Breaking News

IYAYENMU 45-46

 


🅿️4️⃣5️⃣➡️4️⃣6️⃣






Sai kuma tayi shiru tana kallon iyayensu ta mi'e zata fita munir ya furta "ki saurari komai kafin kiyi komai" juyawa tayi tana kallonsa ya mata alamar ta koma ta zauna domin ya lura kan Soyayyar Amaan rasa hankalinta take 





Hawaye dai take yi kanta na asa Nabil ya fara magana...






Ranar da zamu baro Abijan Amaan yazo ya sameni cewa ya janye sakin da yayiwa Umaima wato ya mayar da ita matsayin matarsa hakan ya bala'in 'dagamun hankali amma nayi tunanin zan iya samun mafita da dukda a lokacin ni da kaina nasan Umaima ta kamu da soyayyarsa domin tuni na gane hakan amma nayi tunani idan har nabari tagane nasan haka to kamar na bata damar cibaga da sonsa ne hakan yasa nari'a nuna mata bansan komai ba bayan har saduwar da suke nima nagane a lokacin saidai na jure domin biyan tawa bu'atar 





Ko da mu ka iso ma ya kirani bansan yaya ba ya samu layina na Gida sosai mu kayi rigima Inda ya gayamin cewa zaizo kuma duk abinda zai faru zai faru domin kuwa sai ya anshi matarsa hakan yasa na kira wani a abijan a ranar na sanar masa komai yace zai taimakamin wajen 'daukar mataki kan Amaan hakan kuwa a kayi domin ya kirani ya sanar da ni yasa an kwancewa Amaan burkin mota inda ya samu munnunan hatsari karaya da kuma bugun ashi 





Hawaye Umaima keyi tana kallon Nabil da taji ta fara tsana 




Yaci gaba to da wannan damar na samu kwanciyar hankali ina jiran Umaima ta cika Idda a yadda nasan ta sani domin nasan muddin na fa'da mata Amaan ya mayar da aurensu zan rasata 




To ana jibi zan wuce Mubi a mayar mana da aure à ka turomin da msg ba wasu bane kuma illa Mahfuz 'dan uwan Umaima 




Zaro idanu tayi tana kallon Nabil yayi shiru yana kama goshinsa 





Munir ya furta "Yau babu abin 'boyewa dole ka fito da komai 



'dagowa yayi idanunsa sun 'dan canza ya fara magana..




Dama tun bayan wata biyar da aurenmu da Umaima IYAYENMU su ka bani labarin tarin dukiyar gadonta wanda ita kanta bata ta'ba sanin tanada shi ba 




Cikin rashin fahimta take kallonsa, haka ma sauran iyayen nasu 



Yaci gaba 




To lokacin da Nake yawan kaiwa daddy ararta ya bani labarin basuso ta ara auren bare sabida yadda suka kasa jure lalurarta hakan yana nufin bazasu ri'e mata amanar dukiyarta ba nan daddy ya bani labarin dukiyarta inda ya jaddadamin ma cewa 60%100 na dukiyarsa ta Umaima ce labarin da ya matu'ar 'dagamin hankali har nima na fara ji a lokacin cewa dole na jure rayuwa da ita ko domin dukiyar





Kama kanta tayi tana hawayen ba'in ciki wai don dukiyartA 




Yaci gaba to tun lokacin takun saqa ya shiga tsakanina da Mahfuz wanda na tabbata bazai ta'ba bari kusan labarin wannan dukiya ba hakan yasa nima na mayar da hankali wajen ganin na rufe bakinsa inda mu ka shiga yiwa juna takun saqa har zuwa ranar da abin zai faru 




Saidai a gefe matsalolin suka fara yimin yawa domin itama mummy a gefe tanata bin malamai kan kawo arshen aurenmu batare da tasan mun riga mun rabu ba hakan yasa ban sanar mata maganar dukiyar ba ganin har lokacin duk tsammaninku banki ce ke bin daddy kudi in tagama cire kudinta sai a raba gado 





A na gobe zanje Mubi Amaan ya kirawoni cewa kada nayi tafiya ko'ina a lokacin yaji sau'i amma ko fita bai fara yi ba domin har abijan naje na kuma tabbatar da hakan  



Ban saurareshi ba na ma kashe wayar 




A ranar da zanje mubi ni da kaina na kira wasu escorts aiki na nufi Mubi 




Lokacin da mu ka tsaya dajin ni nasan ana binmu amma ban tsorata ba domin zuwa lokacin na shiryawa komai naganin naci gaba da mallakar Umaima da kuma dukiyarta sabida har lokacin ko mummy ban sanarwa ba 




Saidai a she shima ya  Amaan yasa an gano inada wata manufa kuma manufar zata jawowa Umaima matsala ya turawa Umaima  escorts suna kula da shige da ficenta a mubi shima ya shiga binciken abinda ke faruwa 




Ana haka ashe mutane da dama ke neman mu daga ni har ita Umaima 





Shiru yayi yana kallon Munir ya furta *Mama* kallonsa Munir keyi babu alamar mamaki yasan a rina 




Su kuwa iyayen duk mamaki ya cika su yaci gaba 




Mama itama ashe ranar rasuwar su daddy da zasu 'daurin aure ya sun shirya zasu mayar da aurensu bayan an gama na Madina kuma daddy ya fa'dawa mama akwai sirri da ya keson sanar mata kan Umaima da dukiyar da duk mu ke tsammanin tasa ce







Hakan yasa bayan hatsarin mama ta shiga bibiyar sirrin har zuwa lokacin da ta fara zargina inda kuma ta yanke hukuncin a sace Umaima ta bada shara'din saina fayyace mata sirrin a matsayin fansar Umaima 





Ajiyar zuciya yayi ya share gumi ya ci and gaba sannan itama budurwar Amaan ta turo a sace Umaima domin ta bata wahala ta ja mata kunne ta rabu da Amaan 




A gefe Nina da Mummy sunsa a sato Umaima domin ta haka zasusan komai da ke faruwa a rayuwarmu a lokacin 




Saidai duk babu wanda yayi nasara cikinsu domin escorts in da nima nasasu aiki saidai wacce ta shammace mu wato *Maribell*




Duk kallonsa suke yaci gaba 




Maribell ni nayi kuskuren bata labarin tarin dukiyar da Umaima ta gada na bata labarin Amaan yanada arziki sosai haka kuma yanada tarin dukiya da babansa ya bashi kafin ya rasu don haka bai dace da Umaima ba sabida dukiyarta bata komai a kan tasa ba amma ni arziki ne mai yawa a gurina da zan iya kafa rayuwata har jikoki da shi domin muma daddy da ku'din ya rainemu" inda ita kuma tayi anfani da wannan damar wajen shirya makarkashiyar sace Umaima a kan tabani shara'din saidai mu raba dukiyar kafin ta sake ta 




Inda a lokacin shima Amaan mutanensa sun turo samari 'yen makaranta gurin domin tsiratar da Umaima 



Kwata2 cikin mutanen da nake zargi a lokacin babu Maribell hakan yasa sai da mu ka fara kokawa nagene macece kuma baturiya nafara o'arin cire mata mask domin duk tsammanina Khloe ce har ta caccakamin wuka ban gane wacece ba amma nasan macece kuma wanda khloe ma ta turo yana can gefe yana 'daukar hoto inda ya hanfo igiyar brasia inta ta baya 





Bayan kun kaini asibiti Nina ce tasa a yimin allurar dogon suma domin tuni an gama gayramin ciwuwwukana kuma zan warke da yardar Allah 




Muna magana da ku ne ma likitan yamin allurar batare da kun sani ba a lokacin ne nayi wannan suman a yace muku na mutu manufarsu shine a zargi Amaan domin lokacin Nina ta gano komai tsakanin Amaan da Umaima 



Inda da kanta ta ri'a shiga gidansa tana saka duk wani abu da Umaima zata gani ta zargeshi 




Wani irin zazzafan hawaye Umaima keyi tana kallon Nabil 



Bayan kunje kun binneni ne da mintuna ashirin wanda suka tura ita da Mummy ya haqoni babu 'bata lokaci ya wuce da ni india à can nagama jinya na dawo nan domin tuni na basu labarin dukiyar inda mu ka sayi wannan gidan a kan zamu dawonan in mu ka tabbatar Umaima ta koma hannun Amaan ta samu kwanciyar hankali domin munsan ita soyayyarsa ta dameta ba dukiya ba so sai bayan shekaru sai mu koma gida muyi muku arya  muce dama bamuso wanda yaso kasheni ya san ina raye kuma mu baku sauran 40%100 na dukiyar daddy muce banki ta biya domin komai yana hannuna IYAYENMU sun dan'amin amana ne bayan da sukaga nacika shekara ina jure Umaima da tsammanin zan ri'e mata amanar dumiyarta ma 




Wani irin kama kai Modibbo yayi yana mamakin wai Umaima da Nabil IYAYENSU cikinsu 'daya amma ji abinda suka mata







Shiru yayi yana sharar 'walla ya furta kuma amaan ya dawo Nigeria ne don kawai yayi bincike kan wanda ya kasheni inda bakinsu ma 'daya da D.P.O duk kune baku sani ba kuma tuni suka fara zargin Nina da Mummy hakan yasa suka saka Camera a gida da mu bamu gano ba sai jiya 



Sannan babban tashin hankalin shine yau kwana biyar kenan Takardun Dukiyar gaba ki 'daya mun neme su mun rasa sannan mun rasa a nan Germany waye zai 'dauka 






Ya kalli Umaima yana furta wlh tallahi ban 'boyesu ba sacewa a kayi domin yanzu haka ko su mummy basu sani ba kuma a kansu zasu iso suma tun jiya ma







Kallon juna iyayen keyi cikin tsananin mamakin wannan irin badakala





Jirginsu na sauka suka hau taxi Lubna tace wai mummy sai nex wk in Auta zai iskemu.? Eh mummy tace nace Shukhra ta kawo shi domin dama itama nan zasuzo honeymoon 



Nina tace mummy pls ki kirata kice tazo mana da sauran dambun naman na gunta





Ok mummy tace suka arasa gidan 



Da ke turai ne dama da takalmi a ke shiga gida hakan yasa basu komai ba suka bu'de ofa suka kutsa kai 




Wani irin afewa duk su kayi bakin ofar suna kallon Iyayensu da Munir 




Yawu Nina ta ha'diya..✍🏻


No comments