Breaking News

Gidan Aunty book 2 page 19-20

 


BOOK 2 



Page 19&20

            ??


Gabaki d’aya anrasa Wanda zai kwace Ammey , oumma ce dakanta a wannan karanta karasa inda suke , da ‘karfi ta dam’ki hannun taheee , itama tahee zata kwace hannunta oumma ta d’auketa da mari tare da daka musu tsawa ita da taheer , gabaki d’ayansu sunkuyar da kansu sukai kamar had’in baki , musammann hannun tahee da oumma ta ri’ke , alama tayi wa su khaleed akan su d’auke taheer, hakan kuwa akayi khaleed da sha’aban ne suka d’aukeshi, sai faman zazzare idanuwa Ammeey take musamman wajan idanuwanta da ya fara kunbura ga le’benta shima da ya tashi, duk adon da tayi ya ‘baci sai muninta ya fito sosai, zahra tayiwa alama da tazo , taso wan kuwa tayi dan ita abunda su tahee sukai wa Ammeey taji dad’in sa, a cewarta ma dama idanuwan Ammey suka tsokale kowa ma ya huta. Tana ‘karasowa oumma tayi mata nuni da ta d’akko mata Rubutun ta, kai zahra ta d’aga mata kafun ta bar falon da Sauri , sha’aban yana ganin futarta da minti d’aya shima ya bi bayanta, taheer kuwa gabaki d’aya tashi zai bar falourn oumma tace ya koma, ko da ya koma d’in Wajan small mom yaje , itama small mom gabaki d’aya jikinta yayi sanyi da abubuwan da suke gani yanxu kamar almara , shiyasa ta ri’ke hannun taheer d’in kar yace zai ‘kara tashi, itama tahee da fuskarta take a had’e kallan Ammey da haryanxu take sauke nunfashi tayi, ‘kara tahee ta saki tana dafe kanta , tare da fincike hannunta a hannun oumma , gadan gadan ta nufi ammey, ydda take abu kad’ai zakasan ba ita kad’ai bace , da Sauri cikin mawuyacin hali Ammey ta mi’ke zata musamman yadda taga tahee ta nufota, itama taheen bata dena binta ba daina Sauri da ta ‘karawa tafiyarta, Daidai lokacin da king ya shigo falourn , gabaki d’aya falon sauke a jiyar zuciya sukai tunda suka ga yashigo , shima fuskartasa gabaki d’aya babu walwala da rahma akan fuskar tasa , Ammey na ganinsa ta nufo sa da Saurinta tana sakin masa kukan ‘karya “ son kaga abunda yarinyar nan tayi mun? Bazaka ‘kara zama da ita ba , ka duba kaga yadda tayi mun son ? Kalli irin dukan da tayi mun”, bata ‘karasa ba tayi kamar zata cafkota Sabida fusatar da tayi , da hannu d’aya king ya saka ya janyota jikinsa , shima d’in ‘ko’karin kwace wa take kamar wacce ta fita daga hayyacinta, ganin Dagaske hannunta zata kwace ya sa duka hannunsa biyu ya ri’ke ta sosai tare da daka mata tsaya , a Daidai lokacin da yayi mata tsawan alokacin jikinta ya tafi kamar zata fad’i ya ri’kota , take a lokacin tahee ta suma a jikinsa. Tallafe ta yayi sosai kafin ya kall Ammey da idanuwansa da suka gama yin ja Sabida ‘bacin rai, su zahra ne suka shigo ita da sha’aban da yake d’auke da ruwan da oumma tace, a d’an kausashe king ya furta “ come in”, zaki ne ya shigo cikin falourn bakin sa d’auke da sallama , hannunsa kuma wanine da ya gama cin duka wajansu fuskarsa a kulle , kwance abunda fuskar zaki yayi kafin ya hankad’o mutumin ‘kasa ,gabaki d’aya salati falourn suka d’auka , bakin Abbey har karkarwa yake wajan furta “ saleem?”, d’ago da kansa uncle saleem yayi da ya gama cin duka a hannun su zaki, itama dada salati ta soma taki “ tahanuni me nake gani haka ? ‘Kanin baban naka zaka sa ayiwa wannan dukan? Lapiyar ka ‘kalau kuwa ?”, yadda ran king yake a ‘bace ne yasa gabaki d’aya be bawa dada amsar taba sai ma jijiyoyin kansa da suka tashi sosai, “ DADA”, muryar da dada tajine yasa ta mi’ke tsaye a firgice abbey da su dady ma duk mi’kewa sukai tsaye ,ummey gabaki d’aya jikinta karkarwa yake tana nuna sa da d’an yatsa, Allah sarki samreen da Sauri ta ‘kara inda yake kafun ta furta “ Akhiee”, yadda tayi hugging d’insa ne yasa ta d’an sakar mata murmushi duk da ransa da yake a jagule, kallan ummey da jikinta ke rawa yayi , kafun ya kalli abbey yana sakar musu murmushisa kamar da, hawaye ne suka fara sakkowa akan ummey, kafun ya kalli king da shima shi yake kallo, sai alokacin uncle saleem yaja dogon nunfashi a wahale daga suman zaune da yayi, Ammey kuwa gaba ki d’aya jikinta karkarwa yake , lokaci d’aya ‘Kai’karin jikinta yafu na farko , da Sauri ta fara susar jikin ta Sabida azabar zafi da yake mata, arud’e uncle saleem ya fara duka yah moh , be san lokacin da bakinsa ya furta “ baka mutu ba ? Me yasa baka mutu ba ? Da nasa su kashe ka basun nuna min vidoen ‘konaka da sukai ba ?” Murmushi akhie ya sakar masa tare da girgiza kai “ har yanxu ina raye tun lokacin da kasa a kasheni kai da ita sabida asirinku da na sani “, ya ‘karasa yana nuna Ammey da ke faman susa, d’an kwalin kanta tuni ya cire ya koma gefe shima . Rai a’bace abbey ya kalli uncle saleem “ kai kasa a kashe mun d’ana dama? Me nayi maka da na cancanki wannan cin amanar”, shima uncle saleem a zuciye ya kalli abbey tare da nuna masa dada “ duk ita tajanyo komai , da bata bari naji cewar ba Itace ta haifeniba da duk hakan bata faru ba , me yasa komai sai tace kai kai kai ? Idan zan tanbayeta kud’i da yawa sai tace zanyi almabur ziranci, dan nayi yawo da ‘yan mata ko dan ina kwana dasu zata hanani? Rayuwa tace fa bata kowa ba , duk yadda naga damar jin dad’in rayuwa hakan zanyi , ni ban ta’ba sanku ba, na tsaneku dukanku shiyasa nayi ‘ko’karin kashe ka ,na kashe ‘yayn naka gabaki d’aya ,” sai kuma ya mayar da kallansa kan uncle musaddiq ya ‘kyal’kyale da dariya “ kai ma yanxu haka ka fara shirin jana’izar d’anka dan yanxu haka na tabbata ya zama matacce, idan ya mutu kaje kabarinsa kasanar dashi bana san bin kwakkwafi , tun farko banyi niyar kashe saba , shish shigin da yayi mun lokacin da nake tattaunawa da masoyiya tace yasa na sa a akashesa “ da Sauri momy da uncle musaddiq suka mi’ke tsaye , momy har ta soma hawaye sai ga muryar haroon a bayansu” uncle saleem ban mutu ba , da saura na Sabida yaya king ya ku’butar dani “, gabaki d’aya falan ajiyar zuciya suka sauke , ganin haroon. Had’iye maganar da zaiyi yayi ganin haroon a gabanshi be mutu ba , cikin kuka dada ta soma magana “ ka cuceni saleem kaci amanar ta , na d’auke ka kamar d’an da na haifa amma kaci amanata, na d’auka Amintar dake tsakanina da mahaifiyarka zan ri’keka a matsayin d’ana batare da kowa ya san hakan ba , amma kashhh kai d’in butulu ne saleem , Allah ya isa tsakanina da kai Allah ya tsine maka albarka “, da Sauri abeey yayi ‘ko’karin da katar da ita amma saida dada ta ‘karasa tsine masa , dariya ya saki tana nunata da ya tsa “ idan kin tsinemun sai me ? Nace miki sai me ? Tsinuwarki bazata yi mun komai ba “, ta ya kara sakin wata dariyar kafun ya kalli aunty da gabaki d’aya zuba ta gama jika ta “ Kema duk ‘Kulle ‘kullen da kika akai na nasani , hatta zuwa Wajan boka yan da kike akan kina san king na sani , shiyasa na fara huce haushi na akan amrah, kamar yadda nake kwana dake haka nake kwana da ita kamar matata, sannan tun wuri ki fara zuwa wajan Likita ke da karuwar ‘yar ‘yar uwarki sabida dukanku kuna da cuta me karya garkuwar jiki duk da dama Kema lokacin da na auro ki kin gama bin maza , sannan daga karshe ina miki albishir da cewa na dad’e da sakin ki saki uku, boyanka ce tace na cigaba da kwana dake a haka burina zai cika shiysa na ‘kyaleki kika zama karuwata”. Wannan shi ake kira da tashin hankalin da ba’a sa masa rana , ihu aunty ta saka ita kad’ai kafun itama ta fad’i kasa sumammiya , duk da halin azabar da uncle saleem yake ciki hakan be hanashi sakin dariya ba , ran king ba ‘karamin ‘baci yayi ba , be san lokacin da ya kwantar da tahee akan kujera ba tare da dora mata doguwar rigarsa, inda uncle saleem yake ya nufa gadan gadan, da iya duka ‘karfinsa king ya d’aga ya saukewa uncle saleem a fuska take a Wajan hanci da bakin sa ya ‘kara fashewa , a kausashe king ya soma magana “ magana kake akan wancan ‘kungiyar daku ? Yanxu me yayi muku saura ?” Ya fad’a yana nuna masa tvn da zaki ya kunna , gabaki d’aya hankalin kowa ya koma kan tvn hatta Ammey dake Susa maida kallanta tayi kan tvn, uncle saleem ya ganin abunda yake baruwa ya kurma ihu kamar ba na miji ba , bakomai ne yasashi shiga tashin hankali ba yan ‘kungiyarsu da aka kama , abun mamaki kuma gabaki d’ayansu manyan masu fad’a a jine da attajirai,ga kayan tsafinsu gabaki d’aya an ‘Kona , mutane da yawa sun taru akan sai anbasu mutanen su kashe su da kansu, a firgice Ammey ta bud’e baki zatayi magana bakinta ya karka ce ga hannun ta d’aya da ya lankwa’be kamar wacce bata da jini, babu Wanda be shiga rud’ani ba acikin falon, shima uncle saleem cikin azama ya zari bindigar dake jikin wani soja , take a Wajan ya harbe kansa , wani irin shure shure ya somayi abun tsoratar wa gabakinsa da ya soma futar da wani ‘bakin abu me wani wari, ya dad’e yana shure shuren kafun ya dena motsi gabaki d’aya , gawarsa kuma ta soma tsotsewa kamar Wanda ake tsotsewa Jini.

Ammey ma da ta soma wari sai faman burgima take sabida wani irin azaba da take ji a jikinta, kurajen da suka fito Mata sai fashewa suke suna yin wari, da Sauri king ya bara umarnin afutar dasu daga wajan dan ba’karamin warin Ammey take ba kamar matacciyar ja’ba , gabaki d’aya familyn babu Wanda be shiga tashin hankali ba , babu Wanda zai ce tsoran Allah be shigeshi sosai ba musamman irin mutuwar da uncle saleem yayi ga yadda Ammey ta koma itama . Shiru abeey yayi sabida tashin hankali , Dady ne yayi ‘karfin yin magana “ ya kamata abar komai zuwa gobe tunda tare yayi sosai yanxu “, gabaki d’aya naam sukai da zancensa ita zahra tunda taga uncle saleem ya harbe kansa ta ‘buya a bayan yah sha’aban. Gabaki d’aya kowa nufar makwancinsa yayi , oumma hannun zahra kawai ta kama suka tafi, shima zoya da taheer suka nufi part d’insu shida small mom kamar ydda suka zo , sai alokacin aka yayya fawa aunty ruwa , azabure ta farka sai faman kuka take akan uncle saleem ya mayar da auransu tayi nagama. Shima king taheen sa ya d’auka ya bar part d’in gabaki d’aya . Yana zuwa part d’insu ma direct bedroom ya shiga, ko motsi tahee batayi, shinfid’ata yayi akan gadon su , kafun ya cire kayan jikinsa ya saka bathrub , itama taheen saida ya cire mata Komai na jikinta kafun ya d’aiko ruwa ya shafa mata akan fuska , saida yyi hakan sau biyu kafun ta saki ajiyar zuciya, da kuka ta farka shiyasa yayi saurin hugging d’inta “ it’s okay gani a kusa dake , ki dena kukan nan ya isa haka , okay ? “ kanta kawai ta gyad’a masa , be kuma cewa komai ba Sabida yadda ransa yake a da gule, d’aukar ta yayi suka shige toilet, ko da Suka yi Wanda kayan baccinsu suka saka kala d’ala babu Wanda ya nemi abinci a cikinsu, itama be neme taba sai ma hugging d’inta da yayi a jikinsa taya tapping bayanta , tafi 30 minutes kafun bacci ya d’auketa , sai da ya tabbatar baccin ya dauketa sosai kafun ya kwantar da ita agensa yana sauka daga kan gadon, zuciyarsa zafi take masa sosai ga idanuwansa da lokaci d’aya ya juye zuwa kalar ja, jijiyoyin kansa sosai suka fito rud’u rud’u ajikinsa, hannunsa biyu ya tusa cikin gashin kansa , shi kad’ai yasan rad’ad’in da yake ji cikin zuciyarsa. Dafashi da tahee tayi ne yasashi’ko’karin controlling kansa , sosai ta mike zaune tare da hugging d’insa, ahankali ta soma sosa masa gashin kansa kafun ta soma magana “ cry! Cry!kayi kuka ko rad’ad’in zuciyar ka zai ragu”, lumshe idanuwansa da sukayi ja king yayi da zai samu yayi kukan haka yake so, yadda take tapping d’in bayansa ne yashi wasu hawaye sun fara sakko masa , sosai shima yayi hugging d’inta , rana ta farko tsawan shekarun sa tun yana yaro , sai yau yaki kukan na zuwan masa , sosai ya rungumeta a jikin nata yana kuka ko zai samu zuciyarsa ta rage rad’ad’in da yake ji, kusan 10 minutes yana kukan kafin ya soma sauke ajiyar zuciya, gyara musu kwanci ya tahee tayi sosai tare da dora kansa akan kafadunta ahaka bacci ya d’aukesu bayan adduar da tahee tayi musu.

A cikin gida ma kusan hakance ta faru da kowa da kowa , da kyar suka runtsa, Ammey kuwa a part d’inta aka kulle ta zuwa gobe .


Washe gari tunda Suka je masallaci suka ji part d’in Ammey sai faman wari ke Tashi acikinsa irin warin ja’ban nan , umarni abeey da aduba me nene a Wajan , ana shiga aka ga Ammey duk ta kunbura babu alamar ko rai a tattare da ita ga wasu tsutsa da suke futo mata masu shegen wari, rai abace abbey yasa itama a d’auke masa gawarta a gida harsa dady ya taushesa akan babu kyau maida sharri da sharri, duk da abeey beso hakan ba amma ya kasa musawa aminin nasa , amma yace babu abunda ya had’asu dan haka babu wani dallah da zai musu, king ba sam duk dayya akai dashi akan ya sallace yace bazeyi ba sai Dady ne da kanshi ya bad’a umarnin Akira Wanda zasu yi musu kwanka. Sai alokacin suka ga babban tashin hankali dan gabaki d’aya an rasa Wanda zayyiwa su ammey Wanka Sabida wata iriyar ‘katuwar maciji da ya nannad’eta, ita kad’ai macijiyar sai faman saran jikin Ammey take , uncle Salem ma duk yadda akai akan za a yi masa wanka sai abun yaci tura musamman kawarsa da take da zafi kamar karwashi da an Watsa mata ruwa zai tsotse sabida zafin da tayi har hayaki take , sai da aka d’auko kusan mutane uku amma duk abu d’aya , macijiyar da ta nannad’e  jikin Ammey ta ki bari hakan , shima jikin uncle saleem da yake da zafi ya ki bari a ta’basa , babu yadda za’ayi sai dai abunnesu a hakan. A hakan kuwa aka bunnesu batare da ansallace suba sai rami da aka ha’ka aka rufesu.


INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN, ALLAH KA NESANTA MU DAYIN MUMMUNAN KARSHE , ALLAH KASA MUNA CIKIN RAHAMARKA ALFARMAN ANNABI MUHAMMAD( S.A.W). 


Menene anfanin zalinci,ka mutu ranar tashin Allah agaban ubangiji, me zakace masa akan al’ummar da ka cuta , Allah mun tuba , Allah muntuba????.


*****Duk wanda yaji labarin irin mutuwar da su ammey sukai sai jikinsu yayi sanyi ba kad’an ba , hatta manyan mutanan da suke tare da su ammey an wayi gari inda aka ajjesu ya kama da wuta gabaki d’ayan su babu Wanda yayi rai sabida yadda wutar ta’konasu gabaki d’ayansu.


Gabaki d’aya wunin ranar kowa yana part d’insa babu Wanda ya ‘Kela part d’in junansu. Sannan abeey be bu’kaci ganawa da kowa ba har saida akai kwana uku da faruwar abu kafun ya tara kowa da kowa a falon kamar kwana uku da suka wuce , duk Wanda ka gani zakaga jikinsa yayi sanyi ba kad’an ba . Taro abeey ya bud’e da addua , kafun ya soma yin nasiha tare da fad’akarwa. Ya dad’e yana yin nasihar kafun shima dady ya d’ora nasa wa’azin. Suna zaune akai sallama cikin babban falon , da Sauri oumma ta juyo zuwa inda taji maganar, jin muryar da bazata ta’ba mantawa da ita ba , su Alhaji ismail ne suka shigo palourn sai momy da Mimi sai kuma junior da ke ri’ke da ita , gabaki d’ayansu zuba musu ido yan falon sukai musamman junior da suka fi ‘kurawa ido, yadda suka ga ya kwace hannunsa da gudu ya nufi cikin falon ne ya ‘kara d’aurewa kowa kai, inda tahee take ya nufa,lokacin tana gefen king, a tunaninta ita zai rungume sai kowa ya ga ya rungume king, cikin muryarsa ta yara ya fura “ I missed you dad ! Kace mun zaka zo shine baka zo ba kamun wayo ko?”, d’an hancinsa kawai king yaja lokacin da junior yayi king d’insa , da Sauri kuma junior ya juya wajan tahee da ta d’auke fuskarta ita a dole tayi fushi ga mamakin inda junior yasan babansa take , itama hugging d’inta yayi “ I love you mom! “, gabaki d’aya sai kowa ya zuba musu ido sun kasa magana , abbey yayi wa su uncle ismail iso cikin falourn suma , har yanxu kuma idanuwansa suna kan junior da yaji san yaran yashigeshi lokaci d’aya , kowa sai bunsa da kallo yake kwanin ban sha’awa, binsu da kallo junior yayi sai muna ya gaishesu gabaki d’aya kamar wani me hankali, idanuwansa da Suka sauka kan yah moh ya zaro kafun ya taho da gudu yana rungumeshi “ Big dady , na kamaka bazaka ‘kara guduwar mun ba “, shima yah moh rungume junior yayi abunda , dada ce ta kasa yin shiru ta furta “ kuyi mana bayani yadda zamu gane , ni sai nake ganin yarannan kamar tahanuni d’ina yana yaro”, murmushi yah moh ya saki kafun ya nuna mata junior “ dada wannan da kike gani jikankine d’an tahanuni d’inki ne ,” sai gabaki d’aya kowa ya zubawa su king ido cike da farin ciki, abbey murya har rawa take wajan furta “ d’an sa na cikinsa shida tahee?” Ynxu ma amsa musu yayi da eh, wani irin garin cikine ya kama family d’in kowa so yake ya d’aukesa , lokacin da kowa yaji sunansa ba ‘karamun farin ciki Sukai ba oumma har da kwallar ta , itama ummey saida tayi kuka “ yau Allah ya nuna mata jikanta , Aushe raban zataga nata jikin”,  anan ne yah moh ya sanar dasu tun ‘batansa har zuwan tahee da haihuwar junior da kula dasu da familyn uncle ismail sukai, anan shima uncle Ismail yake sanar dasu yadda ya rabu da oumma har ya dawo nemansu ne gansu , da yadda yasamu tahee . Hajiya dada itama Tasha kuka wai taga d’an tahanuninta, ko yanxu ta muku zatayi farinciki. Lokacin da uncle Ismail yace zasu koma abbey yace babu inda zasuje yana da magana da su nan da sati d’aya , sannan alokacin ysa aka gyara musu ‘ban garan da zasu zauna , dan yace babu me tafiya yanzu sai an gama zumunci .



AFTER ONE WEEK


Junior ya zama d’an gari kuma d’an gata idan yau baya hannun ka kanninsa toh zaka gansa a hannun uncle d’insa,kowa sai nuna masa kauna yake , tsakanin su oumma da ummey kuwa wani irin zumunci ne ya shiga tsakaninsu su uku , oummey , momy , sai kuma oummansu tahee, idan ka gansu bazaka ta’bacewa ba ‘yan uwa bane , gabaki d’aya familyn sai suka had’e kansu, tahee , mimi sai zahra da suke kai d’aya suma sai suka had’e kansu kamar wasu yan uwa haka suke mu’a malarsu, su ihsan da Suka girmesu ma suma sun had’a Kansu su uku kamar wasu twins , ilham , sumayya da firdausi, momy ma da mamy suna ynzu suna zaman su cikin lapiya kamar ba kishiyoyi ba . Small mom da mahma suma ba’a magana , kullum tare zaku gansu , ga taheer da zoya ma da kowa yazama sanin sha’kuwarsu.Mazan ma gabaki d’aya sai suka had’e kansu, king , khaleed , sha’aban, yah moh, sai zaki da king ya sanar dasu amatsayin best friend d’inshi dan tun suna yara zaki yake tare da king, tabbas zaki ya cika d’an Halak na gaskiya Dan sosai a da king yake kwadasa amma kwata kwata duk tsawan lokacin da sukai tare be ta’baci masa Amana ba musamman zaki da ya kasance marayane shi, har kuka sai da yayi lokcin da king yace a wannan karan bazai ‘karayin aiki a ‘kar ‘kashinsa , duk da ad’a d’in ba da yaso haka zakine yace shi yafi jin dad’in aiki a ‘kar kashinsa. Iyaye kullum zaka ga suna tare kusan tare suke cin abincin rana da na dare , Abbey , Dady,uncle Ismail, uncle musaddiq ,a cikin sati d’ayan nan kullum zaka gansu a tare. Aunty ma ynxu gabaki d’aya ta zama abun tausayi duk da abbey yasa likita ya dinga kula da lapiyar ta , sosai tayi nadamar abunda tayiwa familyn sannan gabaki d’aya sai da taje ta nemi yafiyar kowa tare da neman alfarmar komawa gida , tayi jinyarta acan, babu Wanda ya musa mata hakan abeey yasa aka mayar da ita can gida tare da d’ora likitan da zai dunga dubata. 


Yau tun dasu abbey suka shiga falour suke tattaunawa duk da babu Wanda yasan abunda suke tattaunawar akai sai yan samarin gidan da suka umarci gani da kuma matan suma . Amma sun ce basa bu’katar iyayen mata da ‘ya’yansu Kawai xasu gana , sudai su ummey babu abunda suke musu sai dariya , mahmace me basu amsa idan tayi wari zasuji. Lokacin da gabaki d’aya suka had’u a falon uncle Ismail ne ya bud’e taro da adduar, kamar kullum akai salati ga annabi muhammad (S.A.W), kafun abeey ya fara maganar da ya had’asu, kallan khaleed da ilham yayi kafun ya soma magana “ kamar yadda kuka sani abubuwa da yawa sun faru mara dad’in ji amma sai dai mu god’ewa Allah(SW.T), sannan kuma kuyi hakuri da d’aga muku bikinku da akayi, kamar yadda akasa a lokacin baya satin da ya wuce za’a d’ora muku aure toh Insha Allahu, nan da kwana shid’a wato asabar ne zuwa za’a d’aura wa gabaki d’aya aure ,” da Sauri suka d’ago suka kalli abeey banda tahee da king , da suke musu dariya , Mimi, zahra , sumayya , firdausi, gabaki d’aya jiki ba ‘kwari suka amsa sa musu, “ kuna da Wanda yake tsayayye?” Ga baki d’ayansu shiru sukai sun kasa bashi amsa , sau biyu yana tanbayarsu amma sun kasa bashi amsa “, murmushi yayi kafin ya mayar da kallansa kan ‘yan mazan, tanbayar da yayiwa matan shi yayi musu, shima sau biyu yana musu tanbayar, d’an sosa kai sha’aban yayi kafun cikin girmamawa ya soma magana “ abbey ni ina da wacce nake amma ban fad’a mata ba har yanxu “, ashsha cewar dadyn zahra, “ wacece haka ? Dole muje mutanbayo maka ita “, kasa d’ago da kansa yayi Sabida kunyar dadyn zahra da yaji “ wacce ita ?” Uncle Ismail ya tanbaya , d’an sosa ‘ke yarsa yayi kafin ya furta “ zahrace “, wata iriyar kunya ce ta kama zahra sai tayi saurin sunkuyar da kanta ‘kasa ko motsi ta kasa yi, murmushi iyayen sukayi gabaki d’ayansu , babu Wanda yayi magana aciki kafin abbey ya ‘karacewa sai kuma wa?d’an d’agowa yah moh yayi kafun ya furta “

Abeey ni fa ina da mata tuntuni” , dariya ce taso kwacewa tahee dan ta ganosa, sai da king shima ya harareta, kamar wani mara gaskiya yah moh shima ya furta “ abeey mimi ce “ , itama Mimi da Sauri ta sunkuyar da fuskarta, nan ma su abeey murmushin su na manya suka saki kafin ya abbey ya ‘kara furta sai kuma wa? Babu Wanda ya ‘kara magana a cikinsu , king ne ya kalli abbey , “ abbey saura zaki, “ da Sauri zaki ya kallesa kafun ya sunkuyar da kansa kasa “ muhammad wacce kakeso a ciki? “ kasa magana zaki yayi sai ma sunkuyar da kansa kasa da yayi sai da abbey ya kara nanata masa maganar kafun ya furta “ sumayyace “ gabaki d’aya iyayen had’a baki Sukai wajan furta Masha Allah, kafun abbey ya kalli firdausi “ jiya iyayen doctor anwar sunzo mun magana akan aurenki? Hope bazaku bamu kunya ba ?” Sun matan sunkuyar da kansu sukai , Allah yayi muku albarka cewar dady da uncle musaddiq, kafun asalla mesu, suna fita sha’aban ya ce zai yi magana da zahra, mimi ma yah moh ne ya kirata, zaki kasa yiwa sumayya magana yayi , sai da king ya had’e masa rai dan gani yake kamar bazata so shiba , a lokacin itama firdaushi doctor anwar ya kirata, daman su khaleed tuni suka wuce , king ma babynsa ya ja , suna shiga part d’insu ya d’auke abarsa.


Bayan kwana uku wace irin soyayya ce ta shiga tsakanin su duk lokacin da basa tare to tabbas suna na nike da waya a kunnansu , biki ya kama saura 3 days a yau ne kuma gabaki d’aya suka kama hanyar zuwa bunkure , koda sukaje sai da tahee da taheer suka sha mamakin canzawar kaka ta bawa Dan ba ‘karamin saurin suka gani ba , gidan ma sosai aka ‘kara masa girma musamman makociyarsu data rasu d’an ya siyar musu da gidan shiyasa gidan ya ‘kara girma sosai , anan ma sai da su kaka tabawa suka nemi yafiyar du tahee , su dada an samu ‘kawa sai faman hirarsu suke su uku, da hajiya kakarsu zahra, suna zaune gabaki d’ayansu wata gurguwar almajiran tazo musu gidan gabaki d’aya abar tausayi matar , tun daga waje da ta manyan motocin da suka tsaya a cikin gidan take ta rusar kuka sai da zaki yace abarta ta shigo cikin gidan kafun sojoji su ‘kyaleta, tana shiga ta fara kuka gabaki d’aya ta kasa magana har saida abbey yayi magana “baiwar Allah lapiya ? Kike wannan kukan ?” Yanxu ma kuka take sosai saida ta d’ago sosai kafun oumma tace Dije ? Dije tana d’agowa taga oumma , yadda ta ga oumma tayi fess abun ta ga Hutu da ta samu ta ‘kara sakin wani kukan tana neman yafiyarsu kafun ta fara basu labarin abunda ya faru da ita . 

    Aushe lokacin da ta bar gidan burni suka shiga ita da ka warta , basu tsaya a ko ina va sai a gidan karuwai dage Garin borno, sosai harka tayiwa Dije ta dad’i Sabida yadda take samun kudi ko damuwa da sa’bawa Allah da take batayi , haka taci gaba da rayuwarta cikin bariki duk wacce ta samu labarin zataje wajan boka, itace gaba gaba wajan kai su, sosai ta samu kudin karuwancinta , ranar da zasuje Niger a hanyar su ta zuwa wajan wani boka yan fashi suka tare musu hanya , gabaki d’aya dukuyarsu saida Suka kwace sannan sukayi musu wani mugun fyad’e mara kyan gani, sauran yan sharholiyarta gabaki d’aya sun mutu sai ita da suka sarewa ‘kafa,gabaki d’aya Dije talaucewa tayi ta koma bata abincin da zataci ma gagararta yake ga cutar cancer da akace tana dasu akan nonuwanta, hakan ya ja aka yanke Mata su gabaki d’aya guda biyu,gashi bata da kudin siyar magani, kusan 2 biyu da suka wuce ta fad’a mummunan yanayinnan sai ayanxu da wani ya temaka ya sata ciki vot din mota , ya shigo da ita garin Kano, duk Wanda yaga Dije yanzu tabbas yasan ba’karamin shiga tashin hankali ta fad’a ba , sai kuka take tana neman tafiyarsu , gabaki d’aya kowa yace ya yafe mata duk da irin mugancin da ta shuka musu, suna cikin wannan yanayin ne wani yaro ya shigo da gudu wai ga wasu yara sun kawo bintalo,  samarin mazan ne suka fita , ganin yadda aka taru sosai yasa sojoji korar mutane, dogon bugun da yake a shinfid’e zaki ya bud’e take wata gawar mace ta fad’o daga ciki, ga idanuwanta da  zuciyar ta da yake a bud’e da Alama ciresu akai daga gangan jikinta. Lokcin da Dije taga kawar bintalo fad’uwa tayi a sume tunda ta farfad’o kuma take kuka akan bintalo ta yafe mata ita tasaka ta cikin wannan mummunar rayuwar, gabaki d’aya babu Wanda be tausaya mata ba duk da irin mugancin da ta tabka ko wa sai alawadai yake da hali irin nata. A haka aka Samu aka sallace bintalo jikin lunkafanin duk Jini ya ‘batashi. Ko da su king zasu koma gida sai da suka barmusu kudi masu mugun yawa , su dada har da karbar number kaka tabawa. Suma su kaka tabawa basu guje Dije ba kamar yadda oumma ta nuna musu Halacci haka suka bawa Dije d’aki guda itama . Sosai ta zama abar tausayi dan ba ‘karamin nadama ta karashiga ba musamman gawar bintalo da tagani.


????????


Yau ya kama asabar kuma ayau ne dubban jama’a suka shaida d’aurin auren Mohammad zayed Al-nahyan da maryam Ismail, sai auran sha’aban Ahmad da amaryarsa zahra kabeer, sai khaleed kabeer da ilham musaddiq, sumayya musaddiq da angonta Mohammad Mohammed, sai kuma amare na karshe firdausi musaddiq da angonta Dr anwar Auwal. Abun burgewa da mamaki duk irin dukiyar da Allah ya basu basuyi wani bidi’a ba acewarsu Albarkar auren suke bu’kata dukda haka sai da su abbey suka had’a msu gagarumar walima tare da kyaututtuka. 




AFTER 3 YEARS


gabaki d’aya familyn su ‘kara haduwa musamman yanxu da suka ‘kara yawa , acikin shekara ukun nan Allah ya ‘kara albarkar tahee da samun twins mace da na miji, macen ansa mata suhaima wato taci sunan ummey ana kiranta da Baby Fayha, namijin kuma da yaci sunan zayed ana kiran sa da Aahil, ynxu junior kuma ya Xama yaya dan yace baby’s din kannensa su dai na ce masa junior, su mimi ma sun Haifi ‘yar su guda d’aya me sunan mahma wato zarmin ana ce mata Haida , sai zahra da ta haihu itama mace aka sa mata sunan dada  ana kiranta da Afra. Zaki ma sun haihu d’a na miji Yasa sunan king wato tahnoon amma ana ce masa little king, shiyasa duk lokcin da kagansu zaka gansu a tare , a yanxu ne kuma firdausi da ilham suke d’auke da ciki suma haihuwa yau ko gobe . Cikin yan shekarun nan kuma taheer ya cika 25 years shiyasa shima akace yana karasa services dinsa za ayi musu aure shida zoyan sa. 


 Haka rayuwar ahalin nan ta cigaba da tafiya cikin farinciki da ‘kaunar juna, lokaci zuwa lokaci kuma suna had’a family meeting inda gabaki d’aya familyn za a had’u koda kuwa baka nan zakayi settling lokacinka.


**** wasu kyawawan yara ne maza biyu sai mata biyu da suke faman yin gudu, matan sai faman kwalla kiran ammu suke cikin hausarsu da bata fitowa sosai , kofar dana ga an bud’e ne yasa na mayar da hankali na kan kofar, wata kyakkyawar budurwace ta fito daga cikin dakin idanuwanta sanye da farin glass , sosai na zaro idanuwana lokacin da naga budurwar, ba kowa bace face tahee da Hutu da kwanciyar hankali ya ‘kara mata wani irin kyau da kwarjini kallan yaran tayi cikin had’e rai , Fayda , Haida ba na hanaku yin guduba, da Sauri suka had’a baki cikin hausarsu “ ammu su yaya Aahil da yaya small king ne suka biyo mu” Daidai lokacin da mazan suma suka ‘karaso kyawawa dasu , suma ba wani Hausa suka iya sosai ba Amma ahaka suke furta “ ammu baza jin maganane “ hararar su tahee tayi , “ su wanne suka taba mun littles dina ?” Da Sauri suka juya kyakkyawan guy din da suka gani ne suka fara ihu da nufarsa a guje suka rungumeshi bakowa bane face king da ya ‘kara kyau har wani ‘kiba da haske sai da yayi, ledojin hannunsa ya mi’ka musu, suna karba suka saka gudu tare da barin falon girgiza kai king yayi kafun ya kalli tahee da take kunbura fuska daman fushi take dashi , yana zuwa ya d’auke ta tare da king d’in goshinta”baby na tana fushi dani? But nasan zata dena “ yana shiga d’aki ya kwantar da ita ya soma yi mata cakulkuli tana dariya, shima dariyr ya somayi kafun lokaci d’aya su canza alakar jakulkulun zuwa wani abu daban.




ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!!!

Komai yayi farko zai yi ‘karshe anan na kawo karshen book dina me suna GIDAN AUNTY.


Ina mika Godiya ta ga Allah SWT da ya kawoni wannan lokacin da rai da lapiya , sannan ina godewa duka my people na gidan aunty da kuke biye dani nagode nagode ! 


Masoyiya ???? all the best a cikin Romeo

Boss bature  ( kurkukun kaddara ).


Mom sajeeda 

Mom sayyid 

Ummu bulun??

Aunty sadiya 

Mom sayyid

Auta


da saura ku da bazaku lissafuba , na gode nagode nagode sosai da sosai .


SEE YOU ALL ON MY NEXT NOVEL ME SUNA IBTISSAM ????????.


Heart you all.




No comments