Breaking News

IYAYENMU 39-40

 



🅿️3️⃣9️⃣➡️4️⃣0️⃣








Saidai suma basu bari ko iyalansu sun sani ba musamman shi mahaifinta da a lokacin us auri wata 'yer masu ku'di 



Munata neman mafita ni da mahaifiyata musamman da mu ka gano ba kowa yasan da dukiyar ba bayan na dawo service mahaifiyata tace naje na nemi auren Umaima Saidai ni à lokacin ma wlh bawai don dukiyar na ke naje nemanta ba har  zuciyata da gaske na ke sonta




Hararsa Amaan yayi ya ha'diyi yawu yaci gaba..




Ko da nazo kawunta ya'i ememe wai sam bai yarda da ni de ba nayi2 ya hanani inda ya bawa wani 'dan abokinsa attajiri  *Mahmud suka rabu na ara dawowaw ya hanani ta auri Ahsaan nan ma suka rabu ban dawo ba sabida a lokacin mamata tace kada na dawo ta riga ta 'dauki matakin da dole za'à nemeni na aureta ko da na tanbayeta tace tayi anfani da matsalar infection da ya cinye marar umaima ta tura mata aljani wanda shima ya ke zuzuta mata lalurar in mazajenta su sadu da ita hakan ce tasa sai tayita ganin in tabari suka sadu da ita Mutuwa za tayi 




Lunshe idanu Amaan yayi domin wannan 'bangaren na labarin ya masa da'di 



Yaci gaba 




Toh ashe bokan yacewa mamana duk sadda ta rabu da ciwon Infection in asirin zai karye domin da ciwon akayi garkuwar aikin 





Muna haka mu kaji tafiyarsu Waje ita da Nabil wanda mu kayi mamaki bayn muna tsammanin zuwa lokacin sun rabu 



A na haka ta koma gun bokan yace mata aiki ya are tuntuni domin a lokacin Umaima na auren wani kuma rabuwarsu za tayi wahala 



Ajiyar zuciya Amaan yayi kawai yaci gaba 



Toh tun lokacin mu ka sanja manufa akan na hakura da ita kawai mu samu dukiyar a maimakon muyi biyu babu inda mu ka shiga neman mafita





Cikin neman mafita Nina tazo ta sameni kan itama tana neman mafita a kan raba auren Umaima da Nabil wanda a lokacin basusan sun rabu ba inda nima ban bata labarin dukiyar gadon Umaima ba 






Inda cikin neman mafitan ne muka samu labarin kuna tare saidai mu kayi mamakin yadda Nabil ya kasa ganewa saidai ni nagano auren Umaima kayi da yarjejeniya tsakanin ka da Nabil shi a kan son da yake mata da kuma sanin da yayi na cewa tarin dukiyar da suke tsammanin ta babamsu ce ashe ta Umaima ce 




Toh ban fa'dawa Nina ba domin nasan idan tasani tabbas zasu sanja manufarsu kan Iyayyar da suke wa Umaima 




Da maganar aurenku na fara Blackmailing Nabil cewa ko ya saki dukiyar ko kuma nima na tona masa asiri sannan in sanarwa Umaima cewa dukiyarta yasa bayason aurensu ya are 




Yayi ajiyar zuciya sai yayimin alkawarin IA bayan ya mayar da aurensu da Umaima zaizo muyi magana ni da shi da kuma mahaifiyata da haka mu ka samu matsaya da shi a rubuce saidai ashe yaudararnu yayi domin sai yasa muma a na binmu wanda bamu kai ga gane manufarsa ta sawa a ri'a binmu ba mu kaji rasuwarsa inda a ranar da zai rasu yamin msg wai ya maidawa Umaima dukiyarta mu je gurinta mu ansa 





Ajiyar Zuciya Amaan yayi ya kafin ya furta "Baka shirya zayyane gaskiya ba ko?  Ifta idanu yashiga yi yana furta wlh tallahi ni iya abinda na sani kenan 




Ok amaan yace yana mi'ewa ya mayar da soon glass insa ya fito palourn gardawan suka mayar da Mahfuz inda su ka fito dashi







Yana fitowa ya shiga motarsa ya tayar ya nufi Gwarumfa estate







Hamma tayi ta fara bu'de idanunta a hankali har ta ware su tas ta duba gefenta bayanan cikin nutsuwa ta ke zame mayafin da ya rufe ta shi kallon jikinta tayi tik babu komai kama kanta tayi ka'dan sai yanzu taji tsamin da jikinta yayi ka'dan a hankali ta mi'e ta nufi bathroom ruwa ta ha'da tashiga ta lumshe idanunta kusan 28mnts tayi kafin ta fito ruwan ta sake ha'da wani haka tayi sau uku kafin tayi wanka tayi na tsarki ta fito ganin azhar tayi ta yi sallah wata jallabiyarsa ta saka ta sauka kitchen motsi take ji ta waje ta le'a mamaki ne ya kamata ganin gardawa har hu'du da ba'a'en kaya suna shawagi a harabar gidan komawa tayi palour ta 'dauki wayarta ta jefa kira 




Munir na tu'I ya furta "karki damu ina hanyar shigowa yanzu "ok" tace ta tsinke Kiran ta koma kitchen ta shiga girki jolof in macaroni tayi da kaza ruwa2 ta zuba ta 'dauki maktina ta  fito a palourn tana zama Munir na shigowa kunya taji ta kalli rigar Amaan da ke jikinta ta sunkwi da kai 





Murmushi yayi ya furta "ya kike"? Lafiya ta ansa a ta'aice ya fara magana 




Sorry but abin nan shirin da aka masa yafi yadda na ke tunani musamman ta 'bamgaren mijinki kwata2 ya kulle duk wata hanya da zaka iya fahimtar wani abu domin but yanzu ki shirya muje gida meeting da IYAYENMU wanda bakida mafita sannan karki manta duk abinda mu kayi shi a zaki jaddada gaban kowa kin gane? 




Girgiza kai tayi yace kici abincin ki shirya muje 




Wani tsohon building ya shiga yayi parking motarsa ya fito wasu mutane arfafa biyu na tsaye suna jiransa ya arasa suka gaisa 'dayan ya mi'a masa envelope ya ansa ya bu'de ya gama karantawa ya furta *Germany*? 



Eh mutumin yace "ok" ku arasa ku zomin da ita yau 'din nan toh yalla'bai suka furta ya juya ya wuce 





Tana gamawa ta jefa hijabi ta sauko kallonta yayi ya furta har kin shirya kenan.? Eh yaya banida kaya a nan "ok yace ya mi'e suka nufi gidan 





Palourn na cike ma'il da kowa na nan ura mata idanu duk su kayi ganin rigar jikinta ba sai an fa'da maka ta namiji bace 




Yapendo ce ta furta "Ki araso ya jikin na ki"? Cikin dakiya ta furta da sau'I can kusa da Baffa modibbo ta zauna a ka fara magana baffa Rulwanu ya furta 





Umaima wannan auren zaki barshi koda ba'a gama bincike an tabbatar da shi yayi kisan ba Amma ke da kanki kika samo hujjoji a kansa don haka babu maganar aure ke d... Ta saki kuka tana furta baffa ku gafarceni amma bazan iya rabuwa da shi b... Salati duk suka saka yayinda Mummy da su Nina duk farin ciki su ke ciki 




Yapendo ce ta furta "haba mamanmu Rabi'atu kimsan ciki babu abinda baisa mace ki nutsu kigane ba wasu bane a nan illa mu Iyayenku sannan yanada daga cikin adalci ko da bashi yayi kisan ba ta ya taka rawa wajen rugujewar aurenki da 'dan uwanki don haka mutuncinmu da martabarmu zaki duba ki hakura da shi 




Hawayen ta keyi ta sake maimaita wlh goggo bazan iyaba.. 




Cike da muguwar mamaki suke kallonta suna mamakinta..✍🏻💖IYAYENMU💖







No comments