Breaking News

IYAYENMU 31-32

 



3️⃣1️⃣➡️3️⃣2️⃣






Kallonsu baffan mubi yayi ya fara magana





A yanzu banida abinda zance sabida dum dum wa'dan nan abubuwan da suka faru suna bu'atar tunani da nazari kai harma da bincike domin kuwa shi kansa yaron dole sai munyi magana da shi hakkinsa ne a kanmu a matsayinsa mijinta koda kuwa wani mataki zamu 'dauka dole sai bayan munyi dogon nazari da kuma magana da shi da ita kanta sannan kuma duk zamu yi magana da ku yanzu zamu ci gaba da hidimar bikin Shukhra domin bazamu fasa ba sabida wannan dalilin ya kalli 'yen uwansa ko da wanda zai ara wata magana 




Baffa modibbo da su baffa Rulwanu duk sun rasa abin cewa don haka dum suka furta haka ne yaya kariga kada'di komai Allah ya mana jagora duk suka ce amin...!







Bayan tagama kukan tana zaune shiru gashi tafara jin yunwa babu kowa dr yazo ya tafi ta sake fa'dawa tunani 




Wani irin danasani take yi mara iyaka, wani irin jarabawa ne haka.?




Hawaye tafara tana tunano iyayenta shikenan duk mutanen da take so Allah baya barinta da su kukan ta sake farawa sosai har wata nurse ta shigo ta fara rarrashinta ta tanbaye ta ko tasha drugs tace ah ah sabida bata ci komai ba nan nurse in ta samo mata shayi tasha da kyar ma tasha drugs in ta koma ta kwanta shiru tana takure jikinta ga drip ya are 







Kallon Munir mamansa tayi ta furta "kai ina is samo duk wannan labarin.? 




Shiru yayi yana kallon mamansa da haka kawai yaji zuciyarsa na sa'a masa abubuwa a kanta saidai ya basar ya furta 





Haba mama kinfa san no lauya ne bincike abu ne maisauki a guna 



Ajiyar zuciya tayi ta ura masa idanu ta furta amma nasan arya kake da kace kanemi auren Umaima ne domin ka binciketa ina sane ka jima dama kanason aurenta 



.shiru yayi kafin us furta pls mama..





Kallon Nina Lubna tayi cikin tsananin fushi ta furta "kin cuceni koda kinsan wannan ai yasan a ita yazo nem.. mummy ta daka mata tsawa 




Lubna u r very stupid tayaya duk bayanan da a kayi baki fahimta ki gamsu baya sonki kuma kika sani ma ko tare suka shirya hakan don rufe sirrinsu domin ni ban gamsu ba ma wai babu hannunta cikin kisan Nabil 




Kallonta duk su kayi Nina ta furta nima dai mummy haka but in the haka ne ai bazata tona masa asiri ba da kanta 



Shiru mummy tayi kafin ta furta aiki na gaba sai naga angama komai zan yadda 





Haka a kaci gaba da biki gobe 'daurin aure babu wanda yayi tunanin zuwa ganin Umaima sai yapendo ita kuma ayyuka da jama'a suka hanata 






2:47 pm Cikin 'dan baccin da ta fara taji an shigo da sallama a hankali ta juyo yunwa ma take ji 




da 'dan mamaki take kallonta har ta araso ta zauna gefen gado kusa da ita tana kallonta ta furta "ya jiki"? 




Subkwi da kanta tayi ta ansa da sauki.. shiru su duk babu wanda yayi magana cikinsu kafin ta kalli umaima ta furta " inaso kiyimin afuwa ki gafartamin akan abubuwan da suka faru a uruciyarki 'dagowa umaima tayi tana kallonta "mama taci gaba nasan ban ri'eki yadda ya kamata ba amatsayina na uwa kamar yadda bayan rasuwar mamanki daddynku ya kawo ki hannunmu don Allah ki yafe min kinji.? Kwalla tashiga sharewa taci gaba nasan kinsha wahalhalu kan kulawar da bamu baki ba amm.. Umaima ta ri'e hannunta tana kwalla itama ta fara magana 




Mama pls ki daina cewa haka kun ri'eni kamar yerku ban rasa komai ba a rayuwata a hannunku babu abinda bakumin kamar yadda kukewa yaranak.. mama ta katseta ta furta ba gaskiya bane umaima banki ba muna baki komai na duniya amma bamu baki kulawa da uwa ke bawa 'yerta ba musamman loakcin uruciyarta 



Kallonta Umaima keyi bata fahimci inda ta dosa ba ganin haka mama ta kunna mata Voice in da ta na'da na gaba 'daya maganganun Munir 




Kuka tashiga yi tabbas tasha wahala wanda bata ta'ba tunanin zata fita cikinsa ba tana tuna yadda zata kwana ciwon baya da mara sai inta bu'de pant inta taga ruwa mai wari sa'in harda gudaji tsananin kunya da gudun zargi da gori yasa bata ta'ba furtawa kowa ba 





Wani irin tausayi ne ya sake ratsata na Amaan jin voice in ta kowani mahanga ya nuna itace 'daya a gurinsa 




Muryar mama ta jiyo "kin tabbata mijinki ne ya kashe Nabi.?




Kallon mama take tana hawaye tana tuna tabbas mama ta sota saidai a lokacin kishinsu ita da mummy ne ya rufe mata ido bata kulata sosai muryan maman ta ara jiyowa tana maimaita tanbayarta 



.kuka ta saka tana kwantar da kanta cinyar mama ta furta * bashi bane nayi imani bansan maiyasa nakasa gane gaskiyarsa ba tun farko". 'dagota mama tayi ta furta ki kwantar da hankalinki indai bashi yayi ba ni zan taimaka miki mu fitar da gaskiya amma kema inaso kiyimin wani taimako kin amince.?




Girgiza kai tashiga yi





Mama ta fara mata bayanin abinda zata yi tas ta bu'de kula da ta shigo dashi tuwon Alkama miyar kuka ta fara bata tana ci dr yazo yace taji sau'i zasu iya komawa gida ok mama tace ta gyarata suka fito har motar mama ta shigar da ita ta zaga zata tayar umaima ta furta "pls mama inaso ki kaini wani guri can zan kwana gobe sai kizo ki maidani gida..




Kallonta mama tayi ta furta ina..? 




Shiru tayi na jin nauyin abinda zata fa'da kafin ta furta inason duba wasu abubuwa ne a can.. murmushi mama tayi tace ok babu damuwa ta tayar da motar 






Kallonsa Anas yayi yafara magana .. wai kai haka zaka saka idanu kullum kana samun damar da zaka mallaki yarinyarna ka bari ta kubce maka? Murmushi yayi yana kallonsa ya furta yanzu ma bawai na hakura bane domin nasan rabuwa zasuyi da wannan baturen so gara na nuna mata nasan muntuncina hakan ne zai dawomin da ita cikin kwanciyar Hankali IA




Hmmm Anas ya furta yana kallonsa kawai 




Bayan mama ta ajiyeta cikin nutsuwa ta sunkuya ta bu'de asan gate in ta shiga tana kullowa ta fara taku zuwa cikin gidan 



.a palourn ma ta zauna tayi shiru tana tariyo abubuwan da ya faru tsakaninsu a palourn ta fara kuka tayi ta gama ta haura saman nan kam zama tayi asan tiles in ta shiga rusa kuka sosai bayan ta hango wani shirt insa ta ,dauka ta ruumgume jikinta tana kuka sosai tana sha'ar anshin Shirt in 





Anshin taji sosai a kanta wanda bata tuna komai ba illa hancinta da ke koro mata anshinsa ta lumshe idanunta tana sha'ar anshin tana hawaye ta furta * ya Allah ka yafemin ka ku'butarmin da shi, Allah ina sonshi ina son kasancewa da shi koda mai hakan zai jawomin a rayuwa" ta ara sakin kuka saidai anshin take ji sosai cloz da ita cikin nutsuwa ta 'dago kanta 




Ha'diye kukan tayi idanunta ko motsi basu yi tana kallonsa a hankali ta kai hannunta goshinta tana dafawa tsammanin ciwon kai ke damunta shiasa ta ke ganin kamar shi ne 




Kusan 8mnts ara bu'de idanunta ras a kansa sanye da ananun kaya bleu t.shirt da blue jeans sai ba'in cover shoe afarsa da agogo silver Swatch hannunsa ya rame but ya ara kyaw 




a wani irin yanayi ta mi'e da kyar tana son gasgata abinda take gani ta arasa gabansa idanunta ko iftawa bata yi ya shiga shafa cikinsa zuwa irjinsa zuwa fuskarsa ta ura masa idanu tana waye mazu zafi tabbas shine 



Jin kamar zuciyarta zai fashe ta rungumeshi kanta a cikinsa  tana sakin kuka sosai tashiga furta *I love u , I love u x3 




Kwalla shima ya share yana jin wannan ce rana ma fi daraja a rayuwarsa ya 'dagota a jikinsa suna kallon juna ya furta *Baby ina sonki fiye da kaina fiye da rayuwata fiye da dukkan wani mutum ko abu da nake dashi a duniya"




Kuka take masa sosai ta furta "nima haka wlh da gaske tun muna Abijan na ke sonka *Amaan* ina sonka fiye da numfashina wlh ba yaudara b.. ya sunkuya ya kamo lips  inta yashiga wani irin mugun tsotso ta ara rungume cikinsa tana ara tura masa harshenta cikin bakinsa...✍🏻💖IYAYENMU💖





No comments