Breaking News

Gidan Aunty book 1 page 57-58

 


Page 57



Tana idar da sallar isha’i tasaka rigimar bazata kara kwana a dakin ba sai dai ya mayar da ita wajan ammey,yasan abunda take cewa ba mai yuwa bane dan bazai taba yadda ba shima , a hankali ya kama hannunta da take kokarin kwacewa fuskarta a hade ta ki yadda ta kallesa,”am sorry please,ki canzamun wani punishment din amma banda wannan please, I can’t “,kuka ta fashe masa dashi”ai daman ka fadamun bakasona shiyasa kayi kokarin kashe nii, ni dai Allah ka mayar dani”,kwantaccen gashin kansa ya dan shafa kansa har ya fara yi masa ciwo, shi kadan yasan yanda kukanta ke cakarsa har cikin zuciyarsa, har yanzu zazzabinsa be tafiva shima,”look at me”, ya furta a hankali,kin kallansa tayi sai ma kara kawar da kan da tayi, gyada kansa yayi kafun ya taba button din rigarsa “ok shikenan kamar Kari kikeso bari muyi round two”,ba karasa zancan saba tayi saurin rike hannunsa da yake kokarin cire rigar jikinsa,hawaye har sun fara cika mata ido,yanda tayin ne ya so bashi dariya amma ya danne gudun karya kara janyowa kansa wani saban rigimar,a fili kuwa dan tabile bakin sa yayi kadan yana d’auke idanuwansa shima ,marairaice masa fuska tayi ashagwabe ta furta “kace mun fa bazaka kara ba”,be kalletaba ya cigaba da kokarin cirewa “toh yanxu na fasa tunta bakyajin magana “, da sauri ta girgiza masa kai” Allah inajin magana , tsoro nakeji “, yanda ta karasa dinne ya bashi tausayi, kara rike hannunta yayi kafun ya goge mata hawayenta “idan wannan hawayen suka kara sauka toh zanshanye kayana”,da sauri ta goge hawayen nata,”ya ciwonki fa”, kawar da kanta tayi kafun tace masa “Ni lapiya ta kalau”, Tohm shikenan zamu iyayin wani kenan” cewar king ,ynxu ma kanta ta girgiza masa “Allah ban warke ba wajan da zafi,kuma kace mun ka dena fa”, rungumota yayi a jikinsa “ am really sorry zawj, nayi leafi Amin afuwa, kinji, am so sorry “a hankali ta gyada masa kai”banaso ka dena mun kaji”, murmushi ne ya subuce masa a fuska Ba tare da ya amsa mata ba sai dan shafa mata bayanta da yake.”zaki iya tafiya”, kanta ta daga masa alamar eh, mikewa yayi shi yana miko mata hannu “let’s eat something kar ki wanta haka”, a shagwabe ta turo masa bakinta “uhm uhm bana jin yunwa “, lumshe idanuwansa yayi kafun ya kalli bakin nata “ you’re making me to ad more “, ai be kai karshen zancen nasaba ta rufe bakinta ruf,dariya ta so bashi amma ya Waske, taku ta somayi a hankali duk da zafin ya ragu makamar dazu ba, duk yana kallan yanda take tafiyar , da te makonsa suka karasa falon, da kanshi ya ja mata kujera kafun ya soma serving dinta, kadan taci tace ta koshi, be kyaletaba saida ya tabbatar ta koshi sosai kafun su koma ya bata magani.

wajan wanciyama sai da yasha rigimar bazata kwana a dakin ba, saida yace mata ba abunda zai mata sannan ta yadda ya kwanta a gefenta amma taki yarda ya tabata, shima din be tabata har saida yaga tayi bacci kafun ya rungumeta a jikinsa yana kashe gabaki d’aya dum light din. 


➰➰➰➰➰➰➰


Zaune su amrah suke a falon Ammeey gabaki d’aya yan matan su ke su 5, ihsan, sumayya, firdausi,amrah da basma , kowa yana sabgar gabansa, su ihsan suna zaune kan carfet din Ammeey lokacin ta tafi part din data, suna shan fruit jifa jifa suna hira, amrah na kwance kan 3 sitter , basma kuma na zaune kan 1 sitter kafa daya kan daya yayinda take latsa babbar wayarta sai faman ya tsine take, cikin da rigar da sumayya take dannewa ta dan kallesu kafun ta kashewa su firdausi ido d’aya da dan karfi ta soma magana “ Nifa yau banga sis tahee ba, ko da mukaje part din ta kinga yaya king yace mana bacci take ,Anya kuwa su yaya bari dai nayi shiru,” kyalkyalewa da dariya sukayi jin iskancin da sumayya take wa su amrah dan sunsan halinta , itama firdausi dariyar take dannewa” uhm ke dai bari , a yan kwanakin nan da muke zuwa part din ai kinga baya hade mana rai kamar da yanxu fa har gaisuwar mu yake amsawa amma da dane ai bamu isaba,” wata dariyar suka kuma saki , ihsan sai satar kallansu basma take da suka cika fam , daga karshema basma mikewa tayi tare da barin part din ba tare da ta tanka musu ba, amrah kuwa  harara ta dunga sakar musu, tayi alkawari kuwa sai ta haddasa musu wutar da bazasu iya kashewa ba,tunanin abunda zata musu take kafun ta dan saki murmushin mugunta tana barin wajan ba tare da tace musu uffan ba suma . Suna ganin ta bar wajan suka tafa gabaki dayan su , ihsance ta soma magana “wallahi bamu da mutumci, kun iya tsiya, ku kalli yanda fuskar su tayi kamar wanda aka fadawa mummunan abu”, itama firdausi dora tayi “ rabu da yan iska wai su soyayya , in banda ma iskanci irin nasu su kalli kamar yaya king suce wai sai sun aureshi ko da bala’I ai suma sun kwasowa dala da ganmu”, dan murmushi sumayya ta saki” Aah feedy, so sone fa, Kema kinsani duk Wanda ya kalli zubin yaya king ,ko baya sansa sai yaji wani abu aransa ,musamman idan aka samu marasa tsoran Allah, ko ni kunsani naso yaya king kamar raina tun bansan Menene so ba, har zuwan amrah muka fara samun sabani akan shi, amma yanxu na hakura dashi har abada Sabida yayi mana nisa nesa ba kusa ba , ku duba ku gani fa wa ya taba kawowa zai auri sister , duk da irin abunda mukayi mata bata kullacemuba lokacin da mukaje mata, gaskiya masu irin halin sister kadan ne”, jinjina kai sukayi gabaki d’ayansu kufun ihsan ta furta “ Allah sarki AKHII Allah ya jikanka da rahma, har na tuna lokacin da idan yaya king zai hukunta mu zai hana sa , ko uktiii ta hanashi, ban taba sani yana jin maganar su ba sai lokacin da mukai masa lefi akhiii moha ya bashi hakuri shi da ukhti, sai gashi kuwa beyi mana komai ba , da Yaya kabeer ne ko yaya haroon ina tunanin rugu rugu za suyi mana , duk da suma suna tsoran yaya king sosai kamar sunga mala’ika “,gabaki dayan su saida suka shiga jimamin mutuwar akhiiii kafun kuma su fara bada labarin laifikan da suke yake tema kar su da Wanda king yake Zanesu ukhti ke cecensa.” Ku naji fa Ance sun kusa dawowa suma duk da sun makale a turai sunki dawowa gida ,amma naji ance boss yace su dawo nan da one week kafun ransu ya baci” dariya suka sani kin yanda feedy ta kira king da boss, “itama ukhti fa taji anacewa zatazo tunda batazo bikin yaya king ba , ni har na matsu tazo dan nasan dole ko yayane sai anyi mana dinner indai taso kuma yaya king nasan zai amince ko sabo da ita ne”, gabaki dayan su kuwa jin hakan sai suka fara tsara yanda abun zai kasance duk da basu da tabbacin hakan, sunayi suna dariyar kansu musamman in suka tuno yanda king zai ci ubansu.



➰➰➰➰➰

➰➰➰➰➰➰➰


PART DIN DADA 


Ga baki d’aya manyan iyaye ne zaune a falon dada , shiru ko wannansu yayi yana sauraran dada, saida ta kai aya kafun abeey cikin girmamawa ta amsa mata” dada Insha Allahu nan da sati d’aya zasu dawo kamar yanda kikai magana akai, sauran yaran ma insha Allahu zasuyi Auran lokaci ne kawai beyi ba”sallallami dada ta saki” zayeedu,lokaci ne kace beyi bafa , ko dai Bakuyi niyar aurar dazu yanxu ba, Ance zankada zankadan yaya haka babu aure , da alokacin mune ai sai ace baki akai musu , mu duk wacce tayi girman haka ai bazata auru ba, ni dai nagaji inasan ganin jikokina suna zagayeni, Allah ya ji kanka mahamuda Allah ya gafarta maka nasan da kana raye da tuni na fara ganin yan jikokina”, tana kai karshen zancenta ta fara goge hawayen da suke kokarin fitowa, gabaki d’aya sai da tasa jikin kowa na falon yayi sanyi musamman Wanda ta anbata da kowa bazai taba mantashi ba a cikin rayuwar sa, lallashinta suka fara gabi dayansu,kowa yana tofa albarkacin bakinsa. Allah sarki ummey tun lokacin da aka anbato moha jikinta yayi sanyi , addua ta fara masa cikin zuciyar ta , tana kokarin dannewa, amma duk yanda taso boyewan sai da abeey ya ganota, yayi shiru ne kawai bece komai ba dan shima abun yana taba masa zuciya har yanxu.sai da aka gama tattauna na tsawan lokaci kafun mahma ta kalli dada ,toh dada kingama anbato kowa zaiyi aure bamuji naki ba,wani babban salati kaka ta dauka tana kallan mahma da kananan idanuwanta “yanxu auta da yake kin mayar dani kakarkii ni zaki kalla kice na kara aure , toh Allah ya shiryeki dan nasan yanxu ina bude baki masu yan uwa zasu tarar miki” murmushi kowa ya saki dan kowa yasan da su uncle saleem yake , dukda haka kuwa sai da ya tanka,”wannan haqqun ne dada duk Wanda ya taba auta zamu shigar masa “, dan ta bile baki dada tayi tana mikewa tsaye “ daga kai har itan sai na Hana na ci muku mutunci sai naga me shigar muku, ni kunga tafiya ta bacci zanje nayi ma” gabaki dayansu seda fase sukai mata har ta bar part din kafin su dan tattauna gabaki dayan su, ana gamawa kuma kowa ya ya wuce part din da zashi.


➰➰➰➰➰➰

➰➰➰➰➰➰➰

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧


Yau ya kasance Friday kamar kullum kiran sallah azubane ya tashesa, yanxun ma hakan ce ta faru a hankali ya bude fararan idanuwansa da suka kara yin haske dasu gwanin sha’awa, kallan yanda take rungume a jikinsa yayi, yana san mikewa amma bayasan tashinta, gudun kar lokacin sallah ya wuce shi yashi raba jikinta da nashi kadan yana gara mata kwanciyar tata, Dan ya mutsa fuskarta tayi bakinta ature,”stubborn , kina baccin ma bazaki hakura ba”.


Wanka yayi jikin brown din jallabiya da ta kara haska kalar fatar jikinsa , gashin kansa a kwance kamar na larabawa ya nadawa rawanin irin nadin larabawa, duk da fuskarsa ba a sake take ba amma wani irin annuri da annashuwane akan fuskartasa da ya kara wa fuskar tsa kwarjini da haiba, gabaki d’aya kamshin turarensa ma imperial majesty ya cika ko ina, hatta tahee dake kwance lafe kan gadon tana shakar kamshin turaren har cikin ranta.tun motsa warsa ta farko ta farka itama amma taki motsawa , yanxu ma tunanin yanda zata tashi take yi , fatanta d’aya Allah karyace yau ma a dakin zaiyi sallah. Yana kallan motsinta tun dazu yasan ta farka , karasawa yayi inda take kafun ya sunkuyo kadan yayi pecking kumatunta, ai kuwa da sauri ta ware idanuwanta akansa , dan Jan hancinta yayi kadan kafun ya furta “morning “,ya karasa yana tayata mikewa zaune, a hankali ta zuro kafafuwanta kafun ta mike tsaye, tana mikewa kuma ai ta koma tana rintse idanuwanta, ganin hakan yasashi saurin kamata” let’s me help you “, girgiza masa kai tayi,”zan iya, gashican ana kiran sallah kar jam’i ya wuce ka”,ta karasa tana kara mikewa kafun ta soma tafiya a hankali duk da yanda take kokarin daidaita tafiyarta,kallan kafar yayi kafun ya furta “ I have to check it again”, yana ganin shigewarta toilet din ya bar dakin bayan dan jotting din da ya bar mata a cikin wat small paper da wayarta a gefe. A toilet kuwa daurewa tahee tayi ta gasa jikinta sosai kamar yanda taga yayi mata kafun tayi wanka da alwala, sosai taji dadin jikinta kuwa, wani pink material mara nauyi ta saka a jikinta tare da feshe ilahirin jikinta da daddad’an imperial majesty me shegen kamshi, a hankali take yin komai , har ta idar da sallah tayi karatunta kafun , a hankali ta sake mikewa ta koma kan gadon, yar paper din data ganine yafi Jan hankalinta,tana daga gawa taga wani hadaddan handwriting me shegen kyau” take care of your self , I love you “, shine abunda ke jikin paper , bata san lokacin da ta fara murmushi ba ita kadai, rike paper tayi a hannunta kafun ta kwanta baccin da take ji na fusgarta, tun tana Hana kanta bacci har yazo ya dauketa gabaki d’aya .



****Yana shigowa ya tarar da ita kwance lullube da bargo ga kamshin turaransa da ya cika dakin sosai, doso inda take yayi yana kara jin kamshin turaran na kara karfi alamar Itace ta saka , yana sunkuyowa kuwa ga daki hancinsa, kwanciyarta ya gyara mata kafun yayi mata peck a goshinta. A maimakon ya koma bacci system dinsa ya dauka ya fara operating, ya dade akai kafun ya je ya dakko coffe dinsa , har zai kai baki ya tuna lokacin da barar da shayin tana cewa da akwai guba aciki, kawar da coffee din yayi ba tare da yasha ba, kiran wayar sa da akai ne ya dauka ganin me kiran, a hankali yayi sallama, kafun ya dan saki murmushi jin abinda taci kin wayar kecewa, ukhtii ya kike, banji amsar data bashi ba , sai dan murmushin gefen fuska da yayi kadan, sun dade suna tattauna a wayar kafun ya ajje wayar ga ba d’aya , aikin da yake a cikin system dinsa ya cigaba dayi har wajan 11 , har lokacin kuwa tahee na bacci. 


11 :30 am ta fara mutsi mutsi da ido kafun ta bude idanuwan gabaki d’aya cikin hasken dakin, a hankali ta mike zaune babu kowa a dakin sai system dinsa da daya daga cikin wayoyinsa da ke wajan. Mikewa tayi da niyar yin wani wankan da brush taga wayarsa na haske kamar ana kira, sharewa tayi kamar zata wuce taga ta karayi, cikin karan bani ta dauki wayar tasa da niyar kaimasa,message din da aka turo masa ne ya dan dauki hankalinta, bata san lokacin data fara karantawa ba “SWEETHEART NAJIKA SHIRU,BAYAN KACEMUN KAYI MISSING”. saura kadan wayar hannunta ta fadi cikin karo da message din da tayi, a Daidai lokacin da yake shigowa cikin dakin hannunsa dauke da plate.

Mss Lee 💖

07041879581.


58

Kallo d’aya tayi masa ta dauke kanta, a Daidai lokacin da wani message din ya sake shigowa, dan kallan Rubutun da akasawa baby da yar love a jiki tayi kafun tayi saurin d’auke kanta , batasan lokacin da ta jefa wayar kan sofa ba tayi shigewarta , kallan fuskarta yayi yaga ta dauke kanta gabaki d’aya,mamakin abunda tayi yanxu yayi kafun shima yadan fuske ya zauna kan sofa din, wayar da ta jefa a wajan ya kalla daidai lokacin da saban message ya kara shigowa, kamar zai share sai kuma ya dauki wayar, eyes dinsa ya dan ware kadan kan screen din wayar yayi kafun yayi saurin kallan kofar da tashige, maida kallansa yayi kan wayartasa, messages din dazu yagani da private number, alamu ya nuna ankalli message din sai wanda aka turo na ukun “Baby”, ya nanata a kasan zuciyarsa kafun ya saka hannunsa d’aya cikin sumar gashin kansa,” oh my god ,kenan wannan message din ta gani yanxu”,duk da kasancewar private number ce amma sai da number ta fito kan wayarsa , lips dinsa na kasa kawai yake dan taunawa time to time, sosai wani bacin rai ya bayyana a kan fuskarsa, ransa ba karamun baci yayi ba a zafafe yayi dialing wani number , ringing biyu aka daga kiran kuwa, ko amsa gaisuwar da na wayar yake masa Beba sai ma umarni da ya bada cikin kausashashshiyar murya” na baka daga nan zuwa lokaci kadan ka binciko mun wata number yanxun, koma wanene akawomun ita ko shi immediately “

“, kitt ya kashe kiran batare da yace komai ba sai forwarding din number da yayi, wani irin huci yake futar wa shi kadai, bayasan binta ciki, shiyasa ya zauna ,yanaso kawai ya kalli fuskarta , yanda ta bar wajan kuma har yanxu yana jinsa, wani irin bugawa zuciyarsa take, tsawan lokaci yana jirin fitowarta , ganin bata da alamar fitowane yasashi nufar kofar shima.


****Aban garan tahee kuwa tana shiga ciki ta fashe da wani saban kuka me cin rai, kuka take sosai kamar wacce akace wani abu ya sameta, ita kanta bazata iyacewa ga dalilin kukan nata , sai wani abu da takeji ya tsaya mata a makoshi, a hankali ta furta “ Baby ko,har da wani sweetheart , sai yaje su karata ai, har da wani nayi missing dinka”, dan karamin tsaki taja cikin bacin rai ta goge hawayenta, launin idanuwanta har sun canza daga launin fari zuwa ja , Wanka tashiga shaf shaf ba dadewa ta fito fuskarta kwata kwata babu annuri, gefe d’aya na wajan wardrobe dinsu ta bude take a wajan kayan Sawarta suka fito reras dasu gwanin ban sha’awa , a hankali take takawa Sabida har yanxu ciwan ta be gama warkewa ba,shiryawa tayi cikin doguwar rigar abaya me milk colour me kamar bazar bazar , sosai abayar ta zauna mata ajiki duk da bata kamata ba, babu abunda ta shafa sai dan mai da lipstick a bakinta kadan, wani mountain din turare ta fesa a cikinta kadan, take wajan ya bade da kamshin turaran, cikakken lallausan gashin kanta da ya kara rinewa baki sak ta fara tajewa a hankali, har yanxu ranta ba dadi musamman I missed you din da ya fi komai tsaya mata a rai. Tana cikin taje kan ya shigo dakin amma ko saudaya bata dago ta kallesa sai ma cigaba da abunda take takeyi,a hankali ya tunkaro inda take, tana gani yazo daf da ita ta ajje coom din hannunta zata bar wajan, hannu d’aya yasa ya tsayar da ita, kin kallansa tayi sai ma kokarin kwace hannunta dake yi, “why all this please “, ya furta a hankali, a kufule ta kallesa cikin jin haushin maganarsa ta furta” your sweetheart is waiting for you, so please leave me alone ka tafi wajanta”, kallan dan karamin bakinta yayi,kafun wani dan murmushi ya subuce masa a saman labba, wani haushin ne ya kara kamata, tayi kokarin fusgar hannunta amma ta kasa, matso da fuskarsa yayi Daidai tata yana bin kyakkyawar fuskarta da kallo” toh ai gani a gaban ta, me yayi saura”, bata san lokacin da ta zuba mishi idanuwanta kafun tayi nasarar kwace hannunta, kara riko hannun ta yayi tare da rungumota jikinsa, turaren jikinta dake ta shin kamshi ya fara shinshina,a tsorace take kallansa duk da haushin sa da take ji,”kina kishinta ne “,kara kuluwa tayi da maganarsa a zuciye ta furta “akan me zan yi kishi,karshe sai ka dawo da ina kusa  da kai ai sai kuyi karshen soyayya”, ita kanta bata san lokacin da bakinta ya furta hakan ba, a zafafe ya daka mata tsawa” are you mad , ni kike fada wa haka, are you on your senses,”sosai ta tsorata da yanayinsa, ganin yanda ya har zuko mata ne yasata fashewa da kuka, duk da yanda kukanta ke sukan zuciyarsa haka y daure bata re da yace mata komai ba ya bar wajan dakin gabaki d’aya , zubewa a kasa tahee tayi tana kara fashewa da wani kukan , kamar wacce aka tsikara kuwa ta mike tsaye tare da goge hawayenta, fuskarta tawanko tare da gyara fuskarta , mayafin abayar ta yana akanta a matsayin dan kwali bayan ta tufke kan da kyar, wani turaren ta kara fesawa kadan kafun ta bar dakin itama. Zaune ta samesa kan d’aya daga cikin sofa din dakin idanuwansa a lumshe, wuceshi tazoyi itama fuska ba fara’a taji saukar muryarsa “ come back here , dawo ki zauna “ ya karasa zancan cikin sanyi kamar bashi ba, wajan da ya nuna matan ta koma ta zauna, a hankali ya bude idanuwansa, kallan yanda fuskarta take ba walwala yayi kafun ya dan sun kuyar da kansa , abincin da ya zo mata dashi ya dan iba ya kai bakinta, ba musu kuwa ta bude bakin, a hankali ya soma bata a baki har saida yaga ta koshi tukunna ya kyaleta,”nagode “ kawai tace tana kokarin barin wajan ya kamo hannun ta cikin nasa” please stop it, zuciya ta ba dadi”dan sunkuyar da kanta tayi kasa ba tare da tace komai ba” I don’t like it, inason naga daughter dina tada ba wannan va,inasan wacce takewa daddy wasa , take masa hira,take rungumesa,inasan ganin wannan smile din na fuskarta,musamman idan zata kirani dady,I need the old you,zuciya ta ba dadi,anytime na bata miki rai , tell me , ki fada mun, kinji”, maganarsa ta dan sanyaya mata zuciya , kanta ta daga masa kawai , “are you jealous “,kin bashi amsa tayi sai kokarin mikewa datayi ya mayar da ita” tell me are you jealous “bakinta ta turo kadan kasa kasa ta furta harda wani cewa baby, murmushi ne ya bayyana a fuskarsa kafun ya dan ja hancinta kadan yana rungumeta,” my jealousy wife,Nima ban santa ba and karkisa hakan aranki,sabida ke kadai ce a zuciyar TAHNOON zayed al_nahyan”,kafun ya raba jikinsa da nata”you look so beautiful,har da wani kumatu kika kara sai kace ne yaya biyu a ciki”, kunyar maganarsa taji kafun ta dan kallesa ,”inaso naje na gaishe dasu Ammeey “, ta fada a marairaice, hancinta ya karaja kafun yayi mata peck din daya sa ta dan lumshe idanuwanta,”as you wishes, amma ba yanxu ba sai na dawo daga masallaci,okay”, gyada masa kai tayi kafun ta furta “Allah ya kaimu”, ciwan ki fa, saurin Tashi tayi daga cikinsa tana furta “ni lapiya ta kalau”. Wayar ta tadauka kafun ta dauki plate din da taci abinci, zaiyi magana tayi saurin tsayar dashi, “zan iya “,lumshe mata eyes dinsa yayi kawai Batare da yace komai ba, ganin hakan yasa tabar dakin cikin tahunta a hankali.


*******

*********

Tana sakko wa kasa ta tarar da komai a gyara tsaf tsaf sai tashin kamshi yake falon, tazo zata gifta wajan kitchen kenan taga shigen paper din da take ganin, da sauri ta dauke paper din ta cukwi kwiyeta a hannunta kafun ta kai plate din kitchen , tana budewa sakon da ta saba gani ta gani a jikin paper yau ma, gabanta ne ya fadi yau, tsoranta kar wani abu ya samesa,da sauri ta yaga paper din ta saka a shara gudun kar yazo yaga takardar ,kwanukan da ta bata ta wanke da kanta,abinci take san girkawa ,amma ta rasa me zata dafa, pounded yam ne ya fado mata a rai da miyar efo riro, murmushi ta saki yalwatacce , tuno da abincin oummanta. Doya ta dakko manya guda uku, ta feraye tare  ta dora a kan wuta, kafun ta fito da Ganda, nama, kifi da kuma kayan ciki, gyarawa ta farayi cikin kankanin lokaci ta gama gyarawasu ta dora namanta a wuta , Ganda ma haka bayan ta gyara bushashshen kifinta, Attaruhu tayi greating shima kafun ta fara yanka albasa, Daidai lokacin da su firdausi keyin sallama, daga kitchen din ta amsa musu ,amaimakon su zauna sai suka bita kitchen din suma, sakin baki sukai suna kallanta ganin yanda take yanka uban albasa,”sister me nake gani haka , amarya da yin girki”, cewar feedy, murmushi kawai ta sakar musu, aunty feedy sannunku da zuwa,amsa mata sukai gabaki d’ayansu, cikin zolaya ihsan tace “sister amma yaya baya nan ko shiyasa kike tikar aikin nan, kar ya dawo ya tarar da ke haka yasamu tsallan kwado”, dan waro ido tahee tayi kafun ta furta “gashinan a bayanku ai”, ba ihsan da akai wa maganar ba ,gabaki dayansu zuyawa sukai a tsorace,dariya suka bata ta dan dara “wasa nake muku yana sama” wata ajiyar zuciya suka sauke kafun su ajiye mayafansu ,”yanxu me zamu tayaki dashi dan wallahi banshirya yin tsallan kwado ba,tukunna ma me zaki dafa haka ne, ya Wuna ya fara tsinkewa fa inaso naci girkin amarya”,cewar ihsan ,murmushi kawai take “pounded yam da miyar efo riro,”zaro mata idanuwansu sukayi”Menene shi kuma “ wata sabuwar dariya ce ta kamata amma ta danne kafun ta furta “ynxu dai a ina za a samu alayyahu please “, tunani suka fara kafun summy tace bari nasa anemo, cikin kankanin lokaci tasa kuwa aka kawo alayyahun da yawa, ganin doyar ta dafu ne yasata tsane ruwan kafun ta juyeta a flask gudun karyasha iska, message ne ya shigo wayanta dan short” take care of your self, karki famamin ciwona please,ki kula , I love you “, tana ganin message din ta fara blushing ita kadai, hade baki sukai su uku kafun su furga “Awwwwwwwwwqqqn” kunyace ta kamata, ta fara dariya kasa kasa, doyar suka fara daka wa tunda sun hanata yi , kujeran dinning din ta zauna tana nuna musu ynda zasuyi,ita kuma tana ta yasu murmulawa da kyau, ana gamawa tahee ta fara hada miyar efo riro, take a wajan wani kamshi ya karade ko ina , su feedy sai faman santi suke tun kafun su dan dana abincin.miyar ba karamun kyau tayi ba musamman yanda  komai ya fito aciki,ainahin miyar efo riro ta yarabawa tayi da taji ganda,nama ,kifi, da kayan ciki.wani hadaddan cooler me shegen kyau aka dakko mata tazuwa sakwara guda uku a ciki sai miyar da ta iba itama ta ware da ban, kafun ta sakasu su fito mata da wasu flasks masu shegen kyau,abeey ta fara zuwa ba , sai su dada da ummey da Ammeey,sai taga kuma bata kyauta ba in baka kaiwa su mamy ba suma, suma haka ta zuzzubamusu, tasa aka kai musu,abunda tayi ya farantawa su ihsan rai sai suka karajin wani girmanta da kimarta ya kara shigarsu,bayan ankai ko wana part a babban tray ta zuba musu nasu gabaki d’aya suka zauna kan carfet suna cii, suna hira kwanin nan sha’awa, suna gama ci kara gyara gidan sukayi sabida kiransu da ake tayi a cikin gida.har zasu tafi ta roki alfarmar su jirata ta shirya sai su tafi tare , kallan juna sukai kafin su gyada mata kai, a hankali ya’ke taku har ta kai sama, suna ganin wucewarta suka gudu, ihsan ce me cewa” ban shirya yin tsallan kwado ba da Shan mari”, suma gabaki dayan su dariya sukai dan sun san zasu sha drama in sun koma.


Wanka tayi shaf shaf ta shirya cikin wani material blue colour me plazo din wando blue white colour ,mayafin ta ma dark blue ne tare da takalmin ta, shigar tayi mata kyau sosai, kadan ta dan fesa turaransa da ta gani, wayarta ta fara dubawa amma bata gantaba,tunanin inda ta barta tayi kafun ta sakko down stairs, bata tarar da kowannansu a falon ba, sakin baki tayi tana bin falon da kallo, girgiza kai kawai tayi kafun ta nufi kitchen , wayarta data ajiye lokacin da suke aiki ta dauka tana barin kitchen din.


Bata dade da zama ba ya shigo cikin falon sanye da light blue din yadi me shegen laushi , kwantaccen gashin kansa ya kwanto masa , gashin kansa sa faman shining yake baki kirin da shi, fuskarsa kwata kwata ba walwala amma ba a hade take ba, gabaki d’aya falon ya saje da kamshin turarensa da na tahee, bata san da  shigowarsa ba , sai faman game take cikin wayar, jitayi an fiske wayar, a firgice ta mike zata gudu ko kwallan Wanda ya kwace wayar batayi ba, rike hannunta yayi kafin ya furta “it’s me, nayi sallama har na shigo baki sani ba”, ajiyar zuciya ta sauke tana dafe saitin zuciyarta dan ta tsorata,”kayi hakuri ban kulaba”,Kai ya daga mata kafun ya dan ware mata  hannunsa , ba musu kuwa tayi hugging dinsa kamar ynda ya bukata “am hungry “, ya furta a fusge,”ka farayin Wanka sai na kawo maka abincin,” ta fada a rarrabe gudun karya ga zakewarta, ido daya ya kashe mata , “yo muje kiyi mun”, ai da sauri tayi baya tana ware masa ido,murmushin da ya saka dimple dinsa lotsawa yayi , tsayawa kallan dimples din tayi kamar taje ta saka hannu a wjan haka takeji,” matsoraciya kawai”, yana kai karshen zancen maganarsa ya haye sama, itama shaf shaf ta fito masa da abincin da ta girma tare da lemo me sanyi, ta hau masa dashi sama , bai dade ba ya fito sanye da wasu kayan daban sai faman tashin kamshi yake ,zubawa sarautar Allah ido tayi ta kasa ganewa shigarsa ta ynxu da ta dazu waccece tafi kyau take a wajan kuma sai taji wani kishi ya daki zuciyarta” yanxu kamar ynda yake ganin kyansa haka matan waje ma zasu gani kenan”, kamar yasan me ke ranta ,sai saura “You’re the only mine and I’m the only yours,” murmushi tayi ba tare da tace komai ba duk da taji dadin maganarsa. Waje ya samu kan wani dan chair me zaman mutum biyu tayi serving dinsa , bin abincin yayi da kallo kafun ya kalleta alamar Menene wann,”pounded yam with efo riro”, abincin ya ravawa zanci kenan yau,Kai ta daga masa alamar eh , tana gama serving din ta mike da niyar barin wajan ya jawota jikinsa ya dorata kan cinyarsa tare da saka hannunta cikin abincin, batace komai ba ta soma bashi abaki, lumshe idanuwansa yayi jin yanda dadin abincin ya ratsa masa baki, be ce komai harta kara sa masa wani abakin, nan ma still be ce komai sai da yaci sau biyar kafun ya dan kalleta,”wanene yayi abincin nan”,a da rare ta Kallesa,”nice “, dan tabile bakinsa yayi kafun ya ya mutsa fuska kadan “shiyasa beyi dadi ba aushe “sakin baki tayi tana kallansa kafun ta mike daniyar kwashe kwanukan abincin ya Mayar da ita,”your cook is the most amazing part,I love the test so much,inaso wannan hannun ya dunga mun abinci”turo masa bakin tayi kafun kuma tayi saurin daukewa, ganin lokaci na tafiya yasa ta cigaba da bashi abincin,duk ci daya sai ya dan tsotsi yan ya tsunta kafun ya saki, har ta kammala bashi a baki.



🫧🫧🫧🫧🫧🫧


Karfe 6:54 aka kara kiraye kirayen kiran sallar maga riba, sallah tayi har yanxu kuma bata cire hijab din jikinta ba sai kallan agogo take yi ita kadai, shigowarsa cikin dakin ne yasa ta mikewa da sauri ,”sannu da zuwa”, lumshe mata idanuwa yayi alamar amsawa , ruwa ta kawo masa me sanyi yasha,tsawan lokaci tana jiran taji yace su tashi ya kaita part din su dada kamar yanda yai mata alkawari amma sai taji shiru. Duk motsinta yana ankare da ita sai ma gyara kwanciya da yayi, ganin hakan yasa ta yin saurin magana”Yaushe zaka kaini part din su dadan”ta karasa masa a maraice, eyes dinsa ya waro kadan “Yaushe nayi miki alkawarin zuwa part Dinsu, ni ba inda zani dan nagansu”,sakar baki tayi tana kallansa amma duk da hakan bata sadu daba”dazu fa ka fada hakan”, toh shiknn amma da sharadi daya kinyarda”, batare da jiran jin sharadin ba ta amsa da sauri “eh na amince”, kyataccen murmushi ya sakar mata da ya sata tsarguwa, ganin hakan ya fuske tare da dauke kansa, “let’s go amma ba dadewa zamuyi ba “, da sauri tabi bayansa kuwa ya rike mata hannu, suna fitowa waje zaki ya bude masa mota, a maimakon yashiga sai ya zaga ya bude mata kafun shi ya shiga, satar kallansa zaki ya dungayi abunda be taba gani va, Kai tsaye part din dada suka shiga, duk Wanda ya kallesu zaiga alamar kwanciyar hankali da natsuwa a tattare da su, musamman yanda sukai matching da juna, ganin irin kallan da suke binta da shine yasa ta jin kunyarsu, sakin baki aunty tayi tana bin tahee da kallo kamar ta mayar da ita kitchen , mommy da mamy kuwa murmushi suke sakar mata dan ko dazu sai da mamy ta kara cin sakwarar da aka kawo mata dan ba karamin dadi yayi mata, gaishe da gabaki d’aya falon tayi cikin jin kunya, suma cikin kulawa suke amsa mata gaisuwar ta tare da yi mata godiyar abincin da ta basu kowa sai yaba daddadan abincin ta yake , amrah tuni zuciyarta ta tsinke ganin yanda a dan kankanin lokaci tahee ta wani irin murmurewa, ko ita data dade a gidan jikinta bata shining kamar na tahee, basma bata falon. Lokacin, TAHEE kuwa ko ajinkin sai ma dan hararar su ihsan dake mata dariya kasa kasa tayi ,kafun su koma gefe suna hira sai faman tsokanar ta suke, king kuwa ko a jikinsa waje ya samu ya hade ransa kwata kwata babu bara ‘a amma duk motsinta yana ankare dashi,har karfe tara suna zaune a falon. Ganin basu da alamar mikewa mahma ta koresu part dinsu, suna komawa koma wajan shi ya nufa, ita second floor ta nufa shikuma ya wuce 3rd floor , Wanka tayi shaf shaf sabida bancin da take ji na neman fusgarta, cikin wani guntuwar rigar bacci da bata boye komai na jikinta ba ta saka , har da kulle kofar Sabida kar ya shigo, ba dadewa kuwa wani bacci me dadi ya dauketa. Tana cikin baccin ne taji kamar abu na yawo a jikinta,bata motsaba sai da taji abun na mata yawo a Daidai mararta, a mugun tsorace ta farka, cin Karo da kyakkyawar fuskarsa ta soma ja baya tana hadiye yawun da ya tsaya mata da kyar,a mugun tsorace ta furta”’me kakeyi anan bayan dare yayi”, bece mata komai Sabida yanda idanuwansa suka fara canza kala sai faman lumshesu yake, hannunta yake kokarin rikowa tayi saurin mikewa tsaye tana Jan baya, a mugun tsorace take kallansa ganin shima yana bin bayanta, kara ja da baya ta dunga yi shima yana biyota , bata san lokacin da ta karasa jikin bangoma shima a Daidai lokacin ya karaso inda take yayi mata runfa, cikin muryarsa da tayi mugun Dusha shewa ya furta “ i need you now”.



No comments