Breaking News

IYAYENMU 37--38

 🅿️3️⃣7️⃣➡️3️⃣8️⃣





Yana karya kwana zai shiga layin wata atuwar jip tasha gabansa kasancewar layin G.R.A ne da sai kayi sati kana shiga baka ga mutum a waje ba koda da rana kuwa





Kallon motar yayi hankali a tashe ya fara o'arin komawa da baya saidai ina tuni sun bu'de motar mutum biyu suka shiga suka masa umarnin ya tayar da motar can jip in ta tayar shima ya tayar yana bin jip in 






Sanye da ananun kaya red t.shirt da blue jeans da bleu cover shoe sai watch a hannunsa yayi kyaw abin ba magana Amaan akwai kyaw zama ya ara yi gadon ya tallafo kanta zuwa cinyarsa ya ura mata idanu yana kallonta yanajin yadda ko wani numfashinta ke huda ofar kowani gashi na jikinsa yana ara masa tsananin sonta da aunarsa ya kai lips insa kan nata yayi kissing yana shafa kumatunta ya furta "baby I love u" ajiyar zuciya yaga tayi a cikin baccin ya lumshe idanunsa ya ara kissing inta kafin ya maida ta kwance ya fito..





Kallon Munir su Baffa su kayi baffan mubi ya fara magana "amma ta wani dalili za kace muje har Germany don kawai mu raka ka shari'a.? 



Ajiyar zuciya Munir yayi ya furta baffa sabida shari'ar tanada muhimmanci sosai cikin career ina na rayuwa shiasa nake so a ce iyayena duk suna gurin 




Kallon baffa rilwanu midibbo yayi yace ai shikenan yaushe ne tafiyar? Munir ya furta jibi IA kuma har da su yapendo duk nake so muje nagama komai saidai banaso kowa ya sani bayan ku in har zuwa ranar tafiyar 





Toh ai shikenan Allah ya kaimu suka furta "amin munir ya ansa yana musu sallama zai fita" 




Baffa yace amma kafin nan yanda yayan Malbaiwa ya tsara zamuyi taro anjuma kan maganar Umaima domin sam bazai yuwu aurenta da wannan baturen ba don haka anjuma duk kowa ya sauraremu ka tabbaatar tana gurin itama Hajara tace ta 'daukota asibiti tana gidanta ko? "Eh ya furta suka ce to ka sanarwa mummynku da sauran yen uwanka "toh IA ya wuce 





Tas suka gama shirin su saidai Ita Nina a gefe tana wani tunani da bata fa'dawa kowa ba Lubna kuwa har yanzu daure mantawa da Amaan ta keyi bawai don zata iya jure hakan ba 






Cikin asaita ya shiga makeken gidan mai gadin ya bu'de masa yanata mi'a masa gaisuwa ya ansa a ta'aice yaba arasawa wani  falo ya shiga ato ne palourn saidai babu komai ciki sai tiles sannu da zuwa suka shiga yi masa wani ya share masa kujera ya zauna "ya furta ku fito da shi " ok yalla'bai 





Idanunsa a kulle da kyalle haka bakinsa suka fito da shi à ri'e suka dangwarar da shi à asa "kallonsa yayi na mintuna kafin ya musu alamar su cire masa komai suka cire ya saki numfashi da arfi yana ajiyar zuciya ya kalli Amaan 




Babu alamar walwala ya furta "mai kake nema da matata"?  Yawu ya ha'diya bai iya magana ba Amaan ya musu alama da su warming insa ai take suka shiga naushinsa cikin gigicewa  ya furta "yer uwata ce"




Kallonsa Amaan yayi baiyi magana alamar baya wasa da shi" ya share gumi ya fara magana 




'Yer uwata ce IYAYENMU 'daya ma'ana cousin ita ce ta 'bangaren mahaifiyarta 





IYAYENMU sun kasance 'ya'yan sarkin shanu na Banyo wani garin fulani  can arewacin Kamaru  inda yawon kiwo ya kawo su Adamawa anan  ne Mahaifina ya auri matarsa jikar sarkin noma na maibalwa yayinda mahaifiyarta lokacin tana arama bayan da mahaifina yayi auren sai ya koma gida ya 'dauki anwarsa *Hawwa* arama su biyu dama kacal iyayensu suka haifa ya bawa matarsa su ri'e bayan da ta girma sai yaron sarkin Maibalwa ya fara nemanta da aure inda abin ya 'dauki hankalin mutanen garin sunata surutu ganin IYAYENMU ba 'yen asalin garin bane tayaya 'dan sarki zai auri bakuwa saidai cikin ikon Allah haka a kayi auren mai cike da tarihi wanda makota abokanen masarautar maibalwa duk sunzo daga ciki kuwa harda babban abokin ango dan sarkin shanun Yola wato *Muhammad Amin* akayi biki a kai amarya gidanta ranar farko da miji ya tare da amaryarsa farin cikin da a garin a lokacin wata al'adace idan budurwa ta cika budurcinta ango da danginsa zasu yi mata kyawtuttuka daidai da arfinsu "hakan ce ta kasance da itama inda kasancewar su sarakuna masu tarin dukiya surukinta sarki ya bata dawakai ashirin da rakuma biyar da shanu goma sai surukarta ta bata zinare masu yawa da dirhami da azurfa da kaji sai shima angonta ya bata tarin zinare harda 'danyu da kuma garke guda na shanu






Inda ta bawa yayanta duka ya ajiye mata kasamcewar iyayensu a lokacin sun rasu kuma shine kamar uba a gurinta ko da ya tanbayeta me take sonyi da dukiyarta tace kawai yayi ta juya mata zuwa lokacin da zata bu'ata 




Haka a kayi ya shiga juya mata kuwa 





Kwana goma sha uku da aure Allah yayiwa yarima mijinta rasuwa sakamakon ciwon ciki bayan ta fita takaba a ka ara bata gadonta inda dukiyarta ta ara ha'baka saidai tun lokacin mahaifiyata tunaninta ya karkata kan dukiyar 



Ana haka zawarawa suka ara yawa inda mahaifina baya bari kowa yasan yawan dukiyarta gudun kada a samu wanda zai sota domin dukiyar har Allah yasa abokin marigayin mijinta ya fito 'dan sarkin shanun mubi wato Muhammad Amin 





Sarkin shanun mubi shi matansa biyu yaransa goma sha takwas inda kakarsu Umaima itace uwar gida yaranta takwas "baffan suffi, baffa lawandi, baffa Hari, sai Mahaifin umaima sai 'dan wansa mahaifin Nabil sai yadikko sai Goggo Marka..  Innajo yaranta goma, baffa modibbo, baffa Hambari, da yapendo na manta sauran sabida zuri'arsu basu cika alaqa da mutane sai junansu 





Bayan anyi auren Hawwa da wata biyar a ka haifeni bayan ni da shekara shida a ka haifi Umaima inda tunda mahaifiyarta ta haifeta ta daina lafiya ashe cancer ce da ita ta o'olwa shekarar umaima hu'du Allah yayiwa nahaifiyarta rasuwa inda mamata ta nemi a bata danginsu su ka qi a ka maidata gidan yayan mahaifinta a abuja 




Saidai har wannan lokacin hankalin mahaifiyata na kan dukiyar dukda mahaifina baya maganar komai da ita. Kan dukiyar tun sau 'daya da yace mata dukiya ta umaima ce kuma yayiwa mahaifinta magana mahaifinta yace zaiyi tunani har kuma loakcin bai ce masa komai ba 




Ana haka mahaifina us rasu bayansa munata neman waye ya dan'awa dukiyar har mu ka gano mahaifinta a ka dan'awa inda shikuma ya bawa 'dan uwansa ya ri'a juya mata har zuwa girmanta bayan tayi aure ta gama mallakan hankalinta su bata






Wannan shine mafarin duk masifar da ke faruwa yanzu haka...✍🏻💖IYAYENMU💖




No comments