Breaking News

Gidan Aunty book 1 page 61-62

 


BOOK 1

Page 61



Tsayawa yayi a inda yake gabaki d’aya hankalinsa ya gama tashi ganin ta da wuka a hannunta, kalaman dazu take ta kara maimaitawa,gyada mata kai yayi shima “ ok zamu rama muma amma bani wukar nan tukunna”, kin bashi wukar tahee tayi saima fashewa da wani saban kukan tayi, jikinshi har rawa yake dan ya gane ba ita kadai ce ba, tsoransa karsu cutar da ita, sunan dazu da ta kira ne ya fado masa kafun ya kalli yanda take faman hada gumi duk da sanyin Ac dake fitowa, bayanta ya kalla kafun ya furta “NONNA”, da sauri ta juya tana sakin wukar hannunta, yana gani ta juya taku biyu yayi ya damki Dan tsan hannunta, kara ta sakar masa sai faman  fusge fusge take ita kadai, wata iriyar gigitacciyar tsawa ya daka mata yana hade fuskarsa kamar bashi ba, “ki nutsu”, ya furta cikin kausashshiyar murya , nutsuwar kuwa tayi tana sun kunyar da kanta, “ ya sunanki “, shiru tayi tana kara sunkuyar dakanta, “karki bari na sake maimaita tawa “, cikin shashsheka ta furta “sunana LOLA”, dan kallanta yayi jin tayi magana da wata iriyar murya”wacece ke , me yasa kika shiga jikin mata ta”, yanxu ma shiru tayi masa, bece komai ba kafun a cikin dan daga murya yayi Bismillah, rawa jikinta ya fara ,” ah ah zanyi magana ka bari dan Allah “ ta fada cikin rikicewa, banza yayi mata kafun ya fara karatun alkuranin, yanxu kam ihu ta sa masa tana rokonsa karya konata, zaunar da ita yayi kan kujera har yanxu hannunsa na rike da nata kafun ya dakko wani bottle water da ke gefensa ya ajje mata a gabanta, da sauri ta saka hannu zata dauka ya matsar da ruwa nesa da ita “ ruwa , ruwa “ ta fara fada , “zakisha”, ya furta , bata jira ba ta amsa masa da Sauri” zan baki ruwa idan kin gama amsamun tanbayoyina, sabanin hakan kuma zan kona kine “, wacece ke, me yasa kika shiga jikin matata”, cikin wata iriyar murya ta fara kuka , “ ba cutar da ita nake ba, te makonta nake, suna san Kasheta ne kamar yanda suka kashe mun ahalina”shiru yayi na yan sakanni kafun cikin kausashshiyar murya ya furta “Menene hadinki da matata, sannan menene alakar ku da matata da zaki shiga jikinta”, ina bata kariyane kamar yanda Nima ta taba temakona a lokacin baya,ni ba muguwa bace, suna harin rayuwar tane”, su wanene” da mugun firgici ta kallesa , zasu kasheta kamar yanda suka kashe shi, bazan iya va”,wani irin rawa jikinta ya fara,”ruwa !!ruwa!!”, ruwan ya dakko kamar yanda ta bukata amma be bata ba,”banasan jin wannan tatsuniyar taki, kar na sake ganin ki a jikin matata, idan va haka ba zan konaki da ayoyin uban giji, ki gaggauta fita daga jikin matata yanxun nan”,kanta ta daga masa tana rike makoqwaranta, ruwan ya mika bata da mugun sauri ta fara sha, saida shanye duka kafin ta fara sakin ajiyar zuciya,”zan fita daga jikinta, Kai ma nagode da yanda kake kular mun da ita,nasan kana kula da ita amma ka nunkashi sabida kokarin kasheta da suke yi, ganin komai nasu ya fara lalacewa,ka kula da ita “, tana gama fadar hakan tahee tayi atshawa me karfin gaske,kafun ta sulale ta fado kan king da yayi saurin tarota, cikin zafin nama ya dauke tare da kaita cikin bedroom, kallan yanda take bacci peacefully yayi, kokarin kawar da tunanin yun kurin kashe masa mata da akace yake, iska ya furzar a hankali kafin ya furta “ it’s a lie”. System dinsa ya dauka bayan ya canza kayan jikin sa, ya jima yana operating a kanta,lokaci zuwa lokaci yana kara dubata duk da yana kusa da ita, kiran sallah la’asar ne ya tayar dashi, kan gadon ya karasa har yanxu bacci take peacefully abinta, goshinta ya danyi pecking kafun ya bar dakin. 


Mintuna 15 da futarsa ta fara motsa idanuwanta  kafun ta budesu gabaki d’aya, mamakine ya kama ganin ta kwance akan gado, wayar da akayi mada da text message ne kawai ya fado kanta, duk yanda zata tuna zuwan ta kan gadon ta kasa, sakkowa tayi daga kan gadon bakinta dauke da addua, agogon dakin ta duba, 4 ta wuce da sauri tashiga toilet kafun ta fito ta kabbara sallah , tana Idarwa azkar dinta tayi kafun ta mike , kara kallan agogo tayi mamakinta har yanxu be dauke ba ganin be dawo gida ba, dan karamun bakinta  ta turo waje kafun ta bar dakin, shima falon shiru alamar ba kowa a ciki,3rd floor ta hau nan ma shiru sai ac da kamshin turaran da ke buso dakin,dacin da bakinta ya somane yasata nufar fridge din data gani, tana budewa kuwa idanuwanta ya sauka kan kayayyakin ciye ciye dake shake a ciki, fiye da saurin fridge din, wani abun ma bata taba ganin saba, strawberry ice cream din data ganine yafi daukar hankali, janyoshi tayi tana sakin wani murmushin jin dadi, waje ta samu akan gado tana shan ice cream din, tana sha tana sakin dariya sabida yanda dadin ke ratsa mata kwakwalwa, idanuwanta ne suka sauka kan wata yar karamar roba dake kan bedside dinsa, ajje Ice creams din tayi tana janyo robar “ANTI DEPRESSANT” shine abunda  aka rubuta jikin robar, har zata mayar sai kuma ta fara karanta abunda ke jikin robar, da wani irin shock ta mike tsaye, tana karanta abunda ke jikin robar, wasu hawayene suka fara sakko mata kawai ta fada kan gadon ta fashe da kuka , saida tayi me isarta kafun ta mike dauke da robar a hannunta, zata bar dakin kenan shikuma yana shigowa da sallama a bakinsa kasa kasa, cikin zuciyarta ta amsa sallamar tasa fuskarta kwata kwata ba fara’a, kallan yanda fuskarta ta dan tashi yayi kafun cikin sauri yayi yunkurun nufar inda take”what’s wrong with my baby”, hannunta d’aya ta nuna masa alamar ya dakata karo na farko a rayuwarta, da wani irin expression yake kallanta, be gama tunani ba ta dago robar drugs din dake hannunta, “ Menene wannan”, ta fada tana zuba masa idanuwanta da suka kara haske sabida kukan da tayi,wani irin harbawa zuciyarsa yayi” sam ya manta daya sha drugs din ya barshi a fili”, cikin dan daga murya kamar ba ita ba ta furta “ maganin Menene wannan kakesha “, kokarin matsota yake ta kara dakatar dashi” please calm down, am sorry I will explain”, bata san lokacin da ta buga robar a ‘kasaba maganin ciki ya zube” me yasa , me yasa , I thought Dagaske kake da kace kana sona, i though da gaske kake da kace kai dady nane, kana shan wancan pills din dukda kasan illar su, u’re a doctor, I thought ka d’auke ni a matsayin matarka, Aushe nayi kuskure ba haka bane, you’re taking this drugs to…. to…”, ta kasa karasa zancan nata sabida wani saban kukan da yake kokarin zuwan mata tana dannewa, wani irin shock ne ya dake shi, jin kukanta yake kamar ana kara cakarshi da maki a zuciya gabaki d’aya ya rikice , cikin sanyin murya ya furta “ please don’t be angry, I will explain “, manyan eyes dinta ta zuba masa hawaye na sauka akan idon nata” bana bukata” kawai ta furta tare da barin dakin, wani irin jirine yaji yana neman kayan dashi yayi saurin samun waje ya zauna , ga baki daya hannayensa ya tusa cikin gashin kansa yana ya mutsasu “ I’m in a big mess , she’s more angry than ever”, ya rasa Wana irin tunani zaiyi , bayaso koka d’an tayi fushi dashi dan bazan iya daukan fushinta ba, da sauri ya mike ya nufi bayanta, yana shiga ya tarar da bata cikin bedroom dinta, ragowar bedroom din second floor ya duba , shima duk bata ciki, muryar da ya fara ji sama sama a falon kasane yasashi nufar falon kai tsaye, TAHEE ce a falon tare da su sumayya da suka zo falon, wani irin ajiyar zuciya ya sauke yana binta da kallo , adaidai lokacin da ta daga idanuwanta itama, tana ganinshi ta d’auke idanuwanta fuskarta a dan hade kadan ta yanda su Ihsan bazasu gane ba.” Oh my god “ ya furta cikin zuciyarsa har yanxu ya masa dauke idanuwansa akanta, su firdausi na ganinshi suka kara gaishe ganin yanxu yana amsa musu gaisuwarsu bakamar daba, kanshi ya dan daga musu alamar amsawa dan kwata kwata ba shi yake bukata ba,so yake ya rungumeta, ya lallasheta ko zata dena fushi dashi, he want to feel her warm , he can’t take it”, satar kallansa ihsan tayi ganin yanda ya tsaya gabaki d’aya hankalinsa na kan tahee dake dannawa waya,murmushi ta saki kafun ta kalli tahee,” sister yau dai bari na cika miki alkawarin Pam cake din ki”, bata jira amsar tahee ba ta mike ta nufi kitchen, firdausi da sumayya ma duk sun ankara dashi dan haka da sauri suma suka mike “muma bari mu tayaki” dukansu basu jira jin amsar taba sukayi saurin guduwa , bece komai dan Hakan yake bukata, ganin ta tashi zata bi bayansu yayi saurin shan gabanta, hannunsa biyu yayi hade alamun pleading, dauke kanta tayi daga kansa zata wuce yayi saurin riko hannunta, fisge hannun tayi kafin ta furta “ don’t touch me again “, tana gama maganarta tayi upstairs, waje ya samu ya zauna kansa na sara masa, gabaki d’aya launin idanuwansa ya canza Sabida yanda yaji xuciyarsa na masa zafi, ya dau tsawan lokaci zaune a kan kujera kamar ya bita amma yana tsoro karta kara wani fushin, ganin lokacin sallah yayi ne yasashi barin part gabaki d’aya .


Aban garan su ihsan kuwa suna shiga cikin kitchen din suka kulle kofar, kwai kwayar yanda suka ga king na kallan tahee suka fara, “wayaga Romeo and juliet “ cewar ihsan , dariya suka saki gabaki d’ayansu, kan kujerun dake kitchen suka zauna suna dasa saban hira , daman space suka basu kar king ya koresu, sun dade suna hira abunsu kafun su fito falo, ganin babu kowa ne yasasu sakin ajiyar zuciya , da Sauri ihsan tayi hanyar kofa ,kallanta sumayya tayi alamun karin bayani” kun manta pan cake mukace zamuyi mata, tana fitowa kara zaunar da mu zatayi , ni kuma ban shirya shan masga ba Wajan yaya”,ga baki daya basu yi wannan tunanin ba, gudun karta fito tazo ta samesu sukayi saurin barin part din. 


Tahee kuwa tana shiga daki wani saban kukan tayi kafun ta shiga ban daki, Wanka tayi ganin ana kiran sallah tayi alwalarta, ta kabbara sallah bata bar daddumar ta ba sai da akayi isha’i, wasu English wears ta saka masu daukar hankali blue colour , cikakken gashin kanta ya sakko har bayanta duk da hular da ta saka, wani irin masifaffen kyau tayi na musamman amma fuskarta har yanxu a cin kushe take, Fararan hannunta da yan yatsunta sun fito fes da masu musamman da kunshin hannunta ya kara fito da farinsu,Daddadan kamshin turaran princess ne ke tashi a cikin dakin ta ko ina, message din data gani akan wayarta ne ya sata sakin baki “ sorry sis karkizo kiga bamanan ummey ce ta kiramu”, ba kowa bane ya tura mata text din face ihsan, hararar wayar tayi kamar suna gabanta,kafin ta fito daga dakinta, karo suka ci da king da gaba daya yanayinsa ya canza, kallo daya tayi masa kafun ta d’auke kanta “ sannu da zuwa “ ta furta zata bar wajan, ya rungumota ta baya yana sakin ajiyar zuciya, cikin disashewar murya kamar mara lapiya ya furta “ I can’t take it any more , please am so sorry, bayanda Kike tunani bane,” raba jikinta tayi da nashi kafun ta furta “ your dinner is ready”, am not hungry, ya furta yana binta da kallo, bata kuma ce masa komai ba tayi wucewarta kan dining, apple ta dauka guda daya ita ma, ta wuce dakinta, zuciyar ta na raya mata ta kallesa amma ta danne, tana barin Wajan ya dafe kansa dake sara masa, tayi masa kyau sosai yau , and he don’t like her frowning face, cikin sanyin jiki ya nufa dakin shima , yana kallan yanda take shan apple dinta cikin kwanciyar hankali, bece mata komai ba yace toilet,ya dade a ciki bayan ruwan sanyin da ya sakar wa kansa, ganin zazzabin nasa na kara yawa ne yasashi kashe ruwan, shima wasu kayan bacci ya dauka white colour masu kauri sabida yanda yake jin sanyi, turare kawai ya fesa  ya fito, yana fitowa yatarar da fitula aka she sai lamp din da aka dan kunna, sai tun zuciyarsa ya rike yana cije lips ,sallar da ya saba yake so yayi amma ya kasa sabida ynda yake jin jikinsa, a tunaninsa tayi bacci ne shiyasa ya na hawa bed din ya janyota jikinsa yana sakin ajiyar zuciya,kara rungumeta yayi kamar wacce za a kwace masa ita, tun lokacin da ya rungumeta ta bude idanuwanta ga zafin jikinsa dake ratsa nata jikin,tausayi ya bata kamar tayi magana sai kuma tayi shiru har bacci ya dauketa, “ am so very sorry “ yake fada a cikin zuciyar sa….


Mss Lee 💖


GIDAN AUNTY 

07041879581


BOOK 1 


Page 62 


Kallan fuskarta dake bacci peacefully yayi kafun ya mayar dashi kan dan karamin bakin ta, lips din ta da sukai jajawur ya zubawa eyes dinsa kafun ya lumshe ido, kara rungumota yayi a jikinsa sabida sanyin da yaji yana ratsa shi, ya dau tsawan lokaci idanuwansa biyu ko alamun bacci bashi da niyar yi, har 2:30 idanuwansa biyu sai da bacci barawo yazo ya daukesa.


Farkon kiran sallahr asuba ne ya tayar da ita, jinta rungume a jikinshine yasa ta dan motsa a hankali tare da zare jikinta cikin nasa. Kyakkyawar fuskarsa ta zuba wa ido, kafun ta saka tafun hannunta akan goshinsa, tazo zata dauke taji ya rike hannun nata yana bude idanuwansa, da Sauri ta kwace hannunta tashiga cikin toilet, kanshi ya dan girgiza kafun ya bar dakin shima.


Tahee na fitowa simple doguwar jiya ta saka me warwar ash colour sosai kayn sukai mata kyau, tana idar da sallah gashin ta da ya ta kura mata ta soma tajewa bayan ta zauna kan stool din gaban mirror din,ta ciki taga shigowarsa dakin, a hankali ta amsa sallamarsa kafin ta jigaba da gyara kan nata, gaban stool din ya karaso shima, zata mike ya Mayar da ita tare da karbar Kum din hannunta batare da yace mata komai ba,a hankali ya gama taje mata kan nata kafun ya daureshi da ash ban din da yagani ,”ina kwana”, yaji saukar muryarta har cikin kunnansa, wani irin dadi ne ya zuyarcesa amaimakon ya amsa mata gaisuwar da tayi hannunta d’aya ya tare da juyo da stool din da take zaune akai, binsa kawai tahee take da kallo ganin kamar bashi da lapiya yau,bata Ankara sai ji tayi king yayi kneeling a gabanta, da wani irin mugun sauri ta sauka daga kan stool din itama zatayi kneeling ya hanata tare da mayar da ita kan stool din, kanshi kawai ya dora a cinyar tahee batare da yace mata komai ba, tunda ya dora kansa take jin zafin kansa na ratsa mata cinyoyi a hankali ta zura hannunta daya cikin gashin kanta ,”dady jikinka da zafi har yanxu, bari na hada maka breakfasts sai kasha magani, shiru be amsa mata ba ,sannan be dauke kanshi daga kan cinyartaba, sosai ta damu da hakan taga zazzabine a jikinsa ga sanyin Acn dakin da yawa kara mura ya kamasa,” dady please ka koma kan gado sai na kashe mata Acn karya saka mura” yanxu ma be amsa mata ba, gaban tane ya fadi tayi sauri saka hannunta a wajan hancinshi “da..dy,dady” ta kira sunansa murya a harde cikin rawa rawa , a hankali ya bude bakinsa kafun ya furta “am sorry please “, hawayenta da suka sauka akan tashi fuskarne yasashi saurin bude idanuwan, bata Ankara ba taji saukar bakinsa akan kumatunta, eyes dinta ta ware masa , cikin sanyi da rauni ta furta “ karka karashan maganin nan dady”, kansa ya daga mata” na dena tun da princess dina ta fushi dani,” ya furta mata a hankali har yanxu muryarsa bata gama daidaitaba, hannunta me zobe ta mika masa,tare da mike wa tsaye,”toh ka tashi mana”, ta fada tana dan turo masa bakin ta, hannun nashi ya mika mata ita a dole zata mikar dashi, tana rike hannun nasa ya janyota jikinsa suka kwanta kan lallausan cafet din wajan me shegen laushi,bakinsa ta tura masa yayi sauri kuwa ya cafkesu ya fara tsotsa, ganin hakan be masa ba ya juyata ta koma kasan sa bakinsa cikin nata, bakin take kokarin kwacewa amma ya ki bata damar Hakan saida ya tsotsa iya yinsa kafun ya janye bakinsa cikin nata da yake ji kamar karya dena shansu, bakin ta kara turowa tana kauda kai, bata ankaraba ta karaji ya bata wani passionate kiss a wajan, “nifa Allah ka bari” ta fada a shagwabe, “you’re making me to add more “ , girgiza masa kanta tayi “Nima kamun nauyi , hanjin cikina zasu iya fitowa fa”, hannunsa daya ya dora kan cikin nata yana shafawa batare da yace mata komai ba ya dauketa ya kwantar kan gado, zai sauka tayi saurin jiki hannunsa “ dady baka da lapiya fa, yanxu zan maka abinci sabida kasha magani”, lumshe mata ido yayi “ dont worry dear, I have important meeting, am sorry please “, kanta kawai ta daga masa tana sun kuyar da kanta” common ni bana san wannan kalan face din,”murmushi ta dan sakar masa tana boye fuskarta ,”oya let’s go , ya kamata matata ta dunga yi mun wanka fa”, ya karasa cikin zolaya, karamin pillow din dake hannunta ta buga masa “ ni kana sani jin kunya “, murmushi ya saki kawai tare da shiga dressing room.


Tana ganin shigarsa tayi saurin sakkowa kasa , tunanin abunda zata hada masa me sauki ta fara, omelets ne ya fado ranta , cikin sauri ta soya masa shi, tare da coffee me zafi da ta hada masa daga saban abun coffeee dinta, bread ma tayi Toasting din shi, kafun ta koma dakin, a gaban Mirror ta tarar dashi yana taje gashin kansa da ya fara tsaho, wani blue din suit ne a jikinsa me kalar sararin samaniya, fadar irin kyau da haduwar da yayi bata baki ne ga wani irin daddadan kamshin turaran sa dake cika mata hanci, hakanan kawai sai taji wani kishi ya kamata , kenan yarda taga kyansa haka wasu zasu gani, har bata san lokacin daya karaso Wajan ba , sai tray din hannunta da taji ya dauka , a jiyar zuciya ta sauke tana bin bayansa “ kayi kyau sosai fa, kuma ni ..” kallanta yayi alamun ta karasa , itama kan kujerar ta zauna “kuma ke Menene “, kanta ta langwasar to ka gama breakfast dinka kasha magani,” sir maa, your wishes is my command my stubborn wife “, bakinta ta turo ganin coffe kawai ya ke sha , fuskantar hakan ysashi fara cikin omelet’s din ganin bata cine yasa shi kallanta” ni bazan sha coffe ba, kuma bazanci kwai ba,sabida ni bazanyi kiba ba”, kallanta yayi kafun ya furta “ you’re looking for my trouble ko”, dariya ta saki bata kuma ce masa komai ba har ya kammala cin abinci,” thank you, I enjoyed the food , but karki dafa komai , I don’t want you to stressed your self”, sakin baki tayi tana kallansa ganin yana kokarin saka suit din saman yasa ta temaka masa , bata san lokacin da ta furta “ suma mata haka zasu ga kyankya in ka fita , ni Allah ban yardaba”, sai kuma tayi saurin rufe bakin ta jin bara baraman da tayi, forehead dinta ya sumbata “ duk Wanda ya kalleni zan ce a harbeshi matata tace kar a kalleni”, murmushinta me kayatarwa ta sakar masa kafun tayi hugging dinsa “ Allah ya baka abunda kaje nema, Allah ya kare ka da kare warsa, Allah ya tsareka daga Sharrin ma sharrata ya dawo dakai lapiya”, so tie ya rungumeta “ thank you, take care of your self, love you” dariya ta saki kafin ta ce “me too” , hancinta ya dan dan gwale mata “you will explain me too din nan, kinsa na makara ko”, gwalo ta danyi masa tare da rakashi har falon kasa, zataje wajan kofa ya hanata,”take care “ ya furta tare da barin part din, ji tayi kamar an cire mata wani abu me nauyi Akan zuciyarta, shaf shaf ta gyara masa ban garansa , tare da naga ban gwaran, kulu na zuwa down stairs kawai ta gyara, ganin babu wani aikin tahee ta sallameta, taliya da manja take sha’awa shiyasa tayi taliyanta da yaji pepper sosai tana gama ci ta dauki wayarta dagata tayi haske alamar message ya shigo “ I LOVE YOU Angel “, murmushi tayi kafun ta bashi amsa da “ LOVE YOU TOO”, wani irin dadi ne taji ya kara kamata, cikin kan kanin lokaci tayi wani wankan kafun ta nufi part din su dada , sun dade suna hira abinci kafun ta shiga part din ummey da ammeey, hatta prt din su ihsan da su sumayya ko wanne sai da tashiga , sunji dadin zuwan nata kuwa, part din aunty ne da ta shiga har ta karaci zaman ta basu fito ba tun bayan fada mata da me aikin ta tayi tace gatanan zuwa, tana ganin lokaci ya ja ta koma part din dada anan suka ci gaba da hirarsu, dada na ganin 6 tayi ta Koreta acewarta mujinta ya kusa dawowa kuma gobe zata fara zuwa makaranta.

 Tana komawa part din ta , turaran wuta ta saka me shegen kamshi, kafin ta sake wani shirin cikin kananun kaya masu shegen kyau da suka fito da ainahin shape din jikinta, abinda zata dafa take tunani message din da ta gani a wayar ne ya dauke mata hankali , wasu irin kalaman soyayya me tsayawa mutum a rai ya turo mata, da ka karshe ya jaddada mata kartayi abinci, ganin hakan yasa ta dakko pop corn dinta , tana ci tana watching wani cartooon da akeyi, white paper din data hangone yasa tayi saurin dakkota, kamar yanda tayi tsammani kuwa, kalmar da aka saba fada mata shi aka kara fada mata yanxu ma , tayi alkawari  ko Wanene yake ajjewa sai ta kamasa, door bell din da aka dan na sau daya ne ysa ta ajje popcorn dinta, ta karaso wajan door din, lekawa tayi kadan ta hangosa ta kashe mata ido d’aya , tana bude kofar yayi saurin shigowa, kafun yayi magana tayi masa wani fari da ido, cikin wani irin salo tayi masa Sannu da zuwa , kasa motsi yayi daga inda yake, ganin hakan yasa ta karbi ledojin hannunsa ta ajje masa, cikin wani irin saban taku daga canza ne daukan hankali, kamar rakumi kuwa haka ya dunga binta har tasa yayi wanka ta tayashi shiryawa, mamaki ne fal ransa surar jikinta sai faman fusgarsa yake yana kokarin sassaita kansa, ledojin ya bude mata , kayan ciye ciye sosai a ciki, tun daga kan pizza, burger , da shawarma sai ice creams da yawa da ice pops , ga uban chocolate da ke ciki kala kala, dayan ledar kuma, Kifi ne manta guda uku gasassu sai ledar kaji gasasshe shima , sakin baki tayi tana kallansa “ dady wannan abincin fa”, Kai tsaye ya bata amsa “it’s for my baby”, rungumeshi tayi da har saida yayi ajiyar zuciya sabida yanda boobs dinta suka taba masa kirji yayi kewar su sosai, kallanshi tayi kafun ta furta “ wanne zan zuba maka a ciki”, na koshi , ya bata amsa dan gabaki d’aya bashi da mood din cin abinci, so yake kawai ya kasance tare da ita , idanuwansa har sun fara sauya kala sabida duk motsi daya da zatayi sai jikinta ya dan motsa, bataci komai ba itama sai ice creams da ice pops din data iba ragowar duk ta sasu a cikin fridges din da yake shake da wasu kayan ciye ciyen, “ yayi sanyi da yawa , you have to eat dan yau zakiji yunwa “, kallan shi tayi da yace zata ji yunwa , bata gane abunda yake nufi ba shiyasa tace masa ta koshi ita, tana shan ice cream dinta tana lumshe idanuwa, lokaci zuwa lokaci tana bashi shima a baki, sai data gama ciye ciyen ta , tace masa zataje tayi brush , Tom kawai yace mata , tana shiga dakinta ya kashe light din kasan tare da barin dum din, TAHEE na cikin yin brush din ya shigo toilet din, ware idanuwa tayi sabida babu komai a jikinta sai karamin towel ganin shi da towel din ma yasa jikinta daukan rawa, zata fita ya hanata gabaki dayanta y dauketa, duk yanda taso ya ravu da ita be kyaletaba saida sukayi wankan tare , wajan sa kaya ma shine ya saka mata kayan da yake so duk da kasancewar komai na jikinta a bayyane yake cikin rigar.suna kwanciya ya kashe light tare da matso da ita jikinsa, jikinsa har ya fara rawa, bata hanashi yin abunda yake so ba, sai ma biye masa da tayi lokacin da yake sumbatarta bata san kara zautar dashi take ba, daga nan zani ya canza salo a zatanta iya romance zai tsaya sai dataji yana adduar saduwa da iyali,ya dade yana biya wa kansa bukata, wannan karan batayi masa rakin da ta saba ba, ta daure sosai ko shi saida yaga bajintarta, bayan komai ya lafa sun yi wanka ne tace masa yunwa takeji, kifin dazu yayi warming tare da feeding dinta a baki da kansa , ganin yanda take rike kwankwasone yasashi fara matsa mata wajan a hankali, a jiyar zuciya kuwa ta fara saukewa dan ba karamin dadin message din take  jiba,da wuri ya sata tayi bacci sabida school dinta gobe . Shima da wurin ya kwanta rungume da ita.



WASHE GARI


Yau ya kasance Monday ,tun bayan sallar asuba tahee bata koma bacci ba , jinta take kamar a cikin sabuwar duniya , ganin yanda take farin ciki hakan yayiwa king dadi, yanxu ma duk yanda yayi da ita taci abinci taki ita ba tajin yunwa , da kyar taci abincin shima dan kadan, kayan uniform dinta take kalla ita kadai sai faman sakin murmushi take,shiryawa tayi cikin uniform din da ya kasance light blue din sararin samaniya sai wani dark blue din skirt shima , daga sama wani irin jacket ne da baya fito da jikin mutum shima dark blue, wani mini hijab ta dakko shima light blue ta saka tare da saka ta kalminta black colour , OMG sakin baki nayi kawai na zuba wa sarautar Allah ido, kyau iya kyau, fadar irin kyau da kayan sukayi mata bata baki ne,ko makiyi yaga kyan da tayi sai ya yaba mata , beret dinta dark blue ta dauka ganin ta kasa saka wa ne ta  nufi dakinsa, ya na zaune d’auke da system ta shiga dakin, tundaga kan kafarta har zuwa kanta yake binta da kallo, wani irin masifaffen kyau me kayatarwa da tafiya da inajin mutum tayi, shikansa kasa d’auke idanuwansa yayi akanta , a gabanshi ta tsaya tana sakar masa murmushi “ dady nayi kyau”, more than kyau , amma am feeling jealous I can’t leave you ki fita haka , sakin baki tayi tana kallansa kafun ta dubi jikinta ganin babu ta inda jikinta ya fito, raurau tayi masa da ido amma ya dage bazata fita haka ba da kyar ya kyaleta shima sai dai kullum face masks a fuskarta, ta yarda da hakan shiyasa wani light blue din facemask ya baka mata kafun ya saka mata beret dinta,” u look more than beautiful, I love you “ murmushi ta sakar masa tana hugging dinshi, “ thank you sweetheart “, say it again “sweetheart “ ta kara maimaita masa, kokarin janyota yake tayi saurin yin baya tana dariya , lokaci ta nuna masa , bece mata komai ba ya bita dakinta, school back dinta da ta kasance black color ta Rataya aban gare d’aya , wata jaka ya mika mata me shegen kyau cikinsa cike yake da kayan kwadayi, “ all the best “, kallanshi tayi alamun bata gane ba kafun ta furta “ ba tare zamuje ba dady”, am sorry Zanzo wataran,I have to go somewhere, take care masu kula dake sunanan nothing will happen to you, and kar ki cire facemask din sai zaki ci abinci , in kin gama sai ki dakko wani a bag dinki kisaka,ok” murmushi ta saki tana daka masa hannu “okay”,suna fitowa wasu jerarrun motoci ta gani she kyalli suke dukansu ba kake, suna ganin king suka sara amsa tare da tahee itama , ita abun dariya ma ya so bata, wata matace ta karaso wajan me dan jiki da shigar suit a jikinta , ta tunana tahee harya “ this way ma’am “ , kallan king tayi ya jinjina mata kai, bye bye tayi masa kafin ta shiga cikin motar, wannan matar ce ta kulle mata motar kafun sukara sarawa king, zasu jira ya basu umarnin tafiya , a hankali motocin suka fara slow, TAHEE na motar tsakiya sauran motocin biyu muma duk bodyguard ne a cikinsu, 17 minutes ne ya kawosu wani kayataccen building JOLAS PRIVATE SCHOOL, abunda aka rubuta da wani irin design, suna zuwa bakin kofar bodyguard daya ne ya fita yayi wa masu tsaron magana kafun a wangale musu baba nan gate din makarantar ,” wow “ tahee take furtawa a kasan zuciyarta sabida haduwar makarantar tun kafin ta shiga, jefi jefi tana ganin wasu masu irin kayanta, tunda kasancewar private school ce da ba ko wana me arziki zai iya sa dansaba sai da motocin su tahee ya dauki hankali wasu daga makarantar, tafiyar mintuna biyu sukayi sukazo wani babban waje da yafi ko ina haduwa, ga wasu mutane kusan su 7 tsaye a wajan, ana tsayar da motar wannan Matar ta bude mata kofa ta sara mata,ga baki d’aya mutanan da zasuyi ‘ya da ita suka karaso wajan suna gaisheta , banbarakwai abun yayi mata musamman wani girma da suke bata, “ you’re highly welcome maah” suka fada tare da dakko wani rose red colour zasu mika mata wannan Matar ta karba saida ta duba ta sannan ta mayr musu suka bata, Godiya tayi musu kafin ta mikawa matar rose din…..



Msss lee 💖

No comments