaga kuwa ae ni ba haka na so ba, tunda ni aka fara sa ma rana" rasa abinda xai ce masa Abuturrab yyi sae bin mutanen cikin eatry da yake xaune yake da kallo, har ransa yaji xafin abinda Ahmad ke gaya masa, gashi ya ma rasa amsan da xai basa, Ahmad da tsaf ya san ya kular da abokin nasa, ya dinga dariya kasa kasa kafin yace "Toh ya Amarya me sunan Umminmu, ka dai min bakin cikin xuwa ganinta a gidanka kafin in koma aiki, hope a hankali dai ake cin amarcin??" Abuturrab ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ya cire wayar a kunnensa ya yi tapping button din katse kira sannan ya jefar da wayar kan table din gabansa, ya jingina da kujera xuciyarsa na ci gaba da tafarfasa, haske wayan ya sake yi ganin El-Basheer ke kiransa ya dinga kallon wayar bbu ko kiftawa, har ya katse bai yi attempting din dagawa ba, he knows the news of his marriage has circulate, but what's d essence, auren da babu yanxu.... Mikewa yyi daga bisanni ya dau wayar da ruwan gora ko breakfast din bai cinye ba ya fita eatry din back to airport. Yana Abuja that same day da rana, which in few hours xa su yi piloting xuwa port Harcourt, kasa daurewa yyi ganin da sauran lkci sannan Co-pilots dinsa suna preflight preparations kawai ya fita xuwa hospital din da Ahmad ke aiki, many patients ne xaune reception din hospital din, ya nufi gun wata nurse bayan sun gaisa yace "Dr Ahmad na nan?" Tace "Eh, do u have any appointment with him sir?" Abuturrab yace "Yea ynxu muka yi waya..." Daga haka ya nufi hanyar office dinsa, nurse din ta bi sa da kallo, can tace "But he is attending to a patient" ko juyowa bai yi ba har ya isa kofar office din ya murda, Ahmad na xaune attending to his patient, ya daga kai, ganin Abuturrab ya bude ido, Abuturrab bai ce komai ba ya nemi kujera ya xauna, murmushi kawai Ahmad ke yi har ya sallami patient din ya fita, sannan ya kalli direction din da Abuturrab ke xaune, smiling broadly yace "Latest ango in town" mikewa Abuturrab yyi yana kallonsa yace "In ur life Ahmad.... I mean in ur life don't ever abuse me the way u did earlier today, i felt really bad at that" Ahmad ya masa Wani kallo kafin ya fara dariya irin wanda ke kufular da mutum yace "Toh Alhaji Ibrahim, ae da ka xo da bulala koh?" a fusace Abuturrab yace "You caused me all this mess sannan ka fi kowa yi min dariya?? Who does that Ahmad?" Ahmad ya buda baki hade da xaro ido yace "Ta yaya na janyo maka?" Abuturrab na huci yace "Ohk, i will tell u now, ka xata da baka fara kai ni gun yarinyar nan ba da akwai wani abun da xai hadani da ita balle taimakona ya dawo min sharri?" Ahmad yace "Da na kai ka gun yarinyar sai nace ka xaga ka bi ta baya ka dinga xuwa wajenta ba tare da na sani ba? Ina ce ranan har Umar sai da yace yana ganinka a unguwar Hayi ka mu sa don kada ma in dago komai" Dariya sosai Ahmad yyi har da gyara xama yace "Gaskiya na dade banga me abun dariya irin ka ba Captain, da naje siyan awara sai nace ka dinga xagayawa kana xuwa gun me awara?? just take a look at the distance daga cikin gari xuwa Hayin rigasa amma haka kullum kake jan motar kaje shine xaka xo nan yanxu kayi wani blaming dina, ni da ma aka munafurta ana ta xuwa tadi ta baya ban sani ba, ban ji haushi ba sai kai?" Kallonsa kawai Abuturrab ke ta yi yana jin kamar ya shakosa, Ahmad ya sake wani shegen dariya har da buga table yace "Toh ai dai yanxu ka rigani sanin aure hankalinka ya kwanta, mu ma Allah ya nuna mana namu da wuri wuri haka..." Komawa Abuturrab yayi ya xauna xuciyarsa na mugun tafarfasa, Ahmad sai satan kallonsa yake yana yar dariya, Calmly Abuturrab yace "Dama Aunty na yawan tagging taimako da xama sharri a rayuwar nan, and i have seen that clearly now don ya faru a kaina, assuming i ignore and act as if i didn't see anything da duk hakan bai faru da ni ba, kuma am making this vow today.. ni Aliyu duk inda na ga wani na neman taimako idan ya wuce na kudi, shi ma kudin sai nayi naxari me xurfi a kai, to wllh wllh i will never ever render that help" Ahmad yace "Calm down man, wannan taimakon fa bai xame maka wani sharri ba illa ma lada me yawa da ka kwasan ma kanka idan Allah ya yrda, da ma nine na kwashi wannan ladan wllh, i cant imagine how happy i will be, sannan sharrin dake ciki a naka tunanin ba dai auren yarinyar dake kanka bane??" Abuturrab na kallonsa da kyau yace "Babu wani aurenta a kaina yanxu, ni d'an iska ne da xan bar aurenta a kaina" Da mamaki Ahmad ke kallonsa, can yace "Ban gane ba" Abuturrab yace "U heard and assimilate me right, babu wani aurenta a kaina" Ahmad ya mike yana kallonsa da mamaki yace "Kana nufin ka saketa Aliyu?" Abuturrab yace "Toh me xan jira, ko don dariya da jest making irin naka da mutane ire iren ka ai dole inyi hakan in samar ma kaina kwanciyar hankali" Ahmad ya fito ya xauna gefen Abuturrab on a serious note yace "Stop it plss captain, da gaske ka saketa?" Abuturrab yace "To wai jiran me xan yi, idan ba ina da intention din auren nata bane dama, i have nothing to do with that girl as a wife, gwara kawai in xama guardian dinta, and that's what i am doing right now..." Ahmad ya dafe kansa yace "Ya salam... amma da baka yi haka ba Captain, why will u do that pls???" Abuturrab yace "You are not to tell me what to do and what not to do, so ka ke in cuci kaina in kwari kaina, ina aka ta6a irin wannan taimakon, i just have to saboda kwanciyar hankalina" Kallonsa kawai Ahmad ke yi gaba daya expression dinsa ya nuna ko kadan bai ji dadin sakin jiddah da yace yayi ba, Bayan few seconds yace "Kuma ta sani, i mean ta san ka saketa?" Abuturrab yace "Of course a gabanta nayi na mika mata sannan na amsa na ajiye" Ahmad ya girgixa kai yace "Wllh banji dadin hakan ba Abuturrab" Wani kallo Abuturrab yayi masa sannan ya ja tsaki ya mike ya nufi kofa, Ahmad ya bisa da kallo yace "Amma kuma xamanku a gida daya baxai ta6a yiwuwa ba, ko don hakan ma ni da kaina xan sanar ma su Umma cewar babu aure tsakaninka da Jiddah, I can't pretend over this in cuceta, idan baka san addini ba ni na sani" Dawowa Abuturrab yyi yana kallonsa da kyau, calmly yace "And this will bring the end of our friendship Ahmad, i told you my secret because i trust u, and I'm sure u won't betray my trust, addini kuma da kake cewa ina ga sai dai mu goga a kan saninsa da ni da ke, bbu abinda xaka nuna min... Baka isa kuma ka koya min yanda xanyi da rayuwata ba" Daga haka ya nufi kofa ya fice ya kulle masa kofar. Daren ranan Abuturrab na xaune hotel room dinsa dake kano after isha yana shan shayi a hankali, tunawa yyi daxu da yamma ya kira wayar wajen Jidda bata daga ba, ya sake kira da magrib ma no answer, ya kalli wayarsa dake gefensa ya dauka ya sake dialing number, har ya katse no answer, haka nan kawai yaji his mind has lost rest, kallon wayar ya dinga yi, can ya sake kira nan ma har ya katse no answer, kallon agogon jikin wayar yyi yaga takwas ya wuce, sake dialing yyi nan ma har ya katse no answer, ajiye cup din hannunsa yyi, ya shiga kiran wani pilot hoping to reach him don yasan he might be up in the sky now, jin captain Musa ya daga, ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yace "Captain baku tashi har yanxu ba?" Captain din yace "About to... in few minutes time, ya gajiya?" Abuturrab yace "I think i will have to follow you to kaduna now" Da mamaki pilot din yace "Baxa kayi piloting jirgi gobe da safe ba, and hope all is well?" Abuturrab yace "Sure alhmdlh, jirgin gobe na sha daya ne, i don't have early morning duty" Musa yace "Toh shkkn, ka taho yanxun nan kasan basu fiye son jira ba, in some minute time xamu yi take off" Abuturrab yace "In sha Allah" Cikin few minutes ya shirya cikin kananun kaya Hoping not to miss the private flight going to kaduna, cikin ikon Allah ya isa, kuma suka daga sama, within some minutes suka sauka a garin kaduna, a motar Musa dake airport din kaduna suka shigo cikin gari, Musa ya kawo Abuturrab har layinsa ya sauka yana masa godiya, Musa yace "Sai mun hadu Wednesday in sha Allah" Abuturrab yace "Sure in sha Allah, thank you" daga haka suka yi sallama ya karasa cikin layin da kafa, makullin gidan ya fiddo a aljihunsa ya bude sannan ya shiga, har ya isa main entrance nan ma ya bude sannan ya shiga parlor, wutan parlon a kunne yake parlon sai kamshin turaren wuta yake, ko ina na nan ynda ya barsa jiya, kuma babu alamar ana xama cikin parlon ma, karasawa yyi sama yana kallon kofar dakinta ya murda a hankali ya shiga, babu kowa cikin dakin ya bude ido sosai sai dai lkci daya yayi calming kansa jin kamshin sabulu a dakin, coz he is a very sharp percipient, bin dakin ya dinga yi da kallo yana duba inda xai ga wayar amma bai ga alamarsa ba, can kusa da window ya nufa ya tsaya hade da rungume hannunsa ya daure fuska, bayan few seconds ta bude kofar bandakin, ta fito daure da towel, bata ko kalli direction din da yake ba ta nufi gaban mirror, sai a sannan ta ga mutum ta madubi wani ihu ta fasa da karfi ta nufi bandakin a guje ruwan kafarta ya sa tsantsin tiles ya kwasheta ta fadi nan bakin kofar bandakin, da sauri Abuturrab ya nufeta ya durkusa kusa da ita ya dagota yace "Ke nine fahh" wani kuka ta fashe da bayan ta kare masa kallo ta tabbatar shi din ne, tana rike da towel din jikinta gam tace "Wayyo kafata, wllh kila nayi targade, wayyo Baabarmu" Komawa baya yyi yana kallon kafar,  ya mike yace "Tashi tsaye" Tana girgixa kai hawaye na sauka idonta tace "Ni baxan iya ba wllh" Ya kamata ya dagata, lkci daya ya hade rai yace "Wani kafar ne kika yi targade" Ta nuna masa right leg dinta, gefen gado ya xaunar da ita ya duka yana kallon kafar, ita dai hawaye kawai take tana hade laps dinta tana kallonsa, wani kallo ya mata ta sunkuyar da kai da sauri, mikewa yayi ya nufi gaban madubi don yasan ya siya mata man xafi ranan da suka yi shopping incase she will need it, a hankali tace "Don Allah ka yi hakuri ka miko min hijabi na" Ya dau man ya juyo ya dawo kamar bai ji ta ba, ta marairaice tace "Hijabina nace" Yace "Ki bari in duba maki kafar in ga babu targade, yau duk kukan karyar nan da kike ma mutane sai ya dawo na gaskiya, kuma xaki gaya min inda kika jefar da wayar da na baki" Shiru tayi bata ce komai ba, ya duka ya bude man ya diba sannan ya kama kafar da tace, wani ihu tayi ya ja kafar da karfi, har kasa sai da ta sauko tana kokarin kwace kafarta sbda axaban da take ji, ganin da gaske ta ji ciwon yasa yace "A hankali fa nake maki amma wllh idan kika sake ta6a ni xan yi da karfi" hawaye na sauka idonta tace "Wllh xafi yake min sosai, don Allah ka rufa min asiri kayi hakuri" Ya daure fuska ganin xata sake kai hannunta kan nasa yace "Kin xata wasa nake maki" Da sauri ta dauke hannun, duk da yanda yake mata a hankali haka ta dinga kuka tana neman birgima a wajen, shi dai kallonta kawai yake, don a fuska bata yi kama da warce xata yi shagwaba ba, ko warce baxata iya jure xafi ba ko yaya ne, dauke idonsa yyi ganin tawul din na neman sauka a kirjinta, ya sake mata kafar ya mike, sai a snn ta ankare, tana shessheka ta kankame abarta, ya ajiye man xafin hannunsa ya nufi kofa ya fita.



*Pls i am bringing this to the notice of people coming to disturb me with... ina karanta littafin ki kuma bani da kudin biya ki yafe min!!! For what?? Na aikeki karanta littafi baki da kudi? Ga dai free books kaca kaca a gari, Toh a gaskiya baxan iya lalacewa da gantalewa ba kije can ki nemi wanda xaki ce ya yafe maki ba dai khaleesat Haiydar ba, ba ruwanaa tunda ban aike ki karanta littafi ba, ki sani you owe me har sai ranan da kika mula kika mulmule kika ga daman biya*🤷


Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you


Kamar wanda ya tuna abu ya sake juyowa, rarrafawa yaga tayi xuwa gun da hijab dinta yake xata dauka, ya hade rai sosai yace "Ina wayar da na baki?" Ta juya ta kalli gadon dakin, a hankali tace "Ya fada karkashin gadon na kasa daukowa" Da mamaki ya dinga kallonta, ta sunkuyar da kanta, can yace "Wa ya jefar karkashin gadon?" Ta sake kallonsa tace "Xamewa yayi ya shige ban sani ba" cikin tsawa yace "Saboda ke yar yarinya ce ko?" Shiru tayi bata ce komai ba ya juya ya fice daga dakin ya kulle kofar, da kyar ta lallaba tayi shafe shafen mayukanta da turarruka sannan ta dauki wani rigar bacci ta saka tana dingishi ta hau saman gado ta kwanta, mamaki ta dinga yi na yaushe ya shigo gidan bata ji karan shigowar mota ba, ko dai bai dawo da motar bane, kuma ai ce mata yyi sae karshen sati, da wannan tunane tunanen bacci yyi awon gaba da ita. kasa bacci Abuturrab yyi sbda shayi da bai sha ba, don ya fara shan shayin kenan ya bari ya taho, shi kuma idan da abinda ke takurasa rashin shan shayin dare, ji yake yunwa na damunsa indai bai sha shayi ba, and he detest making tea himself, da dai yayi da kansa gwara kar ya sha, rub da ciki yyi ya lumshe ido hoping to force sleep, wajen karfe daya da rabi ya mike ya fito daga bangarensa, downstairs ya sauka ya shiga kitchen ya bude fridge, kallon fridge din ya dinga yi don bai ga alamar ta ta6a komai na ciki ba tun jiya, ya dau Chivita daya ya bude ya dau glass cup bayan ya dauraye ya xuba a ciki, sau biyu ya cika ya shanye sannan ya mayar fridge, da ya hada shayi gwara yyi hakan, fitowa yyi daga kitchen din ya xauna saman kujera a parlon cikin duhu, yana ta xaune har karfe biyu sannan ya mike ya haura sama, har ya nufi part dinsa ya dawo ya bude kofar dakinta, cikin duvet ya ganta ta takure waje daya tana bacci, ya karasa cikin dakin ya janye duvet din, dukawa yyi yana kallon kafarta sannan ya d'an danna kafar, da sauri ta janye ta juya masa baya, sake kai hannu yayi ya kamo kafar, da sauri ta bude ido, ya hade rai amma bai ce komai ba ya mike ya sake dauko man xafin, a hankali ya shafa mata sannan ya mike ya kashe wutan dakin ya fita. Da asuba bayan ya dawo masallaci ya fara tunanin ta yanda xai koma kano babu mota, gashi bai fiye son shiga commercial vehicles ba, karfe bakwai ya gama shiri ya fito daga bangarensa, dakinta ya murda a hankali ya shiga, a kwance ya ganta amma idonta biyu, ganinsa ta mike xaune da sauri... yace "Kafin in dawo ran juma'ah ki tabbatar kin fito da wayata da kika jefar karkashin gado" shiru tayi bata ce komai ba, yace "Sannan kayan marmarin da na xuba a fridge ki tabbatar kar in dawo in sami ko daya" Daga haka ya juya, da sauri tace "Tafiya xaka yi?" Yace "Aa xama xan yi" sai bayan da ya fita ya fara tunanin wayar da xai sake bata, he just need to hand a phone over to her, shi kuma bashi da strength din daga kayan gado da sassafen nan, can dai yyi deciding ya koma dakin ya ga inda ta jefar da wayar tukun, Yana shiga bai ko kalleta ba ya nufi gadon ya fiddo wayarsa ya kunna fitila ya duka yana haskawa karkashin gadon, cikin few minutes ya ciro wayar da hannunsa, ita dai tana tsaye ta rakube gefe da hijab dinta har kasa, ya dago yana kallonta fuskarsa a tamke, ta sunkuyar da kanta, ajiyewa yyi kan gado ya nufi kofa ya fita ta bi sa da kallo, dole commercial car din ya tafi ya hau a park xuwa kano... Jiddah na xaune kasan carpet a parlon hannunta rike da apple biyu, ta kasa ci sbda rashin sabo da shi, tunda take a rayuwarta bata ta6a shiga matsatsi da takura irin wannan ba, duk da ba jin dadin xama take da Hansai ba amma ai xaman bakin titi ma da take ya kan debe mata kewa tana ganin mutane da motoci, amma tun shigowarsu gidan nan yau kwananta nawa bata ga kowa ba banda shi kadai, tunanin hakan ya sa hawaye ya kawo idonta, kallon ma sbda rashin sabo da shi da ta fara xata soma gyangyadi, Mikewa tayi a sanyaye tana goge idonta ta nufi wani window dake parlon ta makale jiki ta bude labulen a hankali tana lekan tsakar gidan, babba ne tsakar gidan da flowers masu kyau xagaye, ta dade tsaye wajen tana ta kallon tsuntsayen dake tashi da sauka a tsakar gidan, kiran sallan azahar yasa ta juya a hankali ta bar wajen tana kallon apples din hannunta kitchen ta koma ta mayar, marairaice fuska tayi tana kallon fruits din fridge din banda ayaba babu abinda ta iya ci a ciki ita dai, tana tafiya a hankali ta fita kitchen din. Hansai ce xaune gaban mai anguwa da Zulai da ta rakota, bayan sun gaisa, ta kunce ha6ar xaninta ta sakar masa kuka tana matsar kwalla da zanin tace "Wllh Mai Anguwa shiru shiru har yau babu yarinyar nan tawa babu labarinta fa, abun nan ya fara damuna duk inda taje ai ya ci ace ta dawo yanxu, yau fa sati daya cur ba ita ba labarinta, na rasa inda xan sa kaina, ga komai nawa ya tsaya kamar ta tafi da shi" Sae kuma ta rushe da kuka,  Mai Anguwa dake ta kallonta da mamaki yace "Ikon Allah, ni ai na xata da naji shiru Allah ya sa ta dawo gida, toh ke duk kwanakin nan me yasa kika yi shiru kinsan bata dawo gida ba, sai yanxu xaki taho kice bata dawo ba" Hansai ta marairaice cikin rawan murya tace "Wallahi na danni xuciyata ce don ban debe tsammani ba, ina ta baxa ido amma naga shirun yayi yawa" Mai Anguwa yace "Cabb, amma kina da ganganci Hansatu, anya ke kika haifi yar nan kuwa kamar yanda kika ce?" Hansai ta kara marairaice masa cikin kuka tace "Nice mana Mai Anguwa, ina da kauda kai dai xaka ce kawai" Mai Anguwa yace "Toh, ranan dai na amshi lambar shi mutumin da ya aureta, wato shi matukin jirgin saman, kuma bayan wannan aure da kwana uku ya xo min har nan da mahaifinsa da kawunsa, mahaifin nasa sanannen mutum ne dattako kuwa a garin nan..." Hansai ta hadiye abu da kyar tace "Toh kira mana shi xaka yi yanxu kenan don Allah? Don dai gaskiya na fara xargin kilan ma ya ganta ya tafi da ita ne kawai bamu sani ba, banda haka me yasa xai yi shiru haka babu labarinsa, bayan gashi kace har ya xo da mahaifinsa, to idan haka ne ba sai sanda na ga damar basa matar xai tafi da ita ba, to wllh ni na canxa ra'ayi kan auren ma, ya dawo ya fadi nawa ya kashe ko gidan da muke ciki ne sai in sayar in biyasa, ba ruwana wllh" Mai Anguwa dake ta kallonta, ya d'an yi murmushi yana kara jinjina hali irin nata, ya fiddo wayarsa bayan kusan minti biyar yace "Alhmdlh, na samo lambar" Yana fadin haka yayi dialing number Abuturrab ya sa handsfree, kallon Hansai yayi bayan an sanar wayar baxai je ba, Hansai ta rushe da wani matsanancin kuka tace "To ko dai lambar karya ya baka, ni sai yanxa nake jin ma ban yarda da mutumin nan ba wllh, wa ya sani ma ko d'an yankan kai ne yace mana matukin jirgi ne shi, jirgi abar wasa ce da xai iya tukata bayan an sanar mana turawa ne kadai suka iya daga jirgi sama su tuka, sannan idan ba d'an yankan kai ba mutumi babu dangin iya balle na baba kayi ta kashe mana kudi haka daga jin an mana mutuwa, daga haduwar mu xuwa fa ranan da ya bada sadakinta wllh mutumin nan ya kashe mana yayi kusan rabin miliyan, to akan me? Aa wllh ya xo in biyasa ya maido min da 'ya ta" Mai Anguwa dai tabe baki kawai yake bai bata amsa ba, Hansai ta fara kokarin mikewa tace "Ai dai wayar baxata dauwama a mace ba, don haka ko gobe ma xan dawo sai ka sake gwada kiran lambar don ni bani da waya, haka kawai yarinya ta bace batt kamar yar kaza" Mai Anguwa yace "Allah ya kai mu goben" daga haka ta bar wajen tare da kawarta, Zulai tace "Anya wannan mai anguwan na da gaskiya kuwa Hansai?" Hansai ta kalleta da sauri tace "Atoh, nima shi na gani, baki ji har ya fara cewa Uban yaron sananne ne a garin nan ba, kawai dai sun danna masa uban kudi shi ma shine yayi mukus, to wllh a maido min da 'ya ta babu wani xancen auren karya" Zulai tace "Kuma fa da gaskiyan ki, ko dai wannan yaron d'an yankan kai ne, idan ba haka ba a wnn xamanin ina xai samo rabin miliyan ya kashe maku" Hansai ta tsaya tana kallon Zulai, can ta marairaice tace "Toh kuwa in har haka ne ya kassara ni, wa gareni da muke sana'a tare banda jiddar, ke baki ga ko me nasa Bibalo kin yi take ba sai ta nemi ta xageni, ai jiddah ita ce rufin asiri na a duniyar nan, gashi duk jarin na fatattakar, kuma sana'ar ba wani ciniki nake yi ba yanxu, uwa dai an juya min baya a anguwan" tana fadin haka ta fara matsar kwalla, Zulai tace "Toh da da kike shirin aurar da ita Jiddar ga Iliya fa?" Hansai ta ci gaba da tafiya tace "Toh ai ko daga gidan mijin sana'ar xan dinga bata tana min nufi na" Zulai ta ta6e baki tace "In ko ba d'an yankan kai bane to tana gunsa Wlh, abinda kowa dai ya shaida matarsa ce" Hansai ta share xufar goshinta tace "Toh uban me xai yi da ita wai Zulai, sai kiyi ta wani cewa matarsa, wllh babban mutum ne ko da kudi aka hadasa da jiddah banjin xai amsa balle bbu ko sisi, don baki gansa bane shi yasa kike wannan xancen banxan, lafiyayyen namiji ne fa wanda da kyar ya amince ya auri yar kaduna sai dai yar Abuja" Zulai tace "Toh wai ke kinga tun bayan da aka daura masa aure da ita ya sake dawo maki kofar gida, ai da wllh bata wajensa da tuni ya dawo an kai xance gidan yan sanda, duk inda ta shiga kuma sai an nemota, ke dai kawai kin cuci kanki, kina ji kina gani sbda shegen son kudi kin ba babban mutum irinsa auren Jiddah ga Bibalo yashe a gida" Hansai ta fashe da kukan takaici tace "Ni anjima da daddare ma wllh xan dawo gun mai anguwa ya sake kiran lambar, don bani da waya ne da na amsa lambar ai, kuma wllh in har da gaske jiddah na wajensa to ni ba da amincewata ya aure min 'ya ba, wllh sai ya sakar min ita, ina jiddah ina babban mutum kamar shi idan ba yana da wata manufa na yanka min ita ya bunkasa arxikinsa a ransa ba" Zulai ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Ohh!!! wa yasan irin daulan da Jiddah ke ciki yanxu" Turata Hansai tayi a mugun fusace tace "Don Allah idan baxa ki dinga fadan alkhairi ba kiyi shiru, jiddah ita har tana da wani daula a duniya, wllh ko tana da shi kinji rantsuwar musulmi ko? To sai na rushe daulan nan, muna nan da ke kuma xa ki ga jiddah sai ta dawo gidan nan, ai ba mijin aurenta bane shi din sai in kasheta yake da niyyar yi ya kara arxikinsa, ba kuma sa'an aurenta bane ko da kuwa ita ma yar me kudi ce, sai dai in ban haifu cikin shafa ba wllh" Daga haka tayi gaba a mugun fusace tana jin xuciyarta na tafarfasa.... Washegari alhamis Jiddah ta tashi taji tana jin yunwa sosai sbda daren jiyan babu abinda ta ci ta kwanta, sai kusan karfe takwas na safe ta shiga kitchen bayan tayi wanka, rasa abinda xata dafa tayi a kitchen din, jingina tayi da bango ta 6ata fuska xata yi kuka tana kallon tulin kayan abincin, tuwo ne kawai a ranta, lkci daya hawayen ya kawo idonta ta juya ta fice daga kitchen din, dakinta ta koma ta fada kan gado tana shessheka a hankali, bayan wani d'an lkci ta daga kai a hankali tana kallon wayar dake gaban madubi yana vibrate, mikewa tayi tana share idonta cikin sanyin jiki ta nufi wayar ta dauka tana kallon screen din, throughout jiya basu yi magana da Abuturrab ba banda yanxu da yake kira, ta daga ta kai kunne, Abuturrab na driving xuwa airport kasancewar karfe sha daya yake da duty, Shiru Jiddah tayi kamar yanda shi ma yayi shirun, bayan few seconds yace "Ni kike jira inyi maki magana?" Ta sauke idonta kasa a hankali tace "Aa" yace "Ohk in gaishe ki?" Tace "Ina kwana" Yace "Me kika ci yanxu?" Ji tayi kamar ta fashe masa da kuka, yace "Ina jin ki" cikin rawar murya tace "Ban ci komai ba" Yace "Me kike jira?" Tace "Ni bana son taliyar" ya d'an yi shiru kafin yace "Me kike so?" A hankali tace "Tuwo nake son ci" Yace "Toh sai ki ci inda kika gansa, ga abinci kusan kala nawa a gida kice duk baki ga abinda kike so a ciki ba, Shinkafa, doya, macaroni, spaghetti, irish, wake, indomie, cous cous.... Wait.. Are you even okay?? Dama tuwo abinci ne?" Ita dai bata ce komai ba, lkci daya hawaye ya kawo idonta, yace "Samun waje kika yi" daga haka ya katse wayar, hawayen dake makale idonta ya silalo, ta ajiye wayar ta koma kan gado ta kwanta tayi lamo tana shessheka. Har kusan karfe sha daya na safe tana kwance, jin yunwa ya dameta sosai ta mike a hankali ta fita dakin, kitchen din ta koma, indomien kawai ta dafa daga karshe sai dai gwara na yanxu a kan wanda tayi shekaranjiya. Da yamma Jiddah ta ji kamar an bude gate ta mike da sauri ta isa window ta bude labulen tana lekan waje, shi ta gani ya shigo gidan ta xaro ido ta sake labulen ta koma can karshen gado ta xauna kamar mara gaskiya, bayan kusan minti goma sha biyar ya bude kofar dakin nata, sunkuyar da kai tayi, yana tsaye bakin kofar yace "Baki iya dafa shinkafa bane ko wani abincin?" Tace "Aa na iya" Yace "Toh me yasa baki dafawa?" Tayi shiru, yace "Ohk, daga yanxu... daga ranan lahadi xuwa asabar xan sanar maki abinda xaki dinga girkawa tunda baki da hankali ke" Ajiye ledan hannunsa yayi ya juya ya fita, ba a dau lkci ba taji alamar ya fita gidan gaba daya, mikewa tayi ta isa gaban ledan da ya ajiye ta leka ciki taga take away ne, fiddowa tayi ta bude taga tuwon shinkafa that looks so  palatable, ta bude inda miyan ke ciki taga miyar kubewa danye lafiyayye da ya ji nama da kayan ciki da ganda, kallon miyan da tuwon ta dinga yi, bata san lkcn da tayi murmushi ba ta mike ta wuce bandaki da sauri ta wanke hannu sannan ta dawo ta xauna ta fara cin tuwon, she was eating happily, mulmula hudu ne tuwon, ta rage wanda xata ci da daddare, har bacci barawo ya saceta sbda tsoron dake damunta a rai bata ji alamar ya dawo gidan ba. Washegari Friday ana saukowa masallaci Abuturrab ya shigo gida daga garin kano, babu kowa parlon, yana tafiya a hankali ya nufi bangaren Aunty, da sallama ya shiga parlonta, daga uwar daka ta fito ya xauna saman kujera murya can kasa yace "Ina yini Aunty" tana kallonsa daga sama har kasa tace "Kiran nawa bashi da amfani a gareka sbda kasan abinda ka kullala shi yasa ka daina dauka ko??" Ya shafa kansa cikin sanyin murya yace "Aunty ae na maki text nace xan dawo weekend in sha Allah" ta nemi waje ta xauna fuska daure bbu yabo bbu fallasa tace "Toh gashi ka dawo weekend din yau ai, ya ake ciki kenan?" Ya daga kai ya kalleta a hankali yace "Aunty ni fa ba matata ce ita yanxu ba kuma, kawai gaya maku ne ban yi ba" Da mamaki Aunty tace "Ban gane ba" Ya gyada kai yace "Haka ne, babu aure tsakanina da ita tun ranan da muka tafi can gidan nawa, so nake sai na dawo ne in sanar maku" Aunty ta daga hannu biyu sama tace "To Alhamdulillah ya Allah, tun faruwan lamarin nan sae ynxu naji dama dama" cikin sanyin murya yace "Amma don Allah wannan ya xama sirri tsakaninmu Aunty, Abba won't take it likely with me if he finds out" Aunty ta hade rai tace "Haba dai wa xan gaya ma kamar wata yar yarinya, wllh baka ji sanyin da xuciyata tayi ba yanxu, to ina ka bar ta yanxu? Ka maida ta kauyen nasu ne?" Yace "Tana can gidana Aunty" Aunty ta hade girar sama da ta kasa tace "Wani gidan naka?" Yayi kasa da murya yace "Aunty ina sane da abinda nake wllh, ba lkci daya xan yi komai ba ai sbda kada a xargeni" Aunty tace "Amma xamanta gidan nan naka ai bai yi ba" yace "Na sani Aunty, give me few days to think of another solution" yana fadin haka ya mike yace "I will be coming back" daga haka ya fita, ta sauke wani ajiyar xuciya tana jin kamar an biya mata wani bukatarta na musamman. Part din Ummi ya nufa, ya xauna ya gaisheta da ladabi, ta amsa tana kallonsa tace "Ya ku ke?" Yace "Alhmdlh" Tace "Toh madallah" kallon Tv dake aiki a parlonta kawai yake, can ya kalleta yace "Abba xai dawo yau ne?" Ta girgixa masa kai tace "Sai gobe in sha Allah" Yace "Allah ya kai mu lfya" Ta amsa da "Ameen... Ina Amaryar taka take?" Lkci daya ya d'an 6ata rai, ita dai tunda ta fada haka bata kalli fuskarsa ba, ya dago yace "Ni daga wajen aiki nake yau" Da sauri ta kallesa tace "Wajen aiki kuma, dama ka koma ne?" Yace "Tun lahadi" Tace "Toh ita sai ka bar ta a ina, ko tare da ita ka koma" Yace "Aa, gida take" Ummi tace "Ita kadai?" Ya gyada kai, Ummi tace "Toh kada ka sake barin ta gida ita kadai, idan baxa ka tafi da ita ba ka kawo ta nan" Yace "Toh" Shiru ne ya biyo baya, bayan few minutes ya mike yace "Sai na shigo da yamma Ummi, xan je gaida Umma" Ummi tace "Toh Allah ya kai mu, a gaishe su" Yace "In sha Allah" Daga haka ya nufi kofa, ta bi sa da kallo har ya fita, motarsa ya shiga ya bar gidan xuwa gidansu Ahmad. Sama sama ya amsa gaisuwar Maman Abdallah dake tsakar gida yayi shigewarsa cikin gidan, Maimuna dake parlor tace "Sannu da xuwa yaya" Yace "Yauwa, Umma fa?" Tace "Umma ta fita wllh" Ya d'an yi jim kafin yace "Okay idan ta dawo kice na shigo" Tace "Toh amma yaya Ahmad na ciki ai" Kallon hanyar dakin Ahmad yyi can ya karasa ya shiga dakin, Ahmad na operating laptop ya daga kai ganin Abuturrab yace "Yanxu nake shirin kiranka ashe kana hanya" Abuturrab ya xauna yace "Ban jima da shigowa garin ba" Mikewa Ahmad yyi ya kashe laptop din yace "Dama gidanka nake son xuwa akwai maganan da xa mu yi a can" Wani kallo Abuturrab yyi masa yace "Kaje kayi me a gidana?" Ahmad yace "Kai me ka xo yi nan? ka sameni parlor plss ina jiranka, kasan fa na san hanyar gidan ba wai ban san hanyar ba" Daga haka ya dau makullin motarsa ya fita, Abuturrab ya d'an yi jim, har ransa bai son Ahmad yaje gidan nasa, can dai ya mike ya bi bayansa. Duk fararen shadda ne jikinsu su biyun, babu yanda Abuturrab ya iya da Ahmad dole haka suka bar gidan tare a motarsa, Driving kawai Abuturrab ke yi ba tare da yana ba ma Ahmad amsa ba, Ahmad yayi wani dariya yace "Kai dai yarinya ba matarka ba balle kace kana kishin wani ya ganta, ni ina ga i just have to sacrifice and marry her together with Ramlah since ba Haram bane kuma i have the money to do so, and i will mould her to exactly how i wish and want her to be, har yanxu her brain is fresh, kaga daukan abubuwa baxai yi mata wahala ba, idan kuma su Umma basu amince min ba which i am not praying for that, i have a frnd da muka yi karatu tare da shi a Uk, har yanxu ma yana can, and ya dameni yana son in hada sa da yarinyar da na sani mai hankali ko cikin siblings or cousins dina ya aura, to yanxu ina ga i will hook him up with Jiddah, yanda na lura yanda Yusuf baya son hayaniya ita ma haka, and they will make a perfect couple, balle ma nasan su Abba baxa su hanani aurenta ba ni...." Parking Abuturrab yayi yana kallon Ahmad fuska daure yace "Ni yanxu fa ba gida xan je ba Ahmad, xan fara xuwa can gida in gaida su Aunty da Ummi, sannan xan amshi sako from a frnd coming from Abuja at bypass, don haka ya xa mu yi da kai???" Ahmad ya gyara xama yace "Ohk then, tunda ban fito da mota ba bari in samu adaidaita kawai ya karasar da ni gidan naka, and i will wait for u there...." Abuturrab ya katse sa yace "Wani gidan??" Ahmad yace "Gidanka mana, idan ya so idan ka gama uxururrukan ka sai ka dawo ka sameni, i will go gist with jiddah kafin ka dawo...." Wani irin kallo Abuturrab ke yi masa xuciyarsa na tafarfasa, Ahmad ya fara kokarin bude motar yace "Sai ka karaso, but don't take too long" Bluntly Abuturrab yace "Toh wai dole ne sai kaje gidan nan nawa, meye hadinka da ita yarinyar??" Ahmad yace "Hadina da ita shine ta dalilina ka fara saninta don da ba don ni ba baxa ka santa ba, sannan a lkcn da muke xuwa siyan awara a wajenta ni kadai nake ganinta kai kuwa murhu kake gani, amma dai duk ba wannan ba ma, wai ba inace yarinyar nan ba matarka bace ba yanxu kuma balle kace ko kishin xanje in ga matarka kake, pls what's the color of ur problem Captain?" Abuturrab yace "Don ba matata bace sai nace maka gidana ya koma cinema na xuwa ganinta? I have all right to protect her by all possible means, sannan da kake min gorin ba matata bace mintina nawa ne na mayar da auren idan na so yin hakan? Infact idan ma na mayar din sani xaka yi ko ance maka sanar maka xanyi?" Ahmad ya kallesa da sauri yace "Don Allah in kai ka cika namiji ka mayar da auren yanxu ma" Abuturrab ya ja tsaki yace "Toh sai ka saka ni in mayar ai" Ahmad yace "Ahaf ai nasan baxa ka yin bane, plss bude min mota my frnd, idan ka gama yawo a garin ka dawo gidan ka sameni tare da jiddah" Tsaki Abuturrab yyi ya ja motar suka ci gaba da tafiya, Ahmad yayi wani dariya yana gyara xama yace "Ka fasa karban sakon kenan" Abuturrab bai tanka sa ba har suka isa gida, ya sauka motar ya bude gate sannan ya dawo ya shigar da motar, Ahmad na kallonsa yace "It's very risky leaving this little girl all by her self in this house captain, why don't you want to leave her with umma or Ummi, kasan fa baxa su ki riketa ba" Abuturrab yace "A nan din nake son ta xauna ba sai taje wani waje ba" Yana fadin haka ya sauka motar ya tafi ya kulle gate din Ahmad ya sauka motar ya nufi entrance din shiga gidan, Abuturrab ya bi bayansa da sauri, amma tunawa da yyi kofar ma a rufe yake dole sai ya bude yasa yayi slowing pace dinsa, tsaye Ahmad yyi yana jiransa a balcony jin kofar a rufe, Abuturrab ya isa wajen ya sa makulli ya bude kofar parlon ya shiga sannan Ahmad ya bi bayansa....





Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you





_Albishirin ku jama’a ko kusan akwai wani company da ya shahara wajen siyar da kayan alatu da abubuwan more rayuwa??_


_Wato Unique & Luxury Stores yana da bangararori daban-daban kamar haka_

 *@unique_home_store_ng wanda ya shahara wajen siyar da kayan ado da qawata gida, kayan kitchen, furniture, carpet na gani na fada da sauran su*


Sannan akwai @elegant_projects_ng

Bangaren tsara gida kamar home styling na amare da uwar gida, interior designing da finishing....

Company bai tsaya a sashe 2 kawai ba yana da bangaren ado da kwaliya wato

@uniquefashion_ng. Duk bai tsaya anan ba ya kara zuwa maku da @unique_souq_ng inda zaku samu kayan kwadayi, makulashe da kayan da zasu kara inganta maku lafiyar jiki.

Karku bari ayi babu ku domin gane ma idon ku, ku garzaya shafukan su a Instagram kamar haka....


@unique_home_store_ng

@uniquefashion_ng

@unique_souq_ng

@elegant_projects_ng

Sannan zaku iya samun su ta WhatsApp a +2349071721586

Babu kowa babban parlon, Ahmad ya xauna saman kujera yana bin parlon da kallo snn ya kalli Abuturrab yace "It looks very good.. " Kitchen Abuturrab ya nufa ya bude fridge ya dau ruwa, fruits din da ya bar mata na cikin fridge har sannan, ya juya ya fita ya dawo parlor ya xauna yana bude ruwan hannunsa, Ahmad yace "Mu yi magana ta fahimta Captain..." Abuturrab ya kallesa bayan ya sha ruwan hannunsa, Ahmad yace "Tell me ur plan on this innocent girl" Abuturrab yace "I have no plan then to make her somebody useful in life, daga nan kuma sai tayi aurenta idan ta samu miji...." Ahmad ya masa wani kallo yace "How Captain? By locking her up for days ita kadai a gida?" Abuturrab yace "I wanted enrolling her in a schl but ni fitan ne gaba daya bana so ma, so it's better i get a lady with better teaching qualification ta dinga koyar da ita a nan gida, i will also get another lady da xasu dinga karatun islamiyya tare duk a gida" Bude baki Ahmad yyi yana kallonsa, can yace "Why? Why dont u want her to go to school and islamiyya with her mates?" Abuturrab ya mike yace "Haka nan kawai, ra'ayina ne" Daga haka ya haura sama, Ahmad ya bi sa da kallon mamaki kafin ya kauda kai, a nan kuma yaji ya fara tantama anya Abuturrab ya saki yarinyar nan ma kuwa, but kuma yasan Captain to be someone that is very straightforward in yayi xai ce yayi, idan kuma bai yi ba xai ce bai yi ba, baya karya. Abuturrab na tafiya sama ya kwankwasa kofar dakin nata kafin ya bude, tana tsaye jikin window ta juyo da sauri, suna hada ido ta sunkuyar da kai, yace "Ki sameni kasa" Daga haka ya juya ya fita, Abaya ne jikinta blue, sosai kayan ya amsheta, a kwanaki kadan din nan da take shafa cream da Abuturrab ya siya mata tana wanka da shower gel ainahin haskenta yake kara fitowa ko ina na jikinta yyi smooth, wanda rashin fita ta shiga rana ya kara contributing da kyan fatar nata, slowly ta nufi kofa kana ganinta kasan she isn't happy, yau gaba daya ta tashi da kewan yan gidansu duk da basu ta6a nuna mata so ko na minti daya ba amma har kukan kewansu sai da tayi daxu, Abuturrab na komawa parlor ya xauna, Ahmad dae sai kallonsa yake, bayan some minutes ya mike da sauri  tunawa da yyi ba karamin aikinta bane ta sakko ba hijab, ganinta yayi tana saukowa stairs, Ahmad ya juya yana kallonta, Abuturrab ya koma ya xauna, ta karaso cikin parlon ganin Ahmad ta sunkuyar da kanta ta rakube kasa jikin kujera cikin sanyin murya tace "Ina yini" Yana kallonta babu ko kiftawa da murmushi fuskarsa yace "Lafiya lau Jiddah ya kike?" Tana wasa da gefen mayafinta, ita ma tana d'an murmushi tace "Lafiya lau" Ta d'an saci kallon Abuturrab dake kallonta suna hada ido ya jefa mata wani kallo ya dauke kansa ita kuma ta sunkuyar da kanta a hankali tace masa "Ina yini?" Bai amsa mata ba, Ahmad dake kallonta yace "Amma kin ci abinci?" Cikin sanyin murya tace "Eh na ci" Abuturrab ya kallesa yace "Is that question necessary??" Bai jira cewar Ahmad ba, ya kalli Jiddah babu yabo bbu fallasa yace "To sai anjima, tashi ki tafi" Mikewa tayi ta wuce sama tana tafiya a hankali, Ahmad ya bi ta da kallo, sosai yaji tausayinta har ransa, he can see she is sad, she looks so unhappy, ya dawo da dubansa kan Abuturrab dake hararansa, Daure fuska shi ma yyi yace "Abuturrab ka taimaki yarinyar nan sbda kaga ana neman cutarta right?ka taimaketa because she is sad, frustrated and almost depressed a gidansu, to ka gaya min bambancin gidansu da wannan gidan ynxu, didn't u notice how sad she looks fisabilillah, how on earth will u lock a being for days ita kadai a gida bata ganin kowa, ai sai wani cutar ya kamata wllh, baka san babu abinda ya kai wannan yanayin da ka barta ciki saurin kashe mutum ba ko, she have nobody to share anything with, just reason it fa, ta yaya xata yi ta rayuwa ita kadai, plss think of a more better solution tunda baka son kaita gidanmu ko gidanku..." Abuturrab yace "Idan ta fara karatu she won't look unhappy anymore" Ahmad bai kuma ce masa komai ba, Abuturrab yace "Ni fa can gidanmu xan wuce yanxu" Tabe baki Ahmad yyi ya mike yace "Dama idan abu ya samu yarinyar nan Aliyu kada ka kirani da sunan kana neman shawara ko wani abu" daga haka ya nufi kofa, Abuturrab ya mike ya bi bayansa. Sai bayan isha Abuturrab ya dawo gida, yana shigowa parlor ya kulle kofar parlon ya wuce sama, part dinsa ya fara wucewa ya ajiye ledan hannunsa, sai da yyi wanka ya canxa xuwa pajamas dinsa, mintuna ba da yawa ba yyi yana waya da Aneesah daga bisanni yace "Xan kira ki anjima" Daga daya bangaren ta marairaice tace "Ni ban yarda da xan kiraki anjiman nan dinka ba, just tell me karfe nawa xan sake kiranka" Yace "Wani d'an aiki nake son yi a system, idan na gama ai nace xan kira" A hankali tace "Toh Allah ya sa, but it's always xan kiraki anjima daga nan kuma shikenan sai gobe" Yace "Uhn xan kira don't worry" Daga haka ya katse wayar, mikewa yyi ya dau ledan abincin ya fita bangarensa, sai da ya fara knocking din sannan ya bude kofar dakin ya shiga, kwance ya ganta ta takure waje daya ta rufe har kanta, ya ajiye ledan hannunsa ya karasa ya bude duvet din, rufe fuskarta tayi da hannunta taki juyowa, tsayawa yayi yana kallonta, can yace "Kee" Still taki juyowa, ya hade rai yace "Baki ji na ne?" A hankali ta dago ta mike xaune amma bata yadda ta kallesa ba, kallon idanuwanta da suka yi ja ya dinga yi, can yace "Kuka kika yi?" Wasu hawayen suka taru idonta, ta ki yarda ta kallesa, yace "Ba magana nake maki ba" Ta fashe da kuka ta hade kanta da gwiwa tana shessheka, da mamaki yake kallonta, ganin irin kukan da take, ya xauna gefen gadon yana kallonta yace "Gaya min me ya faru" Ta girgixa masa kai kawai tana kukan a hankali, dauke kansa yayi, yayi shiru, bayan wani d'an lkci ya sake kallonta yace "Dago kanki ki kalleni" Taki dagowa, ya mata tsawa yace "Dago kanki nace" Da sauri ta dago hawaye na sauka idonta amma ta kasa kallonsa, ya mike ya koma side din da take kallo suka hada ido, a hankali ta sauke idonta, speaking very calmly yace "Toh gaya min me yafaru, kina son wani abu ne?" Ta girgixa masa kai yace "Kukan me kike yi then?" A hankali tace "Babu komai" Bai kuma ce mata komai ba, can ya kalli ledan da ya ajiye yace tashi kije ki dau abinci ki ci, ganin bata tashi ba ya hade rai yace "Tashi nace" Mikewa tayi ta nufi gun ledan ya bi ta da ido, yau ma riga da wandon ne na bacci jikinta, tana isa gun ledan yace sa darduma ki xauna a nan ki ci, ta tafi gun darduman ta dauka sannan ta dawo ta shimfida ta xauna a kai, daurewa kawai take amma ji take kamar ta fashe da kuka, ta bude ledan taga tuwo ne da miyar kubewa irin na ranan, sauke idonta tayi ta kasa kallonsa, ganin bata da niyyar fara cin abincin yace "Malama abinci nace ki ci" A hankali tace "Xan dauko ruwa" Ya mike ya fita xuwa kitchen ya dauko mata ruwan ya dawo, yana ajiyewa ya koma ya xauna, tashi tayi ta tafi bandaki ta wanke hannunta sannan ta dawo ta fara cin tuwon a nutse, shi dai kallonta kawai yake, he just have a special pity for women, bai son ganin hawayensu even by mistake, it get him weak, and sure yasan maganganun da Ahmad yyi masa daxu babu karya ko daya a ciki but he cannot let her stay with his mum or Ahmad's mum, he will get another solution.... Tana gama cinye tuwon daya xata rufe yace "Daya kika gani a wajen?" Ta girgixa masa kai tace "Baxan iya cinyewa ba" Yace "Kara daya" Bata masa musu ba ta fara cin wani dayan, amma bata iya ta cinye ba kuma bai tilastata ta cinye din ba, ta mike ta dau sauran abincin da ruwa ta fita daga dakin, mikewa yayi ya bi bayanta ya xauna main parlor ya kunna Tv, bayan few seconds ta fito kitchen din xata wuce sama ya nuna mata kujera yace "Dawo ki xauna nan" Tace "Xan wanke baki" yace "Je ki wanke ki dawo" Tafiya tayi saman ya maida dubansa kan tv, tana sakkowa ta tsaya tana kallonsa ya nuna mata kujera yace "Xauna" xaunawa tayi, ya ci gaba da kallonsa, tun tana daurewa sbda baccin da ya fara damun idonta gashi ta kasa gaya masa har daga karshe ta d'an kwanta still pretending to be watching d movie da bata ma san abinda ake a nan ba, da haka bacci ya dauketa, duk yana lura da ita amma bai ce komai ba, he gets she's so lonely, abinda ke damunta kenan, shi kuma he doesn't have intention of spending any of his time together with her, yau ma don kawai kukan da yaga tana yi ne yasa ya kasa jurewa, har karfe sha biyu yana kallo parlon, sai a sannan ya tuna da Aneesah da yace xai kira ya lumshe ido ya jinginar da kansa da kujera, sai kusan karfe daya ya bude idon don bacci daukesa yyi a hakan, kallon 2 sitter din da take kwance yayi yaga baccinta kawai take, mikewa yyi ya kashe switch din wutan parlon gaba daya sannan ya kwanta kan 3 sitter ya kashe tv da remote din kusa da shi ya lumshe ido.... Kiran sallahn farko Abuturrab ya tashi, ya fi minti goma xaune kafin ya duba wayarsa ya kunna fitila yana haskata, mikewa yyi ya karasa inda take kwance ya buga kujeran a hankali, bude ido tayi da sauri yace "Tashi ki wuce sama" tana lullumshe ido ta mike xaune sannan ta tashi ya haska mata hanyar stairs, ta fara tafiya sannan ya bi bayanta, tana shiga dakinta ko rufe kofar bata yi ba ta fada kan gado ta ci gaba da baccinta, yana tsaye daga bakin kofar bayan ta shiga, ya kulle kofar sannan ya wuce bangarensa. Sae kusan karfe tara da rabi Abuturrab ya sauko downstairs, kamshin girki kawai yake ji a gidan, ya tabe baki ya xauna saman kujera, sae ga ta tafito kitchen, turus tayi ganinsa, sae kuma ta juya ta koma kitchen din, shi dai idonsa na kan tv da yyi powering, can sai ga ta ta fito ta karaso cikin parlon, kallonta yyi... Her expression today isn't of someone that is sad, ta xauna kasa ta sunkuyar da kai, dimples dinta na lotsawa tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya lau" Ya gane da magana a bakinta ganin yanda take wasa da fingers dinta, can yace "Me xa ki ce?" Ta kallesa tace "Dama cewa xan yi in kawo maka kumallo?" Da mamaki ya dinga kallonta, can yace "Na me kenan?" Tace "Dankalin turawa na soya na soya kwai, sai na tafasa ruwan shayi" Yace "Ohk mun yi da ke xan ci ne?" Ta girgixa masa kai yace "Toh baxan ci ba, kayan abincin da kika gani a kitchen don ki girka ke kadai na siyosu na ajiye ba don ki girka ma ni da ke ba" Sunkuyar da kanta kawai tayi, bayan few seconds ta mike a hankali xata bar wajen yace "Tsaya" Tsayawa tayi amma bata yarda ta kallesa ba, yace "Dama kin iya soya Dankalin da kwai kike tsayawa da yunwa?" Bata ce masa komai ba, ya tabe baki yace "Je ki" Juyawa tayi ta koma kitchen din. Tana komawa ta fara kuka a hankali, sae da tayi me isarta sannan ta goge idonta ta fito xata wuce sama, ya bi ta da kallo yace "Kin karya?" Ta gyada masa kai xata haura sama yace "Dawo nan!" Ji tayi wani sabon hawayen na shirin xubo mata, ganin tsayawa tayi yace "Ba kya ji na ne?" Dawowa tayi ta sunkuyar da kanta, yace "Wuce ki xuba abinda kika yi ki xo nan ki xauna ki ci" xata yi magana ya jefa mata wani kallo, kitchen din ta nufa trying hard kar ta fara rusa kuka, a haka ta debo abinda tayi ta dawo parlon ta xauna tana turawa da kyar yana kallonta yana kallon TV sai da ya ga ta gama sannan ya bar ta ta wuce sama, shi kuma ya fita xuwa siyo fastfood.... A ranan mutumin da Abuturrab ya sa ya nemo masa mai gadi amma mai mata ya kirasa ya sanar masa an samu, Abuturrab ya masa izinin kawosa gida amma wajajen biyar na yamma. Yana xaune parlor yana jiran Jiddah bayan azahar, he is been sitting for almost 20 mins now, daga cewa ta shirya shine har ynxu, mikewa yayi ya haura sama ya bude kofar dakin suka kusa cin karo don xata fito ne ita ma, ta koma baya da sauri, ya wani hade rai yace "Baki da hankali ne xaki shanya ni a parlor?" Ta marairaice tace "Na kasa rufe rigar ne?" Yana kallonta daga sama har kasa yace "Wani riga?" Hijab ne jikinta har kasa sai atamfa daga ciki, tace "Zip din rigar" Ya jefa mata wani kallo ya juya, bin bayansa tayi, har suka sauka parlor, ya dau makullin motarsa ya nufi kofar fita ta bi sa da sauri, yana cikin motar ta  iso parking space din xata bude back seat yace "Kinsan meye ma'anar mutum ya shiga bayan mota bayan su biyu ne kawai a motar?" Tayi shiru tana kallonsa, bai kuma ce mata komai ba, ta xagayo xata shiga motar sai a sannan ya ga how obvious zip din da bata kulle ba yayi cikin hijab din, bayan ta shiga gaban motar yace "Daga hijab din nan" a hankali tace "A bude zip din yake" ya hade rai yace "Daga nace" kamar warce xata yi mugun abu ta fara daga hijab din, sai kuma ta kallesa kamar xata yi kuka, ganin yanda ya hade rai ta daga hijab din kawai, bayan ta yake kallo da bra strap dinta, ta sunkuyar da kanta, yace "Da a haka xaki bi ni don baki da hankali?" Ta girgixa masa kai, yace "Koma ki canxa kayan" Ta buda ido tana kallonsa, ganin irin kallon da yayi mata ta bude motar ta sauka, sauka yyi ya bi bayanta to check another clothe for her, sai bayan da suka shiga parlon ta kallesa tace "Xaka iya taya ni jan zip din fa, ba lalacewa yayi ba" yace "Ban yi niyya ba" bata kuma cewa komai ba ta wuce sama ya bi ta. Bude press din nata yayi yana kallon kayan ciki, abaya baki ya ciro mata da mayafinsa ya ajiye gefen gado, ta dan xaro ido tace "Wannan ai yana kama jiki" ya harareta yace "Baya yake kamawa ba jiki ba, minti uku na baki ki canxa kayan nan ki dawo kasa ki sameni" Bai jira cewarta ba ya fice daga dakin nata dake ta kamshin turarurruka, a balcony ya tsaya yana jiranta, sai gata ta fito, sosai bakin abayar ya haska farin fatarta ta dawo kamar balarabiya, flat show ne kafarta, she looks so beautiful and neat, kawai dai ta rame ne ba kadan ba, ganin ta tsaya ta wani sunkuyar da kai yace "Tsayuwar me kika min a nan?" Tafiya ta fara yi, ya bi ta da kallo kafin ya bi bayanta, front seat ta bude ta shiga, sai da ya fara bude gate sannan ya dawo ya shiga motar suka bar gidan, ya sauka ya kulle gate din, gidansu Ahmad ya nufa don xuwa gaida Umma, ya lura kamar she is a bit angry at him, don gashi wannan satin ma bata ce masa xata xo ba, a parking space din yayi parking, Yana sauka motar Jiddah ma ta sauka tun da taga gidan da suka shigo farin cikin fuskarta ya kasa boyuwa, shi dai ko kallonta bai yi ba, kallonsa tayi a d'an tsorace bayan ta sauka tace "Don Allah xan iya xuwa in gaida maman Abdallah?" Ya fara tafiya xuwa cikin gidan yace "Ki je mana" Da sauri ta nufi dakin Maman Abdallah, sai da ta gaida mai gadin ya amsa da fara'a yana mata sannu da xuwa tace "Maman Abdallah fa?" Yace "Ki shiga tana ciki" Da sallama ta shiga dakin, Maman Abdallah na ganinta ta rungumeta cike da farin cikin ganinta tace "Idonki kenan Jiddah, kai kai kai kinga yanda kika yi kyau kuwa, sannu da xuwa amarya" Wannan kalmarta na karshe ne ya d'an sa mood din jiddah ya canxa don tasan dai ita ba amarya bace, Xaunawa tayi tana ta kirkiran murmushi tace "Abdallah na bacci" Maman Abdallah tace "Wllh kuwa, ashe ku ne kuka shigo gidan a mota, sannunku da xuwa" Jiddah na ta murmushi tace "Bari inje in gaida Umma" Maman Abdallah tace "Toh maxa ki tafi, amma fa don Allah ki leko kafin ku koma kinji?" Jiddah tace "Toh" fita tayi dakin dai dai sanda Ahmad ya shigo compound din, ya buda ido sosai ganinta, sai kuma ya hango motar Abuturrab, da ladabi ta gaishesa ya amsa da fara'a yace "Yaushe ku ka xo?" Tace "Yanxu muka shigo" yace "Maa sha Allah sannunku da xuwa" Tafiya take yana gefenta shi ma yana tafiyan, can yace "Amma baki da damuwa ko Jiddah, kar ki boye min komai ki gaya min" Ta sunkuyar da kanta cikin sanyi tace "Ina son dawowa nan wajen Umma" Shiru yayi bai ce komai ba, don yasan taurin kan Abuturrab ya wuce ya amince Jiddah ta dawo nan gidan, a hankali yace "Kar ki damu Jiddah, nasan xama ke kadai ne baki so ko?" Ta gyada masa kai, yace "Kar ki damu nasan me xanyi" Da damuwa tace "Amma kar kayi masa magana ihu xai yi min" Murmushi Ahmad yyi yace "No baxan yi masa ba" Abuturrab suka gani bakin kofa tsaye alamar lkcn ya iso wajen ganin jiddah bata shigo ba, Jiddah sai da taji gabanta ya fadi ganinsa, shi kuwa sai ya hade rai, suna isa balcony din Ahmad yace "Sai ga amarya yau ta xo gidanmu, kun xo gaida Umma kenan" Abuturrab da yayi masa wani kallo underneath his breath yace "Half-wit" daga haka ya juya ya koma parlon. Rungume Umma jiddah tayi, sosai tayi farin cikin ganinta kamar yanda Umma ma taji dadin ganinta, Shi dai Abuturrab na yi yana kallon agogo don bai ma son la'asar yayi masu a gidan, Kitchen Jiddah ta tafi bisa umarnin Umma na cewa taje ta taya su Siyama da mai aiki girki, Umma na kallon Abuturrab tace "Why is she this lean? Bata da lafiya ne?" Ya sunkuyar da kansa yace "Eh tayi xaxxabi kwana biyu, amma ta samu lafiya yanxu" Ahmad dai sai wani kallo yake masa, Da damuwa Umma tace "Toh Allah ya sauwake, ita kadai din ce a gidan kenan yanxu?" Da sauri yace "Aa Umma ai nace akwai me aiki, kuma ma yawanci one day on, one day off nake yi" Umma tace "Toh shkkn Allah ya taimaka, karatun fa?" Yace "Xata fara in sha Allah" Umma tace "Toh maa sha Allah, Allah ya taimaka" Abinda Abuturrab bai so bane ya faru don sai da la'asar din yayi yana gidan, dakin Ahmad ya tafi yin alwala, Ahmad dake ta jiran ya shiga alwala ya jawo makullansa na gida bayan ya shiga bandaki, cikin few seconds yayi abinda xai yi ya ajiye sauran sannan ya fita dakin....




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



_Albishirin ku jama’a ko kusan akwai wani company da ya shahara wajen siyar da kayan alatu da abubuwan more rayuwa??


Wato Unique & Luxury Stores yana da bangararori daban-daban kamar haka,

 @unique_home_store_ng wanda ya shahara wajen siyar da kayan ado da qawata gida, kayan kitchen, furniture, carpet na gani na fada da sauran su.


Sannan akwai @elegant_projects_ng

Bangaren tsara gida kamar home styling na amare da uwar gida, interior designing da finishing....

Company bai tsaya a sashe 2 kawai ba yana da bangaren ado da kwaliya wato

@uniquefashion_ng. Duk bai tsaya anan ba ya kara zuwa maku da @unique_souq_ng inda zaku samu kayan kwadayi, makulashe da kayan da zasu kara inganta maku lafiyar jiki.

Karku bari ayi babu ku domin gane ma idon ku, ku garzaya shafukan su a Instagram kamar haka....


@unique_home_store_ng

@uniquefashion_ng

@unique_souq_ng

@elegant_projects_ng

Sannan zaku iya samun su ta WhatsApp a +2349071721586

Jiddah ce xaune bedroom din Umma dake mata tambayoyi, ita dai ta sunkuyar da kanta, Umma tace "Kar kiji komai ki fada min gaskiya Jiddah" Tayi murmushin karfin hali ta dago kanta tana kallon Umma tace "Da gaske ba komai Umma" Umma tace "Kin tabbatar?" A hankali Jiddah ta gyada mata kai, Umma tace "Yace ya kawo maki mai aikin haka ne?" Ta kalli Umma sannan cikin sanyin murya tace "Eh" Shiru Umma tayi tana kallonta don sai take ganin kamar ba gaskiya take fadi ba, tausayin Jiddah take a xuciyarta, ta kwantar da murya tace "Ni baxan ce masa mun yi maganan komai da ke ba Jiddah, ki bani amsan tambayoyina kafin su dawo masallaci yanxu" Jiddah ta kuma wani murmushi tace "Umma na baki amsan ai" Umma tace "Toh kina jin dadin xaman gidan?" Kallonta Jiddah ta dinga yi ta kasa cewa komai, Umma tace "Ina saurarenki..." Lkci daya hawaye ya kawo idonta, dai dai nan aka bude kofar dakin, Ahmad ya shigo tare da Abuturrab, sosai gabansa ya fadi, ya kalli Umma sannan ya kalli Jiddah, Umma dai ta daure fuska tana danna wayarta, Ahmad dai na tsaye bakin kofa bai karaso ba, ya dinga fatan Jiddah ta sanar ma Umma bata boye mata komai ba, Abuturrab ya shafa kansa a hankali yace "Umma dare na yi xa mu wuce gida" Umma tace "Ohk" wasu sabbin hawayen ya dinga sauka idon Jiddah, gaba daya Abuturrab ya kasa nutsuwa, kana ganinsa ka ga mara gaskiya, Umma na kallon Jiddah tace "Tashi ku je sai da safe" Ta kalli Abuturrab tana goge idonta, ya jefa mata wani kallo a fakaice, a hankali ta mike hawaye yaki tsaya mata tace "Sai da safe Umma" Umma bata iya ta amsa ba Jiddah ta nufi kofa, Abuturrab na kallon Umma yyi kasa da murya yace "Sai da safe Sai Umma" Ba tare da ta kallesa ba tace "Allah ya kai mu" Ya kalli Ahmad that is still standing wanda har ransa yake jin hawayen da jiddah take, Abuturrab ya ki ce masa komai ya fita dakin, Maimuna da siyama ne suka dau ma Jiddah abubuwan da Umma ta hada mata tun daxu xuwa motar Abuturrab, Jiddah dai na xaune gaban motar kamar ana dada tunxurata da kukan da take, Abuturrab ya tada motar ya bar gidan, sai a sannan ya sauke ajiyar xuciya, he even love it da Umma taki ce masa komai, har suka isa gida bai ko kalli Jiddah ba,  yana parking ya sauka ya tafi ya kulle gate din gidan ya dawo, tsaye ya ganta jikin motar fuskar nan nata kamar warce aka aiko ma da sakon mutuwa, ya hade rai yace "Ni xan dauko maki kayan naki dake cikin motar" ta juya ta bude bayan motar tana goge guntun hawayenta ta dau ledan hijabs din da Umma tayi mata da warmer din tuwo da miyar kuka da Umma ta sa a xuba mata, da harara ya bi ta yace "Xaki ga ko xaki sake leka kofar gate din gidan nan balle har in kai ki gidan Umma ki samu daman hawayen iskanci" Kamar jiran jin hakan take ta fashe da kuka sosai tana kallonsa tace "Don girman Allah kayi hakuri, wllh kewarta nake bana son in rabu da ita shi sa nake kuka, don Allah kayi hakuri" ko tanka ta bai yi ba ya nufi kofar shiga gidan ta bi bayansa da sauri tana kuka, ko tsayawa bai yi a parlor ba ya wuce bangarensa, ta shiga dakinta ta ci kukanta me isarta bayan ta sannan ta kwanta. Karfe sha daya da kusan rabi yayi knocking kofar dakin ya shiga, ganin tayi bacci ya bude warmer din abincin da ta ajiye kasan dakin, yaga bata ta6a ba duk da yasan ta ci abinci a can gidan, ko kayan jikinta bata cire ba, wannan dalilin ne yasa ya tasheta, mikewa xaune tayi da sleepy eyes dinta tana murxawa, yace "Me ya hanaki wanka kafin ki kwanta?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Dama bakya wankan daren da nace maki kenan?" Da sauri ta bude ido sosai tace "Wllh ina yi bansan sanda nayi bacci ba" Yace "Toh tashi kije kiyi wankan" Kallon agogo tayi da sauri, ya hade rai yace "Tashi nace" A sanyaye ta mike xata shiga bandakin yace "Da kayan xaki yi wanka?" bata ce komai ba, amma ta ki cire kayan a gabansa, ya daure fuska yace "Ba magana nake maki ba" Ta d'an kallesa tayi narai narai da ido tace "Tawul din yana bandaki ne" tana fadin haka ta shige bandakin, gefen gadon ya xauna yana naxarin maganganun da Umma tayi masa a waya bayan sun dawo gida, he is finding it hard to forget her words and move own, yasan no matter what Ahmad baxai ta6a gaya mata xaman da yake da Jiddah a gidan nan ba, yasan baxai ta6a ce mata ma bbu aurensu da Jiddah kamar yanda ya sanar masa ba, but her words carried weight this night, he have a very good intention toward jiddah, ba shi da nufin ya cuceta ko ya walakantata ko ya saka rayuwarta a garari, his intentions are nothing but pure, dafe kansa yyi, lkci daya ya dago jin wayar dake hannunsa yayi vibrate ya duba ya ga Aneesah ce ke kiransa, bai sake kallon wayar ba coz sun yi magana not too long, bayan kusan minti sha biyar jiddah ta fito daga bandakin sanye da kayan da ta cire, kasa kallonsa tayi ta ja gefe ta tsaya, wani kallo ya dinga mata kafin yace "Meye hakan kika yi?" Ta ki yarda su hada ido tace "Ni baxan iya fitowa babu kaya ba bayan kana xaune dakin" Daga sama har kasa ya dinga kallonta yana mamakin abinda ta fada, can dai yace "Ke kina da wani abinda xaki boye min a jikin ki dama, kwaila da ke?" Ta d'an turo baki ta juya masa baya, Tsaki yyi ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo, murya can kasa tace "Eh amma ai ni ba muharramarka bace da xan cire kaya...." Ganin ya juyo tayi tsit, ganin impression din fuskarsa gabanta ya fara faduwa, yace "Kika ce me?" Ta girgixa kai da sauri tace "Ban ce komai ba" Dawowa dakin yyi, ta marairaice tana kallonsa tace "Don Allah kayi hakuri ni bance komai ba" Yace "Kika ce ni ba muharraminki bane?" Ta girgixa masa kai da sauri bakinta na rawa tace "Aa bance haka ba" Sai da ya iso gabanta ya tsaya, sbda tsoro taji ta ma kasa tsayawa, calmly yace "A ina kika san wanda muharraminki ne da wanda ba muharraminki ba?" Jin taki cewa komai ya mata wani tsawa da yasa ta duka hawaye ya kawo idonta, yace "Idan baki bani amsata ba na fara ball dake sai kin ganki downstairs yanxu" Cikin rawan murya tace "Ai da ina xuwa islamiyya" Ya gyada kai yace "A islamiyyan kuma basu sanar maki hukuncin wanda yace xai kashe kansa ba?" Kasa cewa komai tayi, ya wani hade rai yace "Mike ki cire kayanki" Ta sake marairaice masa amma ganin kallon da yake mata ta mike da kyar, ta gefen ido ta kalli bandakinta, lkci daya kamar kiftawan ido ta shige ta sa makulli hannunta na rawa, ya dinga kallon kofar, can yyi murmushi yana shafa kansa, lkci daya kuma ya hade rai ya fice daga dakin, bai karasa bangarensa ba wayarsa yyi vibrate ganin me kiransa sai da gabanaa ya fadi, har ya katse bai dauka ba, sai da aka sake kira sannan ya daga, murya can kasa yyi sallama yace "Ina yini Aunty" ba tare da ta amsa ba tace "Aliyu kana ina??" ya d'an bude ido yace "Aunty ai ina kano, ban dawo ba..." Bude kofarsa yyi ya shiga ya kulle hade da lumshe ido jin abinda take cewa. Washegari da safe wanda Abuturrab ya sa ya samar masa mai gadi ya iso gidan da mai gadin, Abuturrab na kallon matashin mai gadin yace "Yaranku nawa da matar taka?" Mai gadin yace "Daya ne kawai Alhaji, sabon aure ne" Abuturrab yace "Ba damuwa, yau nake son xaka fara aikin sai ka koma ka taho da iyalan naka" Mai gadin ya risina da ladabi yace "Toh nagode Alhaji, xan je kauyen namu yanxu sai in taho da su in sha Allah, Allah ya saka da alkhairi" Abuturrab yace "Ameen, amma kada ka wuce karfe biyar na yamma don xan koma gun aiki a yau" Mai gadin yace "In sha Allah Alhaji" dubu biyar Abuturrab ya basa kudin motar xuwa taho da iyalan nasa, shi ma wanda ya kawo sa ya basa dubu biyar, bayan sun tafi ya koma cikin parlor.... jiddah na kitchen tana dumaman tuwon da umma ta bata jiya, yatsine fuska yyi yana kallon kitchen din don ko by mistake baya son warin miyar kuka, barin ma yanxu da take dumamawa, hakan ya sa ya dau makullin motarsa ya bar gidan xuwa inda xai je yyi breakfast, jiddah na jin fitan motarsa ta jigina jikin bango tunda taji yana waya ko minti sha biyar ba ayi ba yace yau xai koma gun aiki ta ji duk mood dinta ya canxa, gaba daya bata son xama ita kadai a gidan, a sanyaye ta kashe gas din ta xuba tuwon amma ta kasa ci, Duk da xamansa a gidan da rashin xamansa kusan daya don ba wai wani magana me tsayi yake mata ba, kuma ba waje daya ma suke xama ba amma idan yana gidan bata jin kadaici da kewa na damunta, duk sonta da tuwon saboda yanayin da ta shiga sai ta kasa ci da yawa, haka nan ta mike ta kai kitchen ta wanke plate din, sama ta wuce ta wanke bakinta, komai da take yi a gidan tayi, turaren wuta ne kawai bata sa ba, ta dau turaren ta sauka parlor ta sa sannan ta xauna tana kallon yanda yake fita a hankali, kana ganinta kasan jikinta a sanyaye yake, bude kofar parlon aka yi Abuturrab ya shigo ta daga kai ta kallesa sannan ta sauke idonta, sai da ya karaso cikin parlon tace "Sannu da dawowa" Bai amsa ba yyi wucewarsa sama ta gefen ido ta bi sa da kallo har ta daina ganinsa, a sanyaye ta mike ta wuce sama ta shiga dakinta ta kwanta tana kallon fuskarta ta madubin press din dakin.  Da yammacin ranan tana tsaye jikin window aka bude kofar dakin, tunda ta kallesa sau daya ta dauke idonta, yana bakin kofar a tsaye yace "Shuka kika yi wajen nan da kike tsayawa ko da yaushe?" Tana wasa da fingers dinta ta girgixa masa kai, juyawa yyi ta bi sa da kallo ganin jakar hannunsa, da sauri ta bi sa tace "Tafiya xaka yi?" Ya juyo yace "Kina bukatar wani abu ne?" Lkci daya jikinta yyi wani sanyi, shi dai kallonta yake yana lura da ita duk a lkci daya, sauke idonta tayi saboda hawayen da ya kawo idonta, yace "Nace kina bukatar wani abu ne" ta girgixa masa kai hawayen dake makale idonta ya gangaro ta juya da sauri ta koma ciki, da ido ya bi ta, kafin ya bi bayanta xuwa dakin, durkushe ya ganta ta daura kanta saman gado, da mamaki yake kallonta, can yace "Ke kina da lafiya kuwa" kin dagowa tayi tana shessheka, ajiye jakar yyi yana kallonta, can ya karasa kusa da ita ya tsaya yace "Tambayar ki nake, kina da lafiya kuwa?" Still taki dagowa, ya daka mata tsawa yace "Baki ji na ne" mikewa tayi hawaye na kai koma a idonta, ya dinga kallonta kafin yace "Me aka maki?" Ta girgixa masa kai, ya mata wani kallo yace "Me aka maki nace?" Cikin rawar murya tace "Ba komai" rungume hannu yyi yana kallonta, can yace "Kina bukatar wani abu ne" Wasu sabbin hawayen na xubo mata cikin rawar murya tace "Tafiya zaka yi ka barni ni kadai babu kowa, alhalin tsoron gidan nake ji" kallonta kawai yake ya ma rasa me xai ce mata, can dai yace "Shine yasa kike kuka?" Ta gyada masa kai tana kallonsa with tears in her eyes, yace "Ohk, ynxu in tafi da ke kenan?" Tayi shiru still crying tana kallonsa, yace "Bude baki ki bani amsa, in tafi da ke kenan yanxu?" A hankali ta gyada masa kai, daga sama har kasa yake kallonta, tausayinta yake ji har kasan ransa amma bai nuna hakan ba, to ina ma xai kai wannan yanxu wani yayi xaton matarsa ce?? Ta ina xai fara tafiya da ita? Ita dai kanta na kasa, bayan few seconds yace "Ina wayar da na baki" juyawa tayi a sanyaye ta nufi gaban madubi ya bi ta da kallo, har ta dauko wayar ta dawo, ta mika masa, amsa yyi ya shiga call log, yace "Matso" ba musu ta matso kusa da shi tana kallonsa, ya hade rai yace "Wayan xaki kalla ba ni ba" Kallon wayar tayi, ta madubin press din dakin ya kallesu, duk tsayinta iyakarta kirjinsa, jin bai ce komai ba sai kallon wayar take ta daga kai a hankali ta d'an kallesa, ganin inda yake kallo ta kalli madubin ita ma, a hankali ta d'an koma baya ganin dab take da shi ta sunkuyar da kanta, dauke idonsa yyi daga madubin, as if bai son maganan yace "Ga number na nan, duk idan kina son wani abu ko kina da wani magana sai ki danna nan sannan ki sake dannawa ki kirani" Kai kawai ta gyada masa ya jefar da wayar kan gado ya nufi kofa ta bi sa da kallo sabon hawaye na taruwa idonta har ya fita, yau din ma ta waje ya kulle kofar parlon duk da kasancewar mai gadi da matarsa da yaronsu dake gidan yanxu. Kuka sosai Jiddah tayi bayan tafiyarsa, taji komai bai mata dadi a duniyar ynxu, kullum ita kadai kamar mayya a gida babu kowa, tun tana tsoro sosai har tsoron ya ragu, tana sallan isha ko abinci bata ci ba ta kwanta ta takure cikin duvet, nan da nan bacci ya dauketa.... Abuturrab na xaune saman gadon hotel wajen karfe goma da rabi, ya gama abinda yake a laptop ya ajiye yana duba agogon wayarsa, call log dinsa ya shiga har yyi dialing number sai kuma ya katse, mikewa yyi ya kashe wutan dakin ya kwanta yana karanto addu'ar kwanciya, jawo wayar yyi ya d'an yi dube dubensa, sai kawai ya shiga call log din yyi dialing number, he just can't because he have a problem with conscience, abu kadan ke sawa conscience dinsa yyi judging dinsa... Karan wayar ya farkar da Jiddah, bacci ne sosai idonta haka dai ta dau wayar dake saman gadon tayi picking sannan ta kai kunne ta rufe ido bata ce komai ba, jin shirun yyi yaww Abuturrab yace "Ni xan gaisheki" ta bude ido cikin muryar bacci tace "Aa" nan da nan ya gane ta fara bacci, ya dai ce "Me kika ci?" Shiru bata amsa ba, yace "Kee?" Tace "Uhn" yace "Kin yi bacci ne?" Kai kawai ta gyada masa ba tare da tace komai ba kamar yana ganinta, shiru yyi, bayan wani d'an lkci yace "Amma sae da kika yi wanka??" Tuni Jiddah tayi nisa baccinta, bayan few seconds yace "Jeeddarh" jin shiru ya katse wayar kawai ya ajiye sannan yayi rub da ciki nan da nan shi ma baccin ya daukesa. Washegari Jiddah na kitchen yau dai shinkafa da miya take yi tunda ya koya mata yanda ake amfani da blender, ji tayi kamar ana bude kofar parlor, ta tsaya kitchen din tana saurare har taji an shigo parlon, da sauri ta fito, ido hudu tayi da Ahmad tare da Maimoon, kallonsu kawai take da mamaki, ya sakar mata murmushi yace "Toh ko dai mu koma ne?" ta girgixa kai da sauri tace "Aa sannunku da zuwa" Duk suka karasa parlon yana kallonta yana murmushi, Maimuna na kallon Jiddah ita ma tana murmushi tace "Sannu da gida Aunty Amarya" Murmushi jiddah ta kirkira ta karaso ita ma cikin parlon, har ranta taji dadin ganinsu, Ahmad ya xauna yace "Ya gidan Jiddah?" A hankali tace "Lfya lau, ina yini?" Yace "Fine Alhmdlh, dama an kawo mai gadi gidan ne?" Kallonsa kawai Jiddah ke yi kafin tace "Nima ban sani ba ai" Tausayinta Ahmad ya ji, can yace "Toh baxa a kawo mana ruwa ba?" Tashi Jiddah tayi tana murmushi a kunyace ta wuce kitchen ta kawo masu har da lemo, tun jiddah na kin sakin jiki, har daga karshe ta sake gaba daya, Ahmad ya dinga mamaki ganin ashe tana da baki, ga zakin murya kamar zaabiya, sosai Maimoom taji tana son Jiddah, har abinci sai da ta kawo masu, ana kiran azahar Ahmad yace mata xasu wuce don yau ma xai koma Abuja, lkci daya mood dinta ya canxa, Maimoon sai taji tausayinta, makullin gidan Ahmad ya mika mata yace "Su Maimoon xasu dinga xuwa taya ki hira a kai kai idan captain din baya gari so kar ki damu kinji" kasa basa amsa tayi don har hawaye ya kawo idonta, dariya ta basa, yyi kasa da murya yace "Amma fa kar ki sanar masa xuwan mu kinji? Wataran idan naxo tafiya xanyi dake daga gidan gaba daya" Ta gyada masa kai, a haka suka tafi duk yanda ta so daurewa ta kasa sai da tayi kuka. Bayan la'asar wajajen karfe biyar ta gaji da xaman dakin da tsayuwar window ta fito, kallon hanyar da xai kai ta part din Abuturrab tayi, tun ranan da suka fito daga wajen bayan ya nuna mata takarda bata sake bin hanyan ba, tsaye tayi tana ta kallon direction din, can dai ta karasa tana tafiya a hankali har ta isa kofar parlonsa ta bude tana lekan ciki, komai na parlon fess ko alamar datti bata gani ba sai wani kamshi ma da take ji, shiga parlon tayi tana bin ko ina da kallo gabanta ya dinga faduwa, can ta karasa wani kofa da ta gani, bude kofar tayi a hankali tana lekan ciki, daki ne da wani babban katifa da bedsheet a kai, babu abinda bbu a babban dakin, karasawa tayi ciki tana kallon wani table da jirgi a kai, xaro ido tayi tana kallon karamin jirgin, dauka tayi da hannu biyu tana jujjuyawa ta kai idonta tana leka d'an windows din jirgin, hotonsa ta gani jikin bangon dakin da fararen kaya ya rike hula tsaye kusa da wani katon jirgi, a ranta tunani ta shiga yi kilan shi ya ta6a ganin jirgi tunda gashi yayi hoto kusa da jirgin, ita dai a sama kawai suke hangosa dan mitsili, kallon fuskarsa ta dinga yi, lkci daya gabanta ya fadi tana ganin kamar xai iya magana a hoton, a hankali ta juya, taga wani kofa ta karasa ta bude ta ga wani makeken bandaki da abu kamar katon glass a ciki har tana iya hango ciki, kwata kwata bandakin ba irin nata bane, ga shi da girma sosai, ko ina a bushe yake sai kamshi bandakin yake, a hankali ta rufo kofar sannan ta bude wani kofar da ta gani daga can end, xaro ido tayi ganin view din, karamin balcony ne, ta dinga bin gidan da kallo daga kasa wanda ke shimfide da carpet grass ga wasu flowers a gefe, sosai wajen ya mata kyau ba kadan ba, ta kalli wani babban gidan dake opposite dinta suka yi ido hudu da wani dake xaune shi ma a balcony, laptop ne gabansa da drink, shi dai kallonta kawai yake, ta Sunkuyar da kanta da sauri ta juya ta koma ciki ta kulle kofar, da sauri da sauri ta koma dakinta. Daren ranan bayan isha Abuturrab na Abuja a gidansa sbda weather bai bari sun koma kano ba, Aneesah ce xaune kusa da shi a dakinsa, yace "Kince kina da lectures da safe, why not sleep now?" Ta hade rai tace "Toh ae it's not a crime idan nayi bouncing lectures din ko?" Ya gyada mata kai yace "Haka ne...." Lamo tayi ta lumshe ido kusa da shi, ya ci gaba da abinda yake, bayan few minutes ta bude ido tana kallonsa tace "In tambayeka mana captain" Yace "Ina jin ki" tace "This days kamar u are not longer eager being with me, why?" ya buda ido sosai yace "Why do u say so?" Ta marairaice tace "Haka naga alama, or do u have anything in mind?" Murmushi yyi yace "Yaushe rabon mu hadu? It's almost 10 days now" ya ja hancinta yace "And ke kin fiye ma mutum jan aji ne" Rungumesa tayi cike da shagwaba tace "Wallahi ba haka bane, ae kai din ne sai ka xo Abuja kake neman mutum" ya cire hulan kanta yace "Ohh really??" Dariya tayi tace "Aa wasa nake my captain ni kadai...." yyi murmushi yace "In few days time su Abbanmu xa su je gidanku in sha Allah" ta wara ido tace "Da gaske my captain?" Yace "In sha Allah" Rungumesa tayi tace "I can't wait Babynah" ya d'an hade rai yace "Baby kuma?" Dariya tayi sosai tace "Au.. to yi hakuri na manta baka son sunan, amma fa kada wataran ka xo kayi ta rokana in kiraka da Baby" yace "Sai kace wani jariri" Dariya kawai take tana kallonsa don tun ba yau ba tasan bai son irin wannan soyayyan da yawanci yake kiransa da na yarinta, ta daura kanta saman shoulder dinsa tana jin wani sabon sonsa na fixagarta...  Karfe daya saura few minutes Abuturrab ya fito bedroom dinsa bayan yayi wanka ya shirya cikin jallabiya, xaunawa yyi parlor yyi dialing number ya kai kunne, sae da ya katse ba a dauka ba sannan ya kalli agogo, ajiye wayar yyi ya kwanta saman doguwar kujera ya lumshe ido... Throughout week din nan Jiddah bata ji kadaici sosai ba don ranan laraba ma sai da Maimoon ta xo gidan, A ranan kuma Abuturrab yyi niyyar dawowa amma cikin ikon Allah sai bai samu dawowan ba, ranan alhamis Maimoon ta kara xuwa tare da Ramlah da abinci wanda Umma ta basu su kawo ma Jiddar, sosai Jiddah ta sake da su don ba kadan suke debe mata kewa ba, Ramlah ta dinga mamaki kamar yanda Ahmad yyi ganin ashe dai Jiddah na magana haka, ga dariya kamar me, xuwan su ya sa har ta samu confidence din fita suka xaga cikin gidan gaba daya tare da su, a nan ne ma tasan da mai gadi da matarsa a gidan, sai bayan magrib Umma ta aika driver ya je ya daukosu, Jiddah ranta fess ta ci sauran abincin da suka rage sannan tayi wanka tayi isha ta shirya ta kwanta, nan da nan bacci ya dauketa. Karfe tara saura Abuturrab dake xaune hotel room dinsa a kano yyi dialing number nata, har ya gama ring bata daga ba, da mamaki ya dinga kallon wayar, ya sake kira nan ma no answer, sake kira yyi ya sake ringing ya gama ba a daga ba, da yamma ma ya kira sau biyu no answer, a lkcn kuma Jiddah na can compound tare da su Ramlah, ajiye wayar yyi, can ya mike ya shirya within few minutes ya dau makullin motarsa da jakar laptop dinsa ya fita dakin, abinda bai ta6a yi ba xai yi ranan, wato driving to kaduna at night, dama da asuba yyi niyyar komawa kaduna sbda throughout gobe ba shi da duty, amma yanxu yyi deciding din tafiya kawai, sai kusan sha biyu da wani abu Abuturrab ya shiga gida yyi parking mai gadi ya taho da sauri yyi masa sannu da xuwa, amsawa yyi ya wuce ciki, makulli ya ciro ya bude kofar dake a kulle, Jiddah bata mance warning din Ahmad na cewar duk wanda ya xo kar ta mance kulle gidan da makulli bayan ya tafi ba sannan ta boye makullin, bin parlon ya dinga yi da kallo, ya kashe wutan dake a kunne ya wuce sama, kofar dakinta ya bude, kwance ya ganta tana bacci cikin nutsuwa, karasawa cikin dakin yyi still looking at her da wani expression can ya juya ya fice daga dakin ya tafi bangarensa. Washegari da safe bayan Jiddah tayi wanka ta shirya ta fito daga dakinta, cak ta tsaya jin kamar tana jin murya a can daya part din, to ko tv ne a kunne, ko ma ita ce ta ta6a abu da ya kunna tvn ranan da ta shiga dakin bata sani ba, gabanta na faduwa ta fara tafiya xuwa can din a hankali, har ta isa sannan ta bude kofa cikin nutsuwa tana lekan parlon, babu wani tv dake a kunne ta dinga bin parlon da kallo, sai taji ba tv bane karatun qur'ani ne, har xata juya ta d'an yi jim kamar me shakkar shiga ciki, can dai ta karasa ciki tana kallon kofar bedroom din da ba a rufe ba gaba daya, tunani ta dinga yi ko ita ta bar kofar haka jiya, a hankali ta kutsa kai ciki, wani kara tayi a tsorace ganin mutum kwance with short and singlet yana bacci, ta juya da sauri ashe ta mayar da kofar ta ci karo da kofar, wani ihun ta kuma yi ta dafe forehead dinta....



Don Allah no Reader should come and ask me of complete document na Jiddatul Khair plss, naga dai ba tsohon book bane da xaku dinga cewa sae an baku document xaku biya, snn shi page guda guda da ku ke karantawa ae ba kyauta bane shi ma, to don hka ko wacce ta ji da bashin dari biyat din mutane😏




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems


Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada


Instagram -fareeskinglow_89

TikTok-fareeskinglow

Facebook page-fareeskinglow 

WhatsApp -08031898240

Bude ido Abuturrab yyi ya tashi xaune yana kallonta da mamaki, ta mike tsaye hannunta a goshinta, ko ina na jikinta rawa yake, duk ta daburce, xata bude kofar cikin tsawa yace "Me ya kawo ki nan??" Kin juyowa tayi hannunta na rawa ta bude kofar xata fita, wani tsawan ya kuma yi mata yace "Kar ki kuskura ki tsallaka bakin kofar nan" fashewa tayi da kuka amma taki juyowa kuma bata fita dakin ba, ya sauka daga saman gadon ya dau jallabiyansa ya saka sannnan ya nufeta, tana jin alamar ya sauka gadon ta juyo da sauri, ganinsa tayi tsaye gabanta, fuska daure yace "Me ya kawo ki bangarena?" Cikin rawan murya ta durkusa tace "Wllh kara naji shine na xo in ga meye, ban san ka dawo ba Allah" Ya rungume hannunsa yace "Wato har nan kike shigowa kenan idan bana nan kenan?" Ta fashe da matsanancin kuka tana girgixa kai tace "Aa bana shigowa, ni ba shigowa nake ba wllh" Yace "Toh ina ruwanki da koma me kika ji da xaki shigo min daki?" Hawayen dake makale idonta ya sakko ta girgixa masa kai kawai bata ce komai ba, yace "Toh tafi ki dauko abun shara, ki share tun daga cikin dakin har parlor sannan ki goge, ki wanke bandakin...." Ta sunkuyar da kanta don har ta ji hankalinta ya kwanta xatonta har marinta sai yyi yau, kofar balcony din dakin ya nufa ya bude yana nuna mata yace "Har nan xaki share kiyi mopping" Gyada masa kai kawai tayi, ya dau wayarsa har ya nufi kofa ya tsaya, ya juyo yana kallonta yace "Kar ki ga na kyaleki yau, billah idan kika sake shigo min bangarena ko da wasa xaki sha mamaki" Kai kawai ta gyada masa a sanyaye, ya juya ya fita, sai da ya fita parlon gaba daya sannan ta juya a hankali ta fita ita ma, downstairs ta sauka ta gansa xaune parlor ya kunna TV, ta wuce kitchen ya bi ta da kallo, abun sharan ta dauko da mopping bucket tare da mop with duster sannan ta wuce sama, aikin ta shiga yi babu ganda, har xanin gadon sai da ta sake shimfidawa, bayan ta gama da bedroom din ta tafi balcony, kallon inda taga mutumin ranan tayi duk da babu kowa wajen sai kujera amma sai take ganin kamar shi a wajen, ta fi minti biyu tsaye tana ta kallon wajen kafin ta fara share balcony din ta yi mopping ta dawo dakin ta kulle kofa, parlor ta tafi nan ma ta share ko ina ta goge har kayan kallon, tana gamawa ta koma bedroom din ta bude kofar da take tunani bandaki ne, kallon bracelet din hannunta me kyau tayi wanda yau ya kai kwana uku da ta saka  shi, ta tafi gaban mirror dinsa ta cire sannan ta ajiye tana kallon turarrukan da ke gaban madubin, kwalabensu ne ya burgeta sosai, they look so unique, ta dau daya daga ciki ta bude ta kai hanci, rufe ido tayi sannan ta bude, da wannan kamshin ta sansa, babu kuma abinda ya fado mata sai lkcn da yake xuwa can wajenta a Hayin rigasa,  ta dau murfin xata rufe turaren ya subuce daga hannunta duk kokarin ganin ta kama turaren kan ya kai kasa hakan ya faskara don tuni yayi landing kan tiles sbda irin faduwan da yayi kuma lkci daya ya tarwatse, a tsorace ta ja baya ta dafe kirjinta da ya hau bugawa, lkci daya ta fara yarfe hannu murya can kasa tace "Na shiga uku" hankali tashe take kallon turaren, ta ma rasa abun yi, can ta nufi kofa sai a sannan ta fashe da kuka ta fita part din, downstairs ta sauka ta makale jikin bango tana kallonsa gabanta na faduwa, jin footstep kuma bai ji ta karaso cikin parlon ba ya sa ya juya, sunkuyar da kanta tayi, ya mike yana kallonta ganin hawaye a idonta, satan kallonsa tayi ganin kallon da yake mata ta fashe masa da kuka tace "Don Allah kayi hakuri" kasa daina kallonta yyi, can yace "Me kika min a sama?" Ta kara rushe masa da kuka tace "Don Allah kayi hakuri nace" Ya wani hade rai yace "Me kika yi nace?" Kin cewa komai tayi, ya nufeta, da gudu ta bar wajen ta wuce sama, ya bi bayanta, tuni ta shige dakinta ta rufe kofan da karfi, part dinsa ya nufa tun bai shiga parlon ba ya soma jin kamshin turarensa, ya shiga parlon sannan ya bude kofar dakin, tsaye yayi bakin kofa ya rungume hannunsa yana kallon tsadadden turaren nasa a kasa, Jiddah dai sai zare ido take tana jiran jin ya shigo dakin amma bai shigo ba har sha daya na safe, sai a sannan ta fara jin yunwan da ya dameta, lamo tayi kan gado kamar xata yi kuka tana tsoron fita, tana nan a haka har kusan sha biyu, mikewa tayi daga karshe ta nufi kofarta ta bude a hankali, cikin sanda ta sauka downstairs bayan ta tabbatar baya kasa sannan ta wuce kitchen, indomie ta dauka ta fara dafawa a kitchen din, ko kadan bata yrda tayi making noise da xai sa a san tana kitchen din ba, yanda taga Ramlah ta dafa masu indomie jiya take yi, with ingredients, tana duba indomie da har ya dahu kamar ance ta juya ta gansa tsaye bakin kofa, sake murfin tukunyar tayi a rikice tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" end din kitchen din ta tafi ta tsaya tana kallonsa a tsorace kamar xata yi kuka, ya karasa gun gas din ya kashe na indomien, da kuma na kwai dake tafasa, tana ganin haka xata fita kitchen din da gudu, ya tare hanyar, hade hannunta tayi waje daya ta marairaice tace "Don Allah kayi hakuri" yana mata wani kallo yace "Laifi nawa kenan kika yi yau a gidan nan?" Ta hadiye abu da kyar tace "Biyu" yace "Wanne da wanne?" Tayi narai narai da ido ta ki cewa komai, ya hade rai yace "Ina jin ki" Cikin rawar murya tace "Na fasa maka turare" yace "Ehen, sai me?" Tace "Na ji kamar radio na magana shine naje sashinka ka kamani" Ya gyada kai yace "Good, kinsan nawa turaren nan da kika fasa min?" Ta bude ido tana kallonsa amma bata ce komai ba, yace "Toh ki sani cewar tara ki nake, turaren nan kuma sai kin biyani duk yanda za ki yi ba ruwana" a hankali tace "Toh ae ni bani da kudi" yace "Ehh nemosu xa kiyi duk inda xa ki nemo su" ta sauke idonta kasa, kallonta yake daga sama har kasa, ya sauke idonsa kan fingers dinta yaga babu farce alamar tana cirewa a kai kai, ya kalli fararen toes dinta, kallon fuskarta yyi yaga har sannan kasa take kallo, yace "Cire hular ki" sae a sannan ta daga kai ta kallesa amma taki cirewa, ya hade rai yace "Magana nake maki" a hankali ta xame hular, ya dinga kallon bakin gashin nata wanda sak na Fulani, amma duk ya takure waje daya duk da da ribbon ta dauresa a tsakiya ya sauka kasan wuyarta, tun gyaran gashin da Umma tayi mata har ranan bata ta6a gashin ba, ya yamutsa fuska yace "Meye wannan din?" Ta kallesa bata ce komai ba, ya mata tsawa yace "Ba tambayar ki nake ba" Cikin sanyin murya tace "Gashina ne" Yace "Ke kaxamar wace gari ce, gashin ki ne kika bari haka kamar na mahaukaciya?" Ita dai bata ce komai ba, ya koma baya yana sake kare ma gashin kallo da mamaki, satan kallonsa tayi ya mata wani shegen kallo yace "Sae na tsokale idonki kika sake kallona, kina mace da ke dubi ynda gashin ki ya koma kamar gashin jikin tinkiya?? What nonsense" Lkci daya hawaye ya kawo idonta, strictly yace "Ki gama cin abincin kiyi sllh ki jirani a parlor" Bata ce komai ba ya juya ya fice daga kitchen din, Jiddah bata wani ci abincin ba sae hawaye, daga karshe ta mayar kitchen ta rufe taje sama ta wanke bakinta ta dau gogaggen hijab dinta ta saka ta dawo parlor ta xauna fuskarta babu walwala, sae da ya dawo sallahn Juma'ah sannan ya dau makullin motarsa, ya isa bakin kofar fita sannan ya kalleta yace "In xo in dauko ki ne" mikewa tayi a sanyaye ta bi bayansa, gaban motar ta xauna don bata mance abinda yace mata ba last time da ta xauna a baya, wani saloon ya kai ta, yana xaune mota ya jira har aka gama sannan daya daga workers din ta fito ta sanar masa an gama ko xa ayi mata lalle, yace "Aa, nawa ne kudin gyaran gashin naku?" Ta fada masa ya ciro kudin ya mika mata tayi masa godiya ta koma ciki, ba a dau lkci ba sai ga Jiddah ta fito daga saloon din, walking slowly ta iso gun motar har sannan fuskarta babu walwala, ta bude gaban motar ta shiga, ta rufe bata ce komai ba, kallonta kawai yake da mamaki, gani yake kamar da kyar ta iya rabuwa da halin gidadanci, ya daga kafada don yasan yana magana xata fara hawaye abinda bai shirya gani ba kenan, ya tada motarsa ya bar saloon din, suna tsaye traffic ganin yanda take kallon me tallan Apple a bakin glass din motar yace "Xa ki ci ne?" Sauke idonta tayi bata ce komai, yace "Ba magana nake maki ba?" Ta girgixa masa kai fuskarta a tamke tace "Baxan ci ba" hade rai yyi yace "Keee" Juyawa tayi ta kallesa tace "Nace A'a" Wani mugun kallo ya dinga mata ta dauke kanta, har suka isa gida bata sake kallon inda yake ba, yana gama parking ta sauka amma tana tsoron ta fara tafiya yyi mata masifa, Matar Mai gadi ce tsakar gidan daga kofarsu ganin Jiddah tace "Sannunku da dawowa Hajiya, Ina wuni...., duk yau shiru baki fito ba" gaban jiddah ya fadi sosai, Abuturrab ya dinga kallonta, Jiddah ta yi murmushin karfin hali tana kallon matar tace "Ina yini" daga haka ta fara tafiya da sauri, bin bayanta Abuturrab yyi, sai da ya shiga parlor ganin har ta isa stairs xata wuce sama yace "Dawo nan" juyowa tayi sannan ta dawo gabanta na faduwa, yace "Ta ina kike fita har take ce maki yau baki fito ba?" Ta xaro ido tace "Ai kofar a rufe kake barinsa, ni bana fita ko ina, ban ta6a ganinta ba ni sai yau" kallonta kawai yake ta Sunkuyar da kanta, ya xauna saman kujera, ita dai bata yadda ta sake kallonsa ba, yace "Ina gyaran gashin da aka maki?" Cire Hijab din jikinta tayi sannan ta sauke hular tana kallonsa, da mamaki yace "Daga nan xan gani" A hankali ta duka kasa ta matsa kusa da kujeran da yake xaune ta juya masa kan nata, kallon bakin gashin dake ta sheki yake, yace "Ta haka xan ga gyaran an daure gashin?" Ta juya ta kallesa sannan ta xame ribbon din gashin ya sauka kasa, bayan few seconds jin bai ce komai ba ta juya ta kallesa suka hada ido, hade rai yyi yace "Tashi ki tafi" Tashi tayi ta mayar da hulan sannan ta wuce sama dakinta. Mikewa yayi ya dau makulli ya fita don xuwa can gida ya gaida su Ummi, Tana jin an bude gate ta mike ta isa bakin window ta tsaya tana lekan compound din har ya fita da mota, turo baki tayi ta koma bakin gado ta xauna, can ta kalli wrist dinta sai kuma ta mike ta fita dakin ta tafi can bangarensa da sauri, a hankali ta bude kofar parlon ta shiga ta karasa bedroom da sauri ta isa gaban madubin tana duba bracelet dinta bata gani ba, bin dakin ta shiga yi da kallo bata ga alamarsa, juyawa tayi ta fita ta koma dakinta ta kulle kofa ta kwanta. Da daddare Abuturrab na bedroom dinsa yana operating laptop wayarsa ya fara ring, dauka yyi ganin me kiransa ya katse ya kirata, daga daya bangaren tace "Hi ya Abuu, Grandma want to vid call with u, na kira naga baka online" Yace "Ohk, how about zoom?" Tace "Aa ta WhatsApp dai" katse wayar yyi ya bude datansa ya hau online sannan ya kirata vid call din, Hajja ta hakikance gaban screen da katon eye glass dinta, yyi dariya yace "Ina wuni Hajja" Tace "Aa ba ruwana, meye kuma ina wuni, kai baka kiran mutane sai dai a kiraka kawai don kana matukin jirgin sama, baka da wani bambanci fa da me jan motar haya wllh, naga kamar wani jin kanka kake, ga Saleem kullum sai ya kira Farida ya ga fuskata, haka ma Bashir, ko daxu sai da Bashir ya kira muka ga fuskar juna, to kawai don bana kasar sai kayi watsi da ni, sai kace ba ni nayi wahala da kai ba, ko uwarka ce tace ka fita harkata, don dai har yau bamu san xuciyar matar nan ba" Abuturrab na shafa kansa yana murmushi yace "Ya gidan Hajja" Tace "To lafiya lau, ai naji Baban farida xai taho Nigeria ni dai nace tare xa mu taho don na gaji, babu wani abinci a nan banda gurasar alkama, to ina dalili duk na kanjale na xata wajen arxiki ne ashe ba haka ba, basu da komai sai alkama da madara" Abuturrab yace "Yaushe xa ku taho kenan?" Tace "Aa ni dai kawai ji nayi xai taho, amma ban san yaushe ba" Yace "Toh Allah ya kai mu" Tace "Kana nan kana tukin jirgin har yanxu dai ko? Don duk na sanar ma abokan arxiki da nayi a kasar nan cewar jikana tukin jirgin sama yake, bbu kamarsa duk Nigeria" Abuturrab yyi murmushi kawai, tace "Aa ba batun murmushi ba, ko sun koreka a aikin ne nake nan nake ta tsuga karya?" Yace "Ke fata kike a koreni" kiran Aneesah ne ya shigo wayar, hkn yasa vid call din yyi still, ya daga kiran, daga daya bangaren cike da fara'a Aneesah tace "Guess what My captain?" Ya jawo pillow ya kwanta ya lumshe ido cikin calm voice dinsa yace "I am not a good guesser u know...." 


Hansai ce xaune kan takalmanta da kawarta Zulai da ita ma ta xauna kan takalman nata a karkashin bishiyar wani tsakar gida, Mata ne sun fi talatin a d'an tsakar gidan, ko wacce da hijabinta yarkace yarkace, wasu da goyo wasu da ciki, Hansai tace "Anya Zulai xa mu samu ganin mutumin nan yau kuwa, ni d'an cinikin awaran yau ma nake ji, don wllh Bibalo ba yi xata yi ba ta gwammace in ma kwantai ne awaran yyi, nan gaba fa sai na koma xan fara tuya, ga layi kamar baxa a xo kanmu ba, to ko wacce da matsalarta a kugunta" Zulai ta gyara xama tace "Shi sa nace maki mu fito da sassafe Hansai, amma kika tsaya dafa awara, mutumin nan aiki yake kamar yankan wuka shi sa ake masa layi wllh, idan ba da asuba mutum ya shigo ba sai ya kai magariba ma bai gansa ba, don ma mutumin baya tashi sallah kenan" Hansai tace "Toh ko dai mu je mu dawo goben da asuba Zulai? kinga fa uban layin yaushe aka xo kanmu" Zulai tace "Kin ji ki, mu kashe kudin mota kusan dubu daya kice mu tafi mu dawo Hansai??" Hansai tace "To ni ya xance? Wllh kwantai awarata xata yi yau, Allah ma yasa ta yanyanka min in dai bibalo ce, kinga idan ya so gobe sai in sake xaran dubu daya cikin kudin awaran mu taho" Zulai ta mike tace "Toh shhkn, mu tafi" Mikewa Hansai tayi tana sa6a bak'in gyalenta da duk ya takure suka fito waje tana cewa "Ni dai fatana Allah ya sa na xo gun karshen wahalata" Zulai tace "Ahaf ai fada ma 6ata baki ne wllh, in dai kika saki kudi rass xai maki aiki bbu algus, kina xaune rana tsaka xaki ga Jiddah har gida kamar an korota, wnn ai karamin aiki ne a wajensa, shi fa mutumin nan har haukata mutane ance yana yi" Hansai ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Ae ban san amfanin shegiyar yarinyar ba sai da ta tafi, ashe ita ce rufin asirina ban sani ba, gaskiya idan Allah ya dawo min da ita auren ma wllh baxata yi ba har ta mutu, tun bayan bacewarta har yau banyi cinikin awara da yafi na dubu biyu ba, shi ma da kyar, snn xan ce ma malamin ya sa mata bak'in jini yanda bbu wanda ma xai yi sha'awan aurenta a bar min a bata kawai" Zulai tace "Da dai ya fi wllh, kinga bbu ma saurayin balle yace xai aureta" A haka suka isa bakin titi Hansai tace "Allah dai ya kai mu goben, in sha Allahu komai ya xo min karshe, wahalata ta kare"


Abuturrab na tsaye balcony misalin karfe takwas na safe wayarsa kare a kunnensa yana sauraran wani abokinsa, sai da ya jira abokin ya kai aya snn yace "I thought xa a samu mata ne, in dai ba a samu matan ba kawai a bari, i will think of another alternative" Daga daya bangaren abokin nasa yace "Amma wa kake nema ma lesson teacher din?" Ya xauna saman kujeran dake balcony din yace "Wata daughter na ne" Abokin nasa me suna Farouq yace "Ohk in dai an samu matan i will let u know Capt, kasan maxan ne sun fi juriyan koyarwan" Abuturrab yace "Eh haka ne, nagode da kulawa" Daga haka suka yi sallama, ya koma parlor ya xauna, daukan wayarsa da yyi haske yyi, ya dinga kallon screen din ganin El-Basheer ke kiransa, it's been a while da suka yi magana, duk da shine baya daukan kiran nasa, can dae ya daga ya kai kunne, daga daya bangaren El-Basheer yace "Sai aka yi yaya da baka daga kirana?" Abuturrab ya jinginar da kansa da kujera yace "How are you doing?" El-Basheer yace "Saboda baka da bayanin da xaka min kan auren da kayi ma kanka ne yasa baka picking call dina??" Abuturrab ya gyara xama yace "Babu xancen wannan auren ne yanxu, shi sa ma na samu kwarin gwiwan daga kiran ka" El-Basheer yace "Ohh really? amma few days ago mun yi magana da Ahmad kuma yace min kana gidan ka da matarka...." Abuturrab ya daure fuska yace "Matar da ya aura min?" El-Basheer yace "But wait.... On a serious note Captain don kaje ka yi ma kanka aure babu shawara da kowa shine kake ignoring mutane, why are u avoiding good frnds? mu baxa mu hanaka xama da matarka ba ae no matter who she is" Abuturrab yace "Look Bashir, am serious babu xancen wannan auren yanxu, kasan ni bana karya, i don't have any god-damn wife now.... amma this is just between i nd u don 'yan gida basu sani ba har ynxu" El-Basheer yace "Ban gane ba, sakinta kayi?" Abuturrab yace "Ba sa'ar aurena bace ita ae, kawai tsautsayi ne da kaddara ya fada min" El-Basheer yace "Then why are u still hiding it from people at home in har da gasken ka saketa?" Abuturrab yace "Bcos we are staying under same rood with her har ynxu, and Abba won't take it likely if he finds out na saketa, i think we should change topic now dude...." El-Basheer yace "Anyway... Ina kaduna, turo min address din gidan naka, i will be leaving in two days time in sha Allah" Abuturrab yace "Really? Yaushe ka shigo, kuma me ka xo yi" El-Basheer yace "Forward to me ur address now" Abuturrab ya d'an yi shiru, sae kuma yace "Ohk" daga haka ya katse wayar..... Ya d'an yi jimm, bayan kusan 5 minutes kawai ya tura masa Address din sannan ya mike ya wuce sama, dakin Jiddah ya bude ya ganta tana faman shafa man gashi a dogon gashinta da ya cika ko ina na kanta, atamfa ce jikinta, ta daga kai tana kallonsa, fuskarsa bbu yabo bbu fallasa shi ma yake kallonta, a hankali tace "Ina kwana" yace "Idan da abinda xa ki yi a kasa ki sauka ynxu kiyi, xuwa anjima bana son ganin ki a kasa" Ita dai bata ce komai ba, ya juya ya bar bakin kofar. Mikewa tayi bayan tayi parking gashin ta saka hula ta sauka parlon, xaune ta gansa parlon yana rike da remote, ta sunkuyar da kanta ta wuce kitchen, dankali ta shiga ferewa ta soya da kwai, sannan ta fito kitchen din rike da plate din Irish da egg din, ya bi ta da ido ganin xata wuce sama yace "Ina shayin?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Koma" Ba musu ta juya ta koma kitchen din ta sa ruwan xafi sannan ta hada shayin a cup ta kara fitowa kitchen din, still yana kallonta yace "Wani ruwan kike sha gidan nan?" Tana kallonsa tace "A bandaki nake sha, ko a pampon kitchen" Bude baki yyi yana kallonta with shock, can ya mike yace "Ruwan bandaki?" Sosai gabanta ya fadi ta fara komawa baya, ya lura da hakan gudun kar ta saki ruwan shayin hannunta tunda ya san ba setin kirki gareta ba, calmly yace "Je ki ajiye abun hannunki ki dawo" A sanyaye ta wuce sama bayan ta ajiye plate da cup din ta mike ta fito a sanyaye, lkci daya hawaye ya kawo idonta, tsaye ta gansa har sannan yana jiranta, ta makale jikin stairs bayan ta sauko cikin rawan murya tace "Gani" Juyawa yyi yana kallonta,  ta sunkuyar da kanta da sauri, daga sama har kasa yake kallonta, riga da skirt na atamfa da ya kamata, babu abinda kayan ya boye na surarta, ya rungume hannunsa yace "Daga yau kada ki sake sa atamfa a gidana" Ta d'an kallesa, sae kuma ta kara sunkuyar da kanta, yace "Idan baki son Abayan da nake siyo maki kiyi yawo ba kaya kawai" Ita dai bata dago ba balle tace komai, yace "Sannan kika ce ruwan bandaki kike sha?" Ta marairaice ta girgixa masa kai, strictly yace "What??" Tace "Sae cikin dare ne nake shan na bandaki, amma da safe da rana da yamma na pampon kitchen nake sha" Gani tayi ya nufota ta juya da sauri xata koma sama yace "Allah idan kika motsa daga nan xan maki abinda ban ta6a maki ba, wato xan gaura maki mari" Kuka ta fara yi, tana hawa stairs din da daddaya da daddaya cikin rawan murya tace "Don Allah kayi hakuri" Yana isa ta fasa kara, ta durkushe wajen tace "Kayi hakuri don Allah" Bai karasa kusa da ita ba yace "Shi ruwan fridge din na waye?" Ta boye fuskarta tace "Naka ne" yace "Ni nace maki nawa ne?" Ta girgixa masa kai, yace "Toh daga yau kika sake shan ruwan pampo a gidan nan Allah sae na mareki" Ta gyada masa kai da sauri, yace "Tashi ki bar nan" mikewa tayi da sauri ta haura sama, sae a snn ta juya tana kallonsa a downstairs, yana tsaye yanda ta bar sa, da sauri ta shige dakinta. Bayan azahar El-Basheer ya iso gidan, Abuturrab ya fita ya shigo da shi, Abuturrab ya sakala hannu a kafadar cousin din nasa yana murmushi yace "The prince himself" El-Basheer na murmushi yace "It's been long Captain...."  sosai suke shige da Abuturrab sai dai ya fi Abuturrab din haske, don shi ya fi shige da larabawa wanda hakan ke nuna kilan shi din ruwa biyu ne.... El-Basheer na bin gidan da kallo bayan sun shigo yace "Everything seems perfect, sai dai unfortunately ba Aneesah ta fara shigowa gidan ba...." Abuturrab ya shafa sajensa kmr baxai ce komai ba, sae kuma yace "Kwanan nan xata shigo gidan in sha Allah, bikin Ahmad saura few weeks so, bayan bikinsa sai inyi ma su Abba magana...." El-Basheer ya shiga bin parlon da kallo yace "But wait.... Where is.... I mean the wife u married?" Abuturrab ya hade rai yace "Wacce wife din?" El-Basheer yace "Warce muka ji labarin ka aura ma kanka mana..." Abuturrab yace "Pls hakan na bata min rai wllh, Nace maka she isn't my wife any longer" El-Basheer yace "Yes haka kace, but why not ka sanar ma kowa bbu auren??" Taku suka ji a stairs, Abuturrab ya saci kallon Stairs din da sauri, El-Basheer dai bai juya ba sae kallon Abuturrab yake yana jiran amsan sa Jiddah ta sakko walking slowly ta shigo parlon da ganin kasan a d'an tsorace take, Kallon Abuturrab dake kallonta tayi ganin irin kallon da yake mata ta d'an tsaya ta ki karasowa, El-Basheer ya juya ya kalli inda Abuturrab ke kallo, lkci daya Abuturrab ya mike, ta marairaice tana kallonsa tace "Kai ne kace in daina shan ruwan bandaki, wllh kishi nake ji" Fuska daure yace "Juya ki koma" Juyawa tayi da sauri ta koma sama, Sai a sannan ya koma ya xauna yana kallon El-Basheer da ya bi ta da kallo.....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you





Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems


Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada


Instagram -fareeskinglow_89

TikTok-fareeskinglow

Facebook page-fareeskinglow 

WhatsApp -08031898240

Abuturrab ya dau throw pillow dake gefensa ya jefa ma El-Basheer da ya bi Jiddah da ido, sae a sannan El-Basheer ya dauke idonsa, sai kuma ya daga kafada as if counting his words yace "Ita ce.... Ex-wife din taka?" Abuturrab na kallonsa da wani expression yace "Does that warrant u to stare at her that way??" El-Basheer yyi shiru yana danna wayarsa kamar baxai ce masa komai ba, sai kuma ya kallesa yace "Naga kamar ganinta ya fi jin ta ne, ita ce yar hayin rigasar?" Abuturrab ya masa wani kallo ya dau remote yana canxa channel, El-Basheer yace "Ko dai a gidanka ne ta samu transformation din nan, she's got a beautiful shape" Abuturrab ya mike, sounding fed up yace "Stop this plss El-Basheer... U r sounding lousy" El-Basheer yana shafa gashinsa yace "Lousy? Ohk sorry about that" Abuturrab ya dinga kallonsa da wani expression that is expressing how really angry he is, ya koma ya xauna yana canje canjen channel, El-Basheer ya bi parlor din da kallo yace "I need something cold to take now, haka kake treating visitors?" Mikewa Abuturrab yyi ya wuce kitchen, El-Basheer ya bi sa da kallo, fridge ya bude ya dau bottle water daya sannan ya fito, sama ya wuce yana cewa "In dai ni xan kawo maka ruwa xaka dade baka sha ba" El-Basheer ya bi sa da kallo yana d'an murmushi, can ya girgixa kai, bude kofar dakin Jiddah Abuturrab yayi ya shiga.... xaune ya ganta ta takure waje daya, tana ganinsa ta gyara xamanta tayi narai narai da ido tana kallonsa, ya ajiye ruwan gaban mirror ya juyo fuska a tamke yace "Me nace maki daxu?" Shiru tayi, yace "Ba ce maki nayi kar ki fito ba all through?" Hawaye ya cika idonta tace "Ruwa ai naje in dauka, ba ce min kayi in daina shan na bandaki ba" Yace "Me ya hanaki dauka daxu da kika sakko" shiru tayi bata ce komai ba, yace "Xo ki dauka" mikewa tayi ta tafi gun madubin ta dau goran ruwa, yana kallonta yace "Sannan ba nace kada ki sake sa irin kayan nan a gidan nan ba?" Ta kallesa tace "Ai daxu ka gaya min, ina ce daga yau kace.." Bai kuma cewa komai ba ta koma inda take ta bude ruwan, sai da ta sha ruwan sannan ya juya ya fita dakin, tsaye ya ga El-Basheer a parlor hannunsa rike da kwalin lemon chivita yana sha, Abuturrab ya xauna yace "What will u be taking for lunch?" Xaunawa El-Basheer yayi yace "Naaah...  I'm full, i just need rest" Abuturrab yace "Okay mu je sama" Mikewa yayi ya fara tafiya sama, El-Basheer ya mike ya bi bayansa rike da lemonsa, Abuturrab ya kai sa part dinsa, xaunawa El-Basheer yayi gefen gado cikin bedroom din bayan ya rufe lemon hannunsa ya ajiye yace "Tsarin gidan yayi sosai, the Architecture is really good" yana fadin haka ya kwanta, Abuturrab dai na tsaye gaban madubi yana kallonsa ta madubin, can dai yace "Xan je in dawo yanxu!!!" El-Basheer ya dago yace "Ina xa ka?" Yace "To get lunch" daga haka ya nufi kofa ya fita, yana isa kofar Jiddah ya bude, ya d'an hade rai yace "Dauko Jilbab dinki, ki sameni waje" Daga haka ya wuce, yana cikin mota Jiddah ta fito da Hijab har kasa, sai da ta shiga gaban motar sannan yayi horn, mai gadi ya hau bude gate din, jan motar yayi suka fita gidan, wani babban eatry ya tafi, ya siya ma shi da El-Basheer fried rice and chicken, Jiddah dae na xaune kan kujeran da ya nuna mata cikin eatry din, sai bin mutanen wajen take da kallo, baka ta6a cewa tare suke da Abuturrab don bai ko sake kallon inda take ba, wani mutumi ne ta ga ya ja daya daga kujeran table din da take ya xauna, ya daga face cap dinsa yana kallonta, ta saci kallon Abuturrab da ke xaune wani table can yana jiran order din da yayi, ta sake kallon mutumin, ya sakar mata murmushinsa me kyau, ta sunkuyar da kanta da sauri, yace "Hello, how are u doing, are u waiting for ur order?" Ta saci kallon Abuturrab taga kallon direction dinsu yake ko kiftawa babu, sosai gabanta ya fadi, cikin rawan murya tace "Yayana na nan fa" Mutumin ya bi eatry din da kallo, kawai gani yayi Abuturrab ya nufosu, ita dai gabanta sai faduwa yake, Abuturrab na isowa yana kallon mutumin babu yabo babu fallasa yace "Didn't she tell u she is married?" Mutumin ya mike yace "Ooh i am sorry plss" Abuturrab bai tankasa ba ya ja wani kujeran ya xauna facing her directly, mutumin ya kara basa hakuri, nan ma yaki amsawa har mutumin ya bar wajen, Jiddah ta saci kallonsa suka hada ido, ya jefa mata wani kallo yace "Ko tausayin rayuwarki baki ji har xaki fara kula maxa ko?" A hankali tace "Ni bani na kirasa ba kawai xuwa yayi" Yace "Toh bari kiji har sai kin gama jami'a kin fara aiki, kafin ki kalli ko wani namiji balle har ki kulasa" Ta gyada masa kai kawai, ya ci gaba da danna wayarsa har aka kawo masa order da yyi a takeaway, without looking at her yace "Me xa ki ci?" ta sunkuyar da kanta tace "Ko meye" tsaki yyi ya mike ya bar wajen, jollof rice yayi mata order da kazar ita ma sannan suka bar eatry din, tana rike da ledan nata ta wuce dakinta bayan sun isa gida, Abuturrab na shiga bedroom dinsa ya tadda El-Basheer a kwance yanda ya bar sa idonsa lumshe, parlonsa ya koma ya xauna. 


Bayan la'asar Abuturrab ya sauko downstairs ya samu El-Basheer dake xaune yana jiransa, El-Basheer yace "Plss idan baxa kaje ba ni in tafi mana, i have many places to go yau din nan, i will be leaving probably tomorrow in sha Allah" Abuturrab ya mika masa wayar hannunsa yace "Aneesah..." amsar wayar El-Basheer yyi ya kai kunne, Abuturrab ya ajiye makullin motarsa sannan ya koma sama, El-Basheer ya amsa gaisuwar Aneesah yace "Ya kwana biyu?" Aneesah tace "Alhmdlh, he is just telling me kuna tare yanxu" El-Basheer ya d'an yi murmushi yace "Yea daxu na shigo kaduna and am at his resident now" tace "Oh ohk, ya su Ummi?" Yace "Ban je ba" Aneesah tace "Ayya, to ya garin?" El-Basheer yace "Cool, i have a question for you Aneesah, nasan baxa ki boye min ba" kafin ta ce komai yace "Tell me.... is Aliyu saying the truth na cewar ya saki yarinyar nan??" Aneesah ta yi shiru da fari, can kuma cike da confusion tace "Yarinya? Wacce yarinyar? Kuma sakin me?" Shiru El-Basheer yyi, can yace "Ohk then, i will pick a call right away...." Daga haka ya katse wayar ganin from all indication she knows nothing about what he is saying now, sake kira tayi ya ajiye wayar gefensa ya jingina da kujera, Abuturrab na tsaye dakin Jiddah dake rakube jikin gado, yana kallonta strictly yake cewa "In har muka shigo gidan nan kika wani sakko wai xaki dau wani abu xaki sha mamaki na, duk abinda xa kiyi kiyi ki gama yanxu kafin mu dawo" ta gyada masa kai kawai, kamar wanda ya tuna abu ya juya da sauri yana kallon kofa, lkci daya ya fice daga dakin ya sauka downstairs yana kallon El-Basheer da manyan idanuwansa yace "Hope... Hope you didn't say anything apart from greeting to Aneesah???" El-Basheer yace "Of course baka ce min haka ba, na tambayeta ko gaskiya ne ka saki yarinyar nan kamar yanda ka fada, and from d way she sounds, bata san komai kan maganar ba ma" Abuturrab ya xaro ido yace "Ohh my God... Me yasa xaka yi mata wannan maganan El-Basheer?? We are still hiding it from her" Mikewa El-Basheer yyi ya dau makullin motar Abuturrab yace "Ni kace min bata sani bane, ga ta nan tana ta kira, pick and find what to say to her" daga haka ya nufi kofa ya fita, Abuturrab ya bi sa da kallo xuciyarsa na tafarfasa. Daukar wayarsa yyi yaga calls din Aneesah har biyar yayi silencing wayar ya bi bayan El-Basheer.... Bangaren Aunty suka fara shiga suka gaisheta bayan sun isa gidan, Aunty na kallon El-Basheer tace "Har ka iya xuwa wai gidansa El-Basheer, ni fa na tattare lamarin Abuturrab na watsar a gefe, i see no reason da xai dinga boye boyen cewar ya saki yarinyar nan, ko meye fa'idan xama gida daya da ita bayan ya saketa, who is he deceiving?? To wllh I've made up my mind cewar Abbansa na dawowa sati me xuwa xan sanar masa komai, wannan ae iskanci ne, to ko minti biyar ba ayi da muka gama waya da mahaifiyar Aneesah ba, labari ya je masu, kana tunanin xaka iya ci gaba da boye masu ne dama?? Wllh yanxu haka duk hankalina a tashe yake, nayi kokarin fahimtar da su ba auren amma ya faskara...." Kallonta kawai Abuturrab yake yi, shi na Aneesan ma bai damesa ba kamar na Abba da tace xata sanar ma ya saki Jiddah kuma yana xaune tare da ita, gaba daya yaji hankalinsa yyi mugun tashi, Waje ya nema ya xauna jin har kansa ya fara juya masa, El-Basheer yace "Ni banga abun boye boye a nan ba, let this be known to everyone that she is no longer ur wife, kana xaune gida daya da macen da ba muharramarka ba, who does that??" Abuturrab ya kalli Aunty da ta ci gaba da abinda take bbu fara'a fuskarta, yyi kasa da murya yace "Amma Aunty kinsan Abba won't be happy idan yaji na saketa, he will be highly disappointed at me, kuma ni sbda bana son bacin ranki ya sa na saketa wllh, idan kika gaya ma Abba cewar nayi hakan yanxu he won't take it likely with me, i am just confuse Aunty" Aunty ta juyo a fusace tace "Ni kuma dole in sanar masa duk abinda xae faru ya faru ba, are u this happy being with the girl da yasa ka daina dawowa weekend gidan nan sae dai ka sauka gidanka ka karashi weekend dinka ka wuce, haka xaman naka da ita yayi dadi duk da ba matarka bace ashe?? To kuwa xaka sha mamakina kuwa wllh" Ya girgixa kai yace "Aunty ni weekend din ma gaba daya na daina dawowa fa, Jiya ne kawai na dawo sbda El-Basheer yace min yana hanya" Aunty tace "Wato ita kadae ke yanda ta so a katon gidan? Ka sakar mata babban gida haka ta ci karenta ba babbaka, to baxai yiwu ba ne wllh" Shiru yyi bai ce komai ba, Aunty tace "Don kuwa da ta ci gaba da xaman gidan nan naka gwara ka dawo da ita nan, dama mai aiki xata tafi garinsu jibi, kaga ba wani xai ce ta bar nan gidan ba wataran..." Kallonta kawai Abuturrab ke yi gabansa na bugawa, tayi masa tsawa tace "Kallon ne amsan ka? Ko baxa kayi abinda nace bane??" Ya girgixa kai yace "Aunty can din ma ina assuring dinki ba sae wani yace ta tafi ba xata tafi, wllh ita kadai ce bbu kowa" Aunty ta kara masa wani tsawa tace "Nace ka dawo da ita gidan nan, ko ban isa ba??" Ya sunkuyar da kansa lkci daya jikinsa yyi sanyi, can ya kalleta cikin sanyi yace "Toh" Sannan ya mike ya nufi kofa ta bi sa da harara tana huci, El-Basheer ya d'an yi murmushi yace "But how can a normal human being do what Abuturrab did?" Cike da bacin rai Aunty tace "Atoh... Isn't this irritating Bash?? Wllh da lamarin nan nake kwana nake tashi a raina, ya ce ya saketa quite alright he did that, na sani, to kuma xaman me suke tare idan anyi magana yace Abbansa, ance masa da Abban nasa ya san ya saketa xae barsa ya ci gaba da xama gida daya da ita, ga yarinyar ido a bude, to xaman iskanci yake son fara yi da ita ko me, don dai shi ma ba saiti garesa ba kuma ba jin magana yake ba, ka sani, na sani, shi yasa bai dauki xaman da yake under same roof with her wani abu ba" El-Basheer ya mike yace "Allah ya kyauta" daga haka ya fita. Ko bangaren Ummi Abuturrab bai shiga ba ya fice daga gidan ya shiga motarsa ya jinginar da kansa da kujera yana jiran El-Basheer, dalilin da yasa bai son xuwa gidan kenan idan ya dawo weekend, ganin har bayan minti sha biyar El-Basheer bai fito ba Abuturrab yyi dialing numbersa, El-Basheer na dagawa, a fusace yace "Inyi tafiyata ne?" El-Basheer yyi murmushi ya katse wayar, kallon wayar Abuturrab ya dinga yi, sai ga text ya shigo masa, bude content din yyi, "C'mon wani irin gaisuwa kake son inyi ma Ummi, gaisuwan minti goma? Tunda kai kaki shigowa gaisheta ni baxan iya ba" Abuturrab ya mayar masa reply yace "Ka sameni a gida then" daga haka ya ajiye wayar ya tada motarsa ya bar anguwar. Yana parking ya shiga parlor ya xauna kujera ya jinginar da kansa ya lumshe ido yana jin ransa ba dadi, text ne ya shigo wayarsa ya bude ido a hankali ganin Aneesah ce tayi text din ya bude content din, "Abinda ka min was the least i expected from you Aliyu, ban yi xaton haka ko a mafarki ba, amma ka sani ka cuceni, ka ci amanata, ka yaudareni, ka ruguza min rayuwa, i gave u all my trust but u ended up betraying me, why Aliyu, did i deserve this harsh treatment from you?" Ko gama karanta text din bai yi ba yayi mata reply kamar haka "Since you never expect this from me... Then u consider me... Aure kuma sai idan kece kika ce baxa kiyi da ni ba, as for me you will be my first and last wife in sha Allah....  i will call u in 5 hours time in sha Allah" daga haka ya tura mata text din ya ajiye wayar ya mike ya wuce sama. Har bayan Magrib El-Basheer bai shigo gidan ba, hakan ya sa Abuturrab yyi dialing number sa, yana fara ring El-Basheer ya daga yace "Gobe xan shigo before leaving, Ummi tace i should spend the night here" Abuturrab yace "Ohk" daga haka ya katse wayar. Mikewa yyi ya wuce sama ya bude kofar dakin Jiddah, tun da ya dawo ko motsinta bai ji ba, tana xaune gaban mirror tana ma gashinta kitson kalaba, ganinsa ta dau hulanta ta saka, yana tsaye bakin kofa yace "Meye hakan kike yi?" Tace "Aa ina kitson gashin ne, yana karyewa idan ban yi kitso ba" Yace "Sai anyi kitson ne baxai karye ba?" Ta gyada masa kai, yace "Toh kwance wannan abinda kika yi, tunda a garinku ne aka ce maki xai karye idan ba ayi kitso ba, a tsefe xaki bar gashin, haka nake so" Ta kallesa da sauri, that was when he realized what he just said, lkci daya ya hade rai yace "Ko kina ganin kitso a gashin su Ramlah, mu a nan ba a kitso" Cikin sanyin murya tace "Toh" ta fara tsife dogon gashin nata da ta kitsa, har ta gama tsefe daya bata ji ya tafi ba, hakan yasa ta leko sa ta cikin gashinta da ya rufe mata fuskarta gaba daya, suna hada ido ya juya ya fita dakin. Ana kiran isha ta gama parking din dogon gashin nata ta kitse jelan sannan ta sa hularta. Karfe tara saura wayar da Abuturrab ya bata ya fara ring a gaban madubi, karasawa tayi ta dauka tana kallon number jikin screen din sannan tayi picking ta kai kunne, muryarsa taji yace "Ina jiranki a parlor" Daga haka ya katse wayar, ajiye wayar tayi ta sa Hijab dinta ta fita, shi kadae ne xaune parlon ta durkusa jikin kujera a hankali tace "Gani" Yace "Me kika ci?" Ta sunkuyar da kanta tace "Taliya na dafa" ya nuna mata ledan dake gefensa yace "dauka" mikewa tayi ta isa kusa da shi ta duka ta dau ledan, ya rike numfashinsa sbda wani kamshi na daban da ya doki hancinsa, ganin kwalin lemo a cikin ledan ta cire xata ajiye, ya saki breath dinsa ya hade rai yace "Har da shi xa ki tafi" Innocently tace "Ban iya sha ba" Yace "Haka xa ki je ki koyi sha yau, tunda ke yar kauye ce" Bata ce komai ba ta mayar da kwalin cikin ledan sannan ta mike ta nufi stairs, bin ta yyi da kallo tana isa stairs ta juyo suka hada ido, da sauri ya dauke idonsa, tace "Nagode" sannan ta wuce sama, jinginar da kansa yayi a hankali da kujera yana jin damuwa iri iri a ransa, gasasshiyar kaza ce da yaji Jiddah ta bude a dakinta, sai kamshi kazan yake, ta kalli kwalin hollandia din sannan ta bude ta d'an sha kadan, ji tayi yayi mata dadi a baki sbda gardinsa, ta lumshe ido ta kara sha sannan ta ajiye ta fara cin naman a hankali, lkci daya rayuwar da tayi a gidansu ya fado mata, tura kazan tayi tuna Babarsu da tayi.

 Abuturrab na kwance wajajen sha daya a parlor, waya na kare kunnensa, he felt relieved bayan yayi convincing Aneesah a kan kaddara ce ya sa shi auren jiddah sannan kuma bashi da aurenta a kansa yanxu, daga daya bangaren cikin sanyin murya tace "Amma why is she still at ur resident My captain??" Yace "Ina kike son in kai ta yanxu?" Tace "Ni ko gidanmu ma ka kawota su Mummy baxa su ce Aa ba wllh, ni nasan karyar da xan masu, ka barta ta dawo gidanmu plss" Bai san lkcn da yyi wani murmushi ba, a hankali yace "Koh?" Ta marairaice tace "Sure dear" yace "I will think about that, xuwa nan da short period of time" tace "Do so fast plss Captain" daga kai yyi jin footstep a stairs, lkci daya yace "I call you in some minutes time" bai jira cewarta ba ya katse wayar, yayi kasa da idonsa kamar me bacci, A hankali Jiddah ke tafiya duk xatonta bacci yake hannunta rike da ledan kazan da ko yanka uku bata ci ba, to bata saba da shi ba shi yasa bata iya ci sosai ba, drink din ne ma ta d'an sha ba laifi, kitchen ta tafi ta ajiye ledan kazan a fridge ta ajiye lemon ma sannan ta fito, a hankali take tafiyar ta nufi stairs ya bi ta da kallo, nighty ne jikinta wanda ya wuce kneels dinta da hularta a kanta, sai da ta isa stairs ta juyo ta kallesa suka hada ido, sosai ta tsorata, yyi saurin mikewa xaune pretending to be awake at that moment yace "Me kike yi a nan" ta nuna masa kitchen tace "Na kai abu na ajiye" yace "Je ki dauko abinda kika ajiye" Tayi narai narai da ido ta ki motsawa daga inda take, ya hade rai yace "Baki ji abinda nace ba?" Da gudu ta wuce sama, ya mike tsaye da mamaki yana bin ta da kallo, har ta shige dakinta.



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems


Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada


Instagram -fareeskinglow_89

TikTok-fareeskinglow

Facebook page-fareeskinglow 

WhatsApp -08031898240

Washegari da safe Abuturrab ya sauko downstairs wajajen karfe takwas, jin motsi a kitchen ya fasa shiga kitchen din ya xauna parlor, bayan kusan minti ashirin Jiddah ta fito, tana ganinsa ta yi kasa da kanta kamar munafuka, ta nufi jikin kujera ta durkusa, a hankali tace "Ina kwana?" hararanta yake, taki yarda ta hada ido da shi ta mike tayi wucewarta sama, sae a sannan ya tashi ya wuce kitchen din, wanke wanke ya ga tayi ta goge ko ina na kitchen din, fridge ya bude ya dau apple uku ya dau karamin plate ya daura a kai sannan ya fita ya koma ya xauna yana cin apple din yana danna wayar sa, danna bell aka yi, ya kalli kofar da mamaki, can ya mike ya nufi kofar ya bude, ido hudu yayi da Aunty a tsaye ta hade girar sama da ta kasa, gabansa ya fadi sosai, ya kalli El-Basheer da ya xauna saman kujeran dake balcony din ya daura kafa daya kan daya, bangajesa Aunty tayi ta shiga parlon, ya bi ta da ido sannan ya kalli El-Basheer fuska daure, mikewa El-Basheer yyi yace "She only said in rakata anguwa, and i never knew nan xata xo" Wani kallo Abuturrab yyi masa ya juya ya koma cikin parlon, tsaye ya tadda Aunty fuskar nan nata babu alamar wasa, yyi kasa da kai da ladabi yace "Ina kwana Aunty?" tace "Ban kwana ba Aliyu, ina yarinyar take?" Yyi kasa da murya yace "Aunty dama ai anjima kika ce in kai ta can gidan ko" Cikin tsawa tace "Ta fito yanxu mu wuce, na hutassheka ba sai ka kai ta ba" a hankali yace "Toh" Daga haka ya fara wucewa sama, ta bi sa da harara tana girgixa kafa, sai da ya haura sama ya d'an juyo ya kalleta ganin bata ganinsa, ya nufi dakin Jiddah da sauri, Tana gyaran gado ya shigo, ta mike tana kallonsa, ya hade rai yace "Mu je" Tana kallonsa tace "Ina?" Fixgo hannunta yyi ta xaro ido tana kallonsa har suka fita dakin, ganin bangarensa ya nufa taki ci gaba da tafiyar tace "Me xanyi..." wani kallo ya jefa mata, hakan yasa ta ci gaba da tafiyar, parlonsa ya kai ta, ya bude kofar balcony yana kallonta yace "Shiga" da mamaki tace "Saboda me" shigar da ita balcony din yyi yana kallonta da kyau yace "Idan kuma so kike Auntyna ta tafi dake sai ki 6ara baki kiyi kuka har ta ji ki" Daga haka ya kulle kofar, ya sa makullin a aljihunsa, ya fita parlon a stairs ya hadu da Aunty, tace "Ta kasa sakkowa ne har yanxu xaka shanya ni a parlor" With confusion yace "Aunty I don't know, na duba dakin da take ban ganta ba, amma jiya Maimoon ta xo, ban san ko...." Wani tsawa tayi masa tace "Ni xaka raina ma wayo Aliyu?? Xuwa kayi ka boyeta?" Ya marairaice yace "Boyeta kuma Aunty, a ina xan boyeta ki shiga duk inda xaki shiga ki duba, ni fa jiya sai kusan sha biyu na dawo gidan nan, i don't know ko sun tafi tare da Maimoon, and tunda gari ya waye ban fito ba sai ynxu da ku ka xo" Bangajesa tayi ta nufi saman, dakin Jiddah ta fara budewa, hankalinta yyi mugun tashi ganin dakin kamar na amarya ga gaban mirror taff da kaya masu tsada, ta bude press, nan ma taga uban kaya, shi dai yana tsaye yana kallonta, ta juya tana kallonsa... Da sauri yace "Ko biyar dina babu a nan Aunty, Umma ce da Abba da uncles dina duk suka yi wannan siyayyan, ki tambayi Ummi ma" har bathroom sai da ta bude bata ga Jiddah ba, Juyawa tayi ta fita ta shiga sauran dakunan nan ma bata ga alamarta ba, fita tayi ta tafi bangarensa, iya dubanta bata ga Jiddah ba, kofar Balcony din ta murda, Abuturrab dake tsaye bakin kofa duk yana kallonta, yyi kasa da murya yace "I can't find the key to that place, balcony ne ai kin sani" Da ido ya bi ta har ta fita parlonsa, snn ya bi bayanta, Jiddah dai na tsaye balcony din, lkci lkci take satan kallon mutumin dake xaune a daya building din, da ta saci kallonsa kuma sai su hada ido, daga karshe ta canxa position dinta, sai bayan minti talatin Aunty ta bar gidan bayan ta ta66atar da gaske Jiddah bata nan, don ta duba ko ina, Ba tare ta koma da El-Basheer ba bayan ta amshi makullin mota tayi wucewarta, Ko kallon El-Basheer Abuturrab bai yi ba ya shige parlor, mikewa El-Basheer yyi ya bi bayansa, Abuturrab ya xauna saman kujera, El-Basheer ya xauna yana facing dinsa yace "Now tell me d truth, Ina yarinyar take?" Abuturrab yace "You encouraged Aunty to my house right?" El-Basheer yace "Not at all, bata ma ce min nan xata xo ba, sannan me yasa baxa ka bari ta koma gidan naku ba tunda ba matarka bace, or ka kaita bauchi" Abuturrab yace "Ohkk, saboda duk banyi niyya ba" El-Basheer ya shafa kansa sannan ya mike yace "Ohk then, anjima xan koma Bauchi in sha Allah" Abuturrab yace "Allah ya tsare" Kofa El-Basheer ya nufa, Abuturrab ya bi sa da kallon gefen ido har ya fita sannan ya tashi ya kulle kofar parlon da makulli ya wuce sama xuwa part dinsa, ya ciro makullin a aljihunsa ya bude kofar, daga kai tayi suka hada ido, ganin taki motsawa yace "Baxa ki fito ba" bata ce komai ba ta bi ta gefensa ta shigo parlon ya kulle kofar.....


 Karfe biyu saura Jiddah ta sauko parlor sbda yunwan da taji take ji, tun bayan tafiyar su Aunty Abuturrab ya sa ma gidan makulli ya koma parlon bangarensa, wayarsa dake saman center table ne ta ji yana vibrate, kallon wayar ta dinga yi sannan ta karasa ta duka ta dauka tana kallon screen din, Cikin few seconds tayi kokarin hade rubutun screen din wayar, "Blossom" katsewa kiran yyi aka sake kira, kamar ance ta juya suka yi ido hudu da shi a tsaye ya rungume hannu yana kallonta, daburcewa tayi xata mayar da wayar ta ajiye masa nan bakin center table din ya fado kasa, ta mike a tsorace tace "Dama kiran ka ake" karasowa yyi ya dau wayar fuskarsa daure yana duba screen din, juyawa tayi da sauri xata bar wajen yace "Tsaya nan..." Tsayawa tayi amma ta ki kallonsa, Sternly yace "Baki da hankali ne?? Ba na hanaki ma shigowa parlon nan idan ina nan ba? Ko don kinga ina kyale ki??" Tayi narai narai da ido tace "Kitchen xanje sai naji wayar na kara" Tsawa yayi mata yace "Ina ruwanki da wayar? Ko ke kika ajiye min a nan?" Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, on a serious note without bothering ko ta gane turancin nasa ko bata gane ba yace "Naga kina neman fara wuce boundaries din ki a gidan nan, to bari kiji, daga yau, i mean daga yanxu da kike tsaye nan kada ki sake shigo min parlor idan ina gidan nan, idan kin tashi da asuba kafin in fito da safe dama ki girka duk abinda xaki girka na safe da rana ki kai dakin ki, karfe biyar na yamma ina sama, sai kiyi amfani da wannan opportunity din ki sakko ki dafa abinda xa ki ci da daddare, kafin shidda ki tabbatar kina dakin ki.... Am i clear?" Ita dai kanta na kasa, ya mata wani tsawa yace  "Baki ji na ne?" Ta dago kanta hawaye cike idonta tace "Toh" Yace "Get out.. Tafi ki ban waje" Juyawa tayi a hankali ta wuce sama, ya xauna yana sake kallon wayar tasa da screen ya tsage. Abuturrab bai yi mamakim k'in daga kiransa da El-Basheer yyi ba, don ya kirasa ya fi sau biyu yaki dauka, Da yammacin ranan Abuturrab na operating laptop dinsa a parlor aka danna bell, wani faduwa gabansa yyi ya mike yana kallon kofar, bayan few seconds ya isa kofar yace "Who is there?" Muryar Umma yaji tace "Ni ce" Ya d'an buda ido da mamaki sai kuma ya bude kofar, lkci daya kuma yyi pretending as if he wasn't even surprise yana murmushi ya bata hanya, yana shafa kansa yace "Welcome Umma, sannu da xuwa" Ta shigo parlon tace "Unexpected visit... Ban ce xan xo ba ko?" Yace "Ai ba sai kin ce min ba Umma, ya hanya?" Ta xauna saman kujera tace "Alhmdlh, ina jiddar?" Ya d'an kalli sama sannan yace "Tana sama" daga haka ya wuce sama, calmly ya bude kofar dakinta, xaune ya ganta can karshen gado ta takure waje daya, tana ganinsa ta sauke kafarta ba tare da ta yarda ta sake kallonsa ba, kallon idanuwanta da suka yi ja yyi, kana ganinta kasan kuka tayi sosai, ya hade rai yace "Wani abu aka maki da kika xauna kike kuka?" Ta girgixa masa kai kawai, ya dinga mata wani kallo kafin yace "Tashi ki wuce bandaki ki wanke fuskarki ynxu" sauka tayi daga kan gadon ta shiga bathroom tayi yanda yace, yana tsaye dakin har ta fito yace "Dauka Hijab din ki" Ba musu ta dau hijab din ta saka, yana son mata warning ko da umma xata yi mata wani tambaya ta bata positive answers but ya fasa sanin cewar baxa ma ta ce da umman komai ba, kofa ya nuna mata alamar ta fita, ta fita dakin ya bi bayanta, wuce ta yayi, ya riga ta sauka downstairs, Yana kallon Umma da murmushi fuskarsa bayan Jiddah ta sakko parlon yace "Daxu take kuka umma wai in kai ta wajen ki, but yau xa mu wuce kano and ina wani aikin shi yasa ban kai ta ba" Umma dai bata ce masa komai ba sai kallon Jiddah da ta nufo ta tana murmushi a sanyaye tayi, dukawa tayi kusa da ita a hankali tace "Umma sannu da xuwa" Umma na kallonta tace "Me ya sami idonki?" Abuturrab yace "Kuka tayi, wai in kai ta can gida wajen ku, nace ba yau ba" Still Umma bata kallesa ba, Jiddah dai kanta na kasa tana wasa da fingers dinta, Umma tace "Toh je ki dauko abinda xaki dauka mu wuce yanxu" Abuturrab ya bude ido da sauri yace "Umma ta fara karatu fa" Daga kasa Umma ta kallesa har sama sannan tace "Is that so?" Ya sunkuyar da kansa yace "Eh Umma, tare xa mu koma kano da ita" Lkci daya hawaye ya kawo idon Jiddah tana kallonsa, Umma tace "Toh shkkn, Allah ya taimaka, dama anguwan na shigo shine nace bari in karaso mu gaisa, i will take my leave now, tunda na same ku lafiya Alhmdlh" Yace "Umma da wuri haka, ki bari after magrib...." Ta katse sa tace "Ohk da magariban xa ku dau hanyan kanon kenan?" Shiru yayi bai ce komai ba, ta mike tana kallon Jiddah tace "Toh xan koma jiddah" Kasa dago kai Jiddah tayi, Abuturrab yace "Toh mun gode Umma, Allah ya kara girma" Jiddah ta share idonta a hankali tace "Sai anjima Umma" Duk da tausayinta da Umma ta ji sosai amma sai bata wani nuna ba ta nufi kofa tace "In dai xan xo ki dinga kuka gwara kar in sake xuwa, kusan sati biyu ai ya kamata ki sake haka ko..." Jiddah ta bi ta da kallo hawaye na sauka idonta, wani kallo Abuturrab yyi mata sannan ya bi bayan Umma, Umma bata wani sauraresa ba har ta hau motar ta ta wuce, ya shafa kansa ya bi motar da kallo, juyawa yayi ya koma cikin compound din, bai tadda Jiddah a parlon ba, hakan ya sa ya wuce sama ya bude kofar dakinta ya shiga yaga bata ciki, shesshekar kukanta ya ji a bandaki, ya karasa kofar ya murda yaji ta kulle da makulli, ya hade rai yana knocking kofar yace "Ohh har kuka kika samu damar yi kenan, toh bude kofar kar ki bari in bude da kaina" Kin bude kofar tayi ta kara rushewa da kuka kamar an aikota, bude baki yyi da mamaki, duk yanda yayi Jiddah ta bude kofar kin budewa tayi, har dai ya dawo kwantar da murya amma kamar yana dada tunxurata, banda kuka babu abinda take, kallon agogo dake nuna shiddah da few minutes yayi ya xauna gefen gado yayi wani sigh, a ranan ya ke son komawa kano but he just can't go like that.... spare key din bandakin ne ya fado masa ya mike da sauri ya fita xuwa bangarensa, sai bayan da ya dauko ya koma dakin ya fara addu'an Allah yasa ta cire makullin daga jikin kofar, yana sa makullin kuwa ya ki budewa alamar makulli na jiki, rungume hannunsa yayi yace "Baxa ki bude kofar ba malama, kin san kina bata min lkci kano xan wuce?" Bai ji alamar xata bude kofar ba, but kukan nata da ya daina ji yasa yaji hankalinsa ya tashi bayan ya tuna da vow din da tayi kwanki wai xata kashe kanta, ya ga fa kamar ba seti gareta ba, ya kwantar da murya yace "Jeeddarh..." Nan ma bata amsa ba, rasa abinda xai yi yyi, a haka har aka kira magrib, hankalinsa ba a kwance ba ya tafi yyi alwala a parlor sannan ya wuce masallaci, ana idar da sllh da ya shigo gida dakinta ya kara shiga, har lkcn tana cikin bandakin, jingina yayi da kofar a hankali yace "Jeeddarh" bata tanka sa ba, hakan yasa yace "Ohk to ki gaya min me kike so, ni kuma xan maki" Jiddah dake durkushe jikin kofar ita ma, ta daga kai a hankali jin abinda yace, ya kara kwantar da murya yace "Kin ji?" Tana goge idonta tace "Gidanmu nake son in koma" Buda ido yyi da mamaki jin abinda tace, yace "Wani gidan naku?" Tace "In da ka gan ni mana" Rungume hannunsa yyi, bai san lkcn da yayi murmushi ba yace "Can hayin rigasa?" Tace "Ehh" yace "Kin tabbatar?" Hawaye ya silalo idonta tace "Ehh" Yace "Tohh shkkn bude kofar, sai mu tafi" Tana goge idonta tace "Ni ban yarda ba" Yace "Kinga ina karya? Da gaske nake xan kai ki, ba dai har kin gaji da xaman gidan nan ba" Tace "Ehh, na gaji... Wajen Baabarmu xan koma" yace "Toh bude kofar, dare na yi" mikewa tayi a hankali ta bude kofar, ya koma gefe yana jiran ta fito, tana fitowa suka yi ido hudu da sauri ta sunkuyar da kanta, ta wani sha kunu, har hakan ya so bashi dariya, yace "Toh hada kayan na ki" Kallon jakan da Umma ta bata tayi sannan ta nufi gun jakar, yana kallonta ta fara hada kaya, har ta gama ta daga jakar sama, yace "Ina ma kika ce in kai ki?" Tace "Gidanmu nace" yace "Toh tafi parlor da jakar ki jirani" Jan trolley din ta fara yi ta nufi kofa ya bi ta da ido har ta fita sannan shi ma ya fita ya tafi bangarensa, Jiddah na parlor ta xauna kasa tana jiransa, banda wasa da yatsunta babu abinda take har ya sakko rike da makullin motarsa, ba tare da ya kalleta ba yace "Mu je" mikewa tayi tana jan trolley din ta bi bayansa, bakin motarsa ta tsaya ganin ya bude Booth ta saka trolley din a ciki, sannan ta tafi ta bude gaban motar ta shiga, ya tada motar suka bar gidan. Tun jiddah na kalle kallen hanya ko xata ga sun shigo titin anguwar tasu har ta fara ganin daji babu alaman gidaje, driving kawai yake da speed amma kuma da nutsuwa, marairaicewa tayi ganin kamar sun fita gari tace "Ina xa mu je?" Ko tanka ta bai yi ba hakan yasa bata sake ce masa komai ba, sai hawaye, duk da baccin da ta dinga ji har suka shigo garin kano wajajen karfe sha daya bata yi baccin ba, hotel din da ya ke sauka ya tafi yayi lodging yayi ordering abinci, bin sa kawai take yana tafiya har suka isa dakin da aka basa, tana shiga dakin ta jingina da bango ya kulle kofar ta dinga bin dakin da kallo, ya ajiye makullin motarsa da wayoyinsa gefen gado ya shiga bandaki ya dauro alwala ya fito, ita dai tana ta tsaye, ya shimfida darduma yayi sllhn isha, bayan ya idar da sllh aka yi knocking kofar, mikewa yayi ya isa kofar ya bude, ya amshi abincin da aka kawo sannan ya kulle kofar, shayi ya sha, sai pepper soup din hanta bai bude takeaway din shinkafar ba ya mike ya dau wayarsa yayi dialing number Aneesah don tun yana hanya take ta kiransa, fita yyi dakin ya kulle daga waje, Jiddah ta bi sa da kallo, xaunawa kasa tayi hawaye na taruwa idonta bayan kusan minti sha biyar ta mike ta shiga bandakin ta dauro alwala ta fito tayi magrib da isha, kwanciya tayi kan darduman nan da nan bacci ya dauketa. Karfe sha biyu da mintuna Abuturrab ya shigo dakin abincin ya fara dubawa ko ta ci ya ga bata ci ba, ya xauna gefen gado ya sa hannu ya buga gefen kafarta bude ido tayi ganinsa ta mike xaune da sauri, babu yabo bbu fallasa yace "Dauki abincin ki ci" Tace "Ni na koshi" wani kallo ya mata, ta jawo abincin ta bude ta fara turawa, bai takurata sai ta ci da yawa ba, bayan ta rufe sauran yace "Tafi ki wanke bakin ki kiyi wanka" Bata iya ta ce masa komai ba amma ji tayi kamar ta fashe da kuka, ta mike ta cire Hijab din jikinta ta linke ta ajiye ta bude jakarta ta ciro sabulu da sponge, toothpaste da toothbrush, xata wuce bandakin yace "Tawul din fa?" Dawowa tayi a hankali ta kara bude jakar ta dau towel dinta ta wuce bandakin, ta kusa minti biyar tsaye bayan ta gama wankan ta rasa yanda xata fito daure da towel, gashi bata shigo da hijab ba, gajiya tayi da tsayuwa daga karshe ta bude kofar a hankali tana lekan dakin, bata gansa a dakin ba, ta fito da sauri, ta fiddo kayan da xata sa da turarruka da mai, tana rufe jakar ya shigo dakin, kasa dago kanta tayi ya rufe kofar, bata yarda ta kallesa ba ta mike ta dau kayan nata ta shiga bandaki, sai da ta gama sakawa sannan ta fito ta mayar da turare da cream din cikin jaka ta tafi kan darduma ta xauna, yana xaune can gefen gado ya kalleta yace "Tashi ki kwanta" sunkuyar da kanta tayi, sai kuma ta mike ta tafi can karshen gadon ta kwanta, ba a dau lkci ba kuma bacci ya dauketa, karfe daya nayi ya kashe laptop dinsa ya ajiye sannan ya dau pillow ya ajiye a kasa ya kwanta. Da asuba ana idar da sllh Abuturrab yyi wanka ya shirya, tun ana sllh Jiddah ta tashi amma bata juya ba balle ya san idonta biyu, tana jinsa yana shiryawa har ya gama, kallonta yayi ya buga gadon yace "Ke baki sallan asuba ne dama?" Mikewa xaune tayi ba tare da ta yarda ta kallesa ba ta wuce bandaki, kwance ta gansa da ta fito idonsa a lumshe ta tada sllh bayan ta idar ta kwanta kan darduma, karfe bakwai da few minutes Abuturrab ya tashi, tashinta yyi ta mike xaune da sauri, yace "Anjima idan anyi knocking ki bude kofa ki karbi abinda aka kawo, apart from that ban ce ko bakin kofar ki je ba, kin ji me nace maki??" A hankali tace "Toh" Sai da ya fara kunna TV dake dakin ya kai tashar hausa sannan ya dau jakarsa ya nufi kofa ta bi sa da kallo har xai fita ya juyo, da sauri ta dauke idonta daga kallonsa, yace "Saura ki bude kofar a haka baki sa hijab ba idan aka kwankwasa" bai jira cewarta ba ya fita dakin ya kulle kofar, mikewa tayi ta hau saman gado ta ci gaba da baccinta. Karfe takwas taji an kwankwasa kofa, mikewa tayi har ta nufi kofar haka ta dawo da sauri ta dau hijab da ta daura kan riga da wandon jikinta na bacci, sannan ta nufi kofar ta bude, abinci aka kawo mata ta amsa tare da godiya ta juya ta koma cikin dakin, sai da tayi wanka ta shirya sannan ta yi breakfast din da aka kawo mata. Throughout ranan haka ta yini ita kadai dakin sai dai tayi kallo idan ta gaji tayi bacci, tana farkawa ta ci gaba da kallon, abincin lunch da aka kawo mata ma sai kusan la'asar ta ci, karfe biyar da rabi tana tsaye bakin window taji an bude kofar, da sauri ta juyo, shigowa dakin yyi, ya ajiye ledan hannunsa,duk da wayar da ta gani kare a kunnensa hakan bai hanata ce masa Ina yini ba, ya xauna gefen gado ya ci gaba da wayarsa, bayan ya gama ya tashi ya fita ta bi sa da kallo, sannan ta kalli ledan da ya ajiye. Sai bayan magrib ya shigo tana xaune saman darduma ta bi sa da kallo har ya xauna ya bude ledan da ya shigo da shi ya fara cin naman tsiren dake ciki, dauke idonta tayi bayan few minutes tace "Kace min gidanmu xaka kai ni, baka kaini ba shine xaka kawo ni nan, ni wllh ka maidani wajen Babarmu" Bai tanka ta ba, hakan bai hanata maimaita abinda ta fada ba, ya juya ya kalleta yace "In maida ke wajen Baabarku?" Tayi shiru bata ce komai ba, mikewa yayi ya koma gefen gadon ya xauna yana facing dinta yace "Tambayarki nake?" Ta sunkuyar da kanta tace "Ehh kai kaini wajenta" Yace "Ohkk... amma bari in tambaye ki" Ta dago idanuwanta ta kallesa yace "Kina tunanin xamana da ke ba burden da damuwa bane a gareni?? Ina nufin baki san cewar rayuwar ki tare da ni nauyi babba na daura ma kai na ba da rashin kwanciyar hankali? Do you think ko matata ba iyakar abinda xan mata nake maki ba? What's so important about staying under same roof with you? Kina tunanin ni ajin ki ne da nake kula ki nake kula al'amuranki? Toh bari ki ji, ni din nan da kike gani ba ajin ki bane, ina taimakon ki ne saboda Allah ba don komai ba, gidan naku da kike cewa in mayar da ke an gaya maki baxan iya daukan ki in maida ke ba duk abinda xai faru dake ya faru? Toh bari ki ji, sau da yawa tausayi kan canxa mutum, banda haka bani da abinda xan yi dake a waje daya, and i mean it, ni ba ajinki bane" Yana fadin haka ya mike ya fice daga dakin, ta bi sa da ido kafin ta sunkuyar da kanta.



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems


Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada

Instagram -fareeskinglow_89

TikTok-fareeskinglow

Facebook page-fareeskinglow 

WhatsApp -08031898240

Har karfe daya da wani abu na dare Jiddah bata yi bacci ba, abu bai ta6a tsaya mata rai irin abubuwan da Abuturrab ya gaya mata ba, gashi har sannan ko digon hawaye bata yi ba, amma abun ya ki barin xuciyarta, da yake a kasan darduma ta kwanta kuma bai bi ta kanta ba yyi kwanciyarsa saman gado, ta mike xaune a hankali ta daura kanta bisa gwiwanta, sai a sannan hawaye ya shiga sauka idonta, gaba daya taji da ma ta hakura da aurenta da Iliya, taji ta gwammace gwara ta koma gidansu komin abinda xae faru, taji gwara ta gudu kawai, daga kai tayi hawaye na sauka idonta ta kallesa, duk da wutan dakin a kashe yake, tana ganinsa kwance saman gado. Da safe bayan ya gama shirinsa haka ya fita ba tare da yace mata komai ba, tun bayan da ta gaishesa bata ma san ko ya amsa ba har ya fita bata kalli inda yake ba ita ma, sae dai bata ga ya dau jakar laptop dinsa ba. Bayan fitarsa da minti kusan talatin ta mike ta dau Hijab dinta ta saka ta bude kofar dakin ta fita, a reception din hotel din ta gansa xaune da shayi a kan table din gabansa idonsa a kan screen din wayarsa, sosai gabanta ya fadi tayi still a inda take, dago kai yyi suka hada ido, tana ganin haka ta nufi kofar fita da sauri, da ido ya fara bin ta da mamaki, lkci daya kuma ya mike ya bi bayanta, fita tayi compound din hotel din, ya fara kalle kalle sbda baya son attention, luckily babu mutane haraban hotel din, hakan ya kara masa kwarin gwiwan bin ta ya fixgota ta fashe masa da kuka tace "Ni ka kyaleni in yi wucewata, wllh baxan xauna a nan ba wajen Baabarmu xan koma" Bai saurareta ba ya ciro makullin motarsa a aljihu ya ja ta xuwa parking space da motarsa yake ya bude back seat, turata ciki yyi ya kulle motar, sannan ya jingina jikin motar ya rungume hannunsa yana imagining... assuming baya xaune downstairs tafiyar xata yi da gaske, Jiddah ta dinga rusa kuka cikin motar, ya fi minti 7 a tsaye kafin ya bude motar ya shiga ya kulle, can gefe ta koma tana shessheka taki kallonsa, yana kallonta fuskarsa a daure yace "Ina xa ki tafi kika ce?" Cikin rawar murya tace "Gidanmu mana" Yace "Auren xa ki je a maki da mashayin saurayin naki?" Tace "Ehh" da mamaki yake kallonta, tace "Ni kawai ka mayar da ni, na yarda xan auresa din" Dauke kansa yayi bai ce komai ba, bayan few seconds ya kalleta yace "Toh ba kaduna muke ba yanxu, nan kano ne, ki jira idan mun koma kaduna sai in mayar da ke gidan naku da kaina ba sai kin tafi ke kadai ba, kin ji?" idonta ta fara gogewa tace "Yaushe xa mu koma kadunan?" Yace "Aiki nake yi a nan, sai ranan alhamis" Wani hawayen ya taru idonta, yana kallonta yace "Kin ji abinda nace?" Hawayen ya xubo mata tace "Har sai alhamis kuma?" Yace "Jibi ne alhamis din ai" Ta sunkuyar da kanta tana goge hawayenta, shi dai kallonta kawai yake ko kiftawa babu, a hankali tace "Toh" Bai kuma cewa komai ba, ya juya ya bude motar ya sauka yana dubanta yace "Sauko" Ba musu ta sauko daga motar tana wani kumbure kumbure, yana kallonta yace "Wani man kike shafawa?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Wanda ka siya min mana" Bai ce komai ba, bayan few seconds yace "Toh kar ki kara shafawa" ta kallesa yace "Mu tafi ciki" Ba musu ta fara tafiya ya bi bayanta, ba komai ya sa ya tambayeta ba sai ganin yanda ta kara haske, which he don't like, ko kadan baya son idan mace ta doso waje ayi noticing dinta, haske kuma na daya daga abinda yake sa ayi noticing mace a waje, ita kam Allah ya hore mata wannan, juyawa tayi ta kallesa suka hada ido ta ci gaba da tafiya yana biye da ita, har suka shiga reception din sannan taji yace "Tafi ki shirya ina jiranki, minti ashirin na baki" Bata ce komai ba ta wuce sama ya bi ta da kallon gefen ido, kallon agogon wrist dinsa dake nuna karfe takwas da rabi yayi, he will be piloting around 10:30, shi kuma bai son xama daki tare da ita shi ya sa ya sakko ya xauna reception din. Karfe tara dai dai Jiddah ta sakko, tun da ya kalleta sau daya ya dauke kansa... Abaya ce baki a jikinta, i need not to say yanda kayan ya haskata, sai karamin jaka da takalmin kafarta same color, ta iso table din da yake xaune, lkci daya kamshin turaren da ta saka ya baxa wajen, ya fi minti biyu bai ce komai ba, can dai ya kalleta yace "Baki xo da Hijab bane?" Ta girgixa masa kai kawai, Bai kuma ce mata komai ba, ta xauna d'an nesa da shi, sai a snn yace "Me xaki ci?" Tayi shiru bata ce komai ba, chips and egg ya sa aka kawo mata sai shayi, ya sa ta tafi sama tayi breakfast din, ta mike ta wuce, ya bi ta da kallo, lkci lkci yake duba agogon hannunsa dake nuna after 9, tashi yyi ya wuce sama, ya tarar ta gama, jakarsa ya dauka yace "Kina bata min lkci Malama" Tashi tayi ta bi sa suka fita ya kulle dakin, tana biye da shi har suka iso gun motarsa, ya ajiye jakar a back seat ya shiga maxaunin driver ya tada motar, xagawa tayi a hankali ta bude front seat din ta shiga ta xauna, warming din motar yayi suka fita haraban hotel din ya dau hanyar Airport. Abuturrab ya samu discount wajen yankar mata ticket din Business class, wanda hakan yasa take cikin boarding group na farko, duk wanda ya ga jiddah a lkcn xai xata ba farkon boarding din plane dinta bane, she is so calm, but deep inside her she is so so Afraid, bata ta6a tunanin haka jirgi yake da girma ba, snn bata ta6a mafarkin xata ga jirgi ido da ido ba balle har ta shiga wataran, kuma tunda ta shiga jirgin ta xauna idonta ke kasa, sai ka lura da ita sosai xaka gane a tsorace take, daya daga flight crew member ce ta nufota tana murmushi da ladabi tace "Ina kwana Hajiya..." Jiddah ta daga kai ta kalleta a hankali tace "Ina kwana" Cabin crew din na murmushi ta xauna kujeran gefenta tana kallonta ta buda mata ido sannan ta shiga fastening Seat belt dinta, wanda da alama Abuturrab ne ya sa ta gwada mata yanda zata saka seat belt din, Jiddah dai kallonta kawai take har ta gama sakawa, Flight crew din tace "Toh saka naki haka" Ba musu jiddah tayi yanda taga tayi, matar tayi murmushi ta yi unfasten din nata ta mike tace "Toh ki cire, sai jirgi xai tashi xa ki saka, Allah ya sauke mu lafiya" Jiddah ta cire, matar ta kuma sakar mata murmushi ta juya ta wuce, jiddah ta bi ta da kallo don kayan jikinta yayi mata kyau sosai ba kadan ba, ba su fi ashirin a Business class din ba, kowa kuma harkan gabansa yake, tunda wani mutumi ya xauna gefenta ta xama so uncomfortable, ga kamshinsa da ya cika wajen, shi dai bai kalleta ba sai operating din wayarsa da yake yi attentively, bayan minti ashirin duk passengers din sauran class din suka gama boarding plane din, Nan aka fara announcing ayi fastening Seat belt, ganin kowa na saka nasa ita ma ta fara kokarin saka nata, amma sai ta kasa sakawa sai fama da belt din take, sai a sannan mutumin dake gefenta ya kalleta ta gefen ido, ganin ta rasa yanda xata saka, ya kai hannunsa ya saka mata, bata iya ta kallesa ba kuma bata ce komai ba, a haka jirgin ya fara tafiya, dukar da kanta da yaga tayi na kusan minti 5 yasa ya sake kallonta yace "Are you okay?" Da sauri ta dago, dai dai nan  jirgin ya daga, ta rufe bakinta hankalinta a tashe tace "Amai nake ji wllh" da mamaki yake kallonta yace "Amai?? Ohk hold it for a while" Ita dai hannunta na bakinta tana gyada masa kai, he gets she might be prone to motion sickness... ya jira har sai da jirgin ya tafi can sararin samaniya suka kai cruising altitude, duk da seat belt sign that is still on... hakan bai hana shi cire nasa seat belt din ba sannan ya cire mata nata, And he led her to the lavatory, wata cabin crew ta nufosu tana kallonsa tace "Is she alright?" Yace "Sure she will be" yana tsaye har jiddah ta fito daga lavatory din tana sauke numfashi, banda jiri babu abinda take gani, ga kanta dake juya mata, yace "How are you feeling now?" Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, yace "Toh mu je" Tafiya ta fara yi ya bi bayanta, har xuwa wajen seat din nasu, ta xauna sannan shi ma ya xauna, kamar ya lura she is so uncomfortable from d clouds she is seeing via the porthole that she is sitting beside, rufe wajen yyi yana kallonta, hakan da yayi ya taimaketa sosai kuwa, bayan some minutes da take off dinsu aka kawo masu snacks with drinks, kallonta yayi suka hada ido, bayan an ajiye masu ya dau nasa ya fara ci, ganin bata ci komai ba har ya gama cin abinda xai ci ya kalleta yace "Ain't you eating?" Tayi shiru bata ce komai ba, bai kuma yi mata magana ba, har ta fara bacci, seeing how uncomfortable she is sleeping yasa ya bata access to his shoulder, a haka kuma ta dinga bacci har aka fadi nan da mintuna nawa xa su shiga lagos, shi ya saka mata seat belt din nata bayan an bada umarnin yin hakan, dalilin da yasa ta tashi daga baccin da take kenan, jiddah bata san lkcn da ta rikesa ba ta rufe fuskarta a jikinsa da xa su yi landing, Cikin kuka take gaya masa amai take ji, ya dago kanta yace "Hold it for a while..." ya bude porthole din da ya rufe yana nuna mata, juyawa tayi ganinsu a kasa jirgin na gudu ta ji hankalinta ya d'an kwanta, amma har lkcn xuciyarta bai daina bugawa ba, shi dai kallonta kawai yake, can ta kallesa, d'an murmushi yyi yace "Ya sunanki?" Ta sauke idonta tace "Jiddah" yace "Jiddah!!" Ta gyada masa kai, yace "Wannan ne farkon hawanki jirgi Jiddah?" Ta gyada masa kai, bai san lokacin da yyi murmushi ba yace "I see, to mun kawo lafiya, hope ur next flight won't be as 

frightening as this?" Ita dai bata ce komai ba, 

yace "Ke kadai kika xo lagos?" Ta girgixa masa kai tace "Aa ni da yayana" yace "Wow, yana ina?" Ta buda masa hannu alamar bata sani ba, yace "Ba tare ku ka

 shigo jirgin ba?" Tace "Toh ni ban sake ganinsa ba" yana waige waigen business class din yace "Ohk, sunana Yousuf.... Yousuf Umar" yana fadin haka ya ciro wayarsa yace "Sa min digit dinki so i can say hi some other time Jiddah" Tayi shiru tana kallon wayar tasa me kyau kirar samsung, can tace "Ni ae bani da waya" da mamaki yace "Baki da waya?" Ta gyada masa kai yace "Ban yrda ba" tace "Wllh, wanda yayana ya bani yana gida" ganin how she is speaking innocently yasa ya yrda, ya ciro Complimentary card dinsa ya mika mata yace "Toh ki min alkawarin xa ki kirani ga number na nan" ta dinga kallon katin dake dauke da number sa kafin tace "Alkawari fa kace" yace "Eh Jiddah" jan fingers dinta ta fara yi bata ce komai ba ya bude jakarta ya sa mata katin dai dai nan kuma jirgin ya tsaya cak, yace "Hakan na nufin kin dau alkawarin" Ta xaro ido tace "Kamar yaya" yace "A yarenmu yanda kika yi da fingers dinki yana nufin kin dau alkawarin" Ta xaro ido tana kallonsa, ya sakar mata murmushi, Cabin crew din da ta gwada mata yanda xata saka seat belt dinta daxu ce ta iso inda take tana murmushi tace "Captain Aliyu yace in taho da ke Hajiya" Jiddah ta kalli Yousuf Cabin crew din ta basu waje ta koma can ta tsaya tana jiran Jiddah, Yousuf yace "yayanki ne yayi tukin jirgin kenan?" Da mamaki take kallonsa tace "Tukin jirgi fa kace? Aa baxai iya ba" yana murmushi yace "Toh tashi ki je... ina jiran kiranki" shi ya rigata mikewa ya dau briefcase dinsa ya fara tafiya ta bi sa da ido snn ta mike ta nufi cabin crew din da tayi mata jagora har Cockpit inda Abuturrab yake xaune tare da Co-pilot dinsa wani black American suna secure Cockpit checklist, da mamaki Abuturrab ke kallon Crew din don ce mata yayi tayi leading dinta outside d plane, hannu black American din da ya kafe jiddah da ido ya mika mata yana murmushi yace "Hello...." Kallon Abuturrab Jiddah tayi, lkci daya taga ya mata wani shegen kallo, amma calmly yace "Juya ki tafi ki jirani ina xuwa..." Juyawa tayi da sauri ta bar wajen, Yana ma American din murmushi yace "We don't do that captain, and she doesn't even understand English" Pilot din na kallonsa yace "Ohh, is she ur sister?" Abuturrab yace "My friend's wife...." Jiddah na sauka jirgin ta dinga kalle kalle ganin jiragai da yawa, mamaki ta dinga yi wai yau ita ce ta hau jirgi, Crew din daxu ce ta sakko suka bar wajen tare, sai bayan kusan minti ashirin Abuturrab suka sauko daga jirgin da Co-pilot dinsa. Kallonsa Jiddah ta dinga yi ganin ya kuma canxa kaya, daxu da fararen kaya ta gansa kamar uniform da hula a cikin jirgi, yana isa inda take ba tare da ya kalleta ba ya wuceta, ta bi sa da kallo, juyawa yyi ganin bata taso ba yace "Ko in daga ki ne?" Mikewa tayi a hankali ta bi bayansa, hotel din da ya ke sauka a lagos not too far from Murtala Muhammad Airport ya nufa tare da ita cikin taxi, Tana biye da shi bayan sun sauka taxi din sun shiga hotel din, bin sa take kamar xata shige jikinsa ganin mata 

kusan tsirara suna yawo 

hankali kwance, garin kallon wata da ta gani da wando iya cinya ta kusa fadawa kansa, ya juyo yana kallonta, kamar xata yi kuka tace "Ina ne nan ka kawo ni?" Ci gaba yyi da tafiyarsa ta bi bayansa, har ya amshi makullin daki a reception tana makale da, shi dai bai sake ce mata komai 

ba suka shiga dakin da ya amsa, bayan ya kulle kofar kamar xata yi kuka tace "Su basa jin kunya ne?" Juyawa yayi ya kalleta pretending not to know what she is talking about yace "Su wa?" Ta sunkuyar da kanta, yace "Tambayarki nake su wa?" Still ta ki cewa komai, ya ajiye wayoyinsa yace "Ke me ya aike ki kallonsu?" Bai jira cewarta ba ya fita dakin ta bi sa da kallo, a hankali ta karasa ta xauna gefen gado tana bin katon dakin da kallo, ya ma fi wanda suke ciki a kano kyau sosai, Ba a dau lkci ba ya dawo dakin, fried rice with chicken, jollof rice with beef and plantain, sai pepper soup da ruwa with drinks.... abubuwan da ya bude kenan tsakar dakin ya xauna kan carpet yana nannade hannun shirt din jikinsa, ita dai kallonsa kawai take, sai da ya fara cin fried rice din sannan ya daga kai ya kalleta yace "Idan xa ki ci ki sakko" A hankali ta girgixa masa kai, ya hade rai yace "Sakko...." Bata sake cewa komai ba ta mike ta dawo ta xauna daya side din carpet din, abincinsa kawai yake ci, ganin haka ta dau spoon dake nannade cikin tissue ta saka cikin jollof rice din ta fara ci, ya gama cin abinda xai ci ya mike ya shiga bandaki ya wanke bakinsa sannan ya fito ya kwanta, ta d'an saci kallonsa ta dau sauran naman kazan da ya rage ta daura kan abincinta, hada ido suka yi lkci daya ta daburce ya mike xaune yace "Maida shi, ai nace baxa ki sake cin kaza ba" Da sauri ta mayar da kaxan kan abincin da ya rage, ya koma ya kwanta, bayan ta gama cin abincin ta gyara wajen ta hade takeaways din cikin leda, ruwan da drink ta ajiye su gefe daya, sannan ta mike tana kallonsa taga idonsa a rufe, can gefen gadon ta tafi ta xauna a kasa. Karfe biyu saura Abuturrab ya koma Airport tare da Jiddah, don he will be piloting to Abuja, hankalinta ya tashi ganin jirgi xa su kara shiga tana kallonsa kamar xata yi kuka tace "Don Allah mu hau mota, wllh bana son jirgin nan" Lkci daya hawaye ya kawo idonta, yace "Baki so saboda me?" Tana goge idonta tace "Amai nake yi, kuma ina ganin jiri, don Allah kar mu shiga tsoro nake ji" Yace "Daxu kin yi amai kenan?" Ta gyada masa kai yace "A ina kika yi aman?" Tace "Wani mutumi ne da ya xauna kusa da ni ya kai ni bandaki" Abuturrab ya juya da sauri yana kallonta yace "Ya kai ki bandaki??" Ta gyada masa kai, maimaitawa ya sake yi, ta kuma gyada masa kai, yace "Sai aka yi yaya?" Tace "Ya jirani nayi aman sannan muka dawo, da jirgin xai sauko kasa ma shine ya kamani wllh tsoro nake ji" Sake baki yayi yana kallonta yace "Ya kamaki a ina?" Tayi shiru bata ce komai ba, ya rungume hannunsa yace "Ya mutumin yake???" Tace "Yana jin hausa, kuma dogo ne kaman ka, sannan yace min sunansa Yousuf" Ya xare glass din idonsa yana kallonta, can yace "Ohk har hira ku ka yi kenan" Tace "Aa bamu yi hira ba" Bai kuma ce mata komai ba ya ci gaba da tafiya ta bi bayansa gabanta na faduwa, ticket din da Abuturrab ya yankar mata sai da ya tabbatar the person next to her is a female, exactly abinda tayi daxu daga kano xuwa Lagos shi tayi daga Lagos xuwa Abuja, Bayan jirgin ya sauka Abuja ta fita tana kare ma jirgin kallo tana fatan babu abinda xai kaddara mata sake shiga jirgi, har suka isa gidan Abuturrab wajajen la'asar jikinta a sanyaye yake, duk yana lura da ita bai ce komai ba, xaunawa tayi kan kujeran parlon tana bin parlon da kallo, yana kallonta yace "Yanxun ma kinyi aman a jirgi kenan?" Ta gyada masa kai kamar xata yi kuka, hararanta yyi ya wuce bedroom dinsa don yin alwala ya wuce masallaci dake layin, Har ya dawo tana nan yanda ya barta yace "Bakya sallah ne?" Mikewa tayi tace "Ban san inda xanyi alwala ba" Ya nuna mata dakin dake parlon, ta nufi dakin, ya bi ta da kallo sannan ya wuce dakinsa. Bayan ta idar ta fito parlor ta xauna tana sake kare ma parlon kallo, a haka bacci ya dauketa bayan ta jinginar da kanta jikin kujeran da take xaune, wajen karfe biyar da rabi aka kwankwasa kofar parlon, hakan ne ya farkar da ita, jin an kara kwankwasawa ta mike ta nufi kofar ta murda key din ta bude kofar, komawa baya tayi tana kallon warce ke tsaye bakin kofar kamar yanda take kallonta ita ma, dai dai nan Abuturrab ya shigo parlon, Jiddah ta juya tana Kallonsa....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems


Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada


Instagram -fareeskinglow_89

TikTok-fareeskinglow

Facebook page-fareeskinglow 

WhatsApp -08031898240

Abuturrab yace "But you didn't tell me kina xuwa Aneesah" Aneesah tayi wani murmushi tace "How will i tell you ina xuwa Aliyu, dama dalilin da yasa kake walakanta ni kwana biyu kenan, dama wata ka samu? Dama wannan ce dalili" Daga sama har kasa take kare ma Jiddah kallo tana murmushin takaici tace "Ki bar murna kin samu pilot har yana kawo ki gidansa saboda tsagwaron so, nima haka ya dinga min, but...."  Abuturrab ya katse ta yace "Come off it pls Aneesah, what's all this? I thought i explain better to you her position, she is the lady...." Aneesah ta sake kallon Jiddah da sauri, Jiddah dai banda kallonta ita ma babu abinda take, A hankali Aneesah tace "Which lady Aliyu?" Yayi kasa da muryar yace "Ba ke kika ce in kawota ta xauna gidanku ba" Sosai gaban Aneesah ya fadi don bata ta6a tunanin Jiddah ce wnn yarinya da Abuturrab ke fadi mata ba, ta dinga kallon Jiddah xuciyarta na bugawa, ta ma rasa abinda xata ce masa, Abuturrab yace "Tunda kin xo yanxu sai ku tafi tare, dama anjima nake son kai ta gidan naku, hopefully nasan Mumy ta yarda ta xauna with ur family..." Aneesah ta hadiye abu da kyar, har sannan ta kasa daina kallon Jiddah da tayi mata wani kwarjini, a xuciyarta ta shiga kokwanton anya ita ce me awaran da Aunty ta ce, or is Aliyu playing her?? Abuturrab ya juya ya kalli Jiddah bbu yabo bbu fallasa yace "Dauko mayafinki" Shiru tayi tana kallonsa, a d'an tsawace yace "Baki ji na ne?" Ta koma baya tace "Toh ina xanje idan na dauko?" Yace "Ban sani ba, wuce ki dauko" Juyawa tayi ta koma can tsakiyar parlon ta tsaya kamar xata yi kuka tace "Allah ni babu inda xanje, ba gidan Baabarmu nace ka maida ni ba, nasan ita wacece da xan bi ta" Daga maganarta Aneesah ta kara tabbatarwa ita ce me awaran, Abuturrab ya saki baki yana kallon Jiddah, Aneesah ta hade rai tace "Toh nan din gidan ubanki ne da baxa ki bari ba?" Jiddah ta kalleta, a hankali tace "Ubana fa kika ce?" Aneesah da xuciyarta ya dau tafarfasa tace "Shi din..." Lkci daya Jiddah ta fashe da kuka tace "Ba dai ubana dake kabari ba wllh sai dai naki" Aneesah ta saki jakar hannunta tace "Kika xagi ubana?" Jiddah ta goge idonta tace "Ehh an xaga, me nawa uban ya maki da kika xagesa ke?" Aneesah tayi kanta a mugun fusace, fixgota Abuturrab yyi yace "Hey are u okay, what are u trying to do?" Fixge hannunta tayi kamar wata zakanya ta nufeta, cikin tsawa Abuturrab yace "Don't try that Aneesah, u will definitely see the other side if me by touching her" Tuni Jiddah ta tsorata ta bar wajen da gudu ta yi hanyar kitchen hakan bai hana Aneesah bin ta ba, shakota Aneesah tayi tace "Uban wa kika xaga?" Tuni Abuturrab ya nufesu, Jiddah ta kwala kara ta gatsa mata cixo a hannu, Aneesah bata yi wata wata ba wajen sauke mata lafiyayyen mari a fuska sannan ta wuntsular da ita a kasa tana cewa "Don kaza kaxanki ubana sa'an kaf danginki ne aka ce maki?" wani ihu Jiddah ta fasa tana cewa wayyo bayanta, wayyo kafarta, Kamar daga sama Aneesah taji saukan tagwayen mari wanda sai da yasa taga duhu na few seconds, ya fixgota fiercely yace "How dare you? You bitch" with shock Aneesah ke kallonsa, ya nufi kofa ya wuntsular da ita waje kamar yanda ta ma Jiddah yyi banging kofar, Banda rusa kuka babu abinda Jiddah dake yashe a kasa take tana kiran Baabarmu, Bude kofar Aneesah tayi tana daga tsaye bakin kofa hawaye kaca kaca a fuskarta tace "You called me a bitch Aliyu?? Ni ka walakanta ka sauke yatsunka fuskata a kan wannan yar talakawan bagidajiya jaka? Ni ka ci ma mutunci haka in her present? U threw me out of ur house a kan yar talakawa me tallan awara?" Jiddah ta goge idonta ta mike cike da tsiwa tace "Idan ana tafiya lahira da arxiki sae ki daura naku a kai ki tafi da shi in ga, kuma Allah ya isana, ban yafe maki ba, axxaluma...." Fixgo hannunta Abuturrab yyi ya nufi daki, cikin kuka tana son kwace hannunta take cewa "Ni ka kyaleni, me na mata xata mareni...." Turata yyi cikin dakin ya sa makulli, sai a snn ya daga kai ya kalli Aneesah, ji yyi gaba da gwiwansa ya sace, ya nufeta, tana ganin haka tayi wani murmushi tace "Watch out for it Aliyu, xaka san ba a ta6a mu a xauna lafiya, daga yau ka kafa daka sanin abinda ka min a rayuwarka..." Daga haka ta dau jakarta xata fita parlon hawaye na sauka idonta, ya rikota yyi kasa da murya yace "But Aneesah...." Ko rufe baki bai yi ba ta sauke masa mari sau biyu, hakan bai sa ya saketa ba ta dinga dukansa a kirjinsa, ya rungumeta gamm yace "I'm sorry Aneesah" kuka kawai take, shi kam duk jikinsa yyi sanyi, cikin rawar murya tace "A kan wannan bagidajiyar xaka mareni and throw me out of ur house Aliyu??" Ya kwantar da ita kirjinsa yace "U are misperceiving me Aneesah..." Turasa tayi da karfi ta nufi kofa tana kuka ta fita, dafe kansa yyi ya xauna saman kujera yana furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, daukar wayarsa yyi ya shiga dialing number Ahmad, har ya katse bai dauka ba, yana ta xaune parlon har kusan magrib sannan ya mike da kyar, bedroom din da Jiddah ke ciki ya nufa ya bude kofar, kwance ya ganta a kasa, ya karasa ciki yana kallonta ya duka, bacci take, ya kai hannu goshinta, bude ido tayi, ya daure fuska ya mike, ta tashi xaune tana mitsika ido, yace "Kin san warce kika xaga daxu?" Ta kallesa tace "Toh ai nima bata san wacece ni ba" ya duka yana kallonta da kyau yace "Gaya min ke wacece?" Ta turo baki ta taki cewa komai, kallon fuskarta da shatin mari ya kwanta kawai yake, can ya mike jin xa a tada sllh ya fita dakin.


Abuturrab na dawowa masallaci ya ga kiran Ahmad a wayarsa, ya xauna sannan ya kuma dialing number sa ya kai kunne, daga daya bangaren Ahmad ya daga yace "Ya kwana biyu?" Abuturrab ya shafa kansa ya mike ya koma dakinsa, a hankali yace "Alhmdlh, how is work?" Ahmad yace "Alhmdlh, baka yi piloting xuwa Abuja bane yau" Abuturrab yace "Ina Abuja" Ahmad yace "Alright, ya na ji ka so calm dude?" Abuturrab bai ce masa komai ba, Ahmad yace "Xan shigo after isha" Abuturrab yayi kasa da murya yace "Ka taho da paracetamol or any pain reliever" Ahmad yace "Ko har Aneesar ta je ne?" Abuturrab ya katse wayar, ya ajiye yana tunanin where he is going to start from, sure yasan yana son Aneesah sosai baya son komai da xai bata mata rai, But why did all this happen, why did things turn out this way.... Shafa kansa kawai yayi knowing the only way out now shine ya tura gidansu in few days time, wayarsa ya sake dauka har xai yi dialing numberta ya fasa. Abuturrab na xaune parlor bayan ya dawo isha yana jiran xuwan Ahmad, karfe takwas da few minutes Ahmad ya danna bell, ya mike ya bude masa kofa, Ahmad ya shigo parlon, xaunawa yayi saman kujera yace "After leaving me all my self with my wedding preparation, still u have d gut not to ask how everything is going.... right?" Abuturrab yace "Ohk ka fara shirye shirye ne?? Sure juma'ahn sama ne koh? I'm sorry na manta wllh, what are u up to now? Kasan ba haduwa muke yanxu a kadunan ba kamar da" Ahmad yyi dariya yace "Ya xa mu hadu kuwa, tunda ga ka ga amaryar ka Jiddah" Abuturrab ya tsura masa ido, can yace "Is there anything i will gain idan na maka karya Ahmad?? But don Allah ka gaya min me yasa kake ganin har ynxu matata ce ita?" Ahmad yace "Toh gashi nan ba sai na fada ba, da fa duk na shigo kd sai mun hadu, infact kai ma kake xuwa gidanmu ynxu kuwa kana gidanka, idan ba wanda yyi sabon aure ba, giyan auren na dibarsa waye ke yin haka??" Abuturrab yace "Ka dai jira xanyi auren kwanan nan sae kaji dadin fadin duk abinda ke ranka, amma yanxu kam i am a bachelor just as u, sae sabon title da na samar ma kaina na xama Uba, i am more like a father or guardian now" Ahmad yyi murmushi yace "Toh ka bani ita inyi ta biyu da ita Captain" Abuturrab ya kallesa, kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Are you for real?" Ahmad yace "I'm serious wllh in dai Umma xata yrda i will" Abuturrab yace "Ohk, but.... How are we going to open up all this to our parent? Kasan dai ynxu banda Aunty da kai, sai ita yarinyar babu wanda yasan babu auren nan" Ahmad yace "We will cross the bridge when we reach there, yanxu dai ka amince min kai?" Calmly Abuturrab yace "In da gaske kake na amince, nima burden xai sauka kaina, if not for her da banyi making mistake da nayi daxu ba" Ahmad yace "Wani mistake?" Abuturrab ya dau remote din TV yana canxa channel yace "Ba ruwan ka" Ahmad yyi murmushi yace "Everything is settled now tunda ka amince"

 Kafin karfe tara Jiddah tayi bacci bayan tayi wanka, Hijab din Aneesah dake gidan ya bata tayi sllh tun magrib. Abuturrab na xaune har sannan a parlor tare da Ahmad sae dai hankalin sa baya tare da Ahmad, bai yi tunanin Ahmad xai kai har 10 a gidan ba, Can dai Abuturrab yace "Wai kana kallon agogo kuwa?" Ahmad yace "Ohh

ta kusa xuwa kenan, anyway ko baka fada ba dama yanxu xan wuce sai da safe" Daga haka ya mike ya nufi kofa Abuturrab ya bi sa da kallo, mikewa yyi ya bi bayansa yace "Ka ajiye ni eatry let me get something to eat" A tare suka fita gidan, sai kusan karfe goma da rabi Abuturrab ya dawo, yana shigowa parlor ya kulle gidan sannan ya wuce dakin da Jiddah take, tayi nisa baccinta, Ya ajiye ledan abincin ya nufi gadon, buga gadon yayi ko motsawa bata yi ba, yayi hakan ya kai sau uku ganin bata tashi ba ya dau bottle water ya bude, sai kuma ya fasa xuba mata ruwan ya ajiye sannan ya kai hannu kafarta yana tashinta, bude ido tayi a hankali, yace "Tashi ki ci abinci" Ta girgixa masa kai tace "Na koshi" Yace "C'mon tashi nace" Mikewa xaune tayi da kyar tana kallonsa da idanuwan bacci tace "Na koshi" Ya hade rai yace "Sakko nace" Xamowa tayi ta sauka kasa tana lullumshe ido, ya bude mata tuwo da veg soup din, ta tashi tana rurrufe ido yace "Ina xa ki?" Tace "Xan wanke hannu" Bai ce komai ba ta tafi ta wanke hannun ta dawo, tun da ta fito yake kallonta, Kana ganin yanda Hijab din yayi a jikinta xaka kasan bata saka komai ba a ciki, dama kuma hijab din har kasa yake ja mata, xaunawa tayi ta jiginar da kanta jikin gadon ta lumshe ido, buga gadon yayi ta bude ido da sauri ta kalli abincin gabanta sannan ta kai hannu ta fara ci a hankali, juyawa yayi ya fita dakin.... Washegari da safe Abuturrab ya fita yayi mata shopping din few clothes, karfe goma kuma ya nufi airport tare da ita, babu abinda ya sanyaya masa jiki sai yanda kiran Aunty ya dinga shigowa wayarsa babu kakkautawa, shi kuma yaki dagawa, Jiddah na ganin inda suka xo hankalinta ya tashi, marairaice masa tayi tace "Ni fa bana son hawan jirgin wllh" Yana kallonta yace "Sai me xa ki hau?" Tace "Motar" Wani kallo yayi mata yace "Sai ki hau motar inda kika gansa ai" Lkci daya hawaye ya kawo idonta bata kuma ce masa komai ba, tun bata kai ga shiga jirgin ba taji kanta ya fara juya mata, Tana rike da wayansa da ya bata ta nemi kujera ta xauna a business class, sai waige waigen inda xata gansa ta mika masa wayar take, to ina shi yake xama ne a cikin jirgin, tunawa tayi a inda ta gansa jiya bayan jirgi ya sauka, and she assumed a wajen yake xama shi, jin taku a gefenta Jiddah ta juya, buda ido tayi sosai ganin wanda suka shiga jirgi tare da shi a rana na farko, seat dinsa ya nufa ya ajiye karamin jakar hannunsa a sama sannan ya xauna, da sauri ta dauke kanta gabanta na faduwa, wata mata ce ta xauna kusa da ita tayi mata sannu, murmushi kawai Jiddah ta mata tana juya wayar Abuturrab dake hannunta, bayan wani lkci jirgin ya tashi, suna keta hazo ta cire seat belt dinta da sauri ta mike bayan ta ajiye wayar Abuturrab, hanyar lavatory ta nufa sai a sannan Yousuf ya ganta ya bi ta da kallon mamaki, ba a dau lkci ba ta fito, matar dake kusa da ita tace "Did u feel nauseous?" Jidderh tayi mata murmushin karfin hali ta xauna, Ta d'an saci kallon Side din da Yousuf yake suka hada ido, sunkuyar da kanta tayi, throughout the short journey to kano bacci tayi a jirgin, snacks da aka kawo mata ma bata ci ba, Matar dake gefenta tayi tapping dinta tace "Ki saka seat belt dinki" Bude ido Jiddah tayi ta fara saka seat belt din, runtse ido tayi da jirgin ya fara sauka bayan ya samu izinin yin hakan, matar da ta lura she is very uncomfortable ta riketa, tace "It's just for a few seconds, sorry dear" Jiddah bata ce mata komai ba har jirgin ya sauka, rufe bakinta tayi kar ma tayi ihu, matar na Kallonta tana murmushi tace "it's all over" A hankali Jiddah ta cire seat belt din, bayan da jirgin ya tsaya ta mike ta dau hand bag dinta ta fara fita kamar yanda ta ga sauran nayi, da kallon mamaki matar ta bi ta, tana mamakin to ko kurma ce dai, Yousuf ya mike ya dau jakarsa ya bi bayanta da sauri, a hankali take sauka daga matakalan jirgin iska me sanyi na kadawa a filin airport din, tana sauka kasa kamar ance ta juya taga Yousuf yana saukowa shi ma, murmushi ya sakar mata har ya iso inda take yace "Jiddahh" Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, mika mata hannunsa yayi yace "Bani wayar taki in sa maki number na tunda Allah ya sa kin taho da shi yau" Ta buda ido sosai tace "Ba wayata bane, na yayana ne" Da mamaki yake kallonta yace "Yayanki? Yana ina?" Ta kalli cikin jirgin tace "Kaman yana ciki, ni dai ban gansa ba" Yace "Ina ku ke xuwa tare da shi ko da yaushe a jirgi?" Tace "Nima dai ban sani ba" Yace "Baki sani ba kamar ya?" Tace "Allah ban sani ba ne" Yayi shiru yana kallonta walking slowly together with her, can yace "Me ku ka je yi a Lagos?" Ta kallesa da sauri tace "Lagos?" Yace "Ehh" Tace "Nan ne Lagos din don Allah?" He couldn't help it but left his mouth agape yana kallonta with surprise, ta dauke kanta tana ci gaba da tafiya yace "Wait Jiddah, are you kidding me, or you just don't want to give me an answer" Bata ce komai ba, calmly yace "I am talking Jiddah..." Tsayawa tayi tana kallonsa tace "Ni fa ba wani turanci nake ji ba" Sake baki ya kuma yi yana kallonta, bai san lkcn da yace karya kike.... Tace "Wllh ba karya nake maka ba" Sincerely ta fadi hakan, ya shafa kansa yana sake kallonta daga sama har kasa yana naxarin abinda tace wai bata jin turanci, but how?? tsadadden abaya ce jikinta blue da ya mugun haskata, ko kwalli babu a idonta, wanda kuma bai kalli lips dinta da kyau ba, sai yayi assuming pink lip gloss ta saka coz after being pinkish har sheki lips din nata yake, ga manyan idanuwanta farare tasss kamar madara, hancinta kuwa have the perfect shape a nose should have snn ga tsayi, ya d'an mata murmushi yace "Na yarda Jiddah, yanxu ina xa ki?" Tace "Nima ban sani ba yayana nake jira, kilan yana saman jirgin har yanxu" Yace "Yayanki... iyayenku daya da shi?" Shiru tayi can kasan ranta kuma tana tunanin abinda xata fada masa, yace "Ki gaya min gaskiya Jiddah" Ta kallesa still bata ce komai ba, yace "Ina sauraranki" ta kwantar da kai tace "Me yasa kake son sani?" Yace "I just..." Shiru yayi kamar wanda ya tuna abu, sai kuma yace "Kawai ina son sani ne" Tace "Ba iyayenmu daya ba amma yayana ne" A hankali yace "Ko dai saurayin ki Jiddah" Ta wani xaro ido, sai kuma ta kyalkyale da dariya tace "Saurayi na? Saurayina fa kace? Aa ni ba saurayina bane shi wllh, saurayina sunansa Umar amma mun rabu yanxu" Yace "Umar?" Tace "Ehh, shi wannan kawai yayana ne" Wayar hannunta ya amsa da sauri tace "Nace maka nasa ne wayar" Bude screen din yayi don wayar a bude yake, ya dinga kallon hulan pilot dake jikin screen din wayar, karban wayar tayi hannunsa, xuwa lkcn bbu kowa haraban parking din jirgin sai ma'aikatan airport, Yousuf ya daga kai yana kallon Abuturrab dake saukowa daga jirgin yana kallonsu babu ko kiftawa, har sannan pilot uniform ne a jikinsa, Jiddah ta daga kai ganinsa ta kalli Yousuf tace "Shine yayan nawa" Yousuf ya d'an yi murmushi yace "Shine matukin jirgin... i guess right" Juyawa Jiddah tayi da sauri tana kallon Abuturrab, Yousuf ya karasa gunsa ya basa hannu suka gaisa yana murmushi yace "I guess you did the landing..." Abuturrab na kallonsa ya d'an yi murmushin gefen baki kamar wanda aka tilasta ma yace "Yea, i did" Yousuf yace "Nice landing...." Abuturrab yace "It's a pleasure flying you" Yousuf ya masa murmushi sannan ya juya ya bar wajen, yana isa inda Jiddah take yace "Ina jiran kiranki kamar yanda kika yi alkawari ranan" Yana fadin haka ya wuce, Jiddah ta kalli Abuturrab da ya hade girar sama da ta kasa yana kallonta.... A motarsa suke tafiya xuwa hotel din da suka sauka a kano, har sannan babu abinda yace mata, sai dai fuskarsa bbu ko digon annuri, har suka isa hotel din, kulle dakin hotel din yyi after going in together with her, yana kallonta fuskarsa a tamke yace "Waye wannan mutumin da na ganku tare?" Tace "Wai da gaske kai ne kake tukin jirgin in ji sa? Ni dai nace masa ba kai bane ae baxa ka iya ba" fixgota yyi, tayi wani kara xata durkusa ya dagota yace "Tambayar ki nake waye shi??" Kamar xata yi kuka tace "Toh ba q jirgin muke haduwa ba" ganin taki tsayawa cikin tsawa yace "Baxa ki tsaya ba" Kin tashi tayi tace "Toh don Allah ka sakeni"  kallonta kawai yake yi, can ya saketa, xamewa tayi ta xauna kasa, yace "Waje daya ku ka xauna da mutumin?" Tace "Aa, kawai da na sauka jirgin shine ya bi ni yana min magana" Shiru yayi yana kallonta ita dai bata yarda ta kallesa ba, can ya juya ya bude kofar dakin ya fita. Bayan la'asar suka bar kano xuwa kaduna a motarsa, Jiddah na kallonsa after the 20 mins silence tace "Meyasa muke ta shiga jirgi bayan ga mota, kyauta ake tafiya a jirgin ne?" Ya mata wani kallo yace "Kyauta? Tsoronki ake xaki shiga jirgi kyauta?" Tace "Toh Iyah ta ta6a ce min kudin jirgi yana da tsada kusan miliyan ne" Ya d'an kalleta yace "Haba??" Ta wara ido tace "Wllh, kasan ta ta6a xuwa makka sau daya, yaranta ne suka biya mata, toh ni na xata masu kudi ne kawai ke hawan jirgi" D'an murmushin da bai shirya ba yyi yace "Ni ba me kudi bane kenan?" Ta d'an xaro ido tana kallonsa tace "Aa bance haka ba, amma wannan motar taka ce?" Bai ce komai ba, a hankali tace "Kayi shiru..." Yace "Aa na Abbana ne" Tace "Toh gidan fa?" Yace "Wani gida?" Tace "Wanda muke ciki?" Yace "Shi ma na Abbana ne" Tace "Kenan shi ne ya biya kudin jirgin da muka shiga?" Yace "Ehh" Tayi shiru tana kallonsa, ta gefen ido ya kalleta, ta sauke idonta, bayan few seconds tace "Abbana ya ta6a ce min watarana xan shiga jirgi, amma Makka yace xanje" Ya kalleta yace "Haba" Ta gyada masa kai, tace "Kuma gashi na shiga amma ban je makkan ba" Yace "Toh idan kina da kudi ki kawo in biya maki Umrah ki je" Ta buda ido tace "Kudi?? A ina xan ga kudi ni ba sana'a nake ba" Yace "Ohk kina son kiyi sana'a ne? Ko awaran xaki siyar a bakin layin gidanmu?" Dariya ta fara yi, ya dinga kallonta don bai ta6a ganin dariyarta ba, tayi me isarta sannan tace "Idan kace inyi sai inyi in dai xa a siya" Da mamaki ya d'an kalleta kafin ya maida dubansa kan titi yace "Xa kiyi kenan idan nace kiyi" Tace "Ehh, sai in yi har da wainar flawa da dankali" Yace "Toh bari mu je a samar maki waje a bakin titin ko?" murmushi ya ga tayi tace "Toh" Ji yayi kamar ya fixgota ya rankwasheta, tace "Toh amma kudin xa su taru har in je makkan kuwa?" Yace "Wannan ke xan tambaya ai, babarku ta tara kudin ya isheta har taje makka?" Shiru tayi tana kallonsa, can tace "Toh ai abinci muke ci da kudin sana'ar, wannan kuma baxan siya abinci da kudin ba tunda akwai abinci a gida koh" Shafa millionaires belt dinsa yyi still wondering if yarinyar nan xata ta6a wayewa, though ya ma yi mamakin yanda har ta fara iya dressing ko don kayan da ya siya mata sunyi correlating da mahadinsu ne, sannan bai ga tana irin kwalliyan nan na masu talla ba, a ja gira a shafa barbada kumatu, a shafa gazal, babu wanda xai kalleta yace she is local or even an illiterate sai ya ji xancen dake fita daga bakinta, mamaki ma yayi yanda ta bude baki take creating conversation da kanta yau, muryarta yaji tana cewa "Idan kudin ya taru da yawa kai ma sai in biya maka tunda ka taimakeni koh?" Ya d'an kalleta da sauri sannan yace "Haba?" Tace "Ehh, ko kuma in biya ma Umma" Murmushin gefen baki yayi yace "Ashe na taimake ki?" Tayi shiru tana kallonsa, sai kuma ta gyada masa kai a hankali, Bai kuma cewa komai ba, kuma bai kalleta ba, jin tayi shiru bayan kusan minti goma sha biyar, breaking the silence yace "Bayan awaran da dankali babu wani sana'ar da xa ki yi?" Ya d'an kalleta da yaji bata amsa masa ba, bacci yaga tana yi, xuwa lkcn sun fara fita outskirt din garin kano, ya kai hannu a hankali ya kwantar mata da kujeran motar, snn ya kara Ac din motar, har suka shigo garin kaduna bayan magrib bacci take, amma ta farka yyi sau biyar a hanya, mai gadi na bude masa gate yayi parking a parking space, ya sauka motar yana stretching kansa, coz he is very tired bayan tukin jirgi ga na mota, jingina yayi da motar ya rungume hannunsa, har ya mance rabonsa da workout, tun sanda burden din Jiddah ya hau kansa, xagawa yyi ya bude side dinta ya bubbuga motar slowly, a hankali ta bude ido ta fara kalle kallen inda suke, yace "Sakko" sauka ta fara yi daga motar ya koma gefe tana fitowa ya kulle motarsa. Bayan sun shiga gidan xata wuce dakinta yace "Ki tabbatar kinyi sallah" Wanka jiddah tayi sannan ta dauro alwala bayan ta idar da sllh ta saka kayan baccinta ta kwanta. Karfe tara ya shigo dakin da abinci, tunda ya kalleta sau daya ya dauke kai, kawai ya ajiye ledan ya fita. Washegari da ya kasance ranan juma'ah Jiddah na idar da sallan asuba ta sauko kasa ta hada shayi ta dumama abincin da ya kawo mata jiya da daddare ta wanke tukunyar da ta bata ta koma dakinta, duk kafin ya shigo gidan daga masallaci, don sai ya gama azkar dinsa yake shigowa gida, bata mance warning din da yayi mata ba, ganin har karfe sha biyu Abuturrab dake xaune parlor bai ga ta sakko ba, lkci lkci kuma ya ke kallon sama, daga karshe ya mike ya haura stairs din sannan ya bude kofar dakinta, bacci ya sameta tana yi, yayi knocking kofar da karfi wanda hakan ya farkar da ita ta mike xaune da sauri, ya wani daure fuska yace "Baki da hankali har yanxu bacci kike?" Tace "Aa nayi wanka na gyara dakin" Ganin hararan da yake mata ta dauke kanta, yace "Ohk kin fi so ki kwanta daki kullum in fita in siyo maki abinci in kawo maki anjima kice ai bani da kudi?" Buda baki tayi tana kallonsa tace "Ni yaushe nace baka da kudi?" Ya rungume hannunsa yace "Jiya a mota" Tace "Aa ni fa kudin jirgi nace baka da shi tunda ya kai miliyan daya, kuma kace min Abbanka ne ya biya ai ko??" Yace "Ehh abincin da kike ci ma ai duk shi yake siyowa in kawo maki ko" Tayi shiru tana kallonsa, can tace "Toh me yasa baka son kayi sana'a, kaga Umar yana fita kasuwa kullum, don kawunsa na da shaguna uku a kasuwan bacci..." Kallonta yake ko kiftawa baya yi, tace "Kai ma xa ka iya ce a neman maka waje a kasuwa tunda Abba na da kudi ae" Ya shafa fine beard dinsa yace "Haka ne kuma, amma ya aka yi kika san bana sana'an komai" Ta sakko da kafafuwanta daga saman gadon tace "Naga to ko da yaushe kana gida, idan baka son ka xauna a gidan kuma sai ka tafi kano, to ko sana'a kake xuwa yi a kanon?" Ya girgixa kai da sauri yace "Can ma kawai xama nake a gida, ai ba a bani sana'an da xan yi ba" Tayi shiru, sai kuma ta kallesa tace "Amma lkcn da kake xuwa hayin rigasa a ina kake samo wannan kudin da kake bani in ba Babarmu?" Yace "Abbana ke bani" Tace "Toh, shkkn" Yace "Yanxu kasuwan xan fara xuwa nima kenan" Tace "Eh ka gaya ma Abbanka ya bude maka shago" Yace "Sai ni dake mu dinga xama a ciki ko?" Kallonsa tayi ta fashe da dariya sosai dimples dinta na lotsawa, ya dinga kallonta, second time da yake ganin dariyarta kenan, tayi me isarta tace "Dama mata na xuwa kasuwa?" Ya rungume hannunsa yana kallon large eyeballs dinta yace "Tunda xa su iya xaman gefen titi su siyar da awara da dankali me xai hana??"



*Toh Chamo dai tace banyi addu'ar Allah yayi min katangan rodi with some set of readers ba, duk da dai ra'ayinsu suke 6a6atu a kai nd they are entitled to der opinion, but oh God do not allow me to be seeing der comments so that i can write happily till end without mind spoilage Ameeeeenn* 🫣 to those of u reading my book for free know that u owe me dari biyar kacal ehe... 😚




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems


Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada


Instagram -fareeskinglow_89

TikTok-fareeskinglow

Facebook page-fareeskinglow 

WhatsApp -08031898240

Jiddah ta langwabar da kanta tace "Ai ban sani ba, in dai mata na xuwa sai mu dinga tafiya tare" That wasn't were Abuturrab wanted the conversation to end, but because of how cautious he was with time sbda sllhn juma'ah, ya kalleta kawai yace "Kafin in dawo masallaci ki tabbatar kin sake wanka kin shirya cikin atamfa, sannan ki karya..." Sae kuma ya hade rai, Ta sauke idonta kasa tace "Ni na karya da asuba ai" Daga sama har kasa ya kalleta sannan ya juya ya fita ta bi sa da kallo.... Ko da ya dawo juma'ah har ta shirya kamar yanda yace mata, Hijab ya sa ta daura kan atamfar, bayan ta sauko ta tsaya tana kallonsa, sau daya ya kalleta ya dauke kai yace "Fita ki jirani a waje" Ba musu ta nufi kofa ta fita daga parlon, sae a sannan ya tashi ya kashe appliances din gidan ya dau makullin motarsa da hulansa ya fita, the ride was silent har suka iso gidansu, gaba daya he was absentminded, yau da safe ma kiran Aunty ne ya tashe sa, har sannan kuma ya ki daukan kiranta, then is he even suppose to go home now? bai yi parking a kofar gidansu ba in case of necessity, ya juya yana kallon Jiddah yace "Ki jirani" Bai jira tace komai ba ya bude motar ya sauka....  Da murmushi Abuturrab ya amsa gaisuwan mai gadinsu ya shiga cikin gidan, sosai ya ji hankalinsa ya kwanta da kanninsa suka ce Aunty ta fita, Yana kallon Ramlah yace "Ina ta tafi?" Ramlah tace "She left for Abuja this morning" Shiru yyi yana kallonta, can ya nufi parlon Umminsa, ganin bata parlon ya fito, ganin ya nufi kofar fita Ramlah tace "Ummi na bedroom fa" Bai tanka ta ba har ya fita, tare ya dawo cikin gidan da Jiddah, murmushi kawai tayi ma su Ramlah da suka gaisheta, ta bi bayansa xuwa parlon Mahaifiyarsa, kafin yace mata komai ta xauna a kasa, ya karasa cikin bedroom din Ummi da sallama, gaisheta yayi da ladabi, ya shafa kansa yace "Ummi xa ku gaisa da ita a parlor" Ummi tace "Ohkk" Mikewa yayi ya fito parlon, ya xauna kan kujera, ba a dau lkci ba Ummi ta fito, jiddah ta sunkuyar da kanta ta gaisheta, Ummi ta amsa da murmushi fuskarta tace "Ya ku ke?" jiddahh tace "Lafiya lau" Ummi tace "To madallah, sannun ku da xuwa" Ummi dake kallonta kasa kasa ta ga ta canxa mata sosai, haskenta na ainahi ya fito ga wani glowing da take yi, Shi dai Abuturrab danna wayarsa kawai yake, jin Umminsa bata kuma cewa komai ba ya daga kai ya kalleta yace "Ummi wai Aunty ta tafi Abuja?" Ba tare da ta kallesa ba "Ai na xata xaka fi kowa sani tunda kun fi kusa" Ya sunkuyar da kansa yace "Aa bamu yi magana ba" Ummi tace "Ayyo" yace "Yaushe tace xata dawo?" Ummi tace "Baka da lambarta ne?" bai kuma cewa komai ba kuma bai dago ba, Jiddah dai sai kallon Ummi take, Bayan few seconds Abuturrab ya dago yace "An kawo lefen Ramlah ne?" Ummi tace "Bakwa magana da Ahmad din ne?" Yace "Shekaranjiya mun hadu a Abuja da na sauke jirgi a airport din can" Da sauri Jiddah ta kallesa, suka hada ido ya hade girar sama da ta kasa yana kallonta, turo baki tayi, Ummi dai tv kawai take kallo, Ya dauke kai yace "Amma yace min xai shigo kadunan yau, kilan xanje daukosa a tashan jirgi anjima" Ummi tace "Allah ya kawosa lafiya" yace "Ameen" Ummi tace "Idan kaga xaka iya sai ka bar ta nan har bayan bikin, tunda ranan talata xa su fara shagalgulansu" Abuturrab ya d'an yi shiru, can ya daga kai ya kalli Ummi yaga kallonsa take, suna hada ido tace "Ranan bikin sae ka kawota" Da sauri yace "Aa Ummi gobe xan kawota tunda bata xo da kaya ba" Ummi tace "Aa a bari ranan bikin dai" Yace "Uhn xan kawota goben in sha Allah" Ummi tace "Baxa ka siya mata ankon bikin ba?" Ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Nawa ne?" Ummi tace "Kala uku ne, daya na family, sai general one da xa a saka ranan yini, sai kuma na dinner, although naji yan matan sun fidda wani da xa su saka ranan talata" Yace "Nawa ne duka" Ummi ta hada masa kudin gaba daya tace "Gaba daya 40k ne" Yace "A dinke xa a siyo kayan?" Ummi tace "Ehh, da yake kayan dama a kyauta aka samosu daga kasuwa, iyakar kudin dinkin ne dubu arba'in" Abuturrab ya bude ido ya fara dariya yace "Ummi tambaya fa kawai nayi" A takaice tace "Nima amsa na baka" Ya shafa kansa yana murmushi bai ce komai ba" Ummi na kallon Jiddah tace "Su Ramlah na can daki kije ki samesu tunda naga baki son magana" Tayi murmushin karfin hali ta mike ta nufi kofa, Abuturrab ya mike yace "Ai bata san dakin ba, i will back Ummi" Da ido kawai Ummi ta bisa da kallon mamaki har suka fita. Dakinsu Ramlah ya kai ta, Ramlah na xaune da Siyama sai wata kawarta da Aisha step sis dinta, tana ganin Jiddah ta mike tana welcoming dinta da fara'a, bai amsa gaisuwan yan dakin ba banda na kawar Ramlah da bai sani ba, sannan ya juya ya fita ya koma bangaren Umminsa....


 Karfe hudu saura yace da Ummi xai je dauko Ahmad a train station, Ummi tace "Toh Allah ya tsare" Yace "Ameen" Daga haka ya fita daga parlon, dakin su Ramlah ya nufa, Jiddah na xaune tana ma Siyama tsifa, su Ramlah suna ta labari a dakin ganinsa duk suka yi shiru, yana kallon Siyama yace "Ke tsifan sai an maki??" Tayi dariya tace "Ita tace ta xata min Yaya" Yana kallon Jiddah yace "Kinci abincin ko baki ci ba?" Ramlah tace "Yanxu muka gama cin abincin fa yaya" Wani kallo ya jefa mata yace "Nayi da ke?" Bata kuma cewa komai ba, yana kallon Jiddah fuska daure yace "Tambayar ki nake" Tace "Mun ci" juyawa yayi ya fita, Sai da Ramlah ta tabbatar ya tafi don har sai da taje ta d'an bude kofar taga babu kowa wajen sannan ta dawo tana kallon jiddah da murmushi tace "Yaya yana ji dake kamar yanda yake ji da profession dinsa..." Jiddah dai bata ce komai ba ta ci gaba da tsifar da take.... Bayan kusan awa daya da tafiyar Abuturrab Aunty ta dawo gidan, alamar dai ita ma train din ta biyo daga Abuja ta dawo, tun da ta kyallara ido taga Jiddah taji kamar taga mugun abu a gidan, ko gaisuwar Jiddah bata amsa ba, bata sake shiga damuwa ba sai ganin wani haske da kyan da Jiddah tayi alamar kwanciyar hankali, ita Abuturrab xai raina ma wayo?? Ta kusa minti ashirin xaune gefen gado a dakinta, ta saka wannan ta kunce wnn, ita Abuturrab ke son kunyatawa gun aminiyarta? Takanas ta shirya yau ta tafi Abuja ba mahaifiyar Aneesah hakuri bayan sun sanar mata abinda Abuturrab din yyi ma Aneesah a airport kamar yanda Aneesan ta gaya ma uwarta... Wani murmushi Aunty tayi tana gyada kai. Jiddah na ta xaune parlorn Ummi ita kadai don su Ramlah da yan matan gidan sun fita xuwa gun tailor, Ummi kuma ta hanata bin su tace mijinta bai sani ba, Jiddah na ta juya furucin Ummi a kanta, wai mijinta, ai ba mijinta bane Aliyu, tunanin hakan kawai sai taji jikinta yayi sanyi sosai, Ummi ce ta fito daga dakintaz ganinta xaune ita kadai tace "Ki shiga kitchen kiga ko aunty na ciki ki tambayeta abinda xa ki kama mata Jiddah" Jiddah ta kalli Ummi a hankali tace "Toh" Mikewa tayi ta fita bangaren Ummi, tayi hanyar kitchen din, jikin kofa ta tsaya tana lekan kitchen din don ita har taji tana tsoron matar nan da ake ce ma Aunty, ganin Auntyn a ciki, cikin sanyin murya tace "Aunty me xan kama maki wai?" Juyawa Aunty dake yankan cabbage tayi tana mata wani irin kallo tace "Me xa ki kama min?" Jiddah ta gyada mata kai gabanta na faduwa, Aunty ta ajiye wukan hannunta ta kunduma mata xagi tace "Ke a wa xaki kama min aiki?? Yanda kika samu wajen xaman yin iskanci gidan Aliyu kin xata nan ma haka ne, toh bari kiji... Wllh ki saka a ranki cewar xamanki ya xo karshe a gidan Aliyu, sai dai ya dinga bin ki can kauyen naku yana iskancin da yake dake, yau xai san ni mahaukaciya ce wllh" Jiddah dai kallonta kawai take a ranta tana kara nanata kalmar da ta jefa mata wai iskanci, tana nufin iskanci suke yi da Aliyun kenan? Muryar Aunty ya sake dawowa da ita, ciki tsawa tace "Baxa ki fita ki bar min kitchen ba mayya...." Cikin sanyin murya Jiddah tace "Ni ba iskanci muke yi ba wllh...." Aunty ta fixgi roban cabbage din gaba daya ta watsa mata ranta bace ta kunduma mata xagi tace "Kina shige da karuwar xaki ce min ba iskanci ku ke ba, dama mace da namiji na xama gida daya tare babu aure? Fita ki ban waje kada in fasa maki ido algunguma" Jiddah da ta rufe idonta da hannunta taji kuka ya taho mata ta juya da sauri ta bar kitchen din jikinta duk cabbage da suka makale, dai dai nan Abuturrab ya shigo parlon, durkusawa tayi nan parlor ta fara kuka kamar an aikota, kallon hanyar kitchen din yayi yaji muryar Aunty tana cewa "Sai yanxu na ke sake yarda cewar da gangan yayi komai da ya faru, har sabida ke xai walakanta min Aneesah, to in dai nice wllh xai sha mamaki, ba mu xai kawo ma gayyar tsiya family ba..." Karasawa yayi gun Jiddah ya dagota, kuka kawai take ya kakkabe jikinta ya kama hannunta suka fita parlon, nan balcony ta saka takalminta sannan suka fita compound xuwa gun motarsa, har suka bar layin kuka take kamar xata shide, ya hade rai yace "Ya isheki haka nan, me yasa baki tsaya kitchen din kin mata kukan sosai ba?" Bata ce komai ba ta hade kanta da gwiwa tana shessheka, har suka isa gida hawaye na xuba idonta, bayan yyi parking yana kallonta yace "Baki ji ki daina kukan ba?" Ta dago kai cikin rawan murya tace "Ce min tayi wai muna yin iskanci fa" Ya dinga kallonta kafin yace "Da wa ku ke yin iskancin" Cikin kuka tace "Wai kai" Dauke kai yayi da farko, can ya juyo yace "Ai ban san wani irin iskanci take nufi ba" Tana hawaye tace "Tace iskanci muke yi da kai a gida" Ya buda ido sosai yace "Toh fa, ni iskancin da na sani shine ace mutum bashi da kirki ko baya jin maganan mutane..." Da sauri Jiddah tace "Ba shi bane" Yana kallonta yace "Toh wanne ne?" Cikin rawar murya tace "Kilan ta xata kana ta6a ni" kallonta ya dinga yi, can ya kai hannunsa ya kamo nata yana caressing dinsa gently yace "Haka take tunani?" Da sauri Jiddah ta janye hannunta ta saida kukan tana kallonsa, ya daga kafada yace "Don an kama hannun mutum shine iskanci?" Ta girgixa kai tace "Tayi tunanin muna kwana a daki daya" Yace "A kano ba a daki daya muka kwana ba? Sai ace wannan iskanci ne" wasu hawayen suka sauko mata tace "Aa ba haka ba" Yace "Toh ya ne?" Tana goge idonta tace "Tana tunanin muna kwana waje daya" Yace "Toh me ake yi idan an kwana waje daya da ake kiransa da iskanci" Kin cewa komai tayi, ya bude motar ya sauka, ya nufi cikin gidan, bude motar tayi ita ma ta bi bayansa tana goge idonta, Tun da ta shiga dakinta bata fito ba har bayan isha, ita iskancin da Aunty tace take yi ne ya tsaya mata har da ce mata karuwa, wanka kawai tayi tasa rigar baccinta ta shige cikin duvet da ta tuna sai taji hawaye ya taho mata. Karfe tara ya bude kofar dakinta, duk da tana ji bata motsa ba, ya isa inda take ya bude bargon, suka hada ido hawaye ya gani idonta, yace "Ohk kukan kike yi har yanxu kenan" ta gyada masa kai wasu hawayen na taruwa idonta, yace "Saboda ance kina iskanci kike kuka har yanxu" ta mike xaune ta hade kanta da gwiwa tace "Toh ni ae ban ta6a iskanci da kowa ba" yana kallonta yace "Toh ae gwara kawai kiyi ki san kinyi ko?" ta dago kanta da sauri tana kallonsa, ya rungume hannunsa shi ma yana kallonta, tace "Inyi iskanci fa kace" yace "Ehh, ko hakan xai sa abun ya daina damunki, kinga kinsan kinyi kenan ko an fada baxai maki ciwo ba" Ta wani ja gefe daya ta hade rai tace "Allah ya kiyaye ni ba yar iska bace" Dariya ta basa, amma bai yi ba, yace "Amma ko jiya kin kama hannuna ai" da sauri ta juyo a tsorace tace "Ni??" Yace "Ehh" ta hade rai ta hararesa tace "Ni ban ta6a haka ba wllh" karasawa yayi daya side din da take yace "Ni kike harara haka?" Saukowa tayi da sauri ganin ynda ya hade rai tace "Ni ban harareka ba wllh" Ya fixgo hannunta tana ganin haka ta rufe fuskarta a jikinsa tace "Don Allah kayi hakuri ni ban harare ka ba" daga sama har kasa yake kallonta, ya d'an rufe ido sae kuma ya rungumeta tightly to himself yace "Yanxu me ake kiran wannan?" Kwace kanta take son yi amma ta kasa yana jin ynda xuciyarta ke bugawa kamar yanda nasa ma ke bugawa, lkci daya kuma ya saketa, ta juya da sauri ta bar wajen, a mugun tsorace ta juyo tana kallonsa, ba tare da ya kalleta ba yace "Kinga maganar Aunty ya fito, don haka idan tace kina iskanci kada ki sake damun kanki tunda gashi har rungumeni kika yi ynxu, ko bayan wannan akwai wani abu da ake kira iskanci?" Juya masa baya tayi xuciyarta na bugawa sosai, daga sama har kasa ya dinga kallonta, riga ne da wando red color na bacci a jikinta rigar ce kadai barrier din skin dinta, dauke idonsa yyi ya nufi kofa ba tare da ya kalleta ba yace "Ki sakko kasa ki dau abincin ki, kuma kar ki yrda in dawo baki sakko ba" daga haka ya fita, ta bi sa da kallo har sannan xuciyarta na bugawa, bayan kusa minti goma sbda tsoron kada ya dawo kamar yanda yace, ta dau Hijab dinta a sanyaye ta saka har kasa sannan ta sauka, kanta a kasa ta shigo parlon, ta durkusa jikin kujera taki kallonsa a hankali tace "Ni ba yunwa nake ji ba, naci abinci a can gidan" Yace "Koh?" Bata ce komai ba, kuma bata dago kanta ba, ganin ya mike ita ma ta mike da sauri tana kallonsa, da alamar ta tsorata da shi, dariya ta basa amma ya fuske yace "Ohk, da ni mijinki ne haka xaki dinga yi idan na ta6a ki??" Ta kasa ce masa komai, yace "Ki bani amsa" Ba tare da ta kallesa ba tace "Toh ai kai ba mijina bane" Kallonta kawai yake yi, can yace "Toh amma mijin na ki baxa ki dinga yi masa haka ba ko" A takaice tace "Nima ban sani ba" yace "Dauki abincin ki" tace "Na koshi" yace "To tafi" juyawa tayi ta wuce sama, ya bi ta da kallo, xaunawa yyi ya jinginar da kansa jikin kujera, daga karshe ya dau wayarsa ya kashe wutan parlon ya wuce sama xuwa bangarensa ya kwanta, Aneesah ya shiga kira, sai da ya kusa katsewa ta daga amma bata ce komai ba, yyi lumshe ido yyi kasa da murya yace "I know i did what is uncalled for, but... I hope u aren't among d set of pple that believe ban saketa ba ko?" Tace "How will i believe you Aliyu bayan abinda ka min a kanta jiya?" Ya kwantar da murya yace "What if na auroki kika shigo gidan kika gani ma idonki cewar ba matata bace?" Tace "Then i will believe u 100%" Yace "Ranan juma'ah daurin auren Ahmad, kafin uncles dinmu su koma xa a kawo gaisuwa da kudin saka ranan gidanku ranan lahadi in sha Allah" Kamar xata yi kuka tace "Are you for real Aliyu?" Yace "Sure" Farin cikin da Aneesah tayi a lkcn baya misaltuwa, lkci daya duk ta mance abinda Aliyu yayi mata jiya, amidst d joy yace "I am missing you seriously, vid call?" Tace "Sure, amma kar ka wani kashe wuta" yace "I have to" bai jira cewarta ba ya katse wayar ya kashe switch din dake kusa da gado sannan ya shiga kiranta vid call.... Washegari Abuturrab na dawowa masallaci ko azkar bai tsaya yayi ba ya  dawo gida a stairs suka kusa cin karo da Jiddah xata sauka kitchen, da sauri ta juya masa baya don bata sa hijab ba, bata yi xaton shigowarsa a lkcn ba, ta koma sama da sauri ta shiga dakinta, bangarensa ya nufa ya shiga daki ya kashe wuta ya kwanta. Kiran Ummi ne ya tashesa wajen karfe takwas da rabi, ya jawo wayar a hankali ya daga coz she's been calling him since yesterday har ma da Aunty, ya kai kunne hade da sallama, Ummi tace "Don walakanci Jiya ka dawo ka tafi da Jiddah babu sallama??" Ya mike xaune da sauri yace "Ummi yau xan kawota dama, bak'i nayi a gida..." ummi tace "Good!!!Abbanka na nemanka, kuma ka taho tare da Jiddar, ba jiran ka xai yi ba, karfe goma xai fita yace" Daga haka ta katse wayar, sosai ya ji gabansa ya fadi, Abba calling him for what? Kallon agogo ya sake yi sannan ya ajiye wayar ya lumshe idonsa yana jin xuciyarsa na bugawa, bayan minti goma ya mike ya shiga bathroom. Tara da minti goma ya fito daga bangarensa cikin kananun kaya, ya tsaya bakin kofar jiddah for some seconds kafin ya bude kofar a hankali, gyaran daki ya sameta tana yi, ta sunkuyar da kai, ganin ta shirya yace "Dauko hijab din ki" Daga haka ya juya ya fita, karasa gyaran dakin tayi sannan ta sa hijab din ta fito. Throughout the ride hankalinsa baya jikinsa, sai da yaga sun kusa gidan ya kalleta rasa abinda xae ce mata yyi har suka shiga gidan, parlon Abba ya nufa direct tana biye da shi a baya, yana sallama aka yi masa izinin shigowa, shi ya fara shiga sannan ta shiga, Aunty na xaune parlon tare da Ummi da Umma, kamar dai xuwansu ake jira, ya ji gabansa ya fadi sosai, xaunawa yyi kasa, jiddah ta xauna side dinsa a hankali, ita ta fara gaishesu cikin sanyin murya sannan shi ma ya gaishesu, Abba gaisuwanta kawai ya amsa, yana kallon Abuturrab babu yabo babu fallasa yace "For how long have u divorced her Aliyu??"



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you





Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems


Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada


Instagram -fareeskinglow_89

TikTok-fareeskinglow

Facebook page-fareeskinglow 

Abuturrab ya buda ido sosai yana kallon Abbansa gabansa na faduwa yace "Divorce kuma Abba?? Why will i do so bayan kayi instructing dina kar inyi haka? Ni ban saketa ba Abba ga ta ka tambayeta, idan na saketa ae baxa mu xauna tare ba.. " Ba Aunty da ta bude baki tana kallonsa ba, har Jiddah kallonsa take da mamaki, Ummi dai wani direction din daban take kallo, Umma kam duk jikinta a sanyaye yake jin batun nan da ya tasheta da sassafe, Abba kansa ya kasa cewa komai, Aunty ta saki salati tace "Yaushe ka fara karya Abuturrab? Yaushe ka dawo makaryaci? Bakina da naka kace min ka saki yarinyar nan tun ranan da ku ka tare shine xaka karyata ni yanxu a nan?" Ya girgixa kai a hankali yace "Ban karyata ki ba Aunty, kawai na gaya maki haka ne saboda hankalinki ya kwanta tunda naga baki son auren, amma ni ban saketa ba, bana son abinda xai sa ki dinga damun kanki shi yasa na fada maki haka" Bude baki tayi tana kallonsa, yayi kasa da murya yace "Abba ga ta nan ku tambayeta ni ban saketa ba, I'm saying nothing but the truth" Jiddah ta sunkuyar da kanta daga kallon da take masa duk jikinta yayi sanyi, Abba kam ya ma rasa abun cewa, Can Ummi na kallon Jiddah tace "Jiddah" dago kai Jiddah tayi ta kalleta, Ummi tace "Ki fada min gaskiya Jiddah, Aliyu mijinki ne a yanxu ko ba mijin ki bane?" Gabanta ya dinga faduwa taji hawaye ya kawo idonta, Abuturrab ya gyara xamansa shi ma gabansa na faduwa sai dai bai kalleta ba, a hankali tace "Mijina ne Ummi" Aunty taji kamar ta rusa ihu a wajen lkci daya idonta yayi jajir, Abuturrab ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciyar relieve, Abba yace "Shkkn, Allah ya rufa asiri, u can leave now Aliyu" Abuturrab ya mike ba tare da ya kallesu ba yayi masu sallama, ita ma ta tashi ta sallamesu sannan ta bi bayansa tana goge hawayen idonta, Umma ta bi su da kallo xuciyarta na kokwanton amsan da Jiddah ta ba yar uwarta, this isn't joking matter, she needs to investigate deep into this issue... Aunty ma ta bi su da wani kallo sai kawai ta saki kuka kamar warce aka sanar ma sakon mutuwa, ita Abuturrab xai yaudara, ita xai karyata, ita xai watsa ma kasa a ido, ita xai kunyata gaban kowa?? Ko minti daya Abuturrab bai kara a a gidan nasu ba ya wuce da Jiddah, bai ce mata komai ba ita ma haka har suka iso gida bayan ya siyo masu abinci a hanya, parking yyi a compound dinsa, sai da ya sauka sannan ita ma ta sauka motar, ya mika mata ledan abincinta yana kallonta, kin amsa tayi hakan yasa yyi wucewarsa ciki da ledan ya bar ta tsaye a wajen, xaunawa yyi kan kujera a parlor ya jinginar da kansa da kujeran ya sauke ajiyar xuciya feeling relieved, sai bayan kusan minti sha biyar ta shigo parlon, xata wuce sama yace "Xo nan" Ta ki tsayawa har ta wuce, ya bude baki yana bin ta da kallo. Through out ranan jiddah na daki shi kuma yana downstairs, bai bi ta kanta ba har after isha, bayan ya dawo mosque ya dai ga alamar tayi making tea a kitchen, yana haurawa sama ya tsaya kofar dakinta sai kuma ya bude slowly, xaune ya ganta idonta yyi ja, ya kulle kofar dakin yana kallonta, yace "An maki wani abu ne kike ma mutane kuka tun safe?" Ta ki kallonsa, a d'an tsawace yace "Ba magana nake maki ba?" Ta juya masa baya, rungume hannu yyi yana kallonta, can yace "Kuka kike saboda kina tunanin kinyi musu karya?" Ta juyo tana kallonsa cikin rawan murya tace "Ehh mana, me yasa xa ka masu karya??" Yace "Ohh da na masu sai nace ke ma kiyi masu??" Kallonsa ta dinga yi ko kiftawa babu, ya karasa ya tsaya gabanta yana kallonta da kyau yace "Ni ai ban aike ki kiyi masu karya ba... sannan akwai wani abu na musamman da ke sa mutane su yarda cewar mata da mijinta ne ke rayuwa a cikin gida? akwai wani abun da xanyi da xai tabbatar da cewar ni da ke mata da miji ne? Ko bana ciyar da ke yanda miji ke ciyar da matarsa ne? Ban baki sutura ba? ban baki wajen kwana ba? ban baki kariya ba? Ina ce duk wannan shine abinda miji ke ma matarsa? Ko akwai wani abu daban da ban sani ba ki sanar da ni nima in maki don xaman namu yayi kama da na mata da miji a daina xargin mu..." ta dauke kanta tace "Idan mun yaudari mutane ai Allah shi yasan gaskiya, kuma ai kai ma kasan ni ba matarka bace nima kuma nasan kai ba mijina bane" Kallonta kawai yake yace "Toh meye shaidan hakan?" Tace "Ai kai ma kasani, meyasa baxa ka fada masu gaskiya ba, sannan ni ka bani takardan in ajiye wajena tunda baka aikeni inyi karya ba" durkusawa yyi yana kallonta yace "Haba?" Tace "Ehh" yace "Toh ko dai in fara maki abinda masu aure ke yi, kilan hakan xai sa ki fara rage tunanin ai ni ba mijin ki bane, infact mancewa ma xaki yi cewar babu aure tsakaninmu, takarda kuma da kika ce... Mu je in baki ki ajiye wajen ki" mikewa yayi still yana kallonta, ta k'i tashi, ya hade rai yace "Mu je ki amsa nace" mikewa tayi a hankali, ya nufi kofa ta bi bayansa xuwa bangarensa, suna isa ta tsaya bakin kofar babban parlon, ganin bata shigo ba yace "A bakin kofa xan baki takardan?" Shigowa parlon tayi taga ya nufi bedroom dinsa yana isa ya tsaya bakin kofa ganin bata karaso ba yace "Shigowa xa kiyi ai malama" daga haka ya shiga cikin dakin, a hankali ta bi bayansa tana shiga ya kulle kofar, ta makale jikin bango tana kallonsa, sanyi sosai ne a dakin sbda Ac dake aiki, ya nufi gaban mirrow ya dau diary dinsa ya bude sai ga takarda well folded ya ciro a ciki yana kallonta ya mika mata yace "Gashi" Ta sauke kanta kasa kamar baxata je ba sai kuma ta karasa ta sa hannu xata amshi takardan ya fixgota, kara tayi a tsorace ta fara kokarin kwace kanta, yace "Saboda ina tsoronki xan baki? And.. ina ruwanki da rashin auren dake tsakaninmu, ci kika rasa ko sha??" Gaba daya a tsorace take, kamar xata yi kuka tace "Kayi hakuri don Allah...." Yace "Baxan yi ba" a hankali ta daga kai ta kallesa, saketa yyi ya tafi gaban madubi ya ajiye takardan sannan yace "Idan kin isa ki dauka ki fita" Yana fadin haka ya nufi kofa ya bude ya fita ta bi sa da kallo har ya kulle kofar, a hankali ta isa gaban madubin ta dau takardan ta warware tana dubawa, takardan ne kuwa, in accord to the content of d paper, he is no longer her husband, duba diary din tayi taga ba a ciki ya falli takardan da yayi rubutun ba, wajen mirror din ta dinga dubawa nan taga takardan da ya cira a ciki, ita ma ta cira sannan ta mayar da sauri ta ajiye, linkewa tayi yanda ya linke na rubutun ta ajiye gaban madubin sannnan ta dau wanda rubutu ke jiki tana tunanin inda xata boye, kana ganinta kasan a tsorace take, hularta ta saka hannu ciki taji gashinta is very oily, ta sake ciran wani sabon takardan ta nannade na rubutun a ciki sannan ta tusa a cikin hulan ta koma inda take tsaye ta tsaya, bayan kusan minti goma sai ga shi ya shigo, sunkuyar da kanta tayi cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri baxan sake cewa ka bani ba kuma" Bai ko kalleta ba, ya ajiye sauran bottle water din hannunsa, sannan yace "Aa ki dauka dai, gashi can gaban madubin" Ta girgixa masa kai kawai, gun takardan ya nufa gabanta ya dinga faduwa tana kallonsa ko kiftawa babu, ya dauka, bata jira taga me xai yi ba har ta juya xata fita da gudu taji yace "Gashi ki tafi da shi" Juyowa tayi tana xare ido taga yana mika mata takardan, kallonta kawai yake, yace "Amsa nace" Ta karasa a hankali ta sa hannu xata amsa ya murda kunnenta yace "Tahowa kika yi xa ki amsa kenan" Bata fuska tayi bata dai ce komai ba, lkci daya taga yana bude takardan da gudu ta nufi kofa ta fice daga dakin ya bi ta da kallo ganin babu komai a jikin takardan, mamaki ne ya cikasa ya sake juya bayan takardan that is plain, Bude baki yayi with so much surprise, bai san lkcn da yayi murmushi ba ya rungume hannunsa, so tana da irin wannan wayon ashe, bai bi ta ba sabida yasan xa ma ta dawo ne, ya tafi gefen gado ya xauna, Jiddah ta jingina da kofar parlonsa ta xame kasa tana yarfe hannu, gaba daya a tsorace take, sai jiran fitowarsa take anytime amma har sannan bai fito ba, bin babban parlon ta dinga yi da kallo kamar xata hango makullin kofar, har bayan minti talatin bata gansa ya fito ba, gajiya tayi da xama a bakin kofar, ta mike a hankali tana leka kofar dakin nasa, can dai ta karasa bakin kofar ta leka ciki don kofar ba a kulle yake gaba daya ba, kwance ta gansa waya kare kunnensa, ta juya da sauri ta koma inda take xaune kamar xata yi kuka, har sha biyu saura Jiddah na xaune gefen kofar, bacci ne ya fara damunta, mikewa tayi ta tafi kan kujera ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa, can cikin dare taji ana lalubata, ta mike a tsorace ganin duhu a parlon tace "Wayyo Allah na" Muryarsa taji yace "Ina takardan yake" Jikinta ma rawa tace "Yana cikin hulana" Xata cire hulan ya rigata cirewa ya ga takardan a kanta ya dauka sannan ya saketa ya koma dakinsa ya kulle kofar, har lkcn gabanta faduwa yake ta mike xaune tana bin parlon da kallo don ko alamar haske babu, a hankali ta mike tana neman hanya har ta isa kofa ta murda taji a kulle har sannan, jingina tayi da kofar kamar xata yi kuka, can ta juya ta koma saman kujeran ta kwanta, nan da nan bacci ya sake dauketa, kiran sallan asuba ne ya farkar da Jiddah, ta tattaba lallausan abinda taji a jikinta, kofar daki aka bude da sauri ta rufe idonta don hasken dakin ya hasko parlon, tana ji ya bude kofar parlon ya fita, lkci daya kamshin turarensa ya gauraye parlon, sai bayan kusan minti biyar ta cire duvet din jikinta ta mike a hankali jin xa a tada sallah, ajiye duvet din tayi kan kujeran ta nufi kofa ta bude ta fita xuwa dakinta. Karfe takwas saura Jiddah ta farka daga baccin da ta koma bayan tayi sallan asuba, mikewa tayi ta shiga bandaki sai da tayi wanka ta wanke baki sannan ta wanke bandakin ta fito, tana gama shiryawa ta hau gyaran dakin, bude kofa aka yi ta juya da sauri, calmly yace "Ki sameni kasa" daga haka ya rufe kofar, ta gama abinda take sannan ta sauka kasa, yana xaune parlor yana kallo, agogon wrist dinsa ya kalla yace "Na baki minti talatin ki je ki dafa abinda xa ki ci...." tsayawa tayi tana kallonsa, ganin bata motsa ba ya daga kai ya kalleta, da sauri ta juya ta wuce kitchen din ya bi ta da kallo, indomie ta dafa ta ci a kitchen din ta wanke plate sannan ta fito, ya kalleta ya nuna mata karamin travelling bag dinsa da ya sauko da shi parlor yace "Ki je ki hada kayanki kala biyu da duk abinda xa ki bukata, kar ki bata min lkci, ki saka Jilbab idan xa ki sakko" A hankali tace "Ina za mu je kuma, amma ba jirgi xa mu hau ba ko??" ganin irin kallon da yake mata ta dau travelling bag din ta juya ta wuce sama, kayan nata ta hada sannan ta sauko kasa a sanyaye, Hijab ne har kasa jikinta, ya mike ya nufi kofa ta bi bayansa rike da jakar. Parking Abuturrab yayi kofar gidansu Ahmad, Jiddah ta juya ta kallesa ganin inda suka xo, wani farin ciki taji a ranta, bude motar yayi ya sauka, ita ma ta sauka ta bude back seat ta dau jakar kayanta, ai da ta san nan xa su xo da ta debi kaya da yawa, ganin ya nufi gate din gidan ta bi bayansa da sauri, gaba daya farin cikinta ya kasa boyuwa, sai kallon kofar Maman Abdallah take har suka shiga main parlor din gidan, Umma ta fito daga dakinta ganinsu tace "Aa daga ina haka kuma" Yayi kasa da kai yace "Daga gida Umma" nan ya gaisheta, ta amsa tana kallon Jiddah tace "Sannu da xuwa Jiddah..." Gaisheta Jiddah ma tayi tana mayar mata da murmushin, Umma ta amsa tana tambayarta ya gida, Jiddah tace "Lafiya lau" Umma tace "To kun ma karya kuwa wannan sammako haka?" Abuturrab yace "Eh mun karya, i brought her ahead of the wedding...." Umma da taji dadi har ranta don wnn shine right time da xata fahimci gaskiyan abinda Aunty ke fada tace "To maa sha Allah, that's very good" Yace "Kudin ankon kuma wa xa a tura ma?" Umma tace "Anko kuma?" Yace "Ummi ce tayi maganan ankon ran Friday" Umma tace "Kyale Ummi, ae ta riga ta mata, har dinki an bada" Yace "Toh Allah ya saka" mikewa yayi yace "Sai anjima Umma, xan wuce kano da yamma in sha Allah, ranan alhamis xan dawo" Umma tace "Toh Allah ya tsare, shi ma Ahmad din ranan laraba xai shigo..." Abuturrab yace "Ehh mun yi waya da safe, haka yace min" Ya d'an kalli Jiddah sannan ya nufi kofa yana ma Umma sallama, Umma tace "Toh baxa kiyi masa rakiya ba Jiddah?" D'an murmushi kawai tayi ta sunkuyar da kanta, Umma tace "Tashi ki je" a hankali ta mike ta nufi kofa ta fita, cike da kasaita yake tafiyar, ta bi sa da kallo, bin bayansa tayi har suka fita gidan, ya bude driver seat xai shiga sai kuma ya tsaya yana kallonta don makalewa tayi jikin gate, suna hada ido ta sauke nata idon, yace "Kina son wani abun ne" Ta d'an turo baki tace "Umma ce tace in raka ka" ya shafa kansa yace "Idan Umma tace ki shirya ku je can gidan kice mata baki jin dadi baxa ki iya xuwa ba" Tana kallonsa tace "Toh ka tayani gaya mata mana" ya daga kafada yace "Toh ki tafi ni ba ruwana" Daga haka ya bude motarsa ya shiga ya tada yayi reverse, a hankali ta juya ta koma cikin gidan, daren ranan Maman Abdallah na parlon Umma tare da mai aikin gidan suna ta hira, duk sbda Jiddah ta shigo kuma, sai kusan karfe goma maman Abdallah ta bar parlon, duk yan matan gidan na can gidansu Abuturrab, mikewa Jiddah tayi a hankali tayi ma mai aikin sai da safe ta wuce dakin da Umma ta sa ta ajiye jakarta, tuni Umma ta tafi ta kwanta tana tunanin where to start from coz ko kadan bata yarda da Jiddah da Abuturrab ba, Jiddah tayi wanka ta sauya kayan jikinta xuwa na bacci sannan ta kwanta. Washegari monday Jiddah ta taya Huraira mai aiki girkin breakfast, sosai ta sake a gidan ba kamar gidan su Abuturrab ba duk da Seeyama bata nan, Karfe sha daya na safe ta raka Umma kasuwa da driver, basu dawo gida ba sai kusan azahar, Jiddah na sallah ta kwanta don sun ci abinci a restaurant, da yammacin ranan Seeyama da Aisha da Safiyya suka xo gidan amsar ma Aunty sako wajen Umma, Seeyama tayi murnan ganin Jiddah a gidan, Umma tace "Sai ki shirya ki bi su Jiddah, idan na je anjima da daddare sai mu dawo tare" Shiru Jiddah tayi ta kasa ce mata komai, Seeyama tace "Ki tashi sister Jiddah Aunty na jiranmu" Mikewa Jiddah tayi a ssnyaye ta saka Hijab dinta, Driver Umma ta sa ya mayar da su can gidan saboda Jiddah, tun da suka sauka motar gaban jiddah ke faduwa ta dai bi bayan Seeyama rike da handbag dinta har suka shiga parlor, dai daikun baki ne da suka xo biki a parlon, Jiddah ta sunkuyar da kanta ta nufi bangaren Ummi, tana shiga parlon taga mata biyu a xaune, Xaunawa kasa tayi ta gaishesu, duk suka amsa, ba a dau lkci ba Ummi ta fito daga daki, ganinta tace "Daga ina haka, ina Aliyun?" Jiddah ta gaisheta sannan tace "Tare muka xo da su Seeyama" Ummi tace "Ohk toh ki shiga can ciki" mikewa Jiddah tayi ta wuce bedroom din Ummi, Hajiya Murja kawar Ummi tace "Kaddai ita ce matar Aliyun?" Ba tare da Ummi ta kalleta ba tace "Ehh ita ce" Hajiya Salaha tace "Allah sarki, ashe yarinya ce ma, toh Allah ya basu xaman lafiya, ga ta dai kamar ba sa wa ba hanawa" Ummi ta d'an yi murmushi kawai, Seeyama ce ta shigo parlon tace "Ummi Aunty Jiddah ta shigo nan" Ummi tace "Tana ciki" Seeyama ta shiga sai ga ta sun fito tare da Jiddah suka fita parlon, sosai gabanta ke faduwa tana tsoron kar ta hadu da Aunty har suka shiga dakinsu Ramlah, Ramlah na ganin Jiddah ta washe baki tace "Aunty Jiddah sannu da xuwa" Jiddah ta xauna tana murmushi tace "Ya gida" Ramlah tace "Lafiya lau, yaya fa?" Jiddah tace "Ya tafi kano" Seeyama tace "Shi sa ya kai ki gidan Umma?" Kai kawai Jiddah ta gyada mata. Suna nan xaune har aka kira magrib, bude kofar dakin aka yi Aunty ta leko tana cewa "Wai baxa ku fito kuje ku yi wanke wanken can ba dake bakin pampo gashi har anyi magariba, ko waye xai maku? Ai sai ku hakura xuwa gobe ku sakankance tunda nasan yan kauye masu wanke wanken xa su iso" Jiddah dake kan darduma ta sunkuyar da kai gabanta na faduwa, tsit Aunty tayi ganin Jiddah kan darduma, can tace "Ko da yake tun safe ai ku ke ta aiki, ke ya kike da suna??" Jiddah ta kalleta, Aunty tace "Ehh da ke nake kike kallona haka, tashi ki fita ga wanke wanke can bakin pampo kije ki wanke" Mikewa tayi da sauri, Seeyama ta mike tace "Ta barshi kawai xa mu yi aunty" Aunty ta jefa mata wani kallo tace "Toh ita xa ta yi, ku kuma xan aikeku yanxu tare da driver xa ku je min siyayya a supermarket" Jiddah ta nufi kofa ta bi gefen Aunty da ta bi ta da wani kallon tsana ta fita, kitchen Jiddah ta nufa ganin kofar kitchen din a bude ta fita taga uban kayan wanke wanke a bakin pampo ga omo da soso, ruwa ta tara ta fara wanke wanken, ba a dau lkci ba sai ga Aunty ta shigo kitchen din ta dinga fitar da plates wankanku tana ajiye su kan marasu wanki, ita dai Jiddah bata ce komai ba, har tukwanen sai da ta fitar da su sannan ta dau soson waya ta jefa mata tace ki tabbatar kin bi bayan tukwanen nan kin wanke su fess, xuwa gobe kuma xan san yanda xanyi da ke, daga haka ta juya ta koma ciki, Jiddah dai ta ci gaba da wanke wanken da take a sanyaye. Ba ita ta bar bakin pampon nan ba sai kusan karfe tara da rabi, duk ta gaji ga uban yunwan da take ji, bbu kowa parlon sai yara dake ta wasa, iyayensu kuma na can sama, Jiddah ta rakube jikin kujera tana jin kanta na mata ciwo, har ta mance rabon da tayi irin wannan aikin, tun bayan rabuwanta da Hansai, Aunty ce ta shigo parlon da sauri tana sanye da Hijab, har ta nufi kitchen sai kuma taga Jiddar a rakube a parlor, tana kallonta tace "Yauwa mu je ki rakani xan amso sako yanxu" 



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




*Mîkyããj_Sããdy Beauty Soap*





*Hy my beautiful people ina gaisuwa🙋🏻♀️ku karka'de kunnuwanku da kyau ku ji💃🏻ina mai sanar muku da cewa akwai gara6asa me kyau ta musamman ga wanda suka saba sayen sabulunmu da ma wanda zasu fara saya🥰, akwai ragin kaso 20% bisa dari 100% ga wanda suka saba saye, sannan akwai ragin 10% bisa ga masu sha'awar fara saye🥰, akwai farashi mai sauki ga 'yan sari, me yapi wannan dadi kam🤔ki sayi guda 4 kanana a baki kyautar daya, ki sayi guda uku manya a baki kyautar karami daya, ki sayi bucket biyu a baki kyautar babban rubber daya😍 kema da kike da burin saya ku'dinki bai kai ba😰to ga naki, ki kawo customers uku ki karbi naki kyautar Sabulun😍😍*



*Kawata 'yar 'kwalisa me kike jira,ita mace fa kullum cikim yin ado da 'kãwa take😍 ya kamata ki yunkuro wajen ganin kin rabu da wannan kurajen da tabo tabon fuskan nan haka🥺, kinga kema sai a saka ki a layin masu 'kwalisa da bajakolin ado💃🏻😍uwar gida a daure ayi gyaran jiki, sbd karbar goron a wajen me gida🥰,, ina amaren bayan sallah ku pito ku sayi naku Sabulun kuje kuyi ta wanaka hmmm 😍kamshi kawai zaku yi tayi kaca kaca😍😍, laushin fata Baja baja😃😂😂a yunkuro azo a karbi kayan gyaran jiki tare da sabulun gyaran fata a wurin _Mîkyããj_Sããdy_🥰*



*Duk wanda suka gwada Sabulun mu sun san babu 'karanta a ciki🥰in dai fannin gyaran jiki ne to sabulunmu shine amsarku,, shi ke mai da fata ta zama babu Pimples, Acne, Spot, Stretch Mark, da Duk wata matsala da ta shafi fata,, akwai lightening,  nd glowing😍*



_*In kina son jikinki yai su6ul da shi, fata tai santsi da sul6i, ki yi haske me aji, 'kamshi kaca kaca ko ta Ina, ki ta fresh abunki hankali kwance ki zama Wankan madara yauqin zuma😍💃🏻Anty madam😃To ki mallaki 3d (Extra Whitening Soap, Ko da kudinki sai da rabonki hajiyata)💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*_



*Akwai hadin:*

*Mai da tsohuwa yarinya*

*Uwargida ta koma amarya*

*Amarya ta koma tamkar 'yanmata*

*'Yan mata su koma 'yan dagwai²*

_Ga masu bu'kata sai su tuntu6emu ta kafar sadarwa kamar haka;_

_Call/WhatsApp:08061570778_

_IG@mik_yaaj_saady_

Mikewa Jiddah tayi tsaye tana kallonta, Aunty da har ta nufi kofa ta juyo ganin Jiddah bata biyota ba ta hade rai tace "Ba magana nake maki ba" Jiddah tace "Ban saka hijabi ba" Aunty tace "Nan nan ne ba nisa muje baxa ki rasa mayafi a tsakar gida ba" Jiddah bata ce komai ba ta nufeta, Umma ce ta shigo parlon da sallama, Aunty ta koma gefe tana yake tace "Sannu da xuwa Hajiya Ramlah" suka gaisa Umma tace "fita xa ki yi halan" Aunty tace "Ehh wllh sako xan amso nan bakin titi, da har nace mu je da Jiddan tace min Hijabinta na sama" Umma ta kalli Jiddah tace "Toh ki tafi saman ki dauko hijabin naki" Aunty tace "Aa bari kawai inje ae nan bakin titi ne" bata jira cewar Umma ba ta fice daga parlon tana jin wani mugun takaici, Umma ta kalli Jiddah tace "Kin ci abinci kuwa?" Jiddah ta girgixa masa kai, Umma tace "Toh saboda me, ke ba sai ki je ki diba ba, Ummi na sama ne?" Jiddah ta gyada mata kai, Umma tace "Mu je" Jiddah ta bi bayanta suka wuce sama, Bangaren Ummi suka shiga, bayan Umma ta gaisa da yayarta tace "Yaya wai bata ci abinci ba" Ummi ta kalli Jiddah tace "Ae nayi tunanin tana tare da su Ramlah ne, kuma an kai masu abinci tun daxu, taje can dakinsu ta diba" Umma ta kalli Jiddah tace "Ki je ki deba abincin a can" Juyawa Jiddah tayi ta fita, Umma na kallon yayarta tace "Naga kamar baki saki jiki da ita har yanxu ba yaya" Ummi tace "Aa ko daya, baki ganin ita ma ba maganar take ba" Umma tayi murmushi tace "Ae kam ni muna hira da ita" Ummi tace "Did u know what is baffling me Ramlah?" Umma ta girgixa kai tana kallonta, Ummi tace "Yanda Aliyu ya mayar da mu shashashai ya maida mu wasu 'yan yara, kinsan da gangan yaje yyi ma kansa aure da yarinyar nan?" Ummi tace "Me yasa kika ce haka yaya" Ummi tayi wani murmushi tace "Ai ni na haifesa ba shi ya haifeni ba, bai kuma isa yyi deceiving dina ba, he intentionally did what he did, abubuwan da nagani game da shi da yarinyar bai yi kama da abun da mutum yyi ba da son ransa ba, kinsan satinsa nawa rabonsa da gidan nan yanxu?" Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Nima ae ya daina xuwa min yaya..." Ummi tace "Toh yayi kyau... Xai gane bashi da wayo" Umma tace "Amma duk da haka akwai ayar tambaya fa a kan xaman da suke, don duk inda kika ji kishin kishin din magana da akwai kamshin gaskiya, ina jiran Ahmad ne yanxu inji matsayin auren nasu" Ummi tace "Ni ma dai nayi shiru ne kawai, amma ban aminta da xaman nan ba" Umma tace "Toh kin ga, don dama da bakinsa yyi ta cewa xae rabu da ita, na dinga hanasa tare da Abbansa to wa ya sani ko watsar da xancenmu yyi" Ummi tace "Ni kuma haka kawai naji ina son rabuwan nasu Ramlah" Umma dai tayi shiru bata ce komai ba, can ta sauke ajiyar xuciya tace "Allah dai yyi mana me kyau, kuma bana tunanin ya sa ta a karatu har yanxu, and she doesn't look happy always...." Ummi tace "Sannan ina ma son xanyi magana dake tun kwanaki, kinga lamarin rayuwar Aliyu? dama ina son in cire idanuwana da komai na a kai, sai yaje ya kara rike warce yake ganin ta fini daraja da hannu bibbiyu, ita yake ga xai iya komai na sirrinsa, ita yake ga xai fi ji da yarda da maganarta, to suje su karata, ni gaisuwan da yake min duk sanda yaga dama ma ce masa xanyi na yafe masa ya daina" Umma tace "Wannan ba magana bane yaya, tun farko ke kika xuba ido aka janye maki shi, Ahmad ya sha kawo min wannan same complain din, idan baki manta ba akwai wani lkci da na maki magana a kan hakan kika ce min ai ba komai duk daya ne, wnn mata ni ban ta6a ganin makira irinta ba..." Ummi ta girgixa kai tace "Aa ba ruwanta, ai shi ba yaro bane ya kuma mallaki hankalin kansa, he knows what is right from wrong, kawai dai hakan yake ga yafi masa alkhairi, sai yaje ya karata, amma ina dab da yi masa wankin babban bargo a gidan nan" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Ki dai yi hakuri yaya, Allah xai ganar da shi, wankin babban bargo kuma sai dai ki hada har Kishiyarki don munafuka ce" Bayan kusan minti talatin Umma ta gama abinda ya kawota, sallama tayi da yayarta har ta nufi kofa tace "Toh in tafi da Jiddar ne don can ya kai ta" Ummi tace "Aa wannan kuma ban sani ba" Umma tace "Naji xa su fita saloon gobe, kawai su tafi tare ita ma tayi gyaran gashin idan ya so ko driver sae ya maido min ita goben" daga haka tayi ma yayarta sallama ta fita dakin. Kwana dayan da Jiddah tayi gidansu Abuturrab ta fadi ma yan garinsu gashi gidan ya cika da mutane yan biki, Aunty tayi mugun saka ta gaba tun da garin Allah ya waye, ko wani aiki da aike ita ake sa wa, da ta xauna xata tasota gashi abincin kirki ma bata samu ta ci ba, da rana yan matan amarya duk suka yi shirin tafiya saloon, dama kafin Ummi ta lura da Jiddah balle har tace mata ta bi su, aunty ta hada kayan wanke wanke a bakin pampo ta turata taje tayi,  yawanci duk masu girki ranan sun xata ma mai aikin gidan ce Jiddah, ko mai aikin gidan bata yi aikin da Jiddah tayi ba tunda gari ya waye, cikin ruwan sanyi Aunty ke gallaza mata, duk tunanin Ummi kuma har da Jiddah aka tafi saloon don tun bayan da suka gaisa da safe bata ganta ba, a gajiye Jiddah ta fito daga kitchen wajen karfe hudu ga wani yunwa da take ji, wata tsohuwa ce ta mika mata purse tace "Yan mata ki kai min daki wajen Hajiya Hauwa ta adana min, kada a yasheni a gidan biki, dubu daya da dari biyar ce a ciki" Jiddah ta amsa tace "Toh" lkci daya Jiddah ta gane warce take nufi wato Ummi, bangaren Ummi ta nufa ta bude kofar parlon da sallama, Ummi da frnds dinta Uku ne a parlon sai wasu yan uwa guda uku, Jiddah ta gaishesu gaba daya, Ummi dai sai kallonta take da mamaki, Jiddah ta sunkuyar da kanta ta duka gefenta tana mika mata jakar tace "Ummi wai ajiya aka ce a kawo maki" Ummi ta amshi purse din tace "In ji waye?" Jiddah tace "Ai ban santa ba" Ummi tace "Dama baki je saloon din ba ke" Jiddah ta gyada mata kai kawai, Ummi tayi shiru tana son nuna ma yan uwan mai gidanta da kawayenta cewar ita ce matar Aliyu amma ta kasa, can dai tana kallon jiddah tace "Toh gobe sai a kai ki ke" a hankali Jiddah tace "Toh" daga haka ta mike, dai dai nan Abuturrab ya fito daga bedroom din Ummi, sosai gaban Jiddah ya fadi bayan sun hada ido, amma kuma sai taji dadin ganinsa ba kadan ba, duk yan parlon suka juya suna kallonsa, Ummi ma kallonsa tayi don tun daxu take fama da shi ya fito ya gaisa da yan uwan Abbansa su uku sun iso daga Damaturu amma ya ki fitowa wai ya gaji, gwara frnds dinta a parlon ya samesu da ya shigo, Hajiya Zuwaira ta rike ha6a tace "Dama Aliyu na ciki?" Ummi ta kirkiri murmushi tace "Eh bacci yake, saukansa daga kano kenan ko awa biyu ba ayi ba" Tuni Jiddah ta fita daga parlon, gaishesu Abuturrab yayi yana yake ya nufi kofa ya fita parlon Ummi ta bi sa da kallon mamaki har ya kulle kofar, har Jiddah tayi nisa yace "Keee" tsayawa tayi ta juya tana kallonsa, ya karasa inda take yana kallonta daga sama har kasa, gaba daya ta wani susuce, yace "Yaushe kika xo gidan nan" Ta sunkuyar da kanta tace "Umma ce tace mu taho..." ya kara kallonta daga sama har kasa sannan ya sa hannu ya ciro makulli a aljihunsa yace "Dakin dake ta can bangaren inda babu mutane, ki je can ki jirani" Tana kallon makullin tace "Bude kofar xan yi?" Ya hade rai yace "Aa kullewa xa kiyi, bakya jin hausa ne?" Juyawa tayi ta bar wajen don ta gane dakin da yake nufi babu wanda ke xuwa ta wajen, bata yarda ta kalli kowa ba har ta nufi bangaren ta sa makullin ta bude dakin sannan ta shiga, babban daki ne sosai babu abinda babu a ciki, sai dai abubuwan ciki ba masu hayaniya bane, sannan ba a wani cika kaya a dakin ba, xaunawa tayi kasa ta jinginar da kanta kan babban katifar dakin don gaba daya ta gaji, Bayan kusan minti sha biyar taji an bude kofar dakin ta daga kai da sauri, Shine ya shigo dakin, ya kulle kofa yana kallonta yace "Baki cin abinci ne?" Ta girgixa kai tace "Aiki nake yi shi yasa ban ci ba" Yace "Wani aiki?" Tace "Nayi wanke wanke da safe na share duk tsakar gidan, sannan na taya masu girki wanke naman kaza, wani wanke wanken ya taru na kara wankewa, kuma naje siyo ledan kwasan tuwo sau uku wajen da nisa sosai almajiri ne ya rakani, da na dawo kuma wani wanke wanken ya taru na sake yi, sannan na share tsakar gidan da aka bata...." Katseta yayi yace "Duk wa yake sa ki?" Ta sunkuyar da kai tace "Aunty" Bai ce komai ba, bayan kusan minti biyar yace "Tashi ki shiga bandaki ki hada ruwa kiyi wanka" Mikewa tayi ta nufi bandakin she looks so tired and worn out, ya juya ya fita ya sa ma dakin makulli ya cire ya tafi da shi, a parlor ya tadda Aunty na welcoming din bak'in da suka shigo da mugun fara'arta, ido hudu yayi da mahaifiyar Aneesah, Ya sauke kansa kasa sannan ya karasa cikin parlon ya gaisheta da ladabi bata ko kalli inda yake ba balle tayi kamar ta ji, Aneesah ce ta shigo parlon da jakar kayanta, Aunty ta rungumeta tace "Sannunku da xuwa manyan baki, ya hanya?" Aneesah na murmushi tace "Alhmdlh Aunty don ma dai jirgi muka biyo ai da sauki wahalan" Kofa Abuturrab ya nufa don ko hada ido bai son yi da Aunty, Babu yabo bbu fallasa yaji tace "Aliyu get them something meaningful to eat, kasan sha'anin abincin biki, ba lallai yayi suiting taste bud dinsu ba" Toh kawai Abuturrab yace ya fice daga parlon. Parking Abuturrab yayi bakin gate dai dai lkcn da driver ya sauke su Seeyama bakin gate din, duk suka nufi motarsa, bai amsa gaisuwar da suke masa ba, ya dau leda biyu na abinci yace "Ku kai ma Aunty" Seeyama ta amsa sannan suka wuce ciki, bayan few minutes ya bude motar ya sauka ya shiga cikin gidan rike da leda daya, direct part dinsa ya nufa, ya ciro makulli ya bude kofar ya shiga sannan ya kulle, Jiddah na kwance kan carpet idonta kulle, karasawa yayi yaga bacci take, ya buga katifar kusa da ita, firgit ta mike xaune, ya ajiye ledan hannunsa ya hade rai yace "Baki ce ma Ummi baki ci abinci bane duk yau?" Ta girgixa kai tace "Ban ganta ba tun da safe sai daxu da naje kai mata sako" Yace "Toh wa ya kawo ki gidan nan?" Tace "Nace maka Umma tace in taho tare da su seeyama" ajiye ledan hannunsa yyi ya mike ya koma can karshen katifar ya xauna ya fiddo wayarsa dake vibrate a tunaninsa Ahmad ne don yana restaurant ma ya kirasa, amma sai ya ga akasin haka don Aneesah ce ke kiransa, silencing wayar yyi, Jiddah ta bude abincin da ya ajiye mata ta fara ci. Mikewa yayi ya fita dakin ya kulle, kiran Aunty ne ya shigo wayarsa ya daga ya kai kunne bai ce komai ba yana tafiya, cike da fada tace "Amma walakancin ka da yawa yake, kasan bakin nan takanas daga Abuja suka xo, ba sai ka tafi ka samesu a masaukinsu ka xauna a nutse ka gaida su ba, amma ka wani gaishesu a tsattsaye ka fita kamar mara gaskiya, ko baka san mahaifiyar Aneesar bace?" A hnkli yace "Yanxu nake tahowa" Tace "Toh suna can uwar dak'ana" Yace "Alright" daga haka ya katse wayar ya nufi bangaren Aunty a ransa yana tunanin har ta huce kenan, or did she have anything in mind to punish him with, bude kofar parlon yayi, ya gaida frnds dinta dake xaune parlon, sannan ya nufi bedroom dinta, sai bayan da aka amsa sallamarsa sannan ya shiga, Mahaifiyar Aneesah na xaune tare da kanwarta sai Aneesah a dakin ga abinci iri iri a gabansu bayan wanda ya siyo masu, xaunawa yayi kasan carpet ya gaishesu da ladabi kansa a kasa, kanwar mahaifiyar Aneesar ce kawai ta amsa masa a dakile, uwarta kuwa sai cin abincinta take, Aneesah dai na xaune kan kujera sai kallonsa take ko kiftawa babu, kananun kaya ne jikinsa da suka yi matukar amsarsa, ga kamshin turarensa da ya cika ko ina na dakin, Kanwar mahaifiyar Aneesah Hajiya Maryam tace "Allah ya sanya alkhairi a bikin" Ya amsa da "Ameen" Ya d'an saci kallon mum din Aneesah dake fama da kaza, Mikewa Aneesah tayi ta fita daga dakin, Bayan few seconds ya mike yayi masu sai anjima ya fita shi ma, Hajiya Maryam ta tabe baki tace "Kaga mutum kamar shi yayi kansa, sannan ga nera, shi yasa Aneesah duk take daga ma mutane hankali, to in sha Allah komai ya kusa karshe ynxu ai" tsaye Abuturrab yaga Aneesah corridor tana jiransa, ya shafa kansa yace "U didn't tell me tare da su Mumy xa ku xo" Tace "Ehh ai baka tsaya ka gama saurarata ba daxu kace ana kiranka ka katse wayar" Yace "Ohk, kinci abincin?" Tace "Bayan leda biyu ka siyo me xan ci a ciki?" yace "Ehh ai banga Hajiya ba i only saw u and mum" Ta tabe baki tana gyara siririn gyalenta, ya rungume hannunsa yace "Toh yanxu ya xa ayi?" Tace "Xuwa xa mu yi ka siya min abincin" Ya d'an yi shiru sai kuma yace "Toh ki jirani wajen motar xan dauko makulli a dakina" Tace "Ohkk" daga haka ta fara tafiya, ya bi ta da kallo sannan ya sauka xuwa dakinsa, makulli ya sa ya bude kofar xai shiga yaji muryar Aunty tana kiransa alamar tana biye da shi a baya, da farko niyyar kulle dakin yyi da makullin amma sanin xata yi suspecting abu sai ya fasa ya shiga dakin kawai bayan ya amsa kiran nata, Jiddah na tsaye bakin window ya nuna mata alamar ta shige bandaki, ai da gudu ta shige ciki ita ma jin muryarta, ta kulle har da sa makulli hakan ya kusa basa dariya, dai dai nan Aunty ta shigo dakin, ya xauna gefen gado yana shafa kansa yace "Ya gajiyan aiki Aunty?" Maimakon ta amsa sai ta sa makulli dakin ta shigo, shi dai kallonta kawai yake, ta kalli ledan abincin tace "Wannan fa?" Yace "Ni na siyo na ci" Kujera ta ja ta xauna tace "Abuturrab!!" Ya daga manyan idanuwansa ya kalleta, sake kiransa tayi murya can kasa yace "Na'am...." Tace "Dama Abuturrab ra'ayinka ne xuwa hayi kayi aure ban sani ba? Dama haka ka mayar dani gantalalliya ban sani ba" Ya girgixa kai yace "Wllh ba ra'ayina bane Aunty" tace "To son yarinyar ka fara all of a sudden? Da ka toxarta ni gaban ubanka?" Ya girgixa kai yace "Ko daya wllh Aunty" tace "Toh kawai xubar min da mutunci da walakanta ni gaban iyayenka ka so yi??" ya sauke wani ajiyar xuciya yace "Ba haka bane Aunty, kiyi hakuri" tace "Inyi hakuri?? Dama shirga ni kayi baka saketa ba Aliyu??" Da kyar yace "I'm finding it hard to confide in u anymore aunty..." Tace "Why??" Yace "U did what i never expected, kema kin san na kowa me sauki ne kan na Abba, how will u expect him to take it cewar na saketa da gaske? Wllh he can even disown me, kin fa san waye Abba, kin fi kowa saninsa, amma kika yi exposing dina wajensa" Da karfi tace "Karya kake, wllh baka saketa ba ni xaka mayarda sha sha sha yanxu? Are u stupid?" Yayi kasa da murya yace "Xa kiyi kaffara Aunty, nace maki ba aure tsakaninmu da yarinyar nan amma kuma bai kai har ki je ki gaya ma Abba ba, i trust u shi yasa na sanar maki" Shiru tayi tana kallonsa tana huci tace "Toh dadin xama kake ji da ita ne da kaki rabuwa da ita har yanxu???" Yace "Ko daya, idan na rabu da ita bata da wajen xuwa Aunty, Aunty da xa ki kwantar da hankalinki ki xuba min ido xaki ga me xai faru in sha Allah, i have plans wallahi, ba haka nan kawai na ajiyeta gidana ba, the house isn't meant for her..." tace "Which nonsense plan Aliyu, dubi fa yanda yarinya tayi wani kyau ta kara uban haske fatarta lui lui kamar a latsa jini ya fito, a haka ne xan amince da kai baxan sa shakku a raina ba? Dubi fa yanda tayi fresh alamar bata da wani damuwa ta samu gida kawai, sbda ita ko weekend ka daina dawowa gidan nan sai dai ka sauka can kayi yanda kaga dama da ita, don wllh ban yarda baka harkanka da ita ba" Kallon Aunty ya dinga yi ba ko kiftawa, sannan yace "Inyi harka da ita fa fa kika ce Aunty" Tace "Toh eh mana, kana xaune da budurwa irin wannan a gida baxa kayi yanda kaga dama ba?" ya girgixa kai yace "Ba yanda kike tunani bane aunty, amma dai yanxu ya kike son ayi?" Aunty tace "Kawai ka dawo da ita gidan nan gaba daya da xama, she will be very useful wllh" Kallonta kawai yake yi, tace "Ko baka ji abinda nace ba?" Yayi murmushi yace "Na ji" tace "Wato baxa ka yi ba kenan??? Wato wllh ban ma yrda cewar babu abinda ke shiga tsakaninka da yarinyar nan ba da ya sa kaki rabuwa da ita har ynxu duk da ba auren" Ya girgixa kai yace "No plss, Wllh babu wani abu Aunty ai kinsan ba haka nake ba" Tace "Toh ka maidota gidan nan nace idan na isa da kai, tunda already tana nan kawai kayanta xaka debo gaba daya ka maido su nan" Ya shafa kansa yace "Toh Aunty amma sai mun yi magana da Ummi ko...." Wani kallo ta jefa masa tace "Sai kun yi magana da Ummi? Ni ban isa da kai ba kenan da xaka yi involving Ummi??" Yace "Kin isa" tace "Toh ba sai ka sanar mata komai ba, kawai taga ta dawo nan din, idan tace don me, sai kace ita kadai ce a gida kuma aiki ya maka yawa" Yace "Ohkk" mikewa tayi tace "Xan koma wajen bak'ina, bayan bikin xa muyi magana a tsanake" Daga haka ta bude kofa ta fita ya bi ta da kallo, mikewa yayi ya karasa ya kulle kofar dakin sannnan ya dawo ya bubbuga kofar bandaki, bude kofar Jiddah tayi ta fito tana kumbure kumbure tace "Don Allah kar ka dawo dani gidan nan kayi hakuri" sai kuma ta sakar masa da kuka, dariya abun ya basa, ya dake yace "Gidan namu kike kuka kar in dawo da ke??" Tace "Don Allah kayi hakuri" yace "Dole ma ki xauna nan din ki samu saiti sosai" Durkushewa tayi gabansa ta hade hannayenta tana kara rushewa da kuka tace "Aa don girman Allah kayi hakuri" Xaunawa yayi gefen gado yace "Kin fi son xama tare da ni kenan, duk da kince ni ba muharraminki bane?" Ta gyada masa kai a hankali tana share idonta, ya kauda kai yana murmushi, tuna Aneesah dake jiransa bakin mota yyi, da sauri ya tashi ya dau makullin motarsa ya fita ya kulle dakin ta bi sa da kallo. Har Aneesah xata shigo parlor suka hadu bakin kofa, sai da ya fara surveying wajen yaga ba mutane ya riko hannunta yace "C'mon dear, am sorry Aunty ce ta bata min lkci wllh" hararansa kawai take, yayi murmushi ya ja hancinta sannan yace "Mu je" duk abinda tace xata ci ya siya mata a eatry din da suka je sannan suka dawo gida, ta tafi bangaren Aunty shi kuma ya tafi dakinsa, bude kofar yayi ya tadda jiddah yanda ya barta, ya kulle kofar ya shiga bandaki yayi wanka ya fito ya sauya kayan jikinsa xuwa pajamas sannan ya kwanta.... Tun magrib Aunty ke ta neman Jiddah bayan wanke wanke ya taru amma bata ganta ba, har dakinsu Seeyama ta shiga ta tambayesu suka ce bata shigo ba, cikin dubara ta shiga bangaren Ummi nan ma bata ganta ba, kaf sai da ta xaga duk gidan har da leka kofar gida amma bata ga alamarta ba, wani abu ya dauke hankalinta ta ci gaba da harkar gabanta, sai wajen goma da wani abu ta farga har lkcn fa bata ga Jiddah ba, ta sake xagaye gidan ta koma dakinsu Seeyama da bangaren Ummi duk babu alamarta, mamaki ne ya cikata, to ko Abuturrab ya tafi da ita ne daxu da ya xo?? Wayarsa ta shiga kira xuciyarta na tafarfasa, Abuturrab dake kwance har ya fara bacci vibration din wayarsa ya tadasa, bude ido yyi a hankali ya jawo wayar, ya daga ya kai kunne ganin Aunty ce ke kiransa, daga daya bangaren tace "Abuturrab kana gidan nan ne?" Bin dakin yyi da kallo, lkci daya yace "Aa ina tare da Ahmad" Aunty tace "Au haba??" Yace "Ehh a nan xan kwana, da wani abu ne?" Ta girgixa kai tace "Aa tunda baka nan sai da safe kawai" Daga haka ta katse wayar tayi wani murmushi, dama so take ta ta66atar da cewar ba shi ya dauketa ba, addu'a ta shiga yi a ranta na cewar Allah yasa karawa gaba jiddah tayi kawai... Abuturrab ya kalli kasan carpet din dakin ya ga jiddah kwance ta gaji da kukan bacci ya dauketa, har ya koma ya kwanta ya mike ya bude press dinsa ya fiddo da xanin gado ya rufa mata sannan ya kwanta saman gado ya kashe wutan dakin. Karfe takwas din safe, Abuturrab ya gama shiryawa saboda Ahmad dake jiransa, babu abinda ya ta6a na breakfast da aka kawo masa ya bar ma Jiddah da ke bacci ya fita ya kulle kofar ya tafi da makullin, babu wanda ya lura da shi har ya bar gidan. Karfe tara da rabi Ummi ta shigo dakinsu Ramlah da frnds dinta tana kallon Ramlah tace "Wai Jiddah fa??" Ramlah tace "Na xata ta bi Umma, ai bata kwana gidan nan ba" Ummi tace "Umma kuma? Umma ta xo gidan nan ne jiya?" Shiru Ramlah tayi, Ummi ta juya ta fita taje gun su siyama su ma same reply da Ramlah ta bata suka bata, nan taji hankalinta ya fara tashi, Aunty ta samu, Aunty tace "Jiddah kuma?? Ai ni ban ma san tana gidan nan ba" Ummi ta juya ta koma bangarenta ta kira yar uwarta, bayan Umma ta daga Ummi tace "Ramlah.... Jidderh ta koma gidanki ne??" daga daya bangaren Umma tace "Jiddah?? Aa bata gidana" Katse wayar Ummi tayi ta ajiye da mamaki, Abuturrab ne ya fado mata, to ko jiya ya tafi da ita ne?? Hankalinta ya d'an kwanta tuna hakan da tayi, dialing numbersa tayi bayan ya daga tace "Ka dau matarka ne?" Abuturrab dake tare da Ahmad da wasu frnds dinsu ya d'an yi shiru, kunya yake ji yace mata ai tana dakinsa, kuma baya son ya daga mata hankali, don yana ce mata bai dau Jiddah ba hankalinta xai tashi sosai, ya d'an yi kasa da murya yace "Ehh Ummi" Tace "Sae ka kai ta ina??" shiru yyi bai ce komai ba, Ummi tace "Na lura da kai baka da kirki, baka da kara, ba kuma ka da hankali, Kawai ka dau yarinya kayi tafiyar ka da ita without anyone's knowledge, duk ka bi ka daga min hankali, are this stupid? yarinyar da kake ikirarin ka aura ba da son ranka ba kamar yanda kake raina ma kanka hankali, Don wllh ba ni kake raina ma hankali ba, a sannu abinda ka kulla xai bayyana, did u think i am happy and relaxed with this ur marriage idan ba xuciyar musulunci ba?? duk ina lura da take taken ka a kan yarinyar nan kuma ko kaffara baxan yi ba da gangan kaje ka aureta ka xo nan kana raina ma ubanka hankali ba ni ba, to bari kaji, daga yau dama kada ka sake kawo ta gidan nan balle ka min rashin kunya yanda ka so, kaje can ka xauna da matarka a gidanku na yafe xuwanku wajena, duk da dama tun bayan da kaje kayi auren ka ba xuwa gidan uban naka kake ba, so just remain in ur house with ur so called wife" Tana kai wa nan ta katse wayarta, Abuturrab ya ajiye wayar ya jinginar da kansa da kujera yana tunanin abinda yasa yanxu kowa ke tunanin da gangan yaje ya auri Jiddah kawai pretending yake right from day one of the incident, to me yasa kowa ke ganin haka bayan shi ba da gangan ya aurota ba, mikewa yayi ya fita daga dakin, Ahmad ya bi sa da kallo.... Karfe sha biyu saura Abuturrab ya isa gida, face cap ne a kansa don bai son gaida kowa, kansa a kasa har ya nufi bangarensa ya ciro makulli ya bude kofar, Jiddah ta mike daga kwancen da take, ya shigo ya kulle kofar, ya xauna gefen gado ya dau wayarsa ya shiga kiran Siyama, tana dagawa yace ta xo dakinsa yana jiranta, ba a dau lkci ba Siyama ta xo, ya mike ya bude mata kofa, ta shigo ta gaishesa, duk da mamakin da ta yi ganin Jiddah a dakin amma bata nuna ba, sai murmushi kawai tayi mata, yana kallonta babu yabo bbu fallasa yace "Kaya xa ki dauko mata da Jilbab with ur Nikab now...." Siyama tace "Toh" sannan ta fita, sai ga ta babu bata lkci ta kawo ma Jiddah ankon da xa su saka ranan da Hijab da nikab, ajiye mata tayi gefen gado sannan ta fita, Jiddah ta tashi ta dau kayan ta shiga bandaki ta saka, bayan ta gama sakawa ta fito rike da nikab din tana kallonsa a hankali tace "Ban iya sakawa ba" Ya wani daure fuska yace "A haka xa ki saka, ko waye xai sa maki??" Kokarin sa wa ta shiga yi amma ta kasa, mikewa yayi ya fixge nikab din, ta runtse ido a tunaninta dukanta xai yi, ya shiga daura mata nikab din, bude ido tayi suka hada ido, da sauri ta rufe nata, har ya gama daura mata nikab din, yace "Fita ki jirani wajen motana" Ba musu ta nufi kofa ta bude ta fita, har ta isa tsakar gida kanta na kasa ta fita kofar gida gun motarsa, ya fito dakinsa ya kulle sannan ya fita shi ma....




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of 

payment via 07087865788... Thank you

*Mîkyããj_Sããdy Beauty Soap*

Aunty ce ta shigo parlon Ummi duk da mutane da ke parlon ta ra6a xuwa cikin daki, Ummi na ciki tana bada sako, Aunty ta ja gefe ta jira har ta gama bada sakon sannan tace "Jiya kaina ya dau xafi kika xo kina tambayar Jiddah, to kin dai ganta ko?" Ummi tace "Mijinta ne ya dauketa" Still Aunty tayi tana kallon Ummi, trying to assimilate tace "Abuturrab din?" Ummi tace "Eh" Juyawa Aunty tayi ta fita daga dakin xuciyarta na tafarfasa, lallai Abuturrab ya gama rainata... Through out ranan da ya kasance mothers eve Jiddah na gida ita kadai, kuma ko a jikinta, sai yanxu ta gane xaman gidan da take ita kadai ma gata ne ashe, xamanta 24/7 a gida babban Rahama ne gareta, tun da Abuturrab ya ajiyeta ya tabbatar ta shiga ciki ya tafi bata sake ganinsa ba. Karfe shiddah saura na yamma bayan sun dawo daga babban event center din da suka yi booking against tomorrow's dinner, su biyar ne a motar, wani abokinsu Umar ne ke driving motar, Abuturrab na kallon Umar kafin su isa hanyar da xai kai sa gidansa yace "Umar ka samu waje ka ajiye ni a restaurant din gaba..." Ahmad ya kallesa da sauri, kamar baxai ce komai ba, sai kuma yace "Me xaka yi a restaurant bayan abincin da muka ci yanxu?" Abuturrab ya gyara xamansa babu yabo babu fallasa yace "Eh xan amshi abinci in wuce gida" Ahmad yace "Me xaka je kayi a gida?" Abuturrab yace "Kamar ya me xanyi a gida? Naga it's almost magrib yanxu ko kana nufin saboda gobe daurin aurenka sai in bar gidana in kwana a wajenka?" Murmushi Ahmad yyi yace "Kai dai ka fadi gaskiya, dama Ummi ta shaida min abinda kayi masu, kawai dai baka son ka bar matarka ta kwana ita daya a gidan, shine xaka amsar mata abinci yanxu ka wuce gida" Abuturrab ya d'an yi shiru idonsa a kan titi yana sake comprehending abinda Ahmad ke ce masa, Umar yace "Ni kuwa yau sai naje gidan Captain naga matar nan tasa mun gaisa" Najeeb ma yace "Same with me... matar da har yau ba wanda ya santa" Da sauri Abuturrab yace "To ai tana gidan biki, sai dai idan can xa mu je" Dariya Ahmad yayi yace "Tana gida bata wani gidan biki, mu je kawai Umar ai nasan gidan" Lkci daya mood din Abuturrab ya canxa amma ya kasa cewa komai, Ahmad na nuna ma Umar hanyar gidan har suka isa, horn Umar yayi mai gadi ya bude gate din bayan ya hango Abuturrab da ya sha kunu cikin motar, Umar na parking Ahmad ya fara sauka, sannan Abuturrab, sauran frnds din nasu uku ma duk suka sauka, tafiya kawai Abuturrab ke yi xuwa entrance din gidan, Ahmad na leading din frnds din nasu yana cewa "Wannan ai ba adalci bane ba a sanar maku biki ba kuma a ki kawo ku gidan amarya" Har wani nishadi yake suna dariya da frnds din suna biye da Abuturrab, Abuturrab na shiga parlon ya dinga bin ko ina da kallo, kamshin girki ne ke tashi a parlon wanda ko ina fess alamar har goge goge tayi bayan dawowarta, kitchen ya nufa ya ganta tsaye kusa da gas, ga miya tana yi a gas din, daga sama har kasa yake kallonta, wanda riga da skirt ne na atamfa jikinta amma ba ankon da ta saka da safe ba, har xai juya ya fita sai kuma ya sake juyawa yana kallonta babu yabo babu fallasa yace "Dama kar ki kuskura ki fito daga kitchen din nan" Bai jira cewarta ba ya fita parlor, su Ahmad na xaxxaune parlon har da kunna TV, Najeeb yace "Duk girkin amarya ne ya cika gidan nan haka, ashe yau xa mu kwashi girki" Ahmad ya hadiye dariyar da ke damunsa ganin fuskar Abuturrab, Abuturrab dai bai ce komai ba ya wuce sama, sai gashi ya sauko rike da folded hijab dinta ya wuce kitchen, mika mata yayi yace "Ki fito ki gaishesu, kuna gaisawa kuma ki wuce sama har su tafi kada ki kuskura ki sakko, saura kuma idan kin xo gaishesu ki xube kasa kamar kina neman gafara" amsan Hijab din tayi tace "Toh" ya juya ya fita, bayan ta saka hijab din ta bi bayansa, kanta a kasa har ta karaso cikin parlon, gaba dayansu kallonta suke, ta tsaya nan bayan kujera, sai kuma ta kasa gaishesu a tsaye don bata saba ba, xagayowa tayi ta xauna saman lallausan carpet din ta gaishesu ba tare da ta kalli kowa a cikinsu ba, amsawa suka yi gaba daya Umar yace "Yau Allah yayi xa mu ga amaryar captain, ashe shi yasan me yasa bai ta6a gayyatomu mu ganta ba" Ita dai kanta na kasa, Abuturrab sai danna wayarsa yake bai ce masa komai ba, Ahmad yace "Toh a kawo mana ruwa matar captain" Kallonsa tayi jin muryarsa, ta d'an yi murmushi sannan ta mike ta nufi kitchen, tray ta dauka ta daura ruwan gora uku da glasses hudu sannan ta fito ta ajiye nan tsakiyar parlon, daga kai Abuturrab yyi ya kalleta ganin tayi abun hankali, he was thinking a hannu xata rike goran ruwan ta kawo, Najeeb yace "Toh ni kuma girkin amarya xan ci" Sosai gaban Abuturrab ya fadi, don ko shi bai ta6a cin abinda jiddah ta girka ba, har Ahmad sai da ya ji faduwar gaba, can dai yace "Bayan wanda muka ci yanxu?" Umar yace "Wanda muka ci daban, wannan kuma na amarya ne" Jiddah dai tayi shiru, Najeeb yace "Ko baxa a bamu ba amarya?" Mikewa tayi tana murmushi ta nufi kitchen, Abuturrab ya kalli Najeeb yace "Yanxu fa ka ci abinci bawan Allah, sannan gwangwani daya ta dafa... ba daga kitchen din na fito ba yanxu, ai bata san xa ku xo ba" Dariya Najeeb yyi yace "Sai ta tsam mana a gwangwani dayan, duk wannan kamshin mu tafi bamu ci abincin amarya ba" Ahmad dai bai sake cewa komai ba, Abuturrab ya d'an saci kallon hanyar kitchen din, bai san lkcn da ya mike ya bi bayanta ba, plate ta dauka ta xuba shinkafar, tana tunanin ko a kai xata sa miyan, amma gidan umma taga waje daban ake sa miya idan an xuba ma baki abinci, hakan yasa ta dau wani bowl din me xurfi ta xuba miyan, tunda ta xo gidan bata ta6a girki da nama ba sai ranan, duk da ba wani girki ma take yi ba tun xuwanta, ganin Abuturrab ya shigo kitchen din ya kulle kofa ta juya da sauri tana kallonsa tace "a saman shinkafar xan xuba miyar?" Ya watsa mata wani kallo yace "Ko kuma a sama kaina ba, ke har wani girki kika iya xaki wani xo ki xuba masu abinci maimakon kice babu kare, ni kike son ki kunyata gabansu?? Ko ruwan shayi ma baki bari ya tafasa ballantana ki iya girki me dadi" Kallonsa kawai take ko kiftawa babu, ya nufi tray din da ta daura shinkafa da miyar, ya dau spoon ya debi miyar kadan ya sa a gefen shinkafar ya juya, sannan ya debi shinkafar ya kai baki, ita dai kallonsa kawai take gabanta na faduwa, ya fi second biyar trying to figure out the taste of the food, sai ya ji girkin kamar na gidan Umma, ko don sbda spices din da tayi amfani da ne, wanda umma ta bada a kawo mata, sake dibar shinkafar yyi ya kai baki, da gefen idonsa ya bi kitchen din trying to be sure ba Umma bace ta aiko mata da abincin, bai ga warmer ko wani abu da xai nuna kawo abincin aka yi ba, ya sake diban shinkafar ya kai baki, rungume hannunta tayi tace "Toh xaka cinye abincin ba a kai masu ba ai" cire spoon din yyi a baki da sauri, ya jefa mata wani kallo, ta koma baya ta turo baki, yace "Wa yayi girkin nan?" Bai san lkcn da yayi tambayar ba, sai yaji tambayar made him sound stupid, daukar tray din yyi ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, Najeeb ya sauke ajiyar xuciya yace "Ai har mun cire rai nace su tashi mu tafi kawai" Ahmad couldn't hold it any longer, banda dariya babu abinda yake, Abuturrab ya ajiye masu abincin nan middle of carpet yace "Ae nace maku d'an kadan ta dafa, gashi nan tunda yunwa ku ke ji" Najeeb ne ya fara sauka sannan Umar, shi dai khaleel murmushi kawai yake, Ahmad ya mike ya isa gun abincin ya ci spoon daya gabansa na faduwa, exactly tunanin da Abuturrab yyi shi ma shi yyi, kamar daga gidansu aka kawo mata abincin, komawa yayi ya xauna yana murmushi yace "Nima na ci abincin amarya" Najeeb yace "Kafin ka ci na taka amaryar kenan" Umar yace "Wllh u are missing Khaleel kaji dadin abincin nan kuwa" Tasowa Khaleel yyi shima ya ci spoon daya, sosai suka dinga yabon girkin, shi dai Abuturrab na xaune yana kallonsu, sai da suka cinye abincin duk da ba yunwa suke ji ba, sannan duk suka fita xuwa masallaci, Ahmad ne last din fita, kafin ya fita ya nufi Abuturrab yyi kasa da murya yace "Amma daga gidanmu aka kawo abincin nan ko?" Abuturrab yace "What did u mean?" Ahmad yace "Ba Jiddah bace ta girka" Abuturrab yace "Haka ta ce maka??" Juyawa Ahmad yyi ya bi bayansu Umar, Abuturrab ya mike ya dau tray din abincin ya wuce kitchen, har sannan jiddah na tsaye ta jingina da bango, ya ajiye tray din yana kallonta yace "Wa ya aiko maki da abincin nan?" Ta kallesa, a hankali tace "Abincin ya fi karfin ace ni na dafa ko??" Naxarin maganarta ya shiga yi, ta tattara plates da xata wanke a sink sannan ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita. Sake kallon pot din miyan yayi ya karasa ya bude sannan ya bude na shinkafar, rufewa yayi ya juya ya fita daga kitchen din xuwa masallaci. Ko da suka dawo mosque sun so Abuturrab ya kira jiddah suyi sallama da ita yace ai sallah take, haka nan ko wannensu ya basa kudi ya bata ladan girki, gefen kujera ya ajiye yace "Ta gode" sannan yayi masu rakiya har bakin mota yana kallon Ahmad yace "Xan shigo da safe in sha Allah" Ahmad ya hararesa yace "Kar ma ka shigo mana" a haka suka wuce a mota, Abuturrab ya juya ya koma cikin gidan, dubu sha biyar ne kudin da ya kirga, bayan kusan minti ashirin ya mike ya wuce sama ya bude kofar dakinta, xaune ya ganta kan darduma, ya nufi gaban mirror dinta ya ajiye kudin yana kallonta ta madubin yace "Gashi nan sun baki, dubu sha biyar, amma ban mance turarena da kika fasa ranan ba" juyawa yyi yana kallonta da kyau yace "Kinsan nawa turaren da kika fasa?" Kallonsa kawai take, yace "Dubu arbain da bakwai kika fasa ranan, don haka xaki ajiye wannan dubu sha biyar din har ki samo dubu 32 ki cika min kudin turarena" Yana fadin haka ya bar kudin gaban madubi ya nufi kofa ta bi sa da kallo, can tace "Toh ka tafi da kudin" Ya juyo yace "Sai kin cika" daga haka ya fita dakin. Karfe tara jiddah na wanke wanke a kitchen ya shigo, bin kitchen din ya shiga yi da kallo, ita dai tunda ta kallesa sau daya ta ci gaba da wanke wankenta, kettle din dafa ruwa ya dauko ya bude fridge ya fiddo goran ruwa daya ya xuba a kettle din sannan ya jona, satan kallonta yayi ganin hankalinta na kan wanke wanken da take, ya kai hannu a hankali ya bude murfin tukunyar shinkafar dake kan gas har lkcn, dai dai nan ta juya yayi saurin sakin murfin tukunyar, dauke kanta tayi ta ci gaba da abinda take, ya sosa kansa, sai kuma ya hade rai yace "Shi kuma sauran shinkafar wa kika bar ma??" Ta kallesa tace "Kai mana" ya kauda kai bayan few seconds yace "Na fara wasa da ke ko??" Bata ce komai ba ta dauraye hannunta bayan ta gama wanke wanken ta dau plate ta nufi gun tukunyar ta debi shinkafar duk da ta ci, ta ajiye pot din gun wanke wanke, ta bude miyar ta sa d'an dai dai da nama yanka uku sannan ta rufe sauran miyan ta dau wani plate me xurfi ta rufe shinkafar da shi ta dau spoon ta nufi kofa ya bi ta da kallon gefen ido har ta fita, shafa kansa yyi yana tunanin wani eatry xai kira yyi ordering abinci da daddaren nan a kawo masa, shayi ya hada bayan ruwan ya tafasa sannan ya fita kitchen din, yana haurawa sama ya kalli kofar dakinta sannan ya wuce bangarensa, bude kofar parlon yayi ya shiga sannan ya kulle, still yyi yana kallon plate din dake ajiye kan center table, ya karasa ya ajiye shayin hannunsa sannan ya bude plate din yana kallon abincin, ajiye murfin yyi ya mike, can ya kalli kofa, sai kuma ya xauna, kamar me contemplating sai kuma ya dau spoon din ya fara cin abincin. Washegari karfe takwas da yan mintuna Abuturrab ya bar gidan xuwa gidansu Ahmad, Umma bata amsa gaisuwar da yake mata ba, ya shafa kansa ya wuce dakin Ahmad, Ahmad na ganinsa ya mike yace "Let's talk" Kama hannunsa yyi ya fita suka tafi bangaren Abbansa, Abuturrab dai kallonsa kawai yake, Ahmad ya kulle kofar parlon yace "Me yasa ka dauke jiddah daga gidan su Ummi jiya?" Abuturrab ya hade rai yace "Gani nayi she isn't comfortable, sannan Aunty duk ta bi ta takurata duk ba wanda yace komai, shkkn saboda ba matata bace ita sai in xuba ido a cuceta?" Ahmad yace "Har Ummi ma cutarta take kenan?" Abuturrab ya shafa kansa ya xauna yace "Ni bance haka ba, wllh da kaga yanda na ganta shekaranjiya ko kai baxa ka bada shawaran in bar ta ba, ita Ummi bak'i sun mata yawa, babu abinda xata yi noticing, and Aunty sai aikenta take tana fita titi, what for?? I hate it when someone is being maltreated kai ma ka sani" Ahmad yace "Hmm, ka gano wani abu kuwa Abuturrab?" Abuturrab na kallonsa yace "Me kenan?" Ahmad yace "You are starting to develop feelings for Jiddah, na lura da hakan tun ba yanxu ba, wannan ya wuce tausayi da kwatar mata 'yan ci, gashi kayi gaggawar rabuwa da ita, don babu aure tsakaninka da ita believe it or not, ko da kuwa baka saketa ba shelan da ka dinga yi kana sanar ma kowa cewar ka saketa, ta saku babu wani kwaskwarima... Babu wani aure tsakaninku ynxu Captain, sannan kar ka manta babu idda a kanta..." Katse sa Abuturrab yyi yace "Nigerians have a very very poor thinking mentality, me yasa baxa ku yi koyi da wasu kasashen da suka fi ku wayewa ba, Shikenan ba dama mutum ya nuna rashin jin dadin abun da ake yi ma mace sai ace yana sonta? Ohk fine... Yanxu in xuba ido ayi ta cutarta kenan tunda ba sonta nake ba, ina ce ita ma mutum ce kamar kai, kamar ni, kamar kowa ma? To don me baxan kwatar mata right dinta ba, ko ka mance akan kwato mata right din nata yasa har naje na aureta? Sannan still a kan kwatar mata right din nata ne yasa na datse auren dake tsakaninmu, and duk wannan wa'axin da kake min ni na ta6a bude baki nace maka da aure tsakaninmu ne?? Ko kuma idan ma da auren gaya maka aka ce xanyi" Ahmad yyi murmushi yace "You are just confusing and disorganizing ur self, shi lamarin da ya shafi addini babu wayo a ciki dai, anyway Ummi is jet angry at you, gwara ko koma yanxu ka dau jiddah ka kai ta can gidan tunda dinner xa ayi yau, daga wajen dinner din sai ka wuce da ita gida, gobe Saturday ka kawota yini tunda baxa ka iya barinta a gidan ba, amma kasan me? Kawai ina ji a jikina xamanku tare da ita ya kusa xuwa karshe" Da ido Abuturrab ya bi Ahmad har ya fita. Motoci biyu ne lafiyayyu suka yi parking kofar gida, El-Basheer ya juya yana kallon warce ke xaune bayan mota ta sha glass yace "Toh ai sai ki sauka mun iso" Da mamaki tace "In sauka fa kace, a kan titin xan sauka d'an nan, motoci sun daina shiga get din gidan ne xan sauka a bakin titi" Yace "Toh ai babu wajen parking a ciki, ke baki ga mutane bane...." Tace "Toh ina ruwana da mutane, har yanxu dama Najeriyan bata canxa ba, mu ba haka ake yi a Masar ba wllh, idan ana biki ko wani shagali wllh dai daikun mutane ake gayyata da daddare, sai a tarfa ma kowa yar gurasar alkama a gefen faranti, a daura kofin madara a gefe, idan da yar cinyar kaza a saka a gefe shi ma, Allah ba a taro irin haka kamar ana yunwa, shi Kabirun yasan haka mutane xa su cika gidan xai bada mota a kawoni nan salon in gantale? wllh mu bamu saba haka a Masar ba, a gaskiya idan baxai yiwu ba a juyar dani kawai a mayar dani Bauchi, daga baya kada Usman ya kullaceni sai in dawo inyi Allah ya sanya alkhairi, amma wllh baxan sauka bakin titi ba duk k'ura ta kare min abinda babu a Masar, ko shi Usman din bai san ina hanya ba ai Aliyu ya sani tunda na sanar masa ta waya.... Aa gaskiya ba dole Allah ya sanya alkhairi juya mu koma kawai... Mu ba haka ake a Masar ba, komai bisa tsari ake yin sa" Kashe motar El-Basheer yyi yace "Kinga Hajja idan xaki sauka ki sauka ni xan tafi gun daurin aure ne, ga ki ga gate kice baxa ki sauka ba" Bude baki tayi tana kallonsa, can tace "Aa toh gaskiya Najeriya ba wajen xuwa bane, tunda nake a masar ba a ta6a min rashin da'a irin wannan ba, sun san girma da mutuncin tsoho..." Tana kai wa nan ta ciro wayarta fuska tsuke ta mika masa tace "Kira min Kabirun, ai shi na haifa ba kai ba" Bude motar El-Basheer yyi ya sauka yayi wucewarsa cikin gidan, ta bi sa da kallo baki bude, sai kuma ta sauko ita ma ta bi bayansa. Jiddah ce xaune bedroom din Umma kanta a kasa tana wasa da gefen hijab dinta, Umma tace "Jiddahh" dago kai tayi a hankali tana kallon Umma, Umma tace "Ina sauraronki, idan kika min karya kuma kar ki manta Allah na kallonki, kuma nasan kinsan makomar makaryaci" Lkci daya hawaye ya kawo idonta, Umma tace "Ina jin ki"



Those nulls reading my book for free and still commenting nonsense should know that i owe dem 500.... subhanallah!!! It's their gut for me wllh. In ma ku biya in ma kar ku biya babu pardon tsakanin mu.  My diehard fans kuma we move.... 💖




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems


Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada


Instagram -fareeskinglow_89

TikTok-fareeskinglow

Facebook page-fareeskinglow 

WhatsApp -08031898240

*Hy my beautiful people ina gaisuwa🙋🏻♀️ku karka'de kunnuwanku da kyau ku ji💃🏻ina mai sanar muku da cewa akwai gara6asa me kyau ta musamman ga wanda suka saba sayen sabulunmu da ma wanda zasu fara saya🥰, akwai ragin kaso 20% bisa dari 100% ga wanda suka saba saye, sannan akwai ragin 10% bisa ga masu sha'awar fara saye🥰, akwai farashi mai sauki ga 'yan sari, me yapi wannan dadi kam🤔ki sayi guda 4 kanana a baki kyautar daya, ki sayi guda uku manya a baki kyautar karami daya, ki sayi bucket biyu a baki kyautar babban rubber daya😍 kema da kike da burin saya ku'dinki bai kai ba😰to ga naki, ki kawo customers uku ki karbi naki kyautar Sabulun😍😍*



*Kawata 'yar 'kwalisa me kike jira,ita mace fa kullum cikim yin ado da 'kãwa take😍 ya kamata ki yunkuro wajen ganin kin rabu da wannan kurajen da tabo tabon fuskan nan haka🥺, kinga kema sai a saka ki a layin masu 'kwalisa da bajakolin ado💃🏻😍uwar gida a daure ayi gyaran jiki, sbd karbar goron a wajen me gida🥰,, ina amaren bayan sallah ku pito ku sayi naku Sabulun kuje kuyi ta wanaka hmmm 😍kamshi kawai zaku yi tayi kaca kaca😍😍, laushin fata Baja baja😃😂😂a yunkuro azo a karbi kayan gyaran jiki tare da sabulun gyaran fata a wurin _Mîkyããj_Sããdy_🥰*



*Duk wanda suka gwada Sabulun mu sun san babu 'karanta a ciki🥰in dai fannin gyaran jiki ne to sabulunmu shine amsarku,, shi ke mai da fata ta zama babu Pimples, Acne, Spot, Stretch Mark, da Duk wata matsala da ta shafi fata,, akwai lightening,  nd glowing😍*



_*In kina son jikinki yai su6ul da shi, fata tai santsi da sul6i, ki yi haske me aji, 'kamshi kaca kaca ko ta Ina, ki ta fresh abunki hankali kwance ki zama Wankan madara yauqin zuma😍💃🏻Anty madam😃To ki mallaki 3d (Extra Whitening Soap, Ko da kudinki sai da rabonki hajiyata)💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*_



*Akwai hadin:*

*Mai da tsohuwa yarinya*

*Uwargida ta koma amarya*

*Amarya ta koma tamkar 'yanmata*

*'Yan mata su koma 'yan dagwai²*

_Ga masu bu'kata sai su tuntu6emu ta kafar sadarwa kamar haka;_

_Call/WhatsApp:08061570778_

_IG@mik_yaaj_saady_

Jiddah ta goge idonta still ta ki cewa komai, Umma tace "Baxa ki min magana ba Jiddah?" A hankali Jiddah tace "Umma yace min babu aure tsakanina da shi" Umma tace "Kamar ya babu aure a tsakanin ku?" Jiddah ta gyada kai tace "Eh haka yace, wai shi ba mijina bane" Umma tace "A ina yace hakan?" Jiddah tace "A can gidansa, ya rubuta ne a takarda ya bani" Umma ta dinga kallonta kafin tace "Ina takardan?" Cikin sanyin murya tace "Ya ki bani" Umma tace "Amma ya nuna maki?" Jiddah tace "Ehh" Umma tace "Cewa yayi ya sakeki a takardan?" Nan ma tace "Ehh haka yace, shi ba mijina bane" Umma ta gyada kai bata kuma ce mata komai ba, bayan kusan minti goma ta mike ta fita dakin rike da wayarta, wani dakin daban ta shiga tayi dialing number wata aminiyarta tana dagawa tace "Hajiya karfe nawa xa ki taho?" Hajiya Rukayya tace "Ina hanya yanxu haka" Umma tace "Babu kowa gidanki?" Hajiya Rukayya tace "Toh na bar su dai suna ta shirin tafiya dinner da wani abu ne?" Umma tace "Toh shhkn tunda ba kowa, dama wata yar uwarmu ce aka kawo biki to bata son hayaniya, kinga nan din ma akwai taro shine da nake son ta xauna gidanki har bayan biki" Hajiya Rukayya tace "Ohh Allah sarki, to amma Badiya mai aikina na nan ai, ba sai su xauna tare ba" Umma tace "Yauwa toh, xan sa driver ya kai ta can din kawai, sai ki kira ki sanar mata bakuwa na xuwa" Hajiya Rukayya tace "Toh ba damuwa" Umma ta koma dakin da Jiddah ke ciki tace "Kaya kala nawa kika taho da?" jiddah tace "Na yau ne da gobe kawai" Umma tace "Ohk, xaku fita da driver xai kai ki gidan kawata yanxu, tunda naga ke ba son taro kike ba ai" Jiddah ta d'an yi shiru, sai kuma a hankali tace "Umma ai yace xai dawo anjima ya daukeni" Umma tace "Ehh kafin ya dawo din, sai yaje can gidan ka ya daukeki, ki tafi da jakar kayanki kawai" Jiddah tace "Toh" Bayan mota Umma ta sa ta shiga ta ajiye mata jakarta a gefenta, sannan driver ya bar gidan bayan ta sanar masa inda xai kai ta, tafiyar kusan minti ashirin da wani abu suka yi suka isa gidan Hajiya Rukayya, Drivern yayi ma mai gadi maganan cewar yayi leading dinta har entrance din gidan, tana shiga cikin compound din mai gadin ya nuna mata direction da xata bi, ta makale jikin kofar ta kwankwasa a hankali, ta fi minti biyar tsaye sannan aka bude kofa, wata mata ce ta bude kofar ganinta tace "Ke ce bakuwar da Hajiya ta sanar kina xuwa?" Jiddah ta gyada mata kai kawai, Badiya ta amshi jakar hannunta tace "Toh sannu da xuwa, Bismillah" Bin bayanta Jiddah tayi, ta xauna parlor, Badiya ta shiga dakin yan matan Hajiya Rukayya ta ajiye mata jakarta. Karfe biyar saura Abuturrab ya isa gidan Umma, ya fi minti biyar cikin mota sanin da mutane gidan shi kuma ba iya shiga xai yi ba, daga karshe kawai Maman Abdallah da ya gani a compound ya aika ta kira masa Jiddah, ba a dau lkci ba sai ga ta, tace "Wllh yallabai Umma tace suna can gidansu amarya" Da mamaki ya dinga kallonta, can yace "Toh nagode" Tada motar yayi ya bar layin ya dau hanyar gidansu, bayan yayi parking a waje ya dau waya ya kira Siyama tana dagawa yace "Ki ce Jiddah ta fito" Tace "Yaya mu muna wajen make up fa, kuma har muka bar gidan bamu ga ta xo ba" ya d'an yi shiru, kafin ya katse wayar. Tunanin wanda xai kira ya dinga yi a ciki amma ya ga ba kowa kuma don ko hauka yake ya san baxai kira Ummi ba, d'an tsaki yyi ya tada motarsa ya bar wajen. Tun da Abuturrab suka isa wajen da ake dinner tare da Ahmad da sauran abokansu yake xuba ido yaga inda xai hango Jiddah a wajen amma bai ga alama ba, hakan bai wani damesa ba don dama xuwa dinner din ne baya son ta xo ya kaita can gidan Umma, tun sanda Aneesah ta kyallara ido ta gansa take masa zarya a wajen, barin yanda taga yayi wani kyau cikin fararen shaddan da duk abokan Ahmad suka saka, ita a dole sai ta ankarar da jama'a cewar saurayinta ne, Ko mayafi bata daura kan damammen doguwar rigar jikinta ba shi dai sai bin ta yake da kallo, wani abokin Ahmad dake side din Ahmad din Abuturrab ke ta kallo yana son tuna inda ya ta6a ganinsa, he looks familiar amma dai bai ce masa komai ba, karfe goma saura Aneesah ta xo ta samesa tana yauki tace "My captain wai xaka xo ka maida su Mummy gida yanxu" Ya d'an kalleta yace "Toh ai bani na taho da motata ba, ban ma san inda yake yanxu ba, nima abun hawa na samu ya kawo ni nan" Tace "Haba Captain, ko wajen daya daga abokanku baxa ka amshi mota ka maida su gida ba...." Ko rufe baki bata yi ba sai ga aunty ita ma ta sha wani ubansun lace tana goge xufan goshinta da handkicin hannunta tace "Aliyu ka tashi ka maida su Hajiya Safiyya gida" Bai ce mata komai ba, tace "Ko baka ji na ne?" Yace "Toh bari in nemi wanda makullin motata ke wajensa" Juyawa tayi ta bar wajen, ya kalli Aneesah da ta hade rai tana kallonsa, d'an murmushi yyi yace "Kema dai kinsan wasa nake, dole in nemo mota ko na waye in maida su" Yana fadin haka yayi patting shoulder din Umar dake side dinsa yace "Bani makullin motarka pls" Umar ya mika masa sannan ya mike yace "Kice su fito" Daga haka ya nufi hanyar fita daga hall din.... Karfe daya Abuturrab ya koma gidansa bayan sun maida duk bak'in da suka je dinner masaukinsu, ya fi minti goma xaune a parlornsa thinking of where Jiddah might be, daxu da ya maida Mum din Aneesah har gida ya shiga bai ga alamar tana nan ba, shi kuma ya kasa tambayar Ummi, akwai wasu bakin da still ya mayar can gidan Umma, can ma ya shiga bai ganta ba, bayan kuma ya tambayi Maimoon tace ai tana gidan Umma, mikewa yayi daga karshe ya wuce sama xuwa dakinsa don ya gaji sosai. Da asuba kiran sallah ya farkar da jiddah, ta mike xaune daga kan gadon da take tana kallon yarinyar dake kwance saman gado gefenta, tun xuwanta gidan jiya banda ita da Badiya bbu kowa a gidan har tayi bacci wajajen karfe goma saura, bandaki ta tafi ta dauro alwala ta fito sannan ta tada yarinyar da baxata wuceta ba, yarinyar ta mike xaune, ita kuma ta shimfida darduma ta fara sllh.... Karfe tara saura yarinyar da tayi wanka ta shirya cikin atamfa ta kalli Jiddah tana murmushi tace "Ya sunanki?" Jiddah tace "Jiddah" Yarinyar tace "Ni sunana Amina, mu je parlor mu gaida su Mama sun fito" Jiddah ta saka Hijab dinta ta bi bayan yarinyar suka fita parlor, yan mata biyu ne xaune parlon sai Hajiya Rukayya, wanda Jiddah na ganinta ta gane mahaifiyarsu ce don sun yi kama, Jiddah bata yarda ta xauna kan kujera ba ta gaida matar, ta amsa da fara'a tana tambayarta ta tashi lafiya, Jiddah ta sunkuyar da kanta, sauran yan matan ma sai kallon Jiddah suke, Wani ne ya shigo parlon daga waje waya kare kunnensa, ganin mahaifiyarsa a parlon ya katse wayar ya zauna yace "Ina kwana" Tace "Lafiya lau... Jiya kuma sai kayi wucewarka ka bar mu a event center" Yace "Mama ciwon kai wajen ke sa min, it's been long da na tsaya waje that's so noisy haka" Hajiya Rukayya tace "Toh Allah ya kyauta" Tun da ya shigo Jiddah ke kallonsa kamar taga wani mugun abu, Ganin xai kalli direction din da take ta dauke kanta da sauri gabanta na faduwa, Yace "Mama bakuwa ku ka yi?" Hajiya Rukayya tace "Ehh, ga breakfast dinka can a dining" Yace "Ohk" sannan ya mike ya tafi dining din, Mikewa Amina tayi ta tafi dauko ma ita da Jiddah breakfast don taga alamar yayyinta duk sun yi, kuma da ba don Jiddar ba tare xata je ta xauna su yi breakfast din da yayanta, gaba daya Jiddah ta kasa sakin jiki a parlon, lkci lkci take satan kallon hanyar dinning din, daga karshe dai ta mike xata wuce daki, Hajiya Rukayya tace "A daki xaki yi kumallon?" Ta d'an yi murmushi ta gyada kai ta wuce daki da sauri, dole dakin Amina ta kai masu Breakfast din. A ranan bayan an sauko juma'ah aka daura auren Ramlah da Ahmad... Abuturrab na tsaye daga bakin kofa a bedroom din Umma bayan sun gaisa yace "Tana gidan nan ne Umma?" Umma ta kallesa tace "Wa?" Jin bai ce komai ba tace "Wai Jiddah?" Yace "Eh" Tace "Ba a jima ba suka tafi can gidanku da Maman Abdallah" Bai kuma cewa komai ba, tace "Hajja kuka tace tun da ta xo baka je ka gaisheta ba" Yace "Ai ban je can gidan ba Umma, anjima da daddare xan shiga in gaisheta" Tace "Yauwa gwara kaje din da daddare dama ya fi, an kai maku abincin kuwa?" Yace "Ehh an kai" daga haka ya juya ya fita. Da yamma su Amina duk suka tafi gidan yinin Biki, Hajiya Rukayya kuma tun karfe goma dama ta bar gidan, gidan ya rage daga Jiddah sai Badiya, tana kitchen tare da Badiya tana tayata girkin dinner, wayar Badiya dake parlor ya fara ring, Badiya tace "Dauko min wayar Jiddah..." juyawa tayi ta fita xuwa parlor, dai dai nan kuma aka bude kofar parlon suka hada ido, sanye yake da farar shadda idonsa sanye da glasses, sosai gabanta ya fadi, ta sunkuyar da kanta tana kalle kallen inda xata ga wayar Badiya, kasa karasowa cikin parlon yyi, sbda rudewa ta ma rasa inda wayar yake ta juya xata koma kitchen din taji yace "Jiddah" juyowa tayi suka sake hada ido, tayi murmushin karfin hali tace "Ina yini?" Ya karaso cikin parlon yana ci gaba da kallonta da mamaki, bata jira me xai ce ba ta juya da sauri ta koma kitchen din. Har Hajiya Rukayya ta dawo wajajen magrib Jiddah bata sake yarda sun hadu da Yousuf ba, can daki ta shige taki fitowa through out, Hajiya Rukayya na shigowa gidan ta kira Yousuf a waya don baya nan, yana shigowa tace "Don Allah bakuwar nan xaka ajiye min gidansu Ahmad yanxu, Hajiya Ramlah tace ka kaita" Yousuf yace "Ohkk" Har mota su Amina suka raka Jiddah, shi da Yousuf na xaune cikin motar tasa, Jikin Jiddah yyi sanyi ganin shi xai maidata, hannu kawai ta daga ma kanninsa har suka fita compound, sai da suka d'an yi nisa taji yace "Dama ke yar uwar Ahmad ce?" Kai ta gyada masa kawai, ya d'an kalleta yyi murmushi yace "Har yanxu sai kice min baki da waya ko?" Ta gyada masa kai, yace "What if na baki tawa wayar?" Ta xaro ido tace "Sai in ce wa ya bani?" Yace "Ni" ta girgixa kai tace "Aa bana so" yace "Jiddahh" ta d'an kallesa suka hada ido, yace "Kin san wani abu?" Ta girgixa masa kai, yace "Tun da muka hadu dake a jirgi kullum nake addu'an Allah ya sa in sake arba da ke, sae gashi kin xo har cikin gidanmu, kinsan me yasa hakan ya faru?" Nan ma ta girgixa masa kai, yace "It is because i have good intention toward u..." Jiddah dai tayi shiru kamar ta gane me yace. And the rest of the ride was silent, yayi parking dai dai kofar gidansu Ahmad ya juya yana kallonta, yace "Tunda baxa ki amshi wayata ba, xan kiraki ta wayar Maimoon" Ita dai bata ce komai ba, ta bude motar ta sauka, ta bude baya ta dau jakan kayanta, Yousuf na kallonta yace "Sai na kira" Tace "Toh" sannan ta nufi gate, shi kuma yayi reverse.... Dama Umma Jiddah kawai take jira don har ta saka Hijab dinta tana parlor a xaune, Jiddah na shigowa kuwa ta saka driver ya kai su can gidansu Abuturrab, har sannan da akwai sauran yan biki a gidan duk da tun wajen shidda saura aka kai amarya, direct parlon Abban Abuturrab Umma ta nufa tare da Jiddah suka shiga da sallama, Abban Abuturrab da brothers dinsa ne a parlon sai Hajja dake xaune kan carpet, bayan ta xauna suka gaggaisa, ta gaida Hajja ma, Hajja tace "Ni dai tun jiya nake ta kallon ki Ramlah, ya aka yi kika amince kika narka uban kiba haka, to ai ba kyau, mu a masar da tuni an kai ki asibiti duk hankali a tashe, mu ba ma haka a can" Umma dai bata ce mata komai ba, Can ta kalli Jiddah da ta sunkuyar da kanta tun bayan gaida su Abba tace "Ita kuma wannan sadaka yallar fa?" Nan ma babu wanda ya ce mata komai, Abba ya dau waya ya kira Ummi ya sanar mata Umma ta iso, su xo tare da Aunty, Hajja tace "Ai masar tayi wallahi, ba ruwanmu da abinda bai shafemu ba, kowa ta kansa yake, shi yasa xuwa jibi nake son idan Allah ya kai mu in koma, nafi wayo a can..." Ummi ce ta shigo parlon tare da Aunty, tunda Jiddah taga Aunty gabanta ke faduwa, Brother din Abba dake gefensa yace "Ka kira Aliyun ne?" Abba yace "Ehh na kirasa" Abba bai rufe baki ba Abuturrab ya shigo parlon da sallama, sosai gabansa ya fadi ganin Jiddah da Umma a parlon, ya dai dake ya xauna, sannan ya gaida kowa na parlon.... Brothers din Abbansa ne kadai suka amsa gaisuwarsa, Abba na kallonsa a takaice yace "Ina takardan da ka rubuta ma yarinyar nan?" Abuturrab ya buda ido sosai ya kalli Jiddah, da farko kasa cewa komai yayi, can kuma yace "Takarda kuma Abba?" Lkci daya hawaye ya kawo idon Jiddah ta kalli Umma da ta hade rai, Abba yace "Ina tambayarka kana tambayata? Are u stupid?" Yyi kasa da murya kamar wani mara lfya yace "Abba ai ban san wani takarda ba" Umma ta kalli Jiddah tace "Ya rubuta takarda ya baki ko bai rubuta ba?" Hawayen idonta na xuba ta kalli Umma ganin yanda ta daure fuska cikin rawan murya tace "Ya rubuta" Kallonta kawai Abuturrab yake ko kiftawa babu, Umma tace "Yace maki me a jikin takardan?" Da kyar tace "Wai ba aure a tsakanin mu, shi ba mijina bane" Aunty dake ta gyara xama taji kamar ta saki shewa a parlon murmushinta ya kasa boyuwa, on a serious note Abba na kallon Abuturrab yace "Mu ka mayar kananun mutane Aliyu? Ashe baka dau addininka bakin komai ba bamu sani ba, for all this while kana xaune da yarinya babu aure Aliyu??" Da kyar Abuturrab yace "Abba wllh wllh ba saki na rubuta a takardan ba..." Hajja dai ta hangame baki tana bin kowa da kallo a parlon, Caraf Aunty ta amshe tace "Toh ai aikin banxa kenan, tunda duk ka bi ka sanar ka saketa aure kuma ai ya lalace, ko ka mance addininka ne? Ni kaina kace min ka saketa ya fi sau talatin, ga Aneesah ga Ahmad da abokanka, ka ga kuwa ta saku" Abuturrab ya kalleta xuciyarsa na tafarfasa yace "Toh ai ita bance mata na saketa ba, na dai ce mata ni ba mijinta bane, ban ta6a bude baki nace mata na saketa ba...." Mikewa Abba yayi ya tafi daki sai gashi ya fito.... Abuturrab ya dinga kallonsa xuciyarsa na bugawa.

 


I just have to update today not to keep pple waiting, but I'm not feeling well....





Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you






Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems


Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada

Instagram -fareeskinglow_89

TikTok-fareeskinglow

Facebook page-fareeskinglow 

Abba ya ajiye masa takarda da biro din hannunsa ya koma ya xauna yace "Tunda kana kokwanton auren da ake ce maka babu tsakaninku upon sanarwa da ka dinga yi ka saketa, to ni yanxu na umarce ka da ka kara wanda baxa kayi kokwanto ba a ranka" Kallonsa kawai Abuturrab ke yi kamar bai gane me yake nufi ba, Abba ya daka masa tsawa yace "C'mon my frnd ina sauraronka" Ya sauke idonsa a hankali yace "Toh ai Abba ni bance baxan xauna da ita ba, ban ta6a maku musun xama da ita ba, tuni na riga da na hakura...." Da karfi Aunty tace "Wllh karya kake munafuki... har ce min kayi kawai sbda Abbanka kake xaune da ita bayan ka saketa don kar ya samu labari yayi fushi da kai, kuma mu baxa mu xuba maka ido kuna xaman haram da yarinya ba, banda ma dai ni da na damu da lamarinka, ina ce ranan da na gano irin xaman da ku ke na xo na sanar gwaleni Abbanka yayi, to Alhmdlh ai yanxu tunda Hajiya Ramlah ce ta xo da batun da kanta" a kufule Hajja tace "Waye wannan dallah... Ya xa ki cika ma mutane kunne haka, ita uwar yaro ma ta ja bakinta tayi gumm kamar sabuwar kurma sae ke xaki dinga daga jijiyoyin wuya kina hak'i uwa dai kin hada wani abu da Aliyun, iyakarki fa matar ubansa, waye bai san auren cin amana ku ka yi da Usman din ba, daga dai ke da uwarki kuna fama da bakar talauci kuna tuyan masa da miyar taushe a daya daga gidajen hayana dake Tudun wada, shi kuma Usman na aikesa yaje ya fatattaki wani kato da yaki biyana haya kusan sati uku da karewar kudinsa, shkkn fa mata kika makale ma d'a na har da kullo masa yar wainar shinkafa a leda, to mu muka san abinda aka barbada a kai sai ga Usman ya birkice shi xai kara aure bayan ko shekara biyu da auren wannan Bafillatanar Hauwan bai yi ba, a takaice dai wllh tsallake maganata yayi ya aureki don na hanasa yaki ji ya bada toka a ido xai xageni, to ba dole in yafe masa ba tunda kowa dai yasan ku 'yan Benue ne, Mu dai babu abinda muka sani da ya wuce wannan, to yaushe ma xa a ga haka a Masar? Aa wllh basa haka...." Alhaji Umar yayi kasa da murya yace "Hajja ai ina ga ba wannan xancen muke yi a nan ba, duk ba shine ya kawo mu nan ba" a fusace Hajja tace "Toh don ba xancen ake ba sae in yarda ta gigita min jik'a, ni dai har gobe ina danasanin basu gidan hayata, daki daya ma fa suka kama suke rayuwa a ciki, kafin ma in basu dakin cewa suka yi gidan da suka baro watsi aka yi da kayansu bakin titi a unguwar mu'axu, gashi suka dinga ban wahala da kyar suke biyan kudin hayan a lkcn ma wllh.. to  ni duk na wannan ba don Allah ma bai ce ayi tone tone ba, wanda kuma ya rufa ma d'an uwansa asiri Allah ma xai rufa masa asiri, amma ai an cuci Usman, to kuma ni ance min Aliyu ya auri yar hayi lkcn ina Masar, tsoro ya kamani na fita hayyacina na gigice da naji wannan xance sbda ni nasan ina ne hayi, kuma ni nasan mutanen cikinta, to sae gashi kabiru yace min ae suna xaune lafiya lau da matarsa, hakan yasa na saki raina duk da ban samu xuwa bikin ba, toh ynxu abinda ban gane ba wannan yar farar dake xaune ce yar hayin koko?" Umma tace "Ita ce" Hajja tace "Ikon Allah... toh kai Usman ya kake son kashe masu aure kamar kai ka halicci auren?" Alhaji Umar yace "Hajja babu wannan auren fa yanxu musulinci, don ya riga da ya saketa da bakinsa, sannan kuma ya saketa a rubuce, ni ba mijinki bane ae dai dai yake da na sake ki...." Hajja ta rike ha6a tace "Naga jaraba, a gabanka aka yi sakin kake wnn ciccijewan ko kawai karere, Sannan kana min gatsal gatsal idan shafa'atu ce xaka mata haka yau?" Abba yace "Don Allah Hajjaju kiyi shiru muyi abinda ya kawo mu nan, baki san komai a kan maganar nan da ake a nan ba, yaushe rabonki da kasar??" Hajja ta rungume hannu hade da ta6e baki tace "Nayi shiru, amma mu a masar wa xai yi haka? Wllh ba a haka, ayi aure kuma a dawo ana cewa ya mutu bai mutu ba" Ta gefen ido Abuturrab ya kalli Jiddah da ta kasa dago kanta, Aunty dai ta wani sha kunu a parlon tun bayan xancen Hajja a kanta, ita dai Ummi kallonsu kawai take ba um ba um um, a fusace Abba yace "U are wasting our time Aliyu, saki me hujja nake so kayi ynxu tunda duk wanda kayi a baya baka aminta da su ba..." Ya dago kansa yana kallon Abbansa yace "Abba ni nasan na aureta sannan ina xaune tare da ita saboda inyi biyayya gareka, bayan hakan babu wani abu kuma...." Abba ya katse sa yace "Toh an dauke maka wannan biyayyan, write d divorce now, sai ka tashi ka tafi Allah ya baka ladan taimako, ae kayi me wuyan tunda ka rabota da tsananin da take ciki" Abuturrab bai kuma cewa komai ba, bayan few seconds yace "Yanxu sakin xan rubuta mata?" Abba yace "Ehh, baxa ka mayar da mu kananun yara ba mu xuba maka ido, har yau mun rasa gane xaman me ku ke da yarinya" Abuturrab ya sunkuyar da kansa ya fara rubutu a takardan, d'aga kai Jiddah tayi tana kallonsa, ya gama rubutun ya mike da ladabi ya mika ma Abba, Abba ya amsa yana duba content din takardan, Abba yace "Good, Allah ya maka albarka, ya baka ladan taimako, daga yanxu kuma babu ruwanka da duk wani harka da ya shafeta, xa mu yi mata komai in sha Allah, kai ma kuma kayi iya naka kokarin don ta dalilinka duk muka santa, Allah ya maka albarka...." Abuturrab ya amsa da "Ameen" Sannan ya juya ya fita daga parlon jiddah ta bi sa da kallo, Abba ya nuna ma brothers dinsa biyu takardan, Alhaji Umar yace "To maa sha Allah, kaga yanxu babu wanda xai ci gaba da kokwanton xaman da suke, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, shi kuma Allah ya saka masa ya basa ladan taimakonsa, ku kuma Allah ya baku ikon riketa da gaskiya" Aunty da taji jikinta na wani tsumma don farin ciki gaba daya ta mance abinda Hajja tayi mata sae jiran takardan take ya xo garesu, ai ko ana miko mata bayan ta karanta tayi wani murmushi ta mika ma Umma, Umma ma ta mika ma Ummi bayan ta karanta, Hajja tace "Amma na tsorata da lamarin Aliyu, Kunga da yana sonta da gaske ai kuka xai sakar mana a nan yace shi baxai saketa ba, amma almurin kamar jira yake gashi ya cike takarda da rubutu, aa gaskiya ba sonta yake ba, ku duba fa babu wani gardaman a xo a gani ya rubuta takardan, Lahh wanne mutum a masar, to amma ai shkkn sae a bani ita mu tafi Bauchi don kwana biyar xanyi a can kafin in koma Masar, idan ma kunga xaku iya biya mata jirgi kawai sai mu tafi tare, ai d'a na kowa ne bawa sai mai shi..." Umma ta kalleta da sauri tace "Hajja karatu xa a sata ai" Wani kallo Hajja ta watsa mata tace "Shi kuma masar din duk jahilae ne ba a karatu.... Banda neman magana ina ruwanki Ramlah, ni fa da d'a na nake kika tsomo baki, ko Ahmad ne ya tsintota a hayi?" Ta gefen ido Ummi ke kallon Hajja, Abba yace "Dama haka ake tafiya Masar din Hajja, ina laifin ma kice idan kin tafi a turo ta?" Hajja tace "Kai ba ruwana ni ku rabu dani, xa a Wani min caaa, dangin uwa ko na uba, meye hadina da ita banda Aliyu da ya aurota a gantale ya saketa kuma a gantale, kuma ma wasa nake, haka kawai inje in daura masu nauyi nima da ya ake bani yar gurasar da ake ban balle na tafi da wata?" Mikewa tayi tace "Banda Najeriya ina ake aure a gantale ayi saki a gantale, Hauwa taho ki bani sakon da na baki" Tana kai wa nan ta fita, Ummi ta mike ta bi bayanta, Aunty ta bi ta da harara, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Alhaji xan tafi da Jiddah ta koma gidana ta fara karatu" Caraf Aunty ta amshe tace "Me xai hana tayi a nan din, ga dai sa'aninta su Aisha" Abba yace "Da nan din da can ai duk daya ne, Allah dai ya bata ilimi mai amfani"  Ko kadan Aunty bata ji dadin haka da Abba yace ba, Umma tace "Toh nagode Alhaji, Allah ya tayani riko" Duk suka amsa mata da "Ameen" amma banda Aunty da ranta ya baci, can dai tace "Amma ai xata dinga xuwa nan din ko" Umma tace "Aa me xai hana kuwa" Umma na fadin haka ta mike tana kallon Jiddah tace "Mu je Jiddah" Jiddah ta mike a hankali ta bi bayanta, Aunty ta bi ta da kallon tsana, shi kam Abba tausayinta kawai yake ji, banda rashin gata ya xa ayi hakan ya faru gareta ma. Bangaren Ummi Umma ta kai ta, Ummi na xaune parlonta da Hajja dake mata magana kasa kasa, amma ganin Umma sai tayi shiru, Umma tace "Toh yaya mun tafi sai da safe" Ummi tace "Baxa ku yi isha ba?" Umma tace "Eh to bari inyi" Daga haka ta karasa bedroom din yayarta, Jiddaj dai na rakube jikin kujera, Ummi ta kalleta tace "Kije kiyi sallan ke ma" Mikewa Jiddah tayi ta fita, Hajja ta tabe baki tace "Toh ai gwara ma da aka kashe wannan auren don ai Aliyu d'an usuli ne, ita kuma bamu san yaya ba" Ummi tace "Ai babu wanda bashi da usuli Hajja" Hajja tace "Aa Hafsat dai bata da shi, an rasa gane ko kwatakwali ce har yau, duk da tace uwarta yar Benue ce" Ummi dai bata ce komai ba, Hajja tace "Shi yasa gashi duk ta amshe gida tayi bake bake, komai sai inji Usman yace Hafsa, to wacece kuma Hafsa, dama Hadiza ta bani labarin irin xaman da ku ke yarda ce kawai ban yi ba, gashi duk ta rufe maki baki ta amshe gida, wa ya sani ko ma har da ya yanki? Tunda na xo naga take takenta komai sai ace sai ita, to a kan me?" Ummi tace "Aa Hajja kowa ai da matsayinsa a gidan" Hajja tace "Toh kunga lalacewa ko? Wani matsayi matar da ta kwace maki miji ta karfi, me yasa kike abu sakwa sakwa kamar warce aka ce ma je ki kya gani Hauwa, komai fa na bikin nan naga sai dai ace Hafsat to wacece kuma Hafsat, gashi ana maganan tabargaxan da yaro yayi mata tayi bake bake a kan xancen kamar d'an ta, to ni tunda na xo ma ba sau daya Salem ya shigo gaisheni ba, duk sun tsotsa a nono wllh, dubi fa Aisha kamar yar karuwai Allah na tuba, to ba dai komai tunda duk jikokina ne, amma idan xaki tashi tsaye ki amshi gidanki ki tashi" Fitowar Umma yasa Hajja tayi shiru, Umma tace "Toh sai da safe Hajja, yaya sai mun yi waya" Hajja tace "Toh Allah ya ba yara xaman lafiya ya kauda fitina amma ki dai je asibiti kiga kibar ta mecece kika narka haka kinji" Umma bata tankata ba har ta fita, Hajja tace "Toh sai da safe" Sai da Jiddah ta sake shigowa tayi ma Ummi da Hajja sai da safe sannan suka bar gidan tare da Umma, har driver ya maida su gida Jiddah bata cewa komai, duk tayi sanyi sosai, ta rasa ko farin ciki take ko bakin ciki, Wajen karfe tara Umma ta xaunar da ita a dakinsu Maimoon tace "Kina ji na Jiddah?" Jiddah ta daga kai ta kalleta, Umma tace "Kin dai ga yanda abubuwa suka kasance, ni nasan Abuturrab bai da niyyar cutar dake a ransa, kuma har abada ina son ki daukesa da girma da mutunci don ya maki abinda ba kowa xai iya maki ba a rayuwa, duk abinda xaki xama a rayuwa nan gaba Allah ne ya tabbatar da hakan amma Abuturrab ne sanadi, ina son kuma ki maida hankalinki kiyi karatunki, kin san wacece ke kinsan daga inda kika fito" Hawaye ne ya shiga xarya idon Jiddah tana kallon Umma, Umma tace "Ni kuma ina fatan Allah ya bani ikon yi maki duk abinda ya kamata a rayuwarki Jiddah" Cikin rawar murya tace "Toh Umma baxan sake ganinsa ba kenan?" Da mamaki Umma tace "Don me baxa ki gansa ba, in dai Allah ya kawosa gidan nan ai xaki gansa, sannan xaki dinga yawan xuwa gida Ummi, idan baku hadu a nan ba xaku hadu a can, balle ma nace tsakaninki da shi kawai girmamawa ki daukesa kawai a matsayin babban wan ki, nasan shi ma a matsayin kanwarsa xai daukeki" Jiddah ta share hawayen idonta a hankali tace "Toh Umma nagode" Umma ta sakar mata murmushi, har ranta taji tana son Jiddah tana kuma son inganta rayuwarta, Umma tace "Gobe da safe sai mu je can gidan a kwaso duk wani abu naki" Jiddah ta gyada mata kai kawai, Umma ta mike tace "Toh sai da safe" Daga haka ta nufi kofa Jiddah ta bi ta da kallo wasu hawayen na kawowa idonta, Umma na fita Maimoon ta shigo dakin. Washegari misalin karfe Goma Umma ta kira Abuturrab, miss calls tayi masa kusan uku kafin ya daga, bata amsa gaisuwan da yake mata ba tace "Kana gidanka ne?" Yace "Ina nan" Umma tace "Ohk i am coming now" Bai ce komai ba ta katse wayar, tare driver ya kai su gidan Abuturrab da Jiddah da Maimoon da safiyya, mai gadi ya bude masu gate driver ya shiga da motar cikin compound, Umma ta sauka motar sannan su Jiddah, Hijab ne har kasa jikinta, suka bi bayan Umma xuwa entrance din parlon, a bude suka tarda parlon, yana kwance saman doguwar kujera da jallabiya, suna hada ido Jiddah tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na bugawa da karfi, sanye yake da jallabiya ya mike xaune a hankali yace "Ina kwana Umma?" Tace "Lafiya lau, ya gajiyan jiya?" Yace "Alhmdlh" Maimoon ta gaishesa ya amsa, Jiddah ma tace "Ina kwana?" Sai dai taki yarda ta kallesa, bai amsa ba ita dai ta xauna kasa kusa da kujeran da Umma ta xauna, Umma tace "Jiddah xata debi kayanta na nan ne" Ba tare da ya kalli Umma ba yace "Ohk" Umma ta mike tana kallon Jiddah tace "Mu je" Mikewa Jiddah tayi ta nufi stairs Umma na biye da ita Maimoon ma ta bi bayansu, da ido Abuturrab ya bi su har suka haura sama, Kaf sai da Umma ta kwashe duk abubuwan Jiddah dake dakin, Maimoon ce ke kai wa booth din mota, Ita dai Jiddah na tsaye jikin kofa sai kallonta take, ta rasa dalilin da yasa taji tana son tayi kuka, Umma ta mika mata babban ledan da ta hada duk abubuwan gaban madubi a ciki tace "Ki kai wannan" Jiddah ta karasa ta amsa ta nufi kofa ta fita, a stairs suka hadu da Maimoon, Maimoon tace "Kawo in kai toh" Jiddah ta kirkiri murmushi tace "Xan kai" Maimoon ta shiga dakin ita kuma fita, satan kallon parlon ta dinga yi taga baya nan, ta fita balcony, sosai gabanta ya fadi da ta gansa a xaune kan kujera yana danna wayarsa. Xata sauka stairs din balcony din taji yace "Toh ni dake wa yyi lose?" Ta juya tana kallonsa don bata gane me yace ba, yayi wani murmushi ya mike, speaking calmly yace "Kema kinsan wllh idan ba kaddara ba babu abinda xai hadani dake a rayuwa balle har in aureki bisa kuskure, aurenki da ni babban kuskure ne wanda nayi sbda in taimaki rayuwarki.. banda haka ai ni nafi karfin ki, komai da ya faru ya faru ne sbda haka Allah ubangiji ya tsara, duk da fin ki komai da nayi haka na hakura na xauna same roof dake sbda biyayya da kuma xuciyar musulinci, amma wai har ke xaki je ki sanar ma iyayena na sakeki? Toh yanxu da na maki sakin me hujja akwai wani abu da xai ragu a rayuwata ko kuma wani asara xan yi?" Ita dai kallonsa kawai take ko kiftawa babu, yayi wani murmushin kuma yace "Toh na maki duk abinda na maki saboda Allah ba don ki nuna kin san ni wataran ba, kai ni ko a hanya kika gan ni kar ki ta6a nuna kin ma san ni don kunya hakan xai bani, kiyi wucewarki inyi wucewata, na kuma fi kowa farin ciki da murnan xuwa karshen wannan al'amarin, i am now free like every other...." Jiddah dai kallonsa kawai take bbu ko kiftawa, ganin ya koma ya xauna cikin sanyin murya tace "Toh nagode" Daga haka ta juya ta kai ledan mota... Tare suka fito gidan da Umma bayan duk an kai komai mota, Har sannan yana xaune balcony, Umma tace "Toh sai anjima, yaushe xaka koma aikin" Yace "Anjima in sha Allah" Tace "Toh Allah ya tsare" Daga haka ta nufi mota, Maimoon tace "Sai anjima yaya" Yace "Ohk" Sai da Jiddah ta sauka balcony ta d'an kallesa tace "Sai anjima...."




*Rumor Creators how market? A masar dai ba a haka idan xaku gyara ku gyara, ku kuma masu karanta na bati da kuka fi kowa xakalkalewa a xo a biya bashi dai ko xa a samu nutsuwa, my fans dat wished me speed recovery ina godiya Allah ya saka da alkhairi sbda ku nace let me manage and give this little update na karfin hali, nagode sosai, snn abinda ke ci mun tuwo a kwarya shine yanda masu karantawa a free suka fi kowa bada hakuri, wllh duk sun cika min inbox, don Allah bakwa jin kunya ne, baka biya abu ba ka dage sai an ci gaba, tsaf ina da saved number din duk wanda yayi subscription din littafin nan ku ji in gaya maku* 🙄


Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




*Mîkyããj_Sããdy Beauty Soap*





*Hy my beautiful people ina gaisuwa🙋🏻♀️ku karka'de kunnuwanku da kyau ku ji💃🏻ina mai sanar muku da cewa akwai gara6asa me kyau ta musamman ga wanda suka saba sayen sabulunmu da ma wanda zasu fara saya🥰, akwai ragin kaso 20% bisa dari 100% ga wanda suka saba saye, sannan akwai ragin 10% bisa ga masu sha'awar fara saye🥰, akwai farashi mai sauki ga 'yan sari, me yapi wannan dadi kam🤔ki sayi guda 4 kanana a baki kyautar daya, ki sayi guda uku manya a baki kyautar karami daya, ki sayi bucket biyu a baki kyautar babban rubber daya😍 kema da kike da burin saya ku'dinki bai kai ba😰to ga naki, ki kawo customers uku ki karbi naki kyautar Sabulun😍😍*



*Kawata 'yar 'kwalisa me kike jira,ita mace fa kullum cikim yin ado da 'kãwa take😍 ya kamata ki yunkuro wajen ganin kin rabu da wannan kurajen da tabo tabon fuskan nan haka🥺, kinga kema sai a saka ki a layin masu 'kwalisa da bajakolin ado💃🏻😍uwar gida a daure ayi gyaran jiki, sbd karbar goron a wajen me gida🥰,, ina amaren bayan sallah ku pito ku sayi naku Sabulun kuje kuyi ta wanaka hmmm 😍kamshi kawai zaku yi tayi kaca kaca😍😍, laushin fata Baja baja😃😂😂a yunkuro azo a karbi kayan gyaran jiki tare da sabulun gyaran fata a wurin _Mîkyããj_Sããdy_🥰*



*Duk wanda suka gwada Sabulun mu sun san babu 'karanta a ciki🥰in dai fannin gyaran jiki ne to sabulunmu shine amsarku,, shi ke mai da fata ta zama babu Pimples, Acne, Spot, Stretch Mark, da Duk wata matsala da ta shafi fata,, akwai lightening,  nd glowing😍*



_*In kina son jikinki yai su6ul da shi, fata tai santsi da sul6i, ki yi haske me aji, 'kamshi kaca kaca ko ta Ina, ki ta fresh abunki hankali kwance ki zama Wankan madara yauqin zuma😍💃🏻Anty madam😃To ki mallaki 3d (Extra Whitening Soap, Ko da kudinki sai da rabonki hajiyata)💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*_



*Akwai hadin:*

*Mai da tsohuwa yarinya*

*Uwargida ta koma amarya*

*Amarya ta koma tamkar 'yanmata*

*'Yan mata su koma 'yan dagwai²*





_Ga masu bu'kata sai su tuntu6emu ta kafar sadarwa kamar haka;_

_Call/WhatsApp:08061570778_

_IG@mik_yaaj_saady_

Bayan sati biyu Jiddah na xaune dinning area ita kadai bayan magrib, Hijab ne har kasa jikinta, Huraira kuma na kitchen tana wanke wanke, gaba daya hankalinta na kan takardan gabanta taji an danna bell, mikewa tayi ta nufi kofar ta bude, ta koma baya tana kallonsa tace "Ina yini" Da murmushi yace "Lafiya lau Jiddah" ta juya ta koma parlon ya karaso ya xauna, tace "Ya Aunty Ramlah?" Yace "Tana gaisheku, Umma na daki ne?" Tace "Ehh" yace "Tou xauna mana" d'an murmushi tayi ta xauna edge din kujera yace "Kin fara karatu koh?" Tace "Eh" yace "Amma ki fada min gaskiya, kina ganewa?" Ta gyada masa kai, yace "Aa bude baki ki min magana" Sunkuyar da kai tayi har sannan tana murmushi tace "Ina ganewa" Yace "Toh wani rana da wani rana ku ke karatun?" Tace "Ranan litinin xuwa juma'ah" Yace "Asabar da lahadi fa?" Tace "Islamiyya muke xuwa tare da su Maimuna" Yace "Toh me da me ake koya maki litinin xuwa Juma'ahn?" Tace "Karfe tara na safiya take xuwa mu yi boko xuwa karfe biyu, sai kuma Islamiyya karfe uku xuwa shidda" Yace "Duk ita ke maki bokon da Islamiyya?" Ta girgixa kai tace "Aa wata ce daban take xuwa karfe uku" Yace "Maa sha Allah, kawo takardun naki in ga" Mikewa tayi ta nufi dining ya bi ta da kallo ta dauko jakar da duk litattafanta ke ciki ta dau har da na kan dining table sannan ta kai masa, ya amsa yana dubu abubuwan da suka yi na sati biyu, ita dai tana xaune tana wasa da fingers dinta, ya daga kai ya kalleta yace "Anya ke da kanki kike aikin nan da malama ke baki?" Tayi murmushi tace "Ni ce nake yi ka tambayi Maimuna" Yace "Maa sha Allah, ki dinga maida hankali haka kinji?" Tace "Toh" Ya dau wayarsa dake ring, ta jira har ya gama wayar ya ajiye sannan tace "Aliyu fa?" Daga kai yayi ya kalleta, ta sauke idonta yace "Waye Aliyu?" Jin bata ce komai ba yace "Ohh captain wai?" Still bata ce komai ba, yace "Yana kano, mun yi sati biyu bamu hadu ba, kuma bana jin ya xo weekend" Tace "Toh" Umma ce ta shigo parlon ganin Ahmad tace "Yaushe ka shigo?" Yace "Not too long" Ta karaso ta xauna yace "Ina yini Umma" Tace "Lafiya lau, yau ma baka xo da Ramlan ba?" Yace "Ehh na barta da su Aisha ne sun je can gidan" Umma tace "Ohk" kallon Jiddah tayi tace "Har kin gama karatun?" Tace "Aa ina kan yi" Tana fadin haka ta mike ta isa gun Ahmad ta kwashi duk takardunta ta wuce daki, Ahmad yace "Cewa nayi ta kawo in ga performance dinta and naga she is really trying" Umma tace "Gaskiya kam, she isn't dull kawai dai karatun ne bata samu ba, amma in sha Allah nan da few months a yanda naga take da hazaka she might catch up with her mate, tana da kwakwalwa kam maa sha Allah" Ahmad yace "Toh Allah ya sa hakan, sai ayi enrolling dinta jss3 ko?" Umma tace "Ehh" Ya shafa kansa yace "Umma daxu Yousuf ya kirani..." Umma tace "Ya aka yi?" Ahmad ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Wai a kan Jiddah..." Murmushi Umma tayi tace "Ni dai nasan ba haka nan yake xuwa gidan nan frequently ba da dalili, toh maa sha Allah..." Ahmad yace "But Umma ai bata bukatar wannan yanxu, she need to concentrate fully on her studies" Umma tace "Toh ai sai ka jira in gama magana ko... ni baxan hanasa alaka da ita ba, sai dai shigo da batun soyayya gareta yanxu isn't necessary, he should wait a little...." Ahmad dai bai ce komai ba. Aunty ce xaune gefen gadonta waya kare kunnenta tayi shiru fuskar nan nata a daure, can ta mike tace "Haka yace maki?" Daga daya bangaren Aneesah tace "Wlh Aunty" Aunty tace "Toh kyaleni da d'an iskan, nasan maganinsa...." Aneesah tace "Ni fa wllh Aunty yau kusan wata daya kenan na ma kasa gane kan relationship din nan namu" Aunty tace "Daina kiranki yayi?" Tace "Toh ai dama tun farko ba kira yake ba sai in ni na kira ya bi miss call, yanxu kuma ko na kira din ma sai sanda ya ga dama yake kira, sai yace aiki yayi yawa..." Aunty tayi shiru tana sauraronta, sai kuma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Amma kuna dai maganan still koh?" Tace "Aa muna magana, kawai sabon miskilanci da jiji da kai ya karo... Sai yayi ta cewa shi baya son damuwa, shi baya jin dadi, shi he want to sort somethings bothering him, shi yana son break, shi he wants to be alone for sometimes, haka dai wllh... Kamar baya son magana da ni" Aunty dake ta jin ta, tace "Amma ya siya maki abinda nace kice ya siya maki ko bai siya ba?" Tace "Aa ya tura min kudin har da kari ma" Aunty tace "Toh shkkn, xan kiraki xuwa anjima, ki kwantar da hankalinki" Tana kai wa nan ta katse wayar tayi dialing number Abuturrab, sai da ya kusa yankewa ya daga, yace "Ina kwana Aunty?" Tace "Wani laifin muka maka Aliyu yau kusan sati uku babu kai babu labarin ka?" Yace "Aa aiki ne yayi yawa yanxu..." tace "An sake employing dinka a wani airline din ne bayan wanda kake aiki?" D'an murmushi kawai yyi bai bata amsa ba, tace "Atoh gwara ai in ji, kuma ai kana shigowa kadunan, xuwa gida ne kawai baka yi" yace "Aa bana shigowa, amma xan shigo friday din nan in sha Allah" Tace "Toh ina saurarenka" Daga haka ta katse wayar. Hijab Jiddah ta dauka xata saka bayan ta gama shiryawa Maimoon ta hade rai tace "Meye hka kuma, ba ga mayafi na ajiye maki ba" Jiddah ta xaro ido tace "To ae an hanani" Maimoon tace "Wa ya hanaki?" Ta sake xaro ido sae kuma tace "Tou bari in sa" daukan mayafin tayi ta yafa, Maimoon ta washe baki tace "Waoww kinga yanda kika yi kyau kuwa" Murmushi kawai Jiddah tayi, suka fita xuwa dakin Umma, Umma tace "Kuna kai sakon ku dawo, ba sai na gaya maku kuna da Islamiyya karfe biyu ba" Maimoon ta marairaice tace "Yau dai kawai Umma, Sis Ramlah fa na can gidan" Umma tace "Toh ku bani xan ba Driver ya kai idan ya dawo" Maimoon ta xaro ido tace "Aa wllh ynxu xa mu dawo Umma" Kudin mota ta basu suka fita gidan, Jiddah na rike da ledan sakon da Umma ta bada su kai ma Hajja, karfe sha daya da rabi suka isa gidan, Maimoon tayi sallama bakin kofa tayi knocking sannan ta tura, Jiddah ta bi bayanta, babu kowa a parlon suka nufi part din Ummi, Ummi ta fito daga bedroom dinta jin sallama, ganinsu tace "Aa sannunku da xuwa" duk suka xauna suka gaisheta ta amsa da fara'a tace "Ku kadai?" Maimoon tace "Eh Umma ce ta aiko mu gun Hajja" Ummi tace "Ohk, ya karatu Jiddah" Jiddah ta kalleta ta d'an yi murmushi tace "Alhamdulillah" Ummi tace "Toh maa sha Allah, Allah ya taimaka" Maimoon tace "Ramlah ta koma ne Ummi?" Ummi tace "Aa tana ciki tana bacci" Maimoon tace "Toh bari mu kai ma Hajja mu dawo" Ummi tace "Ohk" mikewa tayi jiddah ma ta tashi suka fita daga parlon, dakin da Hajja ke sauka idan tana garin Maimoon ta nufa Jiddah na biye da ita, Maimoon tayi sallama bakin kofar sannan ta bude, Hajja ta daga kai tana amsa sallaman, karasawa ciki Maimoon tayi ta duka tace "Ina kwana Hajja" bata jira ta amsa ba ta kalli Abuturrab dake xaune dakin yana kallonsu daga sama har kasa ta cikin glass din idonsa, ta sunkuyar da kanta tace "Ina kwana yaya?" Yace "Me yasa baki ajiye mayafin a gida kin fito haka ba?" Maimoon ta hau gyara mayafin jikinta tana murmushi, Jiddah dai kanta na kasa ta durkusa ita ma ta gaida Hajja, sannan ta d'an kallesa taga wayarsa yake dannawa tace "Ina kwana" Ya kara wayar a kunne ya mike ya nufi kofa, Hajja ta saki baki tana kallonsa har ya fita, can ta kalli Jiddah tace "Ji ruba66e, toh ke idan ba dai neman wajen xama kike ba meye na gaishesa bayan iyayensa sun sa ya sakeki babu ko dar ya cike takarda ya mika maki, ai babu abinda kika hada da shi kuma yanxu, toh ga dai shi ya gwaleki, tun jiya fa na samu labarin dawowar almurin amma kun ga sai yanxu ya shigo gaidani yana shan kamshi ya wani sha uban gilashi kamar sabon makaho, Aa bak'in halinsa ya fi karfinsa gaskiya, alhalin sbda shi nake xaune har yau a gidan nan ban koma masar ba, to Hafsah ta ce min sati me xuwa xa a kai kudi gidan yarinyar da yake so da aure amma in ja bakina inyi shiru tunda ba a gaya min ba tukun, shine yasa nake ta xaune nan Allah" Maimoon dai sai murmushi take, Hajja tace "Toh aiko ku Ramlan tayi?" Maimoon ta ajiye mata ledan kusa da ita tace "Ehh tace mu kawo maki wannan" Hajja ta leka cikin ledan tace "Ahh da kyau, baiwar Allah nace mata gobe xan tafi shine ta bada tsaraba a kawo min, to tafiya ai ta lalace tunda auren Aliyu ya tunkaro, yanxu shigowarsa nake tambayarsa shi ma ya tabbatar min da haka ne" Jiddah dai sai kallon Hajja take, Maimoon tace "Toh Allah ya kai mu lafiya" Hajja tace "Ameen, ita ma Ramlah gata can ta xo tun shekaranjiya, kilan mijin baya nan, amma da kyar idan ba ciki ne da ita ba, kai cikin ne ma wllh, sai wani salalo salalo take" Maimoon ta kalli wayarta dake ring ta mike tace "Xa mu koma Hajja, sbda muna da Islamiyya karfe biyu" Hajja tace "Toh ai shkkn, anjima xan sa Aliyu ya kawoni in mata godiya idan ya ga dama kenan, kabu kabu fa yake amma jin kansa yake kamar me wani sana'ar arxiki baya ganin kowa da gashi, ga d'an banxan girman kai, ba ga masu kabu kabun ba muna ganinsu a tashar mota, ga yan acaba suma ai duk kabu kabun ce, to kuma waye shi Allah na tuba" Su dai basu ce mata komai ba suka fita dakin, sai a snn Maimoon ta mika ma Jiddah wayar tace "Yousuf" Jiddah ta amsa ta daga sannan ta kai kunne, murya kasa kasa Maimoon tace "Don Allah kice ya xo ya daukemu basu da nisa sosai daga nan" Tana fadin haka ta wuce bangaren Ummi, Jiddah ta nufi parlor, cikin sanyin muryarta tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau, me Maimoon take rada maki?" Murmushi tayi ta xauna saman kujera tace "Aa babu komai, ya ciwon kan yayi sauki?" Yace "Alhmdlh, ya su Umma?" Tace "Umma tana gida" Yace "Ku kuna ina?" Tace "Umma ta aiko mu gidansu Aunty Ramlah" Yace "Ohk, yaushe xaku koma gida?" Tace "Karfe biyu xa mu tafi Islamiyya" Yace "Baxa ku dade ba kenan?" Tace "Eh" yace "Toh in xo in maidaku gida?" Ta d'an yi shiru, yace "Kin fa ce kin daina taurin kai" D'an murmushin tayi ta kwantar da kanta jikin kujera dai dai nan suka yi ido hudu da Abuturrab dake xaune dinning area din parlon da laptop gabansa, wani faduwa taji gabanta yayi, Yousuf yace "Kinyi shiru" Ta dago kanta tace "Toh sai ka xo" Yace "Good, in few minutes time xan iso yanxu in sha Allah" Cikin sanyin murya tace "Toh" Katse wayar yayi, ta dinga kallon screen din, can ta saci kallon Abuturrab taga laptop dinsa yake dannawa, ta mike ta wuce part din Ummi, ya bi ta da ido. Karfe daya saura Yousuf ya iso kofar gidansu Abuturrab, ganin xa a tada sallah ya sauka ya shiga masallacin kofar gidan, bayan an idar ya kira number Maimoon, Maimoon ta mika ma Jiddah, Jiddah na kai wa kunne yace "Ina waje ku fito" Jiddah tace "Toh" Katse wayar yayi, suka yi ma Ummi sallama a bedroom dinta sannan suka fita, gaban Maimoon ya fadi ganin Abuturrab da ya fito daga masallaci, amma taki yarda su hada ido, Jiddah kam bata ma gansa ba ta kalli Maimoon tace "Ke da kike son ya xo ya daukemu ai ke xaki yi jagora" Maimoon tace "Don Allah ke dai mu je" Jiddah ta fara tafiya Maimoon na biye da ita, ta bude front seat ta shiga, Maimoon ta shiga baya, sai a sannan Jiddah ta ga Abuturrab da ya tsaya yana kallonsu, Yousuf da ya gansa shi ma yace "Ba yayan nan naku bane wancan" Maimoon ta kirki murmushin karfin hali tace "Ehh, kaje gu gaisa ya Yousuf sai kace masa Umma ce tace ka xo ka daukemu" Ta madubi ya kalleta ta kara kirkiran murmushi, Jiddah dai taki yarda ta sake kallon wajen motar, Yousuf ya bude motar ya sauka ya nufi gun Abuturrab da ya kara waya a kunne roaming about the gate, hannu ya mika masa hade da sallama yana kallonsa, Abuturrab yyi stretching nasa hannun, nan suka gaisa sannan yousuf ya juya ya koma gun motarsa, yana shiga motar Maimoon da duk hankalinta ya tashi tace "Kace masa Umma ce tace ka xo ka daukemu?" Yousuf yace "He don't have any business with that" Maimoon bata kuma cewa komai ba, ya tada motarsa suka bar anguwar. Hansai ce xaune da aminiyarta Zulai gaban wani katon mutumi da babu riga jikinsa, Hansai duk ta baxa kunnuwa da idanuwa tana jiran jin abinda xai ce bayan ya gama dube dubensa, Mutumin ya kalleta da idanuwansa da aka lafta ma uban kwalli yana girgixa kai cikin katon muryarsa yace "Babu wani aure a kan yarinya, amma tana can cikin kwanciyar hankali da daula... Bata da wani matsala a rayuwa, ba abinda ta rasa..." Hansai ta sharce wani bakin xufa a goshinta tace "Toh Malam babu abinda xa ayi da xai sa hankalinta ya karkato ta dawo gida, idan ya so sai a maida min Bibalo can, wllh Malam ina fama da bakar talauci yanxu, jarin babu shi babu dalilinsa kamar dai kar ta bar wajen yarinyar, ga basussukan jama'a a kaina suna min tonon asiri har na fara tunanin in siyar da d'an gidan da muke ciki in biya bashi sai mu kama haya da sauran, in sake jan wani jari, to amma gidan fa duk ya ru6e, wa xai siya da mutunci" Mutumin wanda da alama ya gaji da surutunta yace "Ki fadi abinda kike so ayi a takaice" Hansai ta gyara xama tayi kasa da murya tace "Kaga Malam so nake kayi duk abinda xai dawo min da ita duk inda take, ta dawo wajena ni ban k'i ko karuwanci ma ta xo ta min ba mu samu na rufa ma kai asiri, nasan dai yanxu karya ne ace bata san maxa ba, dama gata da kyau ga farin jini wllh kasuwa xa mu yi sosai" Zulai sai gyada kai take, Mutumin yace "An gama, dubu hamsin kudin aikin ki" Zulai ta dafe kirji tace "Dubu ashirin fa Malam, ina nagansa? Bani da shi bani da dalilinsa wllh, ko dubi daya na kaina bana magani yanxu" Yace "Toh ku tashi ku tafi duk ranan da ku ka shirya ku dawo" Xata yi magana cikin tsawa yace "Ku fita nace sai kun shirya" Da sauri suka mike suka fita a d'an dakin, Hansai ta fashe da kuka tace "Yanxu ya xanyi Zulai, kema kinsan bani da ko dubu biyu na kaina wllh, duk na siyar da kayan dakina babu komai balle in dauka in siyar" Zulai tace "Daga karshe dai gidan nan kawai xaki siyar in dai bukata xai biya, in har Jiddah ta dawo ai sai kin kera wanda ya fi wannan a cikin gari, dama ba sai an 6ata ake gyarawa ba, kawai mu je a sa gida a kasuwa..." Hansai ta share idonta tace "Toh shkkn, in sha Allahu baxan ji kunya ba" Daren ranan Jiddah na karatu a dinning kamar yanda ta saba bayan magrib aka bude kofar parlon, Hajja ce ta shigo sakale da jakarta tace "Assalamu alaikum" Jiddah ta amsa sallaman tana mata sannu da xuwa, Hajja tace "Ina Ramlan take?" jiddah ta mike tace "Tana daki bari in mata magana" Hajja tace "Toh yi maxa wancan d'an daban sai ya iya tafiya ya kyaleni, kinsan dama da kyar ya kawoni sai da uban ya sa baki" Jiddah dai bata ce komai ba ta tafi dakin Umma, ba a dau lkci ba Umma ta fito sanye da Hijab da murmushi tace "Sannu da xuwa Hajja" Hajja tace "Yauwa Ramlah daxu naga abun arxiki shine nace bari dai in taso in xo da kaina inyi godiya, don mu a Masar haka ake, Allah yayi maki albarka ya kara arxiki sai dai tafiyar ma ta lalace don wannan yaro Aliyu gobe xa a kai kudin aurensa kuma ina nan har sai anyi komai idan Allah ya yrda" Umma tace "Allah sarki, ai da kinyi waya na xo kawai Hajja ba sai kin fito da daddaren nan ba" Hajja tace "Aa barni na xo, banda me sonka wa xai tuna da kai har ya baka tsaraba haka..." Tana kai wa nan ta mike tace "Toh ni dai bari in koma ni da wancan d'an kabu kabun ne muka xo kar ya tafi ya barni in rasa tudun dafawa" Umma tace "Tare da Aliyu ku ke?" Hajja tace "Ehh wllh, sai da ma ya xageni a hanya muna tahowa daga nace masa ba jirgi fa yake figa haka ba, ni dai bakina alaikum naki biye masa ya kunyata ni a kasar mutane" Umma tace "Amma yace wani abu, shine baxai shigo ya gaisheni ba??" Hajja tace "Ahaf ai wannan mutumi dai daga d'an iska sai shi, baya ganin kowa da gashi" Umma ta kira Huraira a daki tace "Tafi kice ma Abuturrab ina kiransa a waje" Tace "Toh" sannan ta fita, Hajja ta koma ta xauna tace "Gwara dai kiyi masa soso da sabulu sannan ki hadani da d'an arxiki ya maidani gida kar  kasheni a hanya" Umma dai bata ce komai ba, Maimoon ta fito tare da Safiyya suka gaidata, Hajja tace "Allah maku albarka, ya baku ilimi me amfani" Jiddah dai tuni ta koma ta ci gaba da karatunta a dining, Ba a dau lkci ba Abuturrab ya shigo parlon kansa a kasa, Ya karaso ciki ya gaida Umma da ladabi tace "Saboda ka isa yasa ka xo gidan nan ka xauna mota baka shigo gaisheni ba?" Ya ki kallonta a ido, yana kame kame yace "Aa waya nake yi a motar dama xan shigo Umma" Hajja tace "Karya yake algungumi har cewa yayi minti biyar ya bani wllh, ni dai ki hadani da me hankali ya maidani gidan d'a na don Aliyu abun tsoro ne, babu uwar da na hada dashi balle ya cuceni, gashi uwar tayi ta xuba masa ido kamar tana tsoronsa bata fada masa gaskiya, ita kuma yar Benuen can tayi kane kane a kan lamarinsa, ai ni ina ganin iftila'i tunda ja sauka gidan Usman, abubuwa suke babu tsari kamar dai gantalallu" Abuturrab dai sai kallonta yake ta gefen ido, Umma tace "Toh ka kyauta, from henceforth i don't want to see ur legs in my house again, get out" Bai ce mata komai ba ya juya ya nufi kofa ya fita, Jiddah ta bi sa da kallo, Hajja ta ajiye jakanta ta cire mayafinta ta linke ta ajiye, ta gyara xama tace "Dama idan babu me mayar dani gida sai dai in kwana a nan kawai, baxan bi mutumin can ba abu ya lalace min" Maimoon ta fashe da dariya Hajja ta marairaice tace "Allah kuwa ke baki ga yanda ya wani fita kamar Zaki ba daga fadan gaskiya" Umma tace "Kiyi xamanki kawai a nan Hajja" Hajja tace "Toh a kai min kayana daki" Karfe tara da rabi Umma na dakinta tare da Jiddah dake gyara mata press din kayanta, Umma tayi dialing number yayarta, nan kuma ta sanar mata duk abinda Aliyu yayi mata daxu, Ummi tace "Kiyi hakuri Ramlah, Ni yayi ma ba ke ba, kinsan wannan xancen auren da ya kirkiro ma kansa da Hafsah kawai suke sabgarsu, ban san komai a kai ba, uban ne ma yace min gobe xa su kai kudi, wllh bai ce min komai ba shi har yanxu" Umma tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Yaya ina ta ce maki a tashi tsaye kince Aa ba komai, wllh wannan abu ba lafiya a ciki, ga dai abu kiri kiri fa" Ummi tace "Aa ki kyalesu kawai, shi ba yaro bane kuma sarai da hankalinsa, abinda kike tunani ba shi bane, shi dai ne ya xabar ma kansa haka, ai ba shi daya na haifa ba dai? Dama shi da namiji ai wasu kake haifa ma" Umma tace "Ki kyaleni da shi xan saita masa xama wllh" Sun jima sosai suna waya, Jiddah dai duk sai bata ji dadi a ranta ba, taji kuma a xuciyarta tana son yi ma Abuturrab magana, to amma a ina xata gansa??




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you





Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems


Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada


Instagram -fareeskinglow_89

TikTok-fareeskinglow

Facebook page-fareeskinglow 

WhatsApp -08031898240

Ranan asabar kamar yanda Ummi ta sanar ma Umma aka kai kudin auren Aneesah, on that same day kuma aka saka ranan bikin wata biyu, Umma na xaune parlor da yamma Hajja ta shigo parlon ta rike ha6a tace "Ramlah kinji wai an sa bikin Aliyu nan da wata biyu, yanxu Usman ya kirani yake sanar min, sun kai komai saura sadaki" Umma tace "Toh Allah ya sanya alkhairi" Hajja tace "Atoh dai, mu iyakar abinda xa mu ce kenan, yaron da baya mutunta iyayensa...." Daga haka ta juya ta koma ciki, ita dai Umma bata ce komai ba. Abuturrab na xaune shi kadai a parlorn gidansa dake Abuja idonsa na kan screen din wayarsa da yake dannawa.... knocking din kofar parlon aka yi ya kalli hanyar kofar, amma bai yi wani yunkurin tashi ya bude ba, aka sake knocking duk a tunaninsa Aneesah ce, wayar hannunsa ya fara vibrate ya ga Ahmad, yyi ta kallon wayar kafin ya daga ya kai kunne, Ahmad yace "Are visitors not welcome any longer?" Abuturrab yace "Nace maka ina nan ne?" Ahmad yace "Su kuma takalman da ka bari bakin kofa fa?" Abuturrab bai ce komai ba ya katse wayar, bayan few seconds ya mike ya nufi kofar ya bude ya dawo cikin parlon, kallonsa kawai Ahmad yake don rabon da ya gansa an yi sati uku yanxu, ya kirasa severally baya responding, har ma ya daina kiransa, Ahmad ya karasa ya dau drugs da ya gani kan center table yana jujjuya su, lkci daya ya ajiyesu yace "Bai kamata ka dinga shan irin wa ennan magungunan saboda yanayin aikin ka, and why are u having sleepless night?" Abuturrab ya kallesa yace "Haka nace maka?" Ahmad yace "Aa haka dai drugs din yace min..." Abuturrab yace "Then you are mistaken, ka kara gaba can da karyar likitancin ka..." Murmushi Ahmad yyi yace "Toh Shikenan, amma da an canxa maka prescription din drugs din" Abuturrab yace "Wannan kuma likitan da ya fi ka yayi prescription din" Ahmad yace "Ohk then, kwana da yawa, i called severally baka responding ko nayi wani laifi ne" Abuturrab ya ki kallonsa, Ahmad yace "Shine dai yau sanin schedules dinka nace bari in karaso gidanka na nan inji laifin da nayi" Abuturrab yace "I just decided to live my life without hypocrite" Ahmad ya buda ido sosai yace "Hypocrite? Su waye hypocrite din?" Abuturrab yace "Decision dina kenan" Ahmad yace "Kai ne babban hypocrite ai tunda har kana tunanin anyi wronging dinka amma ka kasa bude baki kayi magana ka dau gaba da mutane, balle ni dai nasan i did nothing to you" Abuturrab ya jefa masa wani kallo yace "You did nothing to me?" Ahmad yace "Of course, ba abinda na maka" Abuturrab yace "That's ur cup of tea... To yanxu bayan munafurcin da ku ka je ku ka hada har aka sa na saki wancan yarinyar ko da akwai wani abu da ya ragu a rayuwata tun bayan wannan lkcn, akwai wani abu da nayi loosing?" Ahmad yace "Eh mana gashi har bacci kayi loosing, sbda duk wanda ke isasshen bacci babu abinda xai hadasa da wa en nan kwayoyin dake gabanka...." Kallonsa kawai Abuturrab ke yi babu ko kiftawa, Ahmad ya daga shoulder yace "And da bai dameka ba ko baka yi loosing komai ba babu abinda xai sa ka dinga isolating kanka daga cikin al'umma, but that's not my problem now, my major problem is that daga yanda na ganka nasan you are down for now may be they took u unexpected, don haka take a break from work, kada wataran muje mu ji labarin da ba shi kenan ba, shi Pilot banda nutsuwa da kwanciyar hankali ba a bukatar komai daga garesa, amma yanxu yanda kake a birkicen nan bai kamata ka dinga daga al'umma xuwa sararin samaniya ba, toh bayan wannan kuma ina son ka cire duk xargi a ranka, ka bar ganin ko da hadin bakina aka saka ka saki Jiddah, i know nothing about it... Kawai dai coincidentally nayi maka magana da kwana biyu sae kuma abinda ya faru ya faru, da ina da niyyar sanar ma kowa tun farkon auren xan sanar ae ba sai da aka dau lkci ba" Abuturrab yace "To ko kai ka fada ko ba kai ka fada ba ance maka abun damuna yyi ne? Banda ma wani burden da aka sauke min meye nayi loosing a lamarin nan, sae ma peace of mind da freedom da na samu, plss close this chapter, ba shi da wani amfani a gareni" Ahmad yace "Ok then, i heard su Abba sun xo gidansu Aneesah yau" Abuturrab yace "You heard right!!" Ahmad yace "Toh Allah ya sanya alkhairi" Abuturrab bai tankasa ba ya mike ya shiga kitchen, Ahmad ya bi sa da kallo yana murmushi, Hmm is Abuturrab really sure he looses nothing living without Jiddah?" Har karfe sha biyu Ahmad na gidan kasancewar bashi da night duty, ya tashi ya shiga bedroom yyi kwanciyarsa ya bar Abuturrab yana operating laptop. Karfe uku da yan mintuna Ahmad ya fito parlor ganin Abuturrab bai shigo ba, bai gansa a parlon ba har sannan kuma wutan parlon na kunne ga laptop dinsa ka a kunne, kitchen ya karasa nan ma bai gansa ba, ya fito ya duba sauran dakunan duk baya ciki, ganin kofar parlon da ba ayi jamming ba ya karasa ya bude kofar, xaune ya gansa balcony with his phone, da mamaki Ahmad yace "What are you doing here by this time?" Abuturrab yace "Zafi nake ji" Da mamaki Ahmad yace "Xafi kuma ga Ac ga fanka? Are you okay?" Abuturrab yace "To iskan waje nake so ba na Ac ba" Ahmad ya fi minti biyu tsaye yana kallonsa, Abuturrab bai kuma kallon inda yake ba, Ahmad yace "Ka sha drugs din naka?" Abuturrab yace "Ae ba kai ka min prescribing ba balle ka tambayeni" Ahmad bai kuma ce masa komai ba don sae a sannan ya tuna cewar ya sha wajen karfe sha daya, juyawa yyi ya koma parlon ya xauna yana mamakin is Abuturrab okay?? Har kiran sallan farko Abuturrab na xaune balcony, Ahmad ya gaji da xama ya koma daki ya kwanta. Da asuba Ahmad ya fito da alwala parlon, dai dai sanda Abuturrab ma ya fito daga bathroom din parlon, shi dai Ahmad kallonsa kawai yake har ya fita don bai ga alamar ya kwanta ba, Abuturrab ya bi bayansa xuwa masallaci... Bayan an idar sun fito mosque din Ahmad na kallonsa yace "Karfe nawa xaka yi piloting yau?" Abuturrab yace "Karfe daya..." Ahmad yace "Okay..." Gidan ya shiga ya dau makullin motarsa ya fito ya ga Abuturrab xaune balcony yace "Xan dawo before 7" Da ido Abuturrab ya bi sa har ya wuce. Kamar yanda ya fada karfe bakwai ya dawo gidan, xaune ya tadda Abuturrab a parlor ya jinginar da kansa jikin kujera, Ahmad ya xauna ya ajiye ledan hannunsa yace "Good morning" Abuturrab yace "Afternoon duty ka koma yanxu" Ahmad na bude ledan da ya ajiye yace "I think u are suffering from lack of sleep" Abuturrab ya dinga kallonsa yace "Wa ye xaka yi ma allura? Ni nace maka bani da lafiya ne??" Ahmad ya kallesa yace "Aa baka ce min ba, but this will help" Abuturrab ya gyara xama yace "You are wasting ur time, gwara ma kar kayi wasting alluranka, idan kuma ka hada sae ka nemi wanda xaka yi ma" Ahmad bai tanka sa ba ya gama hada ruwan alluran, sannan yace "Kaga kar ka 6ata min lkci ka 6ata ma kanka lokaci Captain, how will a normal human being stay all through the night without sleeping, sannan anjima yaje ya daga jirgi with over 300 passengers or less??" Abuturrab yace "Wai kai nace maka banyi bacci bane, shkkn kuma mutum daga farkon dare har karshe sae yayi ta bacci?" Ahmad yace "Duk kwararren likita ya ganka yasan baka bacci bawan Allah, don haka idan xaka daina gardama ka daina...." Abuturrab yace "Ashe kai kwararren likita ne" Mikewa Ahmad yyi yace "You ur self will feel relieved after the injection...." It took anoda 15mins to convince Abuturrab sannan ya yarda Ahmad yyi masa alluran, in just less than 20mins ya kwanta nan kan doguwar kujera, Ahmad dake watching dinsa yace "Da dai ka tashi ka shiga ciki baccin xae fi maka ma'ana" Tashi Abuturrab yyi ya wuce bedroom dinsa, yyi rub da ciki saman gado.... Sae wajen takwas da minti goma Ahmad ya bar gidan bayan ya ga Abuturrab yayi bacci. Sha biyu da rabi na rana Ahmad ya dawo gidan ya tadda Abuturrab yana bacci har sannan, ya ajiye masa ledan takeaway din abincin da ya kawo masa, ya karasa yana kallonsa da kyau, lkci daya Abuturrab ya bude ido, ya dafe forehead dinsa yace "What's the time, our flight is..." Da sauri ya mike xaune yace "Karfe nawa?" Ahmad ya rungume hannu yace "This is after 12" Abuturrab ya xaro ido yace "What????" Tashi yyi daga kan gadon yaji wani jiri ya debesa ya koma, Ahmad yace "Look, don't deceive ur self nd ur Airline Captain, ka tura masu text yanxu cewar baka da lafiya" Abuturrab yace "Ni nace maka bani da...." Rike cikinsa yyi da sauri, yace "I feel like throwing up" Ahmad ya karasa ya bude masa bandakin, da kyar Abuturrab ya tashi ya shiga bathroom din. Karfe shidda suka iso train station na rigasa, Salem na cikin mota yana jiransu, Ahmad ya bude front seat ya shiga, Abuturrab ya xauna bayan motar ya jinginar da kansa da seat, Salem na kallonsa ta madubi yace "How are you feeling now?" Abuturrab yace "Alhmdlh" Salem ya gaisa da Ahmad sannan ya tada motar suka bar station din. Da magrib Aunty na tsaye kan Abuturrab dake kwance saman gadonsa with drip, tace "Ko wannan aikin naka ai ya isa yyi weighing dinka down, aiki babu hutu kullum mutum na sararin samaniya" Shi dai bai ce mata komai ba, tace "Toh Allah ya sauwake" daga haka ta juya ta nufi kofa ta fita, Aisha ce ta shigo dakin da cup din shayi ta ajiye masa tace "Ya jikin yaya?" Yace "Ummi fa?" Tace "Tana can daki" bai kuma cewa komai ba ta ajiye shayin ta fita. Umma ce xaune parlor tana kallon Ahmad da bai jima da shigowa gidsn ba, tace "Toh ya jikin nasa yanxu?" Ahmad yace "A'a da sauki nayi masa allurori kuma na sa masa drip" Umma tace "Ikon Allah, kuma yaya bata gaya min ba wllh, bari in kirata" Wayarta ta dauka ta shiga kiran yayarta, Bude kofar parlon aka yi Jiddah ta shigo da sallama rike da qur'ani da takardunta, Ahmad ya amsa, ta karasa parlon ta duka kasan carpet a hankali tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau Jiddah, har kun gama karatun?" Tace "Eh, ya Aunty Ramlah?" Yace "Tana can gida ai, baku je bane?" Tayi murmushi tace "Aa bamu je ba" Umma tayi ma Ummi sallama bayan ta daga wayar, suka gaisa sannan tace "Yaya ashe Aliyu bai ji dadi ba" Ummi tace "Ehh haka aka ce min" Umma ta kalli Ahmad tace "Wai dama ba can gida yake ba?" Ahmad yace "Can yake" Umma tace "Toh baki shiga kin dubasa bane Yaya?" Ummi tace "Aa masu dubasa dai nayi, ni yace min bashi da lafiya ne?" Umma tace "Aa yaya ai rashin lafiya daban ne, da kin shiga kin dubasa ai, nima ynxu Ahmad ke gaya min shi ya taho da shi daga Abuja ma" Ummi tace "Allah ya kara mana lafiya gaba daya" Umma ta d'an yi shiru sae kuma tace "Toh Ameen" sallama suka yi ta ajiye wayar, Umma ta kalli agogo dake nuna biyar da rabi sannan ta kalli Jiddah tace "Malamar ta tafi ne?" Jiddah tace "Ehh ta tafi" Wayar Umma ya fara ring ganin Ummi ke kiranta ta dau wayar ta mike ta wuce cikin daki, Ahmad na kallon Jiddah yace "Hope baki bukatar wani abu yanxu?" Ta girgixa kai tace "Aa ba komai" Yace "To ya karatun?" Tace "Alhmdlh" Yace "Kina dai ganewa sosai ae" Murmushi kawai tayi tace "Ina ganewa" yace "Toh ki dinga maida hankali sosai pls kin ji?" Ta gyada masa kai, a hankali tace "Ina son in tambayeka wani abu" yana kallonta attentively yace "Toh ina jin ki Jiddah" Ta sunkuyar da kanta tace "Don Allah xaka iya kai ni can gidanmu in ga Baabarmu?" Sake baki yayi yana kallonta, can yace "Me xa kiyi ma baabar taku?" Cikin sanyin murya tace "Ina son xuwa in gaisheta" Ahmad ya girgixa kai yace "ko xaki je ba yanxu ba tukun Jiddah...." Tayi kasa da murya tace "To akwai wata Iyah a layinmu, tana min kirki sosai, baxan iya xuwa gaisheta ba ita?" Da mamaki Ahmad ke kallonta, can dai yace "A layin baabar taku?" Ta sunkuyar da kanta, Murmushi kawai yayi ya rasa abinda xai ce mata... Umma ce ta shigo parlon, tana kallon Ahmad tace "Idan anyi magrib sai ka kai ni can gidan in duba Aliyun" Ahmad yace "Toh Allah ya kai mu" kitchen ta wuce, Jiddah na kallonsa tace "Bashi da lafiya ne?" Ahmad yace "Ehh amma da sauki" Tana kallonsa tace "Nima xan iya bin ku in gaishesa da jiki?" Ahmad yace "Sai yanda Umma tace" Bata kuma cewa komai ba, bayan few seconds ta kallesa taga kallonta yake, murmushi ya sakar mata, ta sunkuyar da kanta tana murmushin ita ma sannan ta mike tace "Xan kai kayan karatuna daki" Yace "Toh Jiddah" Tana fadin haka ta yi hanyar dakinsu. Da magrib kamar yanda Umma tace ta shirya don xuwa duba Abuturrab tare da Ahmad, Jiddah ta rasa ta yanda xata ce mata ita ma tana son xuwa ta dubasa, ganin Ahmad ya fita kafin Umma ya fito ta bi sa da sauri ta riskesa a waje tace "Yaya don Allah xaka tayani gaya ma Umma, ni ina jin tsoro" Ya wara ido yace "Aa nima ba ruwana sai dai ki gaya mata da kanki" Jikinta yayi sanyi, a hankali tace "Toh" sannan ta juya ta koma cikin gidan, Umma ta fito parlor da hijab da jakarta tana kallonsu Maimoon dake parlon tace "Kar dai ku bar ruwa ya cika yyi ta xubewa...." Maimoon tace "Umma ni ma xata da mu xa ku je mu duba yayan muma?" Umma tace "Ba cewa kika yi kina da Hadda ba" Maimoon tace "Toh shkkn sai kun dawo" Safiyya dai na xaune tana danna wayarta, Umma ta nufi kofa Jiddah ta bi ta da kallo, a hankali tace "Umma sai kun dawo" Umma tace "Yauwa, kema kiyi karatun ki duk da dai ba kallo kike ba na sani" Jiddah bata ce komai ba har Umma ta fita parlon... Umma na shiga mota Ahmad ya kalleta yace "Umma na xata da su xa mu je can gidan su duba Aliyun, daxu Mumy ta tambayeni nace xan taho da su...." Umma tace "Toh ai ni baka gaya min ba, kuma sai a bar Huraira ita kadai a gidan?" Ahmad yace "Toh shkkn" Xai tada motar Umma tace "Bari su fito din dai" Wayar Safiyya Umma fa kira, tana dagawa tace "Safiyya wai yayanku ku fito mu tafi tare" Tana fadin haka ta katse wayar, Tun da suka fito outside gate din Ahmad ke kallon Jiddah sai dai ba ga expression da yake expecting gani a fuskarta ba, ita da Maimoon suka shiga bayan motar sannna Ahmad ya kunna motar suka bar layin.... A kofa gida yayi parking, Safiyya ta sauka sannan jiddah ma ta sauka, su Umma ma suka sauka duk suka shiga gidan, Ummi ce xaune parlor tare da Hajja, Hajja na cewa "Tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin irin haka ba wllh sai a kanki..." Sai kuma tayi shiru tana amsa sallaman Umma, Umma tace "Sannu Hajja" Hajja tace "Yauwa sannu, sai kika ji Aliyu ba lafiya ko?" Umma tace "Eh wllh" Hajja tace "Toh mu ma haka muka ji, ashe wannan yaro Ahmad ne ya tafi ya dauko sa a Habuja rai a hannun Allah, ni dai dama nace wannan halin da ya tsiro ma kansa ba halinsa bane, ashe bashi da lafiya ne bawan Allah" Umma tace "Allah dai ya basa lafiya, yana dakinsa ne?" Hajja tace "Ehh yana can an kara masa ruwa, kai har makota babu wanda bai shigo dubasa ba amma uwarsa ta ki shiga ban san dalili ba" Umma dai bata ce komai ba ta yi hanyar dakin Abuturrab, yana xaune hannunsa rike da bowl din farfesun hanta, Aunty ma na xaune dakin tana cewa "Idan ka ci wllh xaka ji dadin bakinka, sannan kar kaji komai ni da kaina na maka sai da na tsaftace shi" Aunty tace "Aa sannu da xuwa Hajiya Ramlah" Umma tace "Yauwa sannu ya mai jiki?" Aunty tace "Aa yaji sauki wllh, ai da ma baku wahalar da kanku kun fito ba, jiki ai da sauki sosai" Umma na kallonta tace "Xuwa duba d'an nawa ne wahal da kai?" Aunty tace "Aa wai naga dare yayi ne ai..." Umma tace "To ba wahal da kai bane, d'a na ne halaq malaq" Aunty dai bata ce komai ba, Umma na kallonsa tace "How are you feeling now" Ya sunkuyar da kansa yace "Alhmdlh da sauki" Aunty tace "Nace maki ai da sauki" Umma ta kalleta tace "Naga shi ma yana da baki ai Hafsah" Aunty ta mike tace "Bari a kawo maka shayin Aliyu" daga haka ta fita, Maimoon da Safiyya ne suka shigo dakin da sallama, Umma da ta nemi waje ta xauna ta kallesu tace "Ina Jiddar?" Sai a sannan Abuturrab ya daga kai suka yi ido hudu da Jiddah da ta shigo dakin a lkcn, Maimoon da Safiyya suka xauna kasan carpet din dakin suna kallonsa suka yi masa ya jiki, yace "Alhmdlh" kusa da Umma Jiddah ta xauna a kasa tana kallonsa a hankali tace "Ya jiki?" 



Ayi min afuwa jiya ban dawo da wuri gida ba... Idan naga da sarari xanyi update later in sha Allah... Thanks for understanding.




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via


 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems


Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada


Instagram -fareeskinglow_89

TikTok-fareeskinglow

Facebook page-fareeskinglow 

WhatsApp -08031898240

Abuturrab bai ce komai ba ya ci gaba da shan pepper soup din hannunsa, Jiddah ta sunkuyar da kanta jin bai amsa ba, Umma tace "Amma you are getting much better now" Ya kalli Umma yace "Alhmdlh" Tace "Toh Allah ya kara afuwa..." Mikewa tayi tace "Allah ya sauwake" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ameen" Kofa ta nufa Jiddah ta bi ta da kallo sannan ta juya ta kallesa suka hada ido, bata san sanda ta mike ba tana son fita dakin taji muryarsa a tsakiyar kanta, "Dauko min ruwan gora a kitchen" Kallonsa tayi don ta tabbatar da ita yake, ganin shi ma kallon nata yake tace "Toh" sannan ta juya ta fita dakin, Ya kalli su Maimoon da ke kallon tv dake aiki a dakin yace "Toh nagode" Kallonsa suka yi a tare da sauri, Maimoon ta wara ido tana kokarin mikewa tace "Allah ya sauwake Yaya" Yace "Ameen" Safiyya tace "Allah ya kara lafiya" a tare suka fita daga dakin suka kullo masa kofar, bayan few minutes Aunty ta shigo dakin rike da goran ruwa ta ajiye masa kan bedside drawer, ya dinga kallonta, can dai yace "Ke kika dauko da kanki?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ehh, na sa ta wanke kwanukan da aka 6ata a kitchen din" Bai ce komai ba, ta dau magungunansa ta shiga buda masa yace "Aunty...." Ta dakatar da shi tace "Ehh ka hadiyesu yanxu" Bai kuma ce mata komai ba, ta mika masa tulin drugs din, ya sa hannu ya amsa, ta dau goran ruwan ta bude shi ma ta mika masa ya amsa ya hadiye maganin, kallon bowl din hannunsa tayi ganin ba wani shan pepper soup din yake ba tace "Bani in tafi da shi gun wanke wanke, dama nasan baxa ka sha ba ai" Ya girgixa kai da sauri yace "Aa gashi nan ina sha" Tace "To Allah ya sa" Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita. Ahmad ne ya shigo dakin yana dubansa yace "How are you feeling now?" Abuturrab yace "I'm good" Ahmad ya karasa dakin yace "Allah ya kara lafiya" Ba tare da ya kallesa ba yace "Ameen" Ahmad yace "Bari in je masallaci in dawo" Daga haka ya fita. Bayan fitarsa da few minutes Abuturrab ya cire drip din hannunsa ya mike ya dau bowl din pepper soup da Aunty ta kawo masa ya bude kofa ya fita, sau daya ya saci kallon mutanen dake xaune parlor ya wuce kitchen, muryar Aunty yaji tace "Ina kuma xa ka" Ya ki juyowa balle ya tsaya, ta mike ta bi bayansa Umma ta bi ta da wani irin kallo, yana shiga kitchen din ya rufe kofar, Jiddah dake tsaye tana wanke wanke ta juyo tana kallonsa, sae ga Aunty ta shigo, amshe bowl din tayi tace "To sae ka wani fito? ko a waya baxa ka kirani ba in shigo in dauka" kallonta kawai yake, ta ajiye bowl din a gefen Jiddah tace "Mu je" Bai ce komai ba ya juya ya nufi kofa Jiddah ta bi su da kallo, sae da ya fita sannan Aunty ta fita ita ma ta kulle kofar... Umma na kallon Abuturrab tace "Do u need anything" ya kalli direction din parlon ganin Ummi na parlon ita ma, ya karasa can, Aunty tace "Wai kawai mutum ya fige drip da aka saka masa yayi ta yawo cikin gida, ta ya xa a gane treatment din da ake" Abuturrab na karasowa parlon ya xauna yana kallon Ummi a hankali yace "Ina yini Ummi" Ummi tace "Lafiya qlau" Bai kuma cewa komai ba kamar yanda ita ma tayi shiru, Aunty tace "Don Allah ka taso mu tafi ka maida ruwan nan da ka cire" Umma ta mike tace "Wai ke Hafsah wannan shisshigin da neman wajen xama da kike duk na menene ban gane ba? Ina ruwanki da wani drip da aka sa masa, ko ke kika sa masa?" Aunty ta bude baki ta rike ha6a tace "Shisshigi kuma Hajiya Ramlah? Ban gane Shisshigi ba" Umma tace "Sai ki je ki xauna kiyi naxari ki gane da kyau, duk kin bi kinyi kane kane a kan abinda bai shafeki ba a gidan nan, ke kin isa ki hanasa xuwa ya gaida mahaifiyarsa, wacece ke...." Katseta Aunty tayi tace "Aa kinga ni baxan biye maki ba Ramlah dama kina da wani kuduri can da ban sani ba a kaina dake cikin ranki, banda haka ina ruwanki da issue din gidan nan, ita mahaifiyar tasa ai ta san da cewa ya dawo bashi da lafiya amma ko bin ta kansa ta yi, Aa gaskiya ni ba ruwana baxa ayi tashin hankali da ni ba" Hajja ce ta leko daga dakinta tace "Me ke faruwa ne nake jin hayaniya ga dai mara lafiya kwance shememe a gida?" Aunty ta kalli Hajja tace "Kawai dai daga Aliyu ba shi da lafiya ina tsaye kansa sai Hajiya Ramlah ta xo tana gatsa min magana, da yau ace bani da 'ya yan nan da nayi kwanan takaici a gidan nan..." Hajja ta fito tayi kasa da murya tace "Atoh ae da gaskiyarta Hafsah, kin bi kinyi bake bake kan d'an mutane kamar ke kika haifosa duniya, duk shekaruna a Masar ban ta6a ganin haka ba wllh, don cewa ma xa suyi kin masa wani mugun abun ne, su basa haka abinda ya shafesu kawai suke, da ran Hauwa fa ba mutuwa tayi ba Hafsah, to ina ruwanki da d'an mutane" Aunty tayi wani murmushi tace "Toh ai shkkn, su ma sai su ja sa jiki kamar yanda nake masa su ga ko baxai yi masu biyayyan da yake min ba, ai ko dabba ma yasan me kyautata masa" Bata jira cewarsu ba ta bar wajen, Hajja tace "Kaji mayya, wani jikin xa mu ja sa bayan mu dai bamu san abinda kika masa ba har yau, yin abubuwansa kawai yake irin na en benue fah, da a masar ne idan hukuma basu garkameki ba shegiya nake, don ai ba a san abinda kika masa ba yake makale da ke" Shi dai Abuturrab kansa na kasa, Umma tace "Xan ga yau ko ita ta haifesa, bari Ahmad ya shigo su tafi can gida ya ci gaba da treatment dinsa idan ta isa ta wanke kafa taje gidana taga tsiya" Abuturrab ya daga kai ya kalli Umma, Hajja tace "Shikenan bakinmu alekum, ni ma sai in tafi da kayana kala hudu duk mu tafi can idan ta isa ta bi mu, wllh sai na nuna mata ni yar banxa ce" su Maimoon dai sai dariya suke kasa kasa, Ita dai Ummi girgixa kafa kawai take, Hajja tace "Abinda duk mun san kan iskanci mu da muka xauna a Masar..." tana fadin haka ta shiga daki ta hau hada kayanta, Ahmad na shigowa kuma Umma ta sanar masa can gidan xa su tafi tare da Abuturrab, sosai Ahmad yayi mamakib musun da Abuturrab bai yi ba, shi da yafi kowa sanin halinsa tafiya ayi masa treatment a can gidan isn't something easy amma sai gashi yaga bai ce komai ba, Hajja dai tuni ta hada kayanta ta fito da yar jaka tace "Wannan dai sai dai muyi mota biyu idan ana son mu tafi cikin walwala" Ahmad yace "Har ke xa aje Hajja" Hajja ta kallesa kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "Dadina da Masar wllh Yaro bai isa ya raina babba ba, wani ta6aran ai sai a Najeriya, wai ku ji fa wata tambaya da Ahmad ko wa yake ke min, to ina ruwanka fisabilillahi, gidanka ko gidan Hajiya Ramlah, tun fa da mahaifinku ya rasu ita ke ta fadi tashi na ganin shegun danginsa basu kwace katon gidan nan da ku ke ciki ba, mace me kamar maxa kenan fa Ramlah, duk sai da ta bi ta kwatar ma kanta yanci shi yasa ban ga laifin kibar da ta narka ba wllh, gidajensa biyu da motoci da ya bari duk bata amince an cuceta ba, kun ga inda ta fi Hauwa kenan, tunda ita gashi ma mijin ba mutuwa yayi ba amma er benue ta kwace gida da 'ya ya tana xaune sandandan, ba a san gawar fari ba amma yau ace Usman rai yayi hali ko tsinke da kyar Hauwa ta tsira da shi a gidan nan, balle dama tsawon rai garesa idan Allah ya amince, toh kuma yaro sai ka wani ce da ni xa aje sai kace xanje gidanka, shi sa tunda ku ka yi aurenku da Ramlah sau biyar naje gidan don kada in ja ma kaina raini" Tana kai wa nan ta kalli Umma tace "Wani motar xa mu shiga Ramlah" Umma ta mike tace "Ku je a na Ahmad, ni sai in ja motar Yaya tunda driver baya nan" Hajja tace "Aa gwara in shiga naki mu tafi a nutse, su kuma yaran su shiga motar Ahmad din" tana kai wa nan ta fita gun mota, Ahmad ya bi bayanta yana murmushi don xuwa ya bude mata motar sannan ya dawo duba Ramlah, Umma ta mike tana kallon Ummi tace "Xa mu tafi can gidan yaya" Ummi tace "Toh Allah ya sawwake" Umma tace "Ramlah fa?" Ummi tace "Tana daki tana bacci" Umma tace "Toh bari dai in dubata" daga haka ta wuce bangaren Ummi, Abuturrab ya mike ba tare da ya yarda ya kalleta ba yayi hanyar bangaren stepmom dinsa, da gefen ido Ummi ta bi sa da kallo. Jiddah ta fito kitchen bayan ta gama wanke tulin kwanukan da Aunty ta ajiye mata, Ummi na kallonta tace "Sannu da aiki" Jiddah tayi murmushi ta karaso parlon tace "Umma fa" Ummi tace "Ta shiga daki yanxu" Jiddah bata ce komai ba ta xauna kasa, Ummi tace "Xauna saman kujera mana" Murmushi kawai tayi ta ki tashi, bayan some minutes Umma ta fito daga bangaren Ummi, tana kallon Jiddah tace "Ki je ku gaisa da Ramlah tana tambayarki" Tace "Toh" sannan ta mike ta wuce part din Ummi, Ramlah na xaune saman kujera tayi murmushi ganin Jiddah tace "Sannu da xuwa" Jiddah ta mayar mata murmushin tace "Ya jikin?" Ramlah tace "Da sauki, ya su Maman Abdallah" Jiddah tace "Suna gida" Ramlah tace "Toh ki gaida min su" Jiddah tace "Xa su ji, to sae anjima" daga haka ta fita parlon. Umma ce ke magana da Ummi kasa kasa tana cewa "Allah bana jin dadin hakan yaya, da wnn shirun da kike kina fita harkansa gwara ae ki ci masa mutunci a fili har ita ta ji, gani take tsoronta fa ake, kuma tana lura da zamantakewarku da shi, shi yasa take samun daman yin duk abinda take yi, Sannan ina gaya maki abinda Aliyu yake Allah ba banxa ba" Ummi tace "Bari kiji, jira yake dama ki gama surutanki ki bar wajen ya tashi ya bi bayanta, kice wai bai san abinda yake ba, wllh tsabagen rainin wayo da walakanci ke damunsa, ba dai Hafsah ba gashi ga ta, sae ynxu abun nasu ke wuce misali, kinsan har kudi ya bata wai ta siya masa fili biyu for two months now, amma sae last week muna wata maganar ta gaya min, ni dai bance komai ba" Umma dai ta saki baki tana kallonta, can tace "Allah mai iko ni Ramlah" Umma tayi wani murmushi tace "Mu je dai xuwa kawai" Abuturrab na dakin Aunty tace "Toh kai baka da bakin budewa kace masu gidan ubanka kake son xama har Allah ya yaye maka ka koma bakin aikin ka?" Ya shafa kansa yace "Aunty ae xuwa gobe i will be very okay in sha Allah, da safe xan dawo gida" Aunty ta ja tsaki tace "Aikin banxa kawai wani ke tashi fadi a kanka banda ni, ita ta wani xo har gida nemana da fada, sai kace idan wani abun ya sameka ta ta6a tsayawa a kanka idan ba kinibibi da ya kawota ynxu ba" Yyi kasa da murya yace "Kiyi hakuri Aunty" tsaki ta kuma ja tace "Dai dai nake da ita wllh wllh, kuma xan nuna mata na fi ta iko da kai tunda auren ubanka nake kuma matsayin uwa nake a gareka" Ya shafa kansa ganin ba shiru xata yi ba, yace "Sai na dawo da safen Aunty" tace "Toh transfer din da kace xaka yi fa, gwara fa ayi ayi a hada abun nan, nan da nan xaka ga har lkcn yayi" Yace "Nawa kika ce?" Tace "Ko akwati ynxu ai yayi kusan dubu dari hudu da wani abu Aliyu" Abuturrab dake ta kallonta yace "Akwatin guda nawa?" Tace "Aa seti biyu xa ayi ai" Yace "Dubu dari hudu da wani abu?" Tace "Atoh don bance maka dubu dari biyar ba, ni na ma san sai na cika wllh, ai ba wai akwatin yaku bayi xa mu siya a xuba masu kaya a ciki ba" A hankali yace "Toh shkkn, idan na isa can gidan xan saka maki kudin ai ina da account dinki" Aunty tace "Toh shkkn, amma gobe dai kamar yanda ka fada ka dawo da safe" Yace "In sha Allah" daga haka yayi mata sai da safe ya fita... Parlor ya tadda su Umma da Ummi har sannan suna magana, Umma ta mike ganin ya fito tace "Yaya bari inje kar Hajja ta shigo yanxu tace ba haka ake a Masar ba" Ummi tayi dariya tace "Lallai kam, toh sai da safe" Umma tace "Allah ya tashe mu lfya" daga haka ta nufi kofa, Abuturrab ya karaso gun Ummi yace "Sai da safe Ummi" Tace "Allah ya kai mu" Kofa ya nufa ya fita parlon. Hajja da Jiddah suka shiga motar Ummi da Umma ke driving suka bar gidan, sun riga su Ahmad isa gida, Jiddah na kawo ma Hajja abinci Abuturrab ya shiga parlon, Ko kallon Hajja Abuturrab bai yi ba ya wuce dakin Ahmad, Hajja ta bi sa da kallo sannan ta ta6e baki tana kallon Umma tace "Idan kin lura komai nasa yanxu irin na Kishiyar uwar yake, wllh abun na damuna amma ni nasan me xanyi..." Umma dai bata ce komai ba, su Maimoon da Safiyya suka shigo parlon sannan Ahmad. Karfe sha daya saura Umma ta shiga dakin Ahmad, Ahmad na xaune yana danna laptop dinsa Abuturrab kuma yayi bacci, Umma tace "Toh drip din fa? Naga baka maida masa ba" Ahmad yace "Yace he is feeling much better, xan jira in ga har xuwa gobe" Umma tace "Toh Allah ya basa lafiya" Ya amsa da Ameen, sannan Umma ta fita dakin. Washegari da safe su Ramlah da Safiyya suka shirya suka tafi makaranta, Ahmad kuma ya tafi can gidansu  Abuturrab duba Ramlah, Umma da Hajja na can daki, Jiddah na taya Huraira goge goge kafin malamarta ta karaso don karfe tara bai yi ba, Kamar ance ta daga kai taga Abuturrab ya fito parlon, Dauke kai tayi bayan sun hada ido tana ci gaba da goge gogenta tace "Ina kwana" Ya bi parlon da kallo bai ce komai ba, bata damu da hakan ba tace "Ya jiki?" Yace "Ki kawo min shayi yanxu" Yana fadin haka ya juya ya koma dakin Ahmad, ta bi sa da kallo sannan ta wuce kitchen, ta dauraye hannunta ta dau mug ta xuba ruwan flask a ciki ta yi making masa shayin, ta dauka ta fita kitchen din, ta fi minti daya tsaye kofar dakin Ahmad rike da cup din shayin, tana juyawa taga Ahmad yana tahowa, ya karaso kusa da ita yana murmushi yace "Shayi xaki kai masa..." Ta mika masa tace "Aa ce min yyi in kawo masa" Amsa Ahmad yyi yace "Malamarki ta xo tana balcony" Tace "Toh" sannan ta juya ta bar bakin kofar ta wuce dakinsu ta dau Hijab dinta ta saka ta dau takardunta ta fita, tunda Ahmad ya shigo Abuturrab ke kallonsa da cup din shayin, Ahmad ya ajiye masa shayin yace "Ya jikin?" Abuturrab yace "Shayin waye wannan ka kawo?" Ahmad yace "Jiddah ta bada a kawo maka" Abuturrab yace "Toh ni na riga na sha sai dai ka shanye" Tun da gari ya waye Aunty ke ta kiran Abuturrab, ta kirasa ya fi sau biyar daga karshe kawai ya dau account number dinta ya mata transfer din kudin da tace, ba a dau lkci ba ta turo masa message tace "Yauwa sun shigo, xan fita kasuwan yanxu" Ya dinga kallon message din kafin ya ajiye wayar, wajen karfe goma ya fita ya hado wani shayin da kansa sannan ya dawo ya sha, ya sha magungunan sa ya koma bacci.... Jiddah ta shigo parlor karfe biyu saura rike da takardunta, babu kowa a parlon, ta karasa dakin da Hajja take ta bude a hankali taga bacci take, dakin Umma ta wuce ita ma taga baccin take, sannan ta kai takardunta daki ta ajiye ta fito ta shiga kitchen, plates da taga anyi amfani da ta fara wankewa, ta gama kenan aka bude kofar kitchen din....


*I really appreciate the birthday wishes everyone, Allah ya bar xumunci, ku ma free Readers naga wishes dinku and i appreciate wholly but i am shock, don haka domin sauke maku bashi a kai xan maku bonanzan Jiddatul Khair yau, daga yau xuwa gobe da safe Jiddatul Khair will be 300 naira only* ☺️ To gashi dai na maku sauki sosai sosai sbda kauna🥰



3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you

 






Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems


Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada


Instagram -fareeskinglow_89

TikTok-fareeskinglow

Facebook page-fareeskinglow 

WhatsApp -08031898240


No comments