Breaking News

Gidan Aunty book 2 page 16

 




Page 16


Runtse idanuwanta tahee tayi tana jiran jin fad’uwarta , batayi auneba sai ji tayi ta fad’o jikin mutum, kamshin turaran da bazata ta’ba mantawa ba yana dukan hancinta,’kara runtse idanuwanta tahee tayi , idan mafarki take ma bata so ta farka, a hankali ta soma kiciniyar bud’e idanuwanta da sukai mata nauyi, Daidai lokacin da ruwa me ‘karfi ya fara sakkowa , ita kanta tahee bata san lokacin da ta rungumesa a jikinta ba , tana faman sauke ajiyar zuciya. King kuwa kasa motsi yayi gabaki d’aya sabida yadda zuciyar sa take bugawa da sauri Sauri, shikansa besan dalilin ba , har ynxu kuma be kalli wadda take jikin nasa ba , amma tabbas sai yau zuciyarsa ta motsa, irin motsawar da bata ta’bayi ba sai a kan mutum d’aya sauyin bugun zuciyar ke canzawa . Da Sauri ya hankad’ata baya batare da ya kalli ko fuskarta ba . Adaidai lokacin da ya hankada tahee kuwa bata san lokacin da ta ri’ko rigar jikinsa ba gabaki d’aya Sukai baya zasu fad’i yayi azamar ri’ko ‘kugu ta tare da zuba mata narkankun eyes dinsa za Suka canza kala zuwa ja, gabaki d’aya king ya canza sosai , Hutu da kud’i duk sunbayyana a jikinsa Amma gabaki d’aya fuskarsa babu d’igon murmushi ko alamun ya ta’ba fara’a a rayuwarsa , bin fuskarta ya soma yi da kallo kamar yadda itama ta zuba masa na ta eyes d’in, yarda fuskarta ta nuna alamun tsorone yasa shi lumshe idanuwa tuno fuskar tahee duk lokacin da take cikin tsoro, da Sauri kuma ya ware idanuwansa akan kande da gabaki d’aya hankalinta na kan kallan kyakkyawar fuskarsa, wani gajeran tsaki king yaja da sauri ya d’auke hannun sa a cikinta take a Wajan ta fad’i kasa Sabida yadda kwankwasanta ya bugu sosai har da ‘yar ‘kararta, yadda tayi karan ne yasashi juyawa a Suka ne yana kallanta, amaimakon ya shiga part d’in dada kamar ydda yace musu zai shigo sai kawai ya juya zuwa part d’insa . Yana shiga part d’in gabaki d’aya jijiyoyin kansa suka mimmike kamar yadda ya saba tun lokacin da ta ‘bata , fresh ruwa ya d’auko tare da fito da wani robar magani a jikinsa , tablet uku ya had’a lokaci d’aya ya shanye su tare da jefar da ragowar magungunan, gashin kansa kawai yake cikurkud’awa ,bai san dalili ba , he just need his wife back, lokaci d’aya kuma ransa yayi mugun ‘baci ganin be tsinka wa kowace mari ba ydda ta fad’o jikinsa haka, “ why ! Why ! Why !” Shine abunda king ke furtawa ,sai kuma ya dafe kansa tare da lumshe idanuwansa.


TAHEE 

Ganin yadda yabar wajan yasa hankalin tahee tashi sosai fatanta Allah ya sa yana lapiya , kamar ta bishi taga halin da yake ciki Haka take jin ranta amma babu dama ganin duhu na ‘karayi  , da’kyar ta samu ta lalla’ba ta mike Sabida zafin da ‘kugunta yake mata dan ba ‘karamun buguwa tayi awajan ba, da ‘kyar ta Samu ta Daidai tafiyar, ganin yadda lokaci ya ja haka sosai jikinta da ya bara ‘baci, tana shiga gabaki d’aya suka zuba mata idanuwa, sosai ta tsargu da hakan dan batasan me zatace musu ba , amma amaimakon taga ‘bacin rai wajan ummey sai kyautar murmushi da ta samu , tun kafin tayi magana ummey ta Rigata “ Hala ruwan sama da aka soma yine ya tsayar daku?” Wata ajiyar zuciya Tahee ta sauke da inka kalleta sosai zaka fahimci Hakan , da Sauri kuma ta d’aga musu kai tana sassaita muryarta " wallahi hajiya na fita ne sai zuwa ya somayi sosai shine na d’an tsaya, da ya ragu kuma sai na manta ‘bangaran sai da nayi ta dubawa sannan na gane “, jinjina mata kai ummey tayi “ Ina saratun?” Zatayi magana saratu ta shigo cikin falon itama cikin girmamawa ta gaishe da gabaki d’aya familyn,tare da bawa ummey hakurin rashin zuwanta da wuri, ummey bata ‘kara cewa komai ba ta mayar da hankalinta kan abincin da take ci, “ ina leman da nace ki taho mun dashi ?” Cewar Ammeey tana kallan tahee , sai alokacin tahee ta tuna da leman da ta watsawa Wanda ya bita , cikin d’an rawar jiki tace “ hajiya dan Allah da manzan sa kiyi hakuri , nazo sakkowa daga matattakala shine ‘kafata ta zame ya zube…” ta ‘karasa a hankali ganin wani irin expression d’in kallon da ta samu wajan Ammeey , Ammey bata san lokacin da ta d’aga murya kamar zata sha ‘kota ta furta “ ya zube ? Menene ya zube ? Leman da nace ki rike ne kika zubar ? Kisan kuwa yadda akai na samo wannan maga….” Bata ‘karasaba tayi saurin toshe bakinta ganin ‘baran ‘baramar da take ‘ko’karin tafkawar ganin gabaki d’aya ilahirin falon sun zuba mata ido , sai ta wayance da “ hope baki ji ciwo ba !? Kinsan irin wannan abun sai kina bi a hankali karya ji miki ciwo “, murmushi abeey ya saki ganin yadda Ammeey ke kula da lapiyar kowa na gidan , Sabida juyawr da tayi yasa yan falon basu kula da gibin taba , ummey kuwa idanuwanta ta zuba Ammeey na d’an sakanni kafun ta d’auke eyes d’inta, itama Ammeey kan kujerar ta koma ta zauna ranta na mugun ta farfasa , wannan ce damar ta ta’karshe da ta samu maganin da zata kashe king, sabida ba ‘karamar guba bace da ko tava ka yayi sai yayi maka illah musamman idan Akace wanine yasha a hankali take tsitstsinka jijiyon cikin mutum,ranta yayi mugun ‘baci sai ‘ko’karin wantar da hankalin ta take , so take ciwan bakinta ya ‘kara kwanaki kafun taje wajan bokanya. Wayarsa Abeey ya d’auka tare da danna wani kira kafun ya kara a kunnansa , bansan me nacikin wayar yace masa ba sai amsar da abeey ya basa “ No son, you have to, zan sa akawo maka can side d’inka “, kafun ya kashe kiran , yana kallan ummey “ ku shirya masa abincinsa akai masa part d’insa yanxu. Hakance kuwa ta faru da kanta ummey ta shirya masa tray d’in hakan ya ‘kara ‘kuntata ran ammey sai bun idanuwansu Kawai take da kallo  rai a’bace, ‘yan Matan kuwa kowa sai kakkaucewa yake gudun kar ace shi zai kai abincin dan sunsan tabbas da kun burarran fuska zasu dawo yau ma , gabaki d’aya king ya canza kuskure kadan Kayi masa sai ka gane kuranka a wajansa.kallan sumayya ummey tayi “ sumayya taso ki mi’kawa yayan ku abinci”. Summy kamar zatayi ihu amma badamar yi haka ta kar’bi tray din kamar zatayi kuka, wata dabara ce ta fad’owa summy tayi saurin kallan tahee “ kande d'an zo ki rakani”. Kallan Ammey tahee tayi , taga ta sakar mata ya’ke alamar suje, ajiyar zuciya ta sauke bayan ta kar’bi tray d’in hannun summyn , tunda suka soma tafiya babu Wanda yayi magana a cikin su musamman yadda tahee taji zuciyarta na bugawa da Sauri sauri, Daidai part d’in king sumy ta tsaya tare da nunawa tahee part d’in “ ki shiga ki kai masa abincin sai ki dawo kinji? “, Toh Kawai tahee ta ce mata, sanyi na ratsa zuciyarta , “ zata gansa? Zata ‘kara san yasa cikin idanuwanta?” Gabaki d’aya tanbayoyine suka taru suka tsaya mata a zuciya ganin tana ‘bata lokacine yasa ta nufi dole d’insa a hankali ta tura ‘kofar tashi sannan ta rufuto, a kan kujera ta hangosa dafe dakansa ga idanuwansa da yake a lumshe , ci gaba da kallansa har ta ‘karaso kan center table d’in bayan ta yi sallama a hankali amma ko motsawa baiyi ba , balan tana tasaka ran amsawar tasa, inda yake ta nufa cikin sand’a ganin idanuwansa a kulle, atunaninta ko yayi bacci ne shi yasa batare da tsoro ko fargaba ba ta nufeshi, fuskarta ta Daidai ta da tasa da take a kulle tun daga kan kyakkyawar sumar kansa ta soma bi da kallo har kyakkyawar fuskarsa tasa,ita kanta batasan ya akai ba sai jin hannunta tayi cikin sumar kansa tana sosa masa kan,da Sauri ya bud’e eyes d’insa , lokaci d’aya sukai eye contact da mamaki yake kallanta “ how dare she?” Ita kuma tahee tsorone ya hana ta motsawa ganin tsananin bacin ran dake kwance kan fuskarsa , da Sauri kamar wacce aka tsikala kuma tayi baya zata fad’a kan center d’in cikin azama yajanyota da hannu d’aya , bata fad’a ko ina ba sai kan cinyarsa , ajiyar zuciyar da besan ko ta menene ba yasauke, itama taheen ajiyar zuciya ta sauke daddad’an kamshin turaransa da bazata ta’ba mantawa ba yana ‘kara shigar hanci, a ydda take tana jin yadda zuciyarsa take bugawa da Sauri da Sauri, gabaki d’aya ta shagala hannunta d’aya ta d’ora a Daidai saitin zuciyarsa, cikin raunin murya hawaye na fara sakko mata ta furta “ we missed you so much “, king be san lokacin da ya fincikota yayi wurgi da ida ba , dukda kalamanta sun shiga kunnan sa , cikin azama ya nufeta da shirin tsinka mata mari tayi saurin kulle fuskar tata cike da tsoro, yadda ta tsoratar ne yasa shi tsayawa kallanta , “ why is she behaving like her ? Why ? Me hakan yake nufi ?” Tana ganin ya janye hannunsa ta mi’ke a guje zata gudu ya ri’ko hannunta, tasan tabbas ta tsaya komai zai iya faruwa da azaba ta fincike hannunta saka gudu, jikinsa ba kwari sosai shiysa ta iya fincike hannun ta , gabaki d’aya ‘ko’karin rasa control d’in kansa yayi lokaci guda,  mamakin wacce yarinyar ya soma yi , a tunaninshi aljana ce ma dan yadda ya gani kamar aljanace take masa gizo , da ya kulle idanuwansa yadda ta saka hannunta a saitin zuciyarsa ne yake fad’o masa da lokacin daya d’ora hannunsa a kan kugunta, yanasan ya hukunta koma wacece koda kuwa aljanar ce , amma duk lokacin da yayi yukurin yin hakan , wifey d’inshi ce take masa gizo, why?” Yake tanbayar kansa kafun yasaka both hannayensa cikin gashin kansa yana ya mutsasu. 


Tahee kuwa tana fita sai da ta sassaita nutsuwar ta kafun ta nufi part d’in dada lokacin gabaki d’aya sun kammala cin abinci suna tattaunawa , dining din data ga su mimi suna gyarawa ta ‘karasa wajan, cike da iskanci Mimi ta ‘kurawa tahee kallo kamar tasan fuskantar wani abu, hararar da tahee ta buga wata lokacin da d’aya daga cikin masu aikin ne Yaso saka Mimi dariya amma ta danne tare da d’aga wa tahee gira d’aya , d’auke idanuwanta tahee tayi akan Mimi tasan ta biyewa Mimi zasuyi abunda zai jawo hankalin mutanan gidan ne Wanda ko kad’an bata san hakan ya faru. Sun dad’e sosai a part d’in dada gabaki d’aya yadda bikin ilham da wasu abubuwan suke tattaunawa akai. Sai wajan 11 suka koma part d’insu , har lokacin Ammey bata ‘kara ce mata komai ba , itama taheen bata damu da hakan ba ta nufi makwancinta , sai da ta tabbatar da ta kulle ko ina na dakin kafin ta cire abun fuskarta, tunaninsa abunda ya faru a tsakaninsu ne yai ta kaikawo cikin zuciyar ta, ita kad’ai sai faman sakin murmushi take , jan zoban nanne ya fad’o mata a rai da Sauri ta d’auko shi a inda ta ‘boye tana ‘kara binsa da kallo haka kawai taji zuciyarta bata kwanta da zoban ba, da Sauri ta sallaba ta shiga kitchen bayan ta mayar da face d’inta ,  ashana ta d’auka ta koma dakin nata ganin babu Wanda ya ganta sai faman sakin ajiyar zuciya take , gabaki d’aya windows d’in d’akin ta kulle hatta fanka sai da ta kashe ta yadda iska bazata motsa ba , zoban ta d’auko cike da Bismillah tana kunna masa asha guda d’aya kawai ya soma ci da wuta , ci sosai kamar Wanda ake fesawa kalanzir, abunda yfi bata mamaki ganin yadda tana kunna ashana tun kafin ta kai wajan zoben ya soma ci da wuta sosai , ‘karane ya soma karad’e ko ina na cikin kunnuwanta, me kama da ihu ihu na abun tsoro, lokaci d’aya ‘kofar d’akin ta soma jijjiga kamar zata cire kanta da kanta , windows d’in d’akin ma sosai suka soma jijjiga da ‘karfi, saurin toshe kunnuwanta tahee tayi tana ambatan sunan Allah sosai , ganin duk lokacin da tayi adduar sai zoban nan ya ‘karaci da wuta, tsawan a wanni biyu , har tsawan lokacin kuma kofar d’akin da windows din basu dena jijjigaba ka guru ruwar da take tashi. Lokaci d’aya kuma sai komai ya dakata , ihun ya dena tashi, ‘kofa da windows din ma kamar ba’a ta’basuba, inda zoban yake ta kalla ganin yadda ya koma ‘baki ‘kirin ga wani hayaki da ya soma Tashi daga cikinsa yana ‘bacewa , lokaci d’aya kuma gabaki d’aya zuban ya ‘bace kamar be ta’ba wanzuwa ba awajan. Addua Tahee ta somayi tun tanayi a zuci har ta soma yi a fili tana ‘kara bin ko ina na d’akin da kallo, Ta dad’e tana addua a bakinta kafun bacci ‘barawo ya d’auketa. 


****** Lokacin da tahee take ‘kona zoban nan da yawa akwai mutanan da basu runtsa ba , musamman mutanan da suke da ala’ka da wannan zoban babu Wanda ya runtsa a cikinsu sabida tashin hankali,ko wannansu cike yake da fargabar abunda zai biyo baya , gabaki d’ayansu kasa ha’kura gari ya waye sukai , karfe 3:00am lokcin da kowa na mahalu’ki yana hutawa gabaki d’aya banda masu ala’ka da zoban da suka bayyana cikin falon su kamar kullum a yola , cike da tashin hankali sai faman kururuwar kiran boyankarsu suke tsawan lokaci, amma babu ita babu alamarta , duk da haka basu ha’kura ba suka dunga kiranta cike da tashin hankali, sun dad’e sunayi kafin suji saukar tsawa akansu , gabaki d’aya suka sunkuyar da kansu alamar girmamawa , bata bayyana ba kamar yadda ta sababa sai amon muryarta mara dad’in ji da ya cika ko ina na falon “ tabbas kun aikata babban kuskure da kuka bari zoben nan ya ‘kone , tabbas lokacin tonuwar asirin ko wannan zai fara daga lokacin da zoben ya ‘bata , yanxu komai ya dawo hannunku Amma kusani gabaki d’aya muguntar da kuka dad’e kunayi tun daga yanxu ya fara warwarewa , ta dawo , ta dawo , bazata ta’ba barin kuba , wannan karan a shirye suke , shirin da bazaku ta’ba warwaresaba,na fad’a muku a farko dawowarta kamar tonuwar asirin kune , toh lokaci yazo , lokacin tonan asirin ko wannan ku yayi “, sai kuma ta ‘barke da dariya mara dad’in ji da saurare. ‘D’aya daga cikinsu ne cike da fargaba ya soma magana “ tuba muke , tuba muke “, sai gabaki d’ayansu suma suka d’au ka , wata tsawar ta daka musu , tun farkon shigowarku na sanar da ku abinda zai biyo baya Aduk lokacin da kuka ‘Kona abun aljanu, kutabbata yanxu lokaci yayi sannan cikin zuri’arku zasu dunga shan jini “ ta sake sakin wata dariyar da ya rud’asu gabaki d’aya. Cike da fargaba d’aya daga cikin su ya soma magana “ ya shigabar mu wannan laifin na abar ‘kauna ce da masoyinta “, yimun shiru , ta fad’a kafun ta cigaba “ babu ruwana da matsalar ku , kanku a had’e yake , duk hukuncin da kuka ga dama kuyi mata babu ruwana , sabida itama yanxu lokacin tonan asirinta ne yazo , lokacin sadaukar da jininkune ya fito , hahahhahahahh, hahahahhahaha jinii, jini,jini , aljanun mu suna bu’katar Jininku, ku tabbata kun gyara abunku a tsakanin ku hahahhahaha “, share gumi kawai suke gabaki d’aya sun rasa bakin magana “ amma wacece wannan shegiyar da take ‘ko’karin ‘bata mana shirin mu ?”, yanxu ma dariya bokanyar tasa kafin ta bud’e musu tafukan hannunta, amaimakon suga wacce ta ‘Kona zoban sai haske ya kashe musu idanuwansu gabaki d’aya , har ‘yar rigan kulle ido suke “bansan taba , bansan wacece ba , sabida duk kogin tsafin mu sun kasa ganin fuskarta, kuma bazaku ta’ba sanin ko wacece ba sai ranar da asirin wasunku zai tonu “, tana kai ‘karshen maganarta ta ‘bace ‘bat. 

Gabaki d’ayan su babu Wanda hankalinsa be Tashi ba , ko wannansu duk da fuskokinsu da yake a kulle hakan bazai hana tsantsan tashin hankalin da suke ciki bayyana ba .


WASHE GARI


Kamar kullum kiran sallar asuba ne ya tasheta, hakanan take jin zuciyar ta a sake kamar ancire mata wani dutse me nauyi a ‘kirjinta, ga farincikin ganin masoyinta kuma mijinta da tayi , wani irin dad’i take ji cikin kasan zuciyar ta musamman idan ta tuna abunda ya faru jiya , komai take yi yau zaka ga fuskarta tana sakin murmushi lokaci zuwa lokaci, ko da bata ga fitowar Ammeey ba hakan kwata kwata be dameta ba , damuwarta d’aya ganin har yanxu be shigo part d’in Ammeey ba kamar yadda ya saba , tun d’azu take kallan hanyar shigowa ko zata gansa amma babu shi babu alamarsa , duk da hakan bata karaya sai da ta ‘kara kusan 30 Minutes, nan ma still shiru be shigoba, a sanyaye ta juya har ta kar kwanar d’akinta taji kamshin turaransa ya ratsa mata hanci , da Sauri ta juyo , shi d’inne kuwa , kamar kullum yana sanye cikin ‘kananan kayan yake ‘kara masa kyau da kwarjini, gabaki d’aya ta maida hankalinta kansa shi kad’ai kawai take kallo, shi kansa yaji alamun ana kallansa , a hankali ya d’ago da dara daran eyes d’insa , zuwa inda taji alamar mutum, yana d’agowa idanuwansu ya shiga cikin na juna , gabaki d’aya babu Wanda ya janye idanunsa  daga shi har ita, kallon kallon kawai suke yiwa junansu, shi mamakin da yake me yasa tun da ya ganta nauyin da ya tokare masa ‘kirji ya sauka kamar wata aljana ? “, da hannu d’aya yayi mata alamar tazo, a sanyaye tahee ta nufi inda yake, tana zuwa ta saukar da inanuwanta , kallan yadda ta sunkuyar da kai tayi kafun a hankali ya furta “ Ammey ?” , bakinta har rawa yake wajan furta “ tun safe bata fito ba ,”kanshi kawai yayi nodding a hankali kafun ya sauke ‘kafarsa d’aya dayi crossing , lokaci d’aya ta bugu da wani glass na ado a wajan , tun kafun ya motsa tahee tayi saurin ta’ba kafartasa Tanaso taga inda yaji ciwan kamar zatayi kuka ta ke furta sorry , da mamaki ya ke kallanta kafun ya furta “ are you mad ? How dare you ? “,ya ‘karasa da d’aga hannunsa zai mareta , yadda ta kulle idanuwan hawaye na sauka akan fuskarsa ne ya tuno masa lokacin da tahee ta zuba masa coffee, the same reaction d’in da ya gani yanxu , cikin d’aga murya yake furta “ why ? Why ? Me yasa komai irin nata ? Why ?” Ynxu kam tsorone ya kama tahee , batasan me yasa ba , duk lokacin da tagansa sai ta kasa controlling kanta . Muryar Ammeey ce ta katse mata tunaninta tare da ajiyar zuciya , shi kuwa har yanxu idanuwansa na kan tahee da ta kasa kallansa , kallan tahee , Ammey tayi tare da yi mata alamar ta bar wajan, cikin gudu gudu sauri sauri kuwa tabar wajan . 

Samun waje Ammey tayi ta zauna a gefensa , duk Wanda ya kalleta zai san ko bata da lapiya ko wacce take cikin damuwa Sabida yadda tayi zuru zuru, kallanta king yayi na tsawan 1 minutes kafin ya furta “ Ammey baki da lapiya ?”, da sauri ta girgixa masa kai “ nashiga cikin damuwa ne ganin yadda gabaki d’aya ka canza , kwata kwata baka damu da rayuwar ka ba kamar da hakan yana sani cikin damuwa “, amaimakon ya amsa mata sai kallanta da ya ‘karayi “ the mouth ?”, da Sauri ta toshe bakinta, ranta a mugun ‘bace amma tana ‘ko’karin tannewa , murmushi ta d’an sakar masa “ karka damu son, burgewa nayi na daki hakwarana”, lumshe mata ido yayi a hankali kafun ya furta “karki damu za’ayi fixing d’insu da wasu, anytime you’re ready go and meet doctor maryam zan sa tayi miki cikin sauki “, cike da murya Ammeey ta amsa masa kafin ta ‘kara kallansa “ son kaci abinci kuwa ? Kalli yadda ka ‘kara Ramewa fa ?”

Shiru yayi mata ba tare da ya amsa mata ba , cike da damuwa ta furta“ zansa yanxu kande ta kawo maka , ka tabbata kaci idan ba haka ba bazan samu kwanciyar hankali ba ,” yanxun ma bece mata komai ba sai lumshe mata eyes da yayi “ am going Ammey , ki kula “ , yana kai ‘karshen zancansa ya bar part d’in , da wani irin shu’umin kallo Ammey ta bi bayansa dashi , kafun ta saki wani murmushin da ita kadai ta san ma’anarsa, d’akinta ta shiga bata jima ba ta fito da wani abu a hannunta , batare da ta nemi temakon kowa ba soma girka masa lafiyayyan abinci , kamshi sai tashi yake , tana kammalawa ta ajje a dinning tare da komawa ta d’auko wani abu, warmers din ta bud’e tare da bar bad’a wani abu d’an kad’an a ciki,duk abunda take akan idan tahee dake kallanta daga nesa yadda Ammey bazata ganta ba , da Sauri kuma ta koma d’aki zuciyarta tana bugawa da Sauri Sauri , kwalla kiranta da taje Ammey nayi ne yasa ta saki ajiyar zuciya, da Sauri ta fito tare da karasowa Indai Ammey take , kamar kullum sai da ta gaisheta cike da bar kwanci, kallanta Ammey tayi sosia kafun ta nuna mata trays din, “ part d’in da kukaje jiya kuka kai abincin nan xaki kai and ki tabbata yaci abincin , kinjini ko ?” Kamar da gaske tahee ta zaro ido tana dafe kirjinta “ Ni hajiya ? Kwarankwatsi ballani zaiyi , ki temaka kiyi hakuri “, ajiyar zuciya Ammey ta saki daman abunda take san ji kenan daga bakinta , d’an had’e rai Ammeey tayi kafun ta nuna mata abincin “ maza ki Tashi kikai “ , cike da tsora tahee ta kalli Ammey , cikin zuciyar ta kuwa dariyar Ammeey Kawai take , zata sake ro’kan Ammey ta daka mata tsawa da Sauri tahee ta mi’ke ta nufi dinning , jikin ta sai karkarwa yake ta nufi hanyar part d’in nasa , sai da tayi nisa sosai sannan ta tsaya tana daidaita kanta , a hankali ta bude babbar ‘kofar falon , bakinta d’auke da sallama, sanyin ac da kanshin turaran wutane ya daki hancin sa , gefe guda kuma ga ‘kamshin turaransa da baya fita daga palourn. Babu kowa a cikin falon kai tsaye dinning ta nufa ta ajje tana tuna lokacin da take bashi abinci a baki , gabaki d’aya sai ta zubawa falon idanu tana tuna rayuwar su da sukayi a baya , sai data gama ‘karewa falour kallo, cikin sand’a ta nufi bedroom d’inta na sama , ko tsoron ya zo ya sameta a wajan batayi , tana shiga nan ma d’akin fess yake sai faman tashin ‘kamshi yake , d’akinta yananan kamar yadda  yake , babu a bunda ya canza , nan ma bata tsaya ba , ta nufi d’akin dressing room dinta , tana bin ko ina na wajan da kallo , sai data gama ‘kare masa kallo ko tsoran ya shigo ya same ta a haka batayi , tasan yana part d’in abeey shiyasa gabaki d’aya bata damuba ta kutsa kai cikin toilet d’in , bataji alamun motsin mutum ba , sai ji tayi an fusgo hannunta da ‘karfin gaske , ta bud’e baki zata sa ido taji an toshe mata bakin nata da ‘karfi  anjin ginata da jikin toilet d’in , zaro idanuwanta tayi a kansa ganinsa sanye da towel kawai , da Sauri kuma ta kulle idanuwanta, azuciye ya furta “ bud’e idanuwanki” da sauri kuwa ta bud’e idanuwan, amma bata kallesa ba sai ‘kasa da ta kalla , akau sashe ya furta d’ago ki kalleni, har yanxu ta ‘ki yadda ta kallesa sai jikinta da ya soma rawa ,  da ‘karfi ya furta “ ba dake nake magana ba ?” , kuka tahee ta saka masa tana d’ago da idanuwanta, hawayen da ya gani akan fuskarta ne yasashi kulle idanuwansa “ why ? Me ke shirin faruwa dani ? Me yasa nk ganin aljana me irin behavior d’inki? Why? “ ya furta cikin zuciyar sa , kafun ya matsa baya kad’an yana nuna mata hanyar waje , “ idan na ‘kara ganin me kama da fuskarki, uhmm” be ‘karasa ba ya nuna mata kofar da finger d’insa , da Sauri zata kwasa a guje , santsi ya nemi kayar da iya , cikin azama ya ri’kota yadda ta fad’o jikinsane yasa towel d’in kugunsa kwance wa , jikinta da nasa suka hadu waje d’aya ,a tsorace tahee ta saki ‘kara jikinta gabaki d’aya ya dena motsi alamar ta suma .


Be san me yasa ba , sai kawai ya tsinci kansa da sakin murmushi, murmushin da ya dad’e beyi irin saba , da hannu d’aya ya d’auketa ya fito daga toilet d’in , akan sofa ya ajjeta ya shirya mintuna kad’an ya dawo d’auke da bottle water d’in gabaki d’aya ruwan ya juye mata a jiki a firgice ta farka zata kurma ihu ya daka mata tsawa “ shut up “,yana kai ‘karshen zancen sa ya juya bayar dakin, tunanin abunda ya faru d’azu tayi kafun ta d’auki hannunta d’aya ta mari fuskarta “ why ? Me yasa bana jin magana “, tunanin yadda zata fita ta soma ganin bata da wata hanyar fita , abincin data kawo masa ne ya fad’o mata arai , yanxu idan yaci abinci fa ? “, dukda yadda jikinta yake a ji’ke Hakan be hana ta saka gudu ba , da Sauri Sauri take taka steps, lokacin da ta sakko har ya gama zuba food d’in da zaiji, ganin yana shirin d’aukar spooon ne yasa tayi Sauri kwalla kara da karfi “ No karkaci “, be gama fahimta me take ba kawai sai ganin tahee yayi ta ture tray d’in gabaki d’aya hatta abincin da ya zuwa sai data ‘barar dashi , rai a ‘bace ya d’ago da eyes d’inta, batai aune ba sai saukar marin shi taji a bothside kumatunta, da Sauri ta dafe wajan tana binsa da kallo ganin yadda ransa ya ‘baci, ‘kara d’aga hannu yayi zai mareta sai kuma ya fasa a kausashe ya soma magana “idan na sake ganin ki cikin part d’in nan zakiga abunda zai faru,leave now “, ya daka mata tsawa , ita kanta ta tsorata zata gudu ya tsayar da ita “ washe kwashe miki Wannan trash d’in “, jijjiga masa kai tayi ta nufi haryan kitchen , duk da yayi mamakin yadda akai tasan hanyar kitchen d’in bece komai ba sbida yadda ransa yake a ‘bace , be san dalili ba amma yaji zuciyarsa tana masa ba dad’i, kayan kashe shara tahee ta kwaso tashare Wajan ta goge kamar babu abunda ya zube , komai a nutse take yinsa gabaki d’aya akan idanuwansa yana kula da movement d’inta hawayen ta da suke fitowa ne ya fi komai tsaya masa arai , ko data gama bata kalli indayake ba tayi hanyar fita , “ hey !” , yace mata , jiyowa tayi har yanxu hawayen be dena sauka ma , yadda ta saukar dakai sosai zata baka tausayi , zai yi magana sai kuma ya fasa “ get lose “, da Sauri ta juya tana goge hawayen fuskar tata , ta ‘kasan ido yake kallanta har ta fice , hannunsa ya d’ora akan saitin zuciyarsa , yadda take hawayene ya soma ya dawo masa akai , at the same time yana tuno hawayen tahee d’insa , he don’t know why he feel bad , kamar ya kira ta , but he will never do so, mamakin kansa yake yadda idan tayi abu take d’aga mata ‘kafa , abunda ya faru a toilet ne ya fad’o masa arai da lokacin da ta taho da gudu ta ‘barar da abincin . Abunda ya faru shekarun baya ne ya soma dawo masa kai “ dady no”, shine abunda ya fad’o masa lokacin da tahee ta ‘barar masa da coffee d’insa . Dafe kansa yayi da hannaye biyu sabida yadda yaji kansa ya fara sara masa , gabaki d’aya memories d’inshi shi da tahee na dawo masa cikin brain d’insa.


**** Tahee tana futa ta gyara fuskarta , zuciyar ta bata mata dad’in musamman abincin da taga beci ba , tana tafiya tana tunanin mafita har ta ‘karasa part d’in Ammeey , tana shiga ta tarar da ita a tsaye tana ganin tahee ta ‘karaso inda yake , “ yaci abincin ?” Shine abunda Ammey ta fara tanbayarta , ‘yake tahee ta sakar mata sabida bata cikin mood d’in “ eh hajiya sai da na tabbatar yaji sosai sannan na fito “, murmushi Ammeey ta saki , kafun ta furta “ zaki iya tafiya “, a sanyaye tahee ta koma d’akinta . Gabaki d’aya rinin ranar tunanin yadda ta bar king take , hannu ta tasaka ta shafi face d’inta da ya mara , kamar wata ‘karamar yarinyar ta turo bakinta waje .


********

*************

Yau ya kama Wednesday ,  ayau ne kuma aka kawo lefin ilham , gabaki d’aya mutanan gidan sun shiga busy , kowa yana harkar tar’bar baki musamman abeey da take part din su dada da za’a kawo lefen , tun lokacin da king ya mareta kuma basu ‘kara haduwa ba amma kullum da tunaninsa take tashi , a cikin lokacin da ba’ki suke zuwane kuma mimi ta samu ta bawa tahee sa’kon yah moh , duk da batayi wani mamaki ba ta ydda kayan suka shigo Amma gabaki d’aya sai da ta saka ‘kananan camera a falon Ammey, hatta d’akinta lokacin da asabe ta bata ta kai mata abinci , Allah ya temaketa ta shiga d’akin Ammey ta saka mata sound recorder d’in da yah moh ya basu , d’akin da har yanxu bata ga Ammey ta shiga ba ne kawai bata sawa , hatta wajan sha’katawar Ammey sai da ta saka .  Yau ne kuma take plan d’in yadda zata shiga cikin d’akin da ba mahalu’kin da yake shiga sai Ammey ita kadai. Ganin yadda kowa yayi busy hatta mutanan gidan kowa yana part d’in dada da ummey masu aiki ma sai faman kai kawo suke , da Sauri Mimi ta shigo palour Ammey tana kallan tahee da ke faman jiran ta “ tahee kiyi sauri bamu da time , zan miki gado gadi, bamu da time kiyi sauri ,” jinjina mata kai tahee tayi bayanta d’auki cameras din da sound record ta nufi d’akin tana tava door d’in taji wani irin zafi ya ratsa mata hannu , ‘kara saka hannunta tayi a karo na biyu wani s azaban da ya fi na farko ratsa mata hannu, da Sauri ta ja baya jin yadda hannun yake kamar an ‘Konashi. Lokacin da tahee ta ta’ba kofar nan sai da zuciyar Ammey ta buga , wani matsananciyar tashin hankali ya ziyarceta , mi’kewa tayi dan ta dawo part d’in ta ummey ta tsayar da ita , jitayi kamar ta sha’ke ummey , tarar ba’kin sukai lokaci d’aya , Adaidai lokacin da tahee ta ‘kara ta’ba ‘kofar . Wannnan karan kasa hakuri Ammey tayi ko sauraran ummey batayi , a hau kace ta  fito daga part d’in dada .


“ kiyi sauri tahee bamu da lokaci , kiyi sauri “, jinjina mata kai tahee tayi tare da ‘kara ta’ba kofar, alokacin da ta ta’ba sabida tashin hankali Ammey har fad’uwa kasa tayi a firgice . Runtse idanuwanta tahee tayi tare da furta Bismillah ta bud’e d’akin , tana bud’ewa wata iriyar guguwa ta karad’e d’akin , addua tahee ta soma jin yadda jikinta yasoma d’aukar karkarwa kamar zata rasa kanta , hatta ‘kafarta da ta taka , wani irin zafi ne yake ratsa mata kafafu, adduar datake cikin saurine yasa lokaci d’aya guguwar  ta tsaya , da Sauri tahee ta soma bin d’akin da kallo komai na cikin d’akin jane kamar yadda yah moh ya fad’a musu , jin muryar Mimi na fad’in Kiyi Sauri tahee . Da Sauri ta fara duban inda zata saka cameras din, tayi sa’ar saka recorder din , zata saka camera d’in bata sani ba ta buge wasu abu kamar tangaran , take a Wajan suka fad’i kasa suka fashe , suna fashewa wani irin ba’kin hayaki yafito daga ciki lokaci d’aya kuma suka ‘bace batt , a rude tahee ta ke duba d’akin inda zata saka cameras d’in kamar zata haukace haka take jin kanta sabida azabar zafin da ya fara ratsata ji take kamar ta kurma ihu dan hauka . A lokacin kuwa da ta kurma ihu da babu abunda zai hana tahee ta haukace , wani d’an waje ta samu daga ba kowa ne zai san da wajan ba ta li’ka cameras din , duk dubawarka bazaka san dasu ba .dai dai lokacin da zatafito daga d’akin ‘kafarta ta buge wani abu take a wajan shima ya fashe , still wani ba’kin haya’kine ya karad’e kafin ya ‘bace , sabida yadda ta rud’e bata san lokacin da ‘kafarta ta zame ba Zata fad’i, Adaidai lokacin kuma Ammey ta saka hannu kan handle d’in kofar shigowa falon, tahee batai aune ba sai ji tayi an funcukota da ‘karfi an toshe mata baki ……..



????GIDAN AUNTY????


07041879581

MSS LEE

No comments