Breaking News

Gidan Aunty book 2 page 3-4

 



Not edited 



Page 3 &4??


Yinin ranar gabaki d’aya kula suke da Tahee tun tana zabura har ta dena sai dai har lokacin babu Wanda tayi wa magana , babu Wanda ya damu da rashin maganarta ta Sabida umarni da baba Malam ya basu, kana kallan Tahee zakagane tana cikin damuwa saidai babu Wanda take cewa komai .

  Haka Suka ci gaba da kula da ita harzuwa ranar da Alhaji isma’il zea koma , bayan ansiya wa Tahee itama abun anfani, sosai tafito  tass da ita duk da bata yiwa kowa magana sai bin fuskar kowa da take da kallo. A cikin jet d’in wani amininsa Alhaji isma’il zai koma shiyasa tafiyar tasu taxo musu da sau’ki, suna zuwa jirginsu ya tashi cikin sararin samaniya zuwa UK.


6 hours 18 minutes ne ya kawo su Uk cikin babban filin Airport d’in kidlington date Oxford, duk inda ya saka ‘kafarsa nan Tahee take sawa , cikin wata katuwar Audi aka zo d’aukarsa, bakowa bane yazo d’aukarsa face Ya moh, yana ganin Alhaji isma’il ya rungumeshi “ welcome back dad”, shima Alhaji isma’il d’in rungumesa yayi a jikinsa , “ Thank you my son, “ gabaki d’aya yah moh bai kula da Tahee dake kusa da Alhaji isma’il ba sai da ya bud’e masa mota, suna had’a ido da tayi yaji zuciyarsa ta buga yana neman nutsuwarsa yarasa , cikin Sauri ya soma karanta adduar da ta zo bakinsa, nuna wa Tahee cikin motar yayi ame makon ta shiga sai ta tsaya kallansa, fahimtar hakan yasashi shiga cikin motar , sai gashi itama ta shiga , ta cikin mirror yah moh yake kallan abunda ke faruwa , azuciyarsa yana ayyana me yarinyarnan take tare da dady duk da yasan da zuwan ta . Mintuna 15 ne ya kawosu gida , tunda Mimi taji saukar mota ta fito a guje zata fita momy ta hanata, ita kad’ai sai faman kunburo baki take , da sallama Yah moh yashigo falon bayanshi kuma Alhaji isma’il ne , Mimi na ganinshi ta saki ihu , dagudu ta nufo Alhaji isma’il daniyar rungume shi amma kallan da yah moh yayi matane yasata dakatawa a sanyaye ta furta “ welcome back dady , nayi missing d’inka sosai..” bata ‘karasa ba idanuwanta suka sauka kan Tahee da ke ra’bewa, kallan dady tayi sannan ta kalli Tahee, kafun tayi magana momy ta fito cikin Adon less meshegen tsad’a , wuyanta kuma sarkar gold ne tare da ma had’inta , ita kadai sai faman walwali take ,ganin sun tsaya ne yasa momy sakin lallausan murmushi “ ku shigo daka ciki mana , gabaki d’ayansu cikin falon suka shigo Tahee na bayan Alhaji isma’il, cike da murmushi momy ta nuna Tahee alamar tabbatarwa “ Itace bakuwar tamu?”, jinjina mata kai Alhaji isma’il yayi , inda Tahee take tanufa, daniyar ta’bata , da Sauri Tahee mi’ke tana kallanta amma ta kasa yi mata magana , Ri’ko hannunta momy tayi cikin tausasawa ta furta “ karki damu daughter na ki kwantar da hankali babu abunda zai sameki insha Allah “, Ajiyar zuciya Tahee ta sauke duk da ta’ki yin magana sai bun fuskokinsu take da kallo, kallan Mimi da ta zuba musu ido momy tayi “ MiMi zoki kaita d’akin da aka gyara nakusa da naki”, Girgiza mata kai Alhaji isma’il yayi , for now akai ta d’akin Mimi , sai ta taima ka mata, idan nahuta zamuyi magana “, Toh momy tace , Mimi zatayi magana Yah moh ya kalleta, d’an ‘karamin bakinta ta turo waje tare da ri’ke hannun Tahee dake binta da kallo, a hankali suka nufi sama tare , Tana shiga d’akin Mimi ta saki hannunta tare da nuna mata ‘kofar Toilet “ ga ban d’aki nan, and nan kuma wajan sallah ne ,ga dadduma da sallaya “, tana gama mata bayani tabar d’akin. Bin ko ina nad’akin tahee tayi da kallo kafun ta tsugunna ‘kasa tana fashewa da kuka , kukan da yake zuwar mata tundaga ‘kasan zuciyar ta , kukane take yinshi me rad’adi, da Sauri sauri numfashinta ya soma yin sama da ‘kasa kamar zai d’auke , cikin Amincin Allah bakinta ya fara kirawo sunayen Allah , a hankali wata iriyar nutsuwa ya fara ratsata tana sakin ajiyar zuciya, ban d’akin da Mimi ta nuna mata ta kalla kafin ta mike ta shigeshi, mintuna kad’an ta fito daga toilet d’in, inda sallaya take ta nufa tare da kabbara sallah, saida tazo Daidai tahiyar‘karshe kuka ya kwace mata , lokacin da Mimi take shigowa d’akin d’auke da tray a hannunta , yadda taji shashshe’kar tahee ne yasa ta kallanta, mamaki abun ya bata ganin tana sallah tana kuka, da sauri ta fita daga d’akin , ita kuwa tahee batasan tanayi bama , har ta idar da sallarta tana kuka gwanin ban tausayi, a haka wani wahalallan bacci ya d’auketa kan sallayar.


Shima Dady wanka yayi ya huta kafun yaci abinci , a ‘ka idar gidan duk lokacin da wani yayi tafiya tare ake zama ayi hira , hakan ce ta kasance a ‘bangaran dady , tunda ya soma cin abinci yake bin fuskokinsu da kallo , kowa kaga fuskarsa zakaga alamar tanbaya tattare dashi, maida kallansa yayi kan Mimi, kin kai mata abincin ?” Eh dady amma da nashiga naga tana sallah tana kuka sai tabani tausayi”, cewar mimi, kallanta momy da yah moh sukai alamar ‘karin bayani , ita ma Mimi kanta ta d’aga musu alamar gaskiyar zancenta. Ajiyar zuciya Alhaji isma’il ya sauke , kafun ya soma labarta musu abinda ya faru har dalilin na tahowa da ita , tunda ya soma basu labarin Mimi take kuka , shima yah moh sosai idanuwansa suka kad’a, hatta momy saida ta share hawaye “ wannan bala’I har ina ? Yar mitsitsiyar yarinyarnan ma baza a barta ba , koma wanene wannan ya cika babban azzalumi Allah bazai barsaba wallahi”, cewar momy, itama Mimi cikin shesh she’ka ta soma magana “ Dady kabar mana ita anan kaji? Zan dunga kula da ita nima “,kallanta yah moh yayi ya d’auke kansa batare da yace komai ba , kallansa dady yayi, “son baka ce komai ba ,” Dady duk ynda kace hakan yayi , ya kamata ta zauna anan d’in gudun karwani ya lahantata “, cike da gamsuwa dady ya jinjina kansa, gabaki d’aya sai suka canza hirar tasu zuwa kan tahee , anan ne dady yake sanar ma momy juna biyun dake jikinta kasan tuwar ta Doctor ce itama .

Duk da Mimi batasan taba , ba ‘karamin murna tashiga ba , hatta dady sai da yayi mamakin murnar ta, yau bata dad’e sosai ba ma ta tafi d’akinta , har lokacin bacci Tahee take , babban blanket Mimi ta d’au ta lullu’be jikin tahee dashi, zata kwanta kenan momy ta shigo d’akin, ganin Tahee kwance a kan daddumane momy ta furta “Subhanallah , me nake gani haka ?”, da Sauri ta ‘karasa inda Tahee take , a hankali ta soma tashin ta, cikin firgita Tahee ta farka da har sai da momy ta ri’keta “ kwantar da hankalinki babu abunda zai sameki kinji”bin momy da ido Kawai tahee tayi , nan ma batace mata komai ba , kama hannunta momy tayi ta mikar da ita zuwa saman bed Inda Mimi take ta kwantar da tahee tare da lullu’barta , kallan mimi momy tayi “ Samuku karatun alqur’ani”, hakan kuwa mimi tayi ta kure volume din yadda zasu fi ji sosai, ‘kasa ‘kasa momy ta furta “ ki kula da ita”, kafin kafin ta kashe musu light d’in ta bar musu mara haske , tunda Mimi ta saka karatun alkuranin nan  take Tahee ta soma  sauke ajiyar zuciya ita kad’ai, a hankali takai hannunta kan cikinta, ganin haka yasa Mimi saurin mikewa , inda tray din dazu yake ta nufa , milk din kan tray din ta suka tare da wasu fruit ta mikawa tahee , karba tahee tayi ta soma cin abincin, sai da ta ci fruit da milk din sosai kafin ta soma ajiyar zuciya , sai a lokacin bakinta ya bud’e, daga sama Mimi taji muryar Tahee “Nagode “, kallar nagode din da ta fad’a masa yasa Mimi kara sakar mata murmushi cikin murna ta furta “ kije ki kuskure bakinki” , hakan kuwa tahee tayi sai da ta kuskure bakinta, ta sake wani alwalan kafin ta kwanta a gefen Mimi duk da har yanxu zuciyarta bata gama sakewa ba . 



WASHE GARI 

Momy da kanta tazo tashin su mimi, lokacin da ta shigo d’akin a kan dadduma ta tarar da tahee na sallah, murmushi ta saki dan sosai ta burgeta, ‘karasa shigowa ciki momy tayi tare da nufar inda mimi take a kwance tana shakar bacci, “Mimi…,Mimi”, cewar momy, d’an motsi Mimi tayi kafun ta furta “Uhmmm “, girgiza kai momy tayi kafun ta furta “ oya ki tashi lokacin sallah yayi “, motsi mimi ta farayi da idanuwanta kafun ta bud’e gabaki d’aya akan momy, a hankali ta mike zaune , sai a lokacin idanuwanta suka sauka kan tahee da ke sallah,sai kuma ta mayar da kallanta kan momy da ta mike ta fita ganin har lokacin sallah tahee take , itama mimin ganin lokaci na tafiya ne yasa ta mikewa , bata dad’e a toilet ba ta fito , lokacin tahee ta idar da sallanta, itama sallahr ta tayar tahee na gefenta kamar mara lafiya sabida yanda tayi shiru kamar me tunani sai kuma hawaye suka soma sakko mata akan kumatunta, duk da ba sosai Tahee ta girmi Mimi ba amma dukda haka cikin tsokana saida mimi tace mata “ Ina kwana Aunty”, d’an kallanta Tahee tayi kafin ta du’kar da kanta kasa , kusa da ita mimi ta matso kafun ta kama hannunta “ ki saki jikinki kinji? , Babu Wanda zai ‘kara ta’baki, duk Wanda ya ‘kara ta’baki sai nayi gunduwa gunduwa da namansa “ kawai kallanta tahee tayi hawayen da take ri’kewa ya fara gangaro mata, zuciyarta ba dad’i tun jiya da tabar Nigeria komai da ya faru na ‘kara yawo a cikin kwakwalwarta, batasan Wana hali mijinta yake ciki ba , Wana hali zai shiga, ya yake ynxu, oummanta , Taheer , gabaki d’aya farincikinta ya rushe , abu d’aya yayi mata saura yanxu, babynta, babynta da mijinta yake matukar ‘kaunar gani, babynta da mijinta yake so , so asalinsu, babynta da yake wa kallan d’an uwansa da yarasu, Amma gabaki d’aya ta rushe musu farin cikinsu da suke ginawa , farin cikin da suke Bu’Kata, ta cutar dasu , cuta sosai , an bata Amana amma taci wannan amanar, ta zalincesu ,sannan tana ‘ko’karin ‘kara salwantar da wani ran , babynta , ace auntyntace ta kashe mata uba, yanxu ma tana ‘ka’karin kashe mata d’a, wani tsantsar tsanar Ammey ne ya ‘kara shigarta, tayi alkawari sai ta koma, sai ta koma ta Nuna wa Ammeey bata isa ta cutar da su ba , idan Allah be nufa ba,hannun da taji akan kumatuntane yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta fad’a,kallan Mimi data share mata hawaye tayi, itama Mimi kallan tayi tare da sakar mata murmushi” kukan nan ya isa haka Aunt, ya kamata ki watsa ruwa , kafin ki fito zan ajje miki kayan da zaki sa, komai da kike bu’kata gashinan agaban mudubi idan kinasan wani abu sai ki tanbayeni kinji”, binta da kallo tahee tayi har ta gama maganarta , kafun ta furta “Nagode “ da kyar, jinjina mata kai Mimi tayi , ita tafita tahee kuma tashiga toilet d’in.


A palour kuwa Momy tsaye a wajan dinning tana shirya breakfast d’insu, Mimi na zuwa kawai ta rungumeta a jikinta, tureta momy tayi “ Mimi har yanxu baza kuyi hankali bako? Kishiga taitayinki fa”, baki kawai mimi ta turo kafun ta furta “ Good morning momy”, ita momy “ morning “, wani ma daidaicin tray Mimi ta d’auka ta fara had’a kayan breakfast a ciki , ko me ta gani sai ta d’inta , kallanta momy tayi alamar ‘karin bayani, turo baki Mimi tayi “ Ni momy batare da ku zan ci abinci ba yau, zan je naci da sabuwar sis d’in da nayi, in dady da yah moh sun fito kice ina gaishe su “, tana gama fad’ar Hakan tabar wajan, binta da kallo Momy tayi “ yau kuma mimi ? Anya Itace kuwa ?” Abin ba ‘karamin mamaki ya bata ba sabida tasan mimi ko cikin mutane batasan shiga amma yau da kanta take furta agaishe da Yah moh , hmmmm, murmushi kawai momy tayi.

Mimi kuwa tana shiga d’akin wata abaya ta d’auko wa Taheee blue colour me adan flowers pink colour , sosai rigar tayi kyau, bud’e kofar toilet d’in da akai ne yasa mimi ta d’ago kanta,”Yauwa Aunt ga kayanki nan, anjima sea naje nayi miki siyayya kinji, yanxu zan dawo “, bata jira amsar tahee ba ta kara barin d’akin bayan ta ajje tray d’in hannunta, kallan rigar da Mimi ta ajje tayi daga gefe wasu set d’in underwear pink colour sababbi’kal dasu a cikin Leda , ajiyar zuciya ta sauke , kafin ta saka kayan kamar dan ita aka yisu duk da tana cikin damuwa kayan ba ‘karamin kyau sukayi mata ba , sosai da sosai kayan sukai mata kyau, kallan fuskarta tayi a gaban mudubi kafun ta ta’ba gashin kanta da yake a jike , momy ce ta shigo d’akin bakinta d’auke da sallama bayanta kuma mimi ce , ganin bataci komai da aka kawo mata bane yasa momy d’aukan tray tare da kamo hannun tahee tana zaunar da ita , cikin raha momy ta furta “ nifa banaso naga daughter na tana cikin damuwa , ki saki jikinki kamar ni na haifeki, ga Mimi nan ki d’auketa kamar kanwar ki kinji”, sunkuyar dakanta tahee tayi kafun a hankali ta furta “ Ina kwana “, sosia momy taji dadin gaisuwarta amsa mata tayi cikin sakin fuska kafin ta d’auko spoon da niyar bawa tahee abinci a baki , kallanta tahee tayi itama momy ta jinjina mata kanta , da kanta momy ta shiga bawa tahee  abinci abaki, tana ci hawaye na bin fuskarta , ko saud’aya momy bata hanata ba dan tasan shine kadai hanyar da zaisa nauyin dake zuciyar ta ya sauka , sai da ta tabbatar ta koshi sannan momy ta ‘kyaleta, hand dryer Mimi ta d’auko tare da sauran abubuwan gyaran gashi, dakanta ta busarwa tahee kanta, tare da gyara mata uban tulin gashin da ke kanta,kallan Mimi, momy tayi , “idan kun gama ku samemu a part d’in dadyn ki”, yana kai karshen zancanta tabar d’akin tare da tray din abinci. Saida Mimi ta gyara mata kanta sosai tayi mata packing d’inshi kafun ta kama hannun tahee suka fito, sai binta da kallo tahee dake , wani waje suka nufa ,tafiya kad’an ya kawosu wani babban falo me shegen kyau da tsa ruwa da yaso yafi Wanda yake a farko, suna shiga mutane uku ne a falon daga Alhaji isma’il sai momy da yah moh da yakw gefe, idanuwan tahee na sauka akan yah moh saida gabanta ya fad’i addua kawai ta soma yi cikin zuciyar ta , kafin ta zauna inda momy take nuna mata, da’kyar tahee ta gaishe da Alhaji isma’il tana bin fuskarsa da kallo da mamakin da ita kadai tabarwa kanta sani, cikin fara’a ya amsa mata, gaishe da yah moh tayi da yake zaune shima, cikin sakin fuska ya amsa mata kamar Mimi, mintuna biyu falon ya d’au shiru kafun Alhaji isma’il ya bud’e taro da addua , sai da ya tabbatar kowa ya nutsu kafun ya mayar da kallansa kan tahee, “baiwar Allah ko zamu iya sanin sunanki”a hankali ta bud’e bakinta “ sunana taheera muhammad “, jinjina kansa Alhaji isma’il yayi alamar gamsuwa kafun ya ‘kara yi mata wata tanbayar da ya ta’bo mata abunda take dannewa a cikin zuciyar ta, hawayen da take kokarin takatarwane sukayi nasarar zubo mata, babu Wanda ya hana ta yin kukan sai ma ‘kara maimaita maganarsa da Alhaji isma’il yayi” ko zamu iya sanin wacece ke , me ya faru har kika bar gidan mijinki da ciki”, share hawayenta tahee tayi tana sakin ajiyar zuciya , ko ba komai sunyi mata hallaci , sun kubutar da ita daga azabar da take ji a jikinta lokacin da take Niger , a hankali ta soma labarta musu labarinta, tun zuwanta gidan su king, da yadda tayi rayuwa dasu , tabin hankalin da ta samu har zuwa auranta da sanadin barowarta gida “, ba momy da Mimi da suke mata ba , hatta Alhaji isma’il da yah moh saida suka goge mata kwalla, momy da Mimi kuwa kuka suke iya ‘karfinsu, itama tahee du’kar da kanta tayi ta cigaba da kukunta, murya a raunane momy ta soma magana “ Wannan mata anyi shed’aniyar mata , insha Allahu sai taga hukuncinta tun a duniya , cikine kuma insha Allahu sai kin haifoshi kuma sai yayi rayuwa kamar kowa da yar dar Allah” kafun ta mayar da kallan ta kan dady “ daga yau ta Xama d’ata, duk abunda uwa take wayarta zan dunga mata shi da yar dar Allah sannan zan ci gaba da bata kulawa har ta haihu”,itama Mimi cikin kuka ta furta “Nima zan zauna da ita bazan ‘bata mata ba , komai tare zamu dungayi har ta haifar min baby”, murmushi Dady ya saki , dan shima sosai yaji wani irin Kaunar yarinyar ya shiga ransa kamar ‘yar da ya haifa a cikinsa , yah moh kuwa babu abunda ya furta sabida yadda kansa ke masa ciwo, lokaci zuwa lokaci yana kallan tahee ga ransa yadda yyi mugun baci,basu wani dad’e a Wajan ba Mimi ta kama hannun tahee suka bar falon dady, sai faman jan ta da hira take , ita de tahee sai binta da kallo take kawai, duk surutun tahee mimi ta dameta sosai tun bata amsa magana maganarta harta dawo amsawa da “eh ko ah ah”, a hankali kuma tana d’an amsawa Mimi hirarta, gabaki d’aya yinin ranar tahee sai tama tamkar wata sarauniya hatta ruwa idan momy ko mimi suka ga za Tasha da kansu suke bata a baki, tun tana jin wani iri harta d’an sake dasu ganin yadda suke kila da ita, da tayi wani motsi momy zatace mata akwai abinda take so, da yamma kuwa da kanta Mimi ta fita driver ya kaita shopping, kome ta gani indai ya burgeta d’aukowa take sosai ta suyo abubuwa masu yawan gaske tundaga kan kayan sawa har zuwa turaruka , gabaki d’aya kuma siyayyar ba tata bace , siyayyar tahee ce. Data koma gida tahee sosai tayi kuka , tun momy na zuba mata ido har ta dakatar da ita ganin kukan nata bana karewa bane , da daddare ma Mimi bata zauna a palour ba , sama ta koma wajan tahee anan Suka ci abincin da ta kawo musu. 



******koda gari ya waye haka momy da Mimi suka ci gaba da kula da tahee , ko sau d’aya basu nuna mata basu da alaka da ita ba , sai ma wani irin kulawa da suke bata, hatta Alhaji isma’il da shima lokaci zuwa lokaci zai tanbayi momy ko akwia abunda suke so, hatta yah moh da ya dawo gida da wasu kayan ciye ciye ya dawo masu shegen yawa cikin ledoji na tahee , sabida yasan masu ciki da ciye ciye , hakan da yayi ba ‘karamin faranta ran momy da Alhaji isma’il yayi, gabaki d’aya sai ya zama kowa tahee yake bawa kulawa, babu Wanda zai ce bata da ala’ka dasu, tun tana no’kewa har ta soma sakin jikinta dasu ganin yadda suke nuna mata kulawa babu hantara ko nuna banbanci.



????????


AFTER ONE MONTH 


NIGERIA 

     LAGOS STATE 


NAHYAN HOSPITAL.


A hankali d’an yatsan king ya soma motsi a hankali , kafun ya fara motsa idanuwansa shima , lokacin gabaki d’aya su Abbey suna d’akin, mahma ce ta fara lura da yanayinsa, cikin sauri ta matso inda yake tana kiran sunansa, a hankali ya bud’e idanuwansa kafun yayi saurin kallesu sabida hasken da ya Haska masa cikin idanu,kara bud’e idanuwansa da suka ‘kara girma yayi, a hankali ya soma bin su Abeey da suka matso Inda yake da kallo, ‘kara dubawa yayi amma still be gantaba, murya a dushe ya furta “ my wife “, duk da rashin lapiyar da yayi babu abunda ya canza daga yanayinsa , fuskarsa ba asake take ba , kuma ba a d’aure take ba , yana bin su oummey da kallo ganin yanda ko wannan su yayi shiru, ‘kasa ‘kasa ya ‘kara furta “ where is she? And my child ?”, yanxu ma babu Wanda ya amsa masa sai ma cikin sauri da abeey ya kallesa , zamuyi magana daka baya bari a fara kiran doctor ya duba ka, be kuma cewa komai har doctor ya shigo cikin d’akin kallan sa king yayi fuska ba fara’a ya furta “for how long?”, cike da girmamawa doctor din ya furta 1 month and 4 days , shiru king yayi yana dafe goshinsa da ya soma sara masa , so yake ya ganta , so yake yasata cikin idanuwansa ko zai ji dady, ‘karasowa su oummey sukai gaban gadon , “ya jikinta “ jinjina musu kai yayi kafun ya lumshe musu ido, sai da doctor ya dubasa yaga ba matsala tukunna,wasu sababbin kaya king yasa a kawo masa , wani toilet ya nufa kamar ba a cikin hospital din yake ba , su kuma su Abeey suka fito zuwa falon inda king yake sabida abarshi ya shirya, cikin murna abeey ya kira samreen da ke tare da dada ya sanar da ita good news din farkawar king, lokacin a kwance ukhti take amma sai da ta mike tsaye da saurinta, har dada saida ta tsorata, “ amma dai anyi yar iskar yarinya, Menene kike mana wannan ihun haka “, murmushi ukhti ta saki lokaci d’aya hawaye na sauka daga cikin idanuwanta “ dada king ya Tashi “, mikewa dada tayi da saurinta “ mu tafi asibitin yanxu “, zasu fita kenan su ilham suka shigo cikin palour , ukhti ce tab kallesu “ Yawwa kwanda da kuka shigo, maza kuje ku cewa su mamy zamu je hospital king ya farka “, ihun murna ilham da su sumayya suka saki har dada tana zaginsu, sumayya ta nufi part din mamy lokacin suna zaune su da momy, sosai sukai farin cikin suma , momy har da mikewa ta kalli mamy “ ya kamata a had’a musu wani abu ko suna bukata “, hakane cewar mamy, firdausi kuwa part din Ammey ta nufa lokacin ta fito daga cikin kitchen hannun ta d’auke da wani plate na tangaran, cike da farin ciki firdausi ta fad’a mata farkawar king , bata jira jin amsar Ammey ba tabar part d’in, a rud’e Ammey ta saki plate din hannunta, kan ‘kafarta ‘karar azaba ta saki ganin yadda yaji mata mummunar rauni amma duk wannan be dametaba, farkawar king ne yafi komai ‘kuntata mata , azuciye ta nufi d’akinta dukda azabar da ‘kafarta ke mata. 


Lokacin da su dada suka ‘karasa cikin hospital d’in cike da farinciki suke tanbayar inda king yake , abbey ya sanar da ita yana shiryawane, Maya finta dada ta kama ta d’an goge kwallar fuskarta “ oh ni ‘yasu , gashi ya farka , Kema Allh ya bayyana ki tahura ta , Allah Yasa kina hannu na gari, nayi musum (missing) d’inki wallahi,Allah ya bayyana ki duk inda kike “, bata ‘karasa zancanta ba Sabida fashewar abu da suka ji, gabaki d’aya maida kallansu sukai wajan , ba komai bane ya fad’i face kantamemiyar wayar king, idanuwansa gabaki d’aya sunyi jajur lokaci ‘kan’kanin, kamar wani zaki ya nufi dada, jijiyoyin kansa gabaki d’aya ta mi’ke , sam ya manta wacece a gabansa, babban glass din dake kusa dashi ya buga hannunsa da ‘karfi har saida hannunsa ya fashe glass d’in ya tarwatse, babu Wanda be tsorata da yanayin da king yake cike ba , da ‘karfi ya furta “ ina matata?”.





????GIDAN AUNTY????


07041879581

MSS LEE ??


No comments