Breaking News

Gidan Aunty book 2 page 1

 


BOOK 2 



   NOT EDITED 


Page 1 


UNITED KINGDOM


OXFORD


A guje wata matashiyar budurwa tashigo cikin wani babban falo me shegen kyau, tana faman ‘kwalla kiran “momy ,momy”, shiru ba a amsaba, wata ‘kofa ta nufa bayan ta ajje wata hand bag d’inta meshegen kyau,”Momy,Momy” ta ‘karan ta fad’a da ‘karfi, wata babbar matace da taji wanka material peach colour me  shegen kyau, kyakkyawar budurwar data ke faman ‘kwalla mata kira ta kallah, cikin hausarta da har yanxu bata gama zama a bakinta ba ta furta “ Mimi, Yaushe zakiyi hankaline , bana hanaki wannan guje guje ba?”, a shagwa’be wacce a kira da Mimi ta ‘karaso zata rungume ta , Momy tayi saurin ja baya “ wallahi Mimi ki fita a idona , kinsan halina sarai “, tsayawa Mimin tayi kamar zata sa kuka “ Haba Momy na, kwanana biyu ban ganki ba amma da Alama ke ko missing d’ina bakiyi ba ,” ta’be baki momyn tayi , “ Allah ya shiryamunke “ dariya mimin ta saki tana cewa “Amin” kafun ta ‘kara da “ Momy albishirinki”, murmushi momyn ta saki kafun ta ce mata goro” momy gobe bro zai dawo, already nayi missing d’insa sosai wallahi kamar nayi shekara ban gansaba”,murmushi momy ya saki “ ya fad’a miki kenan, ai kwanda yazo yayi mun maganinki, duk kinbi kin dami kowa ,” kamar wata yarinya fa fara dure ‘kafarta “ Haba momy , gskiya dady ya fi sona , dole na kira sa ma nace ya dawo kafin bro ya dawo ku had’e kanku”, tana karasa kalamanta ta d’auki handbag d’inta tayi sama dagudu, girgiza kai momy tayi kafin a fili ta furta “ Allah ya shiryeki Mimi bansan lokacin da zakiyi hankali ba , har ynxu bakisan kin girma ba”, .


Asama kuwa wani d’aki mimi ta shiga me girman gaske , komai na cikin d’akin pink colour ne , jakar hannunta ta yar a ‘kasa bayan ta d’akko kantamemiyar wayarta , number MY BRO ??da tayi saving da heart tayi dialling, ringing biyu aka d’aga wayar, tun kafin na cikin wayar yayi magana cikin d’aga murya Mimi ta furta “ Bro d’ina nayi missing d’inka and karka manta mun da tsarabata” cikin kamilalliyar murya Wanda ya d’aga kiran yayi sallama batare da ya amsa mata maganganunta ba ,saurin toshe baki Mimi tayi cikin ‘yar dariya ta furta “ Sorry yayana, am really sorry Wa’alaykumussalm “, shiru kawai yayi Mata batare da yace mata komai ba , kamar zatayi kuka ta furta “ Haba mana Yaya nace maka fa am sorry , kayi hakuri kajiiiii , nayi missing d’inka”,a jiyar zuciya ya d’an sauke “Mimi ba kyajii ko, kina so my ‘bata ?”, girgiza masa kai tayi har hawaye ya fara sakko mata a fuska “ kayi hakuri yaya , na rage rashin ji fa,” yanxu ina aiki, okay bye “, ya fad’a tare da hanging kiran, bin wayar tayi da kallo kafun ta rungume wani babban teddy dake kan gadanta shima pink colour , number wata number da tayi saving da dady tayi dialing amma har kusan 2 missed calls ne d’auka ba , ganin be d’aga bane yasa ta saka music tare da ‘Kure karfin Ac d’in dakin.



???????


NIGERIA 


LAGOS


Gabaki d’aya hankalin kowa a tashe yake musamman neman Tahee da akai aka rasa , a d’aya ‘bangaran king ma haryanxu yana cikin COMA d’in da ya fad’a gabaki d’aya Abeey ya raba hankulansa waje daban daban, ga tashin hankalin da Ammey suka shiga na rashin lapiyar king ,ga ‘batan Tahee itama, a wannan karan gabaki d’aya ummey ta cire kawaicinta Sabida ta na tsoran rasa king kamar yadda yadda ta rasa akhiee d’inta, Ammey ma gabaki d’aya abincin ma bata ci dataga wani ya zo kusa da ita zata soma kiran sunan Tahee , Dada gabaki d’aya ta tarar da hankalinta, gefe d’aya ga fargabar farkawar king da akace zai iya farkawa ako Wana lokaci, gabaki d’aya abeey yashiga damuwa.


Gabaki d’aya anzuba matakan tsaro akan binciken inda Tahee take, hatta sojojin da suke guarding d’in gidan saida zaki ya kamasu gabaki d’ayansu sai angama bincike,kaf cikin familyn NAHYAN babu Wanda be shiga tashin hankali ba , hatta Amrah da Basma da sukaji labarin Accident d’in king kamar wasu zautattu haka suka koma , acikin su babu Wanda ya damu da Tahee gabaki d’aya ita da amrah hankalinsu na kan king. Ganin dare ya farayi ne Doctor yasa doctor Arween da tun d’azu yake zaryar duba king ya kebance da Abi duk da Abeey Yasa an boye zancan gudun kar wani ya kara kai masa hari, cikin wani d’aki ne shegen tsaro a ka kai king da ko hannunka ka d’aga akwia masu kallanka ta camera. Cikin girmamawa Doctor Armeeen ya sanar wa Abeey mutum d’aya ake bukata da zai kula da king tunga zama da king tunda har yanxu yana cikin coma , lokacin da Abeey ya sanar da su Ammey cikin zuciyar ta wani d’an iskan dariyar mugunta ta saki kafin ta furta damata tazo, cikin sha’kewar murya kamar mara lafiya Ammeey ta bud’e baki daniyar magana ummey ta rigaka, sosai kallar ummey ta Dakar mata zuciya , ‘kara maimaita maganar ta ummey tayi “ ZAN ZAUNA DASHI”, da mamaki Ammey ta kalli ummey da gabaki d’aya hankalinta baya kanta , murmushi Abeey ya saki dan yaji dad’in maganar ummey batare da ya ja zancen ba ya kalli Dada cikin girmamawa , itama Dadan cewa tayi zata zauna a asibitin , duk yadda Su Abeey sukai da ita akan ta koma tace ba inda zata hakan da tayi kuwa ba ‘karamin ‘kara ba’kanta ran Ameen yayi ba ,’ko’karin danne fushinta kawai take .


Gabaki d’aya Abeey ya bada umarnin akoma gida bayan uban tsaran da aka kuma sawa a asibitin, duk da babu Wanda yasan abunda ya faru a asibitin sai manyan likitoci gabaki d’aya asibitin a nutse take musamman ko ina mutum ya juya zai ga soja har tsoran kuskure suke.


WASHE GARI


Gabaki d’aya kusan yan gidan gabaki d’aya basu runtsaba ,ana idar da sallahr asuba su Abeey suka nufi hospital shi dasu uncle saleem,har lokacin kuma babu labarin inda Tahee take , su uncle saleem sai faman tausar Abeey suke ganin yadda ya shiga damuwa suma a nasu ‘bangaran sosai Suka sa cigiyar Tahee , har lokacin kuma King baya motsi sai wani irin haske da she’ki da fatar jikinsa ta ‘karayi kamar bashi ba. 

Sai da gari ya fara haske ne mutanan gidan suka fara zuwa asibitin wannan karan Ammey bata biyosu ba Sabida yadda take jin zuciyarta , amma kwata kwata bata nuna musu afili ba sai ma ‘karyar zazzabi datayi duk da Abeey yace tazo a duba ta a asibitin taki, A bangaran Abeey ma bece mata komai ba sai umar ta ummey yayi da taje ta huta a gida, tazo turjewa amma kasantuwar bata masa musu yasa ta koma gida ita da su dada wannan karan aka abar su Abeey a d’akin da king yake . Lokacin da Abeey yaga king wasu irin zafafan hawayene suka sakko masa , ga bugun zuciyar sa da take yawaita, abunda ya faru tsawan shekarune ya soma dawo masa musamman idan ya kalli halin da king yake a ciki, ganin yana ‘ko’karin ‘karawa kansa damuwa ne yasa ya fara tasbihi cikin zuciyar sa yana neman za’bin Allah.


Ummey tana shiga part d’inta ta zaro ido sabida ganin wacce batayi tsammaniba, kyakkyawa matashiyar budurwar da a ‘kalla bazata hakura shekara 35 a duniya bace ta d’ago kanta, fatabarakkallah ahsanin khalikin,kyakkyawar matashiyace da Hutu ya gama ratsa gabaki d’aya sassan jikinta, sosai take kama da ummey wani abun nata kuma sak irin na zoya , murmushi ta saki ganin ummey kafun ta taso kamar ‘karamar yarinya ta rungume ummey , cikin wata daddad’ar murya ta furta da yaran larabci ta furta “ ummey na nayi kewarki gabaki d’aya na dunga kira wayar ku ban samu ba, hatta waccan uban fad’in ran number d’insa a kashe yake abunda be ta’ba faruwa ba “wasu zafafan hawaye ne suke ‘ko’karin sakkowa ummey tayi saurin dakatar dasu, cikin murmushin ta da bai kai zuciya ba ta kalli matashiyar budurwar” Samreen Yaushe kika zo , ko sanarwa bakiyi bafa “, murmushi samreen d’in ta saki , tana bud’e hannayenta “ surprise!!! King ne kad’ai yasan da zuwana Sabida nace bazata zan muku ammeey, tunda kun hanani ganin amaryarsa ai ganinan nazo ganinta da kaina , wannan karan sai nayi good 2 month kafun nabar gidannan”, jinjina mata kai ummey tayi cikin katse maganar “ ya kamata ki huta yanxu, Nima ina bu’katar watsa ruwa “ , ta kara she zancanta da barin Wajan. Bin bayanta da kallo samreen tayi,Anya lapiyar ummey kalau kamar akwai abunda yake damunta , musamman da na shigo naga kamar akwai abunda yayi missing, ta fad’a cikin zuciyar ta amma sanin halin ummey yasa bata bita d’akin ba ta nufi nata da yake a gyare kamar ansan da zuwan ta. Har ta kwanta bacci ta farka bata ga ummey ba sosai mamaki ya ‘kara shigarta, kai tsaye bedroom d’in ummey ta nufa , ta d’aga hannu da niyar kwankwasa mata ‘kofa taci abunda ya kusa buga mata zuciya, da sauri ta tura ‘kofar d’akin ummey, ba ummey dake hawaye ba hatta Abeey tashi tsaye sukai ganin yadda hawaye ya ‘bata mata fuska, cikin kuka ta soma magana “ ummey ? Abeey? Meyasa?me yasa zaku ‘boyemun halinda d’an uwana yake? Meyasa ?ummey banaso na rasashi kamar yadda na rasa Akhieee “, ta karasa tana sakin wani saban kukan me ta’ba rai , itama ummey kuka ne ya kwace mata da kyar Abeey ya lallashesu sukai shiru, yana d’akin kiran mahma yashigo wayarsa, ko ba’a fad’a masa ba yasan tana Lagos kuwa , yana d’aga wa abunda ta fad’ane yasa guntun murmushi bayyana a kan fuskarsa kafin ya kalli ummey, “ ki zauna ki huta zuwa anjima sai kuzo da samreen “, ba ummey da akai wa magana ba hatta samreen girgixamasa kai ta soma , “ zamreen tana asibitin yanxu haka “, yana kai karshe be kuma kallansu ba ya bar d’akin sai a sannan ummey ta saki ajiyar zuciya , tun halinda taga d’anta yake a asibiti kawai taji bata yadda da kowa ba shiyasa ta ce zata zauna amma tunda taga mahma taje babu Wanda zai taba mata d’a da yardar Allah, amma ko kadan bata nuna ko a fuska ba, samreen gabaki d’aya tundata zube a kasan bata tashi ba saida ummey ta dawo tausarta da kanta.



********

************


TAHEEE


Tun data bar gidan ta soma gudu, ita kanta bata san ina taka do saba sai lunguna take wucewa ko wahalar tafiyar bata ji, har wajan karfe goma sai lokacin sallah yayi zata tsaya tayi sallahr ta , tana idarwa kuma zata cigaba da tafiya abinta ,sosai ta dunga kutsa layuka tana tafiya tafiya , duk irin cigiyar ta da ‘yan sanda suke har yanxu babu Wanda Allah yasa ya ganta, duk Inda ta kutsa shiga kawai take har tazo wani lungu da yake da mugun duhu, kan wani ‘karamin benci ta zauna tare da buga uban ta gumi , zoban hannunta ta zuba ido kamar tana san tuna wani abu, sai kuma ta ‘kara maida kallanta kan abun hannunta da sai faman walwali yake, da Sauri ta cire zata jefar ko me ta tuna sai kuma ta mayar dashi hannunta tana zuba masa idanuwa, wasu mashayen maza ne suka zo wuce wa gabaki d’ayansu a buge su, d’aya daga cikin sune ya nuna musu Tahee dake zaune kan benci, gabaki d’aya had’a ido sukai, d’aya daga cikinsu har ya fara cire belt d’in jikinsa . Cikin sanda suka fara nufar inda Tahee take da har yanxu hankalinta yana kan abun hannunta,d’aya daga cikinsu ya d’aga hannu daniyar ta bata kawai yaji saukar mari, da Sauri ya dafe kumatunsa cikin azaba, gabaki d’aya kallan tahee sukai amma abun mamaki tana yadda take d’azu ko alamar motsawa batayi ba , d’aya daga cikinsu ne yayi ‘ko’karin taba Tahee yaji wani gigitaccen mari a kumatunsa dama da hagu, shima cikin azaba ya dafe kumatunsa,ganin har yanxu tananan a yadda take yasa d’aya daga cikinsu rugawa a guje yana fad’in “ wallahi babu ruwana aljanace “, suma ragowar matasan daga jin haka suka saka gudu suna fad’in “ Aljanace Aljanace”.



Taheee kuwa ko ajikinta sai ma Tashi da tayi ta ci gaba da tafiya abunta har taji kafarta ta soma yi mata zafi, wani waje ta samu ta zauna duk sanyi ya gama rufeta sai faman karkarwa take , fashewa tayi da kuka tana kankame jikinta, har wajan karfe biyu da rabi Tahee bata runtsaba tafiya kawai take yi ita kadai ga baccin da take ci amma da ta zauna sai ta tashi a firgice ta cigaba da tafiyar ta. Gabaki d’aya gari yayi shiru baka jin hayaniyar komai sai kukan karnuka kowana mahaluki a irin wannan lokacin ya samu makwanci ya kwanta ban da Tahee da ke ta faman tafiya cikin lungu. Daidai tafi wani babban Titi ta had’u da wasu maza uku da mata guda biyu ko wanne hannunsa da makami a jikinsa. Suna ganin Tahee suka nufo inda take basu tsaya bata lokaci ba suka fesa mata wani abu a fuska matan suka kinkimeta sai cikin ba’kar motar da suka faka . A guje suka ja motarsu da mugun tsiya , ta cikin wani jeji sai gaman sharara gudu suke ko tsoran hanya basa yi har gari ya waye suna tafiyar nan , d’aya daga cikin mazan ne ya d’aha wayarsa da take ‘kara , banji me aka ce masa ba sallan Tahee data  kwance yayi “ Eh Boss mun samo yarinya kamar yadda kace, ynxu haka muna cikin niger, zamu kamo hanyar niamey “, ban san me aka ce masa ba sai “ toh oga” da nayi yace yana kashe wayar. Kallan sa d’aya daga cikin matan sukayi “ wizi me oga yace “ Wanda aka kira da wizi ne yaja d’an ‘karamun tsaki , cikin d’aga murya sak d’an daba ya soma magana “ Kunsan halin oga da shegen zumud’i yace duk yanda zamuyi mu’karaso da yarinyar nan kafun gobe , dan haka munti goma na bawa kowa , yaje yayi abunda zeyi mu cigaba da tafiya kunsan muna cika aiki ze bamu kud’in mu”. Hakan kuwa akai gabaki d’aya fita suka cikin motar yayi saura sai Tahee , muntuna goma sha biyar ne ya dawo dasu motar suka cigaba da tafiya cikin jejin , kowa da jakar abuncinsa. 


Karfe 6:30 pm na yammane ya shigo dasu Niamey, anan ma saida sukayi tafiya me Nisan gaske , lokacin yunwa ya farkar da Tahee amma ta kasa motsawa sabida yadda jikinta ya mutu, ga yunwa d’aya cika mata cikin ta. Wani wayar aka yiwa Wizi , basu dad’e suna wayar ba ya kashe kiran tare da kallansu. “ ku Samu waje mara mutane muyi parking , Sabida yanxu su oga xasu karaso su d’auketa “, amsa masa sukai kafin su isa inda babu mutane da yawan, fita wizi yayi daga cikin motar, “ kusaka idanuwanku akanta ynxu zan dawo”, be jira amsarsu ba ya bar wajan, dogon tsaki wata mace taja “ ni Wlh wani lokaci oga wizi haushi yake bani, kalli fa abunda muke d’urawa cikin mu gaskiya ni ma zanje na dawo dan abinci nake bu’kata. Me tukin ne ya tsayar da ita “ amma Baby kinsan halin wizi”, kanta ta d’aga masa tare da barin motar , ita d’ayar da Sauri tabi bayanta, yayi saura maza guda biyu, shima d’ayan kallan drivern yayi “maganar su gaskiya ce kuma kaga babu mutane da yawa wajan, nasan har mu dawo yarinyar nan bata farka ba kawai muma mu bisu dudu du bazamu wuce mun tuna ashirin ba “. Gyada masa kai driver yayi suka fito cikin ikon Allah kuma sai ya manta be kulle motar ba ya barta a bud’e. Mintuna biyar da tafiyarsu tahee ta mike zaune , kallan inda take yayi da sauri ta zabura  ,jikin kofar motar ta soma bubbugawa da karfi, take a Wajan motar ta bud’e , tana ganin ta fito daga cikin motar ta zubawa Wajan kallo , sai kuma ta cigaba da tafiya abunta, cikin wani lungu ta soma tafiya , saida tayi tafiya me shegen Tazara da Inda motar su wizi take kafun ta yanki wata kwanar ta cigaba da tafiya .


Lokacin da su Baby suka dawo ba ‘karamun tashin hankali suka shiga ba lokacin da Suka ga tahee bata cikin motar, cikin tashin hankali suka bazama neman ta  amma gabaki d’aya basu sametaba, lokacin da wizi ya dawo saban rikici yasaka musu kowa hankalinsa a tashe yake musammman Alhajin su da ya fara kiransa a waya Amma ya kasa d’aga wa , cikin mota suka shiga , suka fara yawan neman inda take kafun mutane su ankara dasu .


Akan wani dakali dake kan babban titi tahee ta zauna gabaki d’aya ta galabaita,sai faman lumshe ido take , wata bakar mota da tun dazu take faman wucewa ne tayi parking inda Tahee take a tsaye , wata babbar matace ta fito bayan motar ganin yanda tahee take agalabaice na yasa ta nufeta Amma duyin duniya tahee bata kulasu ba , kama hannunta matar tayi suka shiga motar dan lokaci d’aya taji yarinyarta kwanta mata ga tsoran kada wasu su cutar da ita yasa ta tafi da ita cikin motar ta.


????GIDAN AUNTY ????


07041879581

MSS LEE ??

No comments