Breaking News

Gidan Aunty book 1 page 21-22-23

 


Free page 21 🦋



Ba kowa bace ta shigo dakin face amrah dake a zabure idanuwanta duk sun kunbura, a yadda ta gansu ne yasata fashewa da kuka tare da barin dakin cikin sauri, da Sauri ya bangaje tahee da batasan meke faruwa ba sabida yadda kafarta ke mata ciwo a kasa  , har ya daga hannu da niyar tsinka mata mari sai kuma ya dungule hannu tare da rintse idanuwansa da suka kada sukai ja, kallo daya kawai yayi mata tare da ficewa a dakin ransa a bace , ko da ya fito falon be tarar da ammi ba hakan ya bashi damar fita daga part din gaba daya, ko part din ummey be karasa ba ya bar gidan .


****Da gudu amrah ta karasa part din aunty, bakowa a falon tai saurin shigewa daki, kuka ta fashe dashi sosai , kome ta gani sai tayi bal dashi, a haukace take fasa abunda taci karo dashi,”taheera “shine sunan da take nanatawa tana hawaye “wallahi sai na kashe ki,sai naga bayanki, shegiya tsinanniya ,wacece ke da zaki rungumeshi har dayi mishi kiss, wallahi sai na la’antaki bazan kara fadawa kowa bama da kaina zan kashe ki har lahira sannan na kashe banza”, bata karasa zancan nata ba aka tsitstsinka mata mari dama da hagu, a tsorace ta dago da idanuwanta a tunaninta aunty ce ta mare ta ganin ba kowa a dakin  ta fara zazzare idanuwa, mafarkan da ta dungayi jiya da daddare ne ya fado mata a zuciya ,da kyar take iya hadiye abunda ke makoshinta, taku ta fara a hankali da niyar barin dakin,talewar da kafarta tayi ne yasa ba shiri ta bige kafar take da sakin azababban kuka, wani saukan marin da ta kuma jine yasa ba shiri ta mike tsaye ga azaba da kafarta kemata kamar wacce tayi targade.”ke “ taji wata razananniyar murya ta kirata,cikin rawar murya ta soma amsawa “naa…am, dan.. Allah kuyi… hakuri innayi muku lefi…”bata karasa maganar taba taji saukar bulala a bayanta,ihu ta soma “nashiga ukuna na lalace,dan Allah kuyi hakuri na tuba bazan sake ba “, kamar wayanda ake zugawa haka suka shiga laftarta saida suka ga ta daku sannan aka daka mata tsawa cikin muryar mata ,”ke, mike tsaye”azabure amrah ta mike fuskarta duk ta baci da majina ga kukan da Tasha “rufe mana baki”aka kara daka mata tsawa, hannayenta biyu tai saurin daurawa abakin mata sai faman waige waige take ga hawayen da ke zuba a fuskarta,”rawa zaki mana yanxun nan , duk rawar da muka saki,kuka kuskura kika fadi zaki gane kuranki, kinajina”, da sauri ta shiga daga kai har ynxu hannunta na kulle a bakinta,dariya muryoyin mace da na mijin suka saka kafun lokaci daya wajan yayi shiru,”maza yi mana rawar dan biri”ana gama fada mata haka aka jefo mata ayaba kuda d’aya, da sauri ta dauki ayabar ta fara tsalle kamar yadda dan biri keyi, fuskarta duk ta baci da hawaye ga guntun gashin ta da ya barbaje sai ta dawo kamar dan birin kuwa, tanayi tana kwantawa alokaci daya kuma tana kuka, sosai taji muryoyin nan guda biyu suna dariya kafin ta karajin wani sautin,”yi mana yadda mage take kuka”, kara fashewa da kuka amrah tayi kafun ta fara “meowwww meowww meowwww moewwww” ta nayi tana share fuskarta da ta baci, sosai suka wahalar da ita, iya rawan dabbobin kam har Wanda bata sansuva tayi rawarsu,ga kafarta dake tsananin yi mata ciwo kamar wacce ta goce a kashi.


********** kwance take kan lafiyanyan gadon dakin nata, hannu daya wayane a ciki yayin da Dayan hannun take rike da apple, waya take sai faman murmushi take saki ita kadai, turo kofar dakin da akai ne yasata dagowa,wacce ta ganine yasata mikewa zaune tare da kashe wayar, Momy kice kuma yau adakina, karasa shigowa wacce aka kira da momy tayi kafun ta samu waje ta zauna daga bakin gadon, “ko na komane”ta fada tana zubawa firdausi idanuwa, dan jinjina mata kai firdausi tayi tare da dage kafadun ta kadan,”akan wana dalili zan hanaki shigowa momy, naga yanxu bakya shigowane tun bayan tafiyar yaya haroon,ta bile baki kawai momy tayi kafun su canza hirar tasu zuwa wata,kallan ta firdausi tayi “amma momy ba kya tunanin waccan yarinyar da Gangan ta bige dan taga mutanan gidan suka tarai rayarta, kalli fa wai yau yaya king ne ya taba wata, ni ko hannunsa aka ce ya dora akan wata ai bazan yadda ba balantana wayancan shashashan da suke wahalar dakansu”,murmushi kawai momyn ta saki ba tare da tace komai ba dan Akan idanta amrah ta tura taheen, ganin momyn tata bata biye mata ba yasa share zancen suka fara zancan dan uwanta.


💖💖💖💖💖


Tunda ya bar gidan a guje zaki ya fara tuka Motan ganin yadda lokaci daya king din ya canza masa kamar wani zaki,a dake ya furta “my house “ya karasa maganar tasa tare lumshe idanuwansa, tafiya akai sosai me dan ta Zara daga banana island kafun suzo kofar wani hadadden building me shegen kyau, tundaga wajan gidan da glass akayi shi komai na cikin sa glass ne , cikin sauri sojojin dake bakin gate din suka wangale baban gate ganin me gayyane da kanshi ya zo, a Daidai parking lot zaki yayi parking inda sauran manyan motocin suke, yau be jira an bude mishi kofarba, yana fito wa ciki ya shiga cikin sassarfa, kofar dake kasa kawai ya bude ya shiga, sosai dakin da yashiga ya hadu, kayataccen falo ne a wajan babban gaske da yafi Wanda yashigo haduwa, Komai na cikinsa whites ne tunda ga kan labulayen dakin har kan lallausan carfet din dake shinfide fari tass dashi, ko ina nawajan tashin kamshi yake kamar ana anfani da shi kullum, kan daya daga cikin white sofa din ya zauna ko takalman kafarsa be cire ba, idanuwansa ya lumshe a hankali ,jijiyoyin kansa ne suka mike sosai , kyakkyawar farar fuskarsa tayi ja sosai, kara rintse idanuwansa yayi da karfin gaske ganin har yanxu yanajin tsayayyun breast dinta a jikinsa, sosai gashin jikinsa ya mike ,a zamube ya fara bal da duk abunda yaci karo dashi, zafi yake ji sosai a cikin Jikinsa,sosai gashin jikinsa ya kara tashi ji yake kamar tana jikin sa haryanzu, adduar ya fara cikin zuciyarsa, tsawan lokaci kafun wata nutsuwa ta fara saukar masa, sosai ya ke ajiyar zuciya ganin lokaci daya azababban zafin dake ratsashi ya tafi sai ma sanyi da yake danji a haka wani daddadan bacci ya dauke sa.


*****har yanxu tana zaune a kasa tun lokacin da ya tunku data, kafarta hannunta rike da kafar tata, shigowar da akai ne yasata saurin dago da kanta?ganin su dada ne yasata sakin ajiyar zuciya, da sauri dada ta karaso inda take “me nake gani haka , tahura ya naganki a kasa duk zafin ciwon ne”, rasa me zatace mata tayi kawai sai ta gyada mata kai alamar a’ah, murmushi ta sakar mata a hankali kafun ta gaishe ta “ina kwana dada” girgiza kai dada tashiga yi “Allah sarki tahura,lapiya ta Lou, jiya da kyar nayi bacci sabida halin da kika shiga “wani murmushin ta kara saki kafun ta gaishe dasu abeey, shima cikin kulawa ya amsa mata tare da tanbayarta ya jikinta, sosai ta dan saki dasu Bayan ta gaisa da su uncle musaddiq da suka shigo daga baya, ganin sauran yan gidan ma suna zuwa yasa duk suka koma falon ammi,sosai kafarta tayi sauki dan tana dan takawa kadan kadan , afalon suka cigaba da hira har ummey ta shigo part din yau batare da zoya Suke ba sabida makarantar da tafi,a haka kowa na gidan ya shigo sabanin amrah , wunin ranar a part din ammi sukayi shi sosai suka nuna mata kulawa musamman ummey dake gefenta.


🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

 

BUNKURE 


Da sassafe kaka ta bawa ta tashi yau kai tsaye dakin su oumma ta nufa , bubbuga kofar dakin ta shiga yi, jin shiru ba abude ba yasata kara bubbugawa “maryama kina ji ina kiranki shine zakimun uwarshegu ko, zaki nunamun ba’kin halin naku kenan ko, bazaki fito bane kina jina”, ganin yadda take faman buga kofar dakin su oumma ne yasa mutanan gidan fara taruwa,Dije dake labe tun lokacin da kaka tabawa ta fito yasata karasowa wajan,kallan kaka tabawa tayi tana kumshe dariyar dake cint kafun ta soma magana”inna ai maryama yanxu ta zama abinda ta zama “kallanta kaka tabawa tayi kamar ya bangane ba,”oh ai inna komai a filine , jiya agaban idanunmu tafita daga gidan nan , har kokarin zagin mu tai da muka yi kokarin tsayar da ita” sosai kaka taba ta kalleta “kina nufin tana yawan dare kenan”, tabe baki Dije tayi”ai kowa nanan sheda ne inna ki tanbayesu”, nan da nan yan gidan kowa ya fara tashi gulmar,babu me fadar alkairi akan oumma su taheer ganin yadda tafita tun jiya bata dawo ba, girgiza kai kawai kaka tabawa tayi rai a bace ta bar wajan” za tazo ta sameni ne duk gidan karuwanci da take zuwa”, da dad d’aya kowa ya fara watse wa ganin hakan yasa cikin sauri Dije ta shige dakin harda taka rawa, kallan ta bintalo tayi,”ya naga sai faman washe baki kike kamar wata tababbiya”a maimakon ta tsawa tar mata akan kalaman ta sai ta kuma kyalkyalewa da dariya, nan da nan ta kwashe duk abunda ya faru ta sanar wa bintalo, itama bintalon sosai tayi farinciki ganin burinta na Auran babban mutum zai cika ,wani shegen murmushi ta saki a zuciyar ta kuwa fadi take “lallai ma Dije baki da hankali,ai wallahi kafin nayi Auran nan sai na ci duniyata da tsinke yanda na fara jin dadin abinnan da boka Yayi mun ,wallahi yanxu na fara anjima ma sai na koma wajan sa dan ya mallake mun duk Wanda yace zai takuramun, ciki kuwa har dake dan ke kika koyamun”,duk wannan maganganun nata cikin zuciyar ta take kafun lokaci daya ta saki wata yar iskar dariya da ita kadai ta san ma’anarta.


Comment and share 


LITTAFIN GIDAN AUNTY NA KUDINE AKAN 300 kacal 

zaku biya kudin ku ta wannan asusun 7041879581 palm pay ayshatou galadima , sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.


Saura few pages na gama sakin free pages dina .



MASU COMMENT INA GODIYA SOSAI DA SOSAI , I HEART ❤️ YOU ALL ✍️.


MSS LEE 💖✍️

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA


💖💖GIDAN AUNTY 💖💖

  (a heart touching love story)


Story & written 

       By 

Mss Lee 💖


PAID BOOK


NA KUSA KAMMALA FREE PAGES DINA 


Mesan KARANTA GIDAN AUNTY DAGA FARKO ZUWA KARSHE ZAI IYA BIYAN KUDINSA TA WANNAN ASUSUN 7041879581 palm pay ayshatou galadima sai a turo shaidar biya ta wanna number 07041879581


BOOK 1


Free page 22 and 23 🦋


A kwana a tashi ba wuya wajan Allah SWT, yau kusan sati biyu kenan da batan su oumma , Tsawan wannan lokaci babu Wanda ya damu da yasan inda suke ,hatta kaka ta bawa da ta share zancen, cikin wannan lokacin sosai bintalo ta fara bin maza ,ganin hankalin yan gidan su nasan komawa kanta ta koma wajan bokannan da mahaifiyarta Ke zuwa, gaba daya ta mallakesu ko dare zatayi babu me tanbayarta dalili, sosai ta baci da kazamin rayuwarnan, Dije kuwa kullum cikin farin ciki take idan bintalo ta Kawo mata kudi ko damuwa da inda ta ke samo kudin batayi,burinta ya cika tun lokacin da oumma tabar gidan,yanxu burinta ta kai bintalo can birni wajan da tahee take sannan itama tasa taheen ta shiga duniya.


🫧🫧🫧🫧🫧


A tsawan kwana kinnan sosai wata shakuwa me karfi tashiga tsakanin zoya da tahee, kullum in ta dawo daga makaranta zaki ganta wajan tahee tana fada mata abunda aka koya musu, yawancin lokuta suna part din ummey ko part din dada da yanxu take kulawa da ita sosai, ta bangaran yan gidan ma haka, momy tana sake mata sosai sabanin mamy da aunty,musamman aunty da ke nuna mata kyautata mata agaban yan gidan , abayansu kuma taita zaginta, ihsan da firdausi ma sosai suka sake mata a yan kwanakin nan, amrah da sumayya ne ko kallo basu  isheta ba,ganin hakan yasa itama bata sake musu fuska. Cikin yan kwanakin nan sosai tayi kewar su oumma tanaso tacewa aunty ta kira mata su amma bata san ta yadda zata tanbaye taba.


Yau ma tunda ta tashi da kewar su oumma ta tashi,so take kawai taji muryarsu sabida mummunan mafarkin da tayi a kansu, sai faman zagaye take a daki tana tunanin ta yadda zata tanbaye ammi  , ganin bata da wata  mafitane yasa ta mikewa tare da fitowa falo a hankali kamar Mara gaskiya, Daidai tana fito wa shi kuma yana shigowa ciki, kamewa tahee tayi wajan tare da rintse idanuwanta,yau sati biyu kenan rabanta da ta gansa, sosai ya kara yi mata kyau kamar kullum kara masa shi ake , a hankali tayi kokarin bude idanuwanta jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri sauri ga kamshin turaransa da ya cika mata hanci, da gyar ta karasa bude idanuwannanta, Ganin baya wajan kamar yadda tayi tunani yasata sakin ajiyar zuciya, ta juya daniyar komawa kenan idanuwanta suka sauka a kansa, kyawawan fararan idanuwanta ta zuba masa duk da yadda zuciyarta ke faman bugawa, sosai shigarsa tayi mata kyau musamman gyaran gashinsa da ya tubke sai faman kyalli yake ,sak ya fito a balaraben sa dan Inba Hausa yayi baza ka taba tunanin yasan Menene kalmar ba, wayace a hannunsa sai faman dannawa yake cikin kwanciyar hankali,fuskarsa kwata kwata ba annuri kamar Wanda yayi rashin lapiya ga kafar sa da yayi crossing lokaci zuwa lokaci yana motsata, a hankali ya motsa pink lips dinsa kamar me sanyin magana sai kuma ya fasa tare da datse lips din nasa,tunda ta Kafe shi da ido ko motsi batayi sam ta manta ma agaban watake, a hankali ya dago da idanuwansa karaf suka hade da nata,bata janye idanuwan ba sai ma sarkewa da idanuwansu sukai  cikin na junansu , bata farga da shirmen da take ba sai jin saukar tsawar sa tayi, sosai ta razana juyawa tayi daniyar guduwa ta ji saukar muryarsa “if you dare “ya karasa kamar be san yin magana , cak tahee ta Tsaya kamar me shirin sakin kuka , ahankali take juyo da fuskarta da ta dukar sosai take jin kunyar abunda tayi ,zuciyarta sai faman bugawa take da sauri da sauri kamar wacce tayi gudu. Lokaci zuwa lokaci take dago da idanta ganin hankalinsa baya kanta cikin rawar murya ta soma magana “ ina wu..ni”, be amsa mata ba haryanxu idanuwansa na kan wayarsa, kara dukar dakai tayi tana wasa da kasan hijabin jikinta,”ina wuni” ta kara gaishesa cikin rawar murya, yanxun ma be amsa mata , ganin hakan itama ta shareshi tana dan turo dan mitsitsin bakinta, dauke gansa yayi daka kallan dan mitsitsin bakin da ta motsa kafin cikin kasa kasa da murya ya furta “coffee”,kara turo dan mitsitsin bakin nata tayi gaba kafin ta nufi hanyar kitchen din , cikin kan kanin lokaci ta kammala hada coffee din azuciyarta sai faman mitar Shan coffee din nasa take ,”coffee ,coffee”, kafun kuma ta sassaita nutsuwarta ta fito falon, a yadda ta barsa a haka tazo ta samesan yana zaune da kafarsa da yayi crossing, duk da yadda zuciyarta ke rawa hakan be sa nutsuwarta fito wa ba” gashi” ta mika masa tana dan russunawa, be fi sakon biyu ba yasaka hannunsa kan dan karamin tray din da ta miko masa, sipping ya fara a hankali,ta kasan ido tahee take satar kallansa “shi wannan kullum cikin Shan coffee ko abincin arziki be ci,nan gaba inaji sai coffee dinnan ya fito masa a jiki”,  ita kadai take hirar ta a zuciya,kamar yasan me take tattaunawa ya dago da idanuwansa ,saurin sunkuyar dakanta kasa tayi, dan ta bile bakinsa yayi kafin ya soma magana” get me something to eat “,da sauri ta dago idanuwanta jin abinda yace , bata ce komai ba sai kitchen da ta nufa, a ba’kin gas ta tsaya tana karewa kitchen din kallo,tu nani ta fara me zata dora masa Mara sauki , ganin tana bata lokaci ne yasa ta nufar babbar freezer din kitchen, manyan tilapia fish ta dakko guda biyu , cikin kwarewa ta gyara kifin kafun ta feraye Irish potatoes dinta, bata dau dogon lokaci ba ta kammala hada grilled fish dinta ,da yaji sauce din Dankali sai faman tashin kamshi yake, kunun ayan da ta ga ammi ta jera a fridge ta dakko tare da zubawa cikin madaidai cin jug, cikin lokaci kankanin ta kammala hada abincin , kafin ta fito falo zuciyarta sai bugawa take, hanyanxun yana zaune a falon sabanin dazu yanzu ya dan jingida da jikin kujeran, sunkuyar da Kai tayi kasa,”ga abincin”, be ce mata komai ma sai gyara zamansa da yayi kafun ya bude plate din, sosai yadda aka kawata abincin ya burgeshi amma a zahiri sai ma tabe bakinsa da yayi, be kulata ba ya faraci a hankali , 3 spoon yayi kawai tare da Shan kunun ayar Daidai lokacin da ake shigowa part din da sallama , ammi ce ta fara shigowa bayanta kuma su amrah ne , duk tsayawa sukai cirko cirko a tsaye kafun ammi ta  karaso falon cikin mamaki,”son Yaushe ka shigo”kamar bazea ce komai ba sai kuma ya bude baki “am looking for u”, murmushi ta sakar masa “sorry son ina tare da su ummey ne”, lumshe mata idanuwansa yayi, cikin rawar murya su amrah suka bude baki tare da gaishesa, ba Wanda ya amsawa a cikin su saima cigaba da tsakurar abincin da yayi kamar Wanda aka saka dole , kallan tahee dake tsaye ammi tayi, “daughter yanaganki a tsaye ke kuma , kisa mu waje ki zauna mana “ dan dago da kanta tayi kadan tare da satar kallansa ,be dena abunda yake ba hakan yasata sauke a jiyar zuciya kadan ,cikin rarrabewar murya ta furta “daman ina gyara dakine “, jinjina mata kai ammi tayi ba tare da tace komai ba ganin hakan tai saurin nufar dakin ta, da kallo su amrah suka bita dashi ko wannansu na mamakin ganinta a falon.



🫧🫧🫧🫧


KANO 


UMC ZHAHIR HOSPITAL 


Wata kyakkyawar yarinyace me matsakaicin kyau zaune kan daya daga cikin kujerun da aka ajje a cikin dakin asibitin, sosai ta zubawa Wanda ke kwance akan gadon ido, kafun ta fara share hawa yan da suka tarar mata a ido, cikin sanyin murya ta soma magana “Allah sarki ummu na ,Allah ya jikanki da rahma”, bata kammala zancan nata ba ta fashe da kuma me cikin rai, tana cikin kukan ne tashi alamun taba kofa , cikin sauri ta goge hawayen da suke zubo mata kafun ta kakalo murmushi a fuskarta, sallama nurse din tayi mata kafin maza wani matashin saurayi ya shigo dakin bayan sa kuma wani kamilllan dattijo ne , drip din da ya kare nurse din ta cire ,cikin girmamawa ta kalli dattijon nan, “insha Allahu ta kusa farkawa a ko Wana irin lokaci “,jinjina mata kai dattijon yayi kafun matashin saurayin gefensa yayi mata godiya, murmushi ta sakar masa tare da barin dakin bayan ta kwashe abin drip din data cire, kujerar da budurwarnan take Kai ta mike tare da sakar wa dattijon nan murmushi “Daddy ga waje ka zauna”, binta yayi da kallo kafun ya sakar mata murmushi shima “nagode daughter” cikin takun dattakon ya karasa tare da zama kan kujerar, kallanta matashin saurayin nayi tare da hararar ta cikin tsokana yace “daman nasan yanxu ba kya sona , harda dauke kai kamar ma bakisan dani ba”dariya matashiyar yarinyar tayi “sorry yaya khaleed , kaima kasan inayinka over “, wani hararar ya je famata “daga baya kenan”, yana gama fadar Haka suka karasa gaban gadon ,cikin tausaya wa yarinyar ta kalli mahaifin nata” daddy Yaushe zata farka” wani murmushin dattijon ya saki, kafun ya bude bakinsa yayi magana hannun ta ya soma motsawa kadan kadan,kafin a hankali ta fara bude idanuwanta ganin hasken da ya haska mata ido sosai ne yasata rintse idanuwan kafun ta kuma budewa hawaye na bin fuskarta, duk zuba mata ido sukai suna kallanta,”taheer!!taheera”, shine sunan da kawai take nana tawa , kallan matashiyar budurwar mahaifinta yayi kafun ya kira sunanta “zahra” cikin Sauri ta amsa da “na’am dady” kallan matar yayi kafun ya kalleta, “tai maka mata”, yanxun ma cikin sauri ta amsa “toh dady”, karasawa inda take tayi ganin ta na kokarin tashi zauna ne yasa ta temaka mata,tunda ta zauna bata ce komai ba sai bin yan dakin da tayi da kallo,duk abunda ya farune ya shiga dawo mata kai cikin sauri ta zabura “taheer “ shine sunan da ta fada tana kokarin sakkowa kasa, kallan ta mutuminnan yayi kafun ya dauke idanuwansa,cikin sanyin murya ya furta “kiyi hakuri kici abinci tukunna inyaso sai muyi magana “katsetsi oumma tayi tana fashewa da kuka “bazan iya ba, ina taheer dina yake , inaso na san halin da yake ciki, su wanene ku, me nake yi a nan wajan”, kallanta mutumin yayi kafun ya soma magana cikin kamilalliyar muryarsa “ kiyi hakuri ,mune wayanda muka kadeki sati biyu da suka wuce , sannan muka kawo ki asibiti sai yanxu Allah yasa kika farka”, waro idanuwa oumma tayi “sati biyu” ta fada cikin rawar murya “kuna nufin satina biyu a asibitin “gyada mata kai mutumin kawai yayi, fashewa da kuka oumma tayi “shikenan na rasashi “, ta kara fashewa da wani saban kukan, kallan ta mutuminnan yayi idan bazaki damu ba zaki iya sanar damu wacece ke , me ya fito dake cikin dare ,naji kina maganar sunan wani da alama wani makusancinki kike Nema “, girgiza kai oumma tayi har yanxu hawayen basu dena zubaba,”zan baku labari na, sannan ina rokon ku da kumayar dani inda kuka dakko ni sabida na nemo yarona”, jinjina mata kai dattijon yayi, yayinda mace da namijin suka samu waje suka zauna suma suna binta da kallo ganin yadda take kuka ,” sunana maryam ni haifaffiyar buzuwace, ‘ya’yana biyu taheer da taheera,mijina Allah yayi masa rasuwa…………..” tundaga farkon labarin ta zuwa karshe sai da oumma ta basu tare da dalilinta na fitowa waje,sosai zahra take kuka shima saurayin da aka kira da khaleed shima sai da ya goge kwalla a idanuwansa , sosai suka tausaya mata, gyaran murya mutuminnan yayi “tabbas labarinki abin a tausaya miki ne, Insha Allahu shima yaron naki zamu binciko miki shi da yar dar Allah, amma kafin nan zansa a baki sallama sai muce gidana gabaki daya in kin yadda damu, ni sunana Alhaji kabeer mai zamani, ga babban d’ana sunansa khaleed , sai autata sunanta zahra, mahaifiyarsu kuma Allah yayi mata rasuwa, ina fatan zaki amince”, shiru oumma tayi kamar me tunani ganin bata da wani zabine yasa ta amince musu ko ba komai zuciyarta ta kwanta da su”, sosai zahra dake sharan kwalla  yin farin ciki har hakan ya bawa mahaifinta mamaki, ba a dau dogon lokaci ba aka rubuta musu sallama ganin wanda ya bada umarnin sallamar, cikin kankanin lokaci suka kama hanyar nasarawa G.R.A dake Garin kano.


🫧🫧🫧🫧🫧

Sosai ya ci abincin yanaci yana babbata fuskarsa, yan matan falon sai faman satar kallansa suke ta kasn ido ganin ammi na zaune a falon , kallo daya yayi musu duk suka mike , kallansu ammi tayi, “sai ina kuma “ cikin sauri suka hada baki “ammi daman zamu je wajan abeey ne “ kallan ammi kawai tayi tare da girgiza kai , suna gita ta kallesa tare da hararansa “ka kyauta da ka koresu” bai ce komai ba lumshe mata idanuwa da yayi tare da mike wa cikin takunsa ya zauna akan kujerar da take ,kansa ya dora akan kafadunta yana lumshe idanuwa, murmushi tasaki tare da zura hannunta cikin lallausan gashin kansa tana masa tausa a hankali “ka rage hade fuskarta nan son , kullum inasan ganinka cikin farinciki kamar yadda nasan ka a baya banasan rashin fara’arka” ta karashe zance cikin karyewar murya , saurin mikewa yayi tare da kamo hannunta,”am sorry ammi na” daga nan bai kara cewa komai ba sai mama tsa mata hannun da yake a hankali, ganin bayasan hirarne yasa ta dakko wani zancen daban, sun dau dogon lokaci suna hirar duk da rabin hirar ammi ce keyi kafin yayi mata sallama, direct part din ummey ya nufa , be wani jima a ciki ba sabida be saba zama ba yana gaisheta ya fito daga part din tare da nufar part dinsa.



🫧🫧🫧🫧🫧


YOLA 

“Aikin ku na kan gangara, baku da dogon lokaci wajan cikar ragowar burinku, watanni biyu ne sukai muku saura ku tabbata kun kawo jininsa,karkuyi saken da Jini biyu zasu hadu waje daya, kuna gab da tafka babban kuskure musamman idan Jini biyun nan suka kasance a waje daya “, a fusace take musu magana cikin bacin rai kafin ta dora “kun tabka babban kuskure kuyi kaggawar gyara abinda kuke kokarin batawa, baku da dogon lokaci kamar yadda kuka kawar da dan uwansa, shima ya zama muku dole Inba haka ba za kuyi kuka da kanku”tana kammala zan centa ta bace bat kamar bata taba wanzuwa ba. Ba Wanda bai razana da maganganun ta ba duk da kasancewar fuskokinsu a rufe yake babu alamar da za a gane mu su wanene, wani mutumine ya soma magana “tabbas yanxu ne ya kamata mu fara aiwatar da shirin mu, duniya ta muce dole mu mulki mutanan duniyar, dukiyar NAHYAN mallakinmuce dole mu karar da tsantsan su”……


Comment and share 

Mss Lee 💖💖

Masu comment ina Godiya…..


‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA


💖💖GIDAN AUNTY 💖💖

  ( a heart touching love story )


Story & written 

      By 

Mss Lee 💖

No comments