Breaking News

Gidan Aunty book 1 page 3

 


BOOK 1📕

 


Bismillahirrahmanir rahim…..


Free page 3 🦋


 ➰➰➰➰➰➰➰➰

Wani kayataccen daki yashiga babban gaske me shegen kyau da tsaruwa , duk da kasancewar komai na part din da glass akayishi hakan be hana tsantsan kyauwun dakin boyuwa ba sai ma kara futo da ainahin kyan da yayi.Direct inda wardrobe din dakin yake ya nufa, daga jikin wardrobe din ya danna wani abu me kamar design , take wardrobe din dakin ya rabe biyu wasu manyan elevator guda biyu ne suka bayyana,na farko yashiga inda ya danna 3, direct floor 3 ya kaishi, wani katafaran falo ne awajan komai na cikin falon white colour ne hatta da labulayen dakin, ga wasu dan ubansun 2 set sofa masu shegen kyau a wajan suma white colour , daga kasanshi kuma wani lallausan farin carpet ne me shegen laushi, daga gefe a kwai standard glass da komai na cikinsa kana iya gani, iya haduwa falon ya hadu , baka jin komai na tashi sai sanyin ac da kamshin turare , a hankalii yake taka kafarsa kamar bayasan takawa, kai tsaye center table din falon ya nufa , remotes din dake center din falon ya danna, a hankali gefe daya na labulen ya fara budewa, tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki, wani kayataccen daki ne ya bayyana komai na cikin dakin white colour din hatta furnitures din dakin , babban gado ne a dakin me girman gaske sai shimfidarsa da ya kasance white and black,, daga gefe daya wani chair ne a wajan me shegen kyau shima white colour , iya tsaruwa dakin ya tsaru, direct toilet ya nufa ya dau kusan 30 minutes aciki kafun ya fito da white din jallabiya fara kal da ita , gaban mudubin dakin ya nufa wanda yake shake da mayuka mabanbanta da turaruka masu shegen kamshi,imperial majesty kawai ya fesa a jikinsa , take dakin yacika da kamshin turarensa , ba’ajin kamshin komai sai na imperial majesty daya cika dakin. Rawanin da larabawa ke daurawa ya daura akansa,inda ya futo cak a balaraben sa,ba karamun kyau kayan sukayi wa fatar saba , iya haduwa ya hadu , daga gefan fuskar sa kwantaccen bakin kashin kansa ne ya fito sai faman kyalli yake, bakin sajan bakinsa me shegen kyau ya futo da ainahin pink lips dinsa,rawanin sai ya kara futo da kyawawan idanuwansa masu zara zaran eye lashes ,tare da bakar gashin girarsa,iya kyau yayi kyau ba karamun na wasa ba, duk wanda ya kallesa sai yaso yasake kallansa, fatabarakallahu ahsanil kalikin shine abunda nake fada kawai a raina. Yanxu ma be zauna ba, wayoyinsa kawai ya dauka tare da ficewa a dakin baki daya.direct down stairs ya nufa yanxu ma ta elevator ya nufa, a kasa ya tarar da zaki, zaki na ganinsa ya sara masa tare da saukar da idansa dan ba karamun kyau uban gidan nasa yayiba , “tabbas ubangidan sa na da kyau , kyau da ake kira kyau” duk cikin zuciyar sa yake magana , cikinsauri kuma ya bude wa king motar da ya dauko kirar mercedez benz ganin ya karaso inda yake ,basu tsaya a ko ina ba sai babban masallacin dake unguwarsu,bayan idar da sallar magriba din ma basu bar masallacin ba sai bayan sallar isha’i, duk kallan da ake masa yanaji amma ko dako wa yaga masu kallan nasa beyiba sai ma kara tsuke fuska da yayi, ana idar da sallah zaki yaja motar tare da barin unguwar baki daya.


➰➰➰➰➰➰➰➰➰

Sallar asubane ya tayar da oumman nasu, tahee!! Tahee, “uhm” cewar tahee, oya a tashi lokacin sallah yayi, yanxu ma “uhm”ta karacewa kafun a hankali ta soma adduar tashi daga bacci,falo takoma tare da tashin taheer, ganin ya’ki motsawane yasa oumman mi’kewa “nasan sarai kana jina maxa ka tashi kafun ranka ya ‘baci”, murmushi yasaki tare dayin adduar tashi daga bacci, dama ya rigada ya tashi tun lokacin da oumma ta fara tashin taheera ya farka.

mimmikewa sukai tare da dauro alwala kasancewar har gidan ana jin kiran sallah yasa su bin jam’i, bayan sun idarne ko wannan su yayi adduar safe da maraice kamar yadda suka saba a kullum,”oumma ina kwana”duk suka hada baki wajan gaishe da oumman tasu, murmushi oumma ta saki”fatan ‘yan biyu na sun tashi lapiya”, “lapiya lou” suka amsa mata.suna zaune sukaji sai faman buga musu kofa ake , tashi oumma tayi tare da bude kofar , ba kowa bace face kaka tabawa , daure da daurin kirji, gaishe da ita oumma tayi, tabe baki kaka tabawa tayi “ba gaisuwarkice ta kawoni ba, maza maza ki tashi kigyara tsakar gidan nan ga wanke wanke na jiranki, sannan kisaka tanbad’ad’d’un ‘ya’yanki su d’ebo mana ruwa,dan ba hutu kuka zoyiba”. “Insha Allahu zamuyi”cewar oumma, yanxun ma tabe baki kaka tabawa tayi”ke kika sani, kar Allah yasa kiyima”tana gama fada ta bar wajan , koma wa daki oumma tayi , yanda ta barsu a haka tazo ta samesu sabanin dazu yanxu ko wanne ya yi cidin cidin da fuska dan sarai sunji me kaka tabawa kecewa, murmushi oumma ta saki “kuyi hakuri yan biyun ummansu wata rana sai labari ai”,jikinsu ne yayi sanyi jin abinda oumma tace.kamo hannunta sukayi tare da sata a tsakiyarsu,”kiyi hakuri oumma ba wai fushi mukai ba , kawai bamasan abunda kaka tabawa da mutanan gidan nan suke miki”,shafa fuskar taheer dake magana oumma tayi,”bakomai taheer komai me wucewa ne bana so kuna sa abunda da suke mana a ranku, yanxu ku tashi kudebo musu ruwan da sukace kunji, ku kula sa hanya banda rigima”, “toh oumma “duk suka amsa mata , itama wajan ta biyosu tare da fara sharan tsakar gidan.

Sun dau dogon lokaci suna d’ebo ruwan , lokacin har oumma ta kammala share tsakar gidan da ya dawo kamar bashine me tarkace ba. Tulun kayan wanke wanken suka hada ‘kuda sai faman bin kwanukan suke, sundau dogon lokaci suna wanke kwanukan , dadin su daya ma haduwa sukai su duka suka wanke dan ba karamun kwanuka aka bata ba ,gama wanke wankensu ba dadewa aka kawo markadan wake , zama tahee tayi ta buga wannan kullun, yayinda oumma ke hura jikakken ican da aka jika duk idanuwanta sunyi ja sabida yadda hayakin ya cika mata ido. 


Duk wannan abun da suke mutanan gidan sai faman kai kawo suke , ba wanda yace dasu ko sannu sai ma banzan kallan da ake binsu dashi da hantara.basu suka kammala ba sai wajan karfe shadaya,ragowar guntun dumamen tuwan jiya kaka ta bawa ta mikowa oumma,” kar alashemu ace bamu baku abinci ba ko akai mu duniya” cewar kaka tabawa ,kallan tuwan da baifi cin mutum daya ba oumma tayi, batace komai ba sai ma daki da ta nufa , anan ta samesu sai faman sauke nunfashin yunwa suke ,kwallace ta tarar mata , ganin suna kokarin mikewane yasata saurin goge idanuwanta kada suga rauninta, tuwan da ke hannunta ta ajje musu, cikin sauri suka mike tare da wanko hannayensu,har sun saka hannu zasu fara ci sai suka fasa tare da zubawa oumman tasu idanu,sarai ta fahimcesu amma ko motsawa batayi ba, langwabar da kai sukayi kamar wasu yara oumma suka kira sunanta , girgiza kai kawai oumma tayi tare da mikewa tare da zama a tsakiyarsu.taheer ne ya kutsuro tuwan tare da kallan oumman tasu “oumma haa” dariya duk suka saki ganin yadda ya bude bakin nasa , cikin kulawa yasa mata tuwan, itama taheera saka mata tayi a baki, hannu oumma ta saka itama ta fara basu a baki , duk da tuwan bashi da yawa amma haka ko wannansu yasamu yaci , cikin farin ciki da kaunar junansu.


➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰

10:20 pm motarsu ta danno kai cikin gidan , kamar ba dare ba har yanxu akwai hasken futullu da ya haska ko ina na gidan, daya daga cikin building din gidan zaki yayi parking , ya dau kusan 2 minutes zaune a cikin motar idanuwansa a lumshe kamar meyin bacci, a hankali ya zuro da kafarsa guda daya kafun a hankali ya juro da gaba dayar kafar tasa yana mikewa,cikin takunshi me kama da na izza ya fara tafiya tare da nufar kofar da zata sadashi da babban falon building din.Babban falo ne me kirgan gaske da ya cika da tsadaddun furnitures na alfarma , iya haduwa falon ya hadu ba abudna yake tashi sai daddadan kamshi da sanyin ac, ganin bata falon yasa ya juya da niyar komawa, foot steps dinta da ji ne yasashi tsayawa kafun ya juyo a hankali,murmushi ta sakar masa”son “ be amsa ba sai ma zuba mata kyawawan idanuwansa da yayi, sannu a hankali ta karaso wajan, sanye take cikin hijab hannunta dauke da tasbaha sai faman sakin murmushi take , sau da ta karaso inda yake kafun ya bude baki a hankali kamar wanda magana take wa wahala, cikin cool voice din shi me shegen dadi ya kira sunanta “Ammi,”hararar wasa ta jefa masa”sai yanxu ka tuna dani”lebensa ya motsa kamar me sanyin magana sai kuma ya fasa tare da dauke kansa, kamo hannunsa tayi tare da zaunar dashi kan daya daga cikin kujerun falon,”oya zauna ka ci abinci nasan yau kwata kwata ba abuncin kirki kaciba , na kusa yi maka aure kwanannan ko zaka shiga taitayinka”,bece komai sai hade fuska da yayi tare da kau da kansa, murmushi ta sakar masa “mai da wukar son wannan hade rai haka, nima wasa nake maka , ai samun wacce zata siyo zuciyar ka sai anshirya “a jiyar zuciyar da ko ammi dake kusa dashi bataji ba ya sauke tare da sassauto da fuskar tasa kadan . Abincin ta dakko masa da kanta tare da jerasu can center table din gabansa,zubawa tulun abincin data ajje a gabansa idanu yayi sai kace mutum goma zasu ci, bece komai ba sai idanuwansa da ya zuba mata ,sarai ta gane me yake nufi”duk suna part din dada tunda kai cin abinci cikin yan uwan naka ne bakaso”, lumshe fararan idanuwansa yayi, itama ammi bata kuma cewa komai ba sai abincin da ta zuba masa cikin hadaddan plate din da ta dakko, “oya haa” bude lumsassun idanuwansa yayi tare da kallanta, yanda tayinne yaso bashi dariya amma kwata kwata be yitanba, a hankali ya bude bakin nasa ta fara feeding din nasa , 7 spoon yayi tare da kawar da kansa,”son karkace mun kakoshi”lumshe mata ida nuwansa yayi, girgiza kai kawai ammi tayi tare da dakko masa hadaddan kunun ayar da tayi masa, sosai kuwa yasha kudin ayar bayan ya kammala shane ammi ta mike, “oya tuzuru aje a kwanta sea da safe”, bai ce mata komai ba sai mikewar da yayi , dariya amminta saki”bani na kar zoman ba rataya aka bani”inda sabo ta saba da halinsa na kinson yin magana tunda tasan halin kayanta,”Ammi sai da safe “ ya fada cikin husky voice dinsa, side hug tayi masa , Allah ya tashemu lapiya ka kwanta da wuri dan na san ka gaji, jinjina mata kai yayi alamar toh tare da ficewa.


Har yanxu zaki na waje kikam kamar bushiya , inda ya barsa anan yazo ya samesa be ce masa komai ba , shima zakim bude masa kofar mota yayi, cikin takunsa na kullum ya nufi motar, haryasa kafa zai shiga sai kuma ya daga idanuwansa tare da kallan wani building sai kuma ya lunshesu tare da shiga cikin motar, daidai part dinshi zaki yayi parking yanxun ma shine ya bude masa kofa . “Sai da safe king”hannu king ya daga masa kabar bazai ce komai ba sai kuma ya bude baki a hankali “good night”. Murmushin jin dadi zaki ya saki be bar wajan ba har saida yaga shigewar king sannan shima ya barwajan.


Direct yana shiga part din sama ya hau ta elevator , yana shiga dakin rawanin kasansa ya bayyana,kofar da zata sadashi da toilet ya nufa, ya dau mintuna a cikin toilet din kafun ya fito da wasu white pj mas masu laushi , imperial majesty ya fesa , dakin ya kara dauka da kamshin turaransa da ke kama daki,kan gadan sa ya nufa kai tsaye cikin luntsumeman gadansa, har ya kwanta sai kuma ya mike tare da dakko wasu magun guna .maganin hannunsa ya sha tare tare da bude bedside drawer. Har ya bude zai zubasu idanuwansa suka sauka kan wani hoto dan karami, daukan hotan yayi tare da zuba masa ido . Wasu matasan larabawane a jikin hoton sun rike hannun junansu, kana ganinsu kasan ba karamun kaunar junansu suke ba. Sauke ajiyar nunfashi yayi tare da mayar da magun gunan, shima hotan mayar dashi ma a daninsa yayi tare da danna wani remotes take futulun dakin suka dauke , wasu kaloli masu kyau da haske suka fara cika dakin me kama da dim lights , sannu a hankali bacci ya daukeshi.


➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰


Comment and share 


💖The talent troupe🔥


Writers of ….✍️


 Duk karfin izzata

Gidan Aunty

Sarki sameer 

 Jini daya 

Ya fita zakka…..

💖GIDAN AUNTY💖

         ( A heart touching love story) 



            By  Aysha galadima 

                  ( mss Lee)

 

💖The talent troupe 🔥

 

PAID BOOK 

No comments