Breaking News

IYAYENMU 27-28

 



🅿️2️⃣7️⃣➡️2️⃣8️⃣








Tun bayan auren Umaima na farko da take ta samun matsala babu wanda cikinku IYAYENMU ya mayar da Hankali ya binciki ainihin matsalarta saidai a yita bata hakuri a na bawa mijin hakuri ayayinda take ganin babu wanda ya damu da ita yadda ya kamata shima mijin naganin ai ba'à damu da 'daukar mataki kanta ba tunta kullum yazo zaice muku tana masa taurin kai kukuma baku nemi ya fayyace muku wani irin taurin kai take masa ba sai ku bashi hakuri kuce zaku mata fa'da 




A gefe itama in tazo ku mata fa'da kuce miji komai yakeso yi ake ayi hakuri da shi ko ba'à so so hakan yasa bata ta'ba yunkurin sanar muku me ke hadata da shi ba har arshe ya kasa jurewa ya saketa 




A kazo aurenta na biyu kamar baza tayi ba kuka nuna mata aure shine mutuncinta musammn ita da ta riga tafara yi in bata yi ba mutuncinta zaiyi rauni hakan yasa tayi badon ta shirya ba sabida fargabar matsalarta 




Hakan kuwa ta kasance da shima na biyun suka ri'à samun matsala har takan nuna masa  makami domin kare kanta daga abinda taga ya zame mata matsala a rayuwarta 




Shima ya kasa jurewa ya saketa 




Inda Hanif ya zo ganin shi na gida ne kuka tasata gaba tun taba i harta hakura kuma zuwa lokacin babu wanda ya tsaya cak yasan matsalarta kawai kunata zargin auren ne bataso ko inda arshe Innajo tace namijin dare ne ya aureta su daddy suka bazama neman maganin aljanu 




Lokacin da ta rabu a Hanif su Daddy su ka je gun wani malami macuci kamar yadda dayawan malamai suke a wannan zamanin shiasa gara damuwarka ka gayawa Allah ya maka magani 




Malamin ganin IYAYENMU masu arziki ne ya ga inba arya ya musu ba bazai tastsesu ba ya kuwa ce musu tabbas Aljanu ne kuma wai ya jima jikinta sai anyi da gaske so gara ayi mata auren gida yadda ana aikin mijin na taimakawa har ayi nasaran rabata da aljanin 



Da haka su daddy suka amince inda suka fara tunanin tsakanina da Nabil sanin tun tana tashinta na ke burin aurenta saidai a lokacin Nabil ya shirya auren Hawwa jikar Saraki a ka fasa dalilin haka daddy ya yanke hukuncin bashi da kashedin kome zai faru kada ya ta'bajin saki sabida a tsammaninsa malamin gaskiya ya fa'damusu 




Bayan anyi aure the same yaci gaba da faruwa inda duk sadda Nabil yazo kusantarta sun ri'à fa'da da kokawa tayi cizo tayi ya'ushi kai da tafiya tayi nisa ma ko bacci zata kwanta sai tasa wuka gefenta 

Ko plate in tangaran 



Salati su yapendo suka saka suna tafa hannu yaci gaba 




Tunda su kayi aure sau hu'du bai ta'ba kusantarta ba hakan ya fara kaishi bango inda ya nemi hanif ya bugi cikinsa Hanif ya zayyane masa ai shima abinda ya rabasu kenan kuma yanajin kunyar sanarwa IYAYENMU ya ara da cewa dukkansu sauran ma sun fa'da masa wannan matsalar ce silar rabuwarsu da ita saidai duk suka jingina matsalar da aljanin dare wanda duk suna fatan ta warke aljanin ya rabu a ita ma su dawo zawarcinta 





To haka Nabil ya fara kaiwa bango tun yana ha'diyewa har ya kai yaje ya zayyanewa daddy shi kuwa daddy yace ai su sunsani ma domin malam ya fa'damusu shiasa yace ayi mata auren gida sabida babu wanda zai jure hakan sai na gida don haka ka kwantar da hankalinka IA zamu rabata da wannan aljanin




A haka dai Nabil yake hakuri sai bu'ata ta taso masa ba hali in yaga zai shiga damuwa ya nema a waje 





A na haka wk in ne su daddy su kazo tafiya auren Aunty Madinan kano inda su kayi hatsari suka rasu ya share kwalla suma su yapendo suka share yaci gaba 




Wata rana kuwa yagaji da nema ya dawo gida ya nema a gurin ta suka fara rigima sosai ta buga masa kwalbar humra yaji ciwo sosai a take yayi mata saki 'daya 




Bayan ya dawo Chemis ya furta mata ya mayar da ita..




Salati su yadikko keyi sosai suna sauraren Munir yaci gaba 




Bayan haka da kwana biyu ta dawo skull zata shiga wanka Nabil ya dawo ganinta sha'awa ta kamashi ya fara nemanta tana 'i ya tun yana lallashi har yadawo yana nuna mata arfi hakan tafara o'arin kwatar kanta inda ta tureshi ya buge da mirror in gadonta ya yanke a baya hakan yasa Nabil ya fusata ya shiga kamata da arfi tana cizo da yakushi har ta yakisar masa inda ya yanke in ya saki ara yana tashi jikinta cikin zafin rai ya furta mata saki na biyu 





Salati Baffan mubi yayi yana kallon 'yen uwansa Munir yaci gaba 




Bayan haka Nabil ya tafi chemis a kayi treating insa bai koma gida ba ya Wuto nan gida inda mummy ta fahimci babu lafiya saidai bata masa magana ba domin dama tayi ta fama da daddy kan batason auren daddy ya'i sauraronta hakan yasa tasaka idanu sosai kan Nabil da Umaima inda a lokacin cikinku IYAYENMU ita ka'dai ke fahimtar babu wani alheri cikin auren Umaima da Ya Nabil yayi ajiyar zuciya  yaci gaba saidai matakin da ta 'dauka shine sanadiyar inda mu ke a yau 




Duk juyawa su kayi suka kalli mummy da ke hawaye kafin suka dawo kan Munir yaci gaba 




Bayan mummy ta anso maganin da zai raba Umaima da Ya Nabil ta zuba masa a abinci batare da tasan a lokacin ma igiya 'daya ta rage tsakaninsu ba 




Bayan yaci abincin da kwana 9 ya dawo daga aiki Umaima na shafa mai ya kalleta kamar zai hakura ya kasa nufe ta dukda har lokacin ko warkewa bai gama yi ba 


Saidai kash kamar kullum suka shiga rigima ta'i emememe shikuma yakai iyaka ya shiga tirsasata hakan kuwa har ya fara, ita kuma Allah ya bata nasarar buga masa kwalbar turare ta tureshi ya fa'di ya ara bugewa 




Wani irin kallon mamaki su duka suke yiwa Munir sunajin labarin kamar cikin fim yaci gaba 



Tsananin azabar zafi ga zuciyarsa da dama kwana da kwanaki yakejin tana sa'a masa abubuwa dayawa akanta ya sashi furta mata saki na uku 




Tashi yapendo tayi tana salati tana kuka Yadikko ta mayar da ita ta zauna yaci gaba 




Bayan ya fita zuwa chemis ne hankalinsa ya dawo yashiga mummunan tashin hankali kamar yadda itama bayansa ne tashiga mummunan tashin hankali ya wuce office can yake ganin e-mail na course in daya nema ya samu a Cote d'Ivoire inda yaga no in incharge na Kamfanin wacce dama da ita yake komai 



Nan take masa bayanin komai inda yaji wani abu da ya bashi tunanin ya samu mafitar matsalar da yake ciki a lokacin 




Ko da ya iso gida da gudu itama ta araso gurinsa tana rokon yaya zamuyi mu gyara IYAYENMU basu ji ba?



Shima da ke tunaninsa kenan a lokacin kuma bayan haka yana sonta sannan shi kansa lokacin ya yarda da maganar su daddy kan aljanu ke damunta saidai yanata tunanin mafita yadda zai arasa aikin da su Daddy suna ce sun fara kuma bayason sanarwa mummy ko 'yen uwanmu mata sanin duk bakinsu 'daya da Mummy da haka ya fara bata labarin ya samu tafiyar da yake ta jita so zasuyi tafiyar tare yaso a can sai ya nemi ko waye ya biyashi ya aureta daga baya ya saketa  domin mayar da aurensu 




Innalillahi su duk IYAYENSU keyi cike da mamaki wannan rikitaccen al'amari Munir yaci gaba 




Da haka suka shirya tafiya saidai yanayin da Mummy ke ganin Nabil yasa ta zargi babu lafiya dukda bata san sun rabu ba a lokacin hakan yasa ganin Nina ta gama waec tace suje tayi wani course kafin shekara ya zavayo tayi jamb hakan kuwa a Kayi saidai wannan dalilin yasa dole Nabil ya sake shawara kan yadda komai zai tafi batare da Nina ta gane komai ba hakan yasa yayi magana da kamfanin a kace akwai training d akeyi na 9mths so sai ya nemi a ka cika masa letter a nan a Firs a kan Can Umaima ke aiki kuma suka turata training in da wannan latter ya itama umaima ya samo mata training a kamfanin suka tafi abijan




Satinsu 'daya Nabil nata tunani mafita ya samu labarin MD na kamfanin bafaranshene mahaifinsa mutumin Abijan ne sai mahaifiyarsa baturiyar France  da yana aiki kuma yana aiki na France a abijan, sannan ri'a'en manemin mata ne wanda yayi alkawarin bazai ta'ba aure ba kasancewar shima bata aure a ka sameshi ba 




Nabil jin wannan labarin ya samu farin cikin samun mafita inda yajewa *Amaan* Lubna ta 'dago a zabure tana kallon yayanta ya girgiza kai yaci gaba 





Ko da Nabil yaje gun Amaan sai ya nuna masa Umaima anwarsa ce uwarsu 'daya ubansu 'daya kuma yanaso taje france wani course saidai wai course in ba'a bawa 'yen Africa sai 'yen europe ko kuka kuma ba'a'en da a ka haifa europe wato masu takardun asashen turai ko kuma in mace ce yazama tana auren 'dan asa haka ma in namiji ne 



Amaan yace wa Nabil babu damuwa sai Nabil yace indai zai musu takardun to shi bai damu ba ko auren sai an 'daura auren da gaske  ya amince zai 'daura na lokacin domin ya ha'da takardun da takardar shaidar auren su *Amaan* ya amince inda Nabil ya ro'eshi auren kawai zai 'daura musu wai domin takardun amma Umaima zata co gaba da zama gida Amaan yace babu damuwa "har Nabil zai tafi ya tuna Amaan mazinaci ne so inyana son biyan bu'atrsa dole ya bashi dama a kan Umaima yasan wannan ma zai saka bu'atarsa ta biya da sauri sanin matsalar Umaima ta wannan 'bangaren ya tabbata duk randa Amaan yayi gangancin ta'bata komai zai lalace ya saketa shikenan sun gyara aurensu da haka ya koma ya zauna ya fara magana inda ya nunawa Amaan bawai don Umaima na gida ba idan ya 'daura musu auren duk aikin da yake so tamasa kada ya damu ya kirashi zata zo "yace ok" su kayi sallama ya wuce cike da farin ciki 




Haka ya sanarwa Umaima nasararsu inda ya nuna mata sunyi da Amaan bazai ri'a kusantarta ba hankalinta ya kwanta itama domin a satin zata fara zuwa office 




Kwana biyu haka Nabil da wasu manyan limamai da ke Central mosq in suka wakilci Amaan Nabil kuma da kansa ya bawa Amaan auren  Umaima 





Salati kawai su yapendo keyi suna ambaton sunan Allah 




Lubna kuwa kuka ta saki da kyaw tana buga hannayenta a cinyarta 





Munir yaci gaba 





Wannan shine kuskure mafi girma da Nabil yayi a rayuwarsa 




Domin baisan waye Amaan ba a ba'dini just yayi anfani da labarin dayaji a bakin mutane 




Bayan auren ne Nabil yasa a ka sakawa Umaima implant batare da ita kanta tasani ba domin yayi tunanin kada ko sau 'daya Amaan ya nemi kusantarta ta arfi kuma hakan ya jawo wata sabuwar masifar 




Zaro idanu mummy tayi itama munir yaci gaba saidai tabbas Nabil yariga yayi kuskure domin ya manta a labarin dayaji an fa'da masa Amaan France a ka haifeshi can ya rayu har zuwa girmansa kuma kowa yasan turawa babu wani abu da suke yi babu bincike ko kuma da ka hakan ne shima da Amaan 



Domin manemin mata ne shi wanda baya anfani da Condom hakan yasa baya kusantar mace sai ya santa yasan inda tafito Kumar yasa an mata check up kafin ya kusanceta ko wacece ita kuma hakan ce ta kansance bayan aurensa da Umaima batare da saninsu ba daga ita har Nabil yasa aka yiwa Umaima check up wanda a ka gano tana 'dauke da mummunan ciwon sanyi wato Vaginal infection wanda yayi girma yana dab da zame mata cancer 




Salati Inna Hajara tasa haka mumny da maman da maman Munir da ke na'dar komai tunda munir ya fara magana 




Likitansa ya fa'da masa ciwon ya da'de jikinta tun uruciyarta yaci jikinta sosai wanda shine ya haddasa mata in namiji ya kusanceta sai ta kwantA rashin lafiya kuma gabanta zai kubura yayita ruwa yana wari matsalar da ta kasa yagawa kowa cikin IYAYENMU sabida babu wacce ke janta a jiki




Kuka yapendo ta saki tana furta Allah sarki marainiya babu wanda yasan halin da take ciki 




Nina Lubna su kansu sai suka ji jikinsu ya fara mutuwa da tausayin Umaima Munir yaci gaba...






A duk sadda Namiji ke saduwa da mace mai irin wannan matsalar zaiyita jin shima baya samun gamsuwa sabida ni'imarta ta bushe ita kuwa azaba ce take sha wata har jini yake fito mata wata kuma gudajin fari2 ne kefito mata yan wari kamar yadda itama Umaima matsalarta kenan saidai rashin kusanci da wata mace 'yer uwarta yasa haka tarika rayuwa da matsalar takasa sanarwa kowa har zuwa lokacin and da Amaan ya gano 




Bayan sun shirya yadda za'a mata aiki Amaan da Likitansa Amaan yasa a ka loda mata aiki a office yacewa Nabil zata kwana aikin bayan haka suka bugar da ita inda a kayi aikin a ka gama batare da ta sani ba 




Sannan magungunanta Amaan yasa ta daina barin office sai 7pm inda yasa ana saka mata drugs inta cikin coffee tanasha har saita sha na yamma kafin ta tashi aiki da haka ta warke 




Yapendo ta furta Allah sarki Allah ya saka masa da alkairi su baffa suka kalleta tayi shiru Munir yaci gaba 




Tun bayan da ta warke Amaan ya fara kusantarta inda tun tana i harta shiga yadda gudun kada asirinsu ya tonu ita da Nabil saidai ko shi Nabil ta'i barinsa yasan Amaan na saduwa da ita har zuwa lokacin da zasu bar asar saidai tuni Amaan ya gano komai na aryar da suka masa da kuma dalilinsu na rokarsa ya auri Umaima shima kuma a lokacin ya riga ya kamu da sonta inda ko bayan da ya cika alkawari ya sake ta a ranar da zasu bar Abijan ya je gurin Nabil yana fa'da masa ya janye sakin da yayi mata 




Nabil ya nuna baisan zancen ba nan yayi blackmailed Nabil cewa yasan komai na yaudarar da suka masa zaije yaga IYAYENSU



Nabil yace masa Umaima bata sonsa, duk biyyayar da tayi tamasa domin shi ne yasata shiasa wannan dalilin ne ya 'dagawa Amaan hankali ya furtawa Nabil shidai ya mayar da Umaima tana matsayin matarsa kuma soyayyarta wannan zai tantance da kansa kafin ya zo ya 'dauketa su fara rayuwa tare kamar kowasu ma'aurata 




Munir yayi ajiyar zuciya yana furta saidai wai bayan sun rabu Amaan yasamu hatsari ya shiga jinya wanda da wannan damar Nabil yari'a o'arin suyi su 3mths andya cika su 'daura mayar da aurensu sabida a lokacin yana tunanin in ya gaggauta abin kafin cikar wa'adin da umaima tasani na cewa tana idda To zata zargi wani abu kuma bazata goyi bayansa ba hakan yasa dole ya hakura yanata fatan kwanakin su cika batare da Amaan ya warke ba duk kuwa da yabi malamai dayawa sun kuma jadadda masa tabbas tunda Amaan ya mayar da ita tana matsayin matarsa ne 




Ana hakan ne a ka wayi gari da rasuwar Nabil 





Ya kama kansa yana furta ni kaina nace zan aureta ne domin tabbatar da binciken shin da hannunta a kisan Nabil 




Kallonsa baffan Mubi da modibbo su kayi modibbo yace kamar yaya kuma da hannunta.?




Yayi ajiyar zuciya yana furta "baffa sabida tabbas Umaima na mugun sonsa kamar yadda yake sonta.. 



Kallonsa Lubna tayi yaci gaba 



Yes sis ya nemeki ne domin ya ara tabbatar da son da Umaima ke masa kuma tabbas tana matu'ar sonsa tana binsa gidansa duk sanda yake so ko yake bu'atarta tana kuma 'boyeshi duk sadda ya biyota gidan nan tana yin biyayya a duk abinda yake so ko wanda bai so hakan yasa kikaga yanzu ko ni bata damuwa da zaman hira da ni dalili 'daya ya sanyata qin bayyana masa soyayyarta duk suna kallonsa ya furta 



Martabar IYAYENMU wanda shine abinda ya ri'eta amma ina tabbatar muku tana sonsa fiye da yadda harshe zai iya bayyanawa 





Bayan dog on shiru Baffan mubi ya furta kana nufin har yanzu da aure kenan tsakaninsu.? 







'Dagowa yayi yana kallon Lubna ya furta "eh baffa" 




Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un 



Munir ya furta baffa ku kwantar da hankalinku domin ita kanta tasan shi yayi kisan shiasa har ta danne soyayyarsa ta jagoranci tona masa asiri  



Duk shiru su Kayi babu wanda ya ara magana..






Da kyar take bu'de idanunta da suka mata nauyi har ta gama bu'dewa ras kama goshinta tayi jin wani irin sara mata da yake yi motsi taji da wani irin anshi da taji take cikinta na hargitsewa ta fara 'dagowa 





Gabanta ne ya fa'di ganin wacce ke tsaye kamar cikin mafarki ta kalli agogo 12:56 na dare ta ara kallonta 




Murmushi khloe tayi ta furta is high tym da ya kamata muyi meeting ni da ke 



.yawu Umaima ta ha'diya tana kallonta ..✍🏻

💖IYAYENMU💖





No comments